Ayi min adalci Hausa Novel Complete
AYI MIN ADALCI
*Story and writing*
Hussein Yusuf
_Bismillahir rahamanir rahim_
*Page 1&2*
__”You’re under arrest” ita ce kalmar da ta fito daga bakin wani É—an’sanda, yayin da yake nunawa wani kyakkyawan matashi ankwa. Tsaye matashin saurayin yayi da mamaki a fuskarsa ya kalli É—an’sandan ya ce “YallaÉ“ai me na yi kuma zaku zo ku kama ni?”
“Ok! Kai ba ka san ma laifin da ka aikata ba ko?” mamaki ne ya Æ™ara rufe matashin ya dubi É—an’sandan ya ce “Wallahi yallaÉ“ai ban san me na aikata ba, ya kamata ka saurare ni…..”
Kallon wajen Æ™ofa É—an’sandan yayi da Æ™arfi ya Æ™wala kira “Sajan ku shigo ku kama shi” nan take kuwa wasu Æ´an’sandan wajen su biyar suka shigo cikin gidan, da Æ™arfin tsiya suka tusa Æ™eyar matashin suka tafi da shi.
Sai faman tambayarsu yake yi akan me za su kama shi, bayan bai san laifin da ya aikata ba. Kallon wani É—an’sanda yayi wanda yake tsaye a waje É—aya ya ce “Don Allah yallaÉ“ai ku daure ku faÉ—a min laifin da na yi muku.”
HaÉ—e fuska É—an’sandan yayi, ya dubi matashin kafin ya daka masa tsawa “Ko ba kaine FAISAL ba?” Da sauri kuwa ya ce “Ni ne yallaÉ“ai” b’ata rai É—an’sandan ya sake yi kafin ya dubi Faisal ya ce “Muna zarginka da kashe uban gidanka Alhaji Hashim mai Dala.”
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un” shine abin da ya fara fitowa daga bakin Faisal, duban É—an’sandan yayi ya ce “Wallahi yallaÉ“ai ni ban san ma ya mutu ba sai yanzu da na ji daga bakink…..”
“Rufe mini baki, munafukin banza da wofi.” ÆŠan’sandan ya faÉ—a a fusace yana kallon Faisal da har ya fara zubar da hawaye a kan kyakkyawar fuskarsa idanunsa sun kaÉ—a sun yi ja wur kamar gauta.
“To idan ba kaine ka kashe Alhaji Hashim ba wanene? Domin matarsa ta shaida mana kai ne mutum na Æ™arshe da yayi magana da shi.” Kuka Faisal ya fashe da shi “Allah sarki Alhaji mutumin kirki Allah ya ji Æ™anka yayi maka rahama ya gafarta maka zunubanka.”
Shine abin da Faisal ya rinÆ™a faÉ—a. Wanda hakan ba Æ™aramin fusata Æ´an’sandan yayi ba, wani kurtun É—an’sanda ne ya dube shi ya kifa masa wani irin mari, saboda Æ™arfin marin har taurarin wuya sai da Faisal ya gani a cikin idanunsa.
Danshi Faisal ya ji a bakinsa, da sauri ya kai hannunsa bakin nasa aikuwa sai ya shafo jini, kuka ya saka yana ce wa “Wallahi ba ni ne na kashe Alhaji ba sharri ne aka yi min.”
Babu wanda ya saurare shi a cikinsu, sai ma kama shi da suka yi suka É—aga shi sama suka wurga shi cikin motar tasu. Kamar yadda ake wurga jaki a cikin mota idan za’a kai su kudancin Najeriya a siyar. Faisal kuwa ji yayi kamar Æ™ashin bayansa zai karye, saboda buguwar da yayi.
Nan take kuwa suka tayar da motar suka nufi division É—insu da shi. Nan take kuwa mutanen da abun ya faru a gaban idonsu, suka hau yin kace-nace akan zancen. Wasu gani suke yi Faisal ne ya kashe uban gidansa, yayin da wasu kuma suke ganin Faisal ba zai taÉ“a iya aikata kisan kai ba. Sai dai masu iya magana sun ce “MUGU BA SHI DA KAMA.”
_ _ _ _ *********_ _ _ _
A zaune take tana akan kujera Æ´ar tsugunne tana tankaÉ—e garin da zata yi musu tuwo da rana. A guje wani matashin saurayi ya shigo cikin gidan, yana zuwa ya zube a gaban dattijuwar matar yana mayar da numfashin gudun da ya sha.
Dakatawa ta yi da tankaÉ—en garin ta kalle shi kafin ta ce “Habibu lafiya kuwa na ganka a irin wannan yanayin?” Sai da ya ajiye ajiyar zuciya sannan ya dubi matar ya ce “Goggo yanzun nan Æ´an’sanda suka tafi da Faisal wai ana zargin shi da kashe uban gidansa Alhaji Hashim.”
Tafa hannuwa Goggo ta shiga yi tana salallami “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Kai yanzu Habibu a bakin wanne maÆ™aryacin ka jiyo wannan maganar?”
Ka da baki matashin yayi ya ce “Goggo a gabana fa suka tafi da shi, motarsu tana tafiya ni kuma ina Æ™arasowa wajen. Shine jama’ar wajen suka shaida mini abin da yake faruwa.”
Da sauri Goggo ta miÆ™e tsaye ta shiga cikin É—akinta, ba jimawa ta fito da hijabi a hannunta. Duban Habibu ta yi ta ce “Yi sauri ka zo mu tafi can police station É—in mu ji abin da yake faruwa a wajen Faisal É—in.”
Ganin yadda Goggo duk ta bi ta gigice ne ya saka Habibu tashi da sauri ya wuce gaba Goggo kuwa da sauri ta bi shi a baya. Suna fitowa daga gidan, Goggo ta shiga gidan wata maÆ™ofciyarsu mai suna Ladi ta ce “Idan Anwar ya dawo daga makaranta ya shigo nan gidan kafin su dawo.”
Bata tsaya jin abin da Ladin take faÉ—a ba, ta juya da sauri ta fice daga gidan. Tana fitowa ta tarar da Habibu yana jiranta, bakin titi suka nufa. Suna zuwa kuwa suka tare wani keke napep suka hau, suka nufi can police station É—in.
********* *********
Dukan shi suke yi kamar Allah ya aiko su, kusan kowacce gaÉ“a ta jikinsa sai da suka dake ta da wani É—an Æ™aramin sanda mai Æ™warin gaske. Amma duk dukan nan da Faisal yake sha a wajen Æ´an’sandan nan, kalma É—aya ce take fitowa daga bakinsa ba ni bane…..
Gaba É—aya jikinsa duk ya É“aci da jini babu kyawun gani. Sai numfashi yake fitarwa sama-sama, yana wani irin nishi kamar ransa zai rabu da gangar jikinsa. Amma saboda rashin imani irin na Æ´an’sandan nan sun Æ™i su rabu da shi, a lallai a dole sai ya amsa laifinsa, shi kuma ya dage akan ba zai taÉ“a amsa laifin da ba shine ya aikata ba.
Ganin ya galaÉ“aita sosai ne yasa suka rabu da shi. Wani kallo É—aya daga cikinsu ya watsa masa ya ce “Kai wai dole mai taurin kai ko? To ka sani Wallahi idan muka dawo ba ka bamu amsa ba, sai mun yi maka horon da ya fi wannan wahala, sakarai kawai banza!” Suna gama faÉ—in haka suka fice suka bar shi a cikin wani irin yanayi.
^^^^^^^^^^^^^
Hajiya Bilkisu ce a zaune a ofishin D.P.O fuskarta a murtuÆ™e kamar fuskar shanu. Kallo É—aya za ka yi mata ka gano tsantsar É“acin rai a tattare da ita, kallon D.P.O ta yi ta ce “Gaskiya ni na gaji me yasa kuke ce wa wai lallai sai ya amsa laifinsa? Bayan akan idanuna ya caka wa mijina wuÆ™a nima yayi yinÆ™urin kashe ni Allah yasa da sauran kwana na a gaba, da tuni nima an binne ni.”
“Kiyi haÆ™uri Hajiya yana amsa laifinsa sai mu rubuta muku R.F.I mu tura shi kotu a yanke masa hukunci a can.” Dakata D.P.O Hajiya Bilkisu ta faÉ—a ranta a É“ace ta kalli D.P.O ta fara magana “Gaskiya D.P.O idan har ba za ku iya Æ™watar min haƙƙina ba zan je gaba inda za’a Æ™watar min. Komai sai ku ce wai sai ya amsa laifinsa bayan dumu-dumu na kama shi da wuÆ™a a hannu yayin da ya gama kashe shi, nima yayo kaina Allah yasa da sauran kwana na a gaba.”
“Hajiya kiyi haÆ™uri insha Allahu za mu yi miki yadda kike so.” Shiru yayi sannan ya cigaba da ce wa “Amma Hajiya na ji kin ce kin ritsa shi da wuÆ™a a hannu lokacin da ya kashe Alhaji, Amma me yasa da muka je ba mu ga wuÆ™ar ba?”
Gyara zama Hajiya Bilkisu ta yi ta ce “WataÆ™ila ku ne ba ku kula ba, amma tabbas wuÆ™ar tana ajiye a falonsa. Ni tun da aka fito da shi ma aka kai shi asibiti na kulle falon ban Æ™ara shiga ba.” Da sauri D.P.O ya ce “Yanzu Hajiya kin tabbatar idan muka je zamu samu wuÆ™ar a can?”
“Of course yallaÉ“ai. Na tabbata idan kun je zaku ga wuÆ™ar indai ba’a É—auke ta ba.”
“Ok kina nufin akwai wanda zai iya zuwa ya É—auke ta kafin mu je?” D.P.O ya tambaya yana kallon Hajiya Bilkisu.
Yatsina fuska ta yi sannan ta ce “Ni gaskiya babu wanda na ke zargin zai É—auke ta amma ka san shi Faisal É—in wataÆ™ila yana da wasu yaran a can waje É—aya, ba mamaki su iya É—auke ta kafin ku je”
Da sauri D.P.O ya ce “Calm down Hajiya. Insha Allahu za mu gan ta ma.”
Wayarsa ya É—auko ya kira wani É—an’sanda ya ce “Ya zo yanzu ya same shi a office yanzu.” Ba’ a É—auki wasu minutes masu yawa ba sai ga wani É—an’sanda ya shigo. ÆŠaga Æ™afa yayi ya sarawa D.P.O ya ce “Ga ni yallaÉ“ai.”
Kallon shi D.P.O yayi ya ce “Inspector yanzun nan zaka bi HAJIYA gidanta, domin ta nuna maka É—akin da aka kashe Alhaji ka duba sosai ta ce wuÆ™ar da aka aikata kisan tana cikin falon don haka yanzun nan sai ka bita. Amma fa ka tabbatar ka duba sosai, domin indai aka ga wuÆ™ar to komai zai zo mana da sauÆ™i” sake sarawa É—an’sandan yayi ya ce “Ok sir.”
Kallon Hajiya Bilkisu D.P.O yayi ya ce “Hajiya zaku iya tafiya.”
MiÆ™ewa tsaye ta yi ta kalli D.P.O ta ce “Shikenan yallaÉ“ai bari na je mu duba”
“Ok Hajiya Allah yasa mu dace.”
Har ta juya za ta tafi sai kuma ta dakata ta kalli D.P.O ta ce “Amma yallaÉ“ai yaushe zaku ba ni mijina domin ayi masa jana’iza kamar yadda ake yi wa kowanne mamaci.?”
Shafa kai D.P.O yayi ya ce “Yanzu Hajiya muna sauraron abin da likita zai faÉ—a mana ne, da zarar sun gama binciken su akan gawar insha Allah zuwa gobe zamu ba ku shi domin ayi masa sutura.”
“Shikenan to yallaÉ“ai bari mu je” buÉ—e kyauren office É—in ta yi ta fice nan take kuwa Inspector ya bi bayanta domin ya je gidanta ya É—auko wuÆ™ar da aka kashe Alhaji da ita.
*:::::::::::::::::*
A firgice Goggo ta shigo cikin station É—in fuskarta taf da hawaye. Kallo É—aya zaka yi mata ka hango tsantsar É“acin rai da damuwa a fuskarta. Wani É—an’sanda ne da yake kan kanta, ya kalleta ya ce “Iya lafiya kika shigo mana a haka?”
Ka da baki Goggo ta yi ta ce “Ina lafiya yallaÉ“ai kun kama min É—ana kun kulle, wallahi yallaÉ“ai Faisal ba shine ya kashe Alhaji Hashimu ba sharri ne aka yi masa.”
“Dakata tsohuwa kar ki yi mana zancen banza anan wajen, dumu-dumu a kama mutum kuma ki zo kina ce wa “Wai ba shine ya kashe shi ba? To idan ba shi bane sai ki fada min wanene.”
“Tabbas gaskiya Goggo ta faÉ—a muku ba Faisal bane ya aikata wannan kisan kan ba. Saboda mu nan shaida ne FAISAL mutumin kirki ne, kuma mai tsoron Allah a duk inda ya tsinci kansa.”
Hararar shi É—an’sandan yayi ya ce “Kai kuma wanene da zaka zo kana yi mana zancen banza anan?”
“Ni sunana Habibu kuma tare nake da Goggo, mun zo ne domin mu yi magana da Faisal.”
Wani murmushi É—an’sandan yayi ya ce “Ko kun manta laifin da ya aikata ne? To babu wanda ya isa ya gan shi, don haka ku juya ku fice daga nan kafin ranku ya É“aci.”
Wata zazzaÆ™ar murya ce ta zo ta daki dodon kunnuwansu “Wacce doka ce ta hana a bar mutum ya ga É—an’uwansa akan ana zargin shi da wani laifi?”
Gaba É—ayansu suka waiwaya bayansu domin su ga mai yin wannan maganar É—an’sandan nan ne ya fusata ya dubi kyakkyawar budurwar cikin É—aga murya ya ce “Ke kuma wacece da zaki zo kina wata magana?”
Zura hannu ta yi a cikin jakarta ta É—auko wani I.D card ta ajiye akan kantar sannan ta ce “Sunana BARRISTER SHAHEEDAH (Littafin AYUSH ABDULLAH)…………”
_*To be continue……*_
_More comment more typing_
Ina son na ga ruwan comment domin shine ƙarfin gwiwar kowanne marubuci, don haka ku nuna min yadda littafin ya karɓu a wajenku ta hanyar comment nagode.
_*HUSSAIN*_
07069475482
Ayi MIN ADALCI
*Story and writing*
Hussein Yusuf
_Bismillahir rahamanir rahim_
*Page 3&4*
Kallonta É—an’sandan yayi ya ce “Sorry Madam ban san ke ba ce shi yasa….”
“Dakata Malam wallahi kai dai ba ka san aikinka ba, wulaÆ™anci da rashin mutunci ba shine zai saka ka cigaba a aiki ba. Wannan shawara ce na baka saboda gaba…”
Kallon su Goggo ta yi ta ce “Kuyi haÆ™uri Goggo insha Allahu yanzun nan za ku gan shi kuma ina mai tabbatar muku da cewa zai fita daga wannan sharrin da aka yi masa.”
Da sauri Goggo ta ce “Allah yasa yarinya mun gode sosai.”
Sake kallon É—an’sandan Barrister Shaheedah ta yi ta ce “D.P.O yana ciki?”
Da sauri ya ɗaga mata kai kamar ƙadangare, duk kunya ta bi ta kama shi kamar ya nutse a wajen haka yake ji.
Sake tambayarsa ta yi nan ma da sauri ya ce “E, Madam yana ciki.”
Murmushi Shaheedah ta yi sannan ta dubi su Goggo da Habibu ta ce “Su biyo ta a baya” da sauri kuwa suka bi bayanta.
Suna isa ƙofar office ɗin Barrister Shaheedah ta kama handle ɗin ƙofar za ta buɗe kafin ta murɗa ƙofar ta ga an buɗe. Hajiya Bilkisu ce ta fito, kallon-kallo aka shiga yi tsakaninta da Barrister Shaheedah.
“Mtssssss!” Hajiya Bilkisu ta ja wani dogon tsaki sannan ta dubi *Barrister Shaheedah* ta ce “Ke nan yarinya da ke zaki É—ebo wasu shegun Æ™afafunki, ki taho wai ke lauya za ki kare wani banza ko?” To bari ki ji “Wallahi summa tallahi ko ke ce shugabar lauyoyin duniyar nan ba ki isa ki fitar da Faisal daga tarkona ba. Sannan ina Æ™ara tabbatar miki a gaban idonki za’a yankewa Faisal hukunci dai-dai da abin da ya aikata.”
Sannan ta mayar da kallonta wajen Goggo ta ce “Ke kuma tsofai-tsofai da ke zaki wani taho ganin wani banza wanda a banza ku ka gan shi, wai ku masu tausayi ku ka dauke shi a matsayin É—a ko? To bari in tabbatar miki wallahi TSINTACCIYAR MAGE BATA MAGE tun wuri ina baki shawara da ki rabu da Faisal, É—ansa ma da yake hannunki ki je can wani wajen ki jefar da shi kafin wani ya sam…..”
“Ke dalla rufe mana baki shashasha kawai” da sauri Barrister Shaheedah ta ce “Me yasa ka tanka mata? Ai da ka bari ta Æ™arasa faÉ—in abin da yake bakinta. Ka san idan kare yana haushi duk wanda ya kula shi akansa yake hucewa don haka ni ban ga abin tsayawa ina cacar baki da wannan abun ba mtssssss!” Ta ja wani tsaki tare da tsartar da miyau da sauri ta buÉ—e Æ™yauren Æ™ofar ta shiga da sauri kuwa Goggo ta bi bayanta sai da Habibu ya watsa mata wani banzan kallo sannan shi ma yayi shigewarsa ciki.
A tsaye suka shiga suka bar Hajiya Bilkisu tana ta faman cizon leɓenta. Tun da take a duniyar nan babu wani mahaluƙi da ya taɓa yi mata kwatankwacin wannan wulakancin da Barrister Shaheedah ta yi mata.
“Gaskiya ya zamar mini dole na dakatar da wannan yarinyar da shiga abin da babu ruwanta. Idan har na yi sake wallahi wannan Æ™aramar za ta watsa mini shiri na, kuma ta tona min asiri a idon duniya.”
“Don haka ya zamo min dole na fara sanin wacece ita waccan yarinyar kafin na san abin da zan aiwatar akan ta.”
Tana gama wannan tunanin ta saki wani shu’umin murmushi sannan ta yi gaba.
A jikin motarta ta tarar da Inspector yana jiranta. Murmushi ta yi ta ce “Ka yi haÆ™uri Inspector na bar ka a tsaye ko?”
Shi ma murmushin yayi ya ce “Babu komai Hajiya tun da kin Æ™araso kawai mu tafi.”
Da sauri direbanta ya zo ya buÉ—e mata gidan baya ta shiga, yayin da shi kuma Inspector ya shiga gaban motar kusa da direba kujerar me zaman banza ya zauna.
Da gudu direban ya ja motar suka bar harabar Police station É—in.
********* **********
Yayin da Barrister Shaheedah ta shiga ofishin D.P.O tare da su Goggo da Habibu. Kallonsu D.P.O yayi kawai ya kawar da kansa, ya cigaba da abin da yake yi.
Ko kaÉ—an Barrister Shaheedah ba ta damu ba, sallama ta yi masa É—agowa yayi daga duba files É—in da yake yi ya amsa mata sallamar sannan ta tsaya yana sauraron ya ji abin da yake tafe da su.
I.D card Barrister Shaheedah ta É—auko ta nunawa D.P.O sannan ta ce “Sunana Barrister Shaheedah ni ce lauyar Faisal wanda kuke tuhuma da laifin kisan kai.”
Murmushi D.P.O din yayi kafin ya ce “Ok na gani, ku zauna mana” gaba É—ayansu suka samu waje suka zauna.
Bayan sun zauna gaba É—ayansu sai D.P.O ya kalli Barrister Shaheedah ya ce “Na ji kin gabatar min da kanki sai dai ban ji kin ce komai akan waÉ—annan da kike tare da su ba.”
Murmushi Barrister Shaheedah ta saki ta ce “Sorry sir wallahi na sha’afa ne” sannan ta nuna Goggo ta ce “Wannan ita ce wacce take riÆ™e da Faisal, domin ba ita ce ta haife shi ba. Mamaki ne ya kama Goggo nan take ta hau tambayar kanta “Wai wannan yarinyar a ina ta san mu har ta san Faisal ba É—ana ba ne? Kuma shi Faisal É—in bai taÉ“a yi min zancenta ba, amma dai ko wace ita da sannu zan sani insha Allahu” tunaninta ne ya yanke yayin da ta ji Barrister Shaheedah ta na gabatar da Habibu.
“Wannan kuma” ta nuna Habibu “ÆŠan wannan dattijuwar matar ne, tare suke da Faisal abokai ne sosai. Sun zo ganin Faisal ne da yake wajenku.”
Mamaki ne ya ƙara kama su Goggo suna mamakin inda Barrister Shaheedah ta san su haka alhalin su ba su taɓa ganin ta ba ma ballantana su shaida ta.
D.P.O ne yayi gyaran murya ya ce “Ok na fahimta, yanzu dai a iya yau zan iya ba su minti goma sha biyar su gan shi. Ke kuma zan iya baki 30 minute.”
Da sauri Barrister Shaheedah ta ce “Mun gode yallaÉ“ai.”
Cigaba D.P.O yayi da cewa “Amma fa ki faÉ—a musu daga yau baza su sake ganin shi ba sai abin da hali yayi, sai dai ke tun da lauya ce always zaki iya ganinsa domin ki yi aikinki yadda ya kamata.”
Fashewa da kuka Goggo ta yi cikin muryar kukan ta dubi D.P.O ta ce “YallaÉ“ai me yasa ba za ku sake barinmu mu gan shi ba?”
Cikin kwantar da murya D.P.O ya ce “Saboda yanzu nan ba da daÉ—ewa ba case É—insa zai bar hannunmu, za mu miÆ™a shi kotu idan muka tabbatar da laifinsa da fatan kin gane?”
ÆŠaga kai kawai Goggo ta yi ba don ta gamsu da bayanin D.P.O ba.
ÆŠaga murya D.P.O yayi ya kira wani É—an’sanda, da hanzarinsa kuwa ya shigo ya sara sannan ya ce “Ga ni na ji kana kirana.”
Je ka da waÉ—annan mutanen za su yi magana da wannan criminal É—in na cikin cell, sake sarawa yayi ya ce “Ok sir an gama.” Kallon su Goggo yayi ya ce “Ku tashi mu tafi.”
Bayan shi suka bi har suka je wani waje mai bala’in duhu amma daga waje akwai É—an hasken rana da ya ratso ciki ta wata Æ´ar Æ™aramar Æ™ofa. Amma cikin É—akin da Faisal yake, ko tafin hannu ba a gani saboda tsananin duhu.
Kallon su Goggo É—an’sandan yayi ya ce “Ku zauna anan” ya nuna musu wani benci mai kyau a ajiye ba tare da gardamar komai ba kuwa suka zauna. Suna kallo ya É—auko wayarsa daga cikin aljihu ya kunna fitila sannan ya haska ya shiga cikin É—akin.
A kwance ya ke, ya yi ruf da ciki ya rufe idanunsa, hawaye ne yake ta faman yawo akan kyakkyawar fuskarsa. Motsin mutum ya ji da alamun shigowa É—akin aka yi, haske ya hango da alamun hasken fitila ne a hankali ya ga hasken yana nufo inda yake da sauri ya tashi zaune yana ihu! yana cewa “Don Allah ku yi haÆ™uri ku yi mini rai wallahi ba ni ne na aikata kisan ba sharri aka yi min.”
Tsayawa É—an’sandan yayi tare da haske shi da tocilan É—in wayarsa. Cikin É—aga murya ya ce “Kai rufe mana baki” shiru Faisal yayi yana sauraron abin da É—an’sandan zai yi masa.
Sake haske shi É—an’sandan yayi ya ce “Taso ka biyo ni a baya” yana faÉ—a masa haka ya juya ya nufi Æ™ofar fita. Da sauri kuwa Faisal ya tashi ya bi bayansa, da kyar yake iya É—aga Æ™afarsa da ta yi masa wani irin nauyi ji yake kamar ya faÉ—i amma a haka yake daurewa yana bin bayan É—an’sandan.
A haka har É—an’sandan ya fito daga cikin É—akin, tsayawa yayi a Æ™ofa yana jiran Faisal É—in ya Æ™araso.
Su Goggo kuwa duk sun zubawa ƙofar idanu, domin su ga FAISAL ɗin ya fito, a hankali suka ga ya fito yana taka ƙafarsa da ƙyar.
Da gudu Goggo ta je ta rungume shi tana kuka shi ma kukan ya saki, Habibu kuwa shi ma tsaye yayi yana kallonsu yana share ƙwallar da take taruwar masa a cikin idonsa.
“Kaiii! Minti goma sha biyar ne kwata-kwata da ku don haka ku yi sauri ku gama abin da ya kawo ku…”
Da sauri Goggo ta saki Faisal tana kallonsa yadda duk ya bi ya rame cikin ƙanƙanin lokaci, tausayinsa ne ya cika mata zuciya, kuka ta cigaba da yi Habibu kuwa kasa rarrashinta yayi saboda ya san kukan ne kadai zai iya rage mata raɗaɗin da zuciyarta take yi mata.
Ganin kukan ya Æ™i Æ™arewa ne Habibu ya dubi Faisal ya ce, “Faisal garin ya haka ya faru? Kawai muka ga Æ´an’sanda sun É—auke ka akan wai kai ne ka kashe Alhaji Hashim, ya gaskiyar maganar take?”
Fashewa da kuka Faisal yayi ya ce, “Habibu tun da nake a rayuwata zuciyata ba ta taÉ“a saÆ™a min wani mugun abu game da wani mutum ba. Ballantana har ta kai ga zuga ni akan na aikata kisan kai, Wallahi ban san wanda ya kashe Alhaji ba kawai sai na ga Æ´an’sanda sun zo sun kama ni wai ana zargina da kashe Alhaji.”
Shiru yayi yana ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa, “Wallahi Goggo ko da ni makashi ne Alhaji ba ya cikin waÉ—anda zan kashe, domin na tsani maci amana da mayauari a rayuwata, amma yau sai ga shi lokaci É—aya rayuwa ta canja min ni ake kallo a matsayin maci amana mayaudari, ya zan yi Goggo da Habibu ku taimaka min don Allah mutane su daina kallona a haka.” Yana kai wa nan a zancensa sai ya sake rushewa da wani sabon kukan, Goggo ma kuwa ita ma sai ta sake rushewa da kuka, Habibu ma duk dauriyar da yake yi sai da suka karyar mai da zuciya nan take shi ma ya fara kukan.
“Ka yi haÆ™uri Faisal dukkan tsanani yana tare da sauÆ™i, kamar yadda dukkan duhu yake tare da haske. Ka sani Allah ne ya tsara maka haka a cikin littafin kundin Æ™addararka idan ka yi haÆ™uri ka fawwalawa Allah komai Insha Allahu da sannu komai zai warware.”
Habibu ne yake fada yayin da yake share ƙwallar da take ta faman zubo masa.
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
-
Kyawuna Jarabta ta
-
Jiddatul khair
-
Wacece Ni Hausa Novel
-
Ahali Daya Hausa Novel
-
Abraham Hausa Novel
“Nagode Habibu, insha Allahu zan zamo mai yin haÆ™uri a duk halin da na tsinci kain…..” Bai Æ™arasa faÉ—a ba kuka ya ci Æ™arfinsa shiru suka yi gaba É—aya suna sauraron sautin kukansa Goggo kuwa zuwa wannan lokacin zuciyarta ta bushe kukan ma ya Æ™i zuwa ballantana ta yi ta ji sauÆ™i a cikin ranta.
Sai da Faisal yayi kuka sosai sannan yayi shiru yana ajiyar zuciya. Duban shi Goggo ta yi ta ce, “Faisal kalmar dai da Habibu ya faÉ—a maka ni ma ita zan Æ™ara jaddada maka. Ka kasance mai haÆ™uri kuma ina son ka saka a cikin ranka cewa babu wanda ya isa yayi maka abun da Allah bai tsara maka a cikin littafin rayuwarka ba. Ka saka a ranka cewa duk abin da ya same ka dama can ya kasance zai same ka, haka kuma duk abin da ba ka samu ba dama can ba rabonka bane. Sannan ko da duk mutanen duniyar nan za su taru akan su cutar da kai ba za su taÉ“a samun nasara akan ka ba, matuÆ™ar Allah bai tsara za su cutar da kai ba, haka kuma ko da dukkan mutanen duniyar nan za su haÉ—u akan su cire ka daga wannan Æ™addarar da ta afko maka matuÆ™ar Allah bai tsara maka haka a cikin kundin Æ™addarar ka ba, ba su isa su fitar da kai ba.”
“Wannan faÉ—in Annabinmu Muhammad (S.A.W) ne, don haka Faisal ka rinÆ™a yawan addu’a kana neman yawan ambaton Allah kar ka manta da wannan Faisal insha Allahu zaka fita daga wannan wahal…..”
Tana kai wa nan kuka ya Æ™wace mata É—an’sandan da yake kula da su ne yayi gyaran murya ya ce, “Lokacinku ya cika don haka ku tashi mu tafi” kallonshi Goggo ta yi ta ce, “Don Allah ka yi mana haÆ™uri ka ji.”
Tausayin Goggo ne ya kama shi jikinsa yayi sanyi cikin sanyin murya ya dubi Goggo ya ce, “Iya ki yi haÆ™uri lokacin da D.P.O ya É—eba muku kenan, nima umarni aka ba ni idan lokacin ya cika na sallame ku.”
“Shike nan yallaÉ“ai mun gode Allah ya saka da alkhairi da kuka bar mu, muka gan shi ma.”
Tashi suka yi za su tafi sai a wannan lokacin Faisal ya ji wani kuka ya zo masa, babu shiri kuwa ya shiga yin abinsa. Cikin muryar kuka ya dubi Goggo ya ce “Don Allah Goggo ki kula min da Ammar, ki ba shi kulawa sosai. Sannan duk lokacin da ya tambaye ki inda na tafi ki ce masa na kusa dawowa.”
Yana gama faÉ—in haka É—an’sandan bai bar shi ya ji amsar da Goggo za ta ba shi ba, ya ja shi ya mayar da shi cikin É—akin duhun nan da yake shi kaÉ—ai a ciki.
Fashewa da kuka Goggo ta yi wata sabuwar soyayya da tausayin Faisal ne yake Æ™ara yin yabanya a cikin zuciyarta…..
Bayan É—an’sandan ya rufe Faisal sai ya juyo ya nufi hanyar fita, tare da yi wa su Goggo alama su biyo shi. Bin shi suka yi a baya har suka isa ofishin D.P.O.
Sarawa É—an’sandan yayi ya ce, “Sir sun gama tattaunawa” kallon su Goggo D.P.O yayi ya ce, “Ok za ku iya tafiya.”
“To yallaÉ“ai mun gode” Goggo ta faÉ—a tana É—an rusunawa D.P.O kallonta ya sake yi ya ce, “Babu matsala ku je kawai.”
Kallon Barrister Shaheedah Goggo ta yi ta ce, “Ranki ya daÉ—e ko mu jira ki ne?”
Murmushi Barrister Shaheedah ta yi ta ce, “No Goggo ku yi tafiyarku kawai don ni daga nan ma ba gida zan nufa ba, akwai wata mata da ta kira ni na je na bata shawara wai akan mijinta zai Æ™ara aure. So don haka kawai ku yi tafiyarku.”
Godiya suka ƙara yi mata sannan suka juya suka tafi.
Bayan fitar su Goggo D.P.O ya kalli Barrister Shaheedah ya ce, “Barrister za ki iya zuwa wancan ofishin ki jira sai a kawo miki shi Faisal É—in amma fa ki sani mintuna 30 kaÉ—ai ki ke da shi.”
Godiya Barrister Shaheedah ta yi wa D.P.O sannan ta miÆ™e ta nufi cikin office É—in da D.P.O ya nuna mata domin ta jira a kawo mata Faisal ta fara aikinta…………….
_To be continue….._
Typing da wahala ku dai ku rinka yi min comment domin shine karfin gwiwata…
_*HUSSAIN*_
07069475482