Hausa Novels

Banbancin Akida Hausa Novel Complete

Banbancin Akida Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

BAMBANCIN AƘIDA

( ƙaddarar Soyayya )

 

Based on true life story

 

Haƙin Mallaka

Queen Nasmerh

&

Nana M Sha’aban

 

*PRESENTED BY KING AIMAR PALACE*

 

 

_NOTE: Wannan labarin anyi shi a gaske, zai taɓa aƙidu daban-daban, dan haka duk wanda ya karanta littafin ya ji bai ji daɗi ba, ko kuma ya yi dai-dai da halin da ya taɓa tsintar kansa yayi haƙuri, ba mu yi shi dan cin zarafi ba, true life story ne. Akan aƙidun da za ku ci karo da su kuma ba mun yi ba ne dan nuna matsalolin aƙidun ba, mun yi ne da bayyana asalin labarin, dan haka ba mun ce lallai haka halayyar su ke ba._

 

*_GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN SAMMAI DA ƘASSAI, YA ALLAH MUNA ROƘANKA YADDA MUKA FARA LITTAFIN NAN LAFIYA MU GAMASHI LAFIYA, ALLAHU, ARRAHMAN, ARRAHIM._*

 

WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHE SADAUKARWA NE GARE KU MASOYAN LITTAFIN NAN.

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
*Wannan Littafin na kuɗi ne. Book one naira Ɗari ne kacal 100#.Domin biyan Wannan kuɗin, ka tura katin mtn na Ɗari zuwa ga wannan number*

*09037591994*

*Domin  nuna shaidar turawa ka tuntuɓi akwatin sirrinmu na whatsapp ta wannan number, 09 121873529*.

*Ko kuma wannan number*

*+234 812 218 8717*, *ku fara biya domin free pages ba mai yawa za mu yi ba gsky, a fara payment.*

 

_*FREE PAGE*_

*_CHAPTER 01_*

 

_______Babban tire ne a gabanta, ledar da ɗanta ya ajiye mata ta buɗe, shinkafa ce kwano ɗaya, miƙewa tayi ta shiga ɗakinta ta ɗauko wani gwangwani, ta fito tana tafiya dakyar kasancewar ƙafafuwanta suna yi mata ciwo, komawa tayi ta zauna, ta shiga auna shinkafar, sai da ta auna gwangwani biyar sannan ta saka gwangwanin cikin ledar ta ɗaure, tsintar shinkafar ta shiga yi, gaba ɗaya ta mayar da hankalinta wajen tsintar, sallamar da akayi ce ta sa ta ɗago da kanta tana kallon me sallamar, murmushi ta shiga yi tare da amsa sallamar da ”wa’alaikassalam ɗan albarka sannu da zuwa”

Ƙarasowa yayi ya zauna akan ƴar ƙaramar kujerar ƙarfe da take kusa da ita yace “Mama meyasa kike tsinta da kanki, ai da sai ki jirani tunda nace miki ba daɗewa zan yi ba”

Mama tace “A’a haba ni meye amfanina, ai ka riga da ka gama aikinka ni yanzu nawa nakeyi, ka shiga ɗakinka ka kwanta dan nasan ka gaji da yawa”

Sani yace “Haba ai kwanciya kam bata kamani ba, saboda rashin imani zanje na kwanta a ɗaki ke kuma kina nan kina fama da tsintar shinkafa, gashi daman ba isarshiyar lafiya gareki ba”

Sani yayi maganar tare da karɓar tire ɗin hannun Mama ya cigaba da tsintar shinkafar, yana gamawa ya zuba shinkafar a doguwar guga, ya miƙe ya nufi babban durum, ya zuba ruwa a cikin shinkafar ya wanke shinkafar ya zubar da ruwan, wajen murhun ya nufa, gyara tukunyar yayi dan ya ga tana ƙoƙarin zamewa, ya buɗe murfin tukunyar ya zuba shinkafar, ya mayar da murfin ya rufe.

 

***

Komawa yayi kan kujera ya zauna suna hira da Mama sama-sama, har sai da ya ga turiri yana fitowa daga cikin tukunyar Mama tace “da alama shinkafar ta dahu”

Sani ya fara ƙoƙarin miƙewa Mama ta dakatar dashi da cewa “tsaya mana Sani! ai ka riga ka yi min me wuyar ka bari na ƙarasa sauran aikin, saboda idan ba na motsa jikinnawa ai ba zan dinga jin daɗinsa ba, koma ka zauna ni kam na yafe maka ka ji ɗan albarka”

Sani yace “to Mama”

Wani yaro ne da ba zai huce shekara biyar ba ya shigo gidan ba tare da yayi sallama ba yace “Wai ance Sani ya zo”

Sani ya miƙe tsaye yana cewa “injiwa?”

Yaron yace “nima ban sani ba”

Mama tace “kai daman ka tsaya tambayar wannan ƙaramin yaron, ka fita mana ka gani koma waye”

Sani yace “to Mama ina zuwa” Yayi maganar tare da nufar hanyar fita daga gidan.

Ko da Sani ya fita waje bai ga kowa ba, ya gama dube-dubensa, ya kalli yaron yace “kace ana kirana, kuma gashi ba kowa”

Yaron yace “eh wata ce, ta aikoni na kiraka, tace ko ka tambayeni waye kar na faɗa maka har sai mun fito waje, tace idan mun fito nace maka Zeenart ce take kiranka, tace ka sameta a bayan gidansu”

Sani ya cika da farin ciki, bai san lokacin da ya zaro naira ɗari biyar ya ba yaron, “yau Zeenart ce ta zo har kofar gidanmu, Allah yasa dai ta amince da soyayyata” yayi maganar a fili tare da fara tafiya, tafiya yake cikin sauri duk irin yadda yake yin saurin gani yake kamar ba saurin yake ba, bashi da wani buri irin ya ganshi a gaban Zeenart ya ji ta furta masa kalmar so, yana zuwa bayan gidansu ya tarar da ita ta juya bayanta dan gudun kada wani ya ganta, sanye take cikin ƙaton hijab.

“Amincin Allah ya tabbata ga kyakkyawa mai tsaftatacciyar zuciya”

juyowa Zeenart tayi tana murmushi tace “kai ma haka Habibi”

“Habibi” Sani ya maimaita kalmar cikin wani irin shauƙi.

Zeenart tace “ko ba ka son sunan ne?”

Sani ya zaro ido yace “niiiii! na isa”

Yadda yayi maganar ne ya ba wa Zeenart dariya, tace “dan Allah daina zaro idon nan, ai sai ka tsorata ni”

Sani yace “Zeenart yanzu kina nufin kin amince da soyayyata, kina sona”

Zeenart ta sauke ajiyar zuciya tace “daban chan ina sonka, kawai dai kishin Aƙidata ne yasa ban amince da kai ba, saboda ba Aƙidarmu ɗaya ba, kai Ɗan ɗariƙa ne, ni kuma ƴar kur’aniyun, amman yanzu na ga zuciyata tana ƙoƙarin ta buga saboda sonka, shiyasa na yar da makamaina, dan kar naje na cuci kai na”

Sani yace “ai gwanda da kika yar da makamanki, Zeenart nayi miki alƙawari ba za ki taɓa yin danasanin kasancewarmu tare ba, zan nuna miki zallar soyayya”

Haka dai suka dinga faɗawa junansu da kalamai masu ratsa zuciya, daga ƙarshe sukayi sallama Zeenart ta zagaya ta shiga gida, Sani kuma ya koma gida, ji yake kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha saboda farin cikin da yake ciki yau.

 

***

“Mamy” Wata kyakkyawar yarinya wacce ba za ta wuce  shekara ashirin da bakwai ba a duniya, ta kalli mahaifiyarta wacce take kusa da ita “Naam Raheema”

Raheema tace “Mamy dan Allah kiyiwa Abba magana ya barni na ƙara ko da sati ɗaya ne a gida, kafin na koma gidana”

Mamy tace “kinsan dai halin Abbanku ba sai na tsaya yi miki bayani ba, idan zaki fara shiri ma ki fara yi gobe ki koma kafin ranki ya ɓaci”

Raheema jikinta a sanyaye tace “shikenan bakomai” tayi magana tare da miƙewa ta shiga wani ɗaki, Mamy ta bi bayanta da kallo, har sai da ta shige ɗaki ta komar da kallonta kan t.v inda take kallon wani wa’azin Malam Jafar.

 

****

Tafiya take cikin nutsuwa, sanye take cikin baƙaƙen kaya, hijabinta iya guiwa shima baƙi ne, ta sanya baƙin niƙaf a fuskarta, kyawawan idanuwanta kawai kake iya gani saboda, niƙaf ɗin ba irin wanda ake rufe har wajen ido ba ne, wani gidan ƙasa na ga ta shiga, ko mintina biyar ba ta yi da shiga gidan ba, suka fito tare da wata kyakkyawar yarinya, hijabi ne a jikinta light blue, doguwa ce, baƙa ce, amman irin baƙin nan ne da turawa suke kira da chocolate colour, siririya ce, riƙe suke da hannun juna suna tafiya suna hirarsu irinta amintattun ƙawaye.

Rukky ta kalli Zainab tace “Masoyiya! sai fa mun biya ta studio ɗin sahibina domin na ganshi na ji daɗi a zuciyata”

Dariya Zainab tayi tare da ɗaga niƙaf ɗinta, ƙare mata kallo nayi baƙa ce, amman ba irin baƙin nan sosai ba, doguwar fuska ce da ita, dogon hancinta yayi dai-dai da ɗan ƙarama bakinta “Lallai kam Masoyiya cewa zakiyi dai ja na zakiyi muje ku barni a gefe ku kuma kuna chan kuna shan soyayyarku” Rukky tace “Aa wallahi ba za mu barki a gefe ba, kuma ba dai-dai wa zamuyi ba, ina ganinshi zamu tafi gidan Aunty Zaliha” Zainab tace “tohm shikenan Masoyiya” Suna isa Studio, Rukky ta shiga ciki, Zainab ta tsaya a waje tana jiranta, dan ita ba me son mutane ba ce.

“Assalamu alaikum” Wani ɗan saurayi yayi sallama tare da tsayawa yana kallon Zainab ɗin, ita kuwa Zainab ganin irin kallon da yake yi mata yasa tayi saurin sauke niƙaf ɗin fuskarta muryarta na rawa ta amsa masa sallamarsa “Wa’alaikummussalam” Shi kuwa duk da fuskanci ta ɗan rikice saboda ganinsa, amman sam ya ƙi tafiya, domin baya tunanin ƙafafuwansa zasu bashi damar ɗagawa daga gurin, idan har ba jin daddaɗar muryarta ya sake ji ba.

“Yammatana wa kike nema ko nace gurin wa kika zo?” Yayi maganar tare da ƙurawa baƙin niƙaf ɗin ido, yana hasko irin kyawun fuskarta da ya gani ɗazu.

“Yammatana!” Zainab ɗin ta faɗa a hankali tana kallonsa ta cikin niƙaf ɗin, shi kuwa bai san ma kallonsa take yi ba, ana haka sai ga Rukky ta fito daga studio, “Laaa Aimar ya gida ya kake?” Rukky tayi maganar tana murmushi, Aimar ya kalli Rukky shima yana mayar mata da martanin murmushin yace “Lafiya ƙalau Malama Ruƙayya” sun ɗauki tsawon lokaci suna hira daga nan suka kama hanya su ka tafi gidan Aunty Zaliha yayar Rukky.

 

 

_Read more mai yawa zai fara zuwa ne da zarar mun gama free pages_

 

*Share & comments*

 

 

*NASMERH AND DIJARTY*

AMINAN JUNA

 

 

 

Name: [My Novels (www.mynovels.com.ng)]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na TelegramPowered by: www.mynovels.com.ng

2 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!