Hausa Novels

Basma Hausa Novel

Basma Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

BASMA _

 

📄Littafi na 1

 

 

 

 

*Ummu maher(miss green)*

 

 

_Noticed:wannan littafin labarine akan wata yarinya wacce ta kasance kurma ce._

 

———————-

Karin wasu littafai da zaku so

*matso kuji*

Babu abin ƙyama a ha

littar Allah matuƙar shi ya yi halittarsa don haka mu kiyaye don muma bamu fi ƙarfin ikonsa ba.

 

—————

 

Bismillahir Rahmanir Rahim

 

 

 

1

 

 

. . . .A hankali na ke share Ƙaton gidan a zuciyata ina ta istigfari don ban taƁa yin shiru da bakina akan ambaton Allah,shiyasa ko da yaushe zaka ganni cikin nutsuwa da kamala,wata sharar naji an watso min na ɗago kaina Maryam na gani a kaina tana ce wa”to uwar shara ga wata ƙarin sharar nan”.bance mata ƙala ba na koma gefe na zauna don nasan tunda Maryam ta fara haka to tabbas tana son ɗebo rigima ne.

 

Cikin fushi ta ce”ikon Allah yanzu don na kawo wata sharar ki haɗa shine zaki koma gefe ki zauna ke ga ki uwar fushi ko?”.sunkuyar da kaina na yi hawaye na bin kuncina Allah sarki baki yana da daɗi wani lokacin,yanzu da ina da baki da tuni ko da wataran banyi magana ba to tabbas wataran zanyi don sha’anin mutanen gidan sai a hankali.

 

Ana cikin hakan Hafsat tazo ta sameni ina kuka ta ce”Basma me ya faru ki ke kuka kuma?”.tasan halina ba lallai in gaya mata ba don aƙwaini da haƙuri kamar dutse don haka ta juya kan Maryam don taga alamar ni da Maryam ne don ta juya ƙeyarta ta yi irin ɗaurin nan na ture kaga tsiya,don ƙarin neman rigima sai ce wa ta yi”to tsigarallahu to da kika zo rama mata zakiyi ko kuwa inji labari?”.ran Hafsat ne ya ɓaci sosai ta ce”kin san ai zan iya rama mata ɗin saboda kin san Basma kurma ce shine ki ke mata duk abinda ki ke so don ki zalunce ta,to wallahi ba zaiyuwuba sai na tsaya tsayin daka na rama mata duk wani cin kashi banza kawai babbar kwabo”.

 

Shaƙo Hafsat Maryam ta yi ta ce”ikon Allah yanzu Hafsa ni ki ke zagi saboda wannan kurmar banzar ko?ko da ya ke ƴan ubanci za ki nuna min saboda ita ƴar ƙanwar Mamanki ce dole ki nuna min haka?to wallahi ki maida hankalinki ko kuma inci ubanki hankali ƙwance”.

 

hayaniya sosai su Hafsat suka fara ita da yayarta Maryam ni kuka babu abinda na ke sai kuka ina rabasu,muna cikin hakan Hajiya Saratu ta fito tana ce wa”ikon Allah ke Hafsat tsabar tsaurin ido ki rasa da wacce za kiyi faɗa sai sa’ar yayarki?amman ke dai baki da kunya wallahi,ko da ya ke aikin munafukar uwarki ne mai zugaku a kan yi wa mutum rashin mutunci”.babu abinda Maryam ta ɓoyewa mahaifiyarta harda ƙarya da sharri duk ta haɗa ta faɗa.

 

 

Tafi Hajiya Sara ta farayi tana ce wa”ai ni daman nasan babu munafukar da ta haɗo wannan faɗan sai wannan munafukar kurmar.sai ana magana ta yi maka wuƙi wuƙi da idanu tana kallon ka kallon rainin hankali.

 

 

Ta yo kaina tana ce wa dukan da Hafsat ta yiwa ƴa ta yasin akanki zan rama,da gudu Hafsat ta yo kaina tana ce wa”wallahi Hajiya babu wanda zai ƙara dukan baiwar Allahn nwn a gidannan,don ita ba jakar ku bace.”tana faɗar hakan taja hannuwa na muka nufi ɗakin mama.

 

Haryanzu ban daina kukan ba,Hafsat ta buɗe fridge ta ɗakkomin ruwa mai sanyi ta ce”gashi kisha Basma,amsa na yi na hau shan ruwan nan sai da na shanyesa duka,Hafsat ta yi dariya sannan ta ce”ki yi haƙuri ƴar uwata kowa da irin ƙaddararsa kuma indai ina gidannan babu shegen da ya isa ya bugeki wallahi sai na rama miki.

 

Wasu hawaye ne masu zafi suka zubomin na kalli Hafsat na yi mata alamun na gode,dariya ta yi sannan ta ɗakkomin wani hausa book mai suna silar fyaɗe na marubuciya Ummu maher.

 

Sosai naji daɗin littafin har Mama ta dawo ta sameni ta ce”to uwar karatun littafi sana’ar a ke yi ne?ƴar dariya na yi sannan na yi mata alama da hannu na ce sannu Mama dafatan kin dawo lafiya,ta ce lafiya ƙlau ɗiyata.

 

Nan muka cigaba da hirarmu da Mama amman da hannu muke yi don sai kace ma ina jin maganar gwanin sha’awa.

*****

 

*ƘAISA PALACE*

 

abinda kenan aka rubuta a babbar masarautar wacce ta haɗa abubuwa masu abin sha’awa shuke shuke masu ƙyau sanyin idaniya.

 

 

A hankali ya ke takawa duk inda yabi sai kaga an zube ana gaishesa,yana amsawa cikin kulawa tsaɓanin Hajara ƴar uwarsa don ta haɗe fuskarta sosai kamar kunun tsamiya.

 

 

 

Yarima Abeed kenan yana da matuƙar mutunci ga mutane ba shida girman kai ko kaɗan amman sai dai fa masarautar ta su aƙwai lauje cikin naɗi don aƙwai abubuwa sosai waɗanda suka kasance na zalunci da kuma kitimirmira kala kala.

 

 

Yana da ƙyau sosai wanda tsayawa faɗar kyaunsa da kuma cikar izzarsa na dabanne,da yawa mata sun kamu da ciwo iri iri saboda shi,sai dai shi sam har yanzu bai ga wacce ta yi masa ba,don mafi akasarinsu ba don komai suke sonsa ba saboda kuɗi da kuma ƙyau don masarautar ƙaisu masarauta ce masu ɗinbin dukiya sosai.

 

Kai tsaye ɗakin mahaifiyarsa ya shiga wacce ake ce mata,Jidda amman ana ce mata sarauniya saboda mahaifinta shima sarki ne mai zaman kansa don yana da kuɗi sosai.

 

 

Zagaye ya same ta tana yi a cikin ɗakin ya yi sallama ya shiga,ta ce”yanzu abeed abinda ka ke yimin kana jin daƊinsa in baka umarni ka Ƙi bi,sai abinda kishiyata ta baka umarni shi ka ke yi,to yau na barka na yafe mata kai”.

 

Cikin fushi ta juya masa baya wannan kuma yana daga cikin tarkon da ta ɗana wa Yarima don ayanzu yana da shekara a duniya35 amman ko zancen aure bayayi shiyasa a wannan karen ta shirya yi masa aure ko ma me zai faru sai dai ya faru don ba za ta yadda kishiyarta ta dinga bawa ɗanta shawara ba don ita bata yadda da kowa ba.

 

 

 

 

 

*Miss green ce*

BASMA*_

 

📄Littafi na 1

 

 

*UMMU MAHER*

(MISS GREEN)

 

 

*arewa book*

*PROFILE NAME* Rabiattu0444

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

 

*LINK*

 

 

*Wattpad*

*PROFILE NAME*

Rabiatu333

 

 

*LINK*

 

 

*Matso kiji*

mu yawaita karatun alqur’ani mai girma don yana wankr cutukan zuciya dana bayyane.

——————————

2

 

A hankali Abeed ya zagayo ta gaban mahaifiyarsa ya kalleta sosai sannan ya Ɗago haɓarta ya ce”ya ke ma’abociyar ƙyau da haiba ina neman gafararki ya ke mahaifiyata abin tinƙaho na,ta gaban goshin sarki babu wani a gabanki ko a bayanki,ke ce agaba ke ce a farko babu wani mahaluƘin daya isa ya tsaya a gabanki ya ce bake bace don cikar izza da kuma Ƙyau da Ƙawa.”dun gure kansa ta yi tana dariya ta ce”kai yarima gaskiya ka raina ni sai kace wata matarka?”.murmushi ya yi sannan ya ce”ai babu wata mace a guna data fiki ya ke mahaifiyata babu wanda ya isa yaja da ke matuƙar ina wajen ba tare da na cire masa yatsanta guda ba,don haka ni ke ce abar ƙauna ta har abada”.

 

wani irin jin daɗi ne ya sauka a fuskar sarauniya Jidda don arayuwarta tana matuƙar son taga an yabe ta kuma duk abinda ta ce ayi to ya zama dole a yisa,don tun a masarautarsu ta sudan babu mai ɗaga mata hannu ba tare da ta saka anyi mata maganinsa ba.sarauniya Jidda tana da izza da kuma mulki bata yadda a kawo wani abu a masarautar ba wanda ba ita ce ta kafa sa ba,don haka kishiyarta fulani Khadija binta ta ke sau da ƙafa don aƙwai lokacin da ta mari Fulanin akan ta karya mata doka,tun Abeed yana ƙarami ta ke sonsa tunda ita alokacin Allah bai bata haihuwa ba sai daga baya ta haifi namiji sai kuma mata 2 ƴan biyu daga nan bata ƙara haihuwa ba.

 

 

Sarauniya Jidda kuwa tana da ƴara guda5 ɗaya namiji huɗu mata ta aurar da biyu matan Hasiya da Husna,yanzu kuma aƘwai Hajara da Bilkisu.

 

 

Hajara ce kawai tayo halin Sarauniya Jidda saboda tana da izza da mulki da kuma wulaƙanta ɗan adam babu ruwanta komai girmanka yanzu zata zageka ta saka aci maka mutunci.

 

 

 

Washe gari da sassafe Fulani da kanta ta isa ɓangaren ɗanta Yarima Abeed yana ta karatun alqur’ani mai girma ta shigo,ta kalli ɗan na ta cikin burgewa aranta tana ƙara son ɗan na ta don aƙwai addini sosai kuma kullun ba shida abokin hira irin qur’ani ya yi karatu a turai na shekara 15 amman ko da yaje ɗin ma bashi da wani aboki sai wani abokinsa Al’amin shima Al’amin irinsu ɗaya da Abeed don yana da matuƙar taka tsantsan sosai da addininsa.

tsayar da karatun Yarima Abeed ya yi sannan ya gaida mahaifiyarsa cikin girmamawa sannan ta ce”yarima anjima ƴan matan nan na masarautu daban daban zasu zo gidannan ka zaɓi wacce ka ke so daga cikinsu kaima ka yi aure ko ns ji daɗi araina”.ransa yaji ya yi masa zafi ammzn saboda mahaifiyarsa taji daɗi sai ya ce”babu komai mai babbar fada insha’Allah ina nan ina jiran zamansu Allah ya zaɓa min tagari a cikinsu.”

 

murmushi ta yi sannan ta ce”Ina alfahari da kai ɗana,saboda ban taɓa baka umarni baka bi ba don haka ina maka fatan alheri a rayuwarka ta duniya ya wanke maka dukksn abinda ke damunka na zuciyarka ya cikamin burina na ganinka a matsayin Yariman ƙaisa babu abinda zai sani farin ciki irin ganin wannan ranar”.

 

murmushi ya yi sannan ya ce”ummi na Allah ya kaimu lokacin yasa muna da rai da lafiyar gani”.murmushi ta yi ta ce”amin”.

 

 

tana fita yabi hanyar da tabi da kallo yana masifar son mahaifiyarsa amman kuma aƙwai wani mummunan hali irin na mahaifiyarsa wanda baya sonsa,yasha yi mata wa’axi akan hakan amman sai ta nuna masa fushinta don haka yana ji yana gani sai dai ya yi shiru ya ƙeleta don mahaifi yafi gaban wasa.

 

Kallon ƙaton mudubin da ke ɗakinsa ya yi,ya kalli kansa ya kalli irin halittar da Allah ya yi masa,amman fa sai dai kash ya rasa wani abu a zuciyarsa wanda ya ke ji kamar ba zai taƁa samunsa ba.

 

Kash nasan masu karatu zasu so suji wannan wata irin matsala ce da Yarima,ku biyo ni ni miss green don kuji wata irin matsala ce haka.

****

 

Ina kitchen ina girki salimat ta shigo Ƙanwar Maryam ta ce”ke kurma har yanzu baki gama girkin bane?yunwaqq muke ji?”.ban ma san me take cewa ba na cigaba da girkina kawai sai ta ɗebo ruwan zafin dana fara zubawa na shayi ta watsomin a kan kyalkyawar fuskata,tsananin zafin dana ji yatsa na ƙwala wani irin ihu ina yarfe hannuwa na don har hannu sai da ya zubar min,abinka da farar fata wajen ya tashi ya yi ja nan da nan,Mama da tazo wucewa ta kitchen ɗin taji ƙara ta da sauri tayo kaina,tana tambaya ta me ya faru?kasa magana na yi saboda tsabar azabar dana ji na rungume Mama ina kuka mai cin rai.

 

Da sauri Salimat ta fita don tasan bata da gaskiya da sauri Mama ta janyo hannunta ta ce”ai wallahi babu inda zakije Salimat don wallahi na gaji da abinda kuke wa yarinyar nan,ana cikin hakan Hajiya Saratu ta fito tana cewa”to wata wainar kuma ake toyawa,nasan babu munafukar data haɗa wannan abin sai kurma.

 

Faɗa sosai akayi ranar agidan don duk da Mama bata ramamin ba amman fa anyi masifa sosai kuma Salimat tasha duka wajen Mama da ƙer Hajiya saratu ta amshe ta tana kuka tana tsine mana ni da mama.

 

 

Alhaji Tasi’u ransa ya ɓaci sosai shine mijin mama yayar mahaifiyata dukanmu ya taramu ya kalli Salimat ya ce”idan na ƙara ganin wani mahaluƙi ya hantari Basma baiwar Allah marainiya,ku me yasa baƙwa tausayin yarinyar nan ne?da wanne zata ji da kurmanta ko da maraici ko da matsalarku,yarinyar nan a bata taɓa ganin mahaifiyarta ba ballanta ma taji Ɗuminta to wallahi bazan yarda a salwantar da rayuwarta ba,ke kuma hajiya saratu ki jawa mutumncinki don wallahi na Ƙara jin wani abu ya faru to tabbas ran kowa sai ya ɓaci”.yana faɗar hakan ya yi tafiyarsa,Abubakar ya kalli Basma ya yi mata alama da hannu ta yi haƙuri baza a ƙara yin hakan ba”.ɗan murmushi ta yi har ƙyawawan dimfil ɗinta ya lotsa ƙyaunta ya ƙara fitowa.

 

Abubakar ma murmushin ya yi yana ƙara jin son yarinyar acikin zuciyarsa ga ta kurma amman Allah subhanahu wata ala ya yi mata baiwa kala kala.

 

Shima faɗa sosai ya yi wa ƙannensa Maryam da Salimat,don su biyu ne yanzu yaran Hajiya Sara mata waɗanda basuyi aure ba ta aurar da mata uku,Abubakar shi kaɗai ne namiji shine kuma ɗanta na biyu.

 

 

 

*Miss green ce*

 

_*BASMA*_

 

📄Littafi na 1

 

 

*UMMU MAHER(MISS GREEN)*

 

_Noticed wannan littafin labarine akan wata yarinya wacce ta kasance kurma ce._

 

 

Wattpad user name

Rabiatu333

 

Arewabooks

rabiattu0444

 

 

*Matso kiji*

yin sallah akan lokaci yana Ƙara kusantamu da ubangiji,sannan Allah yana shiryar da mutum da barin alfasha.

——————————

 

3 -4

 

ranar Hajiya Saratu ƙwanan baƙin ciki ta yi na yadda Alhaji ya ke banbanta su Salimat da kuma ƴar ruƙonsa wato Basma,ji ta ke kamar ta kashe ta ta huta,ko a waje Basma tana da farin jini sosai a wajen mutane don kafin kaga an aiko neman su salimat to sai an aiko neman Basma,abin yana bata mamaki duk da yarinyar tana da ƙyau sosai amman kuma ai ba tada baki,to ta yaya zata yi zancen?ai kuwa bazai yiwu tana kallon wannan kurmar ta yi aure tabar ƴaƴanta ba,don haka idan sun san wata basu san wata ba.

 

 

Kuka sosai na ke yi idan na tuno da mahaifina yana raye amman ban isa yanzu inje gidansa inyi ƙwana ɗaya bama,saboda wani shinge da ya gifta a rayuwarmu,na ɗaga kaina sama ina tuno wani abu daya shuɗe a rayuwata.

 

 

Mahaifina bai taɓa ko da ƙwana ɗaya ba tare da ya kawo mace gidansa ba,aƙwai Hajiya Tani ita daman ta zama kamar matarsa tun a zamanin mahaifiyata tasan da zaman Tani kuma ba aure sukayi ba,sai dai ba yin kansa bane aikin asiri ne.

 

Ban san mahaifiyata ba idan ba a hoto ba ayadda aka bani labari mahaifiyata sunyi auren soyayya da mahaifiyata mahaifina asalin shuwa arab ne dake yankin maiduguri ɗan gatane sosai awajen mahaifansa,tunda Hajiya Tani taga mahaifina sai ta ƙwaɗaitu dashi sosai ta dinga kashe kuɗinta wajen bokaye amman abin bai taɓa cinsa ba,da ta gano mahaifiyata ke karya komai ta hanyar addu’ah da kuma magani sai ta saka mahaifiyata sosai a gaba,ita kuma mahaifiyata fulanine na asali da ke yankin yola,don haka iyayensu suj tsuma su sosai da maganin tsarin jiki,sai da mahaifiyata ta yi shekara biyar da aure sannan ta samu cikina,nan fa mahaifina Alhaji Sa’eed ya dinga kula da mahaifiyata tare da tausayinta,don yana sonta sosai ana haka wataran ta fara naƙuda sosai aka kaita asibiti,tunda Hajiya Tani taji ankai mahaifiyata asibiti bata yi ƙasa a guiwa ba,sai ta nufi asibiti ta saka niƙabi a fuskarta ta yadda ba za a gane taba,ta shigo har cikin asibitin ta samu nurse ɗin da ke duty,ta sakar musu kuɗi ta basu ragama akan kashe mahaifiyata,saboda kuɗi suka aikata abinda suka aikata suka shaƙe mahaifiyata ta mutu tana halin naƙuda,sai dai kash an kashe miciji batare da an sare kansa,ana cikin hakan mahaifiyata ta haifeni,suka ciro ƴar sannan suka kashe ta,babu wanda baisan Hajiya Tani ce ta aikata hakan ba har ƙara aka shigar bayan likitocin sun tona mata asiri ammanfa Hajiya Tani mutum ce me shegen wayo da sanin makamar aiki na asiri don haka tuni ta kashe bakin kowa,don ko da kayi yunƙurin ta yarda maganar to tabbas sai ta kashe ka,yayan mahaifiyata ita ta kasheshi har lahira don ya tayar da maganar,shiyasa babu wanda ya tayar da maganar har iyau,da yayar mahaifiyata ta amshi ruƙona bayan ansha gwagwarmaya da mahaifina akan badani don son mahaifiyata ne ya shafeni,amman fa a yanzu ta manta na yana da wata ƴa mai suna Basma don tuni ya manta dani don Hajiya Tani ta mallakesa sai yadda ta yi dashi.

Wani guntun hawaye na share don tuno da wannan labarin da Mama ta daɗe tana bani,tabbas inason in zama lauya amman babu yadda za ayi in zama hakan tunda ni kurma ce,ina yawan kuka akan kasancewa ta kurma ammanfa idan na tuno shima jin wata ƙaddara ce ta rayuwa sai in share hawayena in cigaba da roƙon Allah akan Allah ya banni ma a hakan don wannan ma wani ladane na daban,don duk mutumin da Allah ya haliccesa da wata tawaya yasan abinda yasa ya barshi a hakan,don shi yasan kaɗai abinda jin zai haifarwa wannan bawan na sa.

 

 

*******

Masarautar ƙaisa

 

 

Cikin takunsa mai ƙyau da kuma tsari ya shigo sashen Sarki Abdulhamid Ƙaisa,sarkine mai mutunci da mutunta mutane kana ganin Sarki Hamid kasan shine mahaifin yarima Abeed don kamarsu ɗaya sosai sai dai yarima Abeed yafi mahaifinsa fari da kuma yarinta.

 

 

“Allah ya ƙara maka lafiya ya Abee,ina gaisheka ina ƙara gaisheka Sarki mai adalci Allah dai ya barmu da kai cikin ƙoshin Lafiya”.

 

ɗan murmushi ya yi irin na Abeed ya ce”ina sonka ɗana,Allah dai ya zaɓa maka mata salihar baiwa wacce duk zamuyi alfahari da ita a masarautar nan,sai dai har yanzu baka kawo mana gimbiyar ba haryanzu, har mun gaji da zaman jira”.

 

Ɗan murmushi ya yi yana sosa ƙeyarsa ya ce”Abee ka tayani da addu’ah don yanzu samun mata ta gari shine komai”. Fatan alkhairi ya yiwa ɗan nasa mafi soyuwa aransa.

 

“Abee insha Allah gobe zan koma aikin nan namu atayamu da addu’ah Allah ya bamu nasara”.ɗan ɓats fuska Sarki Hamid ya yi don arayuwarsa babu abin daya tsana irin aikin Hamid don aiki ne na hatsari wato aikin soja.

 

Ganin hankalin mahaifinsa ya tashi yasa ya zauna sannan ya ce”Abee agurinka kawai na ke samun fatan alheri na wannan aikin nawa,saboda Ammi babu abinda ta tsana irin aikina,kuma babu yadda zanyi ne shiyasa,na tayin addu’ar Allah yasa idan ba alkairi bane aikina Allah yasa inji ya fita daga raina amman kullum ƙara kusanta na ya ke”.sai ya yi kalar tausayi don haka Abee ya ce”babu komai Yarima Allah ya dafa maka ya baka abinda ka keso duniya da lahira,ya tsareka da dukkanin wani sharri”.murmushi Abeed ya yi don jin daɗin addu’ar mahaifinsa ya ce”Amin Abee na gode.

 

Wannan abinda Sarki Hamid ya saba bawa Abeed yauma shi ya bashi yana ƙara ja masa kunne akan ya kula dashi sosai kamar yadda zai kula da kansa.

 

 

 

*miss green ce*

Leave a Comment

error: Content is protected !!