Banida Gata Hausa Novel
Banida Gata
Garin ya yi luf-luf cike da ni’ima. Ga wani ‘dan sanyi-sanyi da ke busowa gami da k’amshin k’asa sakamakon hadarin da ya ha’du sosai, ko wani irin lokaci ruwa zai iya tsugewa. Gefe guda kusa da wani tarin bola da ta yi tsini, wata kyakkyawar yarinya ce da bazata wuce ten years ba du’ke a wajan sai rawar d’ari ta ke yi sakamakon wannan hadari da ya taho da iska da kuma sanyin da ke biyo iskan.
Gashi ba wani kayan arziki ba ne a jikin wannan yarinya da ko ‘dan kwali babu a kanta sai uban tulun gashin da ya zubo har kafa’dunta. ‘Yar ‘karamar shimi (vest) ne a jikin ta, sai wani kod’ad’d’an wando da ya yayyage ta wajan d’uwawunta da kuma guiwar wandon. Shi kan shi wandon iya k’aurin ta ya tsaya. Ha’koranta har ha’duwa su ke da juna saboda tsabar sanyin da ta ke ji, gashi kuma da ma da d’an zazzab’i a jikin ta.
Banida Gata
Ruwa ne ya kece kamar da bakin kwarya. Cikin abunda bai fi minti ‘daya ba wannan yarinya ta ji’ke sharkaf. Da gudu ta mi’ke ta yi bayan wannan tulin bolan da ke cikin wani rusassan kangon da kad’an ya ke jira ya gama zubewa sakamakon wannan uban bola da ake zubawa a wajan.
Inda baiwar Allahn nan ta koma bai hana ruwa dukanta ba, domin babu wajan da za ta gujewa ruwan a wajan. Haka nan ta cigaba da tsugunno a wajan kusan kimanin awa biyu kamin ruwan nan ya tsagaita. A wannan lokacin kuwa har kakkafewa take yi saboda tsabar sanyi. Gashi magriba ta gabato.
Ta na nan kwance a wajan ta soma jin takun tafiyan mutane ga dukkan alamu masallaci za su je. ‘Dan le’ko da kanta ta yi ta wani ‘dan huji ta na kallon mutanen da suke wucewa ta na addu’ar Allah ya sa ta ga Hamdan. Addu’an ta ya kar’bu, sai dai kash! tare su ke da ankul ( uncle) Saban (Sauban) kamar yadda ta ji Hamdan ‘din na kiran shi.
Banida Gata
Ajiyar zuciya ta yi tare da komawa ta lafe a wajan kasancewar ta riga da ta ha’kura da abincin yau. Wasu siraran hawaye ne su ka Shiga zirarowa daga idanunta. Bayan hannunta ta saka ta share tare da fa’din.
Allah ni ba ka bani mama da baba ba kamar kowa. Ni bola ce ta haife ni. Kuma bola ba ta ba ni abinci mai kyau, ba ta kai ni makaranta, ba ta saya min kaya masu kyau, kuma bata wanke min jiki na. Mutane ba sa sona.
To meyasa ni ma ban zama bola ba kamar yar da mama na ta ke? Mutane haka suke kira na ‘yar bola, kuma wai *BA NI DA GATA*, Allah ni ma ka mayar da ni bola kamar yadda mamata take ni ma nai ta girma kamar ta. Kowa ba ya sona, Hadaan (Hamdan) ne kawai ke so na. Shike sammin abinci daga gidan su.
Banida Gata
Shi ya kawo min wannan kayan ma da ke jiki na. Allah ni ma ka mayar da ni bola kamar mama saboda mutane su dai na gudu na”. Ta fa’di hakane ta na kuka, domin a nata wautan bolan da ke wajan ita ta haifeta, ita ce uwarta, ita ce ubanta. Saboda kuma jama’a na kiran ta *Y’AR BOLA* sai ta ke ‘dauka ai bolan ce mahaifiyar ta. Ita kullum burinta, ta zama bola don ta yi magana da mahaifiyar ta suma su koma gidan su.
Har an idar da sallah, kasancewar had’a sallah aka yi, tunda kowa ya shige gida sai garin yai tsit. Gashi dama ruwan ba d’aukewa ya yi gaba d’aya ba. Har yanzu ana yayyafi kuma alamar ruwan sake tsugewa zai yi. Don irin ruwan nan ne da ake kwana ana tsugashi.
Tun ta na ri’ke ciki ta na kukan yunwa, har bacci yai gaba da ita anan wajan sauro na zu’kan jinin ta. Can cikin baccin ta taji ana dukan k’afafunta a hankali tare da kiran sunan ta, wanda Hamdan ne ya ra’da mata sunan wato binty (beauty). Beautyn ne ba ta iya kira ba ta ke cewa binty. A da idan wani ya tambaye ta miye sunanta, cewa ta ke yi *Y’AR BOLA* kamar yadda ta ji mutane su na fa’di.
Idan aka ce mata *Y’AR BOLA* ba su na ba ne. Sai ta ce Binty (beauty) a hankali ku ma sunan na ta ya koma Binty, wasu kuma su ce Binty *Y’AR BOLA*.
.A hankali ta ke bu’de idanuwanta har ta bu’de shi tas a kansa. Duk da akwai duhu ta shaida shi, domin karfe tara ta wuce na dare. Hannu ta kai ta shafi fuskan shi tare da fa’din,
“Hadaan (Hamdan), ina ta jiran ka yunwa na ke ji. Na gan ka za ka sallah kai da ankul Saban, har na cire rai zaka kawo min abinci”.
“Beauty ni ma hankalina na kan ki, ina ta so na fito, amma Mummy ta ki barin sitting room balle in samu in fito in kawo miki food ki ci, now wash your hands with this detergent and water before eaten, it’s a very good hygiene. Understand?”. Fa’din wani kyakkyawan farin yaro da ba zai wuce 13years ba.
Banida Gata Hausa Novel
Ita dai Binty (Beauty) ba ta san mai ya ke cewa ba, ‘ko’karin ta kawai ta ‘karbi take awayn dake hannun sa. Shikuma yak’i ba ta wannan damar.
.”Hey! Easy mana beauty. Zan ba ki, amma firstly sai kin fara wanke hannun ki saboda gudun cuta. Our teacher always tells us to wash our hands before and after every meal. Saboda haka, ga ruwa da detergent nan, ki wanke hannun ki sai in baki Irish and plantain ‘din ki ci”.
Ya fa’di hakane tare da jawo hannun ta ya zazzaga mata detergent ‘din tare da ruwa. Sai da ya sata ta wanke hannun sau bakwai, ka na ya mi’ka mata takeaway ‘din tare da fork na roba. Cikin sauri ta kar’ba ta soma cikin. Shida-shida ta ke ta ha’dawa har ta cinye tas. Ka na ta yar da cokalin tare da saka hannu ta su’de robar tas, sannan ta yar tare da sakin k’atuwar gyasa ta koma ta kwanta a nan ‘kasan wajan ta na mayar da numfashi.
Banida Gata Hausa Novel
“Imaging! How can a human being live and survive here, Allah na gode maka da ni’imar da kai min”. Hamdan ya fa’di hakan ya na mai ‘karewa beauty kallo cike da tausayi da har bacci ya soma ‘daukar.
“She’s very beautiful with long hair. Who must be her parent? Why is she all alone in this garbage? Da ni babba ne da na ne mo mata iyayan ta ita ma ta rayu da su kamar ni da Mummy da Appa”. Hamdan ya sake fad’i ya na shafa dogon gashin da ke kanta da ya yi dak’an-dak’an har cukurku’dewa ya yi ya na so ya koma dada.
Ganin da yai ta yi bacci sosai, sai ya fiddo bedsheet a cikin ledan da ya zo da shi ya rufa mata tare da kunna mata maganin sauro da lighter, duk da yasan babu abunda maganin zai kare mata, don ko kamfanin *SUPER KILL* aka saka a wajan ba zai hana sauro cizon ta ba. Don sauran zamanin yanzu, ka na jan bargo suna ja.
Kamar zai yi hawaye ya mi’ke tare da barin wajan ya lallab’a ya tura get ya shiga gidan da san’da har ya shige ‘dakin sa tare da hawa gado ka na ya saki ajiyar zuciya tare da fa’din,
“Thank God, nobody saw me”.
*ℍE ℝ*
.Sai da rana ta fito sannan Binty ta farka tare da sakin mi’ka gami da doguwar hamma. Gashin da ya barbazo ya rufe mata fuska ta mayar da shi baya tare da janye zanin gadon da Hamdan ya lullub’eta da shi ka na ta mi’ke tsaye.
Banida Gata Hausa Novel
Idanuwan ta ne ya sauka akan pure wata guda uku da brush da maclean a kan wani bulo. Wajan ta nufa domin ta san Hamdan ne ya aje mata su a wajan, domin ya ce a kullum ta tashi da safe ta ri’ka alwala tare da wanke bakin ta da brush, don har koya mata yadda ake brush ‘din sai da ya yi. Brush ‘din ta fara yi ka na ta yi alwala ko in ce shirme. Domin ko alwalar ba ta iya ba, balle a kai ga zancan sallah.
.Bayan ta gama alwalar da brush ‘din, ta zo ta hau kan wannan zanin gadon ta soma sallah haka nan ko ‘dan kwali babu a kan ta sai buyagin gashin ta. Dunguran-dunguran banza tai ta yi. Domin sallar daga sujada aka fara, sannan aka d’ago a kai ruku’u ka na aka k’ara tafiya sujada. Haka tai ta dungurawa har ta kammala kusan raka’a goma. Fitowa tai tare da hawa kan bolan nan tare da fa’din.
Banida Gata Hausa Novel
.”To mama, zan tafi in nai mi abincin da zan ‘karya da shi tunda dai bakya sona. Na san Hadaan ya tafi makaranta, ankul Saban ba zai barshi ya kawo min abinci ba. Zan je na nai mo da kai na”. Ta na gama fa’din haka ta soma saukowa daga can saman bolan. Kallon gyefan daman ta ta yi, idanuwan ta suka sauka akan wani tsoho tukuf, gashin sa fari fat har kafa’da, hannun shi ri’ke da sandar da ya ke dogarawa, ya na mata murmushi. Cikin sauri da wani irin zumu’di ta ‘karisa wajan shi tare da fa’dawa jikin sa ta ruk’unk’ume shi tare da fa’din,
“Kaka!” Sai kuma ta fashe da kuka tare da ‘kara rungume shi.
Shafa kanta wannan tsohon ya yi yana murmushi tare da fa’din,
“Haba Bintyn Hadaan! Mi ye na kukan? Ba ga ni na dawo ba”.
“Guduwa zakayi ka sake bari na a nan, babu wanda ke sona. Yara su na tsokana ta, ba na samun abinci, Hadaan ya je makaranta. Yanzu ma ban karya ba”. Fa’din Binty.
Banida Gata Hausa Novel
“Ki yi ha’kuri Binty, ko mai ya yi tsanani ya na tare da sau’ki. Wannan waje da ki ke, shine kad’ai mafita a gare ki. Yanzu duk bayanin da zan miki, ba za ki ta’ba ganewa ba don kwakwalwar ki ba za ta ‘dauka ba. Amma ki yi hak’uri. Ina mai tabbatar miki maki’yan ki sai sun rusuna a gaban ki. Sai kin zama filita mai haskakawa. Ki yi hak’uri ki daure ki ci jarabawar ki. Tun da har Allah ya raya ki a cikin bola tun ki na ‘kan’kanuwar ki har izuwa yanzu, to lallai Allah ya na so ya nunawa magauta ishara da Isar sa ne.
Lallai ubangiji shine ke rayawa da kashewa”.
Sam Binty ba ta fahimci ko kalma ‘daya daga cikin maganganun kakan na ta ba. Sai ma jefa masa tambaya da ta yi.
“Kaka yaushe zan zama bola irin mamana kowa ya dai na tsana ta?”.
Murmushi wannan tsoho ya yi tare da fa’din
“Binty na, ba za ki zama bola ba, sai dai in sha Allah za ki zama abun kwatance a cikin al’umma, tabbas sai ma’kiyan ki sun duk’a a gaban ki. Tabbas idan rana ta fito tafin hannu ba zai ta’ba iya kare ta ba Binty na”.
“To kaka yaushe ne ranar zata fito? Kuma yaushe ne zan zama abun kwatance?”. Binty ta kuma jefa masa tambaya.
“Ranar na nan zuwa Binty na. Ki je Allah ya albarkaci rayuwar ki. So na ke ki yi gwagwarmaya, ta yadda nan gaba ko mai zai zo miki da sau’ki”. Fa’din Kaka.
Banida Gata Hausa Novel
“To kaka, bari na je na yi bara na samu abinci yunwa na ke ji”.
“To Binty na, Allah ya sa a da ce”. Ya na gama fa’din haka Binty ta bar jikin shi tare da gangarowa daga kan bolan. Sai da ta sauko gaba ‘daya ta ‘daga kanta sama, wayam ta ga ni a wajan. Ko alamar kaka ba ta gani ba. Murmushi ta yi tare da fa’din,
.”Kaka ya ‘kara guduwa ya bar ni”.
Pingback: Hausa Novels Littafan Hausa Guda 10000 Masu Dadi JIKI NA YAKE SO COMPLETE HAUSA NOVEL | My Novels
Allah sarki binty mahakurci mawadaci
Please I need a complete novel please
Please when did next page will be release?
dan allah taya zan samu cplt nashi
Which market will get a complet one pls
Pingback: Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta | My Novels
Please I need a complete novel please