Bani da Hujja Hausa Novels Complete

Hausa novel
Hausa novel

Bani da Hujja Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

.

 

 

 

*BANI DA HUJJA!!*

 

By Maimoon

 

Elegant online writers📚

 

Free book

 

1-2

 

A hankali, cikin nutsuwa ya ke sauƙowa daga benen, but at the same time, cikin kuzari da taku irin na cikakkun mazaje, ƙarasowa falon yayi, ba tare da ya ko kalli sashen da illahirin ƴan gidan ke tsaye cirko cirko ba yayi wucewar sa, da idanu duk suka bisa kowa da irin abinda ya ke saƙawa a zuciyarsa, har ya fito farfajiyar gidan wanda ke shaƙe da motoci na alfarma, direct wata mota ya nufa mai matuƙar kyau, kalar ash, buɗe motar yayi ya shiga sannan ya maida murfin ya rufe yana furzar da numfashi, har lokacin ba’a iya ganin furkarsa, bare asalin yanayin da fuskar ke ciki, saboda p-cap din da ke kansa, da kuma shade ɗin idanunsa, sannan da handkerchief ɗin da ya sa ya toshe daga hancinsa zuwa bakinsa ya ɗaure ta baya. A hankali ya soma driving, har ya fice a gidan bayan mai gadi ya wangale masa tangamemen gate ɗin, tafiyar da baifi ta minti ashirin ba, ta kawo sa ƙofar wani restaurant, wanda daga samansa aka rubuta AMAIRA RESTAURANT AND CO, sauka yayi tare da nufar ciki kai tsaye, cikin sauri wani ma’aikaci da ke sanye cikin uniform na ma’aikatan wajen ya ƙaraso wajensa, yana gaishesa tare da miƙa masa wata leda, karɓa yayi ba tare da ya amsa gaisuwar ba ya juya ya fice a wajen ba tareda ya furta ko da kalma ɗaya ba. Motar ya koma, tareda barin wajen gabaki ɗaya, sai da yayi tafiya aƙalla ta mintuna arba’in zuwa awa ɗaya, kafin yayi parking a ƙofar wani ƙaramin gida ɗan madaidaici, sauka yayi ya tura gate ɗin kasancewar babu mai gadin, sannan ya dawo ya shigar da motarsa, ya maida gate ɗin ya rufe, ledan ya ɗauka sannan ya rufe motar, yana tafiya cikin izza har ƙofar palon, makulli ya ciro a aljihunsa tare da buɗe kofar ya nufi cikin falon da ke da duhu matuƙa, karasawa yayi ba tare da ya kunna fitila ba, har ya kai tsakiyar falon, kafin ya ciro wayarsa tare da kunna haske, ɗaki ɗaya ne a cikin falon, hakan yasa ya nufi ɗakin kai tsaye, wani makullin ya sake cirowa tare da buɗe ƙofar ɗakin ya zura kafafunsa ciki, yana haskawa, kasancewar ya ma fi falon duhu.

Haske ta yayi da fitilar wayarsa, ba tareda ya karasa inda take ba, ya ja ya tsaya daga bakin ƙofar yana ƙare mata kallo.

 

A zaune take, amma ta sanya kanta a tsakanin kafafunta, gashinta da ya gama cukurkudewa ya sauƙo ya rufe daga fuskarta har gwuiwarta kamar wata aljana, baka iya ganin furkarta sam, saboda irin zaman da tayi a cikin ɗakin mai matuƙar duhu.

Ƙarasowa yayi ga tsaya akanta kafin ya buɗe baki a karo na farko ya ce “keeeee” bata ɗago ba, sannan bata motsa ba, hannunsa yasa ya murza goshinsa, kafin ya zazzage ledan hannunsa a ƙasa, wanda da alama yayi watanni babu shara, allura ya zaro ya haɗa, kafin ya saka handgloves a hannunsa, gashin ta ya kama ya ja da ƙarfi, wanda ya bashi damar ɗago fuskarta, amma sai gashinta ya sake rufe mata fuska, ba tare da ya damu ba ya kama, hannunta, wanda ke ɗauke da fararen yatsunta, ya zirara mata allurar, a hankali, ta soma buɗe idanunta, kafin ta soma motsa hannunta, miƙewa yayi, cikin murya mai amo ya soma magana ” ga abinci kici, ga ruwa, idan kinaso zaki iya barinsa anan, saboda i have nothing to do with that, but alƙawarin da nayi ma kaina sai na cika shi at all means”

Daga haka ya juya ya fice tare da rufe ƙofar da makulli, tanajin ya fice, tayi saurin janyo abincin da ya tura mata gabanta, acikin duhun ta soma ci kamar zautacciya, tana ci tana shaƙewa, saboda kukan da take rerawa”.

Yana jinta amma hakan bai sashi waiwayowaba, ya fice tare da rufe gidan gabaɗaya ya shige motarsa tare da barin unguwar ma gabaki ɗaya.

Har ya iso gida, bai daina tsirtar da yawu ba, yana jin duk duniya babu wacce ya tsana irin ta, kuma ya ma kansa alƙawarin ɓatar da ita har abada.

Parking space ya nufa, a hankali ya gyara parking ya ziro kyawawan kafafunsa, masu ɗauke da yatsu masu matuƙar ban sha’awa daga motar bayan ya kashe ta, cikin tafiyarsa ta isa da matuƙar izza da kuzari ya nufi cikin gidan, duk da aransa yana jin ƴan wahalan har yanzu suna zaman jiran dawowarsa.

Kamar kuwa yadda ya yi hasashe, a falo ya same su, ga baki ɗayan su fuskarsu babu yabo babu fallasa,

Ciki ciki yayi sallama, ta yadda bayi da tabbacin wani acikin su ya ji shi, bai bi ta kansu ba ya nufi sama.

 

“Stop right there!”

Ya ji an faɗa a bayansa wanda yana da yaƙinin yayansa hamza ne, ba tareda ya bi takan abinda hamzan ya faɗa ba, ya sake cigaba da tafiya, uncle aminu ne ya sha gabansa yana faɗin

 

“Ba ka ji me yayanka ya faɗa ba? Ko bai kai ya dakatar da kai ba?, iyakar mu kake so ka nuna mana kamar yadda ka saba? Ina tambayar ka?” ya faɗa tare da hankaɗa kafaɗar sa, ko gezau bai yi ba, sai idanunsa da suka kaɗa suka sakeyin jajur,

 

“Me ka mayar da mu mutanen banza? Muzo wajenka dan mu gana da kai ka sauko ka ganmu, sai ka fita ba tare da kace uffan ba, sannan ka dawo zaka sake hayewa sama, wato ga ƴan iska koh? Kai waye, me kake jin kanka?”uncle Muhammad ya karasa fada ransa a mugun bace kasancewar yafi dukkansu zafi.

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Har lokacin bai da alaman zai furta wata kalma, sai ma lumshe idanunsa da yayi yanajin wani mugun raɗaɗi a zuciyarsa

Hamza ne yayi ƙwafa yana kallon uncle muhammad cikin magana da ƙarfi ya ce “Dad ka gani koh na faɗa maka wallahi ba zai ce mana ƙala ba, uwarsa ce ta koya masa duk wannan halin, gaba ɗaya”ya faɗa yana huci tare da kallon sa har lokacin yana tsaye ƙiƙam, sai dai wannan karan yayi folding hannayensa a ƙirji yana sauraron duk abinda suke cewa, jin Hamza ya ambaci umminsa yasa ya ɗago da mugun sauri ya dube sa, “ƙarya yayi ne? Uncle Aminu ya faɗa yana kallonshi , a yanda idanunshi suka kaɗa sukayi jajir wallahi har tsoro zasu baka, jikinsa har wani ɓari yake, cikin jin ɗaɗin zai tanka Hamza ya sake faɗin “Oh sorry, the mistress ya kamata ince, dan na tabbata tana can tana cin mazan mutane, matar da ke zaman kanta, waya sani ko kaima abinda kake yi kenan shiyasa ka keɓe kanka, ka rabu da family house ka dawo gidanka kai kaɗa……” Kasa ƙarasawa yayi jin numfashin shi na shirin rabuwa da gangar jikinsa, sakamakon wani irin shaƙa da ya mai, ya haɗa shi da bangon ɗakin ya shaƙe da iya ƙarfinsa, zuciyarsa har wani racing take yi, handkerchief ɗin da ya sa ya toshe fuskarsa da shi ne ya zame ya dawo ƙasan wuyansa, ya subhanallah wani irin kyakkyawa ne, wanda ko me za ka kalla a jikinsa sai ya matuƙar baka sha’awa, tun daga idanunsa da sukayi mugun ja, wanda kana gani kasan ba asalin kalarsu ba kenan, zuwa dogon hancinsa, da lips ɗinsa da sukayi masifar pink suna rawa tsabar bacin rai, har zuwa cikakken gemu da sajensa baƙi siɗik da ya ƙara ma fuskarsa wani irin jahilin kyau da kuma cikar kamala, har zuwa hannayensa da ya sa ya shaƙe hamza da su masu ɗauke da wasu irin yatsu masu matuƙar birgewa.

In a very shaky voice ya buɗe baki yiya ma Hamza magana cikin warning yana ƙara shaƙesa da iya ƙarfinsa, “Don’t you dare, stay in ur limit, ummina……” Sai kuma ya kasa ƙarasawa bakin sa ya shiga rawa sosai, Hamza da yaji ƙamshin lahira, idanunsa duk sun firfito waje gabaki ɗaya har wani yawu yawu yake

“ABDUL JALEEL” uncle Aminu da uncle muhammad da ya ga ana ƙoƙarin hallaka masa ɗa suka shiga kiran sunan sa dan da alama baya cikin hayyacinsa, “kashe shi zaka yi? Baka da hankali ne JALEEL, ka sake shi na ce” sam babu alamar ma yana jin su dan yanda jikinsa gabaɗaya yake rawa, da ƙyar suka iya raba shi da wuyan Hamza, wanda zuwa yanzu yake ƙoƙarin shurawa, wani wawan mari uncle Aminu ya sauƙe mai a fuska, yana faɗin lallai wuyanka ya isa yanka, ba shakka Asiya ce ta raine ka, to bari kaji dan uwarka ka faro abinda bazaka iya ba, kuma mun baka nan da wata bakwai (7) ka nemo mata muyi maka aure ko kuma kaga mata a gidannan, dan wallahi baka isa kana yawo kana fasiƙanci da yaran mutane a garinnan ba, kana ɓata mana suna, idan mu baka jin tsoronmu sannan baka ɗauke mu komai, to tabbass zaka ji kira daga mai kankat wato mahaifinka UMAR kuma na tabbata kasan haduwarku da shi, dan gwara mu mara mutuncin yaro, ɗan iska,”

Daga haka ya kama hannun Hamza da uncle Muhammad ke bama ruwa ko ta kansu bai bi ba, idanunsa sunyi jajir suka fice a gidan gabaki ɗayansu suka barshi nan tsaye.

 

 

 

 

Ku nuna ƙaunar ku akan wannan littafi, ya banbanta da sauran, akwai rikici mai ƙara rikitar da ƙwaƙwalwa da rikita-rikitar soyayya me rikitar da tunani ita ke wanzuwa a cikin sa.

Kudai ku cigaba da bin mu.

Yanda kuka karbi labarin shi zai bani dama da ƙarfin gwiwar cigaba.

 

Don’t forget, share and comment.

 

# Maimoon ce.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.