Hausa Novels

BANDIRAWO HAUSA NOVEL COMPLETE

BANDIRAWO HAUSA NOVEL COMPLETE

 

 

 

 

 

 

 

 

BANDIRAWO HAUSA NOVEL COMPLETE

KADAN DAGA CIKIN LITTAFIN…

[
“`Godiya ta tabbata ga Allahu (S.W.A) mai komi mai komai da ya yini musulma ya kuma cikamin zuciyata da imani ya kuma bani rai da lafiya sannan ya k’aramin da konciyar hankali nagode wa Allah da ya bani damar fara rubuta wannan littafi nawa lfy Allahu
rabbi ya nufeni da kammalashi lfy
Ameeen ya rabbil izzati“`!..

“`Dan Allah masu juya min novels na Ku bari bana so naga wata ko wani ta juyamin NAMIJI BAYA KADAN
har da cire sunana ko mene dalili ban sani ba zancen gsky a kiyaye bana so sam“`

Wasu motacin Hilux ne kusan guda goma suka fita daga cikin harabar makarantar sojojin dake jihar Kaduna wato *Jaji* a jere suka danno anci nansu kan babban titin da zai kaisu su zuwa cikin k’oryar birnin kadunan
Hilux biyar ne a gaban wata kyakkyawar mota mai matukar d’aukar hankali k’irar
BMW 7series kalar color ta bak’i mai kyau da sheki hatta glass d’in mai duhuce,
sai Hilux biyar kuma dake binta a baya
tafiya suke cikin gudu da k’aran jiniya da suka karad’e kan titin dashi ,

Bandirawo
Sojojin dake cike cikin Hilux d’in gaban BMW 7series da biyar da suke bayan shi duk fuskokin su a mirtuk’e suke ga hancin bindigogin su da suka watsa ta fuskar sauran ababen hawan da ke kaucewa gefen titi suna basu hanya dan jin wannan jiniyar ke shaidawa ma zauna cikin Kaduna cewa yaufa
Brigadier general Aliyu Muhammad Umar Rumoh,
ya shigo gari.

Bandirawo

Cikin BMW 7series yake zaune a baya cikin shigar kakin su na sojojin mai cike da tabburan girma kala-kala da ganin kafad’arsa zai ganar da mai kallonshi tabbas wannan babbane ya taka mata kai da dama.

Cikin lumshe ido da yana yinsa na fuskar kad’aici a hakan yana kallon meke gudana a fad’in garin na kd.

Kai tsaye Ugguwar Sarki suka nufa cikin tafiyar su ta tsarin sojojin kwarai.

Bandirawo

Ido ya tsurawa kan titin yayin da yake ganin wuce warsu ta dakatar da al’ummah
da dama da yawan cikin su masu kai yaransu makaran ta ne dan tun da a kayi sallah yaune makaran tu suka daddawo hutun sallah,
Phone d’inshi yazaro tare da kallon time cikin d’an jan gajeren tsaki ganin har (7:50 Am) tayi a ranshi, yake tuna wannan fitowar tasa yau yara nawa zata jawa makara zuwa makaran ta? waya san adadin yaran da za’a zane a sana dinshi? cikin jin abin bai mai dad’iba ya juya kanshi d’aya gefen titi nan ma motoci ya gani a jere a baking titin sun basu hanyar wucewa yayin da wasu kuma ma da k’afa suke tafiya wasuma matane suna rike da hannun yaran da nufin kaisu makaran ta wasu kuma yan matane.

Bakar Wasika Hausa Novel Complete

Bandirawo

Kai ya kuma juyawa cikin jin wani yanayi na sauk’ar mai ganin wata mace a gefen titi ta jawo d’anta da yake ta sa hannu yana tare fuskar sa dan idon rana yana kashe musu ido ganin haka ta cire tafin hannun ta a fuskar ta,
ta tare mai nashi tare da jawoshi jikin ta tana mai shafa kanshi.

 

Bandirawo

Ajiyar zuciya ganeral Aliyu ya sauk’e tare da rumtse idon shi cikin ranshi yake jinjina soyeyya irin ta uwa a kan d’anta so da tausa yawa da k’auna da kulawar uwa abinda shiko tasa uwar ta kasa bashi.

Ido a lumahen ya bud’e baki cikin bada umurni yace.
“Kai Sani kauce bakin titi ka tsaida motar ban son tafiyata
ta tsare ta wasu.”

Cikin bin umurni ya juya linzamin motar zuwa gefen titi yayi parking sannan Hilux 5da ke binsu suma suka tsaya,
suma guda biyar dake gaba jin k’arar tsayuwar motocin yasa suka tsaya tare da dirowa daga cikin motocin suka dawo suka zagaye
motar da Aliyu ke cikin suka tsaya cikin yanayin bada tsaro ga uban gidan nasu.
Sani dake gabanne yayi saurin fitowa ganin
Ogan nasu na shirin fita ,
cikin hamzari ya bud’emar marfin motar tare da sara mai.

Bandirawo

Cikin zafin nama da jarum ta ya diro daga cikin motar yayin da duk sauran sojojin suka sara mai tare da k’amewa a wurin.

Kai tsaye kan titin ya nufa suko ganin haka yasa suka biyo bayanshi tare da d’ana kunamun bindigogun su .
Jin karan d’anawa wan kata-k’ak’at ya sashi d’aga musu hannu alamun su sauk’e !
ba tareda bata lkciba sukayi k’asa da bindigogin sannan suka tsaya suna masu mmkin me zaiyi kuma me ya fitar dashi yayin da d’aya bank’aren kuma suke tsoron kar wani abu ya sameshi domainko shi jigone ga wannan k’asa tamu ta Nigeria kuma shi Garkuwa ne ga al’ummar wannan k’asa tamu Aliyu shine soja d’aya da sauran rund’unar sojojin k’asa ke jin zasu iya bashi ransu da lfy yarsu dan tsaron lfyarsa domain ko shine daya tamkar da 1000.

Yarima Ashman

yayin da jama’ar gari ko, ke mmkin ganin Wanda suke kaucewa suna bashi hanya sai kuma gashi ya fito yana basu hannu alamun suzo su wuce duk da fuskar sa ba walwala ko fara’a Amman hakan yasa al’ummah sun samu nitsuba dashi yayin da matasa ke bid’ar ganin shi ido a rude a man sai dai su ganshi a fuskar TV da jarida saiko suji jiniyarsa ko suga tawagar sojojin da ke tsaron lfyar sa haka yasa
matasan dake cikin ababen hawa suka rink’a sara mai da cilla mai Addu’ar,
“Allah ya tsare mana kai ya barka ekon bawa mutan kasarmu kariya”.

Cikin minti 5 duk ababen hawan sun wuce sai sauran masu tafiyar k’afa sai kuma gashi ababen hawan sun yanke ganin haka ya juya gun matan nan da d’anta daya fara k’olloh yana cewa.
Littafan Hausa Novels Guda 1000 masu dadi

Matar Makaho Complete Hausa Novel

Hotunan Lalle Masu Kyau Kunshin Gam

Matar Yaro Hausa Novel

Hajiya Gwale Hausa Novel Complete

Gyaran Nono a sari data

Tsofaffafin Hausa Novels Watpadd

” Mami ni dai bazan jeba don ko naje nayi letti za’a dokeni”,
cikin kula ta sunkuyo kan yaro tare da cewa “inkaje ka gaya musu uzurin ka na tabbata zasu barka”

k’arisawa yayi cikin sanyi tare da kauda kai ya mik’awa yaron hannushi,
shima yaro sai yasa nasa hannun cikin nasa yana mai tsoron lek’a fuskarsa shiko jan hannun yaron yayi tare da juyawa zai tafi dashi,
cikin sanyi matar ta bud’e baki da nufin gaya mai makaran da zata kaishi,
hannu ya d’aga mata tare da yin magana a dakile yace.
“ai nasan makaran ta zaki kaishi”.

k’ara binsu tayi tare da cewa.
“toh ai bakasan sunan school din nasu ba kuma baka san inda makantar takeba.”
cikin kauda kai yace .
“ai kinga ni makaho ne banga inifon d’in dake jikin shiba bare na game ina zan kaishi,
shi kuma yaron kurma ne bazai min bayanin inda zan kaishi ba ko?”.

kai ta jinjina tare da juyawa tana mmkin wannan mutumi daga mgn sai fad’a.

Shiko kai tsaye ya d’auki yaron ya kaishi makarantar tasu da taima kon yaron ya kuma hanesu da tab’a yaron.

Kai tsaye suka sake d’iban hanya har cikin Ugguwar Sarki inda gaba d’aya suka cika ugguwar da sowar jiniyar tasu.
wani kata faren gida gidane nagani na fad’a suka dosa kafin su isoma an wangale musu gate cikin iyawa da k’orewa suka kutsa cikin gidan yayin da farfajitar gidan dauke motocin har yana neman k’ari cikin sauri Sani ya fito tare da bud’e mai motar ya fito,
suma sojojin suka rik’a d’iriwo tare da Sara ma,
kai a sunkuye ya d’aga musu hannun tare da yimusu alamar su sauran su tafi lkci d’aya hilux 5 na bayanshi suka juya suka tafi 5 biyar na gaban shi kuma ya wanda ko wanne da sojojin 5 a cikin suko sai suka firfito tare da tsare farfajiyar gidan.
cikin takun kad’aici ya nufi cikin gidan k’ofar ya bud’e tare da kutsa kai cikin wani babban parlour taku biyu yayi ana uku ya tsaya cak tare da d’ago kanshi cikin tsuke fuska.

Ido ta tsura mai cikin murmushin mugunta da salon isa ta watsa mai mugun kallo murya a gadaran ce tace.
“Kai dakata me kake shigo mana gida da gad’ara? da isa ka dai san nan ba cikin Jaji akekeba bare kai mana mulkin mallaka! ka kuwa san
nan ba hurumin ubanka bane bare kai!
bare ka shigo mana kai tsaye cikin gadara!”.
Ido kawai ya tsura mata cikin jin zafin kala manta kai ya kawar tare da kaucewa gefen ya nufi wani babban corridor kanshi a k’asa,
cikin sauri ya rumtse idonshi jin furucin ta.
gabanshi ta kuma tahowa tare dayin murmushi cikin cusa bak’ar mgn race.

” Ba laifin ka bane tarbiya ce baka samu ba tun fari,
koda yake ina zaka samu tarbiyar tunda kai rain non gourone dama ina gouro zai iya bada tarbiya!,
ko daya take duk ba laifin Ku bane shi ya k’asa zaboma uwa ta garine tunda gashi ta watsar da kai,
ka zama tantirin d’an duniya! itama ta shiga tata duniyar ! ta watsar da kai ! wai a hakan kake ganin kai d’an sunnane?! waya ma san tsiyar da take shukawa? kai kuma a hakan kakejin uwace ta haifeka? ai duk uwa ta gari zama take ta kula da d’anta !”.

Cikin jin zafi da d’aci,
ya k’ara rumtse Idonshi tare da damk’e hannushi zuciyar sa tamkar wutu cikin kwayar idanunshi yakeji kamar rushu aka cusa mai lkci d’aya kanshi ya ringa wani irin mugun sarawa.

Cikin azama ya rab’a gefen ta ya wuce da sauri kai tsaye cikin bedroom ya wuce bindigan shi ya cillah gefen tareda fad’awa kan gadon cikin karfi ya rarumi……



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

​

 

 

Name: [BANDIRAWO HAUSA NOVEL COMPLETE]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

7 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!