Hausa Novels

Baiwata Romantic Hausa Novel

Baiwata Romantic Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: baiwata

_Bismillahir rahamanir rahim_

 

 

_1_

 

 

 

 

 

Cike da murna ya shiga ba wa yaran hannu suna tafawa yana fad’in “Yaran kirki kenan, amma fa kunyi k’ok’ari.”

 

Cike da zumud’i *Hameeda* da ba za ta wuce shekara bakwai ba tace “Abba, to za ka siya mana kyautar da ka yi alk’awarin siya mana idan mu ka yi k’ok’ari?”

 

Da fara’a a fuska dattijon yace “Dole na ma, ai ina fita daga nan zan kawo muku kyautarku.”

 

*Hadeeya* dake zaune kusa da shi ne tace “Amma dai Abba ai na fi su k’ok’ari ko? Dan haka kyautata za ta fi ta su kyau.”

 

Hararanta Hameeda tayi tace “Ka ji yarinya, ke da ma ko jarabawar ba’a muku ba, ku fa yara ne.”

 

Kyakyawar matashiyar matar dake zaune gefe da su tana kallonsu da murmushi a fuskarta ce ta bud’a baki cike da gayu a harshen faransanci tace “Calmez-vous les enfants, votre Papa offrira a chacun le bon cadeau (ku kwantar da hankalinku yara, Mahaifinku zai ba ko wa kyautar da ta dace).”

 

Wani kallo ya jefa mata cike da so da k’auna yace “E toi, me za ki basu?”

 

Wani mahaukacin fari ta masa da ido kafin tace “Ce une secret entre eux et moi (sirri ne tsakanina da su).”

 

‘Yar k’aramar cikinsu wato *Hamdeeya* ce ta k’arasa kusa da mahaifiyarta cike da shagwab’a da kuma yarinta tace “Momma, ni ma za ki siya min kyauta?”

 

D’agata tayi ta d’ora a cinyarta tace “Sosai ma yariyata, ai ke ce ma gaba kafin kowa.”

 

Duk farin ciki da murnar nan da ake *Haleematu* na tsaye gefe tana kallo, ganin dai ita ba’a ambaceta ba yasa ta matsowa kad’an kusan mahaifin tace “Abba nima za ka siya min?”

 

Wani mugun kallo ya watso mata daga sama zuwa k’asa kafin ya d’auke kai yace “Da wannan sakaran sakamakon da kika kawo ne zan kashe miki kud’ina?”

 

Sunkuyar da kai tayi a marairaice tace “Dan Allah Abba, ko k’arami ne ka siya min.”

 

A tsawace ya kalleta yace “Matsa ki bani wuri, ba zan siya d’in ba *Saleema*.”

 

Dake sunan mahaifiyarshi gareta sai suke kiranta da sunan Saleema, d’ago kanta tayi ta zuba masa idonta da suka cika taf da hawaye tace “Abba, to idan na yi k’ok’ari a zango na k’arshe za ka siya min?”

 

Saida ya sake hararanta sannan ya yatsina baki yace “Watak’ila.”

 

Murmusawa tayi tace “Tozan yi Abba.”

 

A sukwane ta nufi inda mahaifiyarta ke zaune wacce ka rantse bata falon, sai dai tana zaune tana kallon komai dake faruwa, duk da ranta na suya amma ba ta da yanda za ta yi da ya wuce hak’uri, Saleema na k’arasawa ta zauna kusan Mamanta tana mik’a mata takardar (bulletin) sakamakon, karb’a tayi a raunane tana duba sakamakon, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke ganin sam ba wani k’ok’ari da Saleema ta yi, dan ko a yawan yan ajinsu mutum uku kad’ai ta bari a bayanta.

 

Uwarsu Hadeeya kam dake cike take da farin cikin dake d’awainiya da ita mik’ewa tayi ta nufo inda *Alhaji Yusuf Jiji* ke zaune, *Safeeya* na ganin haka ta yi saurin d’auke kanta dan ta san me amaryar za ta yi. Ai kam *Ardayi* na zuwa d’an rank’wafawa tayi ta d’ora hannunta a kafad’arshi sannan ta sumbaci labb’ansa, daga ita har shi ba wanda ya ji kunyar yaran, dan hakan ba sabon abu bane a wajensu.

 

Saida suka aikawa junansu wani kallo da su kad’ai suka san ma’anarshi kafin ta tattara hannayen yaran ta rik’e a hannunta, d’an juyawa tayi ta harari inda Safeeya da ‘yarta suke tare da fad’in “Alajina zan shiga ciki, kasan yau ina cikin farin ciki saboda nasarar da yarana suka samu, ka san fa abun da ka jini ne, gado sukayi.”

 

Da wani murmushi a fuskarshi ya bi bayanta da kallo cike da so da k’aunarta, kamar yanda soyayya ta sa ya aureta haka yake da matuk’ar son farar mace, dalilin da ya sa ma kenan ya kutsa ya shiga lungu da sak’o ya zab’o buzuwa da ta amsa sunanta, gashi kuma kwalliya ta biya kud’in sabulu tunda har ta zama fitilar gidansa mai haska masa duk wani duhu.

 

Saida suka ga shigewarta kafin ya d’an gyara zamanshi yana matse fuska ya d’an kalli inda Safeeya take ya ga ko tana kallonshi ne, idansu na had’uwa ya szke had’e fuska kamar zai fashe, shi a dole kar ta kawo masa wargi duk da kuwa ya fi kowa saninta akan hak’uri da kau da kai. Murmushi kawai tayi ta d’anyi gyaran murya tace “Abban Hajia, ina ganin me zai hana ka je makarantarsu yaran nan ka ji me ye matsalar Saleema, ta yiwu akwai wani abun da bata ganewa?”

 

Cike da basarwa ya d’an kawar da kai yace “A idonki dai ba k’ok’arin da bana yi akan karatunsu, har malami na musamman na d’aukar musu da ke zuwa gida yana sake musu bitar abinda aka koya musu, a k’alla kowane dare yana d’aukar awa biyu a gidan nan, to idan ba ta fahimta yanzu ba sai yaushe?”

 

Jinjina kai tayi alamar gamsuwa tare da sassauta muryarta sosai tace” A kawo maka abinci ne?”

 

” Sai na yi wanka.” Ya fad’a ba yabo ba fallasa.

 

 

 

*Bayan wani lokaci*

 

 

Rashin damar zuwa da yau malamin na su bai samu ba yasa Alhaji Yusuf zaman dirshen yana koya musu karatun saboda jarabawar da zasu fara gobe ta zangon k’arshe, allon (ardoise) Saleema ya karb’a ya fara mata da lissafi, sosai ya rik’e allin kafin ya rubuta mata 4 a tara da 4 nawa zai bayar?

 

Cikin ikon Allah sai Saleema ta k’urawa rubutun ido tana kallo sam ta ji ta manta da komai ta yanda ta kasa fad’a da sauri, da yatsunta take ta k’idayawa yayin da yatsanta d’aya ke cikin bakinta tana ta motsa bakin. Kafin ta ankara Alhaji Yusuf ya d’auke fuskarta da wani mahaukacin mari yana fad’in “Dan ubanki wannan d’in ne ba zaki iya fad’a ba? Bari ki gani…”

 

Jawo k’afarta yayi bai kulada kukan data fashe da shi ba saboda girman da marin ya ma shekarunta guda goma ya matsata daf da shi, sake nuna mata rubutun yayi yace “Nawa ne nan dan uwarki?”

 

A kid’ime cike da son k’watar kanta tace “Biyar.”

 

Wani marin ya gaura mata yace “Wannan d’in ne biyar? Ubanki ke da biyar d’in.”

 

Kallon Hamdeeya yayi dake k’arama a cikinsu kuma yar shekara hud’u yace “Idan na tambayi Hamdeeya ta fad’a min wallahi ci miki uwa zan yi.”

 

Nunawa Hamdeeya yayi yace “Autata nawa ne nan? 4+4?”

 

D’an jim tayi sai kuma ta furta “8.”

 

Bai jira komai ba kam ya shiga jibgawa Saleema allonta tare da kikkifa mata mari yana fad’in “Me yake shiga kanki ne? Ke baki ji kunya ba yanzu? Wannan fa k’anwarki ce ta uku ma, ke ce babba a cikinsu amma ke ce dak’ik’iya mai k’walwar kifi.”

 

Da sauri Safeeya ta fito daga d’akinta gabanta na fad’uwa, ganin yanda yake dukanta ta ji ba dad’i sosai, a sanyaye tace” Haba Alhaji, a haka ta ya za ta fahimci abinda ka ke koya mata? Dukan ya yi yaw…”

 

A tsawace ya nunota da yatsa yace” Ke rufe min bakinki, dama na jima da fahimta ke kike d’aure mata gindi kina sakata lalaci, duba fa ki gani abinda ta kasa fad’a sai k’aramar k’anwarta ce ta fad’a, wannan ba abun kunya ba ne ?”

 

Ardayi da fitowarta kenan daga d’akinta ita ma tana jinme ke faruwa ta fito tana fad’in” Ta fad’i haka mana saboda bata so a koya mata ilimi, burinta ‘yarta ta zama kamar ita, wannan ma ai abun kunya gareka a ce kana fama da iyalinka akan karatu.”

 

Girgiza kai tayi cike da kissa tace” Karfa ka manta siyasa kake, ta ya za ka nuna iyalinka a haka bayan ba sa gane komai.”

 

Ta k’arashe tana hararen Safeeya, kallonta Safeeya tayi tace” Saboda ba ‘yarki ba ce ake duka ko? Ta hakane za’ a koya mata ana mata dukan mutuwar? Ko kuma a ganin ta hakane za ta fahimta?”

 

A hassale Yusuf yace” Koma dai menene ai gaskiya ta fad’a, saboda hakane fa yasa ko nunaki bana so na yi a matsayin iyalina, ba yanda zanyi ne tunda iyayena ne suka had’ani da ke, amma ‘yata dole na d’orata akan irin tsarina.”

 

Tsamm! Safeeya tayi tana kallonshi da mamakin kalamanshi, bai tab’ a kwatanta fad’a mata haka ba sai yau, me ya yi zafi daga magana har yake cizgata haka? Hawayen da suka malalo mata ne yasa ta saurin juyawa da sauri ta koma d’akinta, da harara ya bita tare da d’auke kanshi ya mayar kan Saleema wacce ke kuka kamar ranta zai fita, sake gyara zama ya yi alamar dai za sucigaba daga inda suka tsaya.

 

 

 

*Bayan sati d’aya*

 

 

 

A shirye dukansu suka fito cikin kyakyawar shiga, sai dai duka yaran na Ardayi riga da wndo ne na siket a jikinsu yayin da kawunansu ke bud’e sai dogon gashinsu da aka mishi fasalin kitso mai kyau. Daga cikin mota yake hangen yaran na tunkaroshi, tabbas ya fi son ‘ya’yan Ardayi, sai dai bai san me yasa ya fi son su ba, saboda kyawonsu da farar fatarsu ne? Ko kuma dai saboda ilinmunsu ne? Maida kallonshi yayi kan Saleema dake bayansu cikin shigarta ta doguwar rigar shadda da kyakyawan hijab d’inta, ba za ka kirata bak’a ba saboda tana da d’an haske, sai dai idan ta jera da su Hadeeya bak’a take komawa saboda haskensu, kyawu kuma ba’a magana dan ba wani kyan fuska gareta ba, shi mamaki ma yake wasu lokutan yanda Saleema ta zama jininshi, duba da shi dai yayi tashen kyawu a zamanin k’uruciyarsa, kuma har yanzu da yake da shekara arba’in da yan kai, sannan mahaifiyarta ma kyakyawa ce dan ta wata fuskar ta fi Ardayi kyau, duhu ne kawai gareta na fata wanda kuma yake k’ara fito da kyawunta. Amma Saleema ba kyan fuska ba hasken na fata, wanda daga shi har uwarta da ta yo d’aya daga cikinsu to fa da ita ma kyakyawa ce, ga kuma wani munin na daban wato rashin ilimi.

 

Drebanshi ne ya bud’e musu inda mahaifin na su ke zaune duk suka shiga, da fara’a ya amsa musu da “Kun gama shiryawa?”

 

“E Abba.” Suka fad’a kusan a tare, a hankali dreba ya fara jan motar suka fita a harabar gidan, cikin sanyayyar murya Saleema ta kalli mhaifin na ta tace “…

 

 

 

 

_Yan uwa barkanmu da sallah, da fatan Allah ya karb’i inadunmu yasa muna cikin ‘yantattun bayi, Allah ya gafarta mana zunubanmu._

 

 

 

 

*Alhamdulillah.*

1 Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!