Hausa Novels

Bafulatana Hausa Novel

Bafulatana Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Bafulatana
Tafiya suke cikin daji tare da shanunsu wata matashiyar yarinya Ce wadda bazata wuce shekaru goma sha hudu ba se kuma dattijon dake kusa da ita da alama dai mahaifin ta ne.

 

 

Cike da damuwa yarinyar ta daga Kanta ta kalli mahaifin Nata cikeda damuwa tace “wllh Baba nagaji kawai ka tafi Gida idan na huta zan tawo da shanun ta Ƙare maganar Da damuwa akan fuskarta.

 

Bafulatana

Tunda ta fara magana mahaifin nata Ke kallonta sannan Yayi murmushi yace “to Rabe Babu damuwa amma fa ki kula sosai Da kanki. a nitse ta amsa da to “Baba.

Shafa kanta yayi sannan ya juya ya Kama hanyar gida Ya barta a Dajin tareda Dabbobin, yana tafiya Rabe ta nufi wata Ƙatuwar bishiya dake gefanta ta zauna dan ta huta a nitse ta Ta fara cire Takalmin Robar dake Ƙafarta.

 

 

Tana Gama cirewa ta Jingina da jikin bishiyar bata jima da kwanciyar ba Wani gajiyayyen bacci ya Samu nasarar ɗauke ta sabda Tsabar gajiyar dake tareda ita, kallo daya Zakayi mata ka fahimci tana jin dadin baccin da takeyi.

 

Gidado ba shege ba

A hankali iska me daɗi ta fara kadawa Tareda ƙamshin ƙasa wanda hakan ya gauraye a guri guda ƙamshin ya canza zuwa wani yanayi me daɗin gaske.

Can kuma se aka fara iska me qarfi wadda itace ta zama sillar farkawar Rabe daga baccin datakeyi a hankali ta daga Dara-Daran idanunta Sama Tana kallon hadarin daya gauraye sararin Samaniya ya koma launin baki.

 

Bafulatana

Aiko da sauri ta mike tafara kada shanun tana fadin su kama hanyar gida cikin harshen fulatanci tayi maganar nan da nan shanun suka fara tafiya kamar yanda tace musu suna cikin tafiya Yayyafi ya fara sauka a hankali can kuma se ruwan ya balle kamar da bakin Ƙwarya.

A maddin ta nemi maɓoya se kawai ta dinga tsalle tana murna Ruwan na sauka a jikinta tana dariya, Haka nan Ruwan yayiwa Rabe dukan tsiya amma itako ko a jikinta wai an tsikari kakkausa inji ‘yana magana lol.

 

Bafulatana

 

 

Name: [BAFULATANA HAUSA NOVEL ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: November, 2021

 


13 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!