Hausa Novels

Babbar Hujja Hausa Novel Free Pages

Babbar Hujja Hausa Novel Free Pages

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

LITTAFI ABOKIN FIRA

 

Ina ma’abota karatun Hausa novel ga dama ta samu

 

Kasance acikin wannan channel d’in domin morewa karatun littattafaina,tun daga na farko har zuwa Wanda nake yi a yanzun wato YAYANA ZAIN

 

Kuyi sharing din wannan channel masoyana

 

 

 

 

*BABBAR HUJJA*

 

Book 1

 

 

“`NA“`

 

 

 

*FATIMA ‘DAHURU FUNTUWA BINTA*

 

 

*HAUSA WRITER’S ASSOCIATION*

 

 

 

 

“`Page“` 1

 

 

*GABATARWA*

*Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai da ya sake had’amu acikin wani sabon littafin mai suna BABBAR HUJJA tsira da amincin Allah suk’ara tabbata ga shugabanmu annabi Muhammad (S A W) da sahabbansa da iyalan gidansa baki daya*.

 

” Na rubuta wannan d’an littafine domin farkar da mutanan mu, musamman ‘yanmata da samari, akan k’alubalen da ya ke acikin soyayya.

Kawai mutum ya yi imani da Allah, akan dukkan abinda bai sa me sa ba, to daga Allah ne, kuma komin son da ka ke yiwa abu, idan ba rabonka bane sai ya tsere ma ka.

Yafi kyau dukkannin mu mukoma ga mika Al amarim mu ga Allah kawai, musammam akan soyayya.

Domin akanta zan rubuta wannan d’an littafi.”

Burina Hausa Novel Free Pages

” So dayawa za ki ga mutum ki na sonshi, ko kuma shi ma ya na sonki, amma k’arshenta ba Alkairi bane a tsakanin ku,to mafi yawan ‘yanmata da samari idan hakan ta faru agaresu, sai ka ga sun tada hankulan su, har ana neman rasa lafiya.”

” Don haka samari da. ‘Yanmata asa hak’uri acikin zuciya komai da ga Allah ne.

Wadda kake hangen, ko Wanda kike hangen karshenta ba shine mijinki ba.

Amma bazance komai ba akan haka, kubiyoni acikin wannan Dan littafi na BABBAR HUJJA kuji yadda soyayyar wasu masoya zata kasance.

Fatanadai adauki abinda ya ke da kyau acikin wannan littafin.”

 

 

“Sannan littafin *BABBAR HUJJA* k’agaggen labarine bawai ya faru akan wani ko wa ta bane, a’a k’irk’irarsa nayi,don haka koda kaga wani abu ko wani hali ya yi kama da irin naka, to bakaid’in ba ne, don wata k’ilama ban sankaba, ko ban sankiba ,k’irk’irar labarinne kawai yazo da haka, don haka idan abin gyarawane sai a gyara.”

*DAGA FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA*

 

*GARGA’DI*

“Ban yarda a juyamin wannan littafi ta wata sigarba har sai da izinin marubuciyar

Gaisuwa ga dukkan masoyana, a duk inda kuke, ina sonku kamar yadda kuke sona”.

“Ayi karatu lafiya”.

 

 

 

Da sallama ta shigo falon, fuskarta d’auke da tsararriyar kwalliya, wanda ya yi ma ta kyau sosai.

Ta sanya d’an madaidai cin hijabinta Wanda ya k’ara fito ma ta da kyawun fuskarta.

 

“Sannu da zuwa yaya Ahmad.”

 

ta fad’a dai-dai Lokacin da ta ke neman wurin zama nesa da shi kad’an.

 

Ya dago kai ya kalleta, sannan ya ce

 

“bayan kingama shanyaniko,har na yi niyyar tashi in tafi, don nayi zaton ko bakida lokacin da zaki fito na ganki”.

 

 

“Tace tuba na ke yaya Ahmad ni na isa kazo nace bazan fito ba, ka yi hakuri don Allah bansan sauri ka ke ba.

Amma kuma yaya Ahmad ko nakai dare ban fitoba, aibaka iya tafiya baka ganniba,kuma ai tsayawa nayi in shirya kawai, amma shine harka gaji da zaman jirana?”

 

 

Yace “to shirin me ki ke yi? Abinda kwalliyarma ba kyau tayi makiba”

 

 

Tayi dariya tare da fad’in.

 

 

“yabawa kayi kenan, lallai yau na tabbatar kwalliya ta ta burge yayan”.

 

 

Yace “hakadai ki ka ce”.

 

 

Tace “kaima haka kagani”tare da sa gefen hijabinta tad’an rufe fuskarta.

 

 

Yace “Hafsat da ma na zone in sanar da ke cewa rana itayau zan tafi kano, kuma idan naje akalla zanyi sati acan, shiyasa nace bari in sanar da ke, tun yanzun,don ki shirya k’ewata”.

 

 

Cikin shagwab’a

tace “yaya Ahmad yanzu nan harsai kayi sati ban gankaba?Ashe kana shirin azabtar da zukata guda biyu kenan,yaya Ahmad bazan iya tsawon sati ban gankaba, don Allah ka sauk’ak’a tafiyar yaya Ahmad karage kwanakin”.

 

 

Hmmm! yayi ajiyar numfashi sannan yace ni kaina saida na jinjina tafiyar nan, don nasan hakan saita faru Hafsat, ni kaina ina tunanin yarda zanje wani guri inyi sati batare da nazo nayi tozali da wannan kyakykyawar fuskar ta ki ba, ni kaina nakan tambayi kaina, shinwai wane irin sone muke yiwa juna? Wanda dai dai da kwana daya bama iya hakura bamuga junaba,

Hafsat inasonki wani lokacin ma har na ke yima kaina azarb’ab’in cewa na k’agara Inga na mallakeki amatsayin matata, a wannan rana zan tasaki inyi ta kallonki, karki ce fa har saina gaji, a’a bazan tab’a gajiya da kallon ki ba, ba za ki ta b’a gundura ta ba”.

 

 

Ya d’aga hannayen sa sama tare da fad’in.

 

 

“Ya Allah ka nu na min ranar da Hafsat za ta zama mata ta”.

 

Azuciyar ta, ita kuma ta amsa da Ameen, sannan a fili tace

 

“mezakaje kayo kano?”

 

 

Yace “Abba ne ya shaidamin cewar d’iyar k’aninsa, MARIGAYI ALHAJI KABIR ta ke dawowa da ga Engila karatu, to shine waini zanje in tare su, daga air port”.

 

 

Cikin muryar kuka tace “amma shine harsai kayi sati?”

 

 

Yace “banda wannan akwai wani aiki da zan yimai a kamfanin sa, to zai dau ke ni tsawon kwana biyar”.

 

 

Tace “ni gaskiya Saidai katafi dani.”

 

 

Yace “ki yi hak’uri Hafsat akwai sauran lokaci, idan Lokacin ya yi ko abayana ki ka ce in zagaye garin kaduna dake to inhar zan iya zanyi,to amma yanzun mud’an K’ara hak’uri kad’an, ko kina so in sanar da Abba cewa kince a d’aura ma na aure da ke kafin in tafi, sai in tafi dake?”

 

 

Tace”. Ahh!! Kaji ka saboda nice sarkin marasa kunya, niba yanzu ma zanyi aureba, sainayi karatu sosai”.

 

 

Yayi dariya tare da fad’in,

 

” kin ji ki, ahaka d’in?”

 

Su kasa dariya gaba daya.

Haka sukaita firar su cike da kaunar juna, hadida soyayyar su mai ban sha’awa.

 

ALHAJI SALISU mahaifin HAFSAT tare da matar sa Hajiya FATIMA su na zaune a falonsu.

Hjy fatima tace

 

“Al- amarin yaran nan ALHAJI, abin gwanin ban sha’awa, su na son junan su sosai, karkaga yadda Ahmad ya ke d’oki a kanta, itama da ance ga shi ya zo ta na farin ciki, kai! mudai wannan al- amarin Allah ya tabbatar ma na da shi,ka gansu da wa sa da dariya komai su na yin sa gwanin ban sha’awa”.

ALHAJI SALISU yace

 

“shi Allah haka yake had’a soyayyar ‘yan Adam, ga shi dai mutane da dama su na gudun auren zumunci, amma mudai yaran mu Allah ya had’a kawunan su….✍

Leave a Comment

error: Content is protected !!