Hausa Novels

Bakar Sakayya Hausa novel complete

Bakar Sakayya Hausa novel complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: BAKAR SAKAYYA

 

Wannan littafin na kuɗi ne, Naira 300 ne for normal group posting sau daya a rana, sai Vip 500 posting sau uku a rana, zaki tura kudin ne ta wannan account number din 2004658577 Muhammad Tukur Bello, KUDA MICROFINANCE BANK, domin neman karin bayani sai ayi min magana ta wannan number 08142904255 Whatsapp only!*

 

Free page

 

Shafi na ɗaya

 

Iska me sanyi da ratsa zuciya ne yake buguna lokacin dana iso rugarsu *YIDI* Ruga me tsananin kyau da tsari! Fili ne fetal sannan tsakiya zagaye da bukkokinsu daga chan hannun hagu kuma garkayen shanu ne, sai gonaki, tafiyace mai tsahon kilomita 250 kafin ka shiga cikin gari! Mutanen Rugar sunan gudanar da rayuwaru cikin jin daɗi! Ilimin addini dana boko be yaiwata ba musanman ma na zamani dan duk garin babu wanda yake zuwa makarantar boko duk da kasancewar ba wani girma ne da rugar ba, kowa yasan kowa.

 

Suna da rafi me girma wanda yakan ɗauki tsahon lokaci kafin aje dan kusa da cikin gari ne, ranar Juma’ah ita c ranar da ake zuwa diban ruwa saboda tsananin nisa, idan ruwanka ya kare kafin next juma’a kana iya zuwa ka debo domin ruwa shine mahadin rayuwa, amma mafi akasari ranar juma”a ce ranar zuwan nasu.

 

Asalin Fulani ne! Kaɗan daga cikinsu ke jin yaren Hausa!.

 

Sunyi riko da al’adunsu na Fulani sosai!

 

Sannan duk karshen mako suna kai Nono cikin gari.

 

Kutsawa nayi cikin rugar. Yara, mata da kuma ƴan mata ne kowa sai harkar gabansa yake domin kyautatawa iyali.

 

A tsugunne na hangota cikin turken shanu ta durƙufar da kanta sai tatsar nonon shanuwa ta ke.

 

Sai da ta cika kwaryar dake hannunta sannan ta miƙe, lallai Allah yayi halitta wajen wannan yarinyar. Tabbas Fulani asalinsu ba ƴan Nigeria bane! They migrated into northern Nigeria daga senegambia region around the thirteenth to fourteenth century, bayan jihad na Uthman danfodiyo, Fulani became integrated a cikin Hausa culture of northern Nigeria.

 

Yarinyar na da tsaho amma ba sosai ba, tana sanye da tufafi irin na Fulani amma sunyi dukun² alamar dauda gashin kanta a cure gaban goshi zanen dake fuskarta ya fito yayi radau sosai kasancewarta Fara sosai. Bazata wuce 13yrs ba amma kham akwai diri da kyau.

 

” *YIDI! YIDI* (Means loving one) Juyowa tayi tana kallon me kiranta. *BODDIYA* (Big girl) ce, murmushi tayi hakwaranta da bata wankewa suka bayya duk sunyi wani iri.

 

Karasowa Boddiya ta yi, tsatsaf da ita ba kamar Yidi ba.

 

Cikin harshen fillanci ta ce ” GABƊO,yana gida ya dawo daga gona”

 

Rufe fuska Yidi tayi tana fad’in ” Toh ni me kike so nace?

 

“Ina ce ke kika ce idan ya dawo nazo na fad’a miki! Me kuma najin kunya?

 

“Kinga ni Maduujo zan kaiwa nonon nan zata tafasashi”

 

Daga haka Yidi ta bar Boddiya a wajen murmushi kawai Boddiya ta yi sannan tana barin wajen.

 

A kan tabarmar kaba ta tarar da mahaifiyarta tana zaune tana bushe geron da za’a yi fura saboda kai Nono cikin gari.

 

A gefenta ta ajiye Nonon tana fad’in ” Maduujo gashi!

 

“Toh Allah yayi albarka! Tashi ki hada wuta sai a dora!

 

Da toh ta amsa tana tashi ta nufi wajen icce.

 

Bayan ta kammala haɗa wutar ta ɗora tukunya sannan ta juya nonon a cikin ta rufe tana fad’in “Moddibo ya ce min zai zo kuma har yanzu bai dawo ba!

 

“Kinsan yanayin aikin mutan birni ko? Kuma mu da mukayi sa’a yana koya mana addini sosai ai ba zamuyi korafi dan bai zo ba saboda shima yana da nashi uzurin ko?

 

Gyada kai tayi alamar eh. Ita kham tana jin dadin karatun Moddibo saboda yana koya musu abubuwan da suka shafi addinin Islama sosai, gashi har Hausa ta fara koya duk ta dalilin Moddibo.

 

Sai da ta cire man shanu sannan ta sauke nonon ta ɗora tuwan dare saboda yamma tayi.

 

Bayan sallar magariba tana zaune tana cin tuwo Boddiya ta shigo.

 

Yidi ce kawai a tsakar gidan daga ita sai hasken farin wata. Zama Boddiya tayi a kusa da ita tana fad’in ” Yidi tun shekaran jiya fa bakiyi wanka ba! Ga GABƊO chan yazo tad’i.

 

“Nifa yau bazanje ko ina ba Aradu! Yidi ta fada tana siɗe hannunta.

 

“Shikenan, ai kin kyauta sai da kika ga an kusa auren sannan kike masa wulakanci ko?

 

“Ba wani wulakanci fa! Kuma shi yace miki an kusa auren? Bayan na ce masa ya turo yaki?

 

“Ba ƙi yayi ba Yidi! Kinsan halin Nene ko? Ita ce ta ki yarda!

 

Cike da mamaki Yidi ta kalli Boddiya ta ce ” Nene? Saboda me toh?

 

“Nene ta gargadeni kar na fad’a miki amma bazan iya boye miki ba, Ja’o ne yaje ya sameta har gida wai muddin bata raba Gabɗo dake ba sai ya hallakashi!

 

“Ja’o? Ja’o dai wanda na sani? Yidi ta fada cikin mamaki. “Eh fa! Rannan ma har duka sukayi wa Gabɗo shiyasa yayi wannan rashin lafiyar ai”

 

Tashi tsaye Yidi tayi tana fad’in ” Lallai ma Ja’o! Nifa bana sonsa! Duk rugar nan kowa yasan GABƊO nake so!

 

Ita ma Boddiya tashi tayi tana fad’in ” Nidai shawarar da zan baki gwanda ki samu Ja’o ki rokeshi ya rabu da rayuwarki dan kinsan ba hankali gareshi ba!

 

Yidi bata ce komai ta fito

 

A zaune ta ganshi kan dutse yana sanye da riga ta yadi me budadden gefe da gefe sai wani dangyalallan wando shima na yadi ne amma kalar sa daban dana rigar sai hula irin wadda Jonathan yake saka wa but nashi ta sakar kaba ce.

 

Namiji ne sosai, wannan dan jikin na Fulani shi kham ba haka yake ba! Yana dan kumari, shekaru bazai wuce 20 ba, shima akwai kyau Masha Allah sai dai bashi da tsagu kamar na Yidi.

 

Daga dan nesa dashi ta rakube tana boye fuskarta. Iskan me sanyi da yaji da kuma ƙaruwar bugun zuciyarsa shi ya tabbatar masa da Abar kaunarsa ta iso inda yake. Juyowa yayi yana me ambatar sunanta.

 

Kamar yadda ya saba ganinta rakube jikin gini hakan nan ya ganta yanzu sai lekansa take take. Murmushi ya sakar ma ta yana gyara zamansa a kan dutsen ya zuba ma ta idanunsa.

 

Ƙasa tayi da nata idanun dan bata iya kallonsa.

 

Boddiya ce ta fito ta wucesu.

 

“Yidina fito mana! Ya fada a sanyaye. Maƙe kafada tayi alamar a’a. Tasowa yayi daga kab dutsen ya nufo inda ta ke, da sauri ta matsa kadan tana sunkuyar da kanta. Rashin tsaftar Yidi sam bata damunsa bashi ba buri daya wuce ya aureta dan baya tunanin idan ya kara jan lokaci zai sameta a matsayin matarsa!

 

Ɗagowar da zatayi ta ga Ja’o da katon icce zai zabgaww GABƊO. Da mugun karfi ta kira sunan GABƊO, kafin ya ankara Ja’o ya sauke masa iccen a keyarsa. A wajen GABƊO ya sulale jini ya fara fita ta kansa.

 

Ihun da YIDI ta yi shi janyo hankulan mutan rugar. Ja’o kuwa tuni ya bar wajen.

 

Mahaifiyar YIDI ce ta fito daga turakarta haka ma sauran mutanen da suka kusa da su Yidi.

 

*SHEWDO* Ne ya nufo GABƊO da sauri yana ɗago dashi. Cikin Muryar Kuka YIDI ta ce ” Ja’o ne ya dake shi kuma ya gudu”

 

“Ja’o? Shewdo ya fada yana kallon Yidi. Kai ta gyada alamar eh.

 

“Tabbas ya kamata a dauki mataki kan Ja’o! Bazai lalata mana gari ba! Ina ce yarinyar nan ga wanda take so! Ai shi soyayya ba’a dole ko? Cewar wani dattijo yana kallon halin da GABƊO yake ciki.

 

“Shewdo shigo dashi ciki” Cewar mahaifiyar YIDI tana kallonsa.

 

Da toh Shewdo ya amsa, yana riƙe GABƊO zuwa cikin gidansu Yidi, dakin marigayi mahaifin YIDI aka kwantar dashi, Maduujo ce ta umarci YIDI ta gado native medicine a dakinta. Da toh YIDI ta amsa tana zubar da hawaye.

 

Mutane kuwa watsewa sukayi suna Allah wadai da halin Ja’o.

 

Shewdo shi ya karbi magunguna ya shafawa Gabɗo bayan Maduujo ta haɗa komai.

 

“Cikin dare zai tashi sai ka kula dashi, bari na je gidansu na sanar da Nene”

 

Cewar Maduujo tana kallon Shewdo. “Toh Maduujo” Shewdo ya amsa yana maida kallonsa ga GABƊO.

 

Tare suka fita da Yidi.

 

A cikin turakata suka tarar da Nene tare da Boddiya.

 

Boddiya na ganin mahaifiyar Yidi tasan zata sanar da Nene abinda ya faru ba ita kuma ta boye ma ta saboda bata son wani tashin hankalin.

 

Gaisawa sukayi cikin mutunci sannan Maduujon Yidi ta ce ” Yaron nan Ja’o shi ya far ma GABƊO! Amma da sauri yanzu na saka masa magani! Zai zauna chan wajena kafin safiya shiyasa nace bari nazo na fad’a miki! Yana chan tare da abokinsa Shewdo”

 

Shuru Nene tayi, daga bisani ta ce ” Allah ya bashi lafiya”

 

Sallama sukayi sannan suka dawo gida. Nene kuwa ta ayyana a ranta ko GABƊO zai yi hauka sai ya rabu da Yidi! Bazata bari Ja’o ya kashehi akan ta ba! Idan yaki zata tura shi birni yaje chan ya nemi na kansa ko gonarta ce zata siyar!……

 

*Note; cikin harshen fillanci suke magana*

 

*Littafina na kuɗi ne kamar yadda na fad’a idan kina son cigaba da karantawa toh ki siya but yanzu zan cigaba da sakin free pages*

 

*For more information u can contact me via 08142904255 Whatsapp only*

 

Autarmama ce.

Leave a Comment

error: Content is protected !!