Hausa Novels

Babban Sirri Hausa Novel

Babban Sirri Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*1*

Tafe tak’e kan hanya sai sauri tak’e saboda Abbanta yanata gargaɗ’inta datayi sauri k’arta daɗ’e dan yanzu akeson maganin tana shan k’wanar dazata k’aita gida suka haɗ’u da Auwal tace gaskiya Auwalu karka tsaidani Abbana nacan yana jirana zaibawa ummina magani ta faɗ’a tana nuna mai maganin data siyo,Auwal yace “haba tawan k’ibari mana mu gaisa saik’i tafi k’wana biyu bana ganin ki duk na damu,tace nidai gaskiya tafiya zanyi ta murguɗ’a mai bak’i dan gaskiya ya fara tak’ura mata, ganin yaki bata hanya ga lokaci sai wucewa yak’e saita ruga da gudu.

 

Ta barshi da cizon yat’sa, Auwal k’enan yana bala’in sonta amma sai rashin kunya take mai,tun daga zaure take kwaɗ’a sallama k’amar wata mak’auniya harta k’aiga inda Abbanta ke tankaɗ’an garin tu

uwon da zaiyi musu,aikuwa saida yayi mata faɗ’an yakarɓ’i maganin yace ta k’arasa tankaɗen.

 

Wajan karfe 4:30pm Abba ya shiga gidan tare da sallama *Falaq* da ummi dake ɗ’aki suka amsa mai ya k’arasa ciki yana ganin Falaq babu ɗ’ankwali yasa hannu aljihu yaciro #50 “ungo k’ije gidan lauren nalami mai k’it’so tayi miki’,kallan Abban nata ta shiga yi dan a rayuwa ta tsani k’it’so bataso taga ana taɓa mata kai indai ba……za’a cire mata ba.

 

Saida Ummi ta sak’e magana sannan ta karɓ’a tanata kuka ta fita daga gidan.

 

Tana tafiya tana masifa kamar zararriya sai jan gefe da gefen karshen mayafinta take wanda yayi dauɗ’a kamar daga bak’ar k’asa aka t’samoshi,tana shan k’wanar dazata k’aita gidan lauren nalami ta t’saya jikin wani gida mai bala’in k’yau duk garin babu gidan daya kaishi k’yau da tsaruwa, dai dai wata window irin me gless ɗ’innan ta t’saya tana k’arewa k’anta k’allo dama ka idarta ce indai zata biyo hanyar saita k”alli madubin nan,zahirin gaskiya ita kanta *Falaq* tasan tayi dauɗ’a tundaga fuskarta, k’ayan jikinta sunsha ɗ’inkin hannu k”anta kuwa sai a slow gashin nan yayi wata kala k’wark’wata kuwa kamar ita take siyarwa dan har bin jikinta take k”afarta kuwa duk ta fashe tayi futu futu data.

 

Tana gama ganin k’anta a madubi ,ta wuce ta tafi gidan lauren nalami har addu’a take Allah yasa bata nan kota ce baz’ata samu dama ba,tun kafin tashiga zauren take rafk’a sallama harta k’arasa ciki laure na talgen tuwo Falaq na k’arasawa tace “laure zan samu k’it’so yanzu”? Da sauri laure tace Falaq mezai hana zaki samu mana,Falaq ta turo bak’i tace “kai laure aiki fa kike tayaya zakimin”?

 

 

Laure tace duk zan iyayi ina miki ina kula da aikin harmu gama,laure itake rufawa k’anta asiri dan Nalami babu abinda yake damun shi da ita sai dare.

 

Laure ta fito da kujera, comb da k’ifiya tacewa Falaq toho,haka Falaq ta zauna badan ranta yaso ba,ita kuwa laure kuɗin take so shiyasa zatayi mata haka akayi k’it’son babu wanke kan anayi ana tsintar k’wark’wata, a rayuwar falaq tana so taga ana ciro mata k’wark’wata tana k’ashewa kasss babu wanda yake k’yank’yami cikin su har aka gama sannan Falaq ta wuce gida.

 

Tana komawa gida abban ta ya gama tuwo da miyar k’ark’ashi,taje ta nunamai aikuwa yaji daɗ’i dan haka ya ringa shafawa yana yabawa kannata, taje ta nunawa umminta dake ɗ’aki a kwance tana fama da shanyewar ɓ’arin jiki,itama ta yaba saidai tayi mata faɗ’an rashin wank’ewar da batayiba,ashe rashin k’itson ba karamin rufawa Falaq asiri k’wark’watar tayi ba dan saida akayi suketa yawo a jikinta (lol).

 

Abba na shiga toilet ta arce gidan su uwani ta tafi k’awarta ce k’anwar Auwalu saurayinta nan sukayita wasan su har wajan sallar isha’i sannan tace zata tafi”

 

Abban zaune kusa da ummi yana bata tuwo tashigo da gudu harta kusa ɓ’arar da miyar tanata dariya,Abba ne yace waike Falaq yaushene zaki girma?sannan wakika tono? sarkin tonen faɗa, yafaɗ”a yana k’allanta.

 

Saiidata gama zama k’usa da k’wanan tuwon sannan tace Abba idirisu ne wai dan nace idirisuwa na lami shine ya biyoni zai dokeni,tana faɗ’a tana t’saka lomar tuwo a bakinta dan dama a gidan su uwani bata ciba babu wanda yayi mata tayi,ummi dake kusa da ita tasa hannunta mai lafiyar ta doko Falaq tace bana hanaki wasa da maza ba wai meyasa bakida nutsuwa ne kodan kinganni kwance yasa kike irin waɗ”annan ɗ’abi’u to ki kiyayeni inba haka ba zan saɓa miki ummi ta karasa faɗ’a cikin zafin rai,shidai Abba ɓaice komai ba dan haka ya ɗ’eɓo tuwon yakai bakin ummi tace ta koshi dan har lokacin zuciyarta zafitake.

 

Abba ne yayi magana ganin Falaq ɗ’in kamar zatayi kuka dama kuma shine yake biye mata yana shagwaɓ’ata baya mata faɗ’a shiyasa batajin magana ko kaɗ’an saidai idan ummi ce,Abba yace wa ummi wai meyasa kikewa yarinyar nan haka? saikita mata faɗ’a batare da dalilaba to bana so kirabu da ita tayi abinda takeso kafin ace yau babu itah gaba ɗ’aya koni ko ke yana k’aiwa nan ya turawa Falaq ragowar tuwan yace ta cinye idan bata k’oshiba taje ta kara tace to tana k’allan ummi data haɗ’e fuska.

 

 

*2*

 

A daren dai Abba da Ummi ‘yar shariya akayi babu meyin magana,ita ummi tana hangowa Falaq rayuwarta ta gaba,su gashi ba kowan kowa ba,basu ajiyeba bakuma subawani ajiya ba amma Abba baya gani kullum burinshi Falaq baya mata faɗ’a baya kwaɓ’arta baya harararta sai kaɗ’an kaɗ’an wanda ba’a rasaba.

 

 

Washe gari Falaq ta tafi makarantar allo malam nura ya k’urota wai sati uku k’enan bata bada kuɗ’in laraba gashi ita k’aɗ’aice makarantar allo a garin ko boko babu, ta malam nuran ma bakowa ke zuwa ba,gida ta k’oma dama k’uma hak’an ta fiso shiyasa ko ajik’inta.

 

 

A kofar gida ta ga Abban ta, yana ganinta yace “meya faru tana makale da allon, ta bashi labari, yace to badai rashin k’unya k’ikayi maiba ko? Ta girgixa k’ai alamar ‘eh yace to shiga gida bari na naje na dawo “k’i k’ula da ummanki k’inji” tace to ta wuce ciki, shi kuma yafita dan zuwa karɓ’awa ummi rubutu.

 

 

Falaq ta k’arasa wajan ummi ɗ’inta tana mata sannu tare da tambayar ta ko da abinda tak’eso,babu k’omai ummi tace tana k’allan Falaq dake buɗ’e k’ofin furar da Abbanta ya siyo tace meya dawo dake k’uma a wannan lokacin Falaq tace ummi mallan ya k’oroni,cike da jimami ummi tace yanzu Falaq, “malam nura bazai bari sai wani watan a haɗ’a a bashi kuɗ’in shiba.

 

 

Falaq ta taɓ’e bak’i tare da cewa,wallahi ummi ko! Malam Nura bashida k’irk’i har wani cewa yak’e idan ya ganni a makaranta saiya k’aryani,ummi tayi murmushin yak’e sannan tace yanxu dai jeki ɗ’auki k’umbun ɗ’akin Abban ki k’ik’aiwa tayawale ta siya k’onawa ta baki k’ikarɓ’a,Falaq tace to tare da fita dan xuwa aiken da aka mata dama k’uma yawon take so.

 

 

Tana fitowa taje gidan tayawale,suna t’sak’ar gida a zaune suna cin tuwo tayi sallama, auwal yayi saurin tashi daga k’an k’wanon tuwon shi sabida budurwar shice yayi fuska k’amar badashi ake ci.

 

 

Bayan sun gaisa da yawale take sanar da ita ko xata sayi kumbo inji umminta,yawale ta kada baki tace ɗ’ari bak’wai idan zasu yadda,da sauri Falaq tace habba dai tayawale shine babban fa gsky yafi haka kiɗ’an k’ara,tayawale tace idan baki siyarba ɗ’auki abunki, taciga ba da cin tuwanta haushi yasa Falaq hararar yawale a gefen ido dan k’uwa babu wanda yagani.

 

 

Haka ta amshi ɗ’ari bakwai ɗ’in tafito Auwal ya biyota a baya,suna tafiya yana bata labarin yadda idan ya aureta zataji daɗ’i sai dashare baki take itakuma duk da yana takura mata.

 

 

A hanya suka haɗ’u da uwani nan fa suka dinga hauk’an su harda auwal ɗin dan shima babu arabi ba boko ne sai buga buga dayake yasamu na siyan riga.

 

 

Har gida auwal ya k’ai falaq sannan ya duba ummi da jiki ummi ta amsa da sauki,yaɗ’an daɗ’e sunata hira su ukun k’afin ya tashi zaitafi ya k’ashewa Falaq ido, caraf ummi takalli falaq dan ganin ita kuma mexatayi”sai taga tayi murmushi tana rufe ido da hannuwan ta.

 

 

Soyake tazo wai suyi sallama ita kuma Falaq tana tsoran ummi sai sign yake mata da hannu tana g’irgi’za kai alamar a’a, saiyayi fushi wai k’ozata fito tana k’okarin tashi tabishi suka haɗ’a ido da ummi saita koma ta zauna tana k’allon kuɗ’in.

 

 

Ganin bazata f itoba yasa Auwal tafiya,a ranshi yana addu’ar Allah ya bashi Falaq dan gaskiya yana mutuwar santa ba kaɗ’an ba,yana tafiya Falaq taje t’abawa ummi kuɗ’in ta.

 

 

*3*

Ummin falaq ta cika da mamaki wai yau falaq ce tasan soyayya lallai sai sun kara sa ido akanta,musamma dataga irin yadda take shigewa Auwal, Auwal na fita ummi ta kalli falaq tace meye haɗin ki da auwal?

 

Sake rufe fuska falaq tayi wai ita nan kunya takeji,”haushi ya kara rufe ummi taji kamar ta tashi ta shaketa dan takaici suna haɗ’a ido ummi ta sakarmata harara sannan falaq ta shiga hankali ta tafara yan soshe soshe na rashin gaskiya.

 

Abban tane ya shigo tayi saurin tashi xuwa gurin shi tana mai sannu da zuwa tare da karɓ’ar ledar hannun sa datake ta kamshin balangu.

 

Abba ya karasa inda ummi take ya zauna tare da kama hannunta yana matsawa cikin tsigar soyayya sukeyi ta yadda yar tasu da hankalinta yayi kan balangon da abbanta ya kawo musu baxata ganeba.

 

kusa da kunnan ummi abba ke mgn a hankali”bari naje na samo miki kankana kishi yau akwai aiki dan ina bukatarki cikin jikina gaba ɗayan su biyun suka k’washe da dariya harda falaq dabata san me sukewa dariyar ba amma saidata dara itama.

 

Falaq ta gama juye musu wake da shinkafar da abba ya kawo ta xuba balangun akai sai abba yace bari yaje yadawo yanxu,”abba ina kuma xaka? Falaq ta faɗ’a dan ta k’agara taci naman kuma duk tare suke cin abinci wanda Abba ke bawa ummi da kanshi.

 

“Abba yace bari yanxu zan dawo ya faɗa yana fita daga d’akin”

 

Ranar dai su falaq ansha daɗi anyi kwanan farin ciki,su abba ma 🙊…….

 

k’yak’yawan saurayine son k’owa k’in wadda ta rasa ɗ’an k’imanin shekara ashirin da biyar,a hankali yake fitowa daga cikin k’atafaran gidan, cike da kasaita har xuwa wajan motar da aka gama wanketa aka fitomai da ita waje.

 

Dak’a ganshi k’aga balarabe sak yana sanye da jallabiya milk colour sai ɗ’aukar ido takeyi ya k’arasa wajan motar sai zabga kamshi yake kamar anyi wankan turare a gurin ya buɗ’e ya shiga ya zauna a driver seat yajawo seat belt yasa.

 

Wayar shi ya ɗ’auka yana danne danne a jiki kome yak’eyi ban saniba sabida na hango muku falaq.

 

Falaq ta dawo daga siyan kosai da koko tana shawo k’wanar dazata kaita gida ta hango wata lafiyayyar motar fara sai ɗ’aukar ido take.Cikin sauri ta taho dan kuwa saita kalli madubi tukunna.

 

Tana zuwa ta fara gyare gyare a jikinta sai wani jujjuyawa takeyi a gaban glass ɗ’in.

 

Arfat na kokarin saka key yaganta sai feleke take kasancewar glass ɗ’in motar bakine ita bata ganin shi,shine yake ganinta.

 

Tsayawa yayi yana kallon ikon Allah da baya k’arewa yafara tunanin kodai tana da jinnu ne shiyasa take ta kallon madubi, a hankali ya zura key ɗ’in ya tada motar yana kallanta.

 

Jin motar ta kunnu yasa cikin Falaq murɗawa tareda xaro idanuwa tana kara makale ledar k’osan da kofin kokon jin ta mutu ta fara kukuku yasata ɗaga xaninta sai gudu.

 

Mamaki yasa ke k’ama shi dan ganin abun gudu baya mata wuya ya girgixa k’ai tare da taɓ’e bak’i yatada motar ya wuce cikin gari.

 

Da gudu ta shiga gida ta kankame ummi tana haki,cikin sauri da ruɗ’ani ummi ke tambayar me ya falaq na nuna mata kofa da hannu dan ta k’asa magana,Abban tane ya fito daga bayi yaji ummi nata tambayar Falaq ko lafiya, karasowa kusa da ita yayi saida ya bari ta dawo cikin hank’alin ta sannan ya tambayeta kumeye.

 

Tana gama gaya mai yace wato yauma k’inje k’in tone shi? Wai me yasa kina girma amma k’in xama sha’sha’sha? Bana san k’ik’ara ko k’alli kofar gidan bare k’ileka mai ɗ’aki k’o motarsa k’inajina? Abba ya faɗa yana t’sareta da ido k’afin tace to tana cokaro baki k’amar zatayi kuka.

 

wajan k’arfe 4:00pm salama k’anwar Abban Falaq ta shigo gidan ta k’arasa har ɗ’aki inda ummi ke k’wance,tunda naga kallon da salama tak’eyiwa ummi nasan bada shiri tazo gidan ba jinayi tana cewa to asartacceya makira nakasarshi walhy ni kurwata ɗ’aci gareta nafi k’arfin k’i nesa ba k’usa ba.

 

Kuma walahi dole k’ibar yaya ya kara aure, mata sai shegen iyayi babu abinda k’ike k’aramai sai rama da asara kullum k’ina k’wance bakida mammora aikin banxa,shikuma yayan nan duk yabi yawani damu k’anshi akanki sai kace wata uwar shi. Ita dai ummi bata ce k’alaba hasalima murmushi ne kwance a fuskarta kamar bata damu da k’alaman salama ba harta yi tagama batace mata komai ba, wannan ya k’ara tunxura salama tadinga masif k’amar sabuwar k’amu, ta fita tana masifa dan dama zuwatayi taci mata xarafi.

 

“Allah sarki ummi sai yanxu ta samu damar yin k’uk’a mai ratsa xuciyar wanda ke saurare”

 

Sallamar Falaq data dawo daga makarantar allo shiyasa tayi saurin share hawayen nata tayi k’amar tana bacci.

 

Falaq ta k’arasa wajan ummi ta zauna k’usa da ita tana k’are mata kallo. umminta me kyau amma bata tafi tana zancen zuci taga idon ummi na k’iftawa da sauri tayi dariya tace Allah ummi bakiyi bacci ba ga idonki yana motsi,maganar tabawa ummi dariya hakan yasa taɗ’an yi dariyar tace ja’ira k’inzo kinsani gaba ai dole na k’asa bacci sukayi dariya gaba ɗ’ayan su.

 

Jin an shigo anata yi musu ball da kaya a tsakar gida yasa Falaq fita da sauri dan ganin meyi musu wannan aika aikar, sallau dillalin gidaje ne ya shigo yana musu ɗ’ibar albarka yana ganin Falaq yace ke ina Abban? ki tace bayanan.

 

Nan yaringa masifar yau sai an bashi k’uɗ’in hayar shi ko k’uma subar mishi gidan,dan yagaji da gafar sa ɓ’ega kahoba.

 

Ummi sallaune kuma sai watsar mana da k’aya yakeyi Allah zanje nayimai rashin k’unya, falaq ne dake tsaye take gayawa ummi hak ranta ɓ’ace dai dai nan Abba ya dawo yaga abinda ake mishi cikin muhallinsa.

 

Ya kalli sallau dillali cike da mamaki da ɓ’acin rai yace bana ce kadena shigar mini ciki ba kodan kana ganin gidan a k’ark’ashinshi ka yake?

 

 

*4*

Sosai ran Abban Falaq ya ɓ’aci dan a rayuwar shi baya san namiji yana shigar mai gida hakan na matukar ɓ’ata mishi rai,shi kuwa sallau dayake ta uwar masifa yana rantse-rantsen sai Abba ya bashi k’uɗ’in shi ko kuma yanxu su tattara k’ayansu sufita dan yanada waɗ’anda zai saka.

Da sauri Abban Falaq yaja sallau zuwa zaure yafara nunashi da hannu cikin ɓ’acin rai yace mai,”idan har nashiga natarar da matata na kuka wallahi Allah bazan baka k’uɗ’in ba k’uma sai nayi k’ararka sabida k’etare iyaka da k’ayimin”, yana k’aiwa nan ya juya ya shiga cik’i, cik’in zafin zuciya.

 

Hank’alin abba a tashe yak’e domin yau shekara ɗ’aya k’enan da wata uku ɓe bada kuɗ’in haya ba, kasan cewar yau wata tak’was ummin Falaq na k’wance babu lafiya yasa har yanxu ɓe bada ba gashi anzo ana mai tijara.

kuɗ’in da yake tarawa dan saima ummi resting chair su yashiga ɗ’akin ya ɗauko dubu shabiyar ne dama ya kalli inda falaq ta nanike ummi kamar zata koma cikinta,sannan yafita yana kara lissafa kuɗin yaje yabawa sallau dubu goma yanuna mai hanyar fita sannan ya dawo ciki shikuma.

 

k’arasawa yayi kusa dasu cikin dakewar zuciya yafara magana da tattausar murya.

 

“Bana san ganin damuwa a gurinku, k’une farin cikina narabu da yan uwana duk sabida ina k’aunarku me yasa yanxu zaku sa damuwa cikin rayuwar ku idan kuka cigaba zaku k’arya min zuciya dan Allah kuyi mana addu’a zata karbu dan baxan iya ganinku cikin k’unci ba ya karasa kamar zaiyi kuka”

 

Bayan sati biyu anyi hutu a makarantar allon da falaq take zuwa k’asancewar lokacin maulidine k’uma ambata karatun dazatayi a wajan nasu maulud ɗ’in,hak’an yasa hankalin Abbanta ya tashi sabida ko k’ayan da zatasa babu yashiga neman aikin da zaiyi amma shiru gashi bawani tsufa yayi ba dan age ɗ’insa bazai wuce 45 ba.

 

Ana cik’in hak’a aka fara neman mai gadi a katan gidan nan sabida wanda yakeyi shima zai tafi garinsu dan ganin iyalinshi daya baro wata 3 kenan nan mutane suka cika gidan liman, danshi akasa ya nema yaya al-ameen babu ruwan shi bacci ne kawai yake agidan ya shirya yabarshi.cikin mane man harda Abban Falaq da yayan shi yaya bashir wanda kuma shine ya samu nasarar zama sabon mai gadi.

 

•••••••••••••••••••••••••••••>

Samun aiki yayiwa Abban Falaq wuyar samu nan yaji ana neman masu gyaran gidan, Allah ya temake shi ya samu aka ɗ’auke shi aikin,yasamu k’uɗ’i yaje ya nunawa ummi itama tayita murna dan tasan zata samu magani acikin k’uɗ’in.

wajan karfe biyar abba ya shiga gidan hannuwan shi ɗ’auk’e da ledoji guda biyu sallama yayi Falaq dake wanke wanke taɗ’ago taganshi da leda dasauri ta tashi tare da yimai oyo yo ta karbi leda guda ɗ’aya suka wuce d’akinda ummi take k’wance.

 

Sunnu da zuwa tayiwa Abba, yace yauwa matata ya jikin naki tace jik’i da sauki ya zauna kusa da ita a gefen gado k’allonta yake cik’e da so da k’auna dan ummi akwai kyau,hannun ta tasa mai lafiyar ta cire mai hular kanshi sukayi murmushi tare.

“Abba na buɗ’e nagani? Falaq ta faɗ’a tana k’allan shi,yace ‘a’a kije ki gama aik’inki sannan munyi sallah sai a buɗ’e ko? Ba haka taso ba dan ita tama manta wanke wanke tak’eyi haka ta tashi tafita daga ɗ’akin tanata hasashin abindake cikin ledar.

 

Falaq yarinyace irin masu shigen surutun nan gata ‘yar kubul kubul like pharty bb,shekarunta bazasu gaza shekara sha 12 ba fara ce saidai farin ya dishashe sabida rashin tsafta,tana da gashi irin mai laushin nan hakan yasa ko kitso akayi mata baya daɗ’ewa sannan k’wark’watar k’anta take binta ajikin kaya.

Bayan sunyi sallah falaq tace Abba a ɗ’akko ledar? umminta ne ta ce tace waike saurin mekike saikace kin aike shi,falaq ta turo bak’i kamar zatayi k’uk’a ganin haka abba yace ɗ’akko dama ai sakon nakine nan da nan ta saki rai tajanyo ledojin yaciro mata k’ayan da yasiyo mata ya bata.

 

Murna sosai Falaq tayi ta rungume Abba dake zaune yana kok’arin ciro atamfar ummi data hajiyarsu,Abba na maulidine k’asiyo min? yace ehh kina sonsu aiko da sauri tace ehh Abba nagode yace yauwa tunda k’inyi godiya bari a k’aramiki.

Yaciro wasu takallama irin yan ɗ’ari #350 ɗ’innan, Allah sarki ta dunga murna ganinsu take k’amar yan 10k, dama ai k’owa da irin arzik’in sa aduniya shikam babu abinda ya saimawa k’anshi raguwar kuɗ’in zaiyo musu chefanelan abinci da maganin ummi,dama Atine matar abokinsa tana ɗ’inki dan haka can zaikai na ummi hajiyarsa kuma yakai mata atamfar dan idan ya ɗ’in ka mata wani rigimar za’a.

 

Karin wasu littafai da zaku so

••••••••••••••••••••••••••••>

Ummi ce ta fashe da kuka sosai ya k’wace mata hak’an yasa Falaq tasowa tazo k’usa da ita,

Ummi meyasa k’ike kuka? ciwan ki yake mik’i ciwo? ummi ta kasa magana hakan yasa Falaq cewa ummi nice ko Abba ne muka saki kuka?

girgiza kai ummi ta hauyi alamar a’a shikuwa Abba yasan abinda tak’ewa kuka dan haka yace da falaq taje ta k’wanta dare yayi,tace Abba ni banajin bacci saidai naje gidan hajiya yace to yabata atamfar yace tak’ai mata kafin yazo tace to takarɓ’a ta tafi za’aje a gayawa su farida ansai mata kaya.

 

Falaq na fita Abba ya maida hankalinsa ga ummi dake ta faman share hawaye da hannu ɗ’aya,gashi ta kasa k’allon shi yace, “Fatima k’in kasa rike kukanki da damuwarki ko? kullum saina yi miki magana indai t’sa’k’anina da hajiyane k’ici gaba da yimin addu’a in’sha Allahu babu mai rabamu sai mutuwa cuta lokaci ɗ’aya take shiga,sauki kuwa sai sanda Allah ya kawo shi k’ici gaba da hak’uri kina min addu’a babu mai rabamu k’inji” ummi tace to Allah yasa amma ni inajin tsoro.

Abba yace kidena tsoro kinsan ina sanki fatima soyayyarki tasa nakasa wani auren duk da bakida lafiya amma ai ina samun abinda ake bukata na auren ko?Ummi ta kalle shi,murmushi ta gani a fuskar shi saita ji kunyar shi hak’an yasa ta juya fuskarta gefe itama tana dariyar.

 

_Allah sarki Allah k’abarmu da masu k’aunar mu duniya walahira_

 

Leave a Comment

error: Content is protected !!