Bakar Fata Complete Hausa Novel

Bakar fata Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Kafeta yay da mayan dara daran idanunshi masu mugun girma yana binta da wani irin matsiyacin kallo na raini da ƙasƙanci.

Gaba ɗaya office ɗin ya ɗauki wani irin mugun shuru bakaji komi se tashin shashsheƙar kukan! datake yi wanda tana yinsa ne da dukkan ƙarfin da Allah ya bata.

“Dan Allah likita…
“Ke! Dallah kimin shuru zaki tashi daga gabana kosena illahta miki rayuwarki talakawan banza marasa hankali idan banda shirme kinsan baki da kuÉ—in magani uban me yasa kizo mana nan Allah in baki tashi a wurin nan ba zan baki mamaki”.

YafaÉ—a a gajiye yana mai watso mata sassanyan ruwan dake cikin gorar gefenshi.

Rintse idanunta tai zuciyarta tana tafasa da sauri ta gyara niƙaf ɗin dake fuskarta batare data ɗaga idanu ta dubeshi ba ta miƙe tana share hawayenta.

Mayar da kansa yay saman kujerar dake office ɗin nashi yana mai lumshe kyawawan idanunshi, sam baya ƙaunar talaka haka zalika baya jin ze iya haɗa hanya dasu da sauri ya ɗauki wayarsa ya soma kiran wata number.

“Hello isah kazo yanzu ina jiranka a office É—ina”
Ƙitt ya datse kiran yana mai taune jajayen laɓɓansa masu kama dana wanda ake shafawa jambaki.

Cikin mintunan da bazasu gaza biyar ba isah ya wanzu a ƙaton office ɗin ogan nashi.
“YallaÉ“ai barka da rana”
ÆŠaga masa hannu yay.

Yana mai jefa masa kallonshi wanda yawanci jama’a ke cewa na rainine.

“Isah waya bawa wancan izinin shigomin office?”.
YafaÉ—a yana zaro masa dukkan girman idanunshi.

See also  Tayi Min Kankanta Hausa Novel Download

“Afuwan…….”
“Dakata isah who give her a permission da har zata shigomin office Æ™ilama ba mutum bace”.
Dariya isa ya danne a bakinshi gudun karta fito tazama illah.

“Ogah aimin afuwa bazan kumaba wallahi tausayi kawai naji kuma su Dr rukaiyyah
“Kaga banson shirmen banza wannan shine last worning dazan maka as from to day kada ka kuma turon mutane any how office É—ina in ba haka ba dai dai yake dana baka.

Bai kaiba isah ya dakatar dashi.

“Afuwan yallaÉ“ai insha Allah hakan bazata kuma faruwa ba na tuba”.

Bai tankawa isah ba ya koma yana lumshe idanunshi bisa kujera.

Ganin haka yasa isah fahimtar yau ogan nasa a sarautar yake da sauri ya rissina gabansa.
“Ogah zan iya tafiya?”
“Kiramin Dr ruÆ™ayya”.

Abinda ya faɗa kenan can ƙasan maƙoshi tamkar anyi mai dole.

“Angama ranÆ™a shidaÉ—e”
Isah ya faÉ—a da sauri ya taka yabar office É—in abakin kofa ya dakata ya gyara nutsuwarsa sannan ya nufi office É—in Dr rukayya.

Tsaki yaɗan ja mai fitar sauti tare da ƙara kora ruwa a cikin bakinsa gaba ɗaya bayajin daɗin yanayin yau kodan yadda garin yake ɗauke da ɗan zafine oho?

Idanunshi lumshe tamkar na mai bacci ya ware ya zubasu bisa bakin kofa yana kallonta.
“Come In dr”

YafaÉ—a still idanunshi arufe ruff
Da sallama ta ƙaraso gabansa cikin nutsuwa ta sami kujera ta zauna.

“YallaÉ“ai Isah yace nazo kana kirana”
TafaÉ—a cikin nutsuwa.
Babbar macece domin zata kai sa’arsa a haihuwa.

“Yeah nike kiranki please zan É—an fita ne amman dan Allah in Abbi ya kira waya kice mai na tafi miÆ™a documents É—inmu can general hospital”
YafaÉ—a batare daya kalli side É—in datake ba.
“Amman Dr baka tunanin ze kira su fu’ad daga can É—in?”.

See also  GIDAN AUREN HAUSA NOVEL

ÆŠaga mata hannu yay.
“Look rukayya bana son wata magana nidai abin da nace maki kenan”.
Yana mai miƙewa tsaye.

“Okey no problem Allah ya tsare hanya kenan kada na jiraka in mun tashi?”
Tsaki! yaja tare da raɓeta ya wuce cikin wani extra room wanda ke cikin ɗakin.

Banko ƙofar yay da ƙarfi yabar ta a dashe.
Cikin murmushi ta miƙe ta fita a office tana jinjina halin ɗan uwan nata.

Abakin tap ya tsaya tare da tsirawa kyakykyawar fuskarshi idanu ta cikin mirrown dake bathroom ɗin, ruwa yake tarawa a tafin hannunshi yana watsawa a saman fuskarshi mai tsananin ja da haske gami da kyawu ɗan gaske na fulanin usul na jahar gombe wanda ya fito daga silsilar ƙabilar fulanin DUKKU.

Ya jima yana wasa da ruwan tafin hannunshi domin baki ɗaya yama gama jiƙe farar Coat ɗin dake jikinshi wadda ta kasance ta likitoci ce kafin ya ɗauki karamin tawul ya goge hannunshi da fuskar shi kana ya fita daga bathroom ɗin ya nufi centern ɗan madai daicin ɗakin wanda ya kasance mai ɗauke da ƙaramin gado daɗan frij se tarkacen kayan wuta danginsu system da tarin takaddun aikinshi.

Sauya kaya yay daga waɗan nan farar rigar da baƙin jeans ɗin dake ƙasan coat ɗin zuwa wasu shegun matsatstsun riga da wandon shadda waɗanda suka fito da zahirin girman Halittar da Allah yay masa na tsayayyan namiji ingarma maiji da karfi da lafiya.

Gyara sumar dake kwance a saman kansa yay tare da É—aukar turare a saman wani É—an table ya fesa sabida shi ma’abocin son Æ™amshine sannan ya fita daga É—an É—akin.

See also  Mijin Babata Hausa Novel Complete

Wani irin rufaffan takalmi ya saka wanda yake aje a bakin office É—in nashi kwasar wayoyinshi yay dake zube a saman table, tare da wani irin agogo na zallar azurfa daya aje a wajan ya É—aura a hannunshi.

Yana kokarin fita wayarsa ta shiga ringing! da azama ya É—agata.

“Bash yaya ne akwai sabbin zubi kokuwa?”
Daga cikin wayar bash yace mai.

“Eh! mai gida akwaisu amman sedai kai matsalar ka kana son masa amman kana gudun maiÆ™wan ta.

*Tofa wannan salon fa daban yake my fans ina zashi waye shi a ina yake yaya sunansa duka bara muje zuwa mugani*???

*ina mata ƴan ƙwalisa? shin kokunsan ƙamshi da gyara shine mace? to matso na baki bayani shahararriyar mai haɗa turarukan mata da kuma kayan gyaran jikin mata wato maman noor yanxu ma ta kara xuwar muku da xafafan kayan ƙamshi dana gyara jiki domin kara kankaro miki da martabarki wajan oga ga kayan nata kamar haka

Turaren wutane
Humrh
Kulacham
Turaren wanka
Turaren Kaya

Gyaran jiki
Na amare
Da masu jego

Da magungun nan mata
Irin su

kaza
Tantabara
Tsumi
Gumbar
Zuma

Sauran bayani dai in mutum yamin magana na masa
gamai neman karin bayani seya kira

Ummu Noor
08067807620
09057713999

 

​

 

 

Name: [BAKAR FATA HAUSA NOVEL ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: November, 2021

 


1 thought on “Bakar Fata Complete Hausa Novel”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top