
BATA KAI KISHIYA BA HAUSA NOVEL
BA TAKAI KISHIYA BA
Na “`MRS BASAKKWACE“`
*GASAN MATASAN MARUBUTA 2021*
Rukuni na biyar
*SHAFI NA ƊAYA*
“Wai Ruƙayya ba kiji mai nace miki ba ne?Taɓa baki wacce aka kira da Ruƙayya, ta yi tare da gyara ɗaurin kallabi ta turashi can bayan ƙeya tai murmushi duk da maganan ya taɓa mata zuciya, amma ta daure ta danne tai namijin ƙoƙari ta ce,”Abban Nanah naji mana ƙwarai da aniya, aure nan da minti sittin masu zuwa za’a ɗaura ma ,so ka ke in fashe da kuka in ɗaura hannu akai inbi titi ina kuru-ruwa ko yaya?
“ko kuma in ce ka fasa?, munafinci ne fa banso irin naku na maza, za kazo kana cemin kyautarta aka baka, Allah ya kyauta yasa albarka, Allah ya haɗa kawunan mu,donni ba kishiya ta bace , *MATAR RUFA’I* ce, innai hauka na tada hankalina wazai aure ƴaƴana ƴammata uku, ɗaya ta isa aure ko yau na kaita zama za ta yi,don haka fatan alkhairi na ke yi maka,Allah ya baka abinda za kaci da mu”.
Tana gama maganan bata jira mai zai ƙara c loewa ba, ta miƙe ta shige bedroom ɗinta
Tunda ta fara magana, ya saki baki da hanci da kunne,yau Ruƙayya tayi matuƙar bashi mamaki, ina duk zafin kishin ta ya tafi ,wanda akan kishin sa ko ƴar aiki taga yana ma magana sai tayi mata rashin mutunci ta koreta, yau shike faɗa mata zance aure take gwada halin ko in kula cabɗi, ƙaran buga ƙofar bedroom ɗinta da tayine ya fargar dashi ashe hara gama surutun tabar wajan.
Ajiyan zuciya yayi mai nauyi ya zura malummalum ɗinshi ya fita inda abokanan sa ke jiran sa, aminin sa Auwal nata kiransa
~ASALIN LABARIN~
Ahmad Rufa’i Musa shi ne asalin sunan Abban Nanah, haifaffen garin dange shuni ne ,sunan mahaifinshi Malam Musa babban manomi ne, yana kaiwa duk wani kasuwan ƙauye yana saidawa,sunan mahaifiyar Rufa’i Dije,Dije tana da haƙuri,wani fannin kuma akwaita da faɗa,ƴaƴan su biyu Allah ya albarkace su dashi duk maza,Rabi’u shine babba sai Rufa’i,Rabi’u da Rufa’i dun samu tarbiya a wajan iyayensu,mahaifin su yana son boko duk da baiyi ba,amma baiyi ƙasa a guywa ba wajan sa ƴaƴanshi,duk neman sa a kansu yake ƙarewa, ga kuma fannin mahammadiya.
Rufa’i na masters ɗinsa, fannin kasuwan ci a ɗan fodio suka haɗu da Ruƙayya da ita lokacin ta shiga aji ɗaya, Ruƙayya fara ce tassss mai matsaikacin tsawo tana da kyawon da biro bazai iya rubutawa, lokaci ƙanƙani suka ƙulla soyayya sosai, Ruƙaiya tana da mugun kishi da ko mafarki tayi ta ganshi da mace, sai tace da gasken ma hakane,da yaga tafara masa masifa yasan mai yafaru saide yai ta kallon ta,in taƙaice muku kusan kullum sai sunyi faɗa sun shirya saboda kishinta,ko course mate ɗinshi mata yadena kulawa saboda ita.
Yana gafda haɗa masters ɗinshi ya tura iyayenshi gidansu maryam akai gaisuwa aka kai kayana nagani ina so,ba’a sa ranan bikin mai tsawo ba, kasan cewar iyayen Ruƙayya suna da rufin asiri.
BATA KAI KISHIYA BA
Asalin su ƴan gwadabawa ne, zama ya kawo mahaifinsu cikin sokoto kasuwanci tumaki ,sunan mahaufin Ruƙayya Abdullahi, mahaifiyarta kuma Atiƙah, ita ce babba sai ƙanan ta biyu Aƙil da Usama,mahaifinta yaci burin tai karatu tazama Doctor,mahaifiyarta tace gwamma yai mata aure ta ƙare karatun a ɗakin ta,nan ya umurce ta da takawo wanda takeso ta fito da Rufa’i.ƙawar Ruƙayya ɗaya da suka taso tare Halima
Bayan wata biyu aka wanketa aka kaimai ita ɗaƙi,sabon gidan da mahaifinshi ya gina mai a kaduna road,tundaga lokacin kishi ya ƙaru yaci uban nada,ko ƴar aiki ta kalle hotonsun dake manne a falo sai ta koreta annemo mata wata,a haka harta samu cikin farko ta wahala sosai amma haka take aiki,batason ƴar aiki tazo ta kallan mata miji,koda ko tsohuwa ce.
Lokacin da tahaifa ɗiyarta ta farko da taci sunan mamar Rufa’i wato Khadija suke kiranta da Nanah, gida ta koma wanka, harsai da tayi arba’in biyu ta dawo,anyi-anyi abata ƴa ta rinƙa temaka mata tace bataso zata iya, haka aka haƙura aka ƙyaleta.
BATA KAI KISHIYA BA
Bayan shekara bakwai ta ƙara haihuwar ɗiya mace, lokacin Nana har ankaita boko play class, yarinyar taci sunan mahaifiyarta ana ce mata Ummie, daganan bata sake haihuwa ba,Ummie da Nanah suna samun gata da kulawa daga iyayensu,gashi suna ƙaunar junan su sosai,saida Ummie ta shekara tara kafin ta ƙara samun ciki ta haifo Hauwa’u,Nana na primary five,yayinda Ummie ke primary two,Nana da Ummie kama suke da ita kamar antsaga kara yayin da Hauwa tabiyo Rufa’i kamar an tsaga kara farin Ruƙayya ne kawai ta ɗauko shima ba sosai ba tafi su Ummie duhu ,rayuwa taci gaba da tafiya musu da daɗi ba daɗi,ko halshe da haƙori suna samun saɓani balle mutum da mutum,kishin Ruƙayya ko ba abinda ya rage shi.
BATA KAI KISHIYA BA
18years latter,lokacin Nana ta zama budurwa sosai tana zuwa SSU yayinda ,Ummie ta ƙare secondry school sun zana jamb tana neman admission a poly don mass com take so ta karanta,Hauwa na primary 6.
_WANNAN KENAN_
BATA KAI KISHIYA BA
Ruƙayya ɗakinta ta koma tana kai komo,lallai Rufa’i tun tuni bai mata kishiya ba sai yanzun da ta tsufa ƴaƴanta sun isa aure,sannan tsabar wulaƙanci yarasa sanda zai gaya mata zai mata kishiya sai ranan bikin sannan awa ɗaya ya rage,zama tayi bakin gado ta rafka ta gumi,ta gode ma Allah da yaranta basa gida Nana da Hauwa sunje makaranta yayinda Ummie taje mabera gidan kakanin ta,da sunji mugun abu da safe tsaka
BATA KAI KISHIYA BA
*********
Ƙarfe shaɗaya aka ɗaura aure Rufa’i da Rashida,sai farin ciki yake da murna kamar anbashi kyauta ɗan mutum da uwarsa.
Yana cikin abokai sai gaisawa suke dashi suna masa murna.
Ɓangaran amarya ma farin ciki da murna take,sai hotina ake da ƙawaye .
BATA KAI KISHIYA BA
Rashida kenan bazawara ce auranta uku,bata haihu ko ɗaya,kasancewat tanw da kwaɗayin abin duniya,abakin shagon na shaddodi ta ɗau number sa,tun tana kira in yaji mace ya kashe har yakai da ya fara kulata,a lokaci ƙanƙani suka ƙulla soyayya.
Inzai shigo gida kashe waya yake gudun ɓacin ran Ruƙayya. Rashida dai akwai salon iya sace zuciyar maza……!
BATA KAI KISHIYA BA
SHARED
ND VOTE PLEASE
BATAKAI KISHIYA BA
“`Na MRS BASAKKWACE“`
*SHAFI NA BIYU*
Ƙissa da kisi-sina yasa tai nasaran sace zuciyar Rufa’i ba kyau ba, in da kyau ne ba abin da zaiyi da ita, sannan kuma ta dafa ta bashi, asalin su ƴan gobir ne sabon birni, sunan mahaifiyarta Sa’adi, Sa’adi akwai son duniya kullum bata godiyan Allah da abinda mijinta ya kawo , mahaifinta Sa’adu,ita kaɗai suka haifa,mahaifinta sana’an saida tabarman kaba yakeyi,mutumin kirki mai gaskiya da riƙon amana, yayinda sam tunda ta taso itama ta raina sana’an mahaifinta inda take ganin ƴaƴan masu kuɗi take sha’awar dama ita ce, bata nuna ma samari gidan su lokacin da ta kai minzalin girma, suma da yake samarin ƴan ƙarya ne , don ita wani ɗan siyasa Alhaji Bukar Maihula,mai gidan babanta inda yake gadi in dare yayi shi yake ɗaura mata aure,amma daga kujerunta suke gane ƴar talakawa ce,don duk ɗiyan Bukar Maihula komi order ake daga turai,itama sai bayan aure take gane duk kanwar jace,anan zata tada ɓalli bata ga ta zama ba,Inna mahaifiyarta taje tai musu ruwan rashin daraja ,dole kasakar mata ƴa, don tace bazata zauna a talauci ba ƴarta ta zauna atalauci ai abin sai yai musu yawa.
Tunda taji labari Rufa’i ta ɗaura aniyar auran sa, tunda ko ta samu ta shawo kansa ya fara kulata suka kai sunan shi gidan malami, inda aka tabbatar musu zai aureta, auran ko bai ja wani lokaci ba aka sa ranan biki.
BATA KAI KISHIYA BA
Duk wainar da ake toya wa Ruƙayya bata sani ba sai ranan bikin yake gaya gaya mata, bayan ya shigo mata da kayan faɗan kishiya.
*WANNAN KENAN*
Ƙarfe biyu da rabi dai-dai suka shigo don Nanah Abban su ya saya mata motor 406 ita ke ɗauko Hauwa a school in tana dawowa, in kuma bata da lecture haka zata je ta ɗauko,bayan ta ɗauko Hauwa ,suka biya gidan kakar su suka ɗau Ummie suka wuto gida.
Da sallama suka shiga falon ,turusssss sukai ganin akwatina sababbi,dai-dai lokacin Ruƙayya ta fito daga bedroom ɗinta.
“Ammie wannan kayan waye “,inji Ummie da take kallo Ammie su.
“Kayan faɗan kishiya ne da ubanku zai ƙara yau”,cikin gatsali tabata amsan.
BATA KAI KISHIYA BA
Haɗa baki sukai alokaci ɗaya suka ce *KISHIYA* Ammie?”
“Tou na taɓa wasan-nan daku ne?
“Kai Ammie kode wasa yake miki?,faɗar Nana da take zama kan kujera.
“Yanzun ma haka an ɗaura”,tabasu amsa ataƙaice.
Dukkan su zama sukai suka tasa akwatin a gaba kowa da abinda yake saƙawa, saida Ruƙaiya ta fito daga kitchen tai musu magana su tashi suci abinci,karsu damu da wannan auran da Abban su zai ƙara,kafin suka tashi suka je suka sauya kaya zuwa masu sauƙi suka fito suka ɗan tsakura abincin,wuni sukai,wuni sukai suku-ku kamar ƙwai ya fashe musu aciki ba kamar da ba,da suke zama cikin farin ciki da annashuwa.
Karanta kishiya bayan mutuwa
Ƙarfe tara suna zazzaune dininig suna cin abinci yau ba hira kamar anmusu mutuwa,suka fara jin diran motoci a cikin gidan su ana guɗa,alama amarya ta iso.
Ruƙayya jitayi gabata yayanke ya faɗi,ta danne zuciyarta don ƴaƴanta lokaci ɗaya ita suka zuba ma ido suga action ɗinta,sai suka ga tana murmushi.
Hayaniyan yana ƙara kusan to part ɗin alaman ankusa shigowa da amarya.
Miƙewa Ammie tayi ta koma cikin falon ta zauna ta naɗe ƙafa, ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tayi tana girgiza ƙafa, shigowa da amaryan akayi ana guɗa.
Gaban Ruƙaiya aka ajeta wata dattijuwa bayan sunyi sallama.
Amsawa tayi ta fuskanta sake tana murmushi.
Bayan sun gaisa a mutunce, Ruƙayya take amsa mata.
“Munkawo amaryane ,ni Gwaggon tace,dan Allah ga amana mun baki amatsayin ki na uwar gida, Rashida yarinya ce “.
Murmushi Ruƙayya tayi tace,”Gwaggo wa ya ce miki ana ba kishiya amanar kishiya, tazo ta kwanta min da miji sai in amshi amanar ta ƙarya ma kenan, ko da yake ba kishiyata bace, don bata kai bata isa ba inyi kishi da ita, *BATAKAI KISHIYA BA* sunan ta, sannan shin naga gidanan part ɗina ne kawai awani part za’a sata?.
Gwaggo da jikinta yayi sanyi da duk wanda ke tsaye a wajan, kanta Rashida tasha jinin jikinta dajin kalaman uwar gidan ,tasan tabbas Rashida yanzun tasamu burinta gidan kuɗi, amma wannan kishiyan nata za’ai daru da ita.
“Ƴarnan shi Ahmadu yace za’a bada key ɗakin shi”,faɗan Gwaggo.
Murmushi Rashida tayi ta taɓa baki tace,”tou ai bai gayamin ba,ita amaryan ƴar matsiyata ce da baza’a kawota da kaya ba,uhm duk bai ma dameni ba,kunga duk jerin ɗakuna-nan ko wacce ƴa da sunan ta a sama,babu sunan wata a ciki, ɗakin mijina ko ban kwashe kaya ba,zaku iya ajeta a falo ta kwana in yaso gobe na kwashe komi nawa ta iya sa nata ta kwanta banda lokacin aiki yanzun.
Tana gama magana ta-tashi ta wucewar ta,su Nana ganin mahaifiyar su ta shige yasa suma suka tashi kowa ta shige bedroom ɗinta.
Duk jikin su yayi sanyi,daga cikin ƙawayenta ne suka fara zage-zage ta inda suke shiga batanan suke fita ba, da ƙyar Gwaggo ta shawo kansu sukai shiru, kiran Rufa’i Gwaggo tayi ta shaida masa ,hankalin shi ya tashi yasan bai mata dai-dai ba.
Sa Auwal yayi da sauran abokanan su suka kwashe ƴan kawo amarya,Gwaggo ta tafi itama bayan ta ma Rashida nasiha, sai kuka take, bata jima da tafiya ba Rufa’i ya shigo gabashi na faɗi,don yana tsoron haɗuwar shi da Ruƙayya, inda aka aje Rasheeda nan yazo ya isketa ba kowa a falon sai ƙaran Tv da Ac.
Haƙuri ya bata kafin yaje ya ƙwan-ƙwasa Ruƙayya, duk ƙwan-ƙwasawar duniyar nan taƙi buɗewa balle ta bashi key haka ya haƙura ,ya buga ma Nanah ta buɗe ya roƙeta Hauwa tadawo ɗakinta su kwana a ɗakin Hauwa, badon ranta yaso ba ta amince, kafin ya lallaɓa Rashida suka shiga ɗakin Ummie.
Koda labari yakai ma Inna Sa’adi tarinƙa zage-zage,da ƙudirin sai tayi maganin kishiyar ƴarta-ta, mai yasa ba’a dawo mata da ƴarta ba, da ƙyar aka bata baki ta haƙura.
Mutane da yawa ko Allah ƙara suke ma Rashida kwaɗayinta yakai ta inda zataci ubanta.
Washegari ko sai 11 suka farka kasancewar yau ba school.
Koda Ammie ta dafa abinci iya cikin ta dana ƴaƴanta tayi, ko shi ba tayi dashi ba kuma ta ce kar ataɓa mata kaya akawo mata nata daga gidan su, bayanda zaiyi saide ya fita yaje ya sayo musu abinci.
Saida la’asar kafin Ammie ta kwashe kayanta a bedroom ɗin Abba,shima saida ya kira Ummah ta yafaɗa mawa ta kirata tai mata faɗa da nasiha, Ruƙaiya tasha kuka sai alokacin zuciyar ta yai sanyi, taji ta dena jin ciwo da raɗaɗin ke damun zyciyarta game da auranan
Zaman doya da manja akayi atsakanin su hartai kwana bakwai,sai Rashida ta sakko kaya taci ado tazo falo ta kame a kujera tana ma miji yanga da rangwaɗa, sai Nana taje ta sakko ko Ummie,don kayan akwatin raba ma Ummie da Nana Ruƙayya tayi,duk iskanci Rashida da gigiwar ta Ruƙayya bata shiga sabgarta ,ta barta da Ƴaƴanta don bata kai tai kishi da ita ba, abin na matuƙar cin ma Rashida tuwo a ƙwarya, duk iskancinta da iya shegenta ko kallo bata isa Ruƙayya ba.
Komai Rufa’i zai sayo ma Ruƙayya inde iri ɗaya dana Rashida ne saide ta miƙa masu Nanah tace ita ba sa’an yarinya ba ne, saide su Nanah.
Innata ko tabi bokayen saide suci kuɗinta ba biyan buƙata.
Ruƙayya ko hatta abincin Rashida basaci, inko ka gansu zaune inuwa ɗaya da ita tou Rufa’i nanan,sannan Ummie ko Nanah ɗaya yasa kaya irin nata da tasa, da ya fita ko sun watse.
Koda Rashida ta ɗauko salon sa riga da wando tuni Ruƙayya ta taka mata burki tace ba hotel bane, ba kuma gidan karuwai bane, dole tasa Rufa’i yai mata magana ta dena sawa
Rashin jituwa ya fara shiga shiga tsakanin amarya da ango, don da gan-gan Ammie ke sayan abu ta fito falo Ummie taje waje ta kira ta suyi ta waya kamar Rufa’i ne ya saya, tayi kamar da ƙawarta take waya, abin na ƙona zuciyar Rashida, harta fara masa gori da habaici, gashi yanzun ba arziki ya aje kuɗi saita sace, ayi juyi duniya ta ce ba ita ba ce.
Har yakai yanzun ta dena fitowa falo tana zama don yaran su rinƙa hira da turanci, itako bata jinko zo in kashe ka da turanci.
Kullum tana kiran Mamanta tana mata kuka akan ta ɗauka mata mataki amma ina duk bin bokayen Inna takasa,anayin maganin amma baci gaba.
Ruƙayya da salon kwantaccen kishinta taringa haɗa su faɗa tsakanin su,watan su biyu Rashida ta tada ɓalli bata son auran cin mutuncin yau daban na gobe daban ,daga ƙarshe ya saketa saki biyu,ko kwana batayi agidan ba ta koma gida.
Ruƙayya ko da ƴaƴanta murna wajan su kamar mi,su za’azo a gwada ma iskanci a iske su a gidan su.yanzun zaman lafiya dajin daɗi ya dawo masu kamar wata Rashida bata zauna agidan ba.
Yanzun Rufa’i ko tunanin ƙara aure ba shiyi,saboka yayi baiji daɗi ba.
Ƙarshe!
PLEASE SHARE AND VOTE
MASSIFAFFAN KISHI
*GASAR MATASAN MARUBUTA 2021*
JIGO: LABARIN KISHI
_BABI NA BIYU KUMA ƘARSHE!_
ganin numfashin Fareedah yaƙi daidaituwa ga kuma hayaniya da hargagin da Na’imah ke yi ya sashi daka mata wata razananniyar tsawa da ta sanya ta firgita, ba shiri tayi baya ta zauna amma bata daina surutan da take. “sai naga bayan ki, wallahi sai na kashe ki tunda dama tun farko na gaya maki ki fita a harkar mijina, Hisham nawa ne ni ɗaya dan ni kawai aka halicce shi, so yanzu tunda ke kika kawo ƙafarki har gidana! bazan bari ki fita hakanan ba batare da nayi maki gargaɗi da babbar murya ba, karuwar banza mai bin mazan mutane.” ta faɗa tana yunƙurin miƙewa tayi kansu gadan-gadan, bai bari ta ƙaraso ya saki Fareedah da niyyar koya mata hankali. da sauri Fareedah ta riƙo hannunsa tana girgiza masa kai hawaye nabin kuncin ta. “Yaya don Allah karka dake ta saboda ni, na tabbata ta kasa fahimta ta ne saboda kishi ya riga da ya rufe mata ido, ni kaina ba’ason raina nazo gidan nan ba saboda ka gargaɗe mu da yin hakan, nayi ta kiranka ne dan in tuna maka gobe karka manta ka biyo min da fils ɗin nan da na baka ajiya, amma kaƙi ɗaga wayar shiyasa nai maka text _’Assalamu Alaikum Barka da safiya, dan Allah karka manta da kayan nan ko kuma ka faɗamin inda zamu haɗuwa nazo na karɓa ina ganin hakan zaifi tunda dama haka muke gudun matsalar matar ka.’_ “abinda na faɗa a saƙon kenan fah Yaya” Hisham yayi shiru yana nazarin kalaman ta cike da son tabbatarwa, Fareedah tace “ka sakar min hannu zan wuce gida” “no ki bari muje asibiti a duba ki” “a’a naji sauƙi sosai ka sakeni” ba musu ya sakar mata hannu tayi hanyar fita tana kuka.
Cikin matsanancin fushi Hisham ya nuna mata ƙofar falon yace “tashi ki fice min daga gida tun kafin na ɓata miki rai” maƙe kafaɗa tayi tace “wallahi bazan fita ba! ka ma isa ka koreni daga gidan nan saboda wata ƴar iska kana wani fakewa da ƴar uwarka ce? ni dama na jima ina zargin akwai wata ƙullalliya a tsakanin da Fareedah, sai gashi yau anyi walƙiya mun gani, maganar tafiya gidanmu kuwa bai taso ba dan kuwa zama daram kuma yanzu na soma rabaka da ƴan mata, Mtsss.” ɗaukar Nu’aiym dake kuka yayi ya kaisa ɗakin mai kula dasu, ya fito fuskarsa ɗauke da fushi da tsananin ɓacin rai sosai, tana tsaye riƙe da Hijab a hannunta ta hangosa riƙe da wata ƙatuwar bulala ai da sauri tayi hanyar waje tana neman taimako, da taimakon mai gadi ta samu ta fice daga gidan, ta iso bakin titi ta samu abun hawa ta shige bayan ta masa kwatancen gidan su.
Cikin kuka ta yiwa Mom ɗinta bayanin komai, faɗa sosai tayi mata tare da nuna mata kuskuren ta “ƙarya kike kice zaki hanasa zumunci da ƴan uwansa, dan ubanki kin manta cewar shi ɗin mijin mace huɗu ne? ubanki ma mata nawa ya aura? dan haka ki kiyaye ni yarinya dan wallahi kika saki yaron nan mai haƙuri da nutsuwa ya juya maki baya kin shiga uku, banason hauka da rashin hankali, muddun kika fusata shi ya sakoki sai dai ki nemi gidan wani uban dan kinsan halin mahaifin ki.” daga haka Mom ta tashi ta shige ɗakinta tabar Na’imah zaune a falon tana dizgar kuka tamkar ranta zai fita dan sai yanzu take hango tarin wautar da tayi da kuma irin haƙurin da mijinta yake da ita. daddare ma haka Alhaji Sulaiman ya tisa ƴarsa a gaba yayi mata tatas ya bata rashin gaskiya. wasa-wasa har kusan sati biyu Hisham bai sake waiwayar Na’imah ba, bawai dan bata ransa bane kawai so yake ya koya mata hankali ta nutsu ta dawo hankalin ta sannan ta farga da cewar shi ɗin mijin mace huɗu ne duk da bashida ra’ayin hakan. itama sosai take kewar mijinta da tausayin shi, tayi laushi sosai tayi danasani marar amfani, ta rame sosai duk ta fita hayyacin ta, ganin haka Alhaji Sulaiman ya samu Alhaji Kabir su ka yi magana suka samu Hisham su ka yi masa nasiha suka kuma umarce sa akan ya haƙura ya mayar da matar sa ɗakinsa ko dan tilon ɗansu, kai tsaye kuwa ya amince musu. bayan kwana biyu kuwa Na’imah ta dawo gidan mijinta Hisham, sosai ta canja amma kishin nan kam yana nan amma ta ɗan rage akan daa!, sosai suke gudanar da rayuwar auren su bisa tsari da kuma mutunta juna. bayan wata tara cikin ikon Allah da hikimar sa Na’imah ta haifi santaleliyar yarinyar ta Nasreen…
ALHAMDULILLAH!!! ANAN NA KAWO ƘARSHEN GAJERAN LABARIN NAN NA MASSIFAFFAN KISHI, ALLAH YA BAMU IKON ƊAUKAN DARUSAN DAKE CIKI YA YAFE MIN KURA-KURAN CIKI.
NU’AYMAH ABDULL
Agaskiya naji ddn wannan novel din
Shiga