Banida Zabi Hausa Novel Complete

Banida Zabi Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Banida Zabi

Zaune take bakin rijiya bayan ta janyo ruwa ta cika buta , hannayenta bibiyu ta dafe kuncinta tana duban daidai kofar gidan, yar datijiwa ce zata kai shekara arba.in da dori, gaba daya yannayinta yannayin cikin damuwa take domin lafiyar kirki ma bata da ita

 

 

 

A hankali take takowa har ta karaso kusan wannan mata ta tsuguna a kusa da ita, ta ce” INNA ki tashi ki yi alwallar kin saba yi da wuri kinga kina zaune har an fara kiraye kirayen sallar magaribar shi kuwa a makaranta malan ya ce a gagauta shan ruwa a jinkirta yin sahur

 

 

Dago da kanta tayi ta sauke kwayar idannuwanta masu wani irin kala tamkar na mage saman yar tata, ajiyar zuciya ta sauke ta ce” Aisha shin da kika je baki cewa Uwa ni nake nemanta ba?

 

 

Wace aka kiraya da Aishar ta furzar da iskar takaici ta ce” Inna na fada mata, aman bara na koma ko wani abin ne ya rike ta

 

 

Kai ta kada tana kokarin mikewa ta ce” kiyi sallah tukunnan, ba kyau tarban magariba,

 

Haka ta shige bayin nasu na laka wanda yayi kasakasa sosai aman an saka wani yadi an rufe shi bazaka hango na ciki ba

 

 

 

 

Uwata kika zaga? Ke Binta kin san na fiki rashin mutunci ko gaban babarku sai na bi ki na daki banza, na yi maki kashedi kula Hamza, ke har kin isa saurayin fa nace bana so ke ki so shi? Ai Hamza ya kade sai dai ya fita ya auro wata ba dai a nan layin ba, shi ne dan na fada zaki ce wai idannuwana girma tamkar na mujiya kwayar ciki sai kace kalar na mage??? Ni? Ni jarin…

 

 

Kau kake ji an dauketa da mari, tana dagowa ta ga yayansu ne Abdul fatah, ai kuwa ta nade hijabinta ta artaya a guje ,,

 

Dubansa ya kai kan Binta dake yashe a kasa tana share hawaye, ya kada kai ya ce” ki tashi ki yi hakuri kin ji???

 

 

Binta ta danyi murmushi ta ce” ba komai Abdul Fatah daman bata fahimci zancen bane kuma sai Anasiya tace da ita wai na zage ta

 

 

Kai ya girgiza ya juya ya bi bayanta

 

Tunda ya shigo ya kasa ya tsare yana jiran ta gama sallar da ta kabarta a dakinsu ita da kanwarta, aman kamar mai sauke alkur.ani a cikin sallar bata da alamar gamawar shi kuwa baya so yayansu Hamza da Babansu malan Laminu su shigo su hana shi yi mata dukan mutuwa

 

 

Juyowa yayi wajen mahaifiyarsu, ya karaso ya zauna a kusanta yanai mata barka da shan ruwa

 

Cike da kulawa take amsa masa ta tura masa kankanar da ya shigo mata da ita tsarabar yan azumi,

Kalon yannayinsa take ta ga sai shan mur yake tayi dan murmushi dan ta san kwannan zancen bazai fice Kanwarsa ta tabo shi ba

 

Asalamu alaikum warahamatulah

 

A tare suka dago suna amsa salamar Malan da ya shigo da carbinsa , ya gama jan salar isha.i kafin ya karaso gidan, bayansa kuwa yaya Hamza ne rike da dardumarsa

 

Yana zama dadaya suna gaishe shi Inna ta mike tana gabatar masa da kayan buda baki dankalin hausa ne ta dafa ta yanyanka danyen tumatur da yar albasa sune mahadinsa

 

Budewa yayi yana murmushi yana yi mata sannu, aman bai ga *WUJDANE* ba

 

Dubansa ya kai wajen Aisha, a hankali ya ce” MAMANA, shin ina yayarki ne? Ko bata shigo gidan ba??

 

Inna ta juyo ta juyar da kanta tana sauke ajiyar zuciya, bata ce komai ba, AISHA ta mike tana fadin ” bara na duba Aba ko ta gama sallar? Tana nan

 

Cike da murmushin yau ta dawo gidan da wuri yake fadin “Masha Allah,

Sannan ya bi Abdul fatah da kalo ya mike yayi gaba cike da fushi can cikin ransa yake yiwa yayan nasa gaba daya adu.ar shiriya

 

 

A hankali ta fito cikin hijabin nata baki wanda ya tsufa iya tsofewa sosai, ta karaso ta duka kusa da mahaifin nata cike da ladabin karya kanta a kasa tace” barka da shigowa baba, an sha ruwa lafiya???

 

Yana murmushi yake amsa mata da” lafiya lau WUJDANE ya gida, na same ku lafiya?

 

Cikin nutsuwa take amsa masa

 

Ya dago yana hangen fuskar Innarsu, ya ce” Allah ya shirye ki Wujdane , Allah ya kara nutsar min da ke kin ji?

 

Inna ta juyo cikin yannayin sanyin nata ta ce” uhum, Malan nutsuwar munafurcin?

 

Kallonta yake yana salamar yaren dan baya son suna irin wannan maganar a gabansu

 

Bayan sun tafi ya nisa yana kallonta ya ce” ba sai na tambaya ba yauma tayi halin, aman da sauki tunda ban tardo ana jirana a kofa ba, sannan ina tsakar ganawa da iyalina ba.a katse ni ba, Fatima Allah yakan jarabtar bayinsa ta hanyoyi daban faban dan ya auna imaninsu, idan sun yi hakuri sun jure sun kawar da kansu sun mika lamarinsu wa shi , zai wanke masu zukatansu, Kaf cikin yayanmu ba wanda ya kai *WUJDANE* konya, aman karatun bokon ya gagara ke kin san na islamiya ba.a rabarta cikin ikon rabah tana da konya, wannan halaya na yau da kulun wanda na sani koda namiji ne sai hankalinmu ya tashi bare a mace, sai mu dauka tamu Salon jarabawar kennan, mu bi ta da adu.a Fatima sai Allah ya shiryar mana da ita

 

 

Inna ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce” malan, ai *BANI DA ZABI* , aman ina tsoron rayuwar WUJDANE, ke mace ? Macen ma mai rauni sosai? A shekarun Wujdane goma sha takwas da doriya yaci ace tana gidanta aman du ba wannan fitinar nan ita ta saka a gaba ya zamu yi???

 

 

Malan ya lumshe idannuwansa ya ce” ADU.A, ita zamu ci gaba da yi, jinkiri ba kin amsawa bane, Allah ya shiryar mana da ita ya bata miji na gari

 

 

 

Ka.ida ne, karfe hudu na bugawa Wujdane zata bude idannuwanta , ita zata bi dakunnan yan uwanta du ta tashe su daga baci dan su fito balbalin gidan nasu su yi karatu kafin lokacin sallar asuba su tafi masalaci su kuwa su yi sallah su yi zaman azkar

 

Yauma hakan ta faru, zaune suke suna karatu kowa a hankali Malan na gefe shima ya bude alkur.aninsa Inna na zaune itama rike da carbinta tana ja

 

 

Wujdane ta juyo tana kallon Innarsu, juyawa tayi ta maida kanta wajen mahaifinsu ta ce” Baba, ni mai yasa inna bata karatun ne,?

 

Dago da kansa ya yi yayi mata nuni da ta maida hankalinta kan karatun ba tare da yayi magana ba, hakan ya saka ta mayar da kanta bata ko lura da irin hararar da Abdul fatah ke watsa mata ba

 

 

Safiya na yi ta fito ta shiga aikin tsakar gidansu, Wujdane akoy kin ji aman kuma shegiyar tsafta tamkar wata mai aljannun tsafta,

 

Yaro ne yayi salama karfe goma na safe ya gota,

Yana gannin Wujdane ya dan rabe yana raraba idannuwa dan tsoro

 

Dago da kanta tayi bayan ta kwashe shara ta wurga masa harara ta ce” shege mai kai tamkar duniya, ubanme kuma kake nema a gidan da safiyar nan? Anzo a ga yau mun samu abin karin ne ko aa ko???

 

Jikinsa ne ya fara bari yana kallonta ya ce” Mama, ( sunnan da ta dorawa du yaran anguwar nan cewar koda wasa shegen da ya kirayeta da sunnanta sai ta karya masa wuya, tsabar balakinta ya saka yaren dake kiran sunnayen iyayensu ma idan suka hadu da ita sai kaji sun ce *mama* dan idan ka fadi sunnan nata har gaban mahaifiyarka zata bika ta daki banza), yaci gaba mama yaya sule ne ke magana a kofa

 

 

Ido ta zaro a fili ta ce” Kan Uba, da safiyar nan ubanme yake nema a kofar gidanmu? Ai kuwa yau zai san bashi da wayo

 

Saurin saka hijabinta take dan ta fita innarsu kuwa na kokarin fitowa da sauri dan ta tsayar da ita

 

Har ta saka kafa guda a zauren gidansu ta ji muryar inna na fadin” *WUJDANE WUJDANE!*

 

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.