Hausa Novels

Bakar Inuwa Complete Hausa Novel

Bakar Inuwa Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*_Typing📲_*

 

 

 

 

 

*_🌳BAƘAR INUWA….!!🌳_*

_{Gara rana dake}_

 

 

 

 

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

 

 

 

*_Da sunan ALLAH mai ramahama mai jinƙai_*

 

 

*_Ya rabbi ina roƙonka da sunayenka ƙyawawa masu tsarki, ka bani ikon rubuta abinda zai amfaneni ni da al’umma. Ka tsareni rubuta abinda zai cutar dani da al’ummar MANZON ALLAH (S.A.W). Yanda muka fara lafiya ALLAH yasa mu kammala cikin farin ciki da kwanciyar hankali🙏🏻_*.

 

*_Ya rabbi ka gafartama mahaifina, ka ƙarama iyayena biyu mata da suka rage lafiya mai amfani.😭🙏🏻_*

 

 

_Littafin *BAƘAR INUWA* ƙirƙirarran labarine da baida alaƙa da kowa da komai. An yisane domin faɗakarwa, nishaɗi, ilimantarwa, harma da ban haushi ta wani sashe. Dan haka a wannan gaɓar ina son jan hankalin mai karatu, yayma kansa adalci yayma marubuci adalci._

 

*_A duk lokacin da mai rubutu ya kafa alƙalaminsa akan takarda ba yana nufin dole zai rubuta irin RAYUWARSA bane, ko irin RAYUWARKU. Malami yakan faɗakar ya tsoratar akan abinda ya dace. Haka shima marubuci yakanyi rubutu domin faɗakarwa ko nishaɗantarwa akan abinda rubutunsa yazo dashi. Idan yasa ƙyaƙyƙyawa, ba dole sai yanada irin wannan ƙyawun bane, domin kuwa kowa yasan a duniya akwai ƙyawawa. Idan yasa mai ƙarancin ƙyau (domin UBANGIJI bai halicci mummuna ba, kowa da irin ƙyawun da yay masa na halitta), ba dole sai yana a cikin wannan jinsin bane, sai dan rubutunsa a haka yazo. Idan yasa mai arziƙi, badan dole sai shima yanada arziƙin ba. idan yasa mai mulki, ba dole sai ya kasance jinin mulki ba. Idan yasa talaka, ba dole sai ya kasance talaka ba. Abinda kawai nasani alƙalamin marubuci zai iya taɓa kowa. Mai kuɗi, talaka, mai mulki, ɗan ƙauye, ɗan birni, musaki, mai ilimi, jahili, ƙyaƙyƙyawa, mai ƙarancin ƙyawu. Mai ƙyawun hali, mugu dama kowa da kowa. Duk kuma abinda ya taɓo idan zaka nutsu wajen zagaye cikin duniya koda ace da tunani ne sai ka samu mai kamanceceniya da LABARIN. Shiyyasa kuskure ne mai KARATU ya tsuke tunaninsa akan dole sai abinda ya sani MARUBUCI zai wallafa ko ya faɗa. Idan akasin hakan yazo kuma shi a gurinsa marubuci baiyi dai-dai ba. Karka manta ALLAH ya haliccemune yaruka daban-daban, jinsi daban-daban, yanki daban-daban, launi daban-daban, addinai daban-daban, yaruka daban-daban. Bai zama lallai sai abinda kai ka sani ko kake gani zai rubuta ba. MARUBUTA da yawa sun sha rubuta LABARANSU ko RAYUWARSU a littatafai daban-daban batare da kunsan nasu bane ba. Saboda basu fito sun sanarma duniya nasun bane ba. Dan haka ina roƙonku idan LITTAFI yazo muku, ku karanta kawai badan lallai sai yazama RAYUWAR wanda ya rubuta ɗin tazam dai-dai da abinda ke ciki ba. Kawai kadai duba darasin dake ciki ka amfana, akasinsa watsar, yi farin ciki da farin cikin da yazo dashi, dan wani abun akan rubutashine kawai domin ƙawata labari ko nishaɗantar da mai karatu wajen cire masa wata keɓantacciyar damuwarsa. Ina fatan za’a fahimceni_*

 

_Banyi wancan dogon bayanin bane dan na canja kowa, nayi ne kawai dan ya zama dai-dai da fahimtar ka a ƙwaƙwalwarka da tuntar da kai wanene MARUBUCI a taƙaice. Domin kuwa KOWA masoyin Bilyn Abdull ne, amma bai zama kallai ita ta zama abin SON kowa ba._☺️

 

*_Alhamdulillahi ZAFAFA BIYAR sun sake dawowa gareku da sabbin salo daban-daban. Muna fata ALLAH ya baibayemu da alkairinsa mu da ku dake tare da mu. Sannan muna roƙon wanda ma basu tare damu, kodan sauke haƙƙi kuzo dan ALLAH ku saya da kuɗinku badan zamu iya furta kalma mara daɗi gareku ba. Dan kuwa koda wasa bama fatan jifan wani ɗan uwanmu musulmi da kalmar (ALLAH ya isa akan littafi). Masu saya ku fitar, dan girman ALLAH kuji tsoron ALLAH. Badan mu ba, badan mun isa ba. Kuyi haƙuri ku daina aikata mana hakan, domin UBANGIJI ya hana zalunci a tsakaninmu._*☺️🙏🏻

 

 

_Masoya kumuje zuwa, domin kuwa yanzu za’a far share filin wasan, dan wannan karon tafiyar ZAFAFA ta dabance😉⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️_.

 

 

_____________________

 

 

*_Episode 1_*

 

 

………….Tafe yake tamkar iska zata kwasheshi ya faɗi dan sauri. Yayinda yake ƙananun surutai kai kace sabon kamune a hauka. Ya sake cin tuntuɓe a karo na biyu, sai dai cikin sa’a ya dafe bangon gwaguyayyen gidansa saɓanin ɗazun da sai da ya kai ƙasa. Dogon tsaki yaja zuciyarsa na sake hasala da kumbura har cikin maƙogwaro. Cikin son huce haushinsa da takaici yasa ƙafa ya daki murfin gidan na sa da duk ya cinye da tsatsa tsabar daɗewar da yay, dan tunda aka gina gidan banajin an taɓa sauya ƙyauran saboda koɗewa da ciccinyewar da yay na tsatsa tamkar tsohon drom ɗin ƙarfe.

Ball ya fara da butar da ke a farkon shigowa, inda alamu suka nuna toilet ɗinsu ne a wajen. Ta tafi ta daki ƙarshen bango, murfin yay gefe itama tai gefe.

Baba Nafi da ke alwalar magrib ta ɗago kai cike da nutsuwa da sanyinta ta dubesa. Sai kuma ta maida kanta ƙasa saboda uwar hararar daya zuba mata kai kace idanun nasa zasu zubo ƙasa ne.

“Kowanne shege da ke gidan nan ya fito!!”. Ya faɗa a kausashe yana dukan langa-langan da aka zagaye saitin inda yake tsaye matsayin kitchen ɗin girkinsu.

Cikin takaici da haushi aka bankaɗe labulen ɗakin tsakkiya, “Kai ko malam ka dinga sassauta ma zuciyarka mana dan ALLAH!, da wannan farar magriban da kowa ke ƙoƙarin kai abincin buɗa baki bakinsa maimakon a ganka bayan liman kana shirin gaida UBANGIJI sai ka lalace da neman masifa da tijarar hana iyalanka su susha ruwa cikin salama kamar yanda ka hana kanka?”.

Fici-fici yay da ido yana duban ta cikin ɓacin rai. Ya tattaro duka takaicinsa da damuwa zuwa cikin baki. Nunata yay da ɗan yatsa yana karkaɗa hannu cikin gargaɗi. “Larai ina rabaki da tararmun numfashi idan ina magana amma baƙya kiyayata. Na rantse miki da ALLAH idan ban sauke dukanin abinda na kwaso bisa kanki ba kice ba sunana DAUDA jikam mai ɗan-wake ba.”

Baki ta taɓe da sakin labulen, sai dai bakinta bai mutuba. Da ga cikin ɗakin take faɗin, “Can kaji da fitinarka ba’a kaina ba. Baka sauke haƙƙin bani abinda zanci a cikin wata mai falala ba bazaka sauken gangar ɗan bazakuɗa ba. Kai da ka kwaso abarka can ta ƙare maka ba Larai ba.”

Duk da ya jiyota sai bai tanka ba, ya cigaba da ƙwala shelar kiran kowa yazo gabansa. Shiru babu wanda yay tari tamkar kowa ya mutu a gidan. Wani ƙududun takaicin baƙin ciki daya taso masa daga tsakkiyar zuciya ya jawo da ƙyar zuwa maƙoshi ya fesar ta baki.

“Eh lallai ta tabbata an gama maidani ɗan iskan ƙasan gada, yo banda ana ɗaukata girman fadar karuwai harni dake amsa sunan maigida a gidan nan zanzo ina magana ku barni ina ɓaɓatu ga ƙwalon shege haihuwar tasha ko?..”

“Kayi haƙuri malam mudai salla muke wlhy, suma kuma nasan…..”

Wuff Larai tayo waje tana gyara zaninta dake neman ɓallewa saboda tsabar sauri, cikin harziƙowa ta tare numfashin baba Nafi mai maganar cikin sanyi da rashin son hayaniyarta “To annamimatu kinsan me? To muma sallar muke sai a maida sherin da ake son ƙulla mana cikin ciki ko?”.

“ALLAH sarki Larai nima ai abinda zance masa kenan bawai wani abu daban ba”. Baba Nafi ta sake faɗa a sanyaye.

Baki larai ta taɓe da juya ƙeya ta tura kallabinta disko gaban goshi, daddagaggiyar ƙeyarta ta bayyana. Murmushi kawai Baba Nafi tai da girgiza kanta ta ɗauke idonta gareta.

Duk abinda suke yana tsaye sai faman kumbura yake da harar ɗakin ƙarshe da ke jerin nasu baba Nafin. Sai dai baice uffan ba. Kusan mintuna biyar aka ɗaga labulen ɗakin aka fito. Mace ce ƙyaƙyƙyawa da bazata gaza shekaru talatin da biyar ba zuwa da bakwai. Daka ganta kaga ƴar duniya bugun farko. Sheƙeƙe ta dubesa shi da matan nasa ta watsar tana taunar chewing gum tamkar ba azumi aka kai ba yanzun nan.

“Wai Lafiya kaketa faman shela da farar magriba ko ruwa bamu kai bakinmu ba? Haba yadai kamata asan da da yanzu akwai banbanci, dan da kana juyamune muna haƙuri da tujaranka saboda kanada uwar kuɗinka a ƙugu, amma yanzu baka barinmu da cikinmu da hidimar ƴaƴanmu ka kuma haɗa mana da tijara da gadara *BAƘAR INUWA……”*

“Asabe! yanzu nan nine baƙar inuwar?”.

“Na tsakkiyar jeji ma kuwa, har gwara *RANA DA KAI”.*

Wata shegen dariya Larai ta bushe da shi, ta callara guɗa tana duban Asabe. “Kina birgeni amarya, idan mu latsamu a tauna baida wahala ke ai kin wuce kanwar lasa”.

Baki Asabe ta taɓe ta ɗauke kanta gefe. Wani irin ƙududun baƙin ciki ya sake kume Malam Dauda. Ya nisa tamkar bajimin sa dake a ganiyar tozon girma yana ballama Asabe ƙarfen ƙafarsa harara. Shikam ai auren bariki bai masa rana ba. Fuska ya sake tsukewa yana kai hannu ya kaɗo mutsiyar tuƙin tuwonsu dake rataye jikin kwanon kitchen ɗin.

“Matsalar mutum ce wannan kuma. Ina son naji wane shege ne tambaɗaɗɗe yaje wajen Jabiru mai shago ya amso lemon kwalba da cin-cin ɗin da matarsa keyi yace injini?”.

Kallon-kallo Nafi da Larai suka shigayi, sai dai komai babu wadda tace tunda sunsan shima yasan wadda zata iya wannan aika-aikar ai. Kuma shine ya bata wannan dama ɗin tun tana amarya, gashi yanzu tsahon shekaru goma sha bakwai har ƴan matanta na yawo galla-galla a gidan harsu huɗu komai ya gagara canjawa……

“Wai ba magana nake ba ne? Ko sai na maida ƙasan gidan nan zuwa sama ne!!?”.

Malam Dauda ya faɗa a matuƙar tsawace tsabar hasalar da zuciyarsa ke sake masa na baƙin cikin bashin da aka cimasa bayan baida ko sisi dana sharesan da akai yana magana. Nanma babu wadda ta tanka sai ƙarar taunar chewing gum ɗin Asabe kawai dake tashi ɗas-ɗas…

 

Matashiyar budurwa da zata iya kaiwa shekaru goma sha shida zuwa sha bakwai a duniya ta fito da ga ɗakin da Asabe ta fito ɗazun. Sanye take da dogon jijjab har ƙasa alamar salla tayi. Tana tsananin kamanni da Asabe tamkar tayi kaki ta ajiye. Cikin ladabi da nutsuwa takai duƙe tana faɗin “Abbanmu barka da dawowa? Ansha ruwa lafiya?”.

“A gidan ubanwa nasha ruwan? ke kuma zaki sake ɓatan rai!”.

Ƙasa tai da kanta ƙwalla na ciko mata ido, dan tanada zuciya matuƙa, sai dai tana da ƙoƙarin dannewa musamman akan mahaifanta guda biyu da halinsu baida maraba da girman haihuwar ƙasan gada.

“Kayi haƙuri Abbanmu, dama zance maka nice na amso lemon a wajen jabiru”.

“Buhun bu*a’uban nan kayyasa (😨🙆🏻‍♀️🙊😆). E lallai na zama ɗan iska haihuwar ƙasan gada kuwa da gaske. To ubanwaye ya aike ki!!?”.

Yanda yay maganar a tsawace ya sata runtse idanunta da ƙarfi tana haɗe kukan dake neman taso mata. “Kayi haƙuri Abbanmu, babu wanda ya aike ni. Babu abinda zamuyi buɗa baki ne da shi shiyyasa na amso mana, nace masa kaine ka aikoni dan inba hakaba bazai bani ba”.

Sake maƙurewa yay jikin bango tamkar tsohon ƙadangaren da ciwon sanyi ya buge yake shaƙo ƙamshin mutuwa.

“Ni DAUDA naga haihuwar jaraba jinin ladin ƙasan gada. Niko wai yaushe lalacewata takai har hakane a gidan nan ne wai? K dan uban uwarki har ni zaki laƙawa sheri ina fama da ƙishirwar azumi na? To wlhy ki rubuta ki ajiye sai kinyi nadamar hakan daga ke har uwar taki, dan nasan itace ta aike kin ta noƙe……”

“Kai Dauda sauraramin. To kodai dama dani ɗin kake bada itan ba da ka haifa? To wlhy ahir ɗinka wahainiyarka ta kiyayi ramata, inba hakaba kaima kasan na fika tsiya da tujara. Ka buga ƙafa kamar na karen mafarauta ka barmu cikin yunwa ga ruwa za’a sha saboda kafi kowa iya babbaku da tujara dan kawai an anso abin nera dubu guda injika shine zakazo tsakar gida gaban magauta da ƴan bani na iya kana zazzage min. To wlhy ina dai-dai da kai”.

“Tsssss!!!!”

Kakeji wani irin gigitaccen mari mai ƙara da alamar zaiyi ɗan karen zafi ya sauka bisa kumatun budurwar nan dake tsugunne ranta a matuƙar jagule, ta amshi laifin ne dama dan gudun karsu raba halin da suka saba a gaban kishiyoyin mahaifiyar tasu. Amma sai gashi dabarar tata batai ba.

Ta dafe kuncin jikinta na rawa. “Wannan marin na hanani zaman buɗa baki wajen Jabirunne da kikayi ke kuma. Saura na ƙaryar da kikaimun itama. Ke kuma Asabe yanzu banda lokacin mai lokacinki, amma ina nan tafe kanki..” ya ƙare maganar yana nuna Asaben.

Caraf Asabe tasha gabansa tana mazurai. “Wlhy ka sake taɓamin yarinya sai na rama mata. Kai barfa ganin uwa ban son ta, son kayana nake ras, idan kuma kaji ƙarya sake taɓata dai-dai nake da kai, danni a yanzu nake da naka lokacin. Banda kai dai kana cikin mazan da sai an tsoma kansu a wuta an ɗauraye musu zunibi ka fita baka ko bamu geron kunu ba dan mun samawa kammu mafita kazo har kana tara jijiyar wuya. To bara kaji ni ba matanka bane daka maida sakarkaru, idan kaji ƙarya kuma sake gwada bugunta ka gani, kaima kasan wacece Asabe autar hajiyar birni shalelen bahago dan mai…….”

Sai kuma taƙi ƙarasawa ta balla masa harara, ganin ya juya fuuuu zai sake ficewa. Taja tsaki da faɗin, “Da ka tsaya mana kaji ko zaka iya latsawa ka kwana lafiya ɗan gidan abun kwari mai yawo da tsinuwar uwa bisa kai”.

Wani irin kuka budurwar nan da har yau ke duƙe ta fashe da shi. Cikin masifa Asabe ta juyo kanta takai mata shiru dan tasan minene dalilin kuka. “Dan ubanki tashi anan kona huce kaf haushinsa a kanki mara mutunci. Ko dan dai nice jinin asara sai na zauna yana cin zarafina gaban kishiyoyi na masa shiru saboda ga jikar ta-salla wadda ta haɗiyi ƙur’ani dan haƙuri. K nifa bar ganina haka zan iya kakkaɓar daku nai gaba dama tausayinku ne yasa nake zaune a wannan gidan da tsiya taima katutu abincima sai anyi kwarakarsa a maƙwafta dan lalacewa”…………✍️

 

 

 

*Tofa jama’a bana ina mukazo haka? Ina alƙalamin namu ya kwasomu ya kawo😹😹?.*

 

_A cikakken Littafin BAƘAR INUWA kawai zamu samu wannan amsoshin. Naira ɗari uku me kacal, tare da duk zafafa biyar naira dubu ɗaya ne kacal. Karku bari ayi babu ku. Dan bakuga komai ba. Yanzu aka fara sharar filin wasan. Cakwakiyar sai wasan ya kankama😉. Dan duk wanda akayi babu shi ALLAH yayi missing🥺._

 

 

Taku

_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

 

 

 

___________________________

 

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥

_Safiyya Huguma_

 

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥

_Billyn Abdul_

 

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅

_Hafsat Rano_

 

*1*~ *_MASARAUTA_*💪

_Miss Xoxo_

 

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥

_Mamuhgee_

 

 

 

Guda 1👉300

Guda 2👉400

Guda 3👉500

Guda 4👉700

Guda 5👉1k

 

 

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

 

Bilkisu Ibrahim Musa

1487616276

Access bank

 

Number shaidar biya👇🏼

 

*_09032345899_*

 

 

*KATIN MTN*👇👇

 

09166221261

 

 

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*

 

 

________________________

 

 

*_BAƘAR INUWA…_*

 

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09

 

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_

 

 

*YADDA AKE BUDE ACCOUNT A AREWABOOKS*

 

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form din kamar haka: –

 

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

 

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

 

*Enter an username* (Sunanki)

 

*Enter your password:* ( misali 12341234)

 

*Confirm password:* (misali 12341234)

 

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

 

*Continue with Google* – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

 

*Register* – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

 

 

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

 

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

 

 

Masu iPhone

 

Zaku iya bibiyar shafinmu

https://arewabooks.com

 

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*

 

 

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

 

+234 903 177 4742

 

 

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.

 

 

 

 

 

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻

*_Typing📲_*

 

 

 

 

 

*_🌳BAƘAR INUWA….!!🌳_*

_{Gara rana dake}_

 

 

 

 

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

 

_Irin wannan katoɓara haka🤭, inda nasa *(Bakatsinen bafulatani episode 2)* an samu mishkilane ba haka bane. Dan babu sunan wannan jihar a ƙasar NAYA. ku ɗauka matsayin mistake Please🙏🏻😹_.

 

 

________________

*_Episode 3_*

 

 

……….Shigarsu secondary school ya ɗan fara canja wasu da ga halayen Raudha, taɗan fara rage kwaikwayon halaye irin na mahaifiyarsu. Bata da yawan magana, bakuma tason taga iyayen nata na faɗa tamkar karnuka a tsakar anguwa kowa na kallonsu yana ALLAH wadai. Hakan kuma ya farune sakamakon ƙulluwar soyayya tsakaninta da malamin islamiyyarsu sayyadi Abubakar. Tun tana zama taita kuka idan suna raba hali harta koma tana nuna musu fushinta. A lokacin da suke ss1 farkon shigarsu wani faɗa da iyayen nata suka tafka har takaisu ga police station sakamakon yanzu Abbansu talauci ya masa katutu, takai ma nauyin gidan iyayen nasu mata ne ke ɗauka. Dan tunda kamfani ya kamashi akan satar kayan da yake jigila suka kafa masa kahon zuƙa, da yaga asirinsa zai tonu asabe ta zugeshi ya kwance tayoyin motar ya saida, motar takai shekara a ajiye, sai da komai ya lafa ya saidama ƴan gwangwan ita ya kawo kuɗin gida suka hau kai shi da Asabe da ƴaƴanta suka dinga cin daɗi sai ɗan abinda ake samma su baba nafi wataran. Acan kamfani kuma akace ya mutu. Ko shekara kuɗin basu ƙullaba komai ya ƙare, dan kuwa dai a ashararancin ɗan-azumi babu abinda ya canja na neman mata da busa sigari da caca. Tunda kuɗi suka ƙare zaman lafiya tsakanin Asabe da Dauda ya ƙaura. Kullum sune faɗa kamar kaji, taje ta nafko masa bashi dolensa ya biya ko bai ƙaunar ALLAH, idan yaƙi biya su tumu sama dan bala’i su dire bisa ƙasa. Dan kullum zancenta shine ya saketa bata halaka rayuwarta da ƙuruciyarta a ƙarƙashin runfar talauci. Shiko yace bata isaba tunda ta shigo ta shigo kenan. A randa taje ta cicciɓo masa wani bahagon bashi da har akazo aka saka wani filinsa kasuwa da yake ta burin gina mata aljannar duniya ta koma tun tana amarya ALLAH baiyiba ya sakasu yin faɗa na tashin hankali harda jima juna ciwo, shine aka kwashesu zuwa ofishin ƴan sanda daya saka Raudha tsananin baƙin ciki. musamman akan habaici da zagin da akema iyayen nasu akan sunyi dai-dai da juna kowa ɗan barikine ai, tunda dama a zauren dandi suka haɗu, wama ya sani koba zaman auren suke ba.

Wannan ƙananun magana sun matuƙar ƙona ran Raudha harta kaita da kasa kuka saboda bushewar zuciya. Kowa baije yay beilingn su ba, sai ita taje duk da ƙarancin shekarunta. Ƙyawunta da ganin ƙarancin shekarunta yasa d.p.o ɗin sonyin amfani da mutuncinta sannan ya sakar mata iyayenta. Da farko taso tai masa zagin ƙare dangi, sai kuma ta fasa saboda wani abu daya zo mata rai. A take ta amince masa akan ya sakar mata iyayen bayan kwanaki biyu zata kawo masa kanta. A tunaninsa bata da wayo, musamman da yay dubi da halin iyayenta na ƴan bariki. Kai tsaye ya sake su, tana ganin an fiddosu tai wucewarta gida ta barsu duk da magana da suka dinga mata. Ta rigasu zuwa gidan, dan haka kowa bai san itane taje ta fiddosu ba. Dama kuma tun a hanya suka taho suna hirarsu ta arziƙi tamkar basune aka amso hanun hukuma ba saboda tazubar ɗinsu.

Koda suka dawo gidanma sun kaɗa sun raya Raudha taƙi tanka musu, taƙi cin abinci ta kuma daina shiga harkar kowa a gidan. Tun suna ɗaukar al’amarin nata wasa harya fara cin ƙarfinsu, da ga ƙarshe dai suka haɗa baki da wani malamin islamiyyar su Raudha ɗin da suke yawan jin sunansa a bakinta da ganin tana tsananin girmamashi dan yana ɗaya daga cikin wanda suka gyara tarbiyyarta dake a bauɗe tunda farko sannan Raudha ta sakko harta nema gafarar iyayen nata (Sayyadi Abubakar). Dan Ya sayyadi Abubakar ya sanar mata su iyaye ba’a fushi dasu, ko wanne irin hali garesu lallaɓasu ake da ƙyaƙyƙyawan kalami. koda anji ciwo akan kuskurensu shanyewa akeyi ayi haƙuri. Saɓawa ALLAH ne kawai ba’a yarda kamusu biyayya akansa ba wannan haramunne.

Raudha taji wannan nasiha hartazo ta bama iyayenta haƙuri. Daga lokacin kuma ta dinga taka tsantsan da harshenta a kansu da fushinta. Idan ma taga abu zai basu saɓani ta gwammace ta amshi laifin ita koda zasu mata hukunci ne. Idan batasan tushen rikicin nasu ba kuma zatabi duk hanyar data dace ta sasantasu cikin hikima. Sai dai kuma kuka ya zame mata tamkar abokin rayuwa, dan sam bata ƙaunar halin mahaifan nata guda biyu ko kaɗan.

A yanzu haka Raudha da sauran ƴan uwanta na sauran ƴaƴan ɗakunan biyu sa’anninta suna akan zana jarabawar gama secondary school ne. A ƙalla shekarunsu Fatisa goma sha takwas, Raudha kuwa sha bakwai ita da Iklima da Binta. Kasancewar babu wani batun Noziri a karatun nasu yasa suka kammala da ƙarancin shekaru, musamman ma ita dasu Binta duk sun girme mata.

Halin talauci da fataran da suke ciki ga shegen son kuɗi na Asabe ya saka ƴaƴanta su Fatisa fara kaucewa hanya wajen biyema samari. Duk da kuɗin da yaran ke shigowa dasu na ban mamaki da kayan kwalliya basu sana’ar ko asi bai taɓa saka Asabe nuna damuwa ba balle tuhumarsu. Sai dai ma ta baje suci su sha mai daɗi tana kiransu masu farin jini. Tabbas *ZINA* tamkar sharri take, dan ƴar aikece komin daren daɗewa saita dawo cikin zuri’arka. Hakanne ya faru akan su Fatisa dama wasu a ƴaƴan mal ɗan azumi na sauran ɗakunan, dan kuwa cikin ƙanƙanin lokaci rayuwarsu ta ɗakko hanyar lalacewa Dauda naji na gani babu halin magana, duk da abun na ƙona masa rai da soya zuciyarsa. Dan ko yayi magana Asabe ta taresa da masifar cewar yanama ƴaƴanta sheri saboda shima aikinsane zina. Maƙiya masu baƙin ciki da hassada wa farin jinin ƴaƴanta na ɓoyewa bayan ƙofa suna musu dariya. Sai dai abinda Asabe bata sani ba na ƴaƴan ɗakintane ya fito, amma itama Larai nada Kangararru irin su Fatisa har su uku. Wani lokacin duk da gogewar ɗan-azumi a bariki, Asabe ta fisa bala’i, shiyyasa idan taja yaja sai ya sakar mata dan zuwa yanzu girma yaɗan fara kamashi, ga ciwo dake cinsa a tsaye na hawan jini wanda ko ba’a faɗaba asabe ce silarsa, gefe ɗaya taba ta gama cinye masa naman jiki sai ƙashi da jijiya da fata.

Halayyar su Fatisa na matuƙar ƙona ran Raudha, sai dai babu yanda zatayi dan ko tayi nasihar basaji. Ita kanta samarin na yawan kawoma rayuwarta hari, musamman daya kasance ta fisu ƙyau nesa ba kusa ba. Hankalinta yakan tashi matuƙa, shiyyasa akoda yaushe cikin suturta jikinta take da kayan mutunci harma da niƙab wani lokacin. Takan yawaita neman tsarin ALLAH daga ƙaddarar zina a gareta.

Rashin samo kuɗi da batayi yasa Asabe tsangwamarta a ɗakin fiye da kowa. Dan hatta Yasmin ta fita daraja duk da kuwa Asaben tafi son Raudha fiye da kowa acikin ƴaƴan nata. Sai dai lallaɓa da lallashin da take mata akan ta dinga kula samarin sai tafi su Fatisa samo kuɗi, amma Raudhan na bijirewa yasa ta ɗauka karan tsana ta ɗaura mata ita da su Fatiman. Kullum cikin caccakarta suke da magana mara daɗi. Da yake miskilace kuma bauɗaɗɗiya ko kulasu batayi ma balle ta nuna ta damu, fatanta kawai tai aurenta tana gama secondary school da ya-sayyadinta Abubakar da kowa yasan suna soyayya zuwa yanzun.

 

A ɓangaren sayyadi Abubakar shima babban burinsa mallakar Raudha matsayin mata. Dan haka suna fara exam ya sanarma iyayensa akai kuɗi. Sunyi farin ciki da farko dan basusan ƴar waye ba a Hutawa. Dan haka suka tambayesa acewar mahaifinsa sai sun fara bincike tukunna. Abubakar ya shiga fargaba, amma sanin Raudha yarinyar ƙwaraice mai kamun kai, kuma da ita zai zauna yasashi jin ƙwarin gwiwa.

Bayan kwana biyu mahaifinsa ya kirasa shida ƙanensa sukai masa wankin babban bargo, tare da gargaɗinsa ya fita sabgar Raudha bata fito cikin gidan arziƙi da mutunci ba, su bazasu haɗa zuri’a da ɗan-azumi ba. Idan ma ƙyawun yarinyar ke ɗiɓarsa yaje akwai ƙyawawa da suka fita ya nemo. Idan kuma ya sake koda yima Raudha magana ne ALLAH ya isa basu yafe ba. Itama sunje har gida sun gargaɗi ubanta akan ta fita hanyarsa. Daga karshe suka hanashi cigaba da koyarwa a islamiyyar su Raudha ɗin baki ɗaya. Sukama maida rayuwarsa can cikin birinin Ɗillo wajen wani ƙanin baban nasa dake can da iyalansa.

Wannan shine sanadin raba Raudha da Sayyadi Abubakar. Tayi kuka kamar yanda shima yayi nasa. Kusan dukansu sai da suka kwanta a asibiti dan ba karamar shakuwace a tsakaninsu ba. Halin data shiga yasa ɗan-azumi da Asabe zuwa har gida sukaima iyayen sayyadi Abubakar tas. Wannan ya ƙara harzukasu suka kara jin tsanar tushen Raudha da ƙyamar haɗa zuri’a da su.

Sosai wannan lalacewar aure taima Larai daɗi, dan kuwa tana ɗaya daga mutanen da suka sake lalata zancen auren, mahaifin Sayyadi Abubakar nada ɗan hali, shiyyasa tun yana zuwa wajen Raudha takeji baƙin ciki da hassadar hakan. Sai dai tabi duk wata hanyar rabasu hakan bai samu ba, sai gashi cikin sauƙi komai ya lalace. Da wannan damar tai amfani wajen zuwa har gida ta sakema Asabe da ɗan-azumi batanci fiye da wanda iyayen Sayyadi Abubakar suka jiyo ga wasu mutanen. Sai ka rantse ɗan-azumin ba mijinta bane.

Raudha ta ɗanɗana azabar rashin Ya sayyadi Abubakar har batasan mi take rubutawa a jarabawa ba har suka kammala. Bayan kammalawar tasu ta sake dawowa gida zaman sabuwar jiyya, a dalilin hakan ciwon Asthma ɗinta da bai cika karfi ba ya sake ƙarfi har takai yana yawaita tashi yanzu. Gefe kuma ga azababben ciwon mara idan zatai period har suma take wani lokacin. Dama dalilin ciwon marar natane sayyadi Abubakar ya yanke shawarar data kammala secondary school suyi aure kawai, sai ta cigaba da karatunta a gidansa. Sanda suna tare saboda tsabar kiyaye yanayin nata da wata ya kama zai kawo mata magunguna da allura ta ajiye, da abin ya fara mata za’a nemo wani yaron makwafcinsu dake da kyamis yay mata allurar. Ta hakane take samun sassauci sai abun yazo da sauƙi..

 

_Wannan kenan😚👌🏼._

 

*_Mun dawo labari_*🏃

 

Kiran sallar isha’i ne ya sata miƙewa da ga kwanciyar kukan da tayi, ta fito daga ɗakin baki ɗaya batare data ko kalli inda su Fatisa ke zaune suna hira da shewa ba su da Mommynsu. Sai ma Yasmin ce data miƙe zumbur tana ƙwala mata kira da faɗin, “Aunty R zanje”. Dan tasan massallaci zataje sallar asham. Bata tanka mata ba, dan ƴan miskilancin na kusa ne, sai dai ta mata alamar tai alwala. Itama kuma ta ɗauka buta ta ƙarasa inda sukeyin duk wani hidimarsu na harkar ruwa a gidan tai alwalar sannan suka fice……….✍

 

 

*_Humm Sayyadu Abubakar Abubakar ya tafi, wa kuma zaizo? Ta ina zaizo? Yaushe zaizo AMINATU Raudha?. Dukkan amsarku na cikin BAƘAR INUWA ne, dan bazan gaji da faɗaba ba’a fara komaiba har yanzun masu karatu. Kar dai ku bari a baku labari😉⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️._*

 

 

 

*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*

 

 

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥

_Safiyya Huguma_

 

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥

_Billyn Abdul_

 

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅

_Hafsat Rano_

 

*1*~ *_MASARAUTA_*💪

_Miss Xoxo_

 

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥

_Mamuhgee_

 

 

 

Guda 1👉300

Guda 2👉400

Guda 3👉500

Guda 4👉700

Guda 5👉1k

 

 

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

 

Bilkisu Ibrahim Musa

1487616276

Access bank

 

Number shaidar biya👇🏼

 

*_09032345899_*

 

 

*KATIN MTN*👇👇

 

09166221261

 

 

*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

 

_____________________

 

 

*_BAƘAR INUWA…👇🏻_*

 

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09

 

 

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_

 

 

*YADDA AKE BUDE ACCOUNT A AREWABOOKS*

 

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form din kamar haka: –

 

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

 

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

 

*Enter an username* (Sunanki)

 

*Enter your password:* ( misali 12341234)

 

*Confirm password:* (misali 12341234)

 

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

 

*Continue with Google* – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

 

*Register* – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

 

 

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

 

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

 

 

Masu iPhone

 

Zaku iya bibiyar shafinmu

https://arewabooks.com

 

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*

 

 

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

 

+234 903 177 4742

 

 

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.

 

 

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

*_Typing📲_*

 

 

 

 

 

*_🌳BAƘAR INUWA….!!🌳_*

_{Gara rana dake}_

 

 

 

 

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

 

 

_“Kamar yanda na faɗa tun farko labarin, Littafin BAƘAR INUWA ƙirƙiraren labari ne, dan haka duk wani sunan gari da zai iya zuwa cikin labarin shima ƙirƙirarsa akayi, komai ma da zai iya shigowa cikin labarin ƙirƙirarsa akayi. Baida alaƙa da wata ƙasa ko wasu mutane. Koda kuwa kaji abinda ya shafeka ko yay kamanceceniya da kai to ka ɗauka kamarce kawai yayi bawai yana da alaƙa da kai bane ba. Dan Bilyn Abdull bata sanki/ka ba balle ta dasa alkalaminta akan ka. Rubutu ne kawai nayi dan nishaɗi, faɗakarwa, ilimantarwa, harma wani abun zai iya zuwa muku da ban haushi saboda wannan karon ma a haka alƙalamin nata yazo.😅🙏🏻_

 

________________

*_Episode 2_*

 

 

*_ƘASAR NAYA_*

 

 

………*_(DALLO STATE): HUTAWA L.G.A._* Da gudu budurwar ta miƙe ta shige ɗaki tana cigaba da kuka, ganin a yanda ta shigo ta wuce tana kuka, ƴammata biyu da za’a iya kira tagwaye kuma yayunta suka kwashe da dariya suna faman taɓe baki da ɗaga kwalbar lemonsu suna ɗaɗɗaka hankali kwance.

Sai kuma suka maida dubansu akan Asabe data shigo tana cigaba da zazzaga ruwan tujara.

“Kina wuta momyn mu!!👍🏼”.

Ƴammatan suka faɗa suna mata jinjina da kwashewa da dariya a karo na biyu. Zama tai kusa da su taja kwalbar lemo guda tasa haƙori ta ɓalle murfin tana huci. Batare data cema ƴammatan komaiba ta ɗaga tasa a baki, kamar ƙiftawar ido sai gashi ta zuƙi kusan rabi sannan ta dire tana sauke ajiyar zuciya.

Wadda tafi hasken sosai dake kallon kwalbar lemon ta ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “Mommy sunan wannan shan lemon naki shan huce takaici”.

Tsaki tayi tana gyara zama da ɗaukar tsokar nama dake gabansu ta danna a bakinta. “Yo wannan uban naku inba shan huce takaicin kakema ni’imar da ALLAH yay maka ba ai tuni yake tsotse maka ruwan jiki, ga waccan mara mutuncin dake abu uwa ba jinina ba.”

“Yo Mommy bayan kamanin da take dake ai sai muce muma ko’an canja miki ita ne a asibiti? Muda yakamata muyo kamanin naki hegiyar mai taurin kan tsiya da kicifi duk an haɗa ita an bata.”

 

Duk abinda suke budurwar nan na jiyosu daga uwar ɗaka. Dan haka ta sake fashewa da kuka zuciyarta na mata ƙuna da raɗaɗin halin iyayen nata da ƴan uwanta. Tun tana ƴar ƙaramarta takejin ana zagi da la’antar halin mahaifanta a cikin layinsu, har gashi yau tsahon shekara goma sha bakwai bataji komai ya canjaba sai ma abinda ya ƙaru a dalilin ƴan uwanta guda biyu da kullum cikin janyo masu wata sabuwar maganar suke. Duk da dai itama ta fara rashin ji mai kama da nasu ALLAH ya tarota ta nutsu sanadin malamin islamiyarsu sayyadi Abubakar.

Hannu tasa ta share hawayenta da gyara kwanciyarta zuwa rufda ciki, duk da yunwa dake cinta saboda azumin data kai hakan bai dameta ba, ta lumshe ƙyawawan idanunta data gada wajen mahaifiyarsu Asabe a hankali Murmushi na suɓuce mata mai haɗe da hawayen tausayin kanta na rasa Abubakar. Tabbas zuwa yanzu ta yarda ta rasashi, ya tafi har abada bazai sake dawowa gareta ba kamar yanda iyayensa suka faɗa. Wannan ciwone a rayuwarta mafi muni da har abada bata tunanin warkewarsa, dan ya zama gyambo a ƙirjinta. A tsaye take da sunanta, amma a zuciya ta jima da mutuwa tun sanda iyayen abubakar suka saka ya fita a rayuwata.

“Ya ALLAH ka ɗauka raina inhar zaifi zama alkairi a gareni”.

Ta faɗa cikin kuka mai ban tausayi da tsum rai.

 

 

Sunanta shine *_AMINATU_* sai dai ana kirana da *_RAUDHA_* sakamakon sunan kakarta da taci wadda ta haifi mahaifinta. Kamar yanda kukaji a bakin mahaifiyarta sunan mahaifinsu DAUDA, sai dai ana kiransa ɗan-azumi. Tun a ƙuruciyar mahaifinsu mutum ne marajin magana. Al’amarin nasa ya sake turewa a lokacin daya fara bin wani ɗan anguwarsu driver matsayin karen mota. Kamar yanda kakarsu ta taɓa basu labari tarbiyyar Abbansu da rayuwarsa ta sake gurɓacewa a dalin wannan bin mota, dan bai rufa shekara ba a hanun uban gidansa sai shima ga tashi motar. Tun yana jan ƙaramar mota harya koma babba irin ta company ɗin nan da ake ɗaukar kaya trailer. Fara jan motar trailer yasa albarka a hanunsa, dan babu wani tazara da hakan kuɗi suka fara zauna masa. Da ƙyar ya yarda ya auri matarsa ta farko Nafisa, wadda ɗiyar ƴar uwace ga kakarsu. Nafisa tanada matuƙar haƙuri, hakan yasa bata taɓa kai karan ɗan-azumi ba a duk gallazawa rayuwarta da yakeyi. Basu rufa shekara da aure ba ya auro sabuwar amarya mai suna Larai. Larai fitinanniyar mace ce mai kauɗi da rashin barin kota kwana. Yanda ta hana Nafi zaman lafiya haka ta hana Mal. Ɗan-azumi. Mahaifiyarsa tayi-tayi ya saketa yaƙi. Babu jimawa da auren Larai Nafi ta haihu, itama Laran bata cika shekara ba a gidan ta haihu. Zamansu ya cigaba da kasancewa babu wani daɗi, yayinda Mla. Ɗan-azumi ya cigaba da sake kutsa kai a yawon tazubar. Dan kuwa a kaso biyu bisa ukun kuɗin da yake samu suna tafiyane ga neman mata da ashararancinsa. Sune manyan ƴan duniyar duk wani gari na baɗala da ire-iren gurare na ashararanci da akasan direbobi na kakkaɓe dukiyarsu a wancan zamanin.

Nafi ce kawai ke damuwa da halin banza na maigidan nasu, Larai ko ko’a kwalar rigarta tunda akwai kuɗi, dan ita kam dama sune matsalar rayuwarta tunda itama acan ya kwasota a tashar ƴan tazubar ɗin. Suna da haihuwa hurhuɗu Nafi da cikin na biyar Ɗan-azumi ya sake sabon aure daga birinin Loss. Ba kowa ya auroba kuwa sai Asabe ɗiyar *Ɗahare (Hajiyar birni)* mai tuwo-tuwo a ƙarƙashin gada.

Ɗahare mace ce mara mutunci da duk wani shege daka sani ɗan yankin nan dake zaman tazubar a Loss ya san da zamanta. Asalinta a ƙasar saudia take tana TIKARI tsahon shekaru, a wani yaya da akayo alƙawarin ALLAH ya cika aka yayota zuwa ƙasar Ghana. Kasancewarta shaharriya acan ɗin ma yasata ko NAYA bata dawo ba ta sake komawa. Dan kuwa yaranta nacan su huɗu wanda ta haifa da wasu larabawa biyu, sai dai dukansu aure tai da su. Na farko rasuwa yay ya barta da yara biyu mata *Samiha da Hannah*, na biyu kuwa rabuwa sukai saboda Ɗahare ta wuce dukan tunanin mai tunani. Kwasotan ma da akai shine yay shunenta dan yana so ya sace yaransa dake hanunta su biyu. Sai dai kuma ta koma domin tanada hanya sosai. Komawar Ɗahare da biyu ne. Na farko da ƙudirin ɗaiɗaita rayuwar balaraben nan ne uban ƴaƴanta guda biyu, *Halima da Nasiba (Asabe)*. Na biyu ƙudirin rabo ƴaƴanta biyu daga hanunsa ne, dan labari yazo mata tana barin ƙasar yana zuwa ya kwashesu yabar wanda ta haifa da mijinta na farko. Kamar yanda ta tsara kuwa hakance ta kasance, dan kuwa dai duk da balaraben nan bawani mai shaharren arziƙi bane, dan kuwa baƙauyene ma. Sai dai yana da arziƙin dabbobi matuƙa na kiwo dana tatsar madara. Duk irin makircin da Ɗahare ta ƙware sai da tabi wajen ganin ta rabashi da wannan dukiyar, jin ana bincikenta a kama yasata tattaro duka ƴaƴanta huɗu ta baro saudia bisa taimakon wasu mutanenmu dake can masu ɗaure musu ƙugu. Koda ta dawo gida kuma babu inda ta yada zango sai tsakkiyar birnin jihar Loss. Inda ta fara tuwo-tuwo yaranta huɗu ƴammata zagaɗa-zagaɗa na taimaka mata.

Game da ƴaƴan nata tamkar kumbo kamar kafinta ne. Dan kuwa a kaf halayyarta babu wacce suka bari musamman ma Asabe mafi ƙyawun fuska da ƙyan sura a cikinsu. Dan kuwa ƙyaƙyƙyawar balarabiyace da kallo guda bai isar mai dubanta. Dan-danan alhazan birni suka fara wawarsu da sheɗanci, dan kuwa inma kace da aure kazo garesu to tabbas kuwa Ɗahare da sunanta ya koma Hajiyar birni ba daga maka kafa zatai ba. Zatai maka wankin babban bargo tace bata gama more wahalarta ba za’a tura mata ƴa cikin ɗaki, sam bata yarda ba.

Ko’a jikin ƴaƴan, dan suma basu buƙatar auren sai harkar neman kuɗin kawai, sai dai banda Asabe. Dan duk kauɗi da rashin mutuncin Asabe ita dai tafi buƙatar aure sama da rayuwar barikin. Bawai batayi bane, a’a bata cika sakin jiki tayi ɗin bane tamkar wata karya. A wannan halin ALLAH ya haɗata da Mal. Dauda ɗan-azumi, wanda yake tsaka da tashen kuɗi. Gashi shima masha ALLAH ƙyaƙyƙyawan bakatsine bafulatani. Dandanan ya fara sakar mata kuɗi na hauka, tare da zazzafar soyayya dan kwashi dai tunda ya ɗana sau ɗaya yaji bazai iya haƙuri yabarta ba sai ya aureta. Duk wani shigi da fici irin na ƴan bariki kwararru ɗan-azumi yayi ga malamsa na masa aiki, cikin ƙanƙanin lokaci ya rikita zuciyar Asabe tace inba shiba sai rijiya mai gaba dubu. Hankalin uwarta ya matuƙar tashi dan tafi kallon sa’arta jikin Asabe fiye da sausan ƴaƴanta saboda ƙyawu da ALLAH ya bata na larabawan asali da ko’a cikin ƙasar saudiyar abin kallo ce. Ganin Hajiyar birni zata bashi matsala itama ya rufe mata baki ruf. Babu ɓata lokaci aka shiga hidimar bikin daya bama kowa mamaki.

An ɗaura auren Asabe da Dauda, aka ɗakko amarya zuwa garin hutawa dake a jihar Ɗillo inda Dauda ke zaune da iyalansa. Ƙyawun Asabe yasa ake layin zuwa ganinta har wasu na faɗin ɗan-azumi ya auro aljana wadda zatai maganin sheɗancinsa. A zahiri ba aljanar bace, amma bakin mutane kam ya bisa dan Asabe ta zame masa *BAƘAR INUWAR..* daya gwammaci aljanar ya aura. Asabe ta take Larai rashin mutunci ta shanye. Dan ita ko kusa ko alama bata shakka ko kunyar tsige Dauda tas a bainar nasi ko gaban ƴaƴansa balle uwarsa. Inhar zai faɗa mata cuta saita mayar masa da mutuwa koda zata kaisu da dambe a tsakar anguwane. A haka ta samu ciki, inda ALLAH ya azurtata da haihuwar ƴaƴanta mata ƴan biyu masu tsananin kamanni da DAUDA. dan ko kaɗan basu biyo Asabe ba sai dai ace ko na jini dole ka gani a fisge. Ko kaɗan bata damuba, dan kuwa ƴaƴan soyayya ma take kiran ƴan biyun nata mata da sukaci sunan Faɗima da Fatisa. Bayan haihuwar su Fatisa ko wata uku bataiba ALLAH ya sake bata wani cikin, wanda shima ta sulluɓo ƴarta mace mai tsananin kamanni da ita a wannan karon. Dan kuwa ƴar nan duk da jinjirace duk wanda ya kalleta sai ya sake duba. Dan ta wani fannin za’ace ta hado ƙyawune na uwa da uba. Saboda ta ɗakko ɗan duhun fatar Dauda da hasken mahaifiyarta. Idan ka kalleta kai tsaye zaka kirata half cast kawai. Itako taci suna *Aminatu* asalin sunan inna kenan mahaifiyar dan-azumi. Sai dai kuma Asabe tace ana ce mata *Raudah* dan duk kishiyar data faɗar mata sunan uwar miji a gidan ranar za’aga ƙarshen bala’i da jidali. Bayan haihuwar Rauda Asabe ta sake haihuwar mace itama mai suna Yasmin. Itama dai kamanni biyu ta ɗakko na Asabe da Dauda. Sai dai itama baƙace sosai ba kamar Rauda ba.

Basai an faɗa makaba, dan kuwa batun tarbiyyar babu ita ga ƴaƴan Asabe a gidan, tasu ta fita daban data saura. (Ƴaƴanmu kan fara koyon ilimine daga ɗabi’unmu iyaye, dan haka sai mu kula dan ALLAH kodan gaba da zasu kai girma su gallabemu). Sam ƴaƴan Asabe ƴaƴane na rashin ƙwaɓo a gidan, duk taɓararsu babu ubanda ya isa nuna musu yatsa har a wajen Dauda. Dan har gori yakema sauran matansa akan basu taɓa haifa masa ƙyawawan yara ba balle mai kama da shi, dan su kam ƴaƴansu tamkar haɗin baki duk kamanninsu suka kwaso. Ko aike babu wanda ya isa aiken ƴaƴan Asabe sai ita, ita ɗin ma sai sun gadama suke zuwa. Hakan kuma bazaisa ta nuna ta damu ba. Hatta da Raudha ma haka ta taso a cikin nasu sai a hankali, dan itamadai halin ƴan uwan natane tsaf sai dai ma ace ta ɗarasu da shegen miskilanci da baƙar zuciyar tsiya da jan magana, dan kullum cikin faɗa take da yara harma da manyan. Sai dai kuma tanada ɗan sauƙin kai ta wani fannin kaɗan idan taso, ba komai ya jawo rashin jin Raudha fin na sauran ƴaƴan Asabe ba sai gatan da Mal ɗan-azumi ke mata a gidan fiye da kowa dan tana da sunan mahaifiyarsa………✍️

 

 

😉karfa ku bari ayi babu ku, dan ba’a far komai ba har yanzun😎🤙🏻.

 

 

*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*

 

 

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥

_Safiyya Huguma_

 

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥

_Billyn Abdul_

 

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅

_Hafsat Rano_

 

*1*~ *_MASARAUTA_*💪

_Miss Xoxo_

 

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥

_Mamuhgee_

 

 

 

Guda 1👉300

Guda 2👉400

Guda 3👉500

Guda 4👉700

Guda 5👉1k

 

 

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

 

Bilkisu Ibrahim Musa

1487616276

Access bank

 

Number shaidar biya👇🏼

 

*_09032345899_*

 

 

*KATIN MTN*👇👇

 

09166221261

 

 

*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

 

_____________________

 

 

*_BAƘAR INUWA…👇🏻_*

 

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09

 

 

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_

 

 

*YADDA AKE BUDE ACCOUNT A AREWABOOKS*

 

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form din kamar haka: –

 

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

 

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

 

*Enter an username* (Sunanki)

 

*Enter your password:* ( misali 12341234)

 

*Confirm password:* (misali 12341234)

 

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

 

*Continue with Google* – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

 

*Register* – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

 

 

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

 

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

 

 

Masu iPhone

 

Zaku iya bibiyar shafinmu

https://arewabooks.com

 

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*

 

 

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

 

+234 903 177 4742

 

 

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.

 

 

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

*_Typing📲_*

 

 

 

 

 

*_🌳BAƘAR INUWA….!!🌳_*

_{Gara rana dake}_

 

 

 

 

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

 

 

________________

*_Episode 5_*

 

 

……….Bada son ran ɗan-azumi ba aka kwashi Raudha zuwa asibiti. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso, inda aka amshi Raudha dake a jigace har batasan inama kanta yake ba zuwa yanzun. Ko sisi Fatima bata da shi, tayi ƙarya ne kawai dan Abbansu ya bari a kawo Raudha asibiti. Tana ganin an amshi Raudha ɗin ta fito ta nufi ofishin Doctor Rufa’i, sai dai anyi rashin sa’a wai baya nan yamaje Ɗillo tun jiya. Dawowa tai inda Mommy da Abban ke tsaye a ƙofar ɗakin da aka shiga da Raudha ɗin. Zama tai itama tabi ayarin ƴan tagumi, a haka har doctor ɗin ya fito yana mai kwantar musu da hankali akan karsu damu komai zai dai-daita, dan zai rubuta musu wasu allurai da zasu sayo, da zaran anma Raudha ɗin inssa ALLAH zata samu nutsuwa. Cikin gamsuwa da rashin damuwa aljihunsa zaiyi tsuwwa ya miƙe yabi doctor ɗin, har yaje ya dawo mommy da Fatisa da Fatima bakinsu bai saɓa ba. Sai da ya dawo da takardar ya mikama Fatisa ɗinne ta ce, “Abba ya zaka bani kuma? Ba cayay a sayo ba?”.

Wani shegen kallo ya watsa mata ita da Fatima fuska a ƙwaɓe. “Kunci bu*a’ubaku, ƴan bu*a’uban yara da basa ko ganin mutuncina. Ni kikema magana haka kamar kina a gaban tsohon kwarto”.

Fuska Fatisa ta ƙwaɓe tana ƙunƙuni, zai sake magana Asabe ta katsesu.

“Wai nikam maganin zaku sayo a cetomin yarinya ko tazubar ɗinne ya motsa muku a bainar nasi?. Kai kullum bazaka ja girmanka ga yaran nan ba balle tauna harshenka da baiko da linzami wajen sakin magana”.

“Kar yayi linzamin mana. Banda shegantaka irin tata ba itace tace tanada kuɗi ba shine zata wani tsareni da idanu na rashin ta’ido. ai sai da nace ku bata ɗan libiya amma tace tanada kuɗi ko……”

“Ni dai ya isa da ALLAH. Ke Fatisa anshi kije ki sayo”.

“Mommy nifa wlhy banda ko sisi anan. Nace inada sune danya yarda akawota asibiti. Dan haka sai yaje ya nemo inma baida su, dansu dai likitocin nan bawai batun lamuni suka sani b…..”

Hannu yakai zai kwaɗa mata mari ta tashi ta fita a guje Fatima na take mata baya. Babu ko kunya ya rufa musu baya shima duk da kuwa tsufa ta fara kamashi, ga sigari duk ta gama cinyesa a tsayee….

“Subahanalillahi! Malam ɗan-azumi lafiya kuwa?”.

Cak yaja ya tsaya yana huci saboda jin an ambaci sunansa. Sai kuma duk ya diririce ganin Falalu mai shago tare da Alhaji Maude Dallatu, ya ɗan tura hularsa baya yana ƙaƙaro murmushi. “A’a Falalu kune anan? Ince dai lafiya ko?”.

“Ai kai ya kamata mu tambaya ko lafiya kuwa baba?”.

Cewar Alhaji Maude duk da kuwa zai iya girmar ɗan-azumin ko suyi sa’anni.

Fuska ya marairaice kamar zaiyi kuka, saboda hangen damar dake garesa ta ƙarshe da mafita kenan. “Alhaji wlhy Raudha ce babu lafiya muka kawo asibiti. Shine waccan ja’irar na bata ta sayo magani take shirin min ƙyuya irin nasu na yaran zamani”.

Fatisa tai saurin waro ido waje suna kallon juna ita da Fatima da gumtse bakunan su jin dariya nason kufce musu.

“Ai sai dai haƙuri baba. Inga takardar”.

Alhaji Maude ya sake faɗa a ladabce yana miƙa hannu ya amshi takardar hannun Abban. Kamar bazai bashi ba dai yana ɗan nannoƙewa sai kuma ya miƙa masa. Koda Alhaji Maude ya amsa bai wani tsaya dubawa ba ya kalli Falalu dake ɗauke da kaya niƙi-niƙi alamar duba wani mara lafiyan sukazo ko makamancin hakan. “Falalu ƙarasa ciki ina zuwa”.

“To ranka ya daɗe, amma daka kawo ni sai naje zai fi”.

“No karka damu jeka ciki kawai zanzo yanzun”.

“To a shigo lafiya”.

Falalu ya faɗa cikin girmamawa yana ɗan murmushi.

“Baba ka jirani nan kaima ina zuwa”. Alhaji Maude ya sake faɗa yana tafiya da kallon mal. Ɗan-azumi. Kafinma yace masa wani abu har yayi nisa. Hannu ɗan-azumi ya ɗaga sama yana godema ALLAH daya kawo masa Alhaji Maude a lokacin daya dace, sai dai a ransa kuma ya ƙudira dolene kuɗin da duk zai biya na maganin sai Fatisa tayi kashinsu. Yana nan tsaye ko mintuna goma ba’aiba sai ga Alhaji ya dawo, da taimakon sa sukaje inda aka kwantar da Raudha ɗin. Babu ɓata lokaci doctor ya amsa dan dama su kawai yake jira.

 

Alhaji Maude na nane da su har kusan awa uku, dan sai da Raudha ta farfaɗo ta koma normal barci da allurar ta sakata sannan yace musu zaije ya dawo zuwa anjima. Godiya suka dinga masa kamar zasu gurfana ƙasa. Yana juya baya Asabe ta warce kuɗin daya mikama Baba tana faɗin. “Ɗan cin rabo, kaci naka zaka hau kan haƙƙina”.

Hannu yakai zai damƙota a fusace. “A gidan wane shege akace rabonki ne? Asabe anya zakiga ANNABI kuwa?”.

“Ai tare da kai zamu gagara ganinsa kwantar da hankalinka jemage maƙi jinin ƙasa sai samaniya..”

Cikin takaicinsu Fatisa tace, “Asibitine fa Mommy. Yanzu dan ALLAH idan ya dawo ya jiku kuma fa? Mudai wlhy kuna zubar mana da mutuncinmu”.

Baki Asabe ta ƙyaɓe. Batare data tanka ba ta zari dubu biyu ta miƙawa baba ta saƙe sauran a zane. Ƙin amsa yayi, sai dubanta da yakeyi cikin takaici da ɓacin rai. “Mikike nufi?”.

“Babu abinda nake Nufi sai haƙƙinka dana baka gashi nan. Tunda ALLAH kaɗai yasan abinda kaci kaima”.

Wata dariyar takaici da tafi kuka ciwo yayi ya ɗauke kansa. “Asabe kina wasa da lamarina wlhy. Ince dai nine silar haɗa auren ko? To wabilahillazi zan iya rusashi a gabanki kuma na bashi wata sai dai ki hangi arziƙin”.

Duk da taji tsoron zancen nasa dan tasan zai iya sai ta balla masa harara. Zatai magana likita daya ƙaraso ya katseta. “Baba zaku iya tafiya da ita babu damuwa”.

Gaba ɗayansu suka juya gareshi, kafinma suce wani abu Fatima da bata tanka musu ba tunda suka fara ta afka ɗakin da Raudhan take Fatisa biye da ita. Asabe ma ɗakin ta juya da niyyar shiga mal. Ɗan-azumi ya samu damar warce kuɗin data saƙe a cikin zani. A wani irin muguwar zabura ta juyo, sai dai kamar walƙiya ya ɓacema idanunta. Ranta yayi ƙololuwar ɓacin da har ma ta kasa bin bayansa balle yin magana har Fatisa da Fatima suka fito riƙe da Raudha. Yini guda harta sake ramewa, sai idanu zuru-zuru ga allurar da akai mata yasa barcin bai gama sakinta ba.

“Mommy mike damunki?”.

Raudha ta faɗa a hankali idonta akan Asabe. Ƙwafa Asaben tayi tana magana cikin ɓacin rai, “Minene kuwa zai dameni idan ba ubanku ba, wanda ƙaddarar rabonku ta zama silar haɗuwata da shi. Wlhy a wannan gaɓar kuwa lallai zan shayar da Dauda zumar mamaki. Yanda yake jinsa tantiri nima tantiriyarce ta gaske, kuma zan tabbatar masa da hakan yau basai gobe ba”.

Dariya Fatima ta ɗanyi dan ita ko’a jikinta. Raudha kam hawayen da suka ciko mata idanu ne suka silalo a hankali. Hannu ta kai ta share da ɗan cije baki saboda kanta dake sara mata.

A haka suka hau mashin ko sisi babu a jikinsu. Sai da sukazo gida Asabe ta shiga ta kawoma mai napep ɗin masifa fal ranta..

 

Har aka sha ruwa Malam ɗan-azumi bai yarda ya dawo gidansa ba, dan yasan halin Asabe sarai. Ya tabbatar yau duk da azumin dake a bakunansu sai sun tara ƴan kallo a cikin anguwa, shi kuma baya buƙatar hakan tunda yasan shine mara gaskiya, shiyyasa ya zaɓi ƙin dawowa gidan har aka sha ruwa. Yadai samu gasashen naman kazarsa da fura mai sanyi yaci yay ƙat. Ya kuma ɗora da indomie da ƙwai da shayi wajen Bello mai shayi. Sannan ya ɗan zuƙa sigarinsa kara uku.

Sai wajen sha ɗaya na dare ya lallaɓo a tunaninsa kowa yayi barci. Sai dai yayi rashin sa’ar cin karo da Asabe dake zaune dakaka tana zaman jiran shigowar tasa. Yanako shigowa tai caraf da rigarsa taci kwalarsa. Tun sunayi iya su har kowa na gidan ya farka. Dama Larai na laɓe tana kallon komai tun farko tana kwasar dariya, tunda taga Asabe zaune taƙi shigewa tasan akwai wata a ƙasa dama, balle itama akwai tsiyar data harbo, dan tun maganar da taji a ɗazun game da Alhaji Maude Dallatu mai son Raudha hankalinta bai kwanta ba, suna fita a gidan itama ta fice.

Rigimace sosai ta harƙume a tsakaninsu harda doke-doke. Dan sai da maƙwafta suka shigo aka rabasu da ƙyar. Kuka sosai Raudha keyi tamkar numfashinta zai bar gangar jikinta. Dan ko leƙe bata leƙo ba dama tunda aka fara faɗan tana ɗaki kwance.

Abu kamar wasa har gabannin asuba wannan faɗa yaƙi rabuwa. Mutane har sun gaji sun koma gidajensu sun barsu. Ƴan gidan kam har yara sun farka dan kowa ya gagara barci. Duk suna a tsakar gida, Raudha ce kawai batako leƙo ba tana lafe a ɗaki tana faman dirzar kuka. Ko sahur ɗin kirki ranar babu wanda yayi a gidan. Kiran sallar asuba yasa Baba Nafi fara roƙona malam Dauda akan ya fita massallaci shi dan ALLAH ko hakan zai kawo masalaha. Shawararta yasa shi fitar yana faman huci, duk da ba yaune karon farko da suke irin wannan faɗan ba, sai yakejin zafin Asabe a yau fiye da koyaushe. Ji yake tamkar ya saketa ya hutama ransa.

 

Koda aka idar da salla maimakon yaƙi dawowa gidan sai shaiɗan ya dinga tunzurasa akan ya shigo yaga ƙarshen haukan Asaben. Yaran kawai ya samu suna kiciniyar alwala a tsakar gida. Dan Baba Nafi da su Fatisa sun lallaɓa Asabe da ƙyar ta shiga ɗaki itama bayan tayi alwala. Tana ɗaki zaune tana rusar kuka ya dawo, dan ko sallar ma haka tayita tana kuka. Wani irin ɗaci da zafin Malam Dauda takeji yau fiye da ko yaushe a rayuwarta.

“Haba Malam mi kuma ya dawo da kai gidan nan a yanzu?”. Baba Nafi dake tattare kayan wanke-wanke ta faɗa lokacin da malam Ɗan-azumi ke shigowa gidan zuciyarsa tamkar zata kama da wuta. Zuciyar tasa dama a kusa take, dan haka cikin masifa yace, “Na dawone dan naga ƙarshen isakancin Asabe yau a gidan nan!!”..

“Kai ɗin banza daka isa kaga ƙarshen iskancina Dauda. Kaima kasan ni nafi ƙarfin kanwar lasarka, dan ina dai-dai da wandama ya fika balle kai ɗin ƙaramin shegen bariki”.

Da wani irin rawar jiki malam Dauda ya cacimi taɓaryarsu ta daka yayi kan Asabe gadan-gadan. “Aiko yau zan tabbatar miki da ni babban Shege ne….!”

Baba Nafi datai saurin shan gabansa ta riƙe taɓaryar da sauri. “Haba Malam waini kam mike damunku yau haka ne? Yanzu akan ƙaramin abu dabai taka kara ya karya ba zance yaƙici yaƙi cinyewa domin ALLAH!”.

Hankaɗe Baba Nafi yayi, cikin matuƙar sake harzuƙa ya fisgi taɓaryar yana ƙoƙarin sake nufar Asabe da itama ta rarumo kujerarsu ƴar tsugunno ta nufosa, su Fatima suka riƙeta. Sake riƙesa Baba Nafi tayi dan taba duk ta gama cinyesa a tsaye ba wani ƙarfin kirkine da shi ba. Cikin matuƙar sake harzuƙa yake nuna Asabe da ɗan yatsa yana faɗin,

*_“Kije na sakeki Asabe. Na sakeki saki biyun daya rage tsakanina da ke!!_* Bana son sake ganin fuskarki, Idan ba hakaba wlhy yau sai na kasheki a gidan nan da hannuna”.

Da sauri Larai ta shige ɗaki wani irin ɗan karen daɗi na saukar mata a rai da zuciya, har ji take tamkar ta daka tsalle ta dire dan yau burinta ya cika. Itako babu abinda zatace da malam ɗan-kande sai godiya. Gashi ya mata aikin da taketa kashe kuɗi tsahon shekaru a cikin ƙanƙanin lokaci. Gwatsar wayarta da tasha ɗaurin ƙyauraye ta ɗauka ta shiga laluben ƙanwarta Haƙila danta guntsa mata wannan daddaɗan labari haka da farar safiyar nan ta juma’a.

 

A tsakar gida kuwa duk yanda Baba Nafi take ƙoƙarin ƙwaɓar Malam ɗan-azumi yaƙi saurarenta sai sake maimaita kalmar saki yake ga Asabe da gaba ɗaya jikinta yay sanyi kuma a lokaci guda. Dan yana ambaton ya saketa duk zafinsa da takeji kuma sai taji ya kau baki ɗaya. Da wani irin sanyin jiki ta saki kujerar hannunta jin hajijiya na neman kadata ƙasa. Riƙota su Fatisa sukayi suma jikin nasu na rawa.

Raudha dake cikin ɗaki zaune tana karatun Al-qur’ani tai saurin miƙewa tana dafe ƙirji, dan kalmar sakin nan tajita tamkar sukar mashi a ƙahon zuciya. Tuni ta nema kukan da takeyi ta rasa. Da gudu ta fito tsakar gidan, taje gaban Mahaifin nasu ta zube gwiwa a ƙasa tan roƙonsa akan yayi haƙuri karya saki Mommyn su dan ALLAH. Duk hukuncin da yakejin zai mata ita yayi matashi dan ALLAH duk zafinsa zata ɗauka.

Hankaɗeta yayi cikin rufewar ido yay waje yana cigaba da kunfar baki. Raudha ta miƙe da gudu ta bisa tana kuka amma ko waiwayenta baiyiba………✍️

 

 

 

*_Tofa yau dai da alama auren zobe ya ɓalle? Ko asabe zata yarda tabar gidane? Duk da kuwa saki uku ne a kanta idan aka tara da guda ɗaya na baya. Shin auren Raudha da Alhaji Maude Dallatu zai yuwu kuwa?. To minenen ma ma’anar BAƘAR INUWAr? Suwaye BAƘAR INUWAr? Mizai biyo baya a gundarin labarin BAƘAR INUWA? Dukan amsoshinku na cikin Littafin BAƘAR INUWA da nakeda tabbacin ya taɓo muku inda ke muku ƙaiƙayi. Karku ɗauka a gidan su Raudha kaɗai cakwakiyar zata ƙare. Sam ba haka bane, akwai wasu rikicin da gidajen a gaba. Sanin alaƙarsu da Littafin BAƘAR INUWA sai ka mallaki naka ankai har ƙarshe da kai. Masoya ba’a fara komai ba, dan kuwa a paidpages ne kawai zaku san minene gundarin labarin BAƘAR INUWA😉⛹🏻‍♀️🥰🥰🙏🏻_*

 

_Ku kasance da ZAFAFA BIYAR domin karanta daɗaɗan labaransu guda biyar dake tafe da salo na musamman masu ƙayatarwa_.

 

 

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09

 

 

Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

 

Please

*_Follow me_*

*_Share_*

*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

 

 

*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*

 

 

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥

_Safiyya Huguma_

 

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥

_Billyn Abdul_

 

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅

_Hafsat Rano_

 

*1*~ *_MASARAUTA_*💪

_Miss Xoxo_

 

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥

_Mamuhgee_

 

 

 

Guda 1👉300

Guda 2👉400

Guda 3👉500

Guda 4👉700

Guda 5👉1k

 

 

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

 

Bilkisu Ibrahim Musa

1487616276

Access bank

 

Number shaidar biya👇🏼

 

*_09032345899_*

 

 

*KATIN MTN*👇👇

 

09166221261

__________________

 

*_JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*

 

 

 

Guda daya=300F

Guda biyu=400F

Uku=500F

Hudu=700F

Biyar=1000F

 

 

*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

 

+227 95 16 61 77

 

 

 

*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

 

_____________________

 

 

*_BAƘAR INUWA…👇🏻_*

 

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09

 

 

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_

 

 

*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

 

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

 

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

 

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

 

*Enter an username* (Sunanki)

 

*Enter your password:* ( misali 12341234)

 

*Confirm password:* (misali 12341234)

 

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

 

*Continue with Google* – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

 

*Register* – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

 

 

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

 

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

 

 

Masu iPhone

 

Zaku iya bibiyar shafinmu

https://arewabooks.com

 

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*

 

 

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

 

+234 903 177 4742

 

 

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.

 

 

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

*_Typing📲_*

 

 

 

 

 

*_🌳BAƘAR INUWA….!!🌳_*

_{Gara rana dake}_

 

 

 

 

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

 

 

________________

*_Episode 4_*

 

 

……….Ruwa kawai tasha tunda aka kai azimin na yau na kusan ashirin da ɗaya, sai dai hakan baisa ta damu ba, duk da yunwa dake cin hanjinta dan koda asuba ma batai sahur ɗin kirki ba kasancewar tuwo sukai na sahur, itako a rayuwarta sam bata shiri da tuwo musamman miyan kuɓewa ɗanye. Sau da yawama idan taci gudawa yake sakata shi da shinkafa. Kai duk ma wani abu irinsu basu ciga damun Raudha ba. Tafi so da buƙatar abinci mai ruwa-ruwa irinsu fura, kunu, koko da sauransu. Suna fita Yasmin ta fiddo goran ruwa madaidaiciya dake ɗauke da kunu ta miƙama Raudha. “Aunty R gashi kisha”.

Cak Raudha ta dakata daga tafiyar da takeyi ta dubi Yasmin ɗin, ganin abu a leda yasata daka mata tsawa dan sam bata fatan abinda zai lalata rayuwar Yasmin ɗin itama. Cikin ruɗewa Yasmin ta fara rantsuwa. “Aunty R wlhy bani akayi, baba ce ta bani (Baba Nafi) sanda naje mata aika gidan kawu Rabi’u (Ƙanin Baba Nafi) na amso mata kunun batare da Mommy ta sani ba. Niko kinga banyi azumi ba shiyyasa na ɓoye miki shi dan karsu aunty Fatisa su gani su shanye ko Mommy”.

Ajiyar zuciya Raudha ta sauke da kamo yarinyar ta rungume a jikinta hawaye na ciko mata idanu. “I’m so sorry my little girl, bana son ki fara koyon hali irin nasu Aunty Fatisa ne shiyyasa. Dan ALLAH ki kiyaye karki bari wani ya yaudareki da abinda bamu da shi ya lalatamin rayuwarki kinji”.

“Inaha ALLAH Aunty R bazan yarda ba ai”.

Yasmin ta faɗa duk da ba komai take fahimta ba da ga gargaɗin ƴar uwar tata kai tsaye, saboda ƙarancin shekarunta. Dan Raudha ta bata kusan shekara shida a duniya, bayan haihuwarta Asabe ta jima kafin ta samu ciki, harma ta ɗauka haihuwar ta kare sai kuma ga cikin Yasmin ɗin..

Kama hanunta tai suka ƙarasa massallacin batare data amshi kunun ba, can gefe ta samu ta saka musu abin salla inda bazasu takura ba, dan sam bata ƙaunar zafi ita, sanyi ma idan yay yawa yana taɓa rayuwarta.

 

An gabatar da sallar isha’i da asham, bayan addu’oi da malam yayi tamkar yanda ya saba kowa yay ƙoƙarin kama gabansa. Raudha bata tashi ba, sai roban kunun da Yasmin ta ajiye a gabansu ta ɗauka ta buɗe murfin, duk da ya huce haka tasha kusan rabi ta miƙama Yasmin dake gyangyaɗin barci sauran dan tasha itama. Amma sai Yasmin ɗin tace mata ta ƙoshi. Sanin kunu bai damu Yasmin ɗin ba sosai yasa Raudha ƙarasa shanyewa sannan suka miƙe.

Sai da ta gama tattare musu kayansu sannan ta duƙa Yasmin tahau bayanta danta lura barci takeji. Yarinyar ta saki sassanyar ajiyar zuciya tamkar yanda Raudhan tayi itama. Koda suka iso gidan a tsakar gida suka iske kusan kowa a ƙofar ɗakinsa. Yaran nata hayaniyar surutu iyayen kowa na sabgar gabansa. Sannu kawai tai musu bayan sallama ta shige ta kai Yasmin ɗin ɗakin barcinsu da gaba ɗaya ƴammatan gidan kan kwana musamman idan ranar Babansu a ɗakin mamanka yake. Idan ɗakin wata yake daban zaka iya kwana a ɗakin mamanka ɗin. Fitowa tai tai ɗan uzirorinta batare data tankama kowa ba ta sake shigewa tai kwanciyarta dan su Fatisa a ƙofar gida ta barsu suna hira.

 

*_WASHE GARI_* Raudha ta tashi da ciwon mara mai tsanani tamkar yanda takeyi duk wata. dama tun kusan jiya takejin alamarsa kaɗan-kaɗan, batai wani yunƙuri ba dan maganin da take sha ya ƙare. dama Ya-sayyadi ne ke saya mata shi kasancewar yasan lalurar tata. Idan har zatai period sai kowa ya sani. ba ƙaramar azaba take sha ba na ciwon mara dana ƙafa. Daga ƙarshe taita kwara amai. Idan ka ganta a irin wannan halin ma saika ɗauka yaron ciki ne da ita. Dan a farkon fara hakan tana jss1 secondary kowa a gidansu dama makaranta sun ɗauka ciki ne da ita, duk da lokacin batafi sa’ar Yasmin ƴar shekara goma sha ɗaya ba. Sai da aka dubata likita yace period zata fara sannan hankalin malaman ya kwanta har sukazo da ita gida akaima iyayenta bayani.

Duk murƙususun azabar da takeyi a ɗakin babu wanda ya sani, dan gidan shiru alamar yaran duk sun fice sabgogin gabansu, manyan kuma kowa barcinsa yakeyi. Sosai take cin azaba, dan tun tana kuka ma har kukan ya gagara, tsanani yay tsanani har takai Raudha da suma.

 

Kamar yanda ya saba shigowa gidan fagan-fagan babu ko sallama yauma haka ya shigo, dan tun fitarsa sallar asuba bai sake shigowa ba yana rumfar ƴan gulma kamar yanda ake kiran majalisarsu. Jin gidan shiru ya sashi fara ƙwala kiran Raudha, dan a rin wannan lokacin ita kaɗai zaka iya samu a gidan tana bautar gyarawa, data gama take wucewarta wajen tafsir sai sha biyu ta dawo.

Shiru babu wanda ya amsa masa, yabi gidan da kallo a harzuƙe, ko’ina kaca-kaca da kwanika da tulin tsummokaran kayansu kusufi-kusufi. Tsaki yaja yana nufar ƙofar ɗakin Asabe. “Asabe! Asabe!!” ya shiga ƙwala mata kira, dan har yanzu haushinta na jiya bai bar ransaba, musamman daya kasance yanzun nan jabiru mai shago ya sake masa maganar kuɗinsa, shine ma dalilin shigowa gidan da yay.

Cikin barci Asabe taji muryarsa bisa kai, ta miƙe a zabure tana

 

Name: [Bakar Inuwa]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


2 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!