Hausa Novels

Bakin Rijiya Hausa Novel

Bakin Rijiya Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

[07/09, 11:07 pm] +234 703 966 0069: 🕸️ *BAKIN RIJIYA*🕸️

( _Ba wajan wasan yaro_ _bane_)

 

Na Khausar Muhammad mashi

 

Bimillahir rahmanurrahim,

 

 

 

 

Gafaran kudai masu gida… wata yar tsohuwa ta fada tana sawo kanta cikin gidan mai wadataccen fili da katuwar bishiyar mangwaro a tsakiyar gidan wacce ta bada inuwa me dadi… Uhm wai ko babu mutane ne acikin gidan an barni inna ta rafka sallama ni kadai…? Siririn tsakin da tajiyo daga gefan tane yasa tsohuwar juyowa da sauri… “Hmmm ai toh yanzu naji batu, daman idan baki nuna halin naki ba ai baki cika diyar Suwai ba, wlh Batula ki fita idona na rufe.. Shegiya ne idanu kamar na mujiya…

Mikewa budurwar tayi gami da rike kugunta tana girgiza cike da tsiwa.. Dadin abinma dai wajan ki na gada shegun idanun, kuma kin shigo gida kina mana sallamar karuwai wazai amsa miki…

Sakin Karamin botikin hannun ta tsohuwar tayi tana rafka salati gami da kuka.. Yanzu Batula nice karuwar… ihuhu wai babu Jama,a ne a cikin gidan ne…

Kamar jira ake ta rufe baki matan gidan suka shiga fitowa dan tun shigowar Nennen sunaji, ba mai sun fitowa ne kawai saboda jarabarta Batula ce kawai ke fadi ma Nennen bakar magana a zauna lafiya sai dai ta gama zagin ta saboda itama Batular ma tsiwaciya ce ajin farko….

Ke maza Saratu jeki ki kiramin Ubanki Dan asabe yaji ya gani an kira Uwarsu karuwa ta fada cikin matsar kwallah…

Cikin kunkuni Saratu tace”Nifa guga nake Nenne ki aiki Habi mana..

Uwarki nace kin wuce ko kuwa.. Harara mahaifiyar Saratu ta wurga ma Nenne tana fadin “Kardai a zageni bani nakar zomon ba ta shige daki… Da kin tsaya kin karasa fitsaran ki Inno wallahi yau da na nuna miki dan asabe ya haihu a cikina. Kin san halina sarai…

Kallon sauran matan gidan tayi tana muzurai kukuma uban me kuke jira ne.. dariya suka sheke dashi kowacce taja yaran ta zuwa daki cikin nishadi, sun san yau ba qaramin tijara Nenne zatayi ma Suwai ba idan ta dawo daga anguwar da ta fita…

“Batula kuwa ba tare da damuwar komai ba ta gama wankin kannen ta ta shigewar ta dakin su tana wake wake wanda ya kara bakanta ran Nenne…

7:09pm na dare

 

Tsuru dukka matan gidan da yaran gidan sukayi suna sauraran Baba Shamsu wanda shine Babban da awajan Nenne, masifaffene dan tijara dan bashi da kirki ko kadan, kullum fuskarsa a daure take dan lokacin baya ma yaran gidan sunji labarin ya taba aikin soja..

Duk gidan tsoran shi akeji harta da Batula tana matukar tsoran sa, batason yau zai dawo daga kudu ba inda yake dan kasuwancin sa shiyasa ta tsulama Nenne tsiya…

Kallon Suwai yayi cikin kakkaurar murya yace inna ita Batulan take? Kanta a kasa cikin girmamawa tace” Wallahi malam tun yamma ta shige ban daki ta rufe nayi nayi ta bude taki…

“Ko kuma kika rufeta ba.. Nenne ta katse ta cikin jin haushi, ai duk rashin mutumcin da Batula keyi ke kike daurata akai.. “Wai yau da girmana tsofai tsofai Batula tace min karuwa nida har na gama kuruciyata ko gidan gala ban sani ba ta fadi tana sharbar hawaye da bakin zani…

Cikin fusata Baba Shamsu ya mike zuwa dakin Suwai, jim kadan sai gashi rike da hannun Batula jiki na rawa, wayar chaji yace Saratu ta miko masa ita kanta da wasu yan group din Batulan har sun fara hawaye, yayin da wasu ke murna sosai…

Babuji ba gani Baba Shamsu ya hau tsular Batula tana ihu Dakyar Baba Dan asabe ya kwaceta daga hannun safe..

“Dakyau Shamsu kabiyani, yanzu saura abokin nata Mahmuda shima kaci kaniyarsa yau da safe na dibo ruwa a buta zan shiga ban daki yaran nan ya min wata wawar bangaza kadan ya rage na fada rijiya…

“Kai Nenne ki fadi gaskiya zagin shifa kikayi.. amshi naka dan nema na sanya bakin gane.. harara Goggo Larai ta makama danta Shafi,u dan ba karamin aikin Nenne bane ta sanya a zane shi…

Kun daiji abunda na fada muku bazan lamunci ana wulakanta mana Uwa ba, shima Mahmudan zai dawo ya sameni da sauran yan uwansa, daga shigo wata unguwar mutum kusan biyar suka kawo min karan yaran gidan nan….

“Kai dakata Shamsu bakuma zan lamunci wannan ba, uban me sukayi da za,a sanya musu ido nifa banaso ato..

Hmmm Nenne kedai ba kyason lefin su kawai, ya fadi yana shigewa dakin Goggo Larai matar sa ta farko..

“Atoh ai gaskiya ne, mikewa tayi gami da nade tabar marta tana yatsuna fuska, hmmm kowa yaci tuwo dani miya yasha tafadi tana shigewa dakin ta.. ahaka taron ya watse Batula kuwa dama tuni tayi daki tana kunjin Kuka…

Hmmm kadan kika gani tunda kunnen ki na kashine… Innaji ko kafin na fita sai da naja kunnen ki akan tanka ma Nenne, amma bakiji ba, daman ai jiki magayi..

Cikin tausayin Yayarsu kannen nata kusan su uku mata biyu na miji daya suke rarrashin ta, ruwan zafi Umma Suwai ta debo tayi bandaki dashi, Batula na kuka Umman ta gasa mata jikinta kana sukayi shinfida suka kwanta, kura ma Yaran nata ido tayi tana tunanin shekarun baya da suka shude….

 

ASALINSU

 

TAKU KHAUSAR MUHAMMAD

[07/09, 11:07 pm] +234 703 966 0069: 🕸️BAKIN RIJIYA🕸️

 

Na Khausar mashi

 

*2*

 

 

MALAM HABIBU KURA

Cikakken sunan Mijin Nenne kenan, mazaunin kauyan Kura ne dake daf da garin kano, anan aka haifeshi yayi karatun allo a kauyan su, neman kudi ya kawo shi cikin birnin kano tsumdum. Tun yana karamin sa Allah yayi ma iyayan shi rasuwa sai rikon sa ya dawo hannun kanin Baban shi Malam Hassan kura..” Alokacin ya shigo kano da kafar dama dan yana yar sana,ar shi ta wanki da guga yana samu daidai babu laifi, hakan yasa bayan ya dan tara kudin sa ya koma gida domin ya samu mata yayi aure.. cikin hukuncin Allah soyayya ta sarke tsakanin sa da kanwar shi Fatiti wato Nenne, Habibu akwai hakuri kwarai da gaske inda Fatiti take matsiwaciya ajin farko, babu wanda bai son tsiwarta ba fada kuwa kullum tayi da yaran makota har an kaji da kawo kara..

Hakan yasa da Habibu ya sanar da Baban sa Malam Hassan yana son Fatiti ya dunga murna dan yason shi kadaine zai iya rike Fatiti yayi hakuri da ita.. “Ba a dauki lokaci ba akayi auren Habibu ya dauki matarsa Fatiti suka taho birni, gidan haya abokin sa Hashim ya kama musu ciki daya da rumfa kyauta wanda yace gudummawar shice, ba karamin dadi Habibu yaji ba dan Hashim na matukar kaunar sa, haka tunda yazo garin kano yake taimakon sa harta da shagon da yake guga na mahaifin Hamshim ne..

Unguwar dawanau suka fara zama anan Fatiti ta haifi danta na farko Shamsu, sai Habibu Dan asabe kenan, sai Hashim mahaifin su Batula, daga nan kuma Fatiti ta dunga bari akai akai, sai da Hashim ya basu shawarar zuwa asibiti mai dakin sa Kulu ta rakasu dan zumunci sukeyi sosai, matsala Fatiti take dashi a mahaifarta dan haka suka juya mahaifar ta huta..” Aikin da Hashim ya samu aka turashi garin Adamawa shiya sanya rabuwar shi da aminin sa Habibu sunyi kuka sosai haka ma matan su, hakanan suka rabu bayan mahaifin Hashim ya mallaka ma Habibu wani katon fili dake na,ibawa..”Godiya sosai Habibu yayi haka Malam Hassan har nan kano yazo godiya wajan mahaifin Hashim,…

“Cikin sauri rayuwa ke gudu Habibu na samu sosai da kasuwancin sa haka yana ginin filin da aka bashi a hankali, “Rasuwar Baba Hassan ce ta riske su cikin tashin hankali suka tafi Kura, sunyi kuka sosai sati biyu tsakani itama Gaggo mahaifiyar Fatiti ta rasu, sai da sukayi kusan wata uku kafin su dawo kano, zumunci tsakanin Habibu da Hashim yayi wuya dan lokacin babu wayar salula sosai, masu kudin gaske ke iya siyan wayar…

Cikin shekaru biyar Habibu kura ya kammala ginin sa yayi sashe kusan hudu dan Yaran sa idan suka taso, yana da sha,awar zama tare da yaran sa har auren su…

 

BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYU

“Cikin shekarun da suka wuce baya Allah yayi ma Malam Habibu kura rasuwa, Nenne ta hada kan yaran ta ta basu tarbiya ingantacciya, haka aka cigaba da tafiya suna matukar bin umarnin Mahaifiyar su Nenne, Baba Shamsu ne ya fara aure da Larai itama yar Kura ce Yaran su biyar da larai maza biyu mata uku, Mahmuda da Shafi,u sai Habi da Lawisa.. sai matarsa ta biyu Goggo Luba itama yaran ta Biyar da Baba shamsu duk kanana ne sai Baba Dan asabe matar sa daya Harira suna kiran ta Inno. Itama yaran ta uku Habu salmanu sai Saratu auta, Sai marigayi Hashimu Allah yayi masa rasuwa sanadin hatsari matarsa daya Suwaiba ita yar cikin Kano ce yaran su hudu Fatima Batula, Raliya sai hajiya da Sauban.. wannan kenan…

 

WASHEKARI

 

Da zazzabi Batula ta tashi, hakan yasa bayan Umma ta kara gasa mata jikinta tace ta kwanta ba sai taje makaranta ba..

Yanzu Umman mu Yaya bazataje makaranta ba yau.. cewar Raliya tana sanya kayan makaranta..

“Eh bazata samu zuwa ba, kuma kuyi sauri ku shirya kubi Saratu..

Toh Umman mu, fita tayi ta hau dama musu kunun da za,ayi kumallo dashi, cikin mazubi me kyau ta zuba ma Nenne dumaman tuwo da kunu cikin wani kofin sulba.. Raliya maza dauki ki kaima Nenne ki dawo ku karya, Toh Umman mu Raliya ta amsa tana hararan kumallon Nennen dan har yanzu haushin Nennen takeji tunda tasa Baba Shamsu ya duki Yaya Batula…

“Nenne na zaune saman tabarmar ta tana kullin kuka dasu kayan kamshi na miya, gefe daya kuma rediyo ce ke ta aiki tana sauraran labarai, jin sallamar Raliya yasa ta dago kanta gami da amsawa. Nenne gashi inji Umman mu..

Au toh ashe za,a kawo min kumallon nawa nayi zaton barina za,ayi da yunwa ta karni tunda na sanya an daki yar gwal dinta.. harara Raliya ta wurga mata gami da dangwarar da kayan kumallon tana fadin kanki akeji ta juya ta fice… Kinyi ma uwarki Suwai kinji ko, mara ta ido zaki dawo ne ai…

Haba Nenne ke dawa da safen nan haka.. “Cikin hararar Baba Dan a sabe tace”Ban sani ba Ubana Hassan.. yo kona fada maka maganin abun zakayi, Shamsu ne kadai kemin maganin yaran nan amma kai da marigayi baku tabuka komai, toh wallahi baku halina ba, in banda tsufa ma akwai me iya ta6a Fatitin Mamman ne na kyale safe… “Hmmm Nenne kenan ai duka baya magani sai addu,a ni yanzu Lamarin Mahmuda ne ke damuna yau da asuba fa a zaure na same shi da alama nan ya kwana abuge dan sai warin wiwi yakeyi, banason sanar da Yaya Shamsu kinsan halin sa…

Cikin daga murya da sallallami Nenne ta shiga tafa hannu.. Yanzu shaye shaye Mahmuda ya koyo, haba da alama mana jiya ya kusa bankadani rijiya ai kuwa dole ka sanar da Shamsu dan muyi ma tufkar hanci, daman shi da Batula ne fitsararrun gidan shiyasa suke shiri sosai ai, yau ma baka gaba dakyar aka aiko min da kumallon safe dan nasa an buga yar gwal. Hmmm haba Nenne ai wlh Suwai na kokari, duk cikin matan gidan fadamin me kawo miki kumallon safe, innaji ko abincin rana aka gama can suke dire miki gaban murhu ya gama gantalinsa… Kaga Dakata ai ba kaunar laifin Suwai kake yiba da yaran ta naji..

Murmushi yayi yace ko daya, watarana inna fatan kema ki gane hakan Nenne, ni zan fita ga wannan kidan rika babu yawa..

Kai Dan Asabe baka gajiya, toh na gode Allah yayi muku albarka baki daya, kadai yi kumallo ko dan nasan halin Inno. Nayi kumallo Nenne bari na tafi, “Toh Allah ya tsare, idan kaga goro Ka tahomin dashi…

Insha Allahu Nenne. Daki ta koma bayan ta adana kudin da Dan Asabe ya bata kana tayi kumallo…

 

Free book

 

Khausar ce

[07/09, 11:07 pm] +234 703 966 0069: 🕸️ ️BAKIN RIJIYA🕸️

 

Na Khausar Muhammad mashi

 

 

*3*

 

MAJALISAR DATTAWA

 

“Hmmm Rayuwa tayi zafi nake fada maka Malam Mudan, wai dan garin kwakin nan da talaka ke siya yanzu nema yake yafi karfin aljihunsa..”Bari kawai Dan Tani, yanzu fitowa ta gida haka na bar iyalaina basuci komai ba, dakyar mai dakina ta samo kullun koko dan kadan zasu kada susha.. “Ai Talaka na shan wahalar rayuwa fatan mu Allah ya sa mucika dakyau da imani..

“Toh Ameen.. Assalamu alaikum barkan mu da hantsi… Au Malam Bashir barka dai har an fito kenan.. Eh wlh mun fito zamu tafi nema kuma.. Toh Allah ya taimake mu baki daya suka fada tare.. Ameen.. Am nace wai wutar unguwar nan ta kara lalacewa ne Malam Mudan, inna ce shekaran jiyan nan muka hada dari biyar biyar aka gyara mana transformer?”Hmm Hakane Malam Bashir, wlh dan banzan Yaron nan Mahmuda na gidan Kura su suka kara sace abunda aka siya, ni ganau ne ba jiyau ba dan cikin dare na fito siyan maganin sauro na ganshi da Hatsabibin yaron nan Tero yake kowa.. “Ai kuwa bazai yihuba dole ne mu fadama Iyay…. “Dan uwarka je kafada masa. Dakus ba, Ka dade baka jeba, sukaji muryan Mahmuda da sauran zugan abokan shi yan daba..

“Cikin fusata Tero ya shako wuyan Malam Bashir da cikin sa ke kadawa ya an taya masa zagi,. Kai baaba daman na fada muku gayen nan dan iyane ne kawai mu koya masa hankali shida bakin munafukin nan yanuna Malam Mudan…

“Kai sakarsa dan Uwarka Mahmuda ya fadi yana hararar Tero, ku kyale shi sunci darajar Iyalan su da muke gaisuwar arziki dasu, kuma dama naji kunkai karar kanne na wajan Dakus aradun Allah idan baku fita hanyata ba sai na sassara mutum… “Kai kumuje yace da zugar yan daban,Kudi Tero ya zara daga aljihun Malam Bashir yana auna masa harara, haka suka bisu da ido babu bakin magana…

 

 

A kofar gidan su ya dakata gami da kallon sauran ku kuje zuwa karfe daya mu hadu arumfar Baushe kai kuma Tero da Master ku biyo ni suka rufa masa baya zuwa cikin gidan rike da sanduna Tero kuma wata sharbebiyar wukace a hannun sa….

“Duk yaran gidan na zaune kasan bishiya suna hira kamar yanda suka saba, Inna Larai bata nan haka Umma Suwai ta leka makota barka, Hajiya Nenne kuwa na bakin kofar dakin ta tana shan iska.. Tun sallamar sa da yayi ya shigo cikin gidan Nenne ta miki da sauri cikin dafe kirji ga tsoro daya kamata sosai..

“Subhalallahi Mahmuda yakin badar na biyu akeyi na gan ku haka da adduna da makamai.. “Cikin daure fuska daman yana kule da ita fadan da tasa Baba Shamsu yayi masa ga dukan Batula da tasa akayi yace”A,ah yakin duniya na uku akeyi zamu fita Jahadi.. dariya su Batula suka gimtse jin amsar daya bata..

“Toh wallahi babu mai shiga mana cikin gida da wadannan makaman, Kai kuma Lurwanu kai ma rayuwar daka dauka kenan tace tana kallon Master,.. Haba Kakus Yawane wlh,.. Ka zagi uwar ka Safiya wlh, maza kufice daga gidan nan yanzun nan..”Kai kumu shige ciki wannan tsohuwar kunsan ba hankali gare taba.. nan suka shige zuwa shashin dakunan Samarin gidan..”Eh annabi yayi gaskiya, nice mahaukaciyar ko ta muzuba mu gani, Ke Saratu dan nomin lambar Baban ku Shamsu.. Toh Nennen mu ta fadi gami da amsar wayar kashe wayar tayi tace”Ai Nenne babu chaji a wayar..

“Toh bari su dawo kawai ayita ta kare..

“Yauwa ke inna Batula ne Mahmuda ya tambayi Saratu dake kwashe shanya a tsakar gida.. “Gani Yaya.. Ta fadi tana fitowa daga dakin su, Yauwa amshi nan Sisto, dahuwa mekyau zakiyi ma taliyar nan akwai kifi a ciki kiyi sauri dan yunwa mukeji.. “Toh Yaya amma nima na dafa zan diba ko, karki damu yi maza ki gama..

Tare da Saratu suka gama girkin gami da kai musu, sunyi rashe rashe a dakin Mahmudan Tero nata aikin banka ma cikin sa sigari..

Hmm Allah Ya shiryi su Yaya Mahmuda cewar Batula cikin damuwa, ameen ai duk abokinsa nan Tero ne ya bata shi… Ki daina fadin haka Saratu shima Allah ya shirye shi tace toh ameen..

 

Washegari Nenne ce tafe da yamma ta dawo daga kasuwa wanbai tayo sarin kayan da take siyarwa kayan kamshi, ita da Raliya suka fita kasuwar ta rakata, suna tafe tana mitar me napep ya cika mata kudin mota ya amshi hamsin.. “Kai Nenne kin fiye korafi wlh yayi mana sauki, daga kasuwa zuwa nan naira tamanin ake biya fa.. “Kinci gidan ku Raliya, ai naga kinfi kaunar dan sahu dani.. “Ba haka bane Nenne yi hakuri… “Nayi mutuniyata, muje gida na baki mazarkwaila, cikin jin dadi tace”Toh Nenne.. Laaa Nenne kinga Ya Mahmuda a teburin baushe.. “Kallon ta takai wajan suna zaune kan benci sun jere kamar masu zaman arziki, su kusan biyarne a wajan Mahmuda da Tero nata zukar sigari Master na gefen su yana zuba zance sai sauran yan kashe wandon dake hirarrakin su.. “Mahmuda ne yayi ma tabar wata muguwar zuka kana ya mika ma Master ya shiga zuka..”Zungurin Mahmuda Tero yayi yana fadin “Mun shiga uku ga Nenne bala’i… Tari ne ya sarke Mahmuda dan jiya da dare kadan ya rage Baba Shamsu ya bugesa, kuma yayi alkawarin idan har aka ganshi yana shan kayan maye sai ya kaishi can Kura kauyan su ansashi a mari, yasan halin Mahaifinsa sarai zai iya.. “Wani mugun dundu Nenne ta sakar mai a bayan sa tana fadin”Ai me hali baya fasa halin sa, wallahi a kunnen mahaifin ka dan battan uba, Kai kuma Ashiru Jummai ce yar bala”i bani ba, yar takardar dake hannun sa a nannade ta fusge gami da zazzage abunda ke ciki a kasa… “Gaskiya Nenne kin min asarar World har dari biyu fa nasiye ta, harara ta wurga masa tana fadin asarar ubanka, wallahi ko kaffara ba zanyi ba dakyar idan kun dungura goshin ku kasa da sunan sallah… “Kai kuma majanuni ta nuna Baushe dake ta gimtse dariya tace”wata rana sai na taro yan banga mun kone taburin naka, Ke Raliya mu tafi gida.. ” A sauka lapiya Nennen mu cewar Baushe yana dariya…

“Toh kundai ji, Mahmuda bazai fasa halin saba, kuma insha Allahu zanje takanas har kura na samu Malam me saje na sanar masa za,a kawo Mahmudan wajan sa, sai ya sauke zai dawo nan.. “Kuka Inna Larai ta fashe nashi cikin kuka tace”Wallahi babu me kaimin dana wata uwa duniya, ai daman Nenne nasan tuni baki kauna ta da yarana…

“Ke Larai ashe baki da hankali ban sani ba, agabana kike fadama uwata magana… “Cikin tabe baki Nenne tace gashi kuwa kaji da kunnuwan ka, yo Allah na tuba Larai mutuncine da ita, wato zaikai Dan ki uwa duniya toh da yake ma can kike taso, wato an zo birni an waye anci jar biya anyi burushi da buredi da kaza ko.. Toh bari kiji, ni ba gantalalliyar suruka bace, atsaye nake kan digadigaina, idan kuma kika kawo min wargi keda Mahmudan zakuyi Kura sai naga ta tsiya…

“Haba Nennen mu me yayi zafi haka ayidai hakuri cewar Goggo Luba cikin jin dadi, daman dazu Inna Larai ta gama mata tijara..

Duk kushiga hankalin ku, shima Mahmudan inna nan zai dawo ne ya sameni.. atoh yadai fi dan bazan yarda a zubar mana da mutuncin gida ba..

 

“Yau Nenne yan kirkin na kanta dan duk ka jikokin nata na dakin ta ana kallon fin din dan ibro suna ta dariya dan Batula ce taje gidan uwar dakin ta Maman Usman ta aro musu dan Nenne akwai son kallo, shiyasa Baban Batula kafin yarasu ya

siya mata harda dvd..

“Sallamar Mahmuda ce ta katse musu kallon su suka amsa masa gami da gaida shi, duk rikicin gidan Yara basa sanya kansu aciki sai dai abunda ba,a rasa ba suna kaunar junan su sosai, “Sannu Nennen mu ana ta kallo ne..? Mahmuda ya fada cikin dadin baki..”Uhm ai idon ka ya gane maka ko, toh nidai ba fada nazo ba ga wannan zan wuce na siyo miki.. ya fada yana mika mata ledar hannun sa, amsa tayi tana yatsuna fuska tace”Menene aciki kuma… “Haba Nenne ki bude bana ko zan baki guba ne..

“Toh na sani ko kun kullo hakan da Uwarka tunda nace za,a kaika makarantar me saje.. kamshin daya bugi hancin tane yasa tayi kum tana hadiyar yawu, soyayyan kifine karfasa sai kwadon zokale me yawa…

Kai amma kuwa na gode yau kace na taki sa,a dan dai nasan iya tarihi ban taba cin abun

hannun kaba sai yau meke tafe dakai dan nema…

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
ABUJA…

 

“Haba Hajia Salma, taya kike zaton zaki samu hankali na bayan damar da nake ganin ta kusa zuwa tafin hannuna na kokarin kufce min, toh wallahi bazata sabuba, nasan duk waccen haddasanar tsohuwar ce ke kitsa komai, amma babu damuwa zan kawar da ita kowa ya huta… “Yanzu naji batu Hajia Falmata, na dade inna fada miki idan har Hajja na raye toh kuwa burikan ki akan gidan Alhaji Tahir bazai taba cika ba, gara tun wuri ki tashi ki nuna musu bakin rijiya ba wajan wasan yaro bane..

“Hmmm hakane Hajia Salma yanzu kuma aka fara wasan, tsakanin ni dake za,aga wake da nasara…

“Ihun diyarta Laila ne ya katse musu maganganun da suke tattaunawa, da sauri suka fito zuwa falon kasa, Layla ce keta tikar rawa cikin matukar murna, rungome Hajia Falmata tayi cikin Myrna tace”Mommy gobe Yaya Tahir zai dawo daga Londan dazu yanzu mukayi waya, cikin farin ciki itama tace”Toh madallah sai ayi masa tanadi na musamman, na sanki da shirme ki kama kanki kinji ko, “Ohk Mum karki samu problem, da sauri tayi upstair cikin farin ciki..

“Numfashi Hajia Falmata ta sauke gami da kallon Hajia Salma suka murmusa tare..

 

 

 

Hmmm har yanzu fa wasan bai fara ba, kudai biyoni..

 

Ruwan comments nake bukata pls

[07/09, 11:07 pm] +234 703 966 0069: 🕸️ *BAKIN RIJIYA*🕸️

 

 

Na Khausar mashi

 

 

*4*

 

 

SANADI..

 

“Nennen mu inna zuwa haka..?cewar Saratu ganin Nennen na kokarin sakayo kofar dakin ta..Toh Uwata nidai shegiyar tambayar nan taki na damuna Saro baki gani baki tanka ba, toh gidan Hajia Laure zani tun jiya take min aiken nazo tana son ganina Allah yayi dawowar ta daga umra, banso zuwa ba sai an kwana biyu kar ace naje kwadayi.. “Dariya Saratu tayi tana fadin” Haba Nennen mu wa zai fadi haka, ai duk unguwar nan ansan kawancen ku keda Inna Laure, dan Allah zan biki Nenne nadan mike kafa..

“Toh uwar yawo, sai ki kira Batula muje tare kar Uwarta ta kullace ni na ware diyar gwal dinta, da sauri Saratu ta leka dakin su Batula ta kirata, jin gidan Inna Laure zasu yasa ta dauko ninkakken hijjabin ta dayaji guga ta sanya ta fito gami da yima Umman su salama..

“Gidan Hajia Laura akwai dan tazara da gidan sosai, dan haka a kafa suka tattaka Nenne na basu labarai na unguwar kafin tayi cikar haka, “Gidan Laure dan ma daidai cine me kyau zaman mutum daya, babban danta ne ya gina mata da yake yana da kudi haka mijin diyarta dan siyasa ne sosai fitacce, shiyasa take hutawa bata nemi komai ta rasa ba, tun zuwan Nenne kano lokacin tana goyon cikin Dan asabe suka hadu da Hajia Laure suna mutumci sosai har ya kawai ga kawance, sai dai har tsufan su Nenne bata fiye shige ma Laure ba dan tace bata son aga kamar kwadayi take zuwa wajan ta, sai dai sukan kaima juna ziyara akai akai wanda na Inna Laure tafi zuwa wajan Nennen.. “Da sallama suka shiga cikin gidan dake lailaye da suminti ko inna tsaftsaf… “Lale maraba da kawalli ashe zaki zo da har inna shirin zuwa tunda kinki zuwa ke.. “Gaida Hajia Laure su Batula sukayi ta amsa tana fadin”Masha Allah jikokin nawa haka suka girma, gaskiya Nenne baki kyautawa yaushe rabon dana gansu, dariya sukayi nan aka kawo musu ruwan sanyi da lemu sai shinkafa da taji nama zuku zuku ga salad a gefe, kallon juna Saratu da Batula sukayi suna hadiyar yawu kana suka murmusa, dan an dade rabon da su kwashi shinkafa haka da nama me yawa.. “Ai yau Nenne albishir ne cike dani taf a bakina me tafe da alkairai masu yawa, dan haka muje daga ciki yanda zamufi samun natsuwa, “Tashi Nenne tayi tabi bayan Hajia Laure zuwa uwar dakin ta..

“Hmmm Albishirin ki Nenne… “Goro fari kal Laure.. “Allah ya hadani da Kulun Hashimu a kasa me tsarki.. “kuru Nenne tayi ma Hajia Laure da ido tana kallon ta, wallahi ingaya miki ban gane taba dan ta canza gabadaya.. ita ta gane ni nan muka koma gefe muka shiga gaisawa cikin murnan ganin juna, tambayar farko da tamin inna kike, nan na fada mata unguwar mu daya ai, munsha hira na tuna baya har sai da wani jikanta dan kyakkyawa yazo muka rabu, washegari muka kara haduwa dan taban adireshin ta, kusan watan ta biyar kasa me tsarki tana ganin likitan kafa ne, tsaraba akwati guda kin ganta can duk takice da jikokinta inji ta, sannan ta anshi numbar na na Nigeria watan gobe zata dawo kuma insha Allahu zata biyo tanan dan ta ganki.. “Hawaye Nenne ta share tana fadin”ikon Allah ashe zamu kara haduwa da Hajja Kulu, annabi yayi gaskiya, shekaru kusan Talatin mun rabbu yanzu gashi za,a sake haduwa, Ya Allah ka nuna min wannan rana ameen..

“Katon akwatin ta sake kallo wai duk kayan tane lallai Hajja Kulu na cikin wadata, nan fa Hajia Laure ta sanya almajirin ta ya taro Napep aka sanya kayan a ciki kana suka shiga Nenne na karayi ma Laure godiya, “Su Batula kuwa mamaki ne ya cika su da wannan kaya amma sun kasa magana ganin yanda Nenne ke daga hanci tayi banza dasu kamar ba cikin fara,a suka zoba, koda suka iso sai kaffa kaffa take da akwatin tana ma me Napep din jarabar karya bari akwatinta ta ko kurzune ba daga kasar nan aka kera taba, cikin jin haushi me Napep din ya dungurar da katuwar akwatin a gaban Nenne dakyar, ya ja Napep dinsa..

“Toh ku kuma da kuka zura mun ido ku kama mushiga dashi.. “Zaro ido Batula tayi tace”Haba Nenne kamar wasu garada zamu kinkimi wannan akwatin, ai tayi mana nauyi sai dai maza.. “Toh haka kika ce kenan, wallahi ko ku kama ko kirasa tsarabar cikin akwatin, cikin tura baki suka shiga jan akwatin dan da nauyi, Zuwan Mahmuda da Salmanu ne ya cecesu… “Ahh Nennen mu gani ma aka kawo mana ne.. “Ta gidan uwarka ba, wallahi Mahmuda ka fita idona bar ganin ka kawo min wani gantalallen kifin Ka da zogale kace zaka min rashin ta ido, ku kama ku shiga dashi saboda yan sa ido…

 

“Allah me iko, Yanzu Nenne duk wanan kayan Baba Kulu ce ta aiko miki dasu… Gasu kana gani kuwa Shamsu, kudai ku bude a bawa kowa nasa a gajiye nake, duk matan gidan da yara na zaune kowa cike da murna, kai kace Nennen ce ta dawo daga kasa me tsarki, kaya ne masu tsada dakyau kuna kowa ya samu awadace tun daga yaran har iyayensu maza da mata Nenne ta bama kowa, kana suka watse suna godiya ma Nennen….

 

“Haba Ya Tahir ta Ya xaka min haka, bayan kace yau zaka dawo amma kace kuma yanzu aka biya Saudia ku taho tare da Hajja.. “A bunda na yanke kenan Nonsense… “Zaro ido tayi tana kallon fuskar wayar nata idanun ta sun rine sunyi jajir, itace Nonsense.. kallon Zeenat tayi aminiyarta tace”Babe kina jin abunda gayen nan yake fada min ba, yau ni Tahir ya kira da Nonsense….

“Hmm duk laifin kine Layla, kin kama kin makale masa kamar shine autan maza, kina da kira mekyau da duk wani da namiji me lafiya da ya kalleki dole ya so ki, amma kin makale ma Tahir wanda bai ganin mutu… “Dakata haka Zeenat karki kara min zafi pls, ke kanki kinsan Tahir ba irin ko wani namiji bane, acikin mazan ma dole a kirasa da jarumisu, yana da wasu irin qualities da ba ko wani namiji ne ke dasu ba sai dai dai ire iren sa, uwa uba kyau da masu gidan rana.. kin ga kuwa dole na jure wulakancin sa dan nasan yana daf da xuwa tafin hannu na, wallahi sai na juyasa kamar waina a tanda sai na bautar dashi alwashi ne wannan… “Tafawa sukayi suna sheke dariya cikin nishadi, ko shedan dole ya jinjina miki Layla, toh idan dai an shiga gidan TT kar a manta damu dai… “Hmmm wane ni ai kece ta hannun damar…

 

BAYAN KWANA BIYAR…

[07/09, 11:07 pm] +234 703 966 0069: 🕸️️ *BAKIN RIJIYA*🕸️

( _Ba wajan wasan yaro_ _bane_)

 

 

*5*

 

 

 

“Rayuwa gudu take kamar tsere, yau farin ciki gobe akasin haka, hakan ce ta kasance dasu Batula yau suna cikin matsanan cin farin ciki, dan yau ce ranar da zasu fara halartar Makaranta bayan sun zana jarabawar fita daga js yau gashi zasu shiga matakin Ss one class.. “Cikin shigar kayan makarantar su sabo dal wanda Baba Shamsu ya dinka musu Baba Dan asabe kuma ya siya musu takalmi da sauran kana nan abubuwan bukata, Saratu da Batula bakinsu yaki rufuwa sai Lawisa da suka fito tare wacce take zuwa makaranta itama a kasan layin su, sallama suka ma Matan gidan Nenne harda basu nera hamsin su raba sai washe baki takeyi, burin ta itama taga jikokinta sun samu ilimi ta kowani bagare dan yana da matukar amfani a rayuwar diya mace.. “SHEKARA GOVERNMENT GIRLS SECONDARY SCHOOL

Dandazon dalibai mata ne wanda sun tasan ma dari uku ke fitowa daga cikin makekiyar makarantar, kowa ka ganshi da abokin tafiyarsa suna hira wasu kuma su kadai..

Tafe suke a hankali rungome da littattafan su, hira suke game da abubuwan da suke faru a cikin aji, Samira sabuwar daliba ce itama haduwar farko suka kulle ita dasu Batul, ta Kalle su tace”Toh yan uwa nifa anan zan tsaya, inna ganin hanyar mu ta banbanta.. “Ohk toh Samira Allah ya huta gajiya ya kuma kara mana fahimta akan karatun mu, “Ameen.. sai mun hadu a schl gobe ta fada tana daga musu hannu suma suka daga mata, “Kinga muma muyi sauri mu wuce gida naga karfe uku na daf dayi, hakane cewar Saratu suka tari napep zuwa gida…

 

Yan zu doctor kana nufin har yanzu hawan jinin ta bai sauka ba?”Kwarai kuwa Sir, ni kaina na kasa shawo kan matsalar, sai dai inna so ka lallabata ta fada maka damuwar ta, kasan tsoffin nan namu saida lallashi.. “Ohk insha Allah Doctor faisal, Thanks again… Haba haba ka daina fadin haka ai an zama daya..

A hankali suke tafiya yana rike da hannun ta kamar za,a kwace masa ita, sannu Hajja na tafi ahankali kinji.. “Toh me sunan Baba kafar ce sai a hankali, kallon matar dake gefen su yayi yace”Umma Sahura pls a bude ma Hajja mota, “Toh me sunan Baba ta fadi gami dayin gaba da sauri wajan dankareriyar motar su, site din baya Hajja da Tahir suka shiga, Sahura na gaba ita da driver, cikin mintuna hamsin suka iso gidan su dake birnin Riyad dake kasar saudia, sannu masu aikin gidan keta ma Hajja tana amsawa Tahir na rike da hannun ta, “Barni na zauna nan falo Dan Albarka Allah ya baka mata ta gari da zata rike min kai Amana… “Murmushi yayi gami da amsawa da Ameen Hajja na, ni bayi na koma dan akwai tayin aiyuka a gabada, gashi yanar Layaba zamu koma Nigeyia, “Toh masha Allah Baba na naji dadi wallahi, ni wai kasar nan basa bada maganine ka iya fadar wannan R din me sunan Baba, Sahura da tafito dauke da ruwan tea me ciki da kayan yaji dan kawo ma Hajja ta murmusa tace”Hajja ai babu maganin irin wannan kam, kin manta da Baba Sambo shima haka yake, toh me sunan Baba gado yayi..

Dariya sukayi kana yayi masu sallama ya fice daga tankamemen palon me cike da kayan more rayuwa, “Numfashi Hajja ta sauke kana ta dubi Sahura tace”Inna matukar tausayin halin da me sunan Baba yake ciki Sahura, ya taso maraya ko dumin mahaifiyarsa be jiba ta koma ga Allah, mahaifinsa kuwa har yau inna ji ajikina mai mutu ba yana raye, wani bakin kulli ne ke bibiyar rayuwarsa Sahura, haka nan hankalina ya kasa kwanciya da hadin auran tsakanin sa da Layla duk kuwa da jikata ce ita..

Hakane Hajja me sunan Baba abun tausayi ne, addu,a zamu cigaba da tayashi Allah ya daura shi akan makiyansa, Ameen Sahura Nagode kwarai..

 

Tafiya takeyi cikin kayataccen lambu me cike da shuke shuke masu kamshi da sanya natsuwar xuciya, hango wani kyakkyawan korama da tayi yasa ta nufar wajan fuskarta dauke da murmushi, cikin dan mamaki take dubar wata mata tsugune gefan koramar ta sanya hannun ta cikin ruwan koramar tana wasa dashi, nufar matar tayi itama jin motsi ya sata dago kyakkyawar fuskarta tana duban ta, hawaye na zuba daga idanun matar, “Sunana Umaima dan Allah inna son ki taimake ni baiwar Allah, Kallon Matar Batula keyi cikin mamaki dan batayi tsammanin ta iya hausa ba.. “Na san Allah ne ya amshi addu,a ta Ya turomin ke nan, kuma naji ajikina zaki taimake ni..”Toh Mama Allah ya bani ikon taimakon ki, hawaye ta share tace” Shekaru ashirin da shida kenan da rasuwata… zabura Batula tayi cikin tsoro tace”Kina nufin kin mutu Mama, amma me yasa ni nake ganin ki a raye, murmushi tayi tace”A hankali zaki fahimci komai diyata, duk da kina da qarancin shekaru amma ke wani haskece ga ahalina Ke alkairi ce diyata bani da Ishasshen lokaci diyata amma ki kalli can, tayi mata nuni da wani waje can gefe guda, photon wani kyakkyawan matashi ta gani me cike da haiba, haka kuma kamar shi sak da matar dake gabanta, wannan da kike gani shine dana Tahir, yana cikin matsanan cin damuwar maraice na uwa da uba, sun rabashi da mahaifinsa tun kafin yazo duniya, haka sun halaka mahaifiyarsa bayan ta haifeshi ko dumin ta baiji ba, wanna yanzu suna bibiyar rayuwar sa dan halakashi, zagaye yake da makiya diyata wajan Kakar shi kawai yake jin sanyi, dan Allah na roke ki kishiga rayuwarsa, ki zamto inuwa a garesa ki taimake shi….. “Firgigit Batula ta farka daga nannauyan baccin da takeyi, sharkaf take da zufa cikin sauri ta sauko daga saman gadon ta ta nufi na Umman su dake kwace ita da kannen ta, makurewa tayi a bayan Umman jikin ta na rawa, har yanzu photon saurayin da na matar ya kasa barin kwanyarta, haka maganganun dasuka tattauna, har aka kira sallar asubahi idan ta kyar ta kasa komawa bacci, duk jikin ta a sanyaye yake har sai da Umma tayi mata magana”Wai ni Batula yau lafiyar ki kuwa, lokaci na neman ya kure kuyi latti tun dazu kin kasa tabuka komai.. “Numfashi ta sauke tana fadin”Wallahi yau Umman mu banajin dadin jikina ne. Toh Allah ya sauwake kije ki juya ruwa ki shiga wanka dan har Saratu ta sanya uniform, toh Umman mu tace da hanzari tana daukar kwandon wanka…

“Wai yau Batula kalau kike kuwa naga duk kinyi suku suku ne kamar mara lafiya, kin rigani fada Saratu, ni kaina tun dazu na lura batajin dadi. Lumshe idanunta tayi tace”Haka kawai yau na tashi sai ahankali, amma zuwa anjima nasan zan wartsake, toh Allah yasa, nan suka ci gaba da bitar karatun su…

 

 

Cikin shiga ta alfarma Layla ta fito tana tafiya dakyar kamar me tausayin kasa, Hajia Falmata ta dubi diyarta cikin farin ciki tace” Inna so ki natsu sosai Layla kinsan Tahir baya son rawan kai dai, Hmm kai Mummy wani rawan kai zanyi, nidai ki cika min alkawarina na mallakar Tahir, Hmm ki saka a ranki kamar kinsamu Tahir Layla, kedai ki zuba ido, “Mommy wai Abba har yanzu bai dawo ba, na kira wayar shi bata shiga, Yau fitan sassafe yayi an kirashi daga wajan aikin sa.., amma shima yana tafe zamu same shi acan airport din, Ohk.. ta fada suka fice daga parlon, tacan get din baya driver

ya fice dasu…

 

 

Hmm muje zuwa, har yanzu comments dinku bai kamsar da niba, wai inna masoya Bakin tulu ne da sauran novel dina, ko kun zama boyayyen readers ne…

 

 

Taku Khausar mashi

[07/09, 11:07 pm] +234 703 966 0069: 🕸️ *BAKIN RIJIYA* 🕸️

 

 

Na Khausar Muhammad

 

 

*6*

 

 

Karfe shadaya na safe jirgin da ke dauke da su Hajja da sauran fasinjoji ya sauka cikin nasara, a hankali fasinjoji suka shiga fitowa, kowa fuskarsa dauke da farin cikin an sauka lafiya, sabanin Tahir dake rike da hannun Hajja fuskar shi tamau ba fara’a suna takawa a hankali, sai Sahura dake tafe a bayan su, fuskar Hajja dauke da yalwataccen farin cikin ganin a halin nata cikin koshin lafiya bayan shafe kusan watanni a kasa me tsarki, sannu ta shiga amsa gaisuwar su kana suka nufi motocin da suka zo daukar Tahir din da Hajja, duk sauran motarsu suka shiga gami da rufa musu baya zuwa DAUDAWA FAMILY HOUSE dake rijiyar zaki, Tahir na zaune gefan Hajja sai dakilar wayarsa yakeyi kanshi a kasa, amininsa kuma dan uwansa Usman yake nema a waya, sunyi dashi zai taso daga Kaduna yazo nan kano tarbar su amma bai ganshi ba haka wayarsa taki shiga… Wai me sunan Malam tunanin me kakeyi ne?..Hajja ta fada tana zungurin sa, lumshe idanun sa yayi yace”Sorry Hajja, wallahi Usman nake nema a waya munyi dashi yau zai taso daga kd yazo nan saboda akwai wasu ayyuka dake gaban mu, amma bangan shiba kuma wayarsa bata shiga… “Toh ka bari anjima ka kara neman sa, nima inna so in mun isa gida ka kiramin BIBA akwai sakon da zata tahomin dashi gobe, “Ohk Hajja na, murmushi tayi tace”Dan Allah ka rage daure fuskar nan, haka Layla na maka magana kayi banza da ita, ka rinka sassauta mata dan masoyi yafi makiyi Babana..”Lumshe idanun sa yayi gami da sauke numfashi…

 

ASALIN SU HAJJA

 

Hauwa,u kulu wacce yanzu jikokinta ke kiran ta da Hajja ita da mijinta Malam Hashimu haifaffun kauyan Daudawa ne dake jahar garin Katsina, mahaifin Hashimu Auwalu Allah yayi masa arzikin dabbobi da gona ki dan yana noma sosai, matar sa daya Habiba da yaron su daya Hashimu, suna son haihuwa amma tun daga hashimu basu sake ba, yan uwa sunyi ta kawo korafin Malam Auwalu ya kara aure duk da Habiba yar uwarsa ce amma yayi biris dasu, a haka suka raini Hashimu cikin so da kauna, lokacin da Hashimu ya zama saurayi sosai Allah ya dauke mahaifinsa malam Auwalu, sunyi kuka sosai, nan aka tattara dukiya aka bawa kanin mahaifinsa ya cigaba da juya masa cikin kasuwan cinsa, da yake yana da amana ya kuma dauki Hashimu ya sanya shi cikin yaransa ya rike, Hashimu yaro me kwazo ya cigaba da karatunsa anan garin su cikin kwanciyar hankali da kulawa, Innar sa kuwa ta sake aure sai dai watan auren bakwai ta rasu sanadiyan barin da tayi gashi babu jini ajikinta, Hashimu ya kara zama maraya sosai saidai yana samun kulawa cikin gidan kanin Baban shi, rayuwa na gudu Baba Manniru kasuwanci ya shigo da shi garin kano da Iyalansa gida ya siya babba suke zaune ciki suna zuwa makaranta har Hashimu ya kammala karatunsa, soyayyace ta shiga tsakanin sa da Hauwa,u kulu Yarinyar kanin Baban shi nan cikin kankani lokaci aka daura musu aure suke zaune cikin kano suma, dukiyarsa Baba Manniru ya damka amsa akan ya Cigaba da juyawa, cikin haka ya samu aikin gwamnati har Allah Ya hadashi da malam Habibu kura mijin Nenne sukayi zumunci me karfi har ta kaisu sun zama kamar yan uwan juna, karin girma na aiki ne yakai Hashimu garin Adamawa lokacin Hajja Yayan ta Uku Tahiru Usmanu Balkisu acan ta haifi Hindatu, shekarar su uku a adamawa Alhaji Hashimu ya tattago aure na wata buzuwa Sailuba, kamar asiri haka ya burkice shidai aure yakeso kuma Sailuba Kanwar abokinsa da yayi anan Adamawar Gaddafi,babu yanda Kulu ta iya akayi auren suna zaune lafiya sai dai Sailuba makirace ta bugawa ajarida, tasha hadama Kulu makirci ta tsallake kota fada, gashi Gaddafi duk ya kanannade Alhaji Hashimu dashi yake duk shawarwarin sa, Shekarar Sailuba uku a gidan am ma haihuwa shiru, nan fa ta tada hankalinta sukayi ta yawan kasashe amma ana fadin lafiyarta kalau, da tagaji ne ta dauko yar kanwar Gaddafi me suna Falmata ta rike ahannun ta, Falmata yarinya ce futsararriya gata bata da kunya ko kadan, rashin kirki har Kulu takeyi mawa a duk gidan Tahir kawai take tsoro matuka, haka ta na bala’in son shi, sai dai shi babu wacce ya tsana irin Falmata, duka yake mata sosai Sailuba tayi ta zage zage, haka rayuwa ta cigaba da tafiya, Sailuba na matukar son hada aure tsakanin Falmata da Tahir, dan taga yaron nada irin arziki, kuma taje an duba mata ance shi ne zai gaji arzikin mahaifinsa, shiyasa ta kwalla fa rai ita da Falmata..

“Wata rana Alhaji Hashimu ya dawo gidan a fusace yana kwala ma Sailuba kira tun daga bakin get,babu kowa a gidan sai Kulu da masu aiki, itama Sailuba fitowa tayi cikin mamaki wannan kiran haka.. “Yau karyar ku ta kare ke da Gaddafi, asirin ku ya tonu, anyi walkiya nagan ku, ashe daman Gaddafi ba

Yayanki bane kwarton kine, shine kuka rufeni abaibai dan kuci dukiyata, toh Allah Ya haskamin komai, saboda haka ki tattara inaki inaki ki barmin gida na sakeki saki uku… “Ihu ta kurma tana fadin”Kayi karya Hashimu, nizaka wulakanta a gaban mutane, kuma wallahi ban saku ba babu inda zani, a zuciye yayi kanta ya hau jibgarta, abunda Kulu bata taba gani yayi ba kenan, dakyar ta janye shi yana sauke numfashi, Allah ya isa tsakanina dake Sailuba wallahi kafin na kara fitowa ki barmin gida, cikin jan kafa tana hawaye tace” Zaka san ka wulakanta ni Hashimu wallahi bakaci banza ba, adaren yasa aka tattara kayanta aka fitar dasu, Falmata kuwa suna boarding school din daya sasu ita da Hindatu… “Kiran Gaddafi tayi nan suka hadu gami da tsaida kudirinsu na hallaka Alhaji Hashimu, kwana biyar da rigimarsu yayi mummunar hatsari da katuwar mota tabi takan shi ya tsaya siyan kayan marmari ma Kulu, kusan kwanan Kulu hudu batason inda kanta yake ba, daga baya suka dangana sai dai mutuwarsa da sati daya aka kashe Sailuba har cikin gidan ta aka kashe ta, tashin hankalin Kulu bazai fadu ba, Alhaji Gaddafi kuwa kullum yana gidan duk ya rame ya lalace, duk wani dukiyar Alhaji Hashimu dake hannun sa ya kawo ma Kulu da takardun kadarorin sa, ranar da Alhaji Hashimu ya cika kwana arba’in da rasuwa Alhaji Gaddafi ya samu Kulu yace”Kamfanonin da Hashimu ya hada hannu dasu ne sukeson ganin takardun daya bata ajiya da kuma laptop din sa, cikin mamaki Kulu tace”Aini Alhaji bai taba bani ajiyar wasu takardun saba, komai cikin latop dinsa yake ajiyewa ko kuma yaba ka, sannan sama da kasa na nemi laptop din na rasa, sai dai ana gobe naga ya fita da ita… “Toh shikenan karki damu zan musu bayani, nan ya fice ranshi abace, Alhaji Babalo da Timo ne zaune a wani kayataccen falo sai Gaddafi dake kai kawo atsakiyar palon kanshi ya dauki zafi yace”Wallahi akan wannan video din babu wanda bazan iya kashewa ba, na rasa inda dan iskan mutumin nan ya boye laptop dinnan, “Tsaki Alhaji Babalo yayi wanda awancan lokacin mataimakin shigaban kasa ne, Oga Timo kuwa minister kudi ne, duk kai kaja komai Gaddafi, kayi saurin kashe Alhaji Hashimu bayan kasan mun kashe majijine bamu sare kansa ba, tunda duk wani sirrin mu na cikin wannan laptop din, na baka nan da kwana uku Ka binciko inda Alhaji Hashimu yakai laptop dinsa ajiya, dan driver dinsa yace tabbas ana gobe zai rasu da ita ya fita, sai dai kuma bai dawo da ita gida ba, kaga baki biyu kenan tunda matarsa ma haka tace maka, bana son a batamin siyasata idan kuma ba hakaba kaima zata shafeka… Ya mike gami da ficewa daga parlon Oga Timo yabi bayan sa, tun daga wannan lokacin Gaddafi ke ta bincike har suka gano inda Alhaji Hashimu ya boye laptop dinsa a gidan gonar sa, nan suka bata komai suka cigaba da siyasa cikin kwanciyar hankali, shima Gaddafi ya amshi diyarsa Falmata wacce daga baya Kulu tagane diyarsa ce, sai dai fuska biyu kareshi baka taba yi masa zargin mugu ne, Falmata ta taso da burin auren Tahir sai dai bai dade da dawowa daga kasar America karatu ba yayi aure da budurwarsa Umaima kyakkyawar bafulata na suna matukar son junan su, Falmata tayi kukan bakin ciki gami da daukar mummunar kudiri akan Umaima, haka nan Alhaji Gaddafi yace ma Kulu a hada Usman da Falmata dan yanason hada jini da Abokinsa, babu yanda Kulu tayi tunda Usman ya amince akayi aurensu suma, wata tara Umaima ta haihu da namiji sai dai ko ganin fuskarsa batayi ba ta rasu, Alhaji Tahir yayi kuka rashin mata tagari, bai yarda da mutuwar matar sa ba dan ya kafa hujjojinsa a kan likitocin, cikin binciken shine ya gano ainahin kalar Alhaji Gaddafi da wasu yan siyasar, haka sakon da mahaifinsa ya taba turo masa tun yana america nan yahau binciken numbar kalmomin bude kundin sirrin, sunan garinsu yasa daga karshe nan yaga duk wani makircin su, abokin sa ya kira Adam ya fada masa komai kuma ya kudurta makashi ga jami,an tsaro masu gaskiya, sai dai bai ko ba karasa gida ba yayi hatsari motarsa ta fada cikin teku sannan an nema gawarsa an rasa…

“Hajja da yan uwansa sunyi kuka kwarai da gaske, lokacin Biba tana da tsohon ciki taso amsar Tahir jariri Hajja ta hana ta, haka taso shayar dashi da ta haihu nan ma Hajjan ta hana ta dan ba,asan abunda zai faru gaba ba..

Sai dai Hajja har yau tanaji ajikinta danta Alhaji Tahir yana raye bai mutu ba..

 

Wannan kenan

[07/09, 11:07 pm] +234 703 966 0069: 🕸️ *BAKIN RIJIYA*🕸️

 

 

Na khausar Muhammad

 

 

*7*

 

 

 

( YAN ZAMAN KASHE WANDO)

 

Kamar kullum, zaune suke saman benchi daidai shagon Baushe gefan layi, duk wani saurayi marajin magana a unguwar toh zaka same shi zaune a wajan, wasu na busa sigari wasu kuma na gefe suna buga karta, duk sun cika wajan da hayaniyar su.. jiniyar motar yan sanda da ta cika babban titi ne yasa dukka samarin wajan mikewa suna shirin artawa da nakare, dan tunanin su cinne aka kawo musu na kame, sai dai ganin wasu jerarrun bakaken motoci wuluk har uku suna gudu a jere ga motar yan sanda tafe bayan su da gaba yasa su sauke ajiyar zuciya, dariya Baushe yayi yace”Ai sai ku zauna matsoratan banza, da alama manyan kasan ne suka tuna da unguwar tamu..

“Tsaki Tero yayi yace”Kaji ka Baushe, ai tsoro halak ne ko, kuma idan aka kwashe mu uban waye zai yi belin mu, kai kanka ba ganin Ka zamuyi ba, barshi kawai Tero, ai gara kowa dani.. dariya suka sanya ma Mahmud dan sunsan me yake nufi, duk ku dakata dan Allah, nifa naji labarin wai za,a bude wani babban supermarket da ya kunshi ko wani irin kaya, toh innaji yaune taron shiyasa manyan motoci keta shige da fice… “Hakane kam Ashiru naji a labarai jiya da dare cewar Baushe, wannan matashin attajirin Tahir Dadawa shine ma mallakin gurin, kuma ana gayyatar dukkanin Al,ummar musulmi taron bude wajan..

“Kai yasa kace taron na mune kenan, kuma kasan Daudawa na burgeni wallahi, akwai taimakon mutane, ni kaina na taba amsar tallafinsa cewar Tero nan suka cigaba da hirar kyawawan aiyukan da tallafin al,umma da yakeyi…

 

“Umman mu na shirya zan tafi, “Batula ta fadi tana kara gyara gyalan kanta me ruwan kwai, duk ranar Alhamis takan kaima yan uwan Umman su ziyara ita da kannen ta, toh jiya kuma Nenne ta kwashe yaran gidan sun tafi biki can kura, itama saboda ganin Umman su babu lafia shiyasa bata bisu ba, amma har Saratu da Inna Larai suna can, yau da dare zasu dawo.. “Toh Batu ki gaishe min da Kawu Mudan, dan Allah karkiyi dare ana salar la,asar ki dawo. “Toh Umma idan Ya Mahmuda ya shigo ki fada masa na gama masa gugan kayan suna cikin kwabar sa, “Toh shikenan Allah ya tsare ki dauki dari biyu saman madubi, cikin natsuwa take tafiya kai kace tausayin kasa takeji, Batula duk da take yarinya yar shekara sha shiddah amma tana da wayo sosai, haka akwai tsiwa dan irin yaran nan ne da kallo daya zakayi musu kasan baza,a tabasu su kyale ba, tayi kyau cikin shigar atamfa mai ruwan kwai riga da siket, sai takalmi sau ciki da ta sanya shima kalar kayan ta anyi masa ado da stones masu sheki sai karamin mayafi data yafa a saman kanta, sau kusan biyu samari na tare ta tana watsa musu harara na karshan har da murguda mai karamin bakin ta, “Kai maza dai kamar mayu suke akan mata wallahi taja tsaki.. “Ke kuma dawa hajiya tsiga taji an fada daga bayan ta, da sauri ta juya suka saki dariya ita da wacce tayi maganar, “Bari kawai Farida, tunda na fito fa samari ke tare ni shine duk abun yake bani haushi, dariya Farida tayi” Tace toh menene laifin su, sunga yar baby ba dole su taya ba, wallahi Batula ki rage masifa, murguda baki tayi tace”Idan anki fa, ni kinga tafiyata idan kun hadu da Esha kice ta kawo min sako na, dariya Farida tayi tace”Zan fada mata mutuniyas, Farida abokiyar fadar Batula ce tun suna primary, daga baya kuma suka koma kawaye, mai napep ta tara gami da fada masa inda zata yace ta shiga, mutumin dake gefan ta ta kalla kana ta gaishe shi ta zauna dan a haife zaiyi jika da ita ma, yana rungome da bakar jaka ajikinsa.. “Baba sai dai na sauke ka anan dan gaskiya babu wajan parking, kamar ma taron wani abu ake awajan, mai napep din ya fada yana kokarin yin fakin, “Toh babu damuwa ai nan din ma yayi, ga kudin ka, sai dai ka cire harda na jikar nan tawa ya fadi yana nuna Batula bayan ya mika dubu daya, ” Murmushi Batula tayi tace”Nagode Baba, amma da ka barshi ma, murmushi kawai yayi yana fadin “Toh a sauka lafiya, binshi da kallo Batula tayi har ya doshi kofar get din wajan dake cike da yan sanda harda sojoji, karar waya da taji ne daga gefan ta yasa tahau dube dube dan tasan dai ba karar wayar ta bane, waya ta daga gefan kujeran hakan yasa ta tsaida me napep tana fadin” Tsaya malam ko wayar wancan mutumin ce ya barta bai sani ba, tsaki me napep din yayi gami dayin fakin, gaskiya babu inda zan koma dan yanzu haka jirana akeyi na dauko yara daga makaranta, idan kuma ke zaki kai masa bazan jiraki ba gaskiya, “Ohk bari kawai na kai masa tunda ba nisa mukayi ba, sauka daga napep din tayi ta nufi kofar get din wajan, sai da akayi sachin dinta kana ta shiga, an kayata wajan sosai mutanen dake wajan bazasu kirguba, cikin sa,a ta hango mutumin yana daga can baya zaune ya dukar da kanshi kasa, nufarshi tayi cikin sauri dan karya bace mata.. “Baba ga wayar ka ka manta dashi a napep, cikin sauri ya dago kanshi da mamaki yana kallon ta kana yayi murmushi ya amshi wayar yana fadin nagode diyata, dan Allah zauna anan akwai wanda bana son ya ganni ne, cike da mamaki da dan tsoro ta zauna tana dan waige waige, mikewa yayi gami da damkar hannun Batula suka shige cikin mutane bayan kowa dake wajan ya mike tsaya, can wajan wani tankin ruwa ya tsaya kana ya dubi Batula da jikinta ke rawa,” Karkiji tsorona diyata ba cutar dake zanyi ba, sai dai inna rokon ki kimin taimako guda daya, kallon sa sake da baki Batula keyi cikin mamakin maganar sa, wani taimako kuma zatayi masa mutumin da bata sani ba, ba kuma ta taba ganin saba, sai dai haka kawai takejin zata taimake shin saboda yayi mata kwarjini, innajin ka Baba, amma dan Allah innason na bar wajan nan kar a gida aji shiru ban dawo ba, wata farar takarda ya zaro daga aljihunsa yace kinga wancan saurayin dake tsaye cikin fararan kaya, daga kanta tayi sosai tana duban saurayin dake nesa dasu yasha fararan kaya harda malum malum, sai dai fuskarsa a daure take tamau, sai ma take ganin kamar tasan wannan fuskar.. “Eh na ganshi Baba, yauwa diyata shi zaki baiwa takardar nan, sannan wannan kuma ya fito da wata karamar bakar jaka kamar walet yace”Ki ajiye min a wajan ki, idan kin bashi ki fice daga wajan nima zan fito daga baya na amsa yar jakar nan, idan kuma ban samu amsa ba ki rikemin amana, karki bawa kowa sai wancan saurayin. “Shiru Batula tayi cikin tantamar Mutumin, ki yarda dani bazan cutar dake ba, taimakona zakiyi saboda Allah, “Ohk shikenan bari na kai masa amma nace inji wa, “Kice masa Barde…juyawa Batula tayi ta kutsa cikin mutanen maza da mata, sai dai saurayin yayi mata nisa haka zagaye yake da masu matsaron lafiyarsa, tana gaf da ta isa wajan shi wani dan sanda ya hanka data baya yana zare mata idanu” Ke inna kike nufin zuwa ne.. “Ba karamin zafin hankade tan da yayi Batula taji ba dan har gurde kafa tayi, cikin jin haushi muryar ta cike da tsiwa tace”Aikoni wajan wancan akayi.. “Tahir dake tsayi suna gaisawa da ministan Ilimi yadan kalleta ta gefan ido ya kauda kanshi..

” Karya kikeyi, maza matsamin daga nan kafin na harbe ki..

Wallahi da gaske nake yace nace inji Barde… Kusan hantar cikin wasu dake tsaye a wajan ta kada, duk da basuga wanda ya furta sunan Barde ba amma sunji sautin sunan har cikin kunnen su, kallon kallo aka shigayi, Tahir ya juyo yana duban Batula dakyau, daga ma Usman dake gefan sa kai yayi nan ya nufi Batula, sai dai kafin ya karaso ya nemita ya rasa, ita kuwa haushi ne ya cikata tabar wajan afusace, sai dai ko alamar mutumin nan bata gani ba, napep ta tara ta shiga, fasa zuwa anguwar tayi dan lokaci yaja sosai, yar jakar take juyawa a hannun ta da takardar har ta isa gida mamaki ne fal a ranta..

[07/09, 11:07 pm] +234 703 966 0069: 🕸️ *BAKIN RIJIYA*🕸️

 

 

Na khausar Muhammad

 

 

*8*

 

 

Wai nikam yau meke damun kine Batu, tun dazu kin zuba ma abincin ki idanu kin kasa ci?Numfashi Batula ta sauke gami da kallon Umman su tace”Kaina ke ciwo Umman mu, amma na amsa magani wajan Nenne dazu nasha, toh Allah ya kara sauki, maza gama cin abincin kizo kidan matsamin kafarnan tawa, ni kwana biyu ma mamakin kumburin ta nakeyi.. “Dan Allah Umma kije asibiti, ko ki bari ranar monday sai na raka ki, toh Allah ya kaimu amma ba akwai makaranta ba?”Ai mun koma ta rana,toh Allah ya taimaka, kadan Batula ta tsakuri abincin ta kai sauran madafarsu dake gefan dakin su ta rufe, tunanin wannan dattijon ya kasa barin ta, har yanzu a tsorace take da abubuwan daya bata, shiyasa ta daga tsohuwar akwatin Umman su dake kasan gado ta watsasu ciki ta rufe, dakin Nenne ta nufa dan jiyo hayaniyar yaran gidan acan…

 

“Cikin tashin hankali Alhaji Babalo yake duban Alhaji Gaddafi, me kake son fadamin Gaddafi, wai daman tuni ba kun kashe Barde ba?” Alhaji Gaddafi dake rike da kanshi yace”Nasaka yara na sun kashe shi dan har photon gawarsa Mugu dauka ya turomin, amma abun mamaki ajiya naji an furta sunan Barde, kuma kamar muryar mace karamar yarinya ma kuwa… “Tsaki Timo yayi yace”Kuji shirme daga kaji Sunan Barde sai kasa zargi a zuciyar ka, haba Gaddafi meyasa baka aiki da hankali ne, mutumin da kusan shekarar sa biyar da mutuwa kuma an tabbatar mana da hakan, haka kuma ai akwai masu suna Barde burjik bashi kadai bane ba, ko ya kuka ce Timo ya karasa maganar sa yana duban sauran dake hakimce saman kujeru, manyan kasar ne kuma kusoshin yan siyasa wanda ake ji dasu saboda gaskiyarsu da amana, amma ta wata fuskar suke rusa zaman lafiya da karya tattalin arzikin mu kasar mu..

“Hakane wannan maganar ta Timo nakan hanya, gyaran murya Alhaji Bala yayi yace” Kuma ni aganina idan ma Barde ne yayi kadan ya tona mana asiri, karku manta muke da kasar fa, sannan shima wannan yaron Tahir me zai hana akau dashi kowa ya huta, wani me lekarmin asiri game da harkokinsa yace min akwai wani bincike da yake yi na bayan fage wanda har yanzu ya kasa gano na menene sai dai ya fadamin na kara masa lokaci zai gado komai.. “Gyara zama Alhaji Babalo yayi yace” Duk naji bayanan ku kuma zanyi nazari akai, sai dai kuma game da batun Barde inna so Gaddafi ka tsaurara bincike akai, sannan kayi bincike cameras na ranar da aka gudanar da taron hakan ne zai tabbatar mana da abunda muke zargi, cikin abincewa da shawarar Ogan nasu taron ya watse

Alhaji Gaddafi har ya isa gida hankalin sa ba akwance yake ba, tabbas shi yanaji ajikinsa Barde bai mutu ba, dole ne ya kara tsaurara binciken sa, hon yayi akofar tangameman gidansa da sauri me gadi ya wangale kofar get din gidan yana gaida Alhaji Gaddafi, fuska babu fara,a kamar kullum ya amsa masa kana yayi parking ya shige cikin gidan, duk girman gidan babu mace acikin sa, abunda yake yawan fada tarayya da mace kamar tonuwar asirin kane, bai fiya kallon mace ba dan basa bashi sha,awa yafi ta, ammali da maza dan kullum cikin kawo masa su ake yana lalata dasu(wa iyazubillah) shiyasa dakyar kaga mace ta shigo gidan ko diyarsa Falmata sai dai taje can gidan shi na cikin gari su gaisa, toh itama ba damuwa da shi din tayi ba idan ba mugun kullinsu zasu hada ba..”Wayarsa dake ringing ya dauka ganin sunan Mugu yasa shi daukar wayar, “Kamar kasan inna neman ka Mugu, “Toh Lafiya dai ko.. “Babu lafiya domin wani aiki nakeso kamin, amma maganar baza tayi awaya ba anjima mu hadu a gidan gona ta, “Shikenan sai mun hadun…

“Numfashi ya sauke kana ya saki murmushi, muje suwa Tahir….

 

A karo na uku Hajja ta kara kai duban ta ga katon agogon bangon dake cikin parlon, tara saura na dare ya nuna mata, cikin damuwa ta kara danno numbar Tahir amma har yanzu a kashe ake fada mata, jin diran motar yasa ta sauke ajiyar zuciya dan tasan watakila shine ya dawo, a gajiye ya turo kofar parlon ya shigo yana rike da wayoyinsa duk biyu, P.a dinsa Mansur na biye dashi dauke da brifcase dinsa da files ahannun sa..

“Hajja na baki kwanta ba ashe, ya fadi yana zare takalmin kafarsa.. “Mai sunan Baba kenan, inna naga ta barci mai gidana bai dawo ba,.. Dariya Mansur yayi yana fadin” Maganar ki dutse Hajja yau aikine yayi mana yawa.. Sunnu Mansur ai kuna kokari wallahi, kallon Tahir Mansur yayi yace”Sir ni bari na karasa gida… “Ohk Allah ya tashe mu lafiya, karka manta da aikin dana saka, insha Allah bazan manta ba Sir, Hajjan mu ni bari na qarasa gida, toh Mansur a gaida iyali, itama kawata kwana biyu ba,a kawo min ita ba, dariya Mansur yayi yace” Mufida rigima ko yau sai da ta tubure ita na kawota wajan ki, toh akwai makaranta shiyasa, amma insha Allahu anan zatayi weekend, toh madallah ina nan innajira, sai da safe yayi musu ya fice daga parlon, “A gogo sarkin aiki ga abincin kacan na jiran ka, nasan kuma dakyar idan kaci na rana.. ” Murmushi Tahir yayi yace”Hajjana bani da wannan lokacin, abubuwa sun cakude ke dai ki tayani da addu a, kullum cikin yi maka ita nakeyi mai sunan Baba, kai ma ka kara dagewa da ibada ka maida komai ga Allah, toh kuwa babu wanda zaiyi na sara akanka, kaga ma naso na manta dazu Baban ka Usmanu yace na fada maka yana son ganin ka gobe kafin ka tafi office inyaso da safe sai kaje ka same shi..

“Insha Allahu Hajja, bari na watsa ruwa sai naci abincin, “Yauwa ko kaifa, Allah dai ya nuna min matar ka don nafison wacce zata kulamin dakai sosai, murmushi yayi ya nufi uptsairs zuwa bedroom dinsa, sai da yayi wanka ya kimtsa jikinsa kana ya fito daga bedroom din yana kunna wayoyinsa, dan tunda suka gudanar da meeting ya kashe ya manta bai kunna suba.. “Yauwa Sahura hada masa abincin sa ki kawo masa nan, yau mutumin ka nayi waina da miya ga kuma farfeson kayan ciki.. “Kai amma kuwa Hajja kin kyauta, yaushe rabon da naci waina, dariya tayi tace to aikuwa ga tanan sai kaci ka koshi, suna dan hira yana cin abincin sa cikin nishadi, da Hajja kawai zaka same shi yana sakin fara,a harda murmushi,sai kuma Usman ko Mansur suma kuma sai idan ta kama.. Sai da ya kammala kana ya raka Hajja dakin ta ta kwanta kana ya nufi nasa dakin, bayan ya shiga laptop dinsa ya jawo ya kunna, kira ne ya shigo cikin wayarsa, ganin sunan Usman ya sashi dagawa, “Man akwai matsala fa, mun tsunci gawar Baba Haladu idan da dama gobe ka shigo asibitin aminu kano, yanzu haka inna hospital din ana gudanar da wasu bincike, dafe kanshi Tahir yayi yace”Insha Allah innan zuwa goben nan sukayi sallama ya ajiye wayar, hannu biyu ya sanya ya dafe kanshi dake sara masa, meke faruwa ne duk wani binciken sa ana rushe masa, babu wanda yasan suna kan bincikar Baba Haladu amma gashi an kashe shi, dole akwai mai yi masa zagon kasa akan lamarin sa, lumshe idanun sa yayi yana tunanin yar budurwar yarinyar da tace Barde ya aiko ta, sai dai har yau suna neman ta sama da kasa basu ganta ba, tsaki ya saki dan shi baima yarda da yar mitsitsiyar yarinyar nan ba, dole ya tashi ya nuna ma makiyansa dan zaki ya girma..

Washegari tun safe Batula ta gama duk wani aiki da tasan nata ne tayi wanka ta shirya dan raka Umman su asibiti a duba lafiyar ta, daren jiya basuyi bacci ba dan jikin Umman yayi zafi haka kafafunta sun kumbura kwarai da gaske, bayan sun fito sai da suka biya dakin Nenne da itama kwana biyu batajin dadin jikinta, adawo lafiya tayi musu Baba Dan Asabe ya rage musu hanya ya kaisu asibitin..” Layi suka tarar sosai Batula ta yanko musu kati kana suka bi layin ganin likita, sannu Umman mu Batula ta fadi ganin yanda kafar Umman ke kara kumburi dan har takalman ta sai da ta cire su, sai wajan shadaya suka samu ganin likita, bayan Batula tayi masa bayani a takaice ya rubuta musu test suje suyi, nan basu samu layi ba nan da nan akayi ma Umman Batula ta biya dubu uku suka dawo wajan likita, karanta bayanin yayi kana ya sauke numfashi yana duban Umma da Batula yace”Zamu rike mahaifiyar ki anan ma,ana babu ishasshen jini ajikinta daga nan sai mu kara bincika sauran matsalolin dake tattare da ita, idan kuna da wanda zai bada jini yazo a diba, nan ya kira Nurse ya fada mata a basu daki tare da rubuta magungunan da za,a bukata kana suka fito, bayan an basu gado Batula ta dauki wayar Umman ta kira Baba Dan Asabe ta sanar masa abunda ke faruwa, “Ohk ganinan Batu ki daina kuka, yanzu zan taho insha Allah…

“Numfashi Batula ta sauke ganin Umman ta samu barci, kar taci komai koda ta bukata hakan, dan idan ana karama mutum jini ba,a cin komai, ga wannan kuma ku siyo muna bukatar sa anjima idan an cire mata jinin, “Amsar takardar tayi tana fadin”Toh mun gode anty, Murmushi Nurse din tayi tace” Karki damu kanwata Maman ki zata samu sauki, gyada kanta kawai Batula tayi tana zuba ma Umman su ido, fita Nurse din tayi Baba Dan asabe ya shigo shida Inna Larai da Inno sai Saratu, duk ya mai jiki sukayi ma Batula ta amsa sun dan jima kana Baba Dan Asabe ya su tashi ya mai dasu gida, anan suka bar Saratu zuwa anjima Inno zata dawo ta zauna da Umman su kuma su koma gida..

“Kinga na manta ban fada ma Baba ance a siya magani ba, ko dayake ma akwai kudi a hannu na bari na siyo kawai, “Dan Allah karki dade Batu, kizo yau akwai labarai masu dadi, dariya Batula tayi tace nasan bai wuce labarin soyayyar ki da abokin Yaya Mahmuda Taro ba, dan wallahi ko jiya ya bani sakon na gaishe ki, tuni Saratu ta hade fuskarta gami da harara Batula, Allah ya tsare ni, kuma na fasa baki labarin, dariya Batula tayi tana fadin” Sorry bari na yi sauri na dawo…

 

“Haba dai malama yanzu wannan maganin ne dubu biyu, nifa nasan kudin sa a unguwar mu dubu da dari biyar ake sai dashi, gaskiya kuncika tsada, “Ke na kula idanun ki a tsakiyar kai yake, idan bazaki siya ba ajiye ki dauki kudin ki bai dameni ba, ko kuma mai ya hana ki zuwa unguwar taku ki siyo, kinzo nan kina mana fitsara, ” Uhm nidai ai gaskiya ta nake fada, bayan ma ance asibitin na gwamna tine.. Tunda bana ubanki bane bar nan wajan matar ta fada cike da masifa, “Tab kika zagi ubana ta fadi da karfi cikin tsiwa, wallahi Allah sai ya saka masa… ” Wai Rakiya meke faruwa ne haka.. “Cewar wani mutum yana karasowa wajan, Sir wallahi yarinyar nan ce daga zuwa siyan magani tahau yimin rashin kunya…

“Kallon Batula mutumin yayi sama da kasa kana yace”Ke meke faruwa ne tsakanin ki da ma,aikaciyar mu?”Matse kwallah Batula tayi cikin hararar Rakiya tace”Magani nazo siya tace min dubu biyu kuma nasan dubu da dari biyar ake sai dashi dan nayi korafin yayi tsada tahau zagina.. “Ohk muga maganin.. mika masa maganin tayo ya duba, cikin bacin rai ya dubi Rakiya yace” Wannan maganin yaushe ya koma dubu biyu, innaji ko dazu nazo siyan shi dubu daya na biya,me yasa baku da tausayi ne.. Kije office ki jirani sannan bata canjin ta katuwar banza, cikin jin kunya ta bama Batula canjin dubu dayan ta, godiya Batula tayi masa ta wuce..

“Kara duba maganin takeyi tana karanta rubutun jikin takardar da aka lika, maganin karin jinine dan Baba Shamsu yana siyo ma Lawisa shi idan bata da lafiya, sam bata lura ba saiji tayi an ban gajeta tayi taga taga zata fadi tuni ta kama hannun matakalar benan dake gefan ta, maganin hannun ta tuni yayi nasa wajan ya fashe.. ” Ihu ta saki mai karfi gami dayin tsalle ta rike rigar wanda ya bangaje tan tamau a hannun ta…

“Idan ka isa ka matsa daga nan Allah ya tsinan Albarka, wallahi sai an biyani tabbb…

Da sauri Tahir ya juyo yana duban ta, ” Tabbas yarinyar da yagani ce a wannan ranar taron bude supermarket dinsa, kaga malam ba zura min ido zakayi ba kawai biyani magani na ka tafi, kasan fafutukar da nayi kafin na siya maganin toh sai da nayi yaki da cin hanci da rashawa, amma gashi kai ka bangaje ni duk wahala ta ta tashi a banza.. “Buge hannun ta Mansur yayi cikin fusata yace” Ke mahaukaciyar inna ce ke sakar shi mana.. “Kai ban sanya dakai ba balle ka dauka, cewa nayi a biyani maganina.. “Ohk munji sakar masa riga cewar Usman dake murmushi.. “Toh naji dan kai na ga kana da kirki, amma shi baya magana n… “Laaa ai nama sanka wallahi, kai baka gane niba.. “Ta fada tana kara kallon fuskar Tahir daya hade ta kamar hadarin dake shirin zubar da ruwa.. ” Nasan watakila ka manta, mun hadu dakai kusan sau uku, har mamarka na sani kuma nice kwanaki wani mutum ya taba aiko ni na kawo maka sako har yace nace maka sunan shi Barde…

“Ohk muje tacan muyi magana kinji, nan mutane na kallon mu kar suyi zaton wani abunne ya faru cewar Usman.. “Toh amma ya batun magani na kuma.. Karki damu zamu siya miki wani, “Ke Batula inna zaki?” Taji muryan Baba dan asabe daga bayan ta.. Da sauri ta juyo ya karaso wajan fuskarsa a hade, duban Tahir yayi cikin bacin rai yace”Tanan kuma kuka bullo, inna kara gargadin ka da babban murya,ku fita daga hanya ta amma bakuji ba… “Cikin takun isa Tahir ya karaso gabansa yana wani murmushi mai cika da ma,anoni masu dama Yace”Malam Habibu kenan idan anki fa, duk wani boye boyen da kakeyi inna sane dakai, har yanzu dai hannu na bai kai kan files din ka ba, amma ka kula ya fadi yana karkada hannun sa..

“Cikin mamaki Batula ke kallon Baba dan asabe dayaja hannun ta sukayi gaba yana sakin tsaki..

“Dole akwai abunda Malam Habibu yake boye mana Usman, sannan a kara bincika min alakar dake tsakanin yarinyar nan da Malam Habibu inna son sanin meke faruwa

[07/09, 11:07 pm] +234 703 966 0069: 🕸️ *BAKIN RIJIYA*🕸️

 

 

Na Khausar Muhammad

 

 

*9*

 

 

“Cikin fusata Baba dan asabe ya hankada Batula cikin dakin da aka kwantar da Umma wanda har lokacin barci takeyi, da sauri Saratu ta mike tana kallon Batula da jikinta ke tsuma, “A she Batula baki da hankali ban sani ba, uban me yafitar dake waje har na ganki tsaye da wadancan samarin, tukunna ma me suke fada miki.. “Gabadaya Batula ta shiga rudu dan ta rasa amsar da zata fara bama Baba dan asabe, hawaye ta farayi ganin bazatayi magana ba yasa Baba dan asabe sauke ajiyar zuciya yace”Samu waje ki zauna ya fada yana nuna mata kujerar roba dake gefan ta, zama tayi saman kujerar a dofane har yanzu jikinta rawa yakeyi. “Ki kwantar da hankalin ki Batu ki min bayani kinji, bana son ki sanya kanki a matsala, tarayyar ki da wancan saurayin Tahir babbar matsala ce a kananun shekarun ki, dan haka kimin bayani ko hankali na zai kwanta kinji..gyada kanta tayi gami da yi masa bayanin komai har sakon da barde ya bata ta boye, sai dai ta boye masa mafarkan da takeyi na Tahir da mahaifiyarsa, wannan kuma sirrin tane..” A furgice Baba dan asabe yake kallon Batula yace”Barde fa kikace Batu, daman be mutu ba..

“Kallon Baban nata tayi tace”Wallahi haka ya cemin sunan sa yake, yanzu haka sakon daya bani yana gida na boye.. Kallon Saratu yayi yace”Ki kula da Umman ku bari muje gida yanzu mu dawo, hannun Batula yaja suka fice daga cikin dakin, akan idanun Usman suka hau napep dinsa suka fice daga hospital din, kallon wani saurayi dake kan mashin Usman yayi nan ya kunna mashin dinsa yabi bayan su shi ma Usman ya shige mota…

“Batula bayan sun isa gida ta shiga dakin Umman su ta dauko masa sakon da Barde ya bata, hannun shi na rawa ya amsa gami da bude karamar jakar, wani garamin USB ne ya fado cikin shi akwai memori, sai wani rubutu adan karamin kati daya kasa gane kan maganar, takardar kuwa babu komai acikin ta, wani dan tunani yayi kana ya dubi Batula da ta zuba masa ido yace ki dauki duk abunda zaku bukata na asibiti nan da mintuna biyar zan dawo na kaiki keda Inno, gyada kanta tayi shikuma ya fice cikin sauri, napep dinsa ya shiga yana kokarin tada ta yaji an shiga bayan napep din, kokarin juyowa yayi yaji kan bindiga a gefan kugunsa,”Karka sake ka juyo idan kuma kayi gardama zan fasa kanka wallahi, amshi nan oga zaiyi magana dakai..saurayin ya fada yana daura masa waya a tafin hannun sa, kangata a kunnen sa yayi sautin murmushi ya shiga cikin kunnen sa, Malam Habibu kura kenan, kana tunanin zaka iya bace min ne, ka bani mamaki gaskiya, kar inja ka da magana, ka bada sakon daya zama mallaki na akawo min kafin ka mikashi ga tsohon jakin ubangidan ka, nasan ka gane me maganan sai haduwa ta biyu kuma… Kit aka kashe wayar saurayin yace”Bani abun da kafito dashi yanzu daga cikin gidan ka… Mika masa takarfar da jakar Baba dan asabe yayi saurayin ya fice daga napep din da sauri gami da hawa mashin dinsa ya jata a guje ya bar unguwar..

“Numfashi Baba dan asabe ya sauke gami da dafe kanshi, gaskiya Barde baka kyauta min ba, dan me zaka sanya ahalina cikin matsala, dole ne na tashi tsaye na dauki mataki akan Tahir ya aiyana hakan a cikin zuciyarsa, cikin gidan ya kara komawa ba jimawa suka fito shida Batula da Inno sai Nenne da itama zata asibiti duba Umman, cikin mintuna Talatin suka isa asibitin Batula na kokarin fita daga Napep din Baba dan asabe ya tsayar da ita, “Batu inna son daga yanzi kar wani ya kara kiran ki ko aike ki amsa, wannan sakon da aka baki zai iya jawo mana fitina ba ke kadai ba har mu, dan Allah ki kara kulawa.. “Numfashi Batula ta sauke tace”Insha Allahu Baba, sai dai naji kace min Tahir yana da matukar hatsari daman ka san shi?”Murmushi Baba dan asabe yayi Batula akwai matukar wayo yace”Nasan Tahir Batula na kuma san mahaifinsa, sai dai akwai abubuwa da yawa wanda ba dole ne kwakwalwar ki ta iya fahimta da ganewa ba, amma insha Allahu gobe idan nazo zan baki labarin wanene Tahir duk kuwa da nima ba wani sanin tarihin gidansu nayi ba, shikenan Baba insha Allahu zan kara kiyayewa, Yauwa haka nakeson ji ya fada suka nufa cikin asibitin tare….

 

“Tahir babu komai fa acikin wannan madaukin haka ma takardar, amsar takardar Tahir yayi yana nazarin ta, kana sun gwada memorin ma babu komai acikin sa, “Wannan abun akwai daure kai sosai Tahir, dole akwai wani abu da muka gagara gane wa, mikewa Tahir yayi idanun sa sunyi jajir ya rasa wani irin tunani zaiyi, kallon Usman yayi yace”Inna son ku kamo min Malam Habibu, da hadin bakin sa aka shirya komai, but mubar abun nan da kwana uku akwai kurciyar da nake son kamawa… “Ohk babu damuwa…

“Cikin kwana biyu Umman su Batula ta samu sauki sosai, dan kumburin kafarta sun sabe haka zazzabi da jirin da takeji ya sauka, dan haka doctor ya rubuta mata sallama, Baba dan asabe ne yazo ya dauke su suka koma gida..

“Batula ta koma makaranta dan kwana biyu bata zuwa saboda ciwon da Umman su tayi, duk dama Saratu da Samira na taimaka mata da note haka Saratu takan yi mata bayanin abunda aka koyar dasu, Yau ita kadai ta samu zuwa schl saboda Saratu batajin dadi tana fada da ciwon mara,karfe hudu na yamma aka tashe su kamar kullum, suna tafe Samira na bata labarin wani dan uwan su dake matukar sonta, dariya Batula tayi tace” Wallahi idan innajin labarin soyayya ashashanci nake daukar ta, ke nifa bazan yi aure ba dan har yanzu ban girma ba…

“Dariya Samira tayi tace”Kai amma Batu kina da abun dariya, ke har yanzu yarinya ce amma ni kinga shekaruna sha takwas fa, shiyasa Inna tace bazan gama karatuna ba zanyi aure nima nafison haka kar wata ta kwace min Haruna na, dariya Batula tayi tace” Toh Allah yabar kauna, ni bari na gangara kasuwar dandali zan siyama Umma tsakin fate da rama.. “Toh shikenan dan Allah ki gaida Saratu da jiki, insha Allahu gobe zan je na gaishe ta… “Karki damu zan fada mata.. Napep Samira ta tara ta wuce Batula kuma ta gangara kasuwar dandali dan babu nisa sosai danan makarantar su, tana tsaye ana auna mata tsaki juyowar da zatayi ta hango mutumin da suka hadu a wajan taron nan har ya fada mata sunan shi Barde, yana tsaye gaban me kayan marmari ana zuba masa a leda, kara ware idanun ta tayi tabbas shine idanun ta ba gizo yake mata ba, yana kokarin juyowa barin da take ne ta juya kanta da sauri dan karya ganta, amsar tsakin tayi gami da juyowa ko zata ganshi, can ta hango shi yana tafiya da sauri da sauri kamar zai kifa, bin bayan shi tayi da sauri dan tanason ganin inda zashi, can wani karamin gida taga ya shiga dake wani siririn lungu kana ya turo kofar gidan ya rufe.. “Numfashi ta sauke kana ta juyo ta tafi zuciyarta cike da tunani daban daban, dole ta sanar da Baba dan asabe abunda ta gani…

“Da dare duk suna zaune a tsakar gida ana shan iska gami da hira, Baba dan asabe yayi sallama ya shigo gidan, sannu da zuwa suka shigayi masa Nenne cikin washe baki tace”Daman kai neke jira tuntuni sai gashi ka shigo da wuri ma..”Toh Allah yasa lafiya Nenne, nim fura da nono na siyo miki tun dazu karyayi tsami nace bari na dawo da wuri na kawo miki.. “Allah sarki nagode sosai, Allah yayi muku albarka.. Ameen Nanne innajin ki, Yauwa inna Hajja Kulu da ta kawo mana tsaraba kwanaki?”Gyada kai Baba dan asabe yayi yace”Allah sarki nagane ta, Nenne tace yauwa toh jibi zata zo nan gidan, dan dazu munyi waya da ita awayar Hajia Laure,dan haka kaida Shamsu ku hada kudi ayi cefene mai kyau har kaji nakeso a siya, Suwai zatayi musu girki dan duk nafi aminta da girkin ta, “Shikenan Nenne insha Allahu gobe idan na fita zan siyo komai dan akwai kudi a hannu na, Allah kuma ya kawo su lafiya…

“Ke Batu dauko abinci na ki biyoni dashi su malam magaji na waje acan zamuci.. Allah sarki yau ya dawo kenan?”Eh Nenne kinsan kanin baban shima babu lafiya ciwon sugar har an yanke masa kafa daya.. “Allah sarki banji labari ba kuwa, kuma ko dazu na hadu Delu bata fada min ba,insha Allahu zan leka gidan gobe, Hijjabin ta Batula ta saka tabi bayan shi dauke da farantin sulba da aka daura kwanan abinci na tuwo da miya,..”Uhm Baba yau naga mutumin nan daya bani sako har yace sunan shi Barde… Da sauri Baba dan asabe ya juyo yana kallon Batula cikin mamaki yace”Da gaske kike Batu?” Wallahi kuwa Baba, yau naje kasuwar dandali siyan tsaki na ganshi yana siyan kayan marmari, dan na tabbatar da shine har binsa nayi naga gidan daya shiga…

“Shiru yayi cikin tunani kana yace”Karki fadama kowa maganar nan Batu, insha Allahi zanyi bincike dan abin akwai daura,lallai akwai kullin da ake hadawa me wuyar kwancewa..

 

 

“Bana tunanin wannan hanyar me bulle wace Usman, dole musan wanda ke fitar mana da sirrin kamfanin mu, wannan file din ka duba akwai sunayen wadan da nakeson a bincika min account dinsu pls inna bukatar ka turamin bayanan komai ta email dina, “Ohk Sir insha Allahu zuwa anjima zan tura maka bayanan, xuwa anjima akwai meeting karfe uku Mansur ka sanar da ma,aikatan mu..

“Insha Allahu Sir… Mikewa yayi gami da duban Usman yace muje pls, tun dazu nake ganin misscall din Hajja Allah yasa lafiya, Dariya Usman yayi yace”Hajja rikima, kaji family meeting ranar friday Mami ma jibi zasu biyu jirgin safe.. “Oh.. “I miss my Mami wallahi, kwana biyu bamuyi waya ba, kaina ya dauki zafi.. ” Mami mahaifiyar Usman ce wato Hajia Bilkisu diyar Hajja ta uku, a karin Adamawa take aure da iyalanta itama,mijin Mami wato mahaifin Usman me kudi ne sosai sai dai mutum ne shi da bai damu ya shiga rayuwar wani ba, zumuncin ma ba damun shi yayi ba shiyasa da wuya kaganshi idan ana sha,ani acan kasar Thailand yake gudanar da kasuwancin sa.. Bayan sun isa gida Mansur yayi parking suka fito zuwa cikin gidan, yau bangaren nasu kamar da baki jin tashin hira da dariya, da sallama Tahir ya shiga parlon Hajja Usman da Mansur na biye dashi a baya, “Cikin farin ciki Layla ta zuba masa idanun ta yau ta taki sa,a ya dawo tana gidan..

“Gaida mutanen parlon yayi kana ya nufi dakin sa zuruf Layla tabi bayan sa, Hajia Falmata cikin murmushi take duban Usman tace”Lallai Usman baka da kirki yaushw rabon da na sanya ka a idanuna, kai ma zakayo halin Tahir ko?” Shafa kanshi yayi yana murmushi yace”Ba haka bane Ummi wallahi ko jiya na tambayi Hajja naji banji mutsin kuba tace bakwa kasar..

“Dariya tayi tace”Allah yasa da gaske kake, jiya muka dawo daga Canada naje bikin wata yar kawata da aka kaita can kasar, gaida ita Mansur yayi ta amsa kanta a dage,a rayuwar ta ta tsani Mansur saboda wani dalilin ta da tabar ma zuciyar ta…

 

“Haba Ya Tahir yanzu bakayi missing dina ba, ni inna can inna tunanin ka…. “Pls Layla get out… Ya fadi adan tsawa ce yana nuna mata hanyar fita daga bedroom din, shikenan zan fita amma inna jiran fitowar ka yau akwai labari me dadi, ba tare da ya saurare taba ya shige toilet yanajan tsaki..

“Shiru Hajja taji Tahir bai fito ba, ga abincin sa angama hada masa, kallon Sahura tayi tace” Inna ga yau dan gidan ki ganin baki ya hadashi saukowa, hada masa abincin akai masa dakin shi..

“Toh Hajja Sahura ta fada nan ta hada masa abincin cikin kuloli masu kyau sai shayin sa da Hajja ta dafa masa, tare da Hajjan suka wuce bedroom dinsa Sahura na dauke da babban tray a hannun ta, “A bakin gado ta same shi zaune yana aiki a laptop dinsa…

“Sannu Hajja na da kokari.. Hannun sa Hajja ta kamo tana fadin”Yauwa naga baka sauko ba nace Sahura ta kawo maka nan.. “Damuwa ce bana so Hajja, ka wannan mara kan gadon tazo gidan damuna zatayi.. “Au wai Layla, bana son haka me sunan Baba yarinya na sonka amma kana kauce maka, ga Jalila ma, ko jiya da mukayi waya sai da ta tambaye ka, tace baka daga wayar ta..” Bude kulolin ya shigayi yana tabe bakin sa yace”Wai ni sa,an sune Hajja, yaran nan sun raina ni wallahi ni bani da ra,ayin aure y….

“Baka isa ba me sunan Baba, aure fa shine cikar kamalar mutum, ga Mansur yaran sa biyu, amma kai da Usman kun tsaya ruwan ido toh zan biyo muku ta bayan gida, sannan gobe akwai unguwar da zaka rakani muje gidan wani aminin Kakan ka ne karka kawo min uzurin aiki na fada maka, ficewa tayi daga dakin ta barshi dafe da kanshi dake sara mishi..

[07/09, 11:07 pm] +234 703 966 0069: 🕸️ *BAKIN RIJIYA*🕸️

 

Na Khausar Muhammad

 

*10*

 

 

 

A karo na uku Batula ta kara jan bargo tana jan tsaki, yau tun karfe shida na safe Nenne ta hana mutanen gidan sakat, ko wani yaro da aikin sa haka iyayensu, ana ta kalkale gidan, wanda baiyi ba yasha fada da masifa, Batula kuwa kusan sau biyu Lawisa na zuwa kiran ta inji Nennen amma taki tasowa..

“Wai ni Batula bata tashi bane, tun dazu fa na aika kiran ta amma tayi min banza Nenne ta fadi tana kallon Umma Suwai da suke ta aikin figar kaji, hararen gefan ido Inna Larai ta watsa ma Nennen tana kunkuni, dan duk haushi ya gama cika ta..”Ki fito ki zage ni kawai Larai, baku san muhimman cin mutanen nan bane awaje na, toh bari kuji, wannan matsugunin da kuke zaune su suka mallaka ma Malam har aka auro ku kuke zaune, da kuna can kun kare a gidan haya ana bin layin shiga bandaki.. Saboda haka dole ayi idan kuma ba haka ba rayuka su baci, ke kuma Suwai idan ke kika hana diyarki fitowa bari ni naje da kaina na taso ta ishasshiya, yo Allah na tuba Batu ta samu gidan hutu ai ko kafar ta baza ka gani ba kofar daki… “Tun kafin ta karasa shiga dakin Batula ta fito tana zumbura baki cikin jin haushi”Sannu ishasshiya matar sarki ke ga yar hutu kin nade saman gado idan aka gama ki debo wadannan kafafun naki kamar sandar ba fulatani kizo kici dan kadan daga aikin ki ne..”Uhm ai da yake kafafun ma irin naki ne..”Iye me kika ce..”Murmushi Batula tayi tace”Cewa nayi an tashi lafiya Nenne.. Tabe baki Nenne tayi tace”Ga alama kin ganni ras dani, yanzu ba wannan ba inna wannan zobon da kika taba hadama Baban ku shamsu da zaiyi baki.. Gyada kai Batula tayi tace nagane wanda kika dunga santi ko.. “Eh yauwa shi, ai duk na siyo kayan zobon dan Allah Batu kiyi shi yayi dadi yanzu ki hada sai ajima akai gidan Maman jiniyo ta samun a firiji, Toh shikenan karki samu damuwa Nennen mu…

“Zuwa karfe takwas sun kammala komai Nenne ansha wanka yau bakin ta yaki rufuwa, “Umma ni bari naje gidan su Naja tamin kitso tace nazo da wuri saboda zatayi wanki Batula ta fada bayan ta gama kama gashin ta mai karfi baki suduk sai dai yana da dan tsayi ba laifi..

“Allah ya tsare ki gaida Maman su amma karki dade kinsan za,ayi baki a gidan.. “Dariya Batula tayi tace”Bakin Nenne yan gayu, yau fa tasa na canza mata labulayen daki kusan sau uku, gajiya nayi na gudu tana ta mita.. Hajjabin ta tasanya me dogon hannu kana ta dauki man kitso ta fice..

“Kusan awanta biyu a gidan su Naja makotansu, har aka gama kitson ta taimaka ma Najan da aikin gida kana tayi mata sallama ta taho gida, tun daga nesa ta hango motoci biyu bakake sai kyalli sukeyi kamar an shafa musu mai,Murmushi tayi ta karasa kofar gidan kallo daya tama Tahir ta gane shi, su uku ne kamar yanda ta gansu ranar suna tsaye duk ya bata fuska kamar zaiyi kuka, duk da ya gane ta amma sai ya fuske ya kauda kanshi, sai dai yana mamakin anya wannan yarinyar ba aljana bace, me tazoyi nan kuma..

“Yauwa kudin maganina kuka kawo min ko me kukazoyi kofar gidan mu?Kallo daya shima Usman yayi mata ya gane ta,yar dariya yayi yace”Wai nawane kudin maganin nan ne, naga idan bamu biyaki bazamu huta ba…”Dubu daya ne, amma ku barshi na yafe masa tunda shi ya fasa min amma kuce masa ya bani ha kuri ta fadi tana rike kugu.. “Kimtse dariya Mansur yayi ganin yanda Tahir ke auna mata harara cikin fusata yace”Ke bay nan… “Dariya Batula ta kwashe dashi haka su Usman sunayi ahankali, tab daman baka iya magana ba wai bay nan kai da zaka ce bar nan wallahi tsamin baki gare ka ta kare maganar ta tana dariya sosai..

“Harara ya watsa ma su Usman kana ya wuce gami da bude motar ya shiga..

“Gida ta shige tana dariya Saratu dake kokarin shiga dakin Nenne tace” Lafiyar ki kuwa Batu, ko duk murnan zuwan bakin Nenne ne?”Bari kawai Saratu yau wani kato na gani mai tsamin baki.. wai zaice ke barar nan wai Bay nan.. “Dariya itama Saratun tayi tace muje mu gaida bakin Nenne ki nuna min shi, dakin suka shiga da sallama Hajja na zaune an baje a falon Nenne duk da bawai irin katon dakin nan bane amma yana da girma babu laifi suna ta hira da dariya..

“Yanzu duk wadannan jikokina ne Fati, kai masha Allahu, gaida ita sukayi ta amsa cikin fara,a tana tambayar sunayen su… “Ni da za,a bani daya a ciki ai dana ji dadi na bawa me sunan Baba,.. Tashi su Batula sukayi gami da fita suka basu waje..

“Murmushin jin dadi Nenne tayi tana gyara zama tace”Wai Tahiru da ya shigo muka gaisa?”Eh shi kuwa, ni daman na fison ya auri karamar yarinya kamar haka, kinga zasu fi fahimtar juna su zauna lafiya..

“Hmm Kulu kenan ai kinfi karfin haka a waje na, kuma suma wadannan yara duk jikokinsu ne sai dai ita yar babbar anyi mata miji dan harya zo ya tambaya anan unguwar yake, ita karamar ce dai tukunna, cikin jin dadi Hajja tace”Ai kuwa na gode, ni baso ma nake a dauki lokaci ba Fatiti,ko adakin ta zata cigaba da karatun ta da izinin Allah, nan tsofin suka gama shawarwarin su cikin jin dadi…

“Wai kina nufin wancan dan gayun Batu?” Dariya Batula tayi tace”Eh shine, wallahi da zaiyi magana sai kinci dariya.. “Kwafa Tahir yayi cikin jin haushin Batula, wato kiran yara ma tayi suzo su kalle shi kenan, a duniya ya tsani ayi masa dariya bai iya fadin R ba, idan akayi masa kuwa ya dunga kuka kenan lokacin yana yaro yaki kula kowa, sai ga yar tsigigiyar yarinyar nan na kokarin raina masa hankali, hade ido sukayi ta murguda masa baki tana dariya kana tabi bayan Saratu zuwa cikin gida…

“Tahir duk ya kagara su tafi amma Hajja tayi rantsuwa idan ya tafi ranshi zai baci, shi har mamakin wannan kauna dake tsakanin Hajja da mutanen gidan yake, a zauren gidan aka shimfida masu tabarmi su Batula suka kawo musu abinci.. Dakyar ya fito daga motar ya shigo zauren gidan yanacin magani, da Batula ya kara hada idanu dake lekensa tana dariya, anya yarinyar nan bata da aljanu, yanda aka shirya abincin ga kamshi ya cika zauren dole ya sasu sha,awar ci, Usman da Mansur kuwa bude ciki sukayi suka ci suka koshi,Baba dan asabe ne ya shigo zauren ganin su Tahir ya sashi zare ido cikin mamaki yana kallon su, toh suma cikin mamaki suke kallon sa Tahir kuwa dauke kanshi yayi yana kai kofin tangaren na zobo me sanyi bakin shi, “Murmushi Baba dan asabe yayi yace”Sannun ku ko kune bakin namu?”Murmushin yake Usman yayi yana shafa kanshi cikin jin kunya.. “Hajja ce tafe tana rike da hannun Batula dan ba karamin shiga ranta Batulan tayi ba, Nenne na biye da ita da sauran matan gidan sunyo mata rakiya au wai ku baku kammala ba?”Hajja ta fada tana kallon su, tuni Tahir ya mike dan daman zaman ya gundure shi.. “Mun gama Hajja, toh Madallah.. Kallon Baba dan asabe tayi ya Gaishe ta, ta amsa cikin fara,a tare dashi aka rakota har motar dan Allah Fatiti idan sun samu hutu ki turomin jikokin nawa mu gaisa..

“Haba dai Kulu ai ranar asabar din nan zaki ganmu insha Allahu, Kai aikuwa da naji dadi, na turo driver ya zo ya dauke ku,.. “Batula kuwa fakar idanun su tayi ta zagaya ta gefan Tahir da tuni ya kame cikin motar, kwankwasa gilas din motar tayi ahankali yayi kasa dashi dan yayi zaton Usman ne, ganin ta ya sashi daure fuskarsa tamau.. “Dariya tayi tace”Bay nan sai anjima.. Gwalo tayi masa ta fella cikin gida da gudu…

“Sallama sukayi sai da motocin suka bace ma ganin su kana Nenne ta shigo gidan tana washe baki, “Kallon Batula tayi dake zaune tana dariya Saratu na taya ta…

“Iko sai Allah, wai ni Batu halan dariyar me kike kamar sabuwar kamu.. Dariya ta kara tuntsirewa dashi tace”Bayi kawai Nenne..

“Toh yau shakiyanci kikeji kenan tunda har makale murya kikeyi, kije kiyi tayi Allah yasa ki zama haka.. “Wallahi ba amin ba Nenne, ai wannan mugun fata ne.. Wannan fa yaron kawar nan taki ne be iya magana ba..

“Au toh yanzu naji batu, murmushin mugunta Nenne tayi ta shige daki tana fadin” Ni kyaleni da shirmen ki da baya karewa kuzo ku kwaso min abin arzikin da aka kawo min, da sauri suka bi bayan Nennen zuwa dakin ta…

 

“Sir kana da bako fa.. Mansur ya fada bayan ya kanga wayar salula akan kunnen sa.. “Yau bazan ga kowa ba Mansur na fada maka fa tun dazu pls..

“Uhm bakon wanda ka dade kana jira ne fa Sir, Habibu kura.. “Dan shiru Tahir yayi kana yace”Shigo dashi, and ka kira min Usman..”Ohk..

“Kusan tare da Usman suka shigo cikin kayataccen office din, Baba dan asabe ya bama Tahir hannu suka gaisa haka sauran, “Nasan zakayi mamakin ganina da yamma haka Tahir, dazu dana riske ku a gidan mu abun yayi matukar bani mamaki, sai dai mahaifiyata Nenne tayi min bayanin kokai waye da amintar dake tsakanin iyaye da kakanni, ita kanta mahaifiyata bata san na sanka ba, amma yau inna son na share maka zargin da ka dade kanayi a kaina…

 

MAFARI…

Add Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!