Bariki Gadona Hausa Novel Complete
Tag: Bariki Gadona Hausa Novel Complete
_(Gado nah)_
Book 1
Page 1&2
Oum Aphnan
Bismillah!
_Gargaɗi_
Ban taɓa zagi akan littafi ba ,Amma bana duk wacce ta karanta mun littafi bata biya ba ,ko aka ɗaura mun Littafi a wani shafukan sada zumunta ko utube mutum shi da Allah. Don haka in kinsan zaki siyane don ki ba ƙawarki kawai na hutar dake karki siya,haƙƙin mallaka nane naki karantawa.
_Paid Book_
Regular 300#, Vip 500# , Special 1000# via Hassana Mohammad 7782217014,Fcmb or wxp dix Number 09065990265
_Laraba,2pm._
“Malam kaiwa darajar tsohuwar ka ,yau dai ka barni in shiga Dan girman Allah!,makona uku kenan ina sintiri ka hanani shiga”
Wata wahalalliyar mata da a ɗebe zamu bata shekaru 25 da haihuwa amma tsabagen wuya,duba da yanda bakinta ya bushe ya tsage yina fidda jini ta tsakiyan leɓenta na ƙasa,ga hijabinta tamkar anci wasar sallah akai,ƙafarta sai kace wacce ta kewaye Nigeria da ƙafa,ya daddare da faso gashi yayi buɗuɗu, Kallon Farko sai an bata shekaru Arba’in . Haka ta manne a jikin ƙarafunan get ɗin ta kakkama tana cigaba da roƙon sikyuritin dake jingine da get ɗin wajen ,saidai tamkar baisan tana magana ba ,sai latsa baby Nokiar wayarsa yike . Alamu dai ya nuna inda sabo ya saba da Nacinta
Sarewa da roƙonsa tayi ,don haka taja wata doguwar Ajiyar zuciya ,saiga hawaye masu raɗaɗin fita suna gangaro mata a dakalin kuncinta
“Ya Allah,Ya Sarkin da kayi talaka kayi mawadaci ,kayi mugu kayi wanda ake zalunta Ubangiji na,ka kawo mun wanda zai tausaya mun ,ya dubi rauni na ya Rabbb” wani shasheƙane ya sarƙeta maganar ya daina fita kawai sai ta haukace da tarin Azaba saboda yanda numfashinta ke barazanar ɗaukewa a ƙirjinta.
Alhaji Saddam Mamman Tamkar wanda aka tsikara ya kalli agogon dake manne a katafaren office ɗinsa, zumbur ya miƙe ganin lokacin azuhur ya shiga ,yina fitowa daga ofishin sa kuwa ma’aikata dake dakon jiransa ,suka dafe masa baya ɗuuuu sukayo waje ,zasu nufi masallacin dake ta bayan wajen .
Har zuwa lokacin bata fasa tari ba ,ga idanuwarta sun duddulo waje sun jajir tsabagen Azaba .
Alhaji Saddam dakatawa da tafiya yayi sannan ya ƙwalawa securityn kira
“Malam Tukur!”
Zumbur yayi ,sannan ya yi saurin jefa wayar a aljihu ,ya amsa a furgice ,sannan ya waigo inda take yana mata alamar gargaɗi da yatsa.
“Dakata!,meke faruwa ne anan wajen?”
Sunkuyar dakai yayi ,ya ɗanyi gungunan maganar da baza’a taɓa fahimta ba
“Shikenan ban son jin komai a buɗe mata ta shigo”
Ji yayi kamar kar yabi umurninsa amma ya ya iya?
Buɗe mata get ɗin yayi ,aikuwa cikin bala’in gudu ta shigo harabar tana cigaba da tarin taje ta zube a gabansa
“Yallaɓai kayi mun rai ka ceceni kasheni zai yi ,kwanakin mutuwa na a ƙiddidige yike yau saura kwana biyar!!!”
A mamakance ya ɗan kalli gabansa da ta turmusu, ya ɗan tattare giran sama da ƙasa
“Baiwar Allah tashi tsaye ,ban fahimceki ba ,waye zai kashe ki ɗin”
“Mijina ne yallaɓai, mijina ne ”
“Mijin ki?!” Ya tambaya a mamakance
“Eh,wallahi da gaske nike ku taimaka mun,Allah shine mai hukunci ,amma kuna taimako,ku taimaka mun kune ƙarshen fatana ,idan kuma baku taimakeni ba,to zan haƙura zan koma maƙabarta da kwana har zuwa ranar mutuwata don nasan tsimayinta nike!”
Kallon wani ɗan sanda dake gefensa yayi “A bata ruwa da Abinci ta natsu muna dawowa daga sallah”
Yina gama bada umurnin ya ɗauki hanyar masallacin ,ya daɗe rabon da yaci karo da irin mutanen nan ko don yakai ƙololuwa ne oho!
****
Bayan minti Arba’in
Tananan zaune yasa aka kirawo ta ,jikinta ko na azaban rawa ta bi bayan massenger Alƙalin
Karanta Littafin Kuruciya Hausa Novel
“Baiwar Allah meye kuken ki?”
Hawaye ne ya cigaba da mata Ambaliya a fuska ,da ƙyar take basa bayani cikin azaban raunin ta ,tsam da rai yayi ,kafin ya umurci massenger ɗinsa da ya kira wanda zai rubuta ƙaran ,sai a kai ma mijin nata sammacin kotu
“Baiwar Allah meye sunan wanda ake ƙaran?”
Shiru tayi ,ta ƙi magana
“Malama ,faɗi sunan mijin naki” cikin sadaƙarwa da raunin murya tace
“Alhaji Sallau Achisu ,Inkiya MAYE!”
Ai bata rufe baki ba ,fuskokin kowa na ofishin ya sauya.,mai rubuta ƙarar a hanzarce ya kekketa takardan Hannunsa
“Wannan matsalar ku ce ta cikin gida Malama ,bazaki tsoma rayukan mutane da yawa a watangariri ba ,tashi ki fita!!” Ya daka mata wani mugun tsawa ,wanda saida taji kamar zata tsullo fitsari a wando
“Me yasa zaka koreta ehem muntari?,A taƙaice ma me ta faɗa da zafi daya tunzura ka?”
“Ranka shi daɗe ,MAYE fa kaji ta ce shine mijinta? Maye fa ,mutumin da ko tsuntsu ya gifta ta inuwar garden ɗinsa kwanansa ya ƙare ……yallaɓai case ɗin matar nan sanannen case ne da ta saba zaga kotuna da ofisoshin ƴan sanda da dama a ƙasar nan kuma kokenta ɗaya shine Su raba mata AURENTA da maye……Amma saidai duk mutumin da ya karɓi ƙarar a ranar baya kwanan duniya !! ,Nikuma a gaskiya ban shirya maida yarana marayu ba ,Matana bazawarai!!…”
Tsam ta miƙe jiri da hajijiya na kwasarta ,a ranta tana Ayyana nan ɗinma babu Nasara,har ta fice ta nufi harabar kotun ,sam bata damu da Muryar dattijon da yaso taimakonta ba dake faman ƙwalla kiran “Baiwar Allah”
A daf da get taja ta tsaya saboda get ɗin da aka kware ma wata ƙatuwar mota ƙirar prado Baƙa da baƙar tint,cak ta tsaya tana jiran su shige ta fice
“BEEEE!!” Wani zabura tayi ta fara waige² tana son ganin ta inda zata mutum ɗaya jal a duniya dake kiranta da Wagga suna
A hankali aka buɗe murfin motar ,wani Ingarman namiji ne ya fito ma’abocin choco skin cikin Black suit da sukayi bala’in kwanciya a jikinsa
Cikin Izzah wanda ya gama bin jinin jikinsa ya ja ya kwanta a jikin motar sannan yasa hannu ya ɗage baƙar shade ɗin da ya sakaye ƙwarar idonsa
Cikin dakuwar bugun zuciya ta nuna shi da yatsa
“SARKI ! …. ” Kawai sai hannunta ya fara rawa
Ko a jikinsa da halin da yaga ta shiga saima hannunsa daya nitsa a cikin sumar kansa ,cikin lallausar muryarsa yace
“Na’am MAKAMA TA!…Zo nan ”
Kallon kanta tayi tun daga sama har ƙasa ,bata taɓa zaton sak ta zama bata da banbanci da mahaukaciya ba sai yau,ina ita ina raɓar Sadiq a haka? ,aikuwa da sauri ta ciɓa ƙafarta tayi waje harda ƙarawa da gudu da sassarfa
“Ku bita kar ku bari ta ɓace” yina bawa yaransa umurni ya danna kai cikin kotun ransa na azalzalarsa
“Me ya kawo ta ?me take so?”
Tambayar da ya soma jifansu dashi kenan ,cikin rawar murya suka labarta masa mai ya faru da tarikhin waye shi mijin nata
Da ƙarfi ya dunƙule hannu ya daki tebur ɗin gaban alƙalin wanda yasa printer ɗin dake kai yayi tsalle ya faɗi gefe ya farfashe
“Zanci uwarka maye ,Sai na raba auren dan uwarka ,yau ina so in bar duniyar”
Abokinsa Yusuf fagachi da sauri ya zo ya dafa kafaɗarsa “Allah ya huci zuciyar yareeman mu,a bi sannu yallaɓai”
A zafafe ya juyo ya watsa masa Idanuwarsa da suka rine suka zama jajaye nan take
“Ina wasa da kaine Yusuf?”
Shiru yayi sannan ya sunkuyar dakai don ba ƙaramar aikin Prince Sadiq bane yanzu ya tsinke sa da mari batareda ya duba abokantakarsu ba.
“Allah ya huci zuciyar yareema” fuuu ya fice ,wanda suka zo tare suka dafe masa baya
Shikuma Yusuf fagachi lafewa yayi a jikin mota ya kwaɗawa Gimbiya Ramlah kira a waya
Ramlah da tashinta a barcin kenan tun da tayi break fast ko kayan barci bata cireba,wani mugun miƙa tayi ta saki Hamma ,sannan ta ɗan jawo wayar ta saki tsaki gamida ɓata fuska
Muryarta can ƙasa a dushe “Fagachi yadai? Ina mijina yike?”
Ɗan jan fasali yayi ,kana ya magantu
“Ranki shi daɗe ,ina tunanin yaufa akwai ƙura ,koda sarki ya dawo ki lallaɓasa don kafiyarsa da taurin kansa da ya sassauto shekarun baya da suka wuce ,to ina ganin ya dawo ,mutum na haiƙe masa yina iya fyarɗe sa,murus mutum zai shaiƙa barzahu ”
Zare ido tayi sannan ta dafe ƙirjinta da sauri kamar yina tsaye yina kallonta
“Yusuf? Kana haukane ? Yariman kake jifa da miyagun zantuttukan nan? Ni ban auri ɗan ta’addaba kar ka sake kiran min miji da siffofin nan,wani shashanci kenan ,kar kayi tunanin don yarimana ya kasance abokinka bazai iya maganinka ba…”
“Ki dakata ki saurareni ” ya faɗa a daidai sanda yike shiga motarsu
Tsaki taja ta kasha wayar tana cigaba da ƙunƙuni ,kafin ta fara ƙwallawa kuyangarta kira .
******
Yareema kam tun da ya shige mota ya manne fuskarsa da baƙar shade ɗinsa bai ƙara tamka kowa ba ,tunanin sa ya tafi wajen tuna Abubuwan da suka faffaru a baya ,har abada bai taɓa tunanin Bilqees zata tsinci kanta a kwatankwacin irin wannan Rayuwar ba.
Haɗe Hannuwarsa yayi waje ɗaya ya matsa da ƙarfi sukayi ƙara
“Ni na ja maki Bilqees inada nawa kamashon zunubin ,dole wannan gayen ya karɓi hukunci daidai laifinsa ,muzuba Ni Ko shi………….”
*Waiwaye…🚶♀️*
©Alheri Writers Association
*Filin Mu Tallata Hajarmu*
Kema zaki iya badawa a sanya maki tallar hajarki a pages ɗin littafina akan kuɗi 2k a page ,a status ɗina kuma 1k.
Mata kuna ina???
Ehem Akace in kin ji kira samu ne
*Hajja mai gyaran aure* ta taho maku da zafafan magungunan mata ƴan gaske,tafiyayyu maras Algus,iya kuɗinki iya shagalinki ,ko mijin ki bai saba ihu ba ,Alƙawarine wannan sai yayi , Magunguna na dai ,Akwai garurruka
Gumba
Tsimi
Tabaje
Jigida me matsi da niima
Jigida mai saka farin jini awarwaron farin jini da mallaka
Zobban farin jini da mallaka
Haɗin Ƴar gata
Zuma na musamman
Cicciɓi
Kaza dahuwar uwargida da amarya .
Ƴan shila
Haɗin kifi
Ɓata jikin Kishiya
Maƙale mata
Haɗin karya gado .da sauransu.
Mu ƙa’idar maganinmu bamu badawa sai mun maki bincike in baki da infection in kuma akwai sai mun maki magani
Hajiya ,maganina nagartattune an daɗe ana yabonsu ,kar in cika ki da zance wani abu sai kin amfani dashi wallahi sai kin kawo ƴar uwarki
Domin ƙarin bayani ki tuntuɓi wannan Numbobin 09060703187
Serious masu saya don Allah
*BARIKI*
_(Gado nah)_
Book 1
Page 3&4
Oum Aphnan
*Gargaɗi*
Littafina Na kuɗi ne ,ban yarda A ɗaukar mun a saka a kowata kafa ta yanar gizo ba.
_Gidan Makaman Gari_
Gidane Tafkeken gaske,Na dandaɓaryan ginin laka,amma an masa zanen gidan sarauta da Hannun magini Tundaga fuskar gidan har can sama wajen indaroron da yike fidda ruwan saman soron gidan musamman lokacin damina….., Gidane mai zurfin gaske da sai ka wuce zauruka guda tara masu tsananin duhuwa,wanda tsabagen duhu da rana sai an sakawa zauran tsakiya fitilar aci balbal. Gidane na dangi ɗaya mai ƙunshe da sasuka biyar ,wanda yafi kowanne girma nan ne sasan MAKAMA
Kaf gidan sasan Makamane kaɗai aka mulmule da sumunti ,akayi wa ƙofar ɗakunan matarsa biyu shaye a gaban ɗakunan su ,kaman varenda luwai da sumunti ,amma sauran tsakar gidan dandaɓaryar ƙasa ne tataaa iya ganinka ,sai ƙatuwar bishiyar mangoro da ta cika sassan da rassan ta wanda ya baiwa ilahirin yaran makama inuwa ,nanne wajen daka da sussuke nanne wajen shimfuɗa taburma aci abinci ko hira .
Ɗuƙe take a ƙarƙashin turken dokin makaman sai faman yankewa dokin farata take da abun datsewa ,gefenta munjagara ne ta kwashe rankatakaf dattin dokin ta tara a gefe ,tana jiran ta ida yankan kofaton ta kwashe ta ɗure a buhu
Ba zato ba tsammani taji an ƙwalla mata kira
“Balkisu?….Balkisu wai kina Ina ne?”
A furgice ta saki abun yankan ,ta ɗago ta sharce zufan da ya tsatsafo mata a goshi
Buɗe iya Muryar da ilahu ya bata tayi ta Amsa da “Na’am umma ina zuwa” ta kwasa a guje zuwa hanyar ɗakin su .
Sadiya da Rahma dake zaune ƙarƙashin Inuwar mangoro ,kallonta sukayi ta yanko a karce suka bushe da dariya
“Wohoho iska na wahalda mai kayan kara ,ƴar na gada ,a gama iyayin dai tas ,ƙarshen alawa ƙasa an tsotsa iskanci dai a nono ko ya kikace sadiya”
Daganan rahma ta miƙo hannu suka tafa da safiya
ɗan jim tayi ta kasa motsa ƙafarta bare ta tafi ,habaicin ƴan ubanta na ɓata mata rai amma ya ta iya? Ji tayi tamkar yau ɗai ta tamka su ,saidai Ummanta ne a wannan karon ta kuma ƙwalla mata kira harda ƙari da mulmuleliyar Ashar.
Ɗauke kai tayi ta shige ɗakin da sauri “Gani umma”
Wata ƙosashiyar Hajiya na gani zaune cikin adon doguwar rigar Atamfa ,kan ɗaya daga cikin jerin wasu ƙosassun kujeru zaka rantse da Allah ɗakin nan ba a cikin gidan yike sbd ynda yasha adon manyan dardumai en Saudi da tafka tafkan labulai ,fanka na sama da na tsaye sai wulwuli suke yi suna fidda Iska
Hannunta riƙe yike da wayarta tana shafa shi a hankali ,tamkar ba itace ta ƙwalla kiran Bilkisu ba da manyan Ashar ɗin da ta zuzzuba .
Ɗan raɓewa Balkin tayi a ƙofa ta riƙe labule,tana kallonta a ido a ido
“Na’am Hajiya mama gani”
Kafeta tayi da daƙwa ²n Idanuwarta cikin tsantsan takaici ,A ranta tana ƙissima wai ɗiyata ce wannan??
Hakan ya bani daman yi mata kallon tsaf Ni kaina.
MashaAllah Yarinya ce matashiya da bazata haura shekaru Goma Sha huɗu ba ,saye cikin wata dark maroon ɗin Abaya da yayi mugun dacewa da kalar fatar jikinta ,farace ,irin tar tar ɗin nan kyakyawace ita tun yanzu kafin maƙerin ƴan mata ya ida zanota ,saidai ƙafafuwan ta da hannunta sunyi futu futu da ƙoran sasan doki
“Balkisu ke wata irin jaka ce? Eyee ?”
Sunkuyar da kai tayi cikin sadaƙarwa tasan yau zata lallasu
“Jibi jikinki…in ƙici in ƙi sha in siya maki Riga dubu sha takwas kije ki gurfana a turken doki kina ma dawakan ubanki bauta ? ”
Karkaɗe hannuwarta ta shiga yi “Umma hannu ne kaɗai na ɓata Allah bansa gwuiwana a ƙasa ba ,kin ma gani”
Wani malolon takaici ne ya ɗebeta ta rarumi wani kofin gefenta ta cillota dashi .
Tsalle ta daka tayi baya da sauri
“Kina taka ƙofar ɗakin nan sai na lahira ya fiki jin daɗi ,kinsan ke nike jira da inda zamu ko?”
Cikin rawar jiki ta ɗauki buta taje ta wanko ƙafarta da hannu ta shafa Vaseline ta wuce kwabanta ta ɗauki hijabinta ta saka ,ta fito falon ta sameta tana nan zaune tana aikin shafa waya
Kallon wutsiyar ido tayi mata ,kana tace “mayafin kayan fa?”
Idonta fal ƙwalla ,ta sunce hijab ɗin ,ta warware ɗankwalin da ta kindima ɗauri dashi ta ɗan naɗeshi a wuya
Sai sannan ta ɗan sakar mata ɗan murmushi
“Maza jeki wajen matar audu in ta gama shirya Abdul ta bakishi ,mu tafi”
Da “Tohm umma” ta Amsa ,ta fice zuwa farfajiyar gidan , fuskarta ba yabo ba fallasa ,Su sadiya sai sannan suke karyawa da wata irin tsinkakkiyar koko da ƙuli ƙuli ba sugar,aun barbazu ƙuda sai parade suke a inda suke
Raɓesu tayi ,ta shige ɗakin matar audu ,wacce ta kasance matar wan babansu ne da ya rasu amma ƴar ɗakin umman bilki ce sosai ,duk wani jugu jugu da yaranta ,hidimar makaranta ,wanke ² itace duk don ta ɗan bata abu mai daɗi
“Mama Sala wai ki kawo Abdul zamu tafi ” washe baki tayi ,ta zabura ta saɓa Abdul a kafaɗa kamar ƙaramin baby
“Je kira Habu yanzu na gansa zai fice aiki kinga sai ya sauke ku da ɗan sahunsa ‘
Da sauri tayi hanyar sauro saboda kar ya fice basu haɗu ba
“Habu ance ance ka jira mu zaka kaimu hanwa da umma yanzu gamunan zuwa” ta faɗa da muryanta mai kama dana shagwaɓaɓun yara
“tohm banda abinki bilkisa ai aiki zani,wayace ki kirani??”
“Mamanku”
“To kuyi maza ina jiran ku a bakin garko”
” uhmmm ” ta faɗa tana juyawa da sauri dan gani take kaman lokaci baya tafiya ta juya abinta ta tafi ,Bako gaisuwa dama bai ɗaura aka ba inji ɓarawon hula….Inda sabo ya saba yaran basa gayar da mutane,itace ma mai saffa saffa tunda ba rashin kunya
Tana hanyar Juyawa saiga Mamanta ,ta fito hannunta riƙe da ƙanninta kallonta tayi ta kwasa mata harara ,ɗan nishi ta tsaya yi,kafin tace “Maama wai ya fito dashi mu yike jira ”
“Ke ja can bani wuri ballagaza kawai” daga haka ta wuceta anan tsaye , noƙai noƙai tabi bayanta suka wuce ,kofar gidan shake yike da tsoffi wanda yawanci iyayen mijinta ne ,amma haka ta shori takalmarta tayi waje da shararan mayafi ta faɗa ɗan sahun Habu suka bar unguwar.
******
Gidan Commisioner of Police (CP)
Hajiya Ladi wanda Akewa laƙabi da _Ladi Police_ Zaune take a makeken falon ta sanye cikin kayan Barcin ta ɓingilar riga rabin cinya mai jikin Nylon da yabi tsokar jikinta ya lafe ,matace shirgegiyar gaske ,ta ɗaura ƙafa ɗaya kan Table ɗaya ta Aje a ƙasa ,mazan kukunta sai kaiwa da kawowansu suke suna gudanar da Aikace²n Girkin gidan .
Tunda Napep ɗin ta tsaya ita ta fara fita bata jira umman nata ba ta zura cikin gidan da ƴar gudunta
“Anty Ladi Ina kwana”
Ware hannu tayi ta miƙo mata alamar ta shiga jikinta ta rungume ta
“Oh my daughter yakike ,ina mama?”
Lafewa tayi akan makamakan nonuwan Hajiya ladi sannan ta nuna mata ƙofa daidai sanda su Hajiya binta suke shugowa
“Aminiya Barka da zuwa ”
A hankali ta zame Balkisu a jikinta ta muskuta ta miƙe sukaje suka rungume juna ,a hankali cikin dubara ta maka ma ɗuwawun Hajiya bintan ɗan marin wasa “Washhh ƙawata ya yau ”
“Zuii na faɗa maki, ya week End ɗin”
“Wallahi lapiya ” daidainan CP ya shiga gangarowa daga stairs yina Amsa waya cikin Shirin fitarshi
Yina hangota ya shiga washe mata baki tun daga Saman matakalan benen har ya sauko ,sakin juna sukayi da hajiya Ladi ta koma kan hannun kujera ta zauna ,itakuma yina zuwa ya kashe wayar ya miƙa hannu suka tafa da Hajiya bintan “Baby girl…Baby girl ”
“Alhaji Bala gomnati…Mai Ƴan sanda mai motoci ,to ya ?”
“Wallahi komai daidai ,kin gani ina hanyane mai girma gomna zai shigo zarian zan sorting yarana da zasu taho tare ”
“Eh naga Alama ,to bye” kashe mata Ido ɗaya yayi “Baby girl…Baby girl”,ya sake maimaita Nick name ɗin Hajiya bintar yina nufan hanyar waje ,gamida ɗagawa matarsa Hajiya Ladi da take zaune ,gefensu Bilkis tana jin shirmensu tana masu wasa ,ko A jikinta da irin shaƙuwar da ke tsakanin Mijinta da so call Aminiyarta .
Ɗaga masa Hannu itama tayi daganan suka canjawa yara channel zuwa cartoon ,ta kira maid ɗinta ya kawo ma su Freshyo da cake ,suka barsu a falo ita kuma ta wuce da Aminiyarta inner room ɗinta
Suna wucewa Bilkisu ta cuno baki cikin takaicin rainin wayon da ake mata “Har yanzu fa matan nan kallon yarinya suke mun ,hmmm”
Tana nan zaune,Abdul yina riƙe da freshyo a hannu yina ɗan zuƙa har barci ya sureshi ya daina kallon ,aiko tana ganin hakan itama ta saɗaɗa ta fice .
©Alheri Writers Association
_*O & A ORGANIC SKIN CARE AND BODY CARE PRODUCTS*_
09065990265
Menene Burinki?
Burina ,shine , In zama Sarauniyar mata ,Tauraruwa ta gaban goshin me gida ,Babbar babes tsole Idon manyan gayu a town ,Saidai kash Abubuwa da Dama sun mun cikas ,wanda suke dakusar mun da self Images ɗina da self Esteem ,kama daga
*Black spots*
*Pimples*
*Sun Burn*
*Knuckles*
*Rough skin* Dasauransu
Ga kuma ni na tafi 1 ɗina
*Ba Nono*
*Ba ɗuwawu*
*Ba lafiyayyiyar fata,mai laushi ,sheƙi da Glowing*
Hakane?? Sune Damuwarki???
Tom In sune Kakarki ta yanke saƙa dama ga sallah na matsowa mata an fara tanajin Atamfar sallah zoki gyara skin ɗinki shine farkon Gayunki
Domin kuwa A wajen Oum Aphnan ne kaɗai zamu baki product ɗin mu ba shayi ki amfani dashi kisha mamaki ,ke in ma baiyi ba akwai refund ,ma’ana zan dawo maki da kuɗinki
Product ɗinmu kala kala ne ,Akwai :
*1) Mayukan ɓatarda munanan Tabon Fuska, Knuckles na gaɓɓan yatsun Hannu ,da na gwuiwoyin Ƙafa da Hannu Da tabon dake fita silar zafin Rana wato Sun burn*
*2) Mayukan da zai saki Haske inke fara ce kiyi tar Kalar gaban Mota*
*3) Mayukan Da Inke baƙace zaki zama Chocolate ,kala mai zafi mai bada ciwon kai ga ɗan karan wuyan samu ,Ki shimfiɗa hannu ki zagi Hannun fararen Fata, kiga kowa na ɓoye nata*
*4) Ina da Mayukan da nike Haɗawa yara daga Shekara 1 zuwa 12 years ,Mun sani sarai kula da Fatar yaro shi yafi komai wuya dakin fara ɗanki yayi haske bauuu a fara surutu wance nawa ɗanta bleaching,zo in baki ƙaryar hassadar maƙiyi ,don shi wannan skin ɗin yaronki ne zai ƙashashar ,kalar ƴaƴan turawa ban cire maki fari ko baƙi ba ,ai a gyara ake gane Ajebota da Ajeɓaku*
Bayan Mayuka ,Munada Supplements Kala kala ,Marasa Illa ,Giredi Gangariya Tafiyayyu daga Thailand…..Mun sani sarai jabun kaya sunyi yawa ,Harma ki kasa tantance mai kyau da Fake ,To kukanki ya ƙare ,this 1 Original ne Hajiyar Allah ,Tafiyayyayyu ne daga Thailand Sai Ƴan Egypt Amma fa na Manyan kai ne ,Ba ina nufin Wacce ta tara dollars kaɗai ba ,uhm uhm harda wacce ta shirya gyara domin fizgo martabarta ,don sarai mun sani wacce ta Isa da kanta itake gyara
Inkin shirya siya sai ki tuntuɓeni ta nan 09065990265
BARIKI*
_(Gado nah)_
Book 1
Page 5&6
Oum Aphnan
Wxp Link Group 2
In kina na Group 1 karki shiga wannan tunda wancan ya cika kibar wasu su shiga wannan Don Allah
https://chat.whatsapp.com/CEJlu3dU481AJRdRQ4WkcN
Kewayawa ta bayan gidan tayi ,inda Ladi police ke kiwon kajin turawan ta da su gis ,tolo tolo da sauran Nau’in tsintsaye masu ban sha’awa .
A hankali ta nufi wajen tulin tantabarun da suka baje a ƙasa fululu,ta shiga ɗiban Alkama tana watsa masu ,aiko kafin ai haka sun fewayeta suna tsinta da en koke koken su mai kamar waƙa
Lumshe Ido tayi tana shaƙar Ni’imtacciyar iskar dake bugawa ,kukansu na saka mata nishaɗin da sam bata samunsa a gidansu
Sadiƙu dake can gefe zaune ƙarƙashin rumfar da aka tanada don hutuwa ,sanye yike cikin gajeren wando da singlet na kakin land soldier, chat yake a kan laptop ɗinsa saidai lokaci zuwa lokaci yina ɗagowa yina kallon yarinyar ,sosai yarinyar ta tafi da Hankalinsa musamman yanda ya gane tanada tausayi da son dabbobi ,hakan yasa in tayi wani abun yikan ɗan tsura mata ido wani abun kuma sai ya mere baki ya cigaba da shafa system ɗinsa irin bai masa ba ɗin nan,amma yinajin bagaga ɗin tantabarun zai kuma ɗagowa
Daga ƙarshe dai ɗan tagumi ya rafka ya dogare hannunsa akan table ɗin gabansa ,ya ɗan karkato kaɗan yina ƙare mata kallo ,zuwa yanzu yafara gajiya da damunta ,don sosai ta fara takura masa ,amma kuma halshensa yayi mugun masa nauyi hakan yasa ya kasa magana tsabagen madarar miskilamci .
Ɗan shaking jikinta tayi ,wanda yasa tattabarun tashi firrrrr ,aiko wani ɗan murmushine ya ƙwace mata wanda yasa dimple ɗin gefen kuncinta loɓawa ,a take kuma wasu hawaye marasa dalili suka silalo a kuncinta.
Ɗan tsai da ransa yayi ,tunanin sa me yasata kuka kuma lokaci ɗaya tana dariya ?
Itakam sam batasan wajen da halittan ɗan Adam ba ,cigaba da bin duk inda wasu farare da grey ɗin tantabaru suka saka ƙafarsu take tana ɗan tafa hannu tana masu waƙa
“Tantabara woooo….Tantabara woooo”
Tana cigaba da binsu gudu gudu sauri² ,cikin rashin zato ta ƙumu da ginin daya ɗan kewaye wajen da yike zaune ,aikuwa ta faɗa rikicaaa cikin flowers ɗin dake a gefe .
Ta kuwa ƙwalla ƙaran Azaba
Dafe kai yayi cikin takaici ,a duniyarsa ya tsani ƙara
Wani ɗan siririn tsaki yaja ,kafin a kasalance ya miƙe yaje gabanta ya tsaya ƙerere ya miƙo mata hannunsa alamar ta kama hannunsa ta miƙe
Bilƙis daga inda take kwance dafe dakai ta ga an sagalo mata kyakkyawar choco hannu lulluɓe da ni’imtaccen gashi
Ɗago lulun eyes ɗin ta tayi ta kafesa da ido ,saidai tana kallonta taji cikinta ya ɗauki jiniya wui wui wui . Saboda kayan da suke jikknsa na ɗaya kenan sannan na biyu ya wani tamke fuska sai hura hanci yake .
Wani sautin marayan kuka ta saka ,zufa ta ko’ina na tsatsafo mata a duniyar ta ta tsani ko kakin ɗan sanda bare na soja
Kansa ne ya sara masa take ya fara jin kansa na masa ciwo ,rayawa yake a ransa meye hadinsa da Wagga yarinyar wacce ruwan hawaye kamar sun mata yawa,da har yike jin ƙolafucin ya taimaketa?
Duddulo mata Idanuwarsa yayi duka waje sannan ya doka mata tsawa ,wanda ya haddasa ma jijiyoyin kansa bayyana
Jikinta ne ya shiga ɓari ,take ta fara mulmule cikin ciyayin wajen ta kuwa shokaresa da takalmin ƙafarta a ƙafa
Wani malolon takaici ne ya ɗebesa baisan sanda ya miƙa hannu ya damƙota ya cikuikuyo wuyar rigarta ya tsinke lafiyayyen kuncinta da mari ba.
Wani ƙara ta saki sai ga jini na tuttulowa ta kuncinta ,take ta shiga Marisa kamar taliya ta yi luuuuu zata zube a ƙasa yayi saurin tallafota ta riɓu akan ƙafafuwan sa
Hajiya Binta da tun kukan bilki na farko ta fito harabar gidan da gudu tana ƙwalla mata kira ,har ta shigo kuma a daidai nan ,Sadiƙ ya kifeta da mari ta sulale kan ƙafarsa
Wani vibration ne ya kama jikin Hajiya Binta ƙif taja ta tsaya ta kasa ƙarasawa har saida Ladi police ta ƙaraso da sauri ,saidai ganinta a saman ƙafan Sadik ya sata tsayawa a gabansa ita bata ɗagota ba sai ma ta hau rawan baki
“My boy ya haka ? Halan ta yi rashin ji?”
Wani kunyane ya kamasa don shi kansa yasan abinda yayi sam bai kyautu ba ,amma saboda aja girma ,kawai sai ya waniyi ball da ita ya zare ƙafarsa ,ya fara taku cike da gadara da ƙasaita ,ba tare da ya tamka Hajiya Ladin ba.
Sai sannan Hajiya Binta ta ƙaraso kan Bilƙis ,ta rarumo kanta “mai gadon zinare ,me ya faru?….” Damtse bakinta tayi da sauri ganin yanda hancin erta ke bulbula da jini jajazir
Wani luuuuu ,tayi da ido kamar wacce zata sume,sannan ta miƙa hannunta tana nuna bayan sadiƙu
“Kambala’i!!” Wani zabura Hajiya Binta tayi taje ta bayansa ta damƙo wuyarsa ,batai wata ² ba ta kafe shi da wani irin gigitaccen mari ta sake ɗaga hannu ta wanke ɗayan kuncinsa
Hajiya ladi ruɗewa iya ruɗewa ko tayi Faɗi take “A’ah Binta karki kuskure ki dakata kinsan shiɗin wanene kuwa?”
Sa hannu tayi ta zungure masa goshi tamkar ta samu ƙaramin yaro
“Yaro na gani wanda aka haifa da jini tamkar yanda na haifa ɗiyata Bilkisu ,don haka ke kika san ko shi wane ne ,mumugunci kawai Azzalumi!”
Dafe kansa yayi da sauri zai iya cewa a iya tsayin rayuwarsa ba’a taɓa zaginsa ba ,kowa girmamasa yike ,sai sanadiyyar zuwan shi wannan Gidan ,dole yau ya koma gidan babansa saidai duk abinda zai faru ya faru
Da kyar ya fara jan sawunsa yina barin hanyar ,ba tare da yace kanzil ba ,itakuwa Hajiya Binta tayi kan ɗiyarta ko a gefen mayafinta ,bata damu da magiyar da Hajiya ladi take ma mumuguncin yaron da taji suna kira da Sadik ba .
Wanene Sadiƙ?
Sadiƙ Yarone na shidda ga sarki Abdul gaffar ,Yinada yayu uku maza ,Adam,sulaiman ,da Ja’afar ,sai mata biyu sadiya da A’isha sai sannan nan shi Abubakar Sadik, bayansa akwai yara Ashirin da takwas wanda suka kasance harda ɗiyoyin ƙwarƙwarorin sarki Abdulgaffar.
Kaf cikin yaran mai martaba ba wanda ya shiga zuciyar mai martaba kamar Sadik ,a yayinda ba ɗa marar ji kamar sa ,sam bai ɗakko halin babansa na dattako da girmama mutane talakawansa ba ,Girman kai da Izza tamkar shine Sarkin ,wannan dalilin yasa tun sanda ya gama secondary school ga buɗe ɗaya daga cikin guest house ɗinsa dake bayan gari ya maidashi fadarsa
Sam baya zaman fadanci tsakaninsa da gida sai in dare yayi ,yina da fadawansa ,da masu hidimta masa ,ana masa zaman fadanci ya hakimce a karaga
Kafatanin Abokan Sadik ,dole su kasance a karkashin ikon sa ,dole ya bautar dasu in ba haka ba a rabu
A gida babansa yike sarki Amma shima a fadarsa sarkine ,don haka kowa sarki yike Kiran Sadiq don kawai a zauna lafiya ,Sadik tun yina karamin sa Allah ya hore masa son Mulki hakan yasa sam baya saka ƙananun kaya sai nauyayan kaya ,kuma ko club zasu da Abokai da kayansa yike zuwa .
Tun bayan da Sadik da babban Abokinsa ,yaron fagachi wanda suke kiransa da sarautan gidansu wato Fagachi ,tun sanda suka gama makaranta fagachi yace shi soja yike son zama ,a ra’ayin Sadik yafison zama lauya amma saboda baison rabuwa da Abokinsa mai fasa masa kai a koda yaushe yina masa fadanci da banbaɗanci yasa yaje ya sama mai martaba ,akan Alankatabir sai a nema masu NDA da Yusuf Fagachi
Soyayyan da mai martaba kewa Sadik yasa shi kasa gane illan kasancewan jininsa Soja
Sun fara karatun soja cikin nasara saidai suna tama 3 A lokacin ne tsautsayi ya afkawa Sadik ,Abunda ko ya faru shine sun shirya get together da abokansa a wajen school sai dai ba daman fita ,yayi duk yanda za’a barshi ya fita amma bai yiwu ba
Ya kuwa fakaici idon kowa ya haure katanga ,dirkansa keda wuya sai a hannun wani major
Ran manjon ya ɓaci gaya ,saboda kowa yina sane da rashin ji irin na Sadik ,ƙaramun laifi ya zama Babba ƙarshe aka koresa aka dawo dashi gida
Kasantuwar hakan babbar abun kunya ne ga mamansa Hajiya mai babban ɗaki ,musamman ga tsakankanun kishiyoyinta da sukayi dace da ɗiyoyi nitsatsu ,yasa tayi shawara da jakadiyarta suka turasa gidan Commissioner of police a matsayin maɓoyan sirri har a gani in za’a iya gyara matsalar sai ya koma makarantar sa batare da kowa ya sani ba ……..saidai kuma kash mai hali bayi fasa halinsa tunda Ladi polis ta ƙyalla ido akan Sadik taji tana azaban sonsa bata damu da ƙananun shekarunsa ba ,yanzu haka kuma taci alwashin sai Sadik ya sota kota halin ƙaƙa ,saidai kuma kashhhhh ,tun kafin ai nisa Hajiya Binta ta kwaɓa mata garinta ,batasan ya zata shawo kan sa ba ,duba da Yarone shi mai azaban zuciya ga baƙin hali ga riƙo da ƙulli.
©Alheri Writers Association
Mu tallata Hajarmu
Mata kuna ina???
Ehem Akace in kin ji kira samu ne
*Hajja mai gyaran aure* ta taho maku da zafafan magungunan mata ƴan gaske,tafiyayyu maras Algus,iya kuɗinki iya shagalinki ,ko mijin ki bai saba ihu ba ,Alƙawarine wannan sai yayi , Magunguna na dai ,Akwai garurruka
Gumba
Tsimi
Tabaje
Jigida me matsi da niima
Jigida mai saka farin jini awarwaron farin jini da mallaka
Zobban farin jini da mallaka
Haɗin Ƴar gata
Zuma na musamman
Cicciɓi
Kaza dahuwar uwargida da amarya .
Ƴan shila
Haɗin kifi
Ɓata jikin Kishiya
Maƙale mata
Haɗin karya gado .da sauransu.
Mu ƙa’idar maganinmu bamu badawa sai mun maki bincike in baki da infection in kuma akwai sai mun maki magani
Hajiya ,maganina nagartattune an daɗe ana yabonsu ,kar in cika ki da zance wani abu sai kin amfani dashi wallahi sai kin kawo ƴar uwarki
Domin ƙarin bayani ki tuntuɓi wannan Numbobin 09060703187
Serious masu saya don Allah
Leave a Comment