BABU MARAYA HAUSA NOVEL

BABU MARAYA HAUSA NOVEL

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*BABU MARAYA…*

_{Sai raggo}_

 

 

 

*NA*

 

 

 

UMAR FARUQ*D*

 

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI.*

 

 

 

0⃣1⃣

 

 

 

Duk da zafin ranar da yake dukan jiki na gumi na yanko mun tun daga tsakar kaina har zuwa tafukan ƙafafuwana na da suke sanye da siɗaɗɗen slipers ɗina, ahaka nake ci gaba da ratsa dubban mutanen da suke cikin kasuwar ƴan katako dake rijiyar lemo, kaina ɗauke da katakwaye masu matuƙar yawa.

Sanye nake da koɗaɗɗiyar jar T.Shet tare da wando Three quarter, wanda yayyage daga bayan sa ta saitin mazaunai na.

Ahaka na cigaba da ratsa jama’ar dake wurin har na ƙara sa bakin rumfar Alhaji Tanimu, wanda shine ya kasance mutumin da ya ai’keni na ɗauko masa katakon domin aƙara sa yan kasu kamar yacce aka yanka waƴan da na ɗebo ɗazu da safe akura, kasancewar shine uban gida na, duk da dai bashi kaɗai na kewa dako ba, amma dai awurin sa nake acikin kasuwar.

 

Tsaye nayi adai-dai wurin da ake ajiye katakwayen, wato daga gaban injin dake aikin yanka su ina jiran azo akama mun na sauke, kamar yacce aka saba ako da yaushe idan na ɗauko aka domin na sauke su aƙasa, amma sai naji babu wani mutum da yayi yun ƙurin tawowa inda nake bare ya har kamamun na sauke su ɗin, duk da dai ga mutanen nan ina jin motsin su daga gabana, alamun dai suna nan awurin.

Ahaka na cigaba da tsayuwa cikin tsantsar gajiya da jigata, gumi na cigaba da yanko mun tun daga tsakar kai na yana dira akan fuska ta, har wani na gangarawa cikin kwarmin idanuwa na, amma har na ɗauki tsayin minti huɗu banji alamun za’a taimaka mun na sauke azababben nauyin nan ba, hakan ne yasa na fara ƙoƙarin yin yarce zanyi in sauke su da kaina, amma gaba ɗaya sai naji katakwayen sunyi gaba riiii suna shirin sheƙewa aƙasa ba tare da na shirya ba, ta yarce har ni kaina nayi gaba tangal-tangal ina shirin binsu, wato na kifa akan su da zarar sun sauka aƙasa, hakan da na gani ne ya sanya ni miƙa hannuwa na da sauri ina mai ƙara tallabo su na dawo dasu tsakar kaina, amma duk da haka sai da na ƙarayin luuu ta baya kamar zan kifa ƙasa, sai kuma Allah ya bani ikon komawa tsaye kamar yacce nake tun farko, sabo da yarce nasa yatsun ƙafafuwa na na danne ƙasar wurin dasu sa ƙarfi.

 

Cikin tsantsar jigata na fara ɗaga idanuwa na da nake jin su kansu sun mun wani irin bala’in nauyi, bayan na samu na ɗan tura katakon baya yarce zanji daɗin hangen abun da ke gabana da kyau, sabo da in gano waƴan da ke zaune abakin rumfar Alhaji Tanimu yau da har baza su iya taimaka mun na sauke wannan uban katakon dake kai na ba.

 

Da sauri na mai da idanuwa na na lumshe su, ƙirji na na wani irin amsawa da matuƙar ƙarfi, sabo da yarce gaba ɗaya idanuwa na biyun suka shiga cikin tsakiyar idanun Alhaji Tanimu, wayan da naga sunyi matuƙar canza launi daga yarce na sansu zuwa wani launin na daban wanda yay matuƙar razana ni, sannan kuma ga riga da wando na dana zo dasu ajiki na ɗauke ahannun sa ya musu wani irin riƙon hulaƙanci da ƙas-ƙanci, domin ko rabin su gaba ɗaya na kwance acikin dusar katakon dake wurin, ga kuma rabin su da suke riƙe ahannun sa duk da kasan cewar su wankakku kuma goggagu, sannan kuma ga dan dazon jama’ar dana gani tsaitsaye agafen sa, suma kuma duk idanuwan nasu akai na ne ni ka ɗai.

Lokaci ɗaya naji jiki na ya fara wata irin kyarma, ƙafafuwa na suka dinga rawa, hannuwa na na karkarwa tayar ce har ban san lokacin da katakwayen dake ɗauke akai na ba suka fara sauka aƙssa tako ina, sai dai kawai sautin dirar su da naji wanda yay sanadin buɗe manya manyan idanuwa na dana lumshe ina mai shirin kaucewa, sabo da yarce naga wasu na shirin dira akan yatsu na.

 

Da matuƙar ƙarfi na cije lips ɗina na ƙasa tare da rumtse idanuwa na da matuƙar ƙarfi, jiki na na tsantsar rawa, gumi na ciga da ɗiɗɗigo mun sabo da yarce naji dirar wani katako akan babbar yatsa ta da matuƙar ƙarfi, tayar ce har sai da azabar zafin sarar ta soke ni har cikin ƙwa-ƙwalwa ta duk da ƙoƙarin da nayi wurin ganin na kauce musu basu same ni ba.

Cikin tsantsar azabar da nake jin tana cigaba da ratsa ƙashi da jijiya na jiki na na fara girgiza kaina ina jan ƙafar ahankali, har lokacin kuma ban fasa taunar lower lips ɗina ba, sabo da yarce nake jin yatsar tamkar babu wani saura da tayi acikin jiki na.

Ina cikin wannan yana yin azabar sai kuma na ƙara jin saukar wasu irin gigitattun marika masu matuƙar ƙarfi da azabar zafi akan fuska ta, tayar ce har sai da naga gilmawar wani haske ta gefen idanuwa na jika ke. Tassss! Tattass!! Tassss!!!

Gaba ɗaya naji an wanke mun fuska da maruka ta ko ina ba tare da waccen azabar da nake ji akan yatsu na ba ta sake ni.

 

Taga-taga nayi baya-baya ina shirin kifawa aƙasa, domin ko har na riga dana saddaƙar da na kai ƙasa hankali na amatuƙar tashe, amma sai naji ni na faɗa jikin mutum, kana daga bisani wanda na fada jikin nasa ya sanya hannunwan sa yana mai ɗago ni ya sake tsaida ni akan ƙafafuwana da suke wata irin bala’in rawa.

Ban iya juyawa na duba wanda ya tare ni ba ya hani ni faɗuwa ƙasa ba, sabo da bashi ne abun da nafi buƙatar gani ba yanzu, sai idanuwa na ma dana ke jin suna mun wani irin raɗaɗi da zugi, sabo da marin da aka mun, na fara ɗaga su ina mai kai su gaba na sabo da inga wanda yayi mun waƴan nan marikan.

 

Ƙam na tsayar dasu akan fuskar mutumin dake tsaye agaba na ba tare da na iya ko ƙifta suba, jiki na na cigaba da tsantsar karkarwa, hankali na idan yayi dubu sai da duka ya tashi, sabo da arba dana yi da fuskar da ban taɓa tinanin ko amafar ki ba mai ita zai iya zagina balle har ya ɗaga hannu ya mare ni, sabo da yarce muke matuƙar mutunci da shi.

Cikin tsantsar ruɗu na fara ɗaga laɓɓana dasu ma ke tsananin rawa ina son buɗe baki na tambaye sa laifin dana masa da har bai sanar dani ba na gyara ya rufe ni da duka abainar nasi, amma sai nai na kasa, sai wata irin karkarwa da laɓɓan keyi suma, yayin da idanuwa na kuma suka kaɗa sukai jajajir kamar gauta, sabo da tsabar tashin hankalin da nake ciki.

 

Alhaji Tani mune tsaye agabana har lokacin hannun sa riƙe da kaya na yana sakin wani irin huci, ga idanuwan sa waƴan da kallo ɗaya zaka musu kasan ba ƙaramun ɓacin rai bane ke ƙunshe acikin su da ya kafe ni dasu yana mai jifa na da wani irin kallon ƙas-ƙanci da ƙyama. Agefe kuma ga uban jama’a nan da suka taru, waƴan da suke zaune awurin tun can da kuma waƴqn da ƙarar sautin marin da Alhaji Tanimu yamun ya janyo hankulan su wurin.

 

Ci gaba da motsa laɓɓana nayi ina mai son buɗe baki na tambayi Alhaji Tanimu laifi na, amma gaba ɗaya naji na kasa, gaba ɗaya ilahirin jiki na kyarma yake, yayin da gumi kuma ke cigaba da tsats-tsafo mun ta kowace kafar gashi da ke cikin jiki na.

 

Cikin tsantsar zafin rai Alhaji Tanimu ya buɗe baki bayan ya jefa ƙwayar idanuwan sa acikin nawa yana mai faɗin. “Wato kana mamakin abun da yasa na mare ka ko?” Ya faɗa yana mai sake kafeni da idanuwa, tukun daga bisani ya ɗora da cewar “shin ko zaka iya faɗamun kayan wane ne wayan nan ɗin?” Ya faɗa yana mai ɗago sutura ta awani irin hulaƙance ya matso da ita saitin fuska ta. Yayin da ni kuma har lokacin baki na ya gaza yin mo wane furuci, sai idanu kawai da nake binsa da su ina mai jin- jina masa kai yarce kasan zakara, alamar eh eh kaya na ne, har kuma lokacin ƙirji na bai fasa bugun ɗari-ɗari ba, dan bazan ce tara tara ba ayarce nake jin sa, ga kuma jama’ar dake ƙara kutsowa inda muke sabo da yarce ake hango taro tun daga nesa.

 

Janye kayan yayi daga saitin fuskata yana mai sakin rigar aƙasa, tukun ya sake kamo bakin wandon dai- dai wurin gidan zariya da ƴan yatsun sa biyu, babba da manuniyar sa kawai yarce kasan wanda ya riƙe wandon kashi yana mai jujjuya sa, har kuma lokacin idanuwan sa suna nan ƙam akan fuska ta, yayin da ni kuma idanuwa na suka kasan ce kafe akan wando na da nake gani ɗauke ahannun sa yana masa juyin hulaƙanci, sabo da inga abun da zai mun da shi.

 

Hannun hagun sa ya sanya acikin aljihun wandon, tukun daga bisani ya janyo sa yana mai futo dashi waje da kuɗaɗe ƴan dubu dubu masu matuƙar yawa daga ciki ɗauke ahannun nasa.

 

Tashin hankali wanda ba asama masa rana kenan. Wata irin juwa juwa naji tana ɗiba na tayarce har take shirin yarda ni aƙasa, lokaci ɗaya gaba ɗaya na nemi zafin marin da nake ji akan fuskata tare zafin dirar katakon da ya sauka akan ya tsata na rasa, domin ko ni dai na san ban ajiye ko ɗari ukku acikin jiki na ba, gashi kuma yanzu akan idona naga anzaro sama sa dubu goma daga cikin aljihun wando na, yayin da idanun al’ummar dake wuri ya ƙara yowa ca akai na kowa na jiran yaji ƙarin bayani daga bakin Alhaji Tanimu.

See also  Fa'idodin amfani da Nonon Akuya

 

Sosai rawar da jiki na take yi tayi matuƙar ƙaruwa tayar ce har haƙora na suke gwaruwa da juna suna bada wani irin sauti da ƙarfi suna haɗuwa da juna.

Ina cikin wannan tashin hankalin na ƙara tsinkayo muryar Alhaji Tanimu cikin amo da hargowa tana mai dukan dodon kunnen na da matuƙar ƙarfi, tayar ce har ban san lokacin da na rufe idanuwa na ba gam ina mal girgiza kai na, kafin daga bisani kuma wasu irin hawaye masu matuƙar gudu suka ɓalle daga cikin su suna dira akan kunci na, ni kaina ayanzu ba zan iya cewa ga adadin kwanankin dana ɗauka rabon da nayi kuka ba duk da ƙalabulen da nake fuskanta akullum rana ta Allah, domin ko zuciya ta ta riga ta daɗe da taurewa, zuwa yanzu kome zai same ni na dena masa kukan fili, amma sai gashi yau ina jin ɗumin ruwan hawaye akqan kunci na.

 

Faɗi yake. “Munafiki! Munafiki!! Munafiki!!! Mayaudarin yaro mara mutunci wanda bai san mutunci ba, macuci azallumi mai fuska biyu, na yarda da kai na ɗauke ka domin na taimake ka kasami abun da zaka na rufawa kanka asiri, ashe kai ɗin macuci ne. Akowacce rana ina maka kallon mutumin kirki, sannan ina jinka araina fiye da yarce nake jin duk sauran yaran dake wurin nan, ashe kai gareka ba haka bane ba so kake ka illa ta ni!” Ya faɗa da tsantsar ƙarfi cikin matsanancin cin ɓacin rai idanuwan sa akan fuskanta yana jifana da wani irin kallon dake bayyana tsantsar tsanar da yamun acikin zuciyar sa, yayin da ni kuma jiki na ya cigaba da kyarma, gumi na yanko mun ta kowace hallitar gashi da ubangijin ƙira ya ƙir-ƙiro mun ita ajiki na, banda girgiza kai ina kallon fuskar sa tare da ɗaga laɓɓa ina son yin magana har lokacin babu abun da nake iyayi, domin ko zuwa yanzu gaba ɗaya na ƙara tsananin gigicewa, wata irin hajijiya naji tana ɗiba na, ga wata irin yana yana da naji tazo taiwa maganai na murfi tayar ce har nake hangen gaba ɗaya mutanen dake tsai-tsaye awurin tare da Alhaji Tanimu da yake kwashe mun albarka biji- biji.

 

“Yau kimanin sati ukku kenan da nake ajiye kuɗi na ina nai mansu na rasa, ada bana fargabar barin kuɗi acikin loka ta, sabo da na riga dana san halin ko wane yaro dake zama acikin rumfa ta, amma tun daga zuwan wannan munafikin yaron wurin nan ko kwana bakwai bai yiba komai ya canza, bani da damar ajiye ko da dubu ce sai nazo naga saura ɗari biyar aciki, amma duk da haka ban taɓa kawowa cewar shine yake ai’kata mun haka ba sai yau da naga zahiri, ta dalilin diɓar da akayi tayau da tasha bam-ban da saurar ɗibar da ake abaya, kasancewar yau na tawo da kuɗi da yawa kasuwar nan.”

 

Ya sake faɗa da ƙarfi yana mai cigaba da aiko mun da matsiyacin kallo, yayin da gaba ɗaya ɗaukacin al’ummar dake tsaye awurin suka ɗauki hayaniya kowa na tofa albarkacin bakin sa akai na, domin kuwa agefe na har da mai cewa amma Allah ya wadaran wannan yaro na jiyo, sai dai ko kaɗan zagin nasu gare ni bai dame ni ba, sabo da ba yauce rana ta farko da aka saba zagi na ba asalima zuwa yanzu dan an zage ni ko haushi bana ji sabo da sabo da nayi da shi, tsinuwa kuwa muddin na fito daga cikin gida nayi yawo cikin jama’a to sai naci karo da ita bila adadin, sai dai duk hakan ayanzu basa damu na na ɗauke su ne suma duk acikin ƙaddara ta.

 

Wasu irin tsutsotsi- tsutsotsin tashin hankali ne naji sun caki ƙwaƙwalwa ta, kana daga bisani naji kaina yayi wani irin jigim, tukun daga baya kuma naji ƙwalwalwa ta na cigaba da juyawa tsigar jiki na na tashi, yanar tashin hankali da ɗimuwa ‘lna cigaba da yiwa idanuwa na ƙawan ya, har kuma zuwa lokacin hawayen da suke futa daga cikin idanuwa na basu dakata ba, tunda nake arayuwa ba ataɓa kama ni nayi satar koda cokali ba, sai gashi yau cikin dubban jama’a ana faɗar ni ɗin babban ɓarawo ne har ga sheda nan annuna.

 

“Shin me yasa Alhaji Tanimu zai yi mun haka? Me yasa ya zaɓi ya tozar ta ni yayi mun ƙazafi dan kawai ya gaji dani awurin sa yana son ya kore ni? Shin mai na masa da zai mun haka?” Na watsowa kaina tambayoyi dana san babu mai bani amsar su ajere akuma lokaci ɗaya acikin zuciya ta, jiki na na cigaba da kar-karwa kamar wanda aka sanya acikin ruwan ƙan-ƙara.

 

Ina cikin wannan yana yin tashin hankalin sai ji nai an funciki hannu na da matuƙar ƙarfi ana jana!

Da sauri na fara gwaggwale idanuwa na dan naga mutumin dake mun irin wannan funcikar wacce har yatsu ƙafafuwa na suke dukan katakwayen wurin.

 

Alhaji tanimu ne dai yanzun ma riƙe da hannu na yana fuzga ta da matuƙar ƙarfi yarce kasan mai jan gardamammen rago.

Bai sake ni ba sai da muka je har bakin rumfar sa, tukun yayi wani irin hurgar dani agefe yana mai cigaba da aiko mun da kallon tsana, har kuma zuwa lokacin hannun sa na riƙe da wando na bai sake saba.

 

“Daga yau daga yanzu bana son na ƙara cin karo da ko mai kama da kai abakin wurin nan, ga kayan ka nan ka ɗauka ka sanya kabar mun wuri, ina son daga yau ko ahanya ka ganni kar ka taɓa gigin cewa zaka nuna kasan ni, domin ni nan daka ganni na tsani duk wani mutum mara amana da alƙawari, na tsani duk mutumin da ya kasan ce mara gaskiya, sannan kuma na tsani munafiki, bazan taɓa iya zama da munafiki ba irin ka mai fuska biyu, dan haka ga kayan ka nan na baka minti biyu kacal kayi gaggawar ɗebe su kabar wurin nan tun kafin zuciya ta ɗebe ni nayi maka dukan mutuwa ko kuma na sanya adakar mun kai!” Ya faɗa cikin hargowa yana mai watsomun wandon nawa akan fuska ta.

 

Ban iya cewa ƙala ba sai durƙusawa da nayi ƙasa ina mai sa hannu na ɗauki wandon yadi na, tukun na ware sa ina mai zura ƙafa ta ɗaya ciki, sannan nasa ɗayar, wato dai na ɗora sa akan three quater dake jiki na ba tare da na iya cire sa ba duk da kasan cewar sa na aiki shi da rigar sa, domin kuwa zuwa yanzu ko cikakken gaba na bana iya gani tsabar tashin hankalin da nake ciki, babu abun da yafi damuna ayanzu sai irin yarce naga duk mutanen wurin suna mun wani irin kallo na tsantsar ƙyama, alamun dai gaba ɗayan su suma sunyi amanna ni ɗin ɓarawo ne, yayin da har zuwa lokacin kunnuwa na basu fasa jiyo mun sautin muryoyin wasu daga cikin su ba suna masu faɗin. “Ai ɓarawo baiyi ba arayuwa, ni fa wallahi idan aka kama ɓarawo ji nake inama za’a bar mun shi, da babu abun da zai hanani ƙone ɗan iska da taya, mutum ya gama neman sa zafi sanyi damuna bazara amma lokaci ɗaya wani ɗan iskan banza can yazo ya ya kwashe su….” Ban gama jin wannan furucin ba kunnuwa na suka sake tsinkayo mun muryar wani agefe na yana mai faɗin. “Idan da wanda nafi tsana aduniya to ɓarawo ne, na tsani ɓarawo ko waye shi, haka kuma duk mutuncin da nake ganin sa dashi daga rananr da akace ɓarawo ne shi to duka nake zubar da mutuncin nan agefe duk girman sa ko ƙan-ƙantar sa kuwa, haka kuma duk yarce ya kaiga fuskar ban tausayin sa tare da shiru shiru ɗin s….” Shima ɗin bai kai ƙarshen furucin saba na sake jiyo wani yana faɗin. “To kai dama mai za’ayi da shiru shirun mutum, ni fah dama can arayuwa na tsani mutumin da bai fiya magana ba, sabo da mafi tari idan ka binciki halin su ko kuma kazauna dasu duk zaka same su babu na Allah cikin su, shi yasa dama can ni yaron nan tunda yazo kasuwar nan ban taɓa bashi kayana ya ɗaukar mun ba, sabo da gaba ɗayan sa zubin munafukai gare sa.”

 

Hhhhhhhh! “To ai kune baku san ko waye wannan yaron ba, kune bakusan shi ɗin wane ba, amma ni da nake ɗan unguwar su aina san sa, yaro ne fa wanda ya kashe mahaifin sa da kansa, yaro ne tsinanne kuma munafiki, sanna mara imani wanda bai mai da lalata yaran mutane abakin komai ba, domin ko ta sanadiyyar hakan mahaifin sa ma ya rasa ransa!” Na jiyo sautin wata murya na faɗa haka da gasken- gaske yarce kasan agaban sa duk abubuwan da ya lissafo ɗin suka faru.

 

Wasu irin zafafan hawaye ne masu matuƙar gudu na sake jin sun tunkuɗo daga cikin idanuwa na suna ƙara bajewa akan fuska ta, cikin tsantsar tashin hankali na fara ɗaure ƙuguna da tazugen jikin wandon nawa hannu na na matuƙar rawa, zuwa yanzu banda wani buri wanda ya huce inga na bar cikin kasuwar nan, ji nake inama ace ina da fuffuke, tabbas da ko second ɗaya bazan ƙarayi awurin nan ba ba tare da na tashi ba ko na dena jin sautin ƙazaman furuciccikan da ake yi akai na.

 

Ɗago kaina nayi ina mai watsa idanuwa na zuwa inda naga Alhaji Tanimu ya saki rigata, domin na tabbatar da tana nan ɗin ko kuwa wani ya yaga ta kamar yacce naji wani yana faɗin. “Ai da tsirara akaiwa shege aka barsa ya tafi daga shi sai boxer da uwar sa ma!”

See also  Babban Sirri Hausa Novel

 

Cikin sauri na ɗaga ƙafa ta ɗaya daniyyar in taka ta da hanzari inje in ɗauki rigar inyi gaba ko kunnuwa na sai daina jiyo mun waƴan nan munanan kalaman akai na daga bakunana jama’a, amma sai naji gaba ɗaya ƙafar tayi mun wani irin nauyi itama, taune lips ɗina nayi na ƙasa ina mai girgiza kaina tare da kallon ƙafafun nawa da idanuwa na da suke zubar ƙwalla, ƙwa-ƙwalwa ta na tsantsar suya da raɗaɗi, yayin da zuciya ta kuma ke wani irin tururi yarce kasan wacce ake dafawa acikin ruwan zafi.

 

Ɗaga ƙafar na sake yi da duka karfi na bayan na sanyawa jiki na jarumta, amma sai kuma naji nayi gefe luuu ina shirin zubewa aƙasa, daƙyar na samu na saita kaina daga shirin faɗuwar da nake yi, tukun na fara ɗaga ƙafafuwa na da nake jin su awani ɗaɗɗaure kaina sunkuye aƙasa ina mai yin wurin da rigar tawa take ayashe dan in ɗauka nai gaba.

 

Fauuuu! Naji saukar abu agadon bayana da matuƙar ƙarfi, hakan yasa ni dakatawa daga tafiyar da nake ina mai rumtse idanuwa na, domin ko duk atinani na jifa ne jama’ar wurin suka fara sanya mun, amma sai naji shiru har tsayin minti na biyu ba tare da na ƙarajin saukar wani abun ba, hakan yasa ni juyawa cikin sanyi ina mai kai idanuwa na wurin dan naga wanda ya doke ni, sannan kuma naga abun da aka buga mun mai matuƙar zafi, duk da dai ma tuni zafin da zuciya da ruhi suke ya danne duk wani raɗaɗin ciwo da nake ji ajiki na da kuma mai zuwa ma ahalin yanzu idan da akawai.

 

Alhaji Tani mun dai na ƙarayin ido huɗu dashi still yana aiki mun da kallon tsana.

Da sauri na janye kaina ƙasa ina mai shirin juyawa dan na cigaba da tafiya, sauke idanuwan nawa ƙasa keda wuya nayi arba da takalma na ayashe awurin, sai ayanzu na fahimci sune Alhaji Tanimu ya jefoni dasu suka dira agadon baya na.

 

Durƙusawa nayi ƙasa na ɗebe su, tukun na ɗago ina mai cigaba da ɗaga ƙafafuwa na nayi gaba, ban tsaya ba sai da naje har inda riga ta take ayarde, tukun na durƙusa ina mai kai hannu na ƙasa na ɗauke ta, wasu irin hawaye naga suna tsiyaya akan ta alokacin da nayi durƙuson ƙasa, ko kaɗan ban san cewa adadin kukan da nake ba yayi yawan da har zai jiƙa wuri, sabo da ba tashi ɗin nake ba, asalima ba sanin lokaci da yake futa nayi ba sabo da tashin hankalin da nake ciki sai yanzu dana ga har ya jiƙa wani wuri arigar tawa.

 

Haɗa su nayi da ita da takalmin na rungume su gam acikin ƙirji na da matuƙar ƙarfi, tukun na sake juyawa baya na cikin ƙarfin hali ina mai dosar inda Alhaji Tanimu yake daniyyar naje na basa haƙuri, sannan kuma na masa godiyar abun da yamun abaya kafun inbar wurin.

 

Tafiya nake kaina duƙe aƙasa ba tare da ina kallon gaba na ba, sabo da ko kaɗan bana son sake haɗa idanu da wani daga cikin mutanen dake cikin kasuwar nan har na bar cikin ta, ban san nazo inda su Alhaji tanimu suke atsaye ba, sabo da yarce kaina ke duƙe aƙasa sai sautin muryar sa kawai da na jiyo daga baya na yana mai faɗin. “Shin ubanka zaka gano idan ka koma cikin ko? Ko kuwa zuwa zakayi ka sake bincikar inda ake ajiyewa ka gani idan da saura sai ka kwashe su sannan kayi gaba?”

 

Muryar Alhaji tanimu ta sake dukan dodon kunne na ba zato ba tsammani.

Cak na tsaya a’inda nake ba tare da na cigaba da tafiya ba, haka kuma ban iya juyowa ɓarin da yake ɗin ba, domin ko sai ayanzu na fahimci cewar har na huce inda suke atsayen ashe rumfa ma na dosa, wato dai banda ya tsayar dani da sai dai kawai na ganni acikin ta.

 

Ina cikin wannan yana yin sai jin saukar hannu nayi akan tsintsiyar hannu na an damƙe ni da matuƙar ƙarfi kamar za’a karya sa ta baya, hakan yasa ni ɗago kai cikin sauri ina mai juyawa bayan sabo da inga wanda yay mun hakan.

 

Alhaji Tanimu ne riƙe da hannun nawa yana mai aiko mun da wani irin matsiyacin kallo tare da futar da numfarfashi, kafin daga bisani kuma naji ya saki hannu nawa, sannan ya maida sa kan kwalar jar koɗaɗɗiyar T.Shet ɗin dake jiki na ya damƙe ta da matuƙar ƙarfi tayarce har sai da idanuwa na sukayo waje, dan ko ataƙaice dai shaƙa ta yayi ba riƙo ba.

Tukun daga bisani ya fara funcike ta da matuƙar ƙarfi cikin zafin nama yana mai kama hanyar da zamubar cikin jama’ar da suka yiwa wurin rumfa, sabo da yarce suka zageye sa.

Funcika ta yake da ƙarfi, yayin da ni kuma nake ta binsa kamar raƙumi da akala kaina durƙushe aƙasa idanuwa na suna kallon ƙasa, har kuma lokacin hannuwa na na rungume da riga ta tare da takalmi na ba tare da na iya sakin su ba.

 

Hankaɗa ni yayi da iyakar ƙarfin sa alokacin da muka bar cikin jama’ar, take kuwa na tafi taga-taga ina mai faɗuwa aƙasa da matuƙar ƙarfi, kai na ya daki wasu katakwaye dake jere aƙasa.

Cikin tsantsar azabar da naji ta ratsa tun daga tsakiyar ƙwa-ƙwalwa ta har zuwa ƴan yatsun ƙafafuwa na, tukun na ɗago ina mai kai tafin hannu na kan goshin nawa na dafe sa dashi tare da rumtse idanuwa na da matuƙar ƙarfi.

Jin da nai na shafo ruwa ne ya sanya ni janye hannun nawa da sauri ina mai kawo sa saitin idanuwa na.

 

Me zan gani? Jini ne kwance akan tafin hannun nawa shaɓe-shaɓe alamar goshin ya fashe kenan.

Girgiza kaina nayi ina mai faɗin. “Akwai Allah.”

Tukun na miƙe tsaye ina mai cigaba da cizon leɓe na na ƙasa, sannan na kama hanyar da zata futar dani daga cikin kasuwa cikin sauri, sabo da yarce naga jama’ar nan suna sake juyowa nan ɓarin da nake.

 

Tafe nake ina cilla ƙafafuwa na aduk inda ya samu ba tare da ina kallon cikakken gaba na ba, ban san yaushe na futo daga cikin kasuwar ba kamar yacce bazan iya cewa ga hanyar dana biyo na futo ba sabo da tsantsar tashin hankalin da nake ciki sai dai kawai jin ƙarar motoci da nayi, hakan yasa ni ɗaga kaina sama ina mai kai idanuwa na inda nake jiyo sautin, sai alokacin na fahimci ashe har na futo titi ba tare dana sani ba ma.

Amai-makon na tsaya na tare mashing ɗin adai daita na hau kamar yacce na saba aduk lokacin da na tashi daga kasuwar, sai kawai na kama hanya gefen titi ina tafiya da ƙafafuwa na waƴan da suke sanye da siɗaɗɗen slipers ɗina na aiki, kasancewar har yanzu ina rungume da wancan takalmin nawa tare da riga ta aƙirji na kai na ɗage asama.

 

Banda zallar suya da raɗaɗi babu abun da nake jin zuciya ta na mun, ga wani irin zafi da ƙwa-ƙwalwa ta ta ɗauka tayarce har nake jin kaina na wani irin sarawa, ko kaɗan ban damu da ciwon dake ɗauke agoshi na balle har nayi tinanin na yatsa ta da katako ya dira akan ta, domin ko zuwa yanzu hatta shi na goshin nawa na daina jin raɗaɗin sa, ba kuma wai dan baya yi ɗin ba ne sai dai kawai raɗaɗin da zuciya da ruhi suke ya zarce na ciwon da zira’i mafi nisan zira’i.

 

Inda sabo yaci ace na saba da irin wannan abubuwan da jama’a suke mun, amma sai dai ko kaɗan aduk lokacin da za’a mun sabo ina jin sa tamkar shine na fari awuri na, gaba ɗaya ni rayuwa ta babu wata sa’a acikin ta, kamar yacce babu wani daɗi dan gane da ita.

 

Ban san wani abu farin ciki ba, sabo da rabo na dashi tun ina ɗan ƙarami na, amafi tarin lokuta idan na zauna ina tinani sai nai ta tambayar kaina shin ni sai yaushe ne zanji daɗi, shin anya ko ina da rabon samun farin ciki agidan duniya irin wanda naga mutane nayi, shin wai me ma nayi ne dana zamto abun ƙyama ga kowa, mai na aika ta, wane laifi nake yiwa Allah da yake hukun tani da irin wannan hukunci mai tsantsar raɗaɗi da ƙuna, ya ilahil alamina ya mujiba da’awati, ya rabbi samawati wal’ardi me zanyi ya zanyi in samu farin ciki da walwala kamar yacce nake gani awurin sauran jama’a? Shin har sai zuwa wane lokaci ne nima zanji daɗi kamar yacce naga sauran mutane naji?”

 

Irin waƴan nan tambayoyin suna nake zama nai tayiwa kaina ni kaɗai, wani lokacin har saɓo ma yi nake, ba kuma wai dan ina tsammanin samun amsar su daga bakin wani ba, domin ko inda nake zaman ma ni kaɗai ke zuwan sa balle har ince ga wanda zai amasa mun.

 

Duk wata ƙyama ta da tsanar da mutane ke nuna mun duk basu fiye damu na ba, domin ko ko da nasa abun araina muddin na tuno ni ɗin waye ne sai naji duk abun ya kauce, sabo da hatta da mahaifiyar data tsugunna ta haife ni ƙyama ta take yi, aduk duniya babu fuskar da ta tsani gani sama da fuska ta, aduk duniya babu muryar da ta tsani jin sautin ta sama da tawa muryar, haka kuma aduk duniya babu motsin da tafi ƙin son ji sama da motsi na.

 

Ta tsane ni! Ta tsane ni!! Ta tsane ni tsana mai tsana ni!!! Ta tsane ni irin tsanar dako shege ba ayi masa ita, ta tsane ni irin tsanar da kafuran farko su kaiwa musulmai, yayin da ni kuma ta fanni na nafi sonta sama da komai da kowa dake cikin duniya idan aka cire fiyayyen hallita annabi muhammad sallalahu alaihi wassalam.

See also  Download Gurbin Ido Hausa Novel

Ina san ta so mai tsanani, ina san ta so mai matukar yawa, ina mata so irin san da baya taɓa ƙiyas tuwa, wato so mara adadi kenan.

Bani da wani buri agidan duniya wanda ya huce in ganni gani gata muna zaune awuri ɗaya muna hira, ason samu ma ace har na ɗora kaina akan cinyar ta ko kuma na yanke mata farce kamar yacce naga abokina ukasha na yiwa umman sa, bani da wani buri wanda ya huce in zauna nai ta kallon ta ina jin daɗi arai na, ban da buri da ya huce ace yau gani gata muna zaune awuri ɗaya muna hira da dariya, ko kuma ta sanya ni aiki ina yi mata. Sai dai kash, duk waƴan nan burikan nawa babu ko ɗaya daya cika, babu wani wanda ya kasan ce yana faruwa ahalin yanzu, domin ko tsakani na da ita sai dai kallo daga nesa, wani lokacin ma sai dai na laɓe ajikin taga ina leƙen ta ina jin daɗi tare da sanyi arai na, shi ma kuma muddin akace ta ganni to kashi na ya bushe, domin ko iya faɗa da zagi ranar sai na sha shi. Ataƙaice dai ita ɗin takasance ɓange guda ce na farin ciki da baƙin ciki na rayuwa ta.

 

Wannan dalilin ne ya sanya koda naji ba daɗi idan mutane na kyara ta muddin na tuna mahaifiya ta na mun kyarar da tayi dubun wacce suke mun sai naji ko kaɗan tasun bata dame ni ba.

 

To waima akan me zata dame ni bayan shi kansa mahaifina ya mutu ne da baƙin ciki na, wato ya tafi da tsana ta acikin zuciyar sa, ya koma ga mahaliccin sa yana mai jin ina ma tun farko Allah bai wanzar dashi aduniya ba ballan tana har ya haife ni, ya tafi yana da ace yasan tun farko nine wanda zai haifah da bai bari ya haifan bama, ya koma ga rabbi samawati, malukul maut ya karɓi ransa ba tare da yana jin sauran ɗigon wata soyayya ta ba aruhin sa.

 

Arana ɗaya akuma lokaci ɗaya cikin ƴan minti na komai ya faru, yayi mutuwa irin mutuwar da bata da daɗin gani duk ta sanadi na, to shin wai idan ma har duniya da mutanen dake cikin ta basu tsane ni ba anya ko zanga dai dai, ada idan an mun wani abu na rashin daɗi sai nake ganin ai komai mai huce wa ne, watara na sai labari, watara na nima zanji daɗi, watara na zanyi dariya zan hau kan cinyar umma ta abun da nafi buƙata kamar yacce abba na yasha faɗamun kafun shima ya dena ƙauna ta, ada yaushe ako da yaushe ina tuna maganar hausa wa ce da suke yawan faɗin kalmar. *INDA RAI DA RABO* wato *IDAN DA RAI RABO ZAYA ZO* (My upcoming novel). Amma zuwa yanzu tuni nayi watsi da wannan kalmar, na cire ta daga cikin babin *MADUBIN RAYUWA TA* da nake yawan hasa-shen sa agaba tun aranar da mahaifina ya koma ga mahallicin mu, domin ko aranar ne gaba ɗaya na cire rai da duk wani farin ciki da nake tinanin zan samu agaba, akuma ranar ce na tabbar da babu wata sauran sa’a da nake da ita agidan duniya, sai dai kuma ako da yaushe inawa kaina fatan samu alahira, wato ina sa rai da rahamar Allah idan na koma gare sa akowace rana da lokaci.

 

Girgiza kaina nayi bayan na tura leɓena na ƙasa cikin baki na, tukun nasa haƙwara na na sama dana ƙasa na danne sa da matuƙar ƙarfi, sannan daga bisani na ɗaga laɓɓa na ina mai buɗe baki na da ƙarfi nace. “UMMA TA BATA SONA ABBA NA YA TSANE NI, TO KO TAYA MUTANEN DUNIYA ZASU SO NI.”

Na faɗa da ƙarfi wasu irin hawaye masu matuƙar ɗumi suna tsiyaya daga cikin idanuwa na, tukun naja na tsaya a inda nake ina mai ɗaga kaina na fara kallon wurin da nake cikin tsantsar mamaki, wai ashe atafiyar nan da nake yi har nazo ƙofar ruwa tun daga rijiyar lemo da ƙafafuwa na ko kaɗan ban san nayi taba sabo da gaba ɗaya hankali da tinani na basa wurin, sai kawai yanzu dana ɗaga kaina sama nayi arba da under pass na ƙofar ruwa…………….✍

 

 

 

 

*KU TSAYA KU KARANTA BAYANAN ƘASAN NAN DUKA KAMAR YACCE KUKA KARAN TA LABARIN DUKA DAN GIRMAN ALLAH, DOMIN KO DUK AMSAR TAMBAYOYIN KU DA KUKA DINGA AIKO MUN DASU AKAN HUBBAN HAƘIƘAN DAMA SHI KANSHI BAYANIN WANNAN SABON YANA WURIN.* 👇👇👇👇

———————————————————————-

 

*TO FAN’S GA SABO NAN NA ZO MUKU DA SHI, BAN SANI BA KO ZAI MUKU DAƊI KO BA ZAI MUKU BA, NI DAI KAWAI ABUN DA NA RIGA NA SANI SHINE NI YAMUN DAƊI KUMA YA SHIGA RAINA KAMAR YACCE DUKA SAURAN LABARAN DA NAKE TSARAWA SUKE SHIGA RAINA.*

 

_*HAƘIƘA KO KAƊAN BANSO NA FARA TYPPING YANZU BA, DOMIN KUWA AYANZU NE BAN DA LOKACI, KUMA BANA TINANIN ZAKUNA SAMUN SA ASATI SATI MA DUK DA KASAN CEWAR SA DOGON LABARI, SABO DA MUN KOMA MAKARANTA, YANZU HAKA MA RANAR LAHADIN NAN ZAN TAFI MUN DAWO SALLAH BREAK NE, ND KUMA KU KAN KUN SAN RUBUTU BAYA TAƁA YIWUWA ALOKACIN DA AKE KARATU, BARIN MU DA SAI MUN DAFAWA KANMU HATTA ABUN DA ZAMUCI MA, SO BANDA LOKACI KO KAƊAN WALLAHI AMMA IDAN NAGA DA DAMA ZAN NAYO MUKU, IDAN KUMA NAGA ABUN BAZAI YIWU BA MAYBE ZAN AJE TYPING ƊIN SANE GABA ƊAYA HAR ZUWA LOKACIN DA ZAMUYI HUTU, WANNAN DALILIN SHINE YA SANYA NACE MUKU BAZAN FARA SABO YANZU BA, AMMA MUTANE SUN TAKURA MUN DA MAGANAR CEWA DAN ALLAH IDAN BAZA’A CIGABA DA HUBBAN HAƘIƘAN BA TO AFARA MUSU WANI, WANNAN DALILIN SHINE KAWAI YA SANYA NI NA FARA WANNAN ƊIN, AMMA BAWAI DAN NA SHIRYA MASA BA, DOMIN NI ATSARI NA MA BAN TAƁA SAKIN PAGE ARANAR DANA RUBUTA SA BA, ASALIMA SAI NACI RABIN LABARI TUKUN NAKE FARA SAKI, SAI DAI DUBA DA ABUN DA YA FARU DANI AKAN LABARIN HUBBAN HAKIKAN YASAN YA NACE BAZAN KARA AJIYE PAGE BA, GWANDA NA DUNGA SAKIN SA ADUK LOKACIN DANA RUBUTA SA, DAN HAKA YANZU SAI KUN DINGA HAƘURI DANI, SABO DA BAZA KU TABA SAMUN UPDATE AKAI KAI BA KAMAR DA, DAN DA ƊIN MA ƊAUKOWA KAWAI NAKE INA TURO MUKU SHI, FATAN ZAKU FAHIMCE NI GABA ƊAYAN KU.*_

 

 

*YAWWA SAI KUMA MASU CEWA DAN ALLAH HUBBAN HAKIKAN ASAKE RUBUTA MUSU WANI ASANYA MUSU FARASHI KO NAWA NE ZASU IYA BIYA, INA SON KU SANI SHI RUBUTUN KIR-KIRARREN LABARI YANA DA BAMBANCI DA SAURAN RUBUTUTTUKA, DOMIN KUWA SHI ABU NE WANDA YAKE FUTOWA DAGA CIKIN KWAKWALWA ADAI DAI LOKACIN DA AKE KAN RUBUTA SA, ASALIMA YAWAN CI SHI KANSA MARUBUCIN BAYA SANIN KOMAI DA ZAI FARU A PAGE DIN SA NA GABA SAI ALOKACIN DA YA RIKE AL’KALAMI YA FARA RUBUTUN TUKUN YAKE ZUWA, WATO IYA KARMU DAI KAWAI TSARA LABARI AGEFE, AMMA SANIN KOMAI DA YAKE CIKIN SA BAYA YUWUWA, DOMIN KO SHI RUBUTU BAIWA NE, HAKA KUMA BABU TAYAR CE ZA’AYI KO PAGE DAYA NE IDAN YA GOGE IN MUTUM YA TASHI RUBUTA SA YA SAKE SA TAMKAR YACCE YAYI NA FARKO, HAKAN BAYA TAƁA YIWUWA DUK BASIRAR MUTUM KUWA WALLAHI, SABO DA ABU NE WANDA YAKE ZUWA ALOKACIN DA KAKE KAN YIN SA, KUMA WANI WURIN DA ZARAR KA WUCE SA TO YA TAFI KENAN SAI DAI KUMA LOKACI BAYAN LOKACI KA DINGA TUNA SA.*

 

*TO KUNGA KUWA HAR DAI PAGE ƊAYA YANA WUYAR SAKE RUBUTAWA TAYA YA NI ZAN IYA SAKE RUBUTA PAGE SAMA DA ARBA’IN AGABA BAYAN KUMA DUKA NA RUBUTA SU ABAYA, SANNAN KUMA CIKIN SU GABA ƊAYA IDAN AKA CIRE GOMA SHABIYAR ƊIN FARKO BABU PAGE ƊIN DA YAKE DA WORD ƘASA DA DUBU BIYAR, KAI ASALIMA HAR PAGE MAI DUBU BAKWAI DA WANI ABU NAYI SU WLLH ACIKIN LABARIN HUBBAN HAKIKAN, NI KAINA SHINE LABARIN DANA ZAƁA ACIKIN DUK SAURAN LABARAN DANA RUBUTA, DOMIN KO NACI WUYA AKAN SA KUMA NA DAƊE INA TSARA SA, TSAWON SAMA DA SHEKARA GUDA INA BINCIKE AKAN SA TUKUN NA FARA RUBUTA SA, NI NE HAR PSYCHIATRIC HOSPITAL NA DAWANAU SAI DA NAJE AKAN LABARIN NAN, BAYAN HAKA KUMA SAI DA NA SAKE SANYAWA AKA HAƊANI DA LIKITAR ƁANGAREN TA WHATSAPP NA SAKE MATA WASU TAMBAYOYI TANA FAƊA MUN AMSO SHIN SU, BAYAN DUK NA GAMA BINCIKE AKAN SA NAZO NA FARA RUBUTA SA SAI DA NAYI TSAWO WATA HUƊU INA RUBUTA SA TUKUN NA FARA SAKIN SA, AHAKAN MA KUMA FA KO RABIN LABARIN BANYI BA, SANNAN YAZO YA GOGE DUKA NA RASA SA, BAYAN HAR NA GAMA BOOK 1 NA KUSA YIN RABI ACIKIN BOOK 2, KUNGA KENAN IDAN HAKA NE GABA ƊAYA CIKIN KU BABU WANDA YA KAMA KO FARCE NE WURIN JIN BAƘIN CIKIN RASA SA, TO DA WANNAN BAYANIN NAKE CE MUKU DAN ALLAH KUYI HAƘURI DASHI KAMAR YACCE NIDA NACI WALAHA AKAN SA NA HAƘURA DA SHI, DUK DA YARCE NASHA KAI ƘARFE BIYUN DARE INA RUBU TASA, DAN HAKA GA SABO NAN FATAN ZAI MUKU DAƊI SHI MA DUK DA BA ZAKU SAME SA AKAN LOKACI BA GASKIYA.*

 

 

 

———————————————-

*INA TAYA ƊAUKACIN AL’UMMAR MUSULMAN DUNIYA MURNAR BIKIN BABBAR SALLAH TARE DA FATAN ALLAH YA MAI MAI TA MANA*

 

 

 

 

 

 

#COMMETS

#FOLLOW

#VOTE ND SHARE PLS

 

 

 

 

 

_Umar dayyan_

1 thought on “BABU MARAYA HAUSA NOVEL”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top