Hausa Novels

Bakar Daula Hausa Novel Part 1

Bakar Daula Hausa Novel Part 1

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Bakar Daula Hausa Novel Part 1

 BAƘAR DAULA na Ameera Adam

 

 

©AMEERA ADAM

 

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

 

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

 

1

 

A duk lokacin da Allah (S.W.A) ya ƙaddara wanzuwar hallitar Ɗan adam a doran ƙasa, ko ya ƙi ko ya so akwai waɗansu abubuwa da suke yin jerin gwano a gangar jiki da ruhinsa. Inuwa! Wata aba ce da Ubangiji ya ke ƙaddara wanzuwarta manne a jikin kowanne abu, walau mai rai ko akasin haka. A kodayaushe tana bibiye da su matuƙar bawa zai zuba maganansa zai lura da haka. Kalmar ƙaddara! Kalma ce mai ɗauke da rassa biyu walau ƙaddara mai kyau ko kishiyarta. Ƙaddara abokiyar tagwaitakar inuwa ce domin bawa ba ya taɓa shallake wa ƙaddararsa, sanin haka ya sa na fahimci karin maganar Malam bahaushe ta: ‘Tun ran gini tun ran zane.” ta zauna ɗaram kwatankwacin yadda ake ɗora ƙwarya a gurbinta.

 

10/06/1022

Shekara Dubu Ɗaya baya.

 

Hankalinsa ya fi na kowanne lokaci kai wa matuƙar ƙolokuwar tashi, yana tafe yana taku da sandarsa Waziri da sauran muƙarraban cikin daular suna take masa baya. Tamkar waɗanda saƙon mutuwa ya dirar wa haka fuskokinsu suka fasalta saƙon da ke ƙunshe cikin birnin zuciyoyinsu. Sarki Damina yana kai ɗora ƙafarsa kan jan dutsen da ke a matsayin matattakalar benen hawa tsauni tsidik! Wani gajiyayyan talakansan ya dira a gabansa cikin firgice da tashin hankali, kuka yake tamkar hawayen idanunsa za su ƙare. Ya ruƙo ƙafafuwan Sarki Damina a ɗimauce yana faɗin, “Ya kai babban Sarki, Sarkin sarkunan duniya bakiɗaya sarkin da yake share mana hawaye. Ka taimaka ka roƙar mana afuwa wurin Sarauniya Sha-kundum, yanzu haka ɗana Rabo yana can yana aman jini ta hanci ta baki don mai ɗakina naƙuda take jini ya ɓalle mata tana gangarar…” Tun bai rufe baki ba Sarki Damina ya daka masa razananniyar ƙarar da sai da hantar cikinsa ta kaɗa, yana shirin sake magana Sarki ya fisgi takobin da ke maƙale a kafaɗar Waziri kafin Bawan ya yi wani yunƙuri tuni ya sauke kansa ƙasa. Da sauri wasu ƙaratan Dogarai suka ƙarasa wurin suka zube suna yi wa Sarki godiya, “Godiya muke Sarki Damina mai masoya da yawa, Sarauniya Sha-kunduma ta yi ruƙo da hannayenka. Haushin zuciyarta ya gushe domin ta faɗa mana hanyar maganin samun lafiyar Yarima, idan wannan bai wadatar da kai ba ka yi mana umarni mu kawo maka wani ko da a cikin mu ne ka sake datse rayuwarsa matuƙar zai sanyaya zuciyarka” Bai tanka musu ba ya miƙa wa Waziri takobin da ke ɗigar da jini, har sun cicciɓi gawar bawan da kansa tuni ta samu mutsuguni a gefen wata bishiya, Sarki ya dube su yana cewa. “A gaggauta ƙone gangar jikinsa tare da yaron nasa da ba shi da lafiya. Ita kuma mai ɗakinsa a zaro jaririn cikinta a kai wa babban dodo sannan a salwantar da gangar jikinta” Yana gama magana ya haye kan tsibirin maƙarrabansa suna biye da shi a baya.

 

Kamar yadda yake farillah a wurinsu duk lokacin da za su shiga cikin kogon dutsen a yanzu ma sai da suka aiwatar, sai da kowannensu ya saka ƙanƙanuwar aska ya yanki gefen ɗan yatsan hannunsa suka yarfar da jinin a jikin wani sassaƙaƙƙaen gunki, hannun gunki ɗauke yake da kwari da baka daga bayansa an jingina masa takobi a jiki. Kansa a sunkuye yake alamar ƙasƙantar da kai ga wani dungulmin kan mace da suka ɗora masa a gadon bayansa. Sarki Damina ne ya fara yin gaba sannan su Waziri suka rufa masa baya, daga bakin shiga dutsen suka tsaitsaya don sun san ko karan hauka ne ya cije su ba za su taɓa haure bakin ƙofar dutsen ba. Kai tsaye Sarki Damina ya kutsa ciki sandarsa ta zame masa abokiyar tafiya. Daga tsakiyar kogon dutsen ya hangi Boka Mai zamani zaune da wasu ƙanana tukwane a gabansa, daga shi sai ganyen ayaba wanda ya yi makari don rufe al’aurarsa.

 

“Yau ba ranar zuwan ka ba ce kamar yadda yake a bisa al’ada, me yake tafe da kai don na tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa.” Boka mai zamani ya faɗa yana karkatar da hankalinsa wurin Sarki Damina. Duk tsananin izza da taƙama irinta Sarki yau ya sauke ta a gefe ya fusakanci Boka yana mai bayyana damuwarsa, Sarki Damina ya zube gwiwowinsa kamar wanda ya aikata wani mummunan zunubin da yake neman gafara. Murya ɗauke da damuwa ya furta, “Ya kai Boka Mai zamani lamarin halin da talakawanmu suke ciki tabbas tura ta fara kai bango. A yau mun wayi gari da samun ɓillar annobar haɓo a cikin gari fiye da tsammani, babban abin da ya ɗugunzuma hankalina abin bai tsaya iya waje ba hatta ahalina na fuskantar wannan barazanar, a taimaka a roki Sarauniya Sha-kundum ta yafe mana tun da laifin wani ba ya taɓa shafar wani.” Boka mai zamani ya miƙa masa busasshen hannunsa mai ɗauke da zaƙwa-zaƙwan farata, taurin hannunsa tamkar busasshen katako sannan ya ce, “Ina tukwicin ziyarar Sarauniya Gunki Sha-kundum kafin na san abin yi? Domin sanin kanka ne tuni bakin alƙami ya riga da ya bushe.” Sai a lokacin Sarki Damina ya tuna da ƙoƙon tukwicin ziyara, cikin sake ƙanƙan da kai ya furta. “Sha-kundum ta dafa aikinka ta shiga lamuranka boka mai dogon zamani. Ka ga taka ka ga ta kakanninmu, iyayenmu duka sun wuce sun barka. Ya kai wannan boka mai dauwamamman ruhi da dogon zamani a yi mini afuwa bisa mantuwar da na yi, amma duk wani hukunci da Sha-kundum za ta yanke ni mai biyayya ne.” Boka na gama jin haka ya miƙe ya tunkari bakin wata rijiya wacce faɗinta ya fi girman ƙaramin ɗakin, yana zuwa ya fara taka matattakalar da ke cikinta ya shige. Shigarsa ke da wuya bakin rijiyar ya shafe tamkar ba a taɓa wanzar da komai a wurin ba. Yana shiga kai tsaye ya tunkari gunkin wata mace da ke tsaye da tulelen tsohon ciki a jikinta, hannunta ɗaya tallafe da tsohon cikin ɗayan kuma yana riƙe da garkuwa alamun ta kare kanta da shi. Sai da ya sunkuya ya miƙa gaisuwa sannan ya furta, “Ya ke Sarauniya sha-kundum! Ya ke mammallakiyar wannan Daular a yau ma na sake dawowa da neman yafiyar al’ummarki.Na tabbata kina saurarena kamar yadda kika daɗe kina jina. Haƙiƙa talakawanki sun dawo da wata buƙata domin a yau sun wayi gari da samun annobar haɓo shin wane taimako za ki yi musu?” Hawayen ne ya ziraro daga cikin idanun gunkin, boka ya ƙarasa ya kanga kunnensa a jikin ƙirjinta. Ya jima a haka sannan ya ɗago cike da girmamawa ya ce, “Tabbas zan isar musu kamar yadda kika buƙata, ki ƙara haƙuri nan ba da jimawa ba za ki dawo cikin ainihin hallitarki ta zahiri. Za ki ci gaba da mulkar al’ummarki kamar yadda kika mulke su a ɗaruruwan shekarun da suka gabata. Komai ya zo ƙarshe tun da ke kika tabbatar min da haka, sarauta da izzar mulki na baibaye da rayuwarki. Taɓewa da hallaka tana ga Maharba da Mafarauta har ƙarshen rayuwarsa.” Yana gama maganar ya juya jiki a sanyaye kamar kazar da aka jefa da gishiri, yana taka matattakalar bene ɗaya rijiyar ta fara dawowa kamar yadda take da farko a wurin.

 

Kan shimfiɗarsa ta farko ya koma ya zauna ya dubi Sarki Balarabe yana faɗin, “Ta faru ta ƙare…” Da sauri Sarki ya katse shi da cewar, “Allah sa ba laifinmu ne ya sake hauhawa ba.”

Littafan Hausa Guda 1000 Download
“Ka buɗe kunnenka da kyau ka saurari abin da Sha-kundum ta gaya min game da ku.” Boka mai zamani ya faɗa fuska babu walawa. Shiru Sarki ya yi yana sauraron Boka. “Tabbas Sarauniyarmu Sha-kundum ta sake dawo wa kamar yadda ta faɗa a lokacin da numfashin zai ɗauke…” Baki na rawa Sarki ya katse boka da cewar, “A ina aka wanzar da ruhinta? A wane yanki ne mu sa a kawo mana ita? Idan ta kai bangon duniya na rantse da hatsabibanci Sarauniya da izzar mulkina sai na sa an ɗaukota a faɗin duniya.” Boka ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya har yana birgima a ƙasa tamkar jakin da yake birgima a cikin sahara. Sarki sai da ya fusata ya doki ƙasa da tafin hannunsa sannan Boka mai zamani ya koma kan buzunsa ya furta, “Haba Sarki Damina ai duk gaggawar ungozoma ta bari a haihu, haka duk mai niyyar yin sammako ya bari duhun dare ya gifta. Sarki Damina a kwai gaggarumar matsala, kamar yadda duk faɗin garin nan babu wanda ya taɓa gani ko jin sautin Sarauniya Sha-kundum sai ni, to tabbas a wannan karon ko ni ba ni da masaniyar a ɓangaren da wannan sabuwar sarauniyar take. Babban abin baƙincikin ma waɗanda suka sulwantar mana da ruhinta a cikinsu halitar Saruniya ta sake wanzuwa…” Tun bai ƙarasa magana ba jikin Sarki Balarabe ya fara rawa kamar wanda ake kaɗa wa gangi, a fusace ya miƙe tsaye yana huci tamkar kumurcin macijin da ke tsaka da fusata. A fusace ya furta, “Boka mai zamani ka na nufin Sarauniyarmu ta ɓullo daga cikin zuri’ar maharba da mafarauta ne?” Boka ya jinjina kai yana faɗin, “Ba harsashe ba ne Damina domin Sha-kundum ta tabbatar mini kuma kai shaida ne bata taɓa yin ƙarya, ta ba ni muhimmin saƙo gare ku na farautar Maharba a ko ina suke a faɗin duniya. Sai dai babban tashin hankalin ta yi alƙawarin ba za ta sake magana ba har sai na sada da ta da ainihin ruhinta. A sanyaye Sarki Damina ya furta, “Tirƙashi! Ana dara ga dare ya yi. Bayan wannan ina tafe akan buƙatar Yarima Nomau, babban boka lamarin ciwon yaron nan a kullin ƙara ta’azzara yake. A da muna haɗa shi da ƴan mata ɗaya zuwa biyu a rana amma yanzu har ta kai ga mata biyu ba sa iya gamsar da shi, kafi kowa sanin shi kaɗai na mallaka kuma har abada ba zan sake haihuwa ba. Idan na tuna ba ni da magaji lamarin na sake ɗugunzuma hankalina.” Boka mai zamani ya hura ƙasar gabansa nan take wata ƴar ƙorama ta bayyana a wurin, sai da ya barbada wani garin magani sannan ya zura hannunsa ya warasu haɗe da runtse idanunsa tare da fara karanta waɗansu irin ɗalasuman tsafi, ƙirjin Sarki Damina ban da bugawa babu abin da yake yi saboda fargabar abin da Boka zai sanar da shi. Boka mai zamani ya jima a haka sannan ya buɗe idonsa yana kallon Sarki Damina haɗe da furta, “A kodayaushe maganar ɗaya ce! Kamar yadda na sanar maka Yarima Nomau ba zai taɓa warkewa ba matuƙar bai sadu da da inuwar wannan macen da nake gani a tattare da shi ba. Tabbas zai warke sai dai bazan taɓa ce maka ga wa’adin lokacin da zai ɗauka cikin wannan tuburewar ba. Na ga haske jingine da su daga inuwar yarinyar nan na ga akwai rabo a tsakani, sai dai ka fi kowa sanin yadda aka yi aka samu Yarima Nomau don haka idan har ya samu rabo da wannan yarinyar Ɗa ko Ƴar da za su haifa dole zai zama mallakin Babban dodo ne, idan ba haka ba duk daren daɗewa za su zama masifa a daular nan. Kuma wannan hasken ba komai yake bayyana mini ba illa kusantowar warakarsa, don na lura akwai yuwuwar samun waraka nan ba da jima wa ba.” Ajiyar zuciya Sarki ya yi don tun da yake zuwa wannan kogon bai taɓa jin labarin da ya faranta ransa kamar na wanan ranar ba Ya dubi Boka fuska ɗauke da murmushi ya furta, “Ya kai babban malamin madogararmu shin zan iya sanin wacece yarinyar nan kuma a wane yanki take?” Boka Mai zamani ya girgiza kai yana cewa, “Lamarin Yarima Nomau ya wuce duk yadda kake tsammani, daga ni har bokayen duniya babu wanda yake da wannan amsar don haka ina mai baka shawara kar ka wahalar da gangar jiki da ruhinka akan abin da babu takamaimar amsa. Wani hanzari ba gudu ba, daga bayan wannan inuwar na hango wata baƙar ƙura wacce ta lulluɓe sarararin samaniya sai dai ni kaina ban fahimci wacce irin ƙura ba ce koma dai wacce iri ce ina fatan za ta zame mana alkairi.” Sarki Damina ya miƙe ya fara zagaye cikin kogon dutsen sai da ya zagaye boka mai zamani sannan ya ce, “Wannan ba zai zame mana matsala ba domin mun dogara da Sarauniya Sha-kundum da babban dodo na tabbata su za su kawo mana waraka a rayuwa. Yanzu wanne irin magani ta ba mu wanda za mu aiwatar mu da al’umnarmu?”

 

Boka mai zamani ya miƙe ya ƙarasa bakin rijiyar ya miƙa hannu ciki nan take ruwan cikinta ta kawo har sama sannan ya ɗebi ruwan da ƙoƙo ya miƙa wa Sarki Damina yana faɗin, “Wannan ruwan a je a zuba shi cikin kogon Ɗanbille duk wanda wannan annobar ta same shi ya ɗauka ya sha kai koda bata kama mutum ba zai iya wanka domin yin rigakafi. Wannan ce iya maganar da ta umarce ni na sanar da ku don haka za ka iya tafiya ya sarkin sarakunan duniya.” Sanin ƙa’ida da dokar Sarauniya ya sa Sarki bai musa ba ya miƙe ba tare da ya furta koda kalma ɗaya ba, har ya je bakin ƙofa ya ji muryar Boka yana faɗin, “Ka da ka manta a kai wa Babban dodo Mai tsohon ciki biyu da idanun dattijai biyu.” Gyaɗa kai kawai Sarki ya fice daga kogon dutsen.

 

Garin Dabur

 

Daga cikin bukkar da nake kwance ina bacci na fara jin hayaniya sama-sama, ina yunƙuri tashin na ji muryar mahaifiyata ta karaɗe majiyar sautina da cewar, “Yau wacce baƙar rana muke gani da yammacin haka? Ya abar bauta kada ki yi fushi da wannan mummunan zunubin domin ba mu da sa hannu a ciki, ka hukunta masu wannan zunubin da gaggawa don sun cutar da ƴar tsintuwar da bata ji ba bata gani ba.” Ihun da Kandala take jerawa ne ya sa ni fito wa saboda duk wanda ya ji kukan nata ya san ba na lafiya ba ne. Jikina ne ya ɗauki tsuma sakamakon ganin halin da take ciki kace-kace da jini, a gefe ɗaya mutane daga jinsin maza da mata sun yi carko-carko a kanta suna kallon halin da take ciki. A gabanta na tsugunna raina ya kai ƙololuwar ɓaci, na dube ta fuska babu walwala na furta “Waye ya yi miki haka Kadala?” Ilahirin jikinta rawa ya ke don haka na kama hannunta na haɗa su da nawa na sake furta, “Babu abin da zai faru da ke ki gaya min waye ya yi miki haka?” Cikin yanayin azaba ta furta, “Ban san sunansa ba amma na ji wasu suna ce masa Barde.” Ban jira ragowar maganar ta ba saboda tun farkon ganin halin da take ciki shi ne mutum ba farko da ya fara faɗo min a rai, saboda sanin hali ya fi sanin kama. Barde riƙaƙƙen ɗan akuya ne baya iya kwana biyu ba tare da ya kusanci wala macen bil’adam ko dabba ba.

 

Ina miƙe wa na riski muryar Goga ya fara fito yana busa ƙaho wanda yake alamtawa sauran ƴan uwa na nesa da na kusa akwai fita ta gaggawa. Kafin ya gama busar da yake tuni gidanmu ya cika damƙam da sauran ƴan uwa maharba da mafarauta kowanne yana tafe cikin shirin dawa, ɗaya bayan ɗaya na kalle su kowannen su yana jiran umarnin da zan bayar. Jin na yi shiru ya sa Goje ya ɗaga gorarsa sama da hannun ɗaya, ɗayan hannun mai riƙe da kwari da baka ya sauke ya fara zabga mini kirari. “Burugu ce da kanta ba aike ba mace mai kamar maza ko cikin maza sai an tona. Cau cau cau cau ƙurungu mugun kifi sa’a a dawa sa’a a cikin gari wani aiki sai jan wuya makutsa daji, a lafiya uwar gidan kere amanar kura kyaci da gashi. Dawa dai, dawa gidan maza tsanani yana dajin Gurɓu ku bar faɗa musu wahalar sanar da su daɗin maza na cikin dawa mata na gida suna yin girki, wuya a dajin gwiɓau wuya a dajin fatalaki wuya ta ƙare a kan Barde yau ya taɓo ajalinsa.” Ilahirin jikina ban da rawa babu abin da yake yi saboda tsumin da ya tayar min har nake jin da ace Barde na gabana babu abin da zai hana ban tsarge ruhinsa gida biyu ba, duk da kowa ya san Barde a cikin garinmu ba kanwar lasa ba ne.

 

Da sauri na faɗa bukkarmu na ɗabo gurun damatsan hannuwana da wuya, na kunce fatar mesar da ke ɗaure a ƙuguna na ɗaura ta damisa sannan na ɗauko kwari da baka haɗe da zabgegiyar adda na fito wurin da su Goga suke tsaitsaye. Suna ganina suka yi yunƙurin saka kai a hanzarce na dakatar da cewar, “Wannan fitar ba taku ba ce saboda Barde gidanmu ya taɓo ba ku ba, na yi rantsuwa da abar bauta ba zan dawo gida ba sai na sauke kan Barde daga gangar jikinsa, weeeehuuuuhuuuuu sai ni sarauniyar baka jikar marigayi Baushe amanar kura kawanciyarka ka huta muna tafe idan dabbobi sun ƙare. Sai ni yaƙi ban san wasa ba Abar bauta ta buɗa mana matuƙar na saka kai ko yau ko yanzu ban san namiji ba sai na ga tabo a jikinsa, wahala a hanyar tugu wuya a hanyar badake wuya ko da magani babu daɗi ko ana ha maza ha mata sai na dawo da kan Barde a hannuna.” Ina gama zabga kirari cikin haɗin baki tawagar da ke wurin suka furta, “Dawa dai Sarauniyar kwari da baka, Abar bauta ta buɗa miki a dajin Gurɓu.” Har na saka kai zan fita na dawo wurin Mahaifiyata na russuna saitin kunnenta ina faɗin, “Ki roƙar mini abar bauta da ta rinjayi ɗayan ruhin kar ya ziyarce ni ina tsoron kada Barde ya yi nasara akaina.” Cike da ƙwarin gwiwa ta furta min, “Sa’a dai Sarauniya abar bauta ta buɗa miki ɓoyayyan ruhi ba zai ƙara ziyartar ki ba.” Ina gama sauraronta na fice daga cikin gidan cike da ƙwarin gwiwa na nufi wurin da na tabbatar Barde na zama da ƴan koronsa.

 

Daular Sarki Damina.

 

Daga kogon boka mai zamani ya so kai ziyara bukkar babban dodo amma sai ya ga mafi dacewa ya fara zuwa wurin al’ummarsa ya umarci rundunar mayaƙansa da su fita yi masa farautar duk wata halitar bil’adam, musamman daga tsagin maharba da mafarauta kamar yadda suka saba yi a baya. A tsaitsaye suke dubbanin mutanen daular don a zatonsu maganin warakar annobar da ke damunsu aka kawo musu, Waziri ne ya yi gyaran murya sannan ya furta, “Ya ku waɗannan jama’a ya kamata kowa ya nutsu don jin saƙon da Sarauniya sha-kundum ta aiko.” Tamkar ɗaukewar ruwan sama haka wurin ya yi tsit, Sarki Damina ya yi gyaran murya sannan ya dube su ɗaya bayan ɗaya ya sanar da su duk yadda suka yi da boka Mai zamani sannan ya ɗora da cewa, “Ina umartar manyan mayaƙan dakarun daular nan da su hanzarta fita cikin gaggauwa don yi mana farautar bayi kamar yadda suka saba a baya, kuma su yi sani cewa ya zama wajibi su farmako mana La’anannun hallitar can ta maharba da mafarauta a ko ina suke a faɗin duniya. Wannan umarni ne daga Sarauniya sha-kundum idan ba haka ba bala’in da muka shiga da wanda muke ciki a yanzu shafar mai ne akan abin da zai faru da mu a gaba.” Yana rufe baki zaratan dakarun mayaƙan suka fara fita a guje zuwa mahallansu kowanne na fito wa da manyan makamai, runduna guda suka yi tsaya a gaban sarki Damina. Sai da ya ƙare musu kallo sannan ya kasa su gida huɗu, manyan zaratan mayaƙan ya ce su bi gabas hanyar da za ta sada su da ƙasar Dabur. Runduna ta biyu ya ce su bi Yamma hanyar da za ta sada su da ƙasar Baƙasud, runduna ta uku ya ce su bi kudu hanyar da za ta sada su da ƙasar Mubali sai tawaga ta huɗu da ya umarce su da Arewa wacce za su isa da Ƙasar Surima. Lokaci ɗaya suka bazama a yunwace da farauto kowanne irin bil’adam kamar yadda Sarkin da yake mulkarsu ya ba su umarni.

 

 

*KU MATSO KU TAHO*💃🏼

 

Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananjn ban tausayi😰 ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂

 

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.

 

Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼

Karanta Littafin Jariri Hausa Novel

Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera ‘yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰

Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na’isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba’a nuna masa hanya, sa’a dai ‘yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER’S* Amanar Marubuta La’ilaha’illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚

 

*Ummou Aslam Bint Adam*🌚

[12/10, 2:15 pm] +234 813 916 3088: *BAƘAR DAULA*

 

 

©AMEERA ADAM

 

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

 

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

 

2

 

Fita ta ke da wuya na ci karo da Mahaifina da ya sawo kai ciki kafaɗarsa maƙale da barewa da ingarman zaki, ganin yanayina ya tabbatarsa masa akwai wani abu da yake faruwa don ya san fitarsa ban yi da shi zan shiga dawa ba. Cike da ladabi na miƙa masa gaisuwa irin tamu ta maharba ina faɗin, “Dawa dai Sarkin sarakuna uban dawa ga tsini ga mashi, ina gwanin wani ga nawa gamji kake ka fi ƙarfin saran maƙiya ɗan butar uban nan. A lafiya garnaƙaƙi uƙubar Gabatarawa, Abar bauta ta buɗa maka ka ci gaba da maganin munafukan mafarauta, sha zamanka ka ci gaba da kai dabbobi ƙasa wallahi ko yau ko gobe ko baka nan muna yi maka yaƙi.” Cikin jin daɗi Mahaifina ya jingina gorar hannunsa da tawa sannan ya furta, “Dawa dai Sarauniya Abar bauta ta buɗa miki ko dare ko rana a dokar daji. Cau cau cau amanar Baushe wata wuyar sai a tsakiyar tsaunin Mani.” Ɗora kokarata na yi a wuya na saɓi hanya tare da furta, “Sa’a dai ruwan saman mai dukan basarake da faƙiri, shawarar Duba amanar Duna.” Kai tsaye mazaunin Barde na tunkara da ke cikin ƙasurgumin dajin Gurɓu, duhun almuru har ya fara karaɗe gari don haka na ƙara ƙaimi domin na cin musu don ba na son Barde ya sake shaƙar doguwar iskar numfashi.

 

Ganin dajin na sake yi min nisa kuma ina gudun rasa Barde a yammacin, ya sa na lalubi ramin bushiya cikin nasara na fisgota da ƙarfi tsiya, ƴar ƙaramar aska na ciro ya tsaga bayanta sannan lalubi ganyan tunfafiya na murje a bayanta, na damƙi ƙayoyi na soka a tsakiyar kanta. Sai da na kalli kusurwa huɗu da ita a hannuna sannan na saita hanyar da za ta sada ta da mazaunin su Barde na dire ta a ƙasa tare da furta, “Bisa ga Barde amanar Lado, ko tsuntsu kika gani kar ki bar shi ya kubce.”

 

Tun ban rufe baki ba ta zabura da matsanancin gudu sannan na rufa wa sawunta baya. A lokacin da na ƙarasa wurinsu tuni na riski zaren carbin rayuwarsu ya kusa tsinkewa, ilahirin jikinsu ƙayoyi ne kwatankwacin yadda suke lulluɓe a jikin bushiyar da na aika musu, ganina ya harzuƙa Barde ya dube ni cikin huci yana cewa, “Uwar dawa me ye haɗina da ke da za ki aikata min haka ina cikin shaƙatawata? Ba don ina ganin mutumcinki ba da tuni na roki Abar bauta ta la’anci ruhinki kamar yadda kullin muke yi wa Baƙar Daula wannan addu’ar…” Tun bai rufe baki ba na ƙarasa wurinsa haɗe da yi masa mahangurɓar da ta kusa gigita lissafin rayuwarsa, a fusace na sake kai masa duka a maƙoshi ina faɗin, “Barde yau akuyancinka ya kai ka wurin da ba za ka sake sanin wata ƴa mace ba sai a rayuwarka ta gaba idan ka na da rabo, ka roƙi Abar bauta da ta yafe maka zunubinka wataƙila ka samu sauyi a rayuwar da za ka dawo nan gaba.” Wata sakaran dariya Barde ya saki sannan ya ce, “Wai kina nufin ƴar shilar da na latsa ta gidan ku ce? Ya aka yi haka bayan na san ke kaɗai kika wanzu a cikin gidanku?” Ban ba shi amsa ba sai wani mahaukacin duka da riƙa kai masa ta ko ina, ganin haka ya sa ya damƙi ƙasar gabansa haɗe da ɗaukan cinnaka ya ɗora a kai ya dunƙule su wuri ɗaya sannan ya ɗaga hannunsa sama ban yi aune ba na ji ya watso min ƙasar da ta rikiɗe zuwa jinsin cinnaku. Nan take muka fara sabon artabu kowanne yana son nuna ƙwarewarsa da ƙarfin jarumta da na tsatsuba, ganin hanyar da ya ɓullo da ita ba mai ɓille wa ba ce ya sa ya dube ni cikin hakki yana faɗin, “Kin cika zabuwa mai tsoro don na tabbata da ace ƙarfin damtse za mu gwada babu abin da zai hana ban yi nasara a kan ki ba, ya ke ƙasƙantacciya la’ananniya marar rabo, ya ke gajiyayyiya watsatssiya ƴar taka hayen maharba ba ƴat na koya ba. Wallahi ko giwa ta yi mushe ta fi ƙarfin bakin karnuka, dawa dai dawa ga mazaje ba mata ba Aradu mai tarwatsa ƙananan la’anannu ni Barde kabari nake duk daren daɗewa ina sauraronka.” Wata irin kuɗa na ji har tsakiyar kaina yayin da maganganun Barde suka fara amsa-amo a majiyar sautina, daga bayana na fara jiyo sautin haniniyar dawakai tare da ƙarar ƙarafa da miyagun makamai, sannu a hankali na waiga don ko kaɗan na ƙi jinin wannan yanayin da nake riskar rayuwata a ciki. A duk lokacin da wannan yanayin ya riske ni na kan gaza sarrafa gangar jiki da ruhina don na banzatar da abin da nake gani a zahiri ba tare da wanda nake mu’amala da su sun riski abin da nake tozali da shi ba. Kamar wacce guguwa take fisga haka na riƙa jin ana fisgar gangar jikin da ke jingine da ruhina zuwa ga mayaƙan da nake riska suna tunkaro ni gadan-gadan, a koyaushe ina jin baƙincikin yadda nake yaƙar ƴan uwana wato jinsin Maharba da Mafarauta waɗanda su ne nake ganin rundunarsu cikin ƙwayar idona.

 

Ƙaddara wata abada ce da take sarƙe da gangar jiki da ruhi! Ni tawa ƙaddarar salonta mai tafiyar kura ne, ko a tarihi ban taɓa riskar makamanciyar irin tawa ƙaddarar ba.

Na fito daga cikin jinsin Maharba da Mafaruta, don haka na fi jin daɗin rayuwar cikin dabbobin daji akan mutane. Sai dai kash! Na tsinci ruhina a jikin wani gangar jikin da ba ta ahalina na Maharba ba, na rasa yadda aka yi nake iya rayuwa cikin jinsi biyu. Ko na aikata wani mummunan zunubin a rayuwata ta baya ban sani ba? Idan haka ne na cancanci hukunci irin wannan tun da gangar jikin da nake rayuwa da ita bata ji ba bata gani ba? Ban gama zayyana wa kaina jerun gwanon tambayoyin ba na hangi yadda suka zagaye ni tamkar yadda ale zagaye bakin rijiya, kamar yadda kullin nake ji a wannan karon haka gangar jikina ta riƙa ingiza ruhina ba don na so ba tafi da gudu na riƙa kai sara ina kare kaina. Da alama Barde mamakin abin da nake aikatawa yake don duk wanda yake tare da ni ba ya gani ko fuskantar abin da nake gani a maganaina. Ganin ya samu wannan damar ya sa ya biyo ta bayana a zabga min sara a kafaɗata, wanda fitar jini daga jikina ya haddasa wata irin gigitacciyar tsawa a dajin kamar yadda yake faruwa a duk lokacin da jini ya fita daga jikina. Abin sai ya haɗe min hagu da dama don na rasa wanne daga ciki zan kare duba da rundunar dake kawo min sara ga Barde da yake niyyar yin galaba a kaina. Ban yi aune ba wata irin juya ta fara katantawa da ni tun iya daga tsaye har na gagara mallakar kaina, wani saran na sake riska a gadon bayana wanda silar haka ya sa na durƙushe a wurin ga rundunar da ke gabana na son hallaka ni nan take.

 

Daular Sarki Damina.

 

Bayan watsewar tawagar rundunar mayaƙan Sarki Damina, daga harabar wurin kai tsaye keɓaɓɓan gida ya nufa wurin da Yarima yake rayuwarsa a ciki. Gidan an keɓe shi ga Yarima kaɗai saboda gata da kulawar da ake bashi sakamakon mummunar larurar da yake fama da ita, idan kuka zauna kuna ma’amala da shi ba za ka taɓa tsammanin yana da wannan ciwon ba har sai ya motsa za ka tabbatar da haka. Tun daga bakin ƙofar gidan har zuwa ƙofar ɗakin Yarima Maza ne suke gadinsa sakamakon mummunar lalurar da yake tare da ita, wannan dalilin ya sa hatta masu yi masa hidima maza ne don gudun abin da kaje-ya-zo. Saboda kafin a farga da lulararsa a baya mata ne suke yi masa hidima wani abin mamaki duk ranar da aka wayi gari sai an samu gawarwakin ƴanmata waɗanda ya yi musu fyaɗe, waɗansu su galabaita gudun ƙarin wahala Sarki ya sa a ƙonne su ko a binne su da ransu. Ba wannan ne dalilin da ya sa Sarki Damina ya kwashe mata ya sa aka zuba masa maza ba, saboda duk wani abu da zai faranta ran Yarima shi ya ke so bai da mu ba ko da matan yankin za su ƙare. A lokaci wata jarabta ce ta same su matan daular suka daina haihuwar ƴaƴa mata sai maza, wannan ne ya fargar da Sarki Damina ya taka tsibirin Boka mai zamani ya tuntuɓe shi game da haka, nan take ya sanar masa da matuƙar Yarima zai ci gaba da salwantar da rayuwar ƙanana yara mata tabbas za su wayi da ƙarewar ƴaƴa mata a gabaɗaya yankin. Idan kuwa haka ta kasance Sha-kundum za ta yi fushi da su fushi mai tsanani. Wannan dalilin ya sa Sarki yake saka ake zaɓar cikakkun mata da ƴan matan da suka isa ake kaiwa Yarima duk lokacin da larurarsa ta motsa.

 

Shigar Sarki ɗakin ya tarar da Yarima na ta wani irin kakari tamkar wanda yake gargarar mutuwa, hakan ce take faruwa a duk lokacin da larurar Yarima ta tashi idan ka ga yana wannan halin sai ka rantse ba zai ƙara rayuwa ba. Cike da tausayawa Mahaifinsa ya ƙarasa gabansa yana zura masa ido, duk dakiya irinta Sarki Damina sai da ya zubda masa ƙwallah. A haukace Yarima ya cakumo Mahaifinsa cikin fitar hayyaci da ɗimauta yana yunƙurin haike masa, da sauri Sarki Damina ya fara yunƙurin ƙwatar kansa amma tsananin ƙarfi irin na Yarima ya sa ya kasa, a kan dole dogarawan da ke kewaye da ɗakin suka runƙuro suka taimaka wa Mai martaba. A wahalce Sarki ya ke sauke ajiyar zuciya sannan ya furta, “Ku ɗebo masa ƴan mata biyar don ba na son na rasa yarima, shi kaɗai na mallaka ko matan garin nan za su ƙare sai an nemo masa wasu a faɗin duniyar nan.” Tun bai kai ga rufe baki ba wata gihitacciyar tsawa ta ratsa ciki da wajen ma’adanar sautinsu. A razane Yarima ya rungume mahaifinsa don wannan ita ce tsawa karo ta biyar da suka sake riskar irinta. A baya duk ranar da aka yi musu tsawa irin wannan lokaci ɗayamatan Daular suka riskar kansu cikin ɓallewar jinin Al’ada har tsofaffi waɗanda lokacin yin su ya gushe musu, a gaggauce ya fita don isa ga bukkar babban Dodo don ya sanar musu wannan tsawar da wacce irin masifa ta zo musu. A daidai ƙofar keɓantaccan gidan Yarima ya tsaya ya ɗaga kansa yana kallon sararin samaniya, kururuwar dattijuwar ce ta dawo da shi daga duniyar harsashen da yake yi. Waɗansu manyan barada ne riƙe da gashin wata mai tsohon ciki da alama naƙuda take jini na bin ƙafarta, ɗayan yana riƙe da wani matashin saurayi da fuskarsa ke fidda habbon jini daga hancinsa. Tsohuwar na riƙe da su ana jan su tare tana kururuwa da roƙon Dogaran akan kar su aiwatar da abin da Sarki ya umarce su, gyaran murya ya yi lokaci ɗaya Dogarawan suka tsaya cak kamar waɗanda suka haɗiyi taɓare nan take. Bawan da ke tsugunne a gabansa ne ya lura da inkiyar da Sarki ya yi don haka ya furta musu, “Sarki na buƙatar ganin ku a gabansa.” A gaggauce suka ƙarasa gabansa bisa lura da yanayinsa suka fahimci ƙarin haske yake nema game da busasshiyar tsohuwar da take riƙe da mutanen da ya bayar da umarni a binne su. Wani narkeken Dogari mai ƙirar samudawa ne ya kwanta a gaban Sarki Damina, sai da ya lashi saman ƙafarsa sau bakwai sannan ya yi sujjada a gabansa yana faɗin.

 

“Abar bauta ta ja da zamanin adalin Sarki mai cikakken iko. Wannan tsohuwar mahaifiyar baiwarcen ce, muna ƙoƙarin cika umarninka ta nemi…” Bai ƙarasa maganarsa ba Sarki Damina ya ɗaga masa hannu tare da faɗin, “A kawo min ita.” Tun Sarki bai gama maganar ba Tsohuwar ta yunƙura cikin tsananin firgici, ganyen da ke maƙale a ƙugunta wanda ya kasance shi ne tufafin da suke rufe al’aurar su, tuni ya samu matsuguni a ƙasa. Tun daga sama har ƙasa gudawa ce take bin ƙafafuwanta, jan ciki ta fara yi cike da tashin hankali da nadama tana cewa. “Ya Abar bauta ki yi gaggawar kawo min mafita daga wannan baƙin zalincin azzalumin bawan na ki.” Da ƙarfin gaske Dogarin ya ƙarasa ya fisgi ƙafarta ɗaya wacce nan take ta yi ƙara ƙaras! Da alama ya karya ta ya fara ja bai dire ta ko ina ba sai a gaban Sarki Damina. Sandar da ke hannunsa ya saka ya dokare wuyanta nan take ta fara kakari sannan ya miƙa hannu zuwa idanunta, zaƙwa-zaƙwan faratansa ya saka ya zaro ƙwayar idanunta nan take ta ƙwalla wata gigitacciyar ƙara jini ya wanke fuskarta. A cikin wani ƙanƙanin ƙoƙo ya jefa ƙwayar idon sannan ya yi gaba, Fadawan da ke take masa baya ne suka bi shi sannan ya juyo ya ce, “Kada a binne ta a kaina ɗakin zuma ta ƙarasa tsokar jikinta.” Daga haka kai tsaye ya wuce Bukkar babban dodo don lamarin tsawar da ta saba haddasa musu tashin hankali ba ƙaramin tsinka hantar cikinsa ta yi ba.

 

Tattakawa ya yi har ya shige gidan ƙasa wanda a nan ne bukkar babban dodo ta samu matsuguni, sai da ya yi sujjada sau bakwai a gaban bukkar sannan ya zura idanun tsohuwar a wata ƙanƙanuwar ƙoramar da ke gefen bukkar. Ta gefen tagar ya fara zayyane buƙatar da ke tafe da shi, sai da ya gama bayanin matsalolinsa daga cikin bukkar aka fara magana da wani irin yare cikin murya mai matuƙar ban tsoro. Ga wanda zuwansa ne na farko a lokacin da ya saurari muryar za ta iya kurumta sauraronsa, sai da aka yi yare sama da goma sannan aka fara maganar cikin harshen hausa.

 

“Tabbas jinin sarauniya Sha-kundum ne yake zuba a daidai wannan lokacin, hasalima rayuwarta tana cikin wani hali. Rasa rayuwarta a karo na biyu tamkar rushewar daular na ne gabaɗaya, na yi rantsuwa da tsabbun da na gada a wurin iyaye da kakannina matuƙar sakacinku ya sa kuka sake rasa Sha-kundum shakka babu kun rinƙa ganin masifu kala-kala kenan har ƙarshen rayuwarku.” Hankalin Sarki Damuna ya fi na kowanne lokaci tashi, ga rabuwar shawarwari da ya samu daga wurin Boka mai zamani da babban dodo. Cikin damuwa ya furta, “Ya babban Dodo mai share mana hawaye kai ne mai ciyar da mu da shayar da mu a wane yanki wannan Sarauniya tamu take saboda na…” A tsawace aka furta, “Idan za ka zagaye faɗin duniya babu wanda zai tabbatar maka a nahiyar da take. Hasali ko da za ka yi tozali da ita ba za tantance fa ba sai dai alamu su nuna mana da isowarta ga mahaifarta, a kaf faɗin duniyar nan Boka Mai zamani ne kaɗai ya san kalar surar Sarauniya Sha-kundum kasamakon abin da ya faru a shekara ɗari biyar baya da suka shuɗe, kuma ko da ta ƙaraso daular nan ba na jin jinin da ta sake wanzuwa a ciki na Maharba da Mafarauta zai bar jinin daular nan ya yi tasiri a jikinta. Sarainiyarku ta sake wanzuwa a cikin jinsin Maharba da Mafarauta, haka kundin ƙaddarar yake don haka ba mu da damar ninke babin ƙaddararta. Game da lalurar matan Daular nan ka ɗauki Mahaifiyarka mai babbar turaka kai ta wurin Yarima ya mu’amalanceta ni nake gaya maka ciwonsa zai daɗe bai sake tashi ba kuma munanan al’amura za su jima ba su sake faruwa ba. Idan ya gama ka kawo min dattin al’aurarsu zan taimaka muku na yi wani aiki da shi amma idan na gama haɗa shi wajibinka ne ka sadu da Mahaifiyarka domin kammalar aikin bakiɗaya.”

 

Ajiyar zuciya Sarki ya sauke sannan ya furta, “A duk lokacin da aka ambaci wannan jinsi na Maharba zuciyata da raina na matuƙar ɓaci, amma babu komai haka shafin ƙaddarar yake za mu karɓe shi hannu bibbiyu. Ya kai babban dodon mai azurta wannan daular ka yi sani ko jinin Mahaifiyata ka ce na bawa Yarima zan bashi matuƙar sarautar nan ba za ta kuɓuce daga ahalina ba.” Yana gama maganar ya sake yin sujjada sau bakwai sannan ya fice daga bukkar, kai tsaye ya wuce gidan mahaifiyarsa da suke yi mata laƙabi da mai babbar turaka. Yana shiga bayin da ke yi mata hidima suka fice don haka suke yi a duk lokacin da Sarki Damina ya ziyarce ta duk da sun fahimci a mafi yawan lokuta zuwansa ba alheri ba ne. Mahaifiyarsa Ladi na ganinsa gabanta ya faɗi tana shirin yin magana ya ce, “Ta so mu je na sadaki fa yarima.” Idanunta ne ya ciko da ƙwalla ta ce, “Har gobe ba zan daina dana-sanin haihuwarka ba Damina, Mai martaba ya cuce ni shi da baƙon bafulatani…” Bata rufe baki ba Sarki Damina ya fisgi hannunta daga wurin da take zaune ya furta, “Saboda kin ci darajar Mahaifiyata shi ya sa na tako da kaina, wannan girma ne da daraja na baki da a cikin bayi ne Dogarai zan aika musu. Ki gode wa Abar bauta da ba dauwama za ki yi da Yarima yana mu’amala da ke ba, babban dodo ya kawo mana waraka ko ki taso ko na sa dogarai su fitar min da ke.”

 

Hmmmm Wace ce sha-kundum kuma meye alaƙarta da ƴar maharba? Waye baƙon Bafulatani? Kuma ƴar maharba na mutuwa ko yaya? Me ye silar ciwon yarima kuma yaushe zai warke? Amsoshin na gaba ku dai kar ku bari a yi babu ku🏂💃🏼

 

Na gaishe ku kyauta Cau cau cau cau, Allah buɗa mana fans🏂

 

*KU MATSO KU TAHO*💃🏼

 

Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananjn ban tausayi😰 ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂

 

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.

 

Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼

 

Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera ‘yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰

Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na’isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba’a nuna masa hanya, sa’a dai ‘yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER’S* Amanar Marubuta La’ilaha’illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚

 

*Ummou Aslam Bint Adam*🌚

[12/10, 2:17 pm] +234 813 916 3088: *BAƘAR DAULA*

 

 

©AMEERA ADAM

 

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

 

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

 

3

 

 

*KU MATSO KU TAHO*💃🏼

 

Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananin ban tausayi😰 ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂

 

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.

 

Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼

 

Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera ‘yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰

Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na’isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba’a nuna masa hanya, sa’a dai ‘yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER’S* Amanar Marubuta La’ilaha’illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚

 

Takunsa mai girgiza hankulan ƙananan dakuru ne ya karaɗe majiyar sautina, haniniyar dokinsa ta musamman ce a duk lokacin da ya ziyarce ni don ya kasance zara a cikin dubbannin taurari. A kodayaushe na kan rasa wane ne shi da yake faɗo wa cikin duniyata har ya kawo mata agaji a duk lokacin da nake yunƙurin sare wa da miƙa wuya ga mutuwa. Idanuwan suna kan fuskarsa ya yin da na faɗa duniyar tunanin samuwarsa, ban yi tsammani ba na riski sautinsa ya karaɗe dodon kunnena yana faɗin. “Sare wa da rashin nasara ba taki ba ce, a kullin ina gaya miki ke ɗin mai nasara ce! Ke ta daban ce don haka rayuwarki ma ta daban ce! Don haka kada ki sallama wa mutuwa rayuwarki don ba ki cancanci mutuwa yanzu ba, ki taimaka ki cika muradi da burinki. Surarki, nasabarki, tsatsonki, zuciyarki da asalinki ba sa daga cikin jerin masu rauni.” Nutsuwata da hankalina gabaɗaya na sallama masa ina sauraron maganganun da yake furta min, ba yau na saba jin haka daga gare shi ba sai dai kalaman yau sun sha bambam da waɗanda yake sanar min. Ina yunƙurin yi masa magana cikin tsawa na ji ya furta, “Ki tashi na ce ki aiwatar da ƙudurunki cikin jarumta domin ke ba ki kasance gajiyayyiya ba.” Tamkar wacce aka ƙarawa ƙaimi haka na ji wani masifaffan ƙarfi ya mamaye ilahirin jikina, a zabure na waiga wurin Barde da ya yi yunƙurin kawo min duka sai dai ɓarin makauniyar da na yi masa a fuska ne ya azabtar da ruhinsa. Ƙaraji yake tamkar wanda ake zare wa rai saboda azaba, kamar yadda na ƙudura a zuciyata haka na sake jadaddawa. Daga jikin ƙuguna na zaro wata ƙanƙanuwar wuƙa na ƙarasa gaban Barde kafin ya yi wani yunƙuri na kauda kai gefe haɗe da tsige al’aurarsa daga gangar jikinsa. Maƙarrabansa su baƙi-baƙi na ganin haka kowannensu ya cika wandonsa da iska saboda sun lura a yunwace nake da su ina iya tsalle na dira a gabansu na yi musu makamancin abin da na yi wa Barde, saboda duk tafiyarsu ɗaya hallayarsu ɗaya duka tare suke aikata kowanne irin ɓarna sai dai Barde ya fi su yin ƙaurin suna wurin aikata badaƙala.

 

Ina yunƙurin juya wa wurun tawagar da ke farmakar rayuwa na neme su na rasa tamkar ɗaukewar ruwan sama, jinin da ke ci gaba da zuba daga jikina ne ya haddasa min raunin garkuwar jikina, na fara takawa ina layi ga idanuna da suke yi mini dishi-dishi har ta kai ba na iya bambamce takamaimar hanyar da zan bi na koma ga muhallina. Kwatsam! Ban yi aune ba na ji na faɗa jikin makamanciyar halitata ta bil’adam wanda hakan ya haddasa min sakin ragowar jikina a jikinsa. Muryarsa ba baƙuwa ba ce a gare ni hasali ma takan faranta zuciyata domin shi ɗin wani ɓangare ne daga tsakin zuciyata, ya kasance jini da tsokata ta yadda a kowanne hali nake ciki ina iya tabbatar da siffarsa mai cikar haiba da kamala. Idanuwana ne suka fara lumshewa, na riski ya huro min iskar bakinsa akan fuskata yana faɗin, “Abar bauta ta dafa miki a duk lamuranki ya ke sarauniyar maharba amanar Goje, ba kyau ba daɗi murucin kan dutse baki fito ba sai da kika shirya. Wane Mutum wawan mutum rana mai haske duniya kowa ya ƙarasa a bar shi ya kawo ƴar tsatson maharba. Cau cau cau cau sai ke Damisa amanar Duna, da wuya a dajin Gurɓu da wuya a dajin Dagumba wata wuyar sai mun tsallaka dajin Bagege. A lafiya shawarar Goga a lafiya amanar Goga, a lafiya wakiliyar Goga ko yau ko gobe kwarankwatsa dubu ko bakya nan ina yi miki yaƙi.” Kirarinsa ne ya sake ƙarfafa zuciyata na ɗago a wahalce na jingina kerena (Ɗaya daga cikin makamin maharba ne.) A jikin Barandaminsa cikin amsa gaisuwa irin tamu ta Maharba na furta, “Sa’a dai mai dawa amanar Shamuwa amana sai ɗan amana, amana ta kai maka har dajin Gaduru.” Ina rufe baki ya cicciɓe ni ya ɗora a kafaɗa sannan ya wuce gida da ni. Tun a cikin dajin na ji yana yagar ganyayen magunguna da zan yi amfani da su, muna ƙarasawa gida aka kwantar da ni akan fatar kura wacce ta zame mana mashinfiɗin da muke hutawa. Hayaniya ce ta fara tashi a wurin matasa maza da mata suka cika damƙam, ganin halin da nake ciki ya sa Mahaifina ya sallami sauran mutanen da ke tsaitsaye a kaina, cike da takaici ya tsugunna a daidai kaina ya yin da ya yi tozali da irin jini da yake fita daga jikina sakamakon mummunan saran da Barde ya yi, yanayin fuskarsa ne ya bayyana min ɓacin ran da ya ziyarci zuciyarsa. Runtse ido ya yi ya furzar da iska mai zafi sannan ya furta, “Abar bauta ta ci gaba da dafa wa lamuranki ya ke sarauniya. Haƙiƙa ina baƙinciki raunin da yake ziyartar ruhinki, wanda dalilin haka yake sa a yi yunƙurin yin galaba a kan ki.” Hannunsa na kama da hannuwana biyu, ina jin hawayen baƙinciki na neman ɗiga daga idanuna. Sarewa da karaya ba hali ko ɗabi’ata ba ce amma a wannan karon ina jin ƙwarin gwiwata ta yi rauni fiye da kullin, Mahaifina na lura da halin da nake ciki don haka ya shafa kaina tare da furta, “Namiji ba ya sarewa da ƙarfin magauta. A zahiri ke macece amma ni nasan nagartaccen jarumin namiji na haifa. Kada ki taɓa bari wani ya lura da rauninki, ko da wasa kar na sake ganin ruwan hawaye a ƙwayar idonki domin zai ba wa magautanki ƙwarin gwiwa a kan ki har su yi nasara su kai ruhinki kushewa.” Daga wurin da nake kwance na dube shi sannan na furta, “Wuya bata raunata zuciyar ‘yan maza koda kuwa a tsakiyar rundunar mayaƙan maƙiya ne, raunina ya dogara a kan ɓoyayyan lamarin da yake faruwa da ni ta yadda ba na iya mallakar gangar jiki da ruhina. Na yi rantsuwa da abar bautar da ke raya dare zuwa rana ta samar da yalwatacciyar ni’ima da kyautata noma, ba zan sake bayyana raunin da zai bawa magauta dama akaina ba koda kuwa rikicitaccen al’amarina zai ci gaba da farmakar rayuwata.” Mahaifiyata ce ta miƙo masa ƙaron marke da ganyen zaƙami, ya saka su akan fatar zomo ya ƙwanƙwasa su da dutse sannan ya fara shafa min a wurin da yake zubar da jini. Ba a ɗauki lokaci ba jinin ya tsaya na riski muryar mahaifiyata tana faɗin, “Baushe me za a yi wa yarinyar nan a kan karyewar asirin jikinta, tun da abar bauta ta wanzar da ruhina ban taɓa bada maganin ƙarfe ya karye ba. Amma yarinyar nan babu abin da ba a bata ba duk lokacin da wannan al’amarin zai same ta sai ta rasa duk wani tsarin jikinta.” Da kansa ya ɗauke ni ya kaina cikin bukkar mahaifiyata sannan ya tsaya a bakin ƙofar bukkar yana faɗin. “Kyauta ita kaɗai gare ni a faɗin duniya, don haka ba zan yi ƙasa a gwiwa ba don sake roƙar mata abar bauta akan ta shiga lamurunta idan akwai zunubin da ta aikata ta shafe mata shi. Ban san zunubin da ta aikata ba da farauta take yi mata gudun mutuwa, ban san ya aka yi tsatson maharba yake son bijirewa zuri’arsa ba. A duk binciken da na yi babu tasirin tsafi ko asiri a jikin Kyauta, rauhanai sun sanar mini akwai wani ɓoyayyan al’amari game da ita sai dai sun garara sanar da ni komai daga cikin al’amuranta. Zan ziyarci abar bauta da mataimakanta ta taimaka min domin ita ce madogararmu mai taimaka mana da kawo mana mafita, ba zan rasa ki ba Kyauta domin lokacin mutuwarki bai zo ba har sai mun shiga Dajin Mugazu ta karɓo kambun sarauta da hannunta.” A hankali na yunƙura na tashi zaune azabar da nake ji ta sa na cije bakina sannan na furta, “A taimaka a sada ni da Abar bauta akwai maganar da nake son tattaunawa da ita.” Da mamaki ɗauke a fuskokinsu na ga sun kalle ni, Mahaifiya ta ƙaraso wurina ta ɗago ni tana cewa. “Abar bauta za ta saka miki albarka ziyararki babbar nasara ce albarkacin tsafi da farauta.” Mahaifina ne ya kama ni muka wuce tsaunin Abar bauta ya yin da Mahaifiyata ta ci gaba da ba wa Kandala kulawar da ta da ce tana gasa ta da ruwan zafi don warkewar raunin da ke ƙasanta.

 

Daular Sarki Damina.

 

Duk yadda Mai babbar turaka ta kai ga ƙin amince wa da buƙatar Sarki fir ya ƙi sauraronta, da ƙarfin tsiya ya fisge ta ganin tana son kunto masa matsala ya cicciɓe ta ya ɗora a kafaɗa. Ciccila ƙafa ta rinƙa yi tana dukan kafaɗarsa bai saurari roƙonta ba ya fice da ita, a tsakar gidan keɓaɓɓan gida ya dire ta sannan ya kalli waɗansu ƙosassun dakaru masu siffar adawa ya ƙwala musu kira, tun bai rufe baki ba suka ƙaraso wurinsa sannan ya ce, “A gaggauta sada ta da Yarima almuru ya ƙarato zan kai gaisuwar ibada da roƙon ruwa.” Kuka Mai babbar turaka take rusawa kamar ranta zai fita, yana shirin tafiya ta rarrafa tana jan ciki haɗe da ruƙo ƙafarsa tana faɗin, “Damina ni ce fa mahaifiyarka wacce ta ɗauki cikinka tsawon lokaci yanzu da kanka za ka sada ni da Yarima ya haike min ina ji ina gani?” Taɓe baki Sarki Damina ya yi ya tsugunna sannan ya ruƙo haɓarta ya furta, “Ban fiya son ja’inja da ke ba don ina matuƙar ganin mutumcinki.” Ya ɗago yana kallon dogaran tare da furta, “A yi gaggawar wuce wa da ita.” Daga haka ya fisge ƙafarsa mai babbar turaka ta faɗi gefe haɗe da kifa kanta a ƙasa tana ci gaba ta rusa kuka mai cin zuciya. Da ƙarfin gaske suka fisge ta duk irin magiyar da take yi musu bai sa sun saurara mata, saboda sanin kansu ne matuƙar suka saɓa wa umarnin Sarkin Damina tabbas za su tsinci talatarsu a laraba domin na su hukuncin sai ya ninka nata sau dubu.

 

Suna gab da shiga ɗakin, Mai babbar turaka ta dubi Nalami dogari cikin karayar zuci ta furta, “Ka taimaka ka bar ni ko na taƙi kaɗan ne zan bar musu wasiyyar da ba na son ku buɗe ta har sai bayan babu rayuwata. Jikinsu ne ya yi sanyi duk da kasancewar ba sa daga cikin masu tausayi, ganin tausayi na neman tasiri a zuciyarsu ya sa suka fisge ta da ƙarfin tsiya. Kamar mayunwacin zaki haka Yarima ya kurma wata uwar ƙara haɗe da janyo Mai babbar turaka da ƙarfin tsiya, ganyan da ke maƙale a ƙugunta da ƙirjinta ne ya faɗi gefe Yarima ya haɗe ta da jikinta tare da sauke buƙatarsa a haukaca akanta. Cikin fitar hayyaci ta riƙa ambatar sunan Damina tana tsine masa da aibanta shi da miyagun kalamai marasa daɗin saurare, sai da Yarima ya dawo cikin hayyacinsa ya fahimci Mai babbar turaka ta galabaita. A wahalce ta dubi Yarima yana faɗin, “Yarima mahaifinka ya yi min abin da ba zai taɓa albarka ba, akwai laƙanin da nake son taimakon wannan daular da shi amma yana cikin turakata…” Da sauri Yarima ya tallafo kanta yana faɗin, “Laƙanin me ye kar ki tafi ba ki gaya min ba.” Cikin kakari ta furta, “Ka tabbatar da ka yi tozali da sabuwar sarauniyarmu kuma ita ce za ta ɗauko…” Daga haka harshenta ya sarƙe idanunta suka ƙafe ta faɗi matacciya.

 

Zuwanmu tsibirin keda wuya muka samu dubbannin jama’ar yankinmu sun yi dafifi akan tsiribirin, da yake duk ranar talata da daddare muna taruwa akan tsibirin domin miƙa buƙatunmu ga abar bauta. Mun yi amanna akan duk wanda ya faɗi buƙatarsa a kan tsibirin tabbas buƙatarsa za ta biya. Kasancewar sun lura da halin da nake ciki ya sa suka buɗe min hanya muka wuce don isa ga abar bauta saboda akwai ƙudurin da nake son sanar da ita duba da rikitattun al’amuran da suke baƙuntar rayuwata. Muna gab da ƙarasawa muka riski sautin wakiliyar Abar bauta, ba mu sake tsinkewa daga lamarin ba sai da muka yi tozali da ita ta fito matsayar da ko a tarihin rayuwa ban taɓa jin ta fito harabar wurin ba. Kamar ɗaukewar ruwa sama haka wurin ya yi tsit kowanne ya baje majiyar sauti da maganansa, ko a mafariki ban taɓa tozali da siffar wakiliyar Abar bauta ba sai dai labarin da magaba suke ba mu akan samuwarta da tasirinta ga rayuwarmu.Tun bayan kafuwar yakinmu a tarihin da muka taɓa fuskanta, abar bautar wancen yankin bata taɓa fito wa ba sai a ranar da wani mummunan al’amari ya faru da su wanda sanadin haka ya sa aka kafa tarihi har muka mayar da ranar Talata a matsayin ranar karɓar addu’a kuma ranar biyan buƙata, domin a cikinta ne al’ummar Maharba suka samu ƙarfin iko da nasara akan Baƙar Daular da ke gaba da yankinmu. Sannan mahaifina ya tabbatar min a bisa al’ada duk lokacin da Abar bauta ta bayyana akwai wani mummunan al’amari da zai faru wanda zai hargitsa al’ummarmu. Ban gama dawo wa daga duniyar tunani ba na riski sautinta tana faɗin, “Ya waɗannan al’aumma yau na bayyana kaina ne domin na shaida muku mummunan al’amarin da yake tunkaro mu kwatankwacin mummunar ƙaddarar da ta faru a baya. Kogon bincike ya ƙone ƙurmus! Hasken wutar abar bauta ta ɗauke. Buzun zakin abar bauta ya miƙe yanzu haka yana cen yana fidda aman wuta.

 

A yau na tsaya a gabanku domin na tabbatar muku da bala’in da yake tunkaro rayuwarku, ga taron rundunar baƙar inuwa tana tunkaro mu don haka ya zama wajibi mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu sake tserartar da yakinmu domin gujewa abin da ya faru ɗaruruwan shekarun da suka gabata, a zahiri dukkan alamun da suka bayyana a baya sune suke sake bayyana a wannan lokacin domin yanzu haka tazarar da ke tsakaninmu da wannan baƙin yaƙin bai fi taƙi kaɗan ba. Ina jin tsoron kada farmakin Baƙar Daula ya wanzu a gare mu duk da muna da tsarin da ko tsuntsu ba za su iya gani da idanunsu ba matuƙar ya kasance ɗaya daga cikin ahalinmu na Maharba.” Ras! Na ji gabana ya faɗi musamman da na tuna Kandala bata daga cikin zuri’ar Maharba, hasalima tsarinmu ya katange da ita.” Ina tsoron kar wani mummunan al’amari ya faru da ita. Hankali a tashe na furta, “Ba zan bari ba Kandala! Ba zan taɓa bari a cutar da ke ba tun da kaina na ɗauki alƙawarin kulawa da rayuwarki. Zalincin baƙar Daula ba zai taɓa ɗarsuwa a kanki ba koda zan rasa rayuwata tun da ni ce sillar salwantar iyayen da suka haifo ki don haka zan bada jini da ruhina akan ki.

 

*Ummou Aslam Bint Adam*🌚

Leave a Comment

error: Content is protected !!