Hausa Novels

Batsa Novels Complete

Batsa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Batsa Novels Complete

Tag: Batsa Novels Complete

[01/10, 9:27 pm] +234 703 966 0069: _*ABIN CIKIN RUHINA*_

 

*{RE-POST}*

 

Mrs bb

Mom muhseen.

 

Wattpad name

Humaira7531.

 

Free book

 

🅿️…….1

 

*1998*

 

Wani yaro ne da ba zai ga za shekara tara zuwa goma bah, ya tusa mahaifiyarsa ga ba kuka kawai ya ke saboda irin yadda ya ga halin da take ciki na tsananin labour………..murk’ususu take duk ta fice da ga hayyacinta, fita ya yi karo na babu iya ka tsakar gidan,wani d’aki Ya shiga Ya na kuka.

 

“Antu lantana ki yi hakuri ki zo ki taimaki Maah kar ta mutu……ga ta can ta na yin irin abun nan kamar na mutuwa………Cikin Wata irin tsawa da tun da ya zo duniya bai tab’a jin irin ta bah……. Tace,

 

“Idan na sake ganin bak’ar fuskar ka Cikin d’akin nan wallahi sai na yi maka dukan da za, a kasa ganeka…….fita anan shegen yaro Mai shegen naci, nima halin da nake ciki kenan fita.”

 

Haka ya juya ya na kuka bai koma d’akin ba waje ya fita ya shiga wani gida da ke kallon na Su da kukan sa……tun kafin ya fad’i abunda ya ke so matar ta tare shi cikin kulawa………

 

“ya a Kai *Areef*?lafiya kuwa? me ya faru gidan naku?maman ka tana lafiya kuwa?.”

Duk lokaci d’aya ta jera masa wad’annan tambayoyi kamar tana yiwa wani babba.

 

Yana shashshekar kuka muryar ta kasa fita sosai yace,

 

“Maah…….maah…….za ta mutu…… Ki taho karta mutu…..”

 

Cikin tashin hankali ta jashi suka fice ko gidan bata tsaya rufewa ba.

Sadda Su ka je har faya ta fashe tana nishin wuya d’an na son fitowa……..waje ta kora shi ta shiga tai makonta Cikin yar dar Allah sai ga jaririya ta fad’o wani wahalallen nishi ta sauke……..dan danan jaririyar ta fara tsanyara kuka asan dai ta iso duniya…. Cikin lokaci k’an k’ane aka gyare su sannan aka d’ora sanwar wanka……….Areef sai tsallen murna ya ke kamar ya anshe ta hannun maah da ke bata nono, d’akin da Areef ya fara shiga ne Wata mata ta fito Cikin tashin hankali tayi waje………duk kiran da Anni ke kwala mata ba ta saurare ta bah, zuwa can ta dawo nan ma Anni sai tambayarta take ta yi mata banza………ita sai ma ta k’yaleta…. Lantana aka fiddo aka Kai Asibiti.

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
 

Alhaji farouk haifeffen garin Katsina ne,ne man Arzik’i ya kawo sa gari Abuja. Alhamdulillah an same shi kuwa don yanzu ya na zuwa Dubai da Sudan sarin kaya,matansa biyu Saudah ita ce mace ta farko da Allah ya bashi wacce A kullum ya ke Alfahari da ita, saboda aurenta shine Abun da ya d’aukaka shi har ya samu rufin asirin Allah,ya na masifar son matar sa sai dai matsalar farko da suka fara fuskanta, ita ce matsawar danginsa akan rashin haihuwarta da wuri, don alokacin sai da suka shekara goma da Aure Saudah ba ta yi ko b’atan Wata ba…….tsegumi dacece kuce ya ringa tashi akan wannan lamarin Idan ta shiga mutane an ringa harararta kenan, gashi Saudah ba mafad’aciya bace za ka jima ka na mata abu ba za ta tab’a tan ka ma ba,sai dai ta sha kukanta idan ya na kusa ya lallasheta ya ba ta hakuri, don idan ba shi ya bata ba bai San me zai ce mata ba, ana Cikin hakan tafiya ta same shi, bai saurari kowa bah ya d’auki matarsa suka cana Dubai…………wannan tafiyar ta tun zura mahaifiyarsa.

“tace Don nayi ma ka Maganar k’arin aure shine ka gudu kaida matarka ko, to kaje ko inane ka dawo Ina nan Ina jiranka.”

 

Basu dawo ba sai da suka shekara biyu.

 

Abun mamakin shine ganin Saudah da su Kai da yaro, Areef Kenan.

nan ma wata maganarce tai ta tashi, matar farouk ta haihu saboda bai d’auke mu bakin komi ba shine babu Wanda ya sanar ma.

………..hakan bai hana wannan auren ba Saudah tayi kuka kamar idon ta zai fita saboda bak’in Cikin halin da ta ke ciki, me ta yi masu su ke mata irin wannan k’iyayyar haka mai zafi.

 

Haka saudah ta ci ga ba da zaman hakuri da dangin mijinta, ta na ci gaba da kulawa da yaronta Areef wanda ta ke ma wata kalar soyayya, Wanda idan so samunta ne ko k’uda karya ta b’a mata shi………….wata biyu da da wowarsu akai bikin Alhaji farouk da d’iyar k’awar mahaifiyarsa……..ko kad’an ba ya son lantana, ba ma lantana kad’ai ba shi duk wata mace kallon na miji ya ke mata idan ba saudar sa ba, jinta ya ke har Cikin *RUHINSA* kuma ya yi alkawarin har abadan ita ce *ABIN CIKIN RUHINSA* bai tab’a cewa ba ya son lantana ba,Ya barwa ransa don Annabi Muhammad [S A W ] Ya yi hani akan furta k’iyaya ga wanda baka so.

 

Zaman lantana da Saudah kamar zaman doya da manja,ko misk’ala zarratin lantana ba ta Kaunar ta,haka ko ya Areef ya rab’eta sai dai duka shi yasa Saudah ke kaffa kaffa da Yaronta…….Areef na da shekararsa hud’u Saudah ta sake samun wani Cikin, y’an uwanta sun ta ya ta murna da mijinta, mace da namiji ta haifa aka sa ma macen *SHAHIDA* namijin kuma *SHAHID* zan iya cewa wannan haihuwar ta janyo ma sauda wata irin kauna wajen dangin mijinta,

Aka fara juya ma lantana baya, yayin da su ka ta so ta gaba kan cewar bata iya komi ba sai dai taci ta yi kashi.

wasa wasa sai da lantana ta shekara biyar ko b’ari ba ta yi ba, nan fah kuma tsanar da ake ma Saudah ta dawo ga lantana,saboda daman ko kad’an ba ta ganin girman innah mahaifiyar Alhaji farouk,sai ta yi wata uku ba ta je ta gaida ta bah, idan gidan ta zo a wulak’ance ta ke kallon ta……….su ma sauran dangi duk haka take masu……. Kan Ka ce me sun dawo da kulawarsu A kan Saudah wadda Su ke ganin da can zalintar ta Suke.

……yanzu kuwa kamar su goye ta su ke ji………..haka lantana ta ko ma saniyar ware saboda bak’in halin ta,wanda hakan da ta ga su na mata bai sa ka ta canza hali bah……….haka rayuwar ta ci gaba da tafiya Areef ya na ji da y’an uwansa nan mak’otansu akwai matar abokin Alhaji farouk……..lawisa yaran ta biyu, namijin sa,an Areef ne Macen kuma sa,ar Su SHAHIDA,tun da aka auri Saudah su ka kulla k’awance,don Mazajen su ma aminnan juna ne shiyasa su ma su ka had’a kansu abun gwanin sha,awa………wanda takai har dangin Saudah sun san da lawisa,ita ma lawisa danginta sun san Saudah,

Akwana A tashi ba wuya wajen Allah, lantana su ka samu Ciki kusan lokaci d’aya da Saudah…………wanda shine yanzu sauda ta sauka, ita kuma ta na kan hanya da sauran Aiki tukun……….Alhaji farouk ba yanan ya je Dubai akan wani kasuwanci da yake Fatan ya tabbata, Wanda idan hakan ta samu ba karamar nasara ya yi bah,don arzikin sa zai linka na da fintinkau……….da zai tafi twins suka matsa akai Su wajen ummin Dubai [yayar saudah ce d same father d same mother]

Dole ya tai da su don ganin halin da Saudah ke ciki na haihuwa yau ko gobe, koda akai ma Areef tayin zuwa yace Aa shidai ya na tare da Maah d’insa………….

 

*wannan kenan*

 

[Mrs bb]ce kuma

Mom muhsen

[01/10, 9:27 pm] +234 703 966 0069: _*ABIN CIKIN RUHINA*_

 

 

*{RE-POST}* @2019

 

Mrs bb

Mom muhseen.

 

Watt pad name

Humaira7531

 

 

🅿️…….3

 

Alhamdulillah gida ya tsaru iyakar tsaruwa,babban gidane mai fat Kala Kala wanda saboda girman Abota irin ta su Alhaji farouk yace da Amininsa jafar yazo su zauna tare,har kuka yayi saboda farin ciki haka suka dawo gidan rana guda, komi sabo aka loda masa yayinda tuni angyaare ma Inna wancan gidan ba zaka tab’a cewa shine bah.

 

Rayuwar ta cigaba da kasance masu Cikin jin dad’i da kwanciyar hankali,yayin da Wata irin shak’uwa mai K’arfin gaske ta shiga tsakanin *AREEF* da k’annensa *khairat da salma* idan Sun dawo makaranta shine wankansu ya shiryasu ya zubo abinci yaringa basu har sai sun koshi, sannan assessment d’insu zai zauna ya tusasu gaba yana guarding d’insu yaga Sunyi shi lafiya lau, Areef saboda k’annensa ko fita baya yayi, Duk nacin *mujahid* haka zai rabu dashi, haka shahid da shahida Duk yadda suka so Cikin weekend ya ringa binsu shopping sai yace bazai bisu bah, saboda suna cin zalin sweetheart dinshi,dole sukai hakuri saidai driver ya kaisu shikuma Ya ware rana ya kaisu da kanshi………wata guda kenan da kammala secondary d’insa,tunda twince suka girma Maah ta hana yaringa masu wanka da shiryawa,tunda yanzu ko wacece zata iya yiwa Kanta wanka da shiryawa, yanzu suna js one yayinda shahid da shahida Suke ss2, Muhajid tare sukai graduation da Areef, Neenah ce take js3.

 

Shirye shiryen tafiyar Areef da Muhajid ake zuwa UK jamia,wanda idan suka tafi baza su dawo bah sai Sunyi har masters d’insu……..

 

Motarsu na tsaya wa suka fito Aguje suna kyalkyata dariya,kowa so take ta riga y’ar uwarta isa cikin gida wajen yah Areef kafin Su shiga saiga su sun fito shida mujahid Aguje sukai kanshi, dariya suke masu shida mujahid……kafin ya ankare *salma* ta mamuk’eshi tana dariya har da yiwa *khairat* gwalo aikuwa me zatayi banda kuka, bilhakki da gaskiya ta shige gidan tana rera kukan shagwaba,duba Maah tayi bata ganta ba yasa ta nufi b’angaren Anni tana shiga sukai kacib’is Anni ce ta tatareta.

 

“lalalala kairyn Anni waya tab’aki zo zo taho muji.”

Ta jata jikinta Maah tace,

“Uhm bai wuce rigirmarsu ita da salma, yanzu haka riganta tayi isa wajen Areef.”

 

Annin tace,

“wai haka ne yar gidan Anninta.”

Wani kukan ta sake fashe wa dashi tana cewa,

“Anni kingani salma ko, kullum sai ta ringa rigana wajen Yah Aree,kuma nace mata yau ta barmun in rigata shine ta k’iya,gasu can suna mun dariya.”

……….ta sake rushewa da kuka.

 

Dariya Maah tayi tace,

“ai na gaya maki kullum rigimar kenan, salma ta rigani,salma ta rigani tunda ke lusara ce komi babu hanzari,ba dole komi salma ta rigaki ba ko wanka da shiryawa sai bakina yayi tsawo kike gama wa inhar Areef baya nan.”

 

Anni zatai magana Areef ya shigo rik’e da hannun salma, har tayi wanka da ga dawowar ta ga lollipop nan Areef ya bata tana ta sha.

 

“Ayya sweetheart gamu munzo biko,ke baki yin zuciya kiringa riganta kema, Amman kullum sai Kinyi kuka, Kinga zo zo mu shirya.”

 

Maah dai ficewa tayi tabarsu Inda sabo sun saba wannan fad’an basu wuce d’an lokaci kad’an sun shirya.

 

Anni ta mik’e tace,

“sorry y’ar gidan Anni kije yayanku zai shirya ku,sanan kiyi wanka anjima ma zaku rakani unguwa.”

 

Salma tace,

“Anni irin wannan gurin da kikaje damu rannan,har aka bamu chocolate.”

 

Dariya tayi tace,

“shazumamu sarkin Shan zaki bacan ba,wani wajene kama hannun y’ar uwarki kuje ki taya ta shiryawa. ”

 

Kan ma salma ta iso wajenta ta fashe da kuka,

“ba zanje wajensu bah.”

Ta ruga can cikin gidan Annin ta barsu sake da baki.”

 

Don irin hakan bai tab’a faruwa ba, Duk yadda suka b’ata da juna to kafin anjima sun shirya kansu, ko kuma wata sa, in Yah Aree ya shiryasu.

 

Salma tace kamar zatayi kuka, don idan sukai fad’an duk rud’ewa take ko kau itace aka kwara.

“Yah Kaga sweetheart ko.”

Idonta ya cika da kwallah

Murmushi yayi ya d’an sunkuyo yace”kar kidamu my Angel, sweetheart dinki zata huce zo muje muci abinci.”

 

Anni tace,

“zan lallasar maki ita kinjiko salma yar albarka.”

D’aga Kai tayi tana sake goge kwallarta,janta yayi suka fita, Annin ta wuce wajen Khairat d’in.

 

💕💕💕💕💕💕💕💕

 

Wasa wasa Khairat ta k’i shirya wa da salma, haka Shima Areef d’in ta daina shige masa,tama koma gaba d’aya wajen Anni bacci ne kurun yake maido ta cikin gidansu, hakan ya saka salma cikin damuwa saboda tunda suka taso irin haka bata faruwa tsakaninsu.

shi kanshi Aree ya shiga damuwa ba kamar k’iriniyarta da tsalle tsallenta, da rigimar ta.

 

Amman duk yadda yaso ya jawota jikinsa ta k’iya,don da ya tunkarota zata fashe da kuka,dole zai barta don subiyun baya son kukansu.

 

shahida ce ta sameta b’angaren Annin tace tazo Yah Aree yana kiranta,

Dole tataso suka taho shahidar nayi mata fad’an fushin da take da salma, wadda gata can bata da lafiya saboda taurin kanki Khairat.

 

Cikin muryar kuka tace,

“da gaske kike Addah.”

 

“gata can ma tak’icin Abinci har yah Aree yayi yayi Amman ta k’icin komi. ”

 

Aguje ta k’arasa cikin gidan falon farko ta same su,

Zube wa tayi gabanta tana kuka tace,

“sweetheart Miye haka, don kawai Ina fushi shine zaki wani sheme kina wani pretending,kinga ki tashi na huce bazan sake fushi da sweetheart d’ina ba,tashi kici kinjiko inhar baki son na cigaba da fushin.”

 

Kamar almarah haka suka ga salma ta Mike tana cin abincin,suna hirar su cike da so da kauna.

Areef wani sanyi yaji don ko kad’an baya son fushin ko wace cikinsu.

Cikin k’an k’anen lokaci komi ya daidai ta, saidai fah Khairat ta canza salo ta daina shigewa Areef, ko assignment ne ta k’asa yah mujahid shine zata je ya koya mata, ta daina rigima da salma akan Areef, ko k’iriniyarta da take masa ta daina Magana ma sai ta Kai makura take masa……..gashi lokacin tafiyarsu ya taho don yanzu bai wuce 2 weeks masu zuwa.

 

Amman gefe guda Khairat kullum cikin lissafin tafiyar take, duk kwanan duniya sai tayi kuka ahankali ta fara ramewa duk ta fice hayyacinta,haka akai jarabawa tashiga js3 aman saboda rashin maida hankali saida aka mata repiting……wannan dalilin ya jawo b’atawar *Khairat da Areef*

 

 

Taufah ana wata ga wata.

 

Mrs bb ce

Mom muhsen.

[01/10, 9:27 pm] +234 703 966 0069: _*ABIN CIKIN RUHINA*_

 

 

*{RE-POST}*

 

Mrs bb

Mom muhseen.

 

Watt pad name

Humaira7531

 

 

🅿️…….2

 

 

Sai dare Saudah ta San cewar lantana tana Asibiti labour ta ke, lawisa ke sanar da ita Abun da ya faru da yamma.

 

Sai da suka natsu sannan Saudah tace,

“Annin Muhajid ya kama ta akira Abun Areef a gaya masa.”

 

“tun d’azu na so inyi masa albishir to na duba wayar taki babu Kati, hankalina ya ya d’auku ga wannan tsaleliyar babyn,wallahi ba batun son kai bah Saudah baki tab’a haihuwar k’yak’k’yawar baby irin wannan ba, tun yanzu ma angane kyanta inaga ta girma.”

 

Murmushi tayi tana gyara ma babyn kwanciyar ta.

tace,

“Anni kenan ai kuwa duk wanda zan haifa to saidai ya biyo bayan Areef A komai ma,don yaro na kin san indai ta nan ne to sai dai Ashafa fatiha.”

 

“Ai nasan da shi nace haka nufina Cikin wad’anda kika hai……………innalillahi lawisa! Don Allah kiyi shiru Meyasa zakiyi maganar nan please na rok’eki karki k’ara irin haka,yanzu Idan Areef idonsa biyu kikai wannan maganar wallahi akwai damuwa, kin san shi da kaifin basira Abun zai zauna masa karshen ya titsiyeni akan maganar.”

 

“yi hakuri Qawata wallahi na shafa,a Amman bazan sake wannan maganar ba nai maki alkawarin hakan.”

 

Ajiyar zuciya ta sauke tace,

“Qawatah,wallahi son da nake ma Areef shahid da shahida bana masu irin sa,duk da kuwa haihuwar su nayi da cikina Amman ba na jin Su irin yadda na keji da Areef, saboda shine silar kawar mun da duk wani k’unci da nake ciki na rashin haihuwa,ta dalilin sa dangin mijina da surukata Su ka fara martaba ni, Ya fitar dani halin kuka da damuwar da na fuskanta don haka ko zan haifi singa da sabon gari wallahi bayan Areef suke,kuma insha Allah Cikin yara na babu maijin wannan sirrin,ke ma don na yarda da ke ki taya ni b’oyon sa don Allah.”

 

“insha Allah Qawata daga bakina dai babu maijin wannan sirrin.”

 

💕💕💕💕💕💕💕💕

 

Sai washe gari aka sanar da y’an uwa da abokan arzik’i wannan haihuwar, Wanda Alhaji farouk ya kejin kamar an masa albishir d’in gidan Aljannah.

Saboda ana gama sanar da shi wannan labarin, abokin kasuwancinsu yayi masa albishir d’in burinsa ya cika, nan take ya yi sujjadar shukru, yana mai tsananin godiya ga Allah Lallai Saudah alkhairi ce garesa,haka zalika wannan Yarinya tazo da arzik’i,nan take yake sanar da Amininsa mijin lawisa cewar asaka ma yarinyar *UMMUL— KHAIRI*.

 

Saida lantana tayi kwana hud’u tana labour baiwar Allah,duk ta fice daga hayyacinta Akwana na biyar likita yace saidai aimata aiki, ranar Alhaji farouk ya dawo duk yadda lantanar take k’unziga mashi hakan bai hana yaji tausayinta ba, nan yasa hannu aka shiga da ita theater room y’an uwanta kuka kawai Suke da iyayenta.

 

Saudah Kanta taji tausayin halin da take ciki saboda duk taurin zuciyarka idan kaganta sai ka tausaya, har kuka tayi Areef kansa yaji babu dad’i.

Ba,a fito da ita ba sai bayan awanni biyar, ansamu nasarar fiddo jaririyar wadda ke kama da babanta kamar Alhaji farouk yayi kaki,anyi murnar sosai kafin ashiga nemo ran uwar saidai tun abun suna ganin baida wuya har hankalin Su ya fara tashi, don duk wata kafa ta sadarwar jikinta sun duba Amman babu alamun tana da rai………….sun kwashe awa biyu akanta Amman babu wani alamun zata tashi……….dole suka fito jikinsu yayi sanyi k’alau,da gudu y’an uwanta suka tare shi yaya lantanar.

 

Girgiza Kai likitan yayi yace kuyi hakuri Allah ya amshi Abunsa………….inna lillahi wa Inna ilaihir taju,un hazbunallahu wani imal wakil………..abunda Alhaji farouk ke ta Nana tawa kenan babu ji babu gani sauran kuwa banda ihu da kururuwa babu abun da suke, daga mai suma sai mai fad’uwa haka wannan rana ta zo babu dad’i,duk wani wanda keda alak’a da lantana yayi kuka kamar idonsa zai fita, na yarda da maganar hausawa da akace ko naman jikinka mutun yake yanka kullum,duk randa babu shi za kaji babu dad’i balle ace ma ya rasu…..hazbunallahu wani imal wakil Allah ya jikan lantana Allah ya yafe mata tayi shahada Allah ya haska kabarinta.

 

Abunda Saudah ke ta fad’a kenan,

Areef ganin halin da maah d’in sa take ciki Shima sai ya kama kuka, Duk yinin ranar ummul kairi tana wajensa sai idan tayi kuka ya kaita ta sha mama.

 

Haka akai sadakar uku Saudah ta anshi yarinyar tace zata shayar dasu tare, Allah ya bata ladar shayarwar, babanta yayi mata hud’uba da *ummu salma*

 

Haka aka share zaman makoki kowa rai babu dad’i, yayin da Saudah kejin gidan yayi mata girma, daga ita sai yaranta guda biyar ikon Allah kenan, kamar ba itace ke kukan rashin haihuwa bah shekarun baya, sai gashi yau Allah ya azurtata da yara biyar Cikin shekaran da basu Gaza bakwai bah.

 

Babu wani taron suna da akai, Alhaji farouk yadai yanka ma yaransa ragunan suna daga nan suka cigaba da kalawa da Yaransu.

 

Rayuwar taci gaba da gara wa yayin da Areef yake primary 5 zai zana common interest yaje js one, shahid kuma shida shahida suna primary 2 sai twince Dake da y’an watannin,kulawa Suke samu sosai shiyasa suke Wata irin kib’a tajin dad’i, Abunda Saudah ta lura shine Areef yafi nuna kulawarsa ga UMMU SALMA saboda acewarsa UMMUL KHAIRI ta cika kuka da fitina,da ya dawo daga makaranta ita zai fara d’auka yana mata wak’a, yana mata rawa duk kuwa ba wai yana k’in d’aukar UMMUL KHAIRI ba Aa yana d’aukarta Amman da ta fara kuka zaice,

“Maah wallahi *khairy* nine bata son na d’auketa kowa yana mata wasa lafiya lau Amman ni da nazo zan mata sai ta yi tayin kuka.”

 

Sai tace,

“haba babban yaya ai shi yaya babba hakuri aka sanshi dashi, dukansu k’annenka ne kowa ce kuma tana buk’atar kulawar yayanta.”

 

Tun daga nan komi zai ma guda to zaima d’ayar,har takai yanzu khairy ta daina masa kuka, har bata yarda da kowa saishi haka Itama SALMA.

 

Alhaji farouk likafa tayi gaba don yanzu ya bud’e sabon kamfanin sa na sarrafa yadiddika materials, boyels ne Gasunan wasu ma bazan ce ga sunan Su ba,ya zuba ma akata da yawa hada amininsa jafar mijin lawisa.

 

Hakan ya ka’ra karfafa zumuncinsu sosai har iyalinsu, don wata sa,in idan su shahida basu nan to tabbas suna gidan Dadyn Muhajid da Meenah,mujahid abokine ga Areef don babu Nisa tsakaninsu ashekaru,Areef zai bashi shekara biyu Meenah kuma kanwar Su shahid ce zasu bata shekara uku……..don yanzu duka shekarar ta uku.

 

Gida Alhaji farouk ya fara ginawa na nuna ma sa,a yayin da zai gyara ma mahaifiyarsa wannan da suke ciki.

 

*shekara kwana inji y’an k’arin magana har gashi y’an yaran Maah sun girma, don yanzu kowace nada 12 years*

 

Mrs bb ce kuma

mom muhsen.

Leave a Comment

error: Content is protected !!