Hausa Novels

Bakar Tafiya Hausa Novel

Bakar Tafiya Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: BAƘAR TAFIYA

 

( *HORROR STORY* )

 

*BY MEEN@T A YANDOMA*

*MARUBUCIYAR FATALWA*

 

*BISMILLAHIR RAHAMINIR RAHIM*

 

 

MANAZARTA WRITER’S ASSOCIATION*

 

 

*WANNAN LABARIN ƘIRƘIRARREN LABARINE, SUNAYEN GARURUWA DA WASU WURAREN DUK ƘIRƘIRARRUNE*

 

 

*BAN YARDA AJUYA MANI LABARI TA KOWACE SIGABA SAI DA IZININA, DAN ALLAH A KIYAYE*

 

____________________

*PAGE* 1️

 

….Wallahi ƙarya kake Habib, baka isaba ka hanani zuwa bikin ƙawata dole ne inje duk wani tsoratar dani da kake akan kar inje.”

 

Miƙewa yayi a fusace.

“Ke harni zaki kallah kice ina maki ƙarya, to in har kika bar gidan nan bada yawuna ba kuma duk abinda yabiyo baya kada ki kuka dani ki kuka dakanki.”

 

“Oho dai! Tafiyace ko kana so ko baka so sai nayi, yardarka da rashinta kai suka dama banga wanda ya isa ya hanani tafiyar nan ba.”

 

“Haka kika ce?, to Basma jeki zaki gani, sai kinyi nadama kuma kada ki sake ki jemani da Ɗa ko ƙofar gidan nan ne.”

 

“Ina zani da Ɗanka haka kawai ya takura mani, shakuruminka Ɗanka gida zani barshi.”

 

Ficewa yayi daga gidan zuciyar shi na matuƙar yimashi ƙuna.

__________

….Kuka take kamar ranta zai fita ga mahaifinta tsaye kanta da wayar wuta, jibgarta kawai yake babu ƙaƙƙautawa,

“Ni zaki zubda ma mutunci Salma! Ince maki kiyi hakuri amma ki kafe sai kinje bikin wata ƙawar banza, kinko san illar dake tattare da hanyar da zakubi?, to ƙara in karya ƙafafunki inga da wadanne ƙafafun zaki tafi,”

 

“Haba Alhaji!, kasheta kakeson yi?, dan Allah karabu da ita hakanan kada kayi mata zata illar kanakasa ta.”

 

 

“Ki barni in nakasata inga da wadanne ƙafafun zata bar gidan nan, wurgar da bulalar yayi ya fice daga falon.”

 

“Yanzu Mama ace duk yadda muke da hajara amma ace Daddy ya hana ni zuwa bikinta, kawai dan ance hanyar nada haɗari.”

 

“Ke fah sakara ce, yanzu so kike a gabanshi in goyi bayanki, ai dole ne kije bikin hajara kada ki damu in lokacin yayi ce mashi zaniyi kinje biki a dangin mu.”

 

 

(Kuji abun takaici uwa daya kamata tabada tarbiyya itake watware wadda mahaifin yabada, Basma kinyi kuskure kina kai kanki ga halaka dakinsan mizaku iske ga tafiyar da kinyi zamanki gida  muje zuwa.)

 

Rungume momyn ta tayi tana murna.

“Yawa momy na shiyasa nike ƙara sonki, yanzu Momy zani nunawa daddy na haƙura da tafiyar dan kada yayi zargin wani abu.”

 

“Yauwa kinuna mashi, shima nasan dan yaga ke ɗaya ya mallaka shiyasa bai so kiyi tafiyar, ga kuma abokinshi munafuki daya ce mashi Wai hanyar bata da kyau.”

 

Tashi Salma tayi ta nufi ɗaki.

“Momy na tafi in shirya kayana kinsan wallahi na ƙagara inga lokacin nan yayi.”

_______________

“Jafar abinda zani faɗamaka kaji tsoron Allah aduk inda kake, tafiyar nan da zakayi nemo Mahaifinka daya daɗe da bacewa aka ce an ganshi achan garin, Jafar ka riƙe addu’a ka kiyaye yin sallah a duk halin daka tsinci kanka, wallahi jinike badan Mahaifinka daya bata zakaje nema ba da na hanaka tafiyar nan saboda an ce hanyar wata shu’umar hanya ce sai dai addu’a.”

 

Tunda ta fara maganar kanshi yake ƙasa sai yanzu ya ɗago.

“Umma addu’arki nike nema i ta ce kaɗai nike buƙata a duk inda nike Umma.”

 

“Jafar Allah ya tsare hanya, Allah ya kareka a duk inda kake, yanzu tashi ka fara haɗa kayanka.”

 

“To Umma nagode da addu’arki, insha Allah kamar yadda kika buƙata zani kasance mai ruƙo da addini da kuma addu’a.”

 

 

______________

“Yanzu Rabi’u tafiya zakayi ka barni, katai maka kada kayi rafiyar nan ance hanyar shu’umar hanya ce, kada kaje a kashe mani kai.”

Ta ida maganar hawaye na wanke mata fuska.

 

“Haba! Haba!! Haba!!! Kaka nifa kidaina ce mani Rabi’u, Rabson guy nike haba in cikin abokaina ne ai saiki kunyatani.”

 

“Nidai ina roƙonka ka janye maganar tafiyarnan Rabi’u.”

 

“Kutt! In zanye fa kika ce?, Kaka ai dole in yi tafiyar nan ga inda ɗan ladi yace zani samu kuɗi amma kina maganar in zauna ai sam bazai yiwu ba, kinga bari inje in fara shin tafiya.”

Ya fice yana tafiya yana yin doro kamar waninzabo irin tafitar gayun zamanin nan.

 

Binshi tayi da kallo zuciyarta na mata ƙuna saboda kinjin maganarta da jikanta yayi, ahalin yanzu shi kadai ya rage mata tun bayan rasuwar iyayenshi sanadiyyar gobara shi kadai ya tsira.

 

Shima gashi yanzu yana shirin kai kanshi ga halaka, dan tun tana budurwa takejin labarin dajin kai kazo, mugun daji ne wanda indai ka fita cikinshi ka auna babban arziƙi

 

____________

“Biba ba wai banison tafiyarki bane, Aa ina jin tsoron hanyar da zaku bi, Biba Mahaifinku ya rasu tunda Allah ya amshi abunshi ke kike sana’a kina hidima damu yanzu ace kema karatu zaki tafi, ni babbar damuwata wannan shu”umar hanya da zaku bi ta wurinta, in na tuna hankalina na matuƙar tashi Biba.”

 

“Mama addu’ar ki a duk inda nike ita nike buƙata, Mama in na zauna banyi karatun nan ba dami zani taimake ku nan gaba nidai kiyi mani addu’a Mama.”

 

“Shikenan Biba Allah ya tsareki a duk inda kike, biba ki riƙe maraicinki kada ki banzatar da rayuwarki Allah yayi maki jagora Allah ya kareman ke abduk inda kike.”

 

“Amin Mama.”

 

“Bari inje in samo rancen sayayyar da zaki ida.”

 

“To Mama sai kin dawo.”

 

 

*MUJE ZUWA LABARIN BAI FARABA, SOMIN TABI NE NAN,KUDAI KU BIYO NI.*

 

 

*COMMENT*

*SHARE*

 

 

 

 

 

*MEEN@T…*

1 Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!