Hausa Novels

Ban Sake ta ba Hausa Novel Complete

Ban Sake ta ba Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Ban Sake ta ba Hausa Novel Complete

Yauma kamar kullum tana ‘kasan dalbejiyar data zame mata tamkar ďakinta aduk lokacin da bata da lecture’s.

Kallo ďaya zaka mata kagane tana cikin duniyar tunani, da sauri taďago kai tana dube2, taja numfashi mai ‘karfi, cikin sanyin murya ta ce, “hancina kadaina faďa min ‘karya, ka daina sha’ko min abinda ba gsky ba, tunda nake awajen mutum ďaya nata6a jin wannan ‘kamshin, kuma tunda yanisan ceni ban sake jiba, ban bashi damar dazan sake jiďinba, domin shi ya kasance mugu azzalumi, macuci!!!….ta faďa tana mai zubar da hawaye.

Wlhy na tsaneka Isma’il!!! mayaudari kawai ta fashe da kuka mai ban tausayi.

Haba iman kina ganin haka rayuwa zata kasance kullum cikin kuka da tunani??, maganar miss xoxo takatsema iman surutan datakeyi, iman mu masoyankine masu ‘kaunarki ‘kauna irinta ‘yan uwan juna, tundaga randa muka fara ganinki a school ďin nan mukaji muna ‘kaunarki, dan ALLAH badan muba ki sanar mana damuwarki kozaki samu sau’ki, idan kuma munada taimakon dazamu yimiki saimu taimaka miki koda da addu’ane.

Gsky ne Miss xoxo yakamata iman tasanar mana damuwarta inhar ta yarda damu kamar yanda muka yarda da’ita, yau kusan shekararmu biyu da watanni tare bamu ta6a 6oye miki sirrinmuba, duk abinda yadamemu muna sanar da junanmu, ke kaďaice acikinmu kike 6oye mana sirrinki, bamusan dalilin hakanba kokuwa bamu cancanci sanin taki damuwar bane oho??, amma kinsan damuwarki itace tamu, farincikinki shine namu, wlhy inaji ajikina tamkar uwa ďaya uba ďaya suka haifemu.

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng

Gskyarki ne Reefat xoxo tafaďa tana gyara zama, takamo hannun iman ta rumtse anata, iman inhar kin ďaukemu a matsayin ‘yan uwa ko ‘kawaye na kwarai to ki sanar damu damuwarki, koda addu’ane mutayaki, mungaji da ganinki haka iman, shekara biyu ba kwana biyu bace, inkuma bazaki faďa manaba bazamu takurakiba, saidai zamu taimaka miki da addu’a insha ALLAHU.

tami’ke Reefat tashi mutafi xoxo tafaďa tana kama hannun Reefat.

Iman ta fashe da kuka dan ALLAH xoxo karku tafi, kuyi ha’kuri ku saurareni.

Ya za’ayimu saurareki iman kullum haka kike faďa mana amma kin kasa faďa mana komai, kina ganin zamu cigaba da takuraki harsai kin sanar damune??, dammi zamu takura miki akan abinda bakida ra’ayin faďa mana???.

Naji na amsa laifina amma dan ALLAH kudawo karkuyi fushi dani, wlhy nima ina ‘kaunarku inajinku tamkar ‘yan uwana najini.

ALLAH sarki xoxo akwai tausayi dan haka saita jawo hannun Reefat suka dawo suka zauna, tsakiya suka saka iman, Reefat ta ce, “iman muna jiranki dan ALLAH ki sanar damu damuwarki kinji, ‘kila mu iya taimaka miki da wani abu.

Iman tasa hannu ta share hawayenta tareda ďanjan hancinta, tabi aminan nata da kallo, miss xoxo Reefat kuyi ha’kuri ban ta6a 6oye muku wani abu daya danganci rayuwata saboda rashin yarda daku ba, a’a ina ganin abinda yafaru dani tamkar sirrinane tunda yafaru dani a shekarun bayane kafin na haďu daku, sannan ina ganin abinda yafaru dani yariga ya faru ya wuce, amma ina neman afuwarku gareni, insha ALLAHU a wanan karon zan faďa muku wacece SAUDAT!?” saidai kuyi ha’kurin zuwa weekend sanan muna free saimuyi maganar atsanake.

Zan faďa muku tushen rugujewar rayuwata da tushen tubalin ginin damuwata……ta fashe da kuka mai tsuma zuciya da ruhi, ganin haka Reefat da xoxo suka shiga tayata suma, saida sukayi kuka mai isarsu babu mai lallashin wani, saida suka gaji dan kansu sanan sukayi shiru.

Mi’kewa sukayi suka nufi class kowa zuciyarsa babu daďi, iman sai waige2 takeyi danjin tamkar ‘kamshin turaren yana bibiyarsu, Xoxo ta ce, “iman wai mikike nemane??, lokaci da dama nakan ganki kina waige2 miyasa??.

Murmushi Iman tayi na takaici, wanan duk yana cinkin tarihin rayuwata xoxo karki damu asannu zaki gano abinda yakesani waige2 a wasu lokuta da dama.

Daga nan suka shiga aji, babu daďewama malami yashigo suka fara ďaukar darasi……………

 

 

 

Tofa masu karati komi wanan littafi ya kusa??, shin miye damuwar kawarsu Miss xoxo ne??, dani daku duk akan tambaya ďaya muke, domin nima bansan komai gameda hakaba, sai munbi wanan labari sannu ahankali sannan zamu samu amsar tambayoyin dake fal a zuciyarmu.

 

Takuce dai Bilyn Abdul.


Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [ Ban Sake ta ba Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake ku shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!