Bawa na Hausa Novel Oum Hairan
Tag: BAWA NA!
OUM HAIRAN
PAGE 1-2
Zamani ke tafiyar da yanayi, yanayi kuma ke shuɗawa da Lokaci, Masarautar Yamlash babbar masarauta ce me ƙarfin faɗa aji da ƙarfin mulki gami da jin izzar sarauta, wanda a wannan ƙarni babu wata masarauta da take taka rawarta yanda takeso kamar wannan masarauta.
Al’ummar dake rayuwa a birnin Yamlash sun kasance ma’abota bautar rana ne ita suka ɗauka abar dogaronsu sun bada gaskiya da ita sannan sun yarda komai baya faruwa Saida lamuncewar Rana.
Farfajiyar gidan sarautar cike yake maƙil da mutane barori bayi da kuyangi gabaɗayansu sun tattare a guri guda, kowannensu ka gani fuskarsa cike take da fargaba zullumi da tsoron da yake bayyana asalin halin da suke ciki.
Daidai wannan lokacin ne aka buga tambarin daya kaɗa zuciyar kowanne mahaluki dake wanzuwa a wannan farfajiya, cikin amon murya me amsa kuwwa zagin fada ya fara gabatar da shelarsa da take ƙara shigar da kowa hankalinsa faɗi yake.
“Yekuwa jama’ar masarautar Yamlash maza da mata manya da yara tsoho da tsohuwa bawa da baiwa! kuyi sani Gimbiya Samha tana gab da fitowa, tabada sanarwar bata buƙatar kowa cikin wannan fada ya kasance cikin yanayin dariya tanason taga fuskar kowa a murtuke kamar an aiko da sakon mutuwar ubanninku saɓawa wannan doka daidai yake da siyawa kanka wulaƙancin da bazakaso ko a labari kaji anyiwa wani irinsa ba, in kunne yaji ita gangar jiki zata zauna lafiya…..”
Sosai mutane suka ƙara shiga hankalinsu don sun riga sun sani saɓawa wannan umarni daidai yake da taro guguwar ajalinka, tsayin lokaci me tsaho bayin suka ɗauka shanye a rana sai zufa sukeyi kowanne da irin nasa cin maganin abin sai wanda yagani.
Can saitin busar sarewa ya fara tashi da amo me daɗin sauraro daidai lokacin ne kuma wasu yammata kyawawa guda arba’in suka fito a jere tsakiyarsu kuma wata kyakkyawar halitta siririyar budurwa ce wacce kyawunta ya zarce tsayawa fasaltawa saidai gani da ido, sanye take da wani bakin yadin siliki ɗinkin doguwar riga da taci ado da duwatsu masu babbar daraja, rigar tana sharar ƙasa waɗannan kuyangi arba’in na hagu da dama suna naɗewa tare da karkaɗewa.
Cilla ƙafarta takeyi saman shimfiɗar dardumar da akayi wa inda zata taka wata ƙara na tashi ta haɗuwar sarƙoƙin adon dake ɗaure a sangalalin ƙafarta, saman kanta anyi mata rumfa da wani yadi me kauri da ƙyalƙyali da haka suka rinƙa takawa har suka iso tsakiyar gidan sarautar inda bayin nan ke tsaye ƙiƙam a rana, daidai kuma lokacin ne wani bawa ya kutso cikin taron ya nemi guri ya tsaya shima amma saɓanin sauran bayin shi fuskarsa a naɗe take da wani farin ƙyalle.
Tsayawa tayi a inda aka tanada dominta ta fara bin bayin da kallo cikin ƙasƙanci da wulaƙantarwa tana wani yatsina fuska, yanda take kallonsu kamar mai nazarin wani abu yabawa idanunta damar hango mata wannan bawan daya naɗe kansa da cikin tsananin mamaki da baƙin ciki ta zuba masa idanu ranta yana tambayarta “waye shi a cikin bayi?” Juyawa tayi ta nufi hanyar da zata kaita ɓangarenta bayan wuccewarta kowa ya watse cike da mamakin ko meye ya dagula walwala Gimbiya daga fitowarta?
Babu me ikon yin wannan tambayar saboda haka kowa ya kama aikin gabansa inda cikin bayin masu gajen hƙr da son sanin abinda bai shafesu ba suka fara tambayar junansu kamar yanda yake faruwa yanzu a Madafi inda na hango wasu mata guda biyu suna aikin gurza kwakwa.
Ɗaya ce ta ɗago ta dubi ƴar uwarta tace “Salame yau gidannan fah babu alamun lafiya ran Gimbiya Samha ya jagula” riƙe haɓa Salame tayi tace “Yo ashe bani kaɗai nayi wannan baƙin ganin ba ko meye yasata rashin walwala?” Goge hannu Jaɓɓe tayi jikin zaninta tace “Yau har ɓangaran sarauniya saidai ayi na dole wato hƙr
Saboda ran ƴar lele jinin gwal ya ɓaci na kowa ma zai iya ɓaci….” Shiru sukayi tare da ɗora hannunsu saman bakinsu jin motsi alamar akwai me shirin shigowa, wata kuyanga ce cikin kuyangin Gimbiya Samha ta shigo ta tsaya bakin ƙofa tace “Gimbiya na buƙatar tataccen ruwan kwakwa da markaɗaɗen dabino…..” Tun kafin rufe bakinta suka ɗauki tambulan na gilashi suka tsiyayo cikin wani nau’in abin adana sanyi ta karɓa ta fice daga madafin ta nufi sashin Gimbiyar tana zuwa ta ishe ta ta miƙe sai zagaya ɗakin nata takeyi tana dukan hannunta, daidai shigowar kuyangar ta juyo ta karɓi ruwan kwakwar ta kafa bakinta ta kwankwaɗa cikin bazata tayi jifa da cup ɗin ta cizge hular kanta ta jefar dogon gashinta ya bazu a kafaɗarta zuwa gadon bayanta tace.
“Wayeshi Baiwa Sambur wayeshi da yake zuwarmin da siffar da bana ganewa kowa baya ganewa? Meye yasa Ni kaɗai nake ganinsa cikin bayin gidannan…. Sambur a bincikomin wayeshi inason sanin wayeshi meye yasa yake zuwa da ɓatacciyar siffa……..
[23/09, 8:31 pm] +234 904 674 2752: BAWA NA
OUM HAIRAN
F PAGE 3-4
Follow me
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza 3
-
Zuciya ta
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi
-
Aure da haihuwa
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya
-
Gangar Shedan
-
Angon mata biyu
-
A gidan mu take
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
Powered by: www.mynovels.com.ng
Cikin ladabi Baiwa Sambur ta rusuna kamar me shirin aikata sujjada ga uwar gijiyar tata tace “angama ranki ya daɗe lallai za’a bincika don sanin meye yake tafe dashi” iska Samha ta furzar ta faɗa kan wani gadon hutawa me lulawa tana sauke numfashi idanunta ya kada yayi jawur alamun da gaske ɓacin rai ya shigeta, tana nan zaune aka buɗe ƙofar aka shigo ta ɗauki idanunta ta ɗorasu ga ƙofar ba kowa bace illa mahaifiyarta sarauniya Nuwaira, bayi na take mata baya har zuwa iyakarsu sukaja suka tsaya tare da juya bayansu gasu Gimbiya Samha da mahaifiyarta.
Cike da murmushi Sarauniya ke takawa har zuwa mazaunin ɗiyar tata ta zauna a gefen Gimbiya tare da ɗora hannunta a fuskarta tace “fuska me kyau da murmushin aminci ta dace yake ƴata tabbas labari ya isheni yau ma kamar wancan makon baki samu nishaɗin da kike buƙata a fitowar makonki ba hassali ma zuciyarki jagula tayi shin ko zan iya sanin dalilin shigar Gimbiya damuwa a yau?”
Miƙewa Gimbiya Samha tayi daga inda take kishingiɗe tace “Idan ya kasance mutum ne kamar Ni zanyi masa azaba me raɗaɗin da sai ta sanyashi nadamar wasa da hankalina da yayi, yake mahaifiyata idan kuma ya kasance jinnu ne to zansa a gina masa kurkuku a ƙarƙashin ƙasa wadda zansa aljanu dubu arba’in su rinƙa yi masa azaba salo salo har zuwa lokacin da ajalinsa zai riskeshi, tabbas yayi wasa a inda ba’a wasa yake mahaifiyata. Waye shi? Meye taƙamarsa kuma meye yasa yake zuwa da fuskarsa a rufe wanne matsayi gareshi cikin bayin gidannan?”
Cikin rashin fahimta sarauniya Nuwaira take kallo da sauraron ɗiyar tata har Saida taga taja numfashi sannan ta miƙe tace “waye ne kike magana akansa yake abar ƙaunata meye haɗinki da bawa cikin bayin gidannan?” Iska Gimbiya ta furzar tace “Lallai ne nabada yau zuwa gobe a bincikomin wayeshi idan hakan ta gagara to raina zai ɓaci zan kasance cikin ƙunci dana kasance na rasa samun biyan buƙata a karon farko a tarihin rayuwata….”
Da sauri sarauniya tace “Aa yake ƴata na rantse da hasken abar Bauta bazaki taɓa rasa abinda kikeso ba dole ne a binciko ko waye….” Tana faɗin haka ta juya ta fice daga sashin na ɗiyarta ta nufi sashin bayin gidan tun kafin isarta sanarwa ta isa garesu su daidatu akan kafafunsu ga sarauniya nan da kanta, nandanan kowa ya fara neman nutsuwarsa yana sanyawa kansa kafin isowar sarauniya gurin ya nutsu yayi cif tana zuwa ta tsaya a gabansu tana ƙare wa kowacce fuska kallo cikin nazari da son gano bawan da ɗiyar tata takeson sani can ta ɗago cikin isa da izza tace “Inason ku fitomin da baƙon bawan da yazo taron tsaiwar fitowar Gimbiya wancan makon sana ya kuma zuwa wannan makon” nandanan suka fara rarraba idanu kowa yanason gane fuskar bako a cikinsu amma sun kasa ganowa can wani cikin tsofaffin bayin gidan yayi gyaran murya tare da takowa ya gurfana gaban Sarauniya Nuwaira yace “Rana ta baki nasara ya shugabata shiɗin ya kasance ba zaunannen bawa bane a cikin gidannan yana shigowa ta ƙofar kudancin masarauta sannan yana fita ta gabashinta na naƙalci hakanne tun shigowarsa ta farko lkcn ina saman tsauni me tsarki ina addu’a naga ketowarsa akan doki ya sauka ya saki dokinsa a saura ina tsaye ina kallonsa har ya iso wajen taron fitowar makon Gimbiya ya naɗe fuskarsa da farin alawayyo, ban gajiya ba har zuwa lokacin da naga ya sulale daga cikin taron ya nufi gabashin masarauta can naga dokinsa ya tafi da gudu gareshi ya haye samansa ya fice.
Sai na cika da al’ajabi gashi dai yazo da shigarmu ta bayi kuma ya fice da wata shigar daban to wannan tasa yauma na sake zuwa don ganin meye zai faru ilai kuwa ya kuma shigowa kamar yanda ya shigo wancan makon”
Shiru gurin yayi sarauniya Nuwaira ta tafi nazari can ta ɗago tace “Tsoho Hikam kaine kasan inda wannan bawa yabi lallai ne ina buƙatar ƙasar gurin daya taka” tana faɗin haka ta juya ta nufi hanyar da zata sadata da sashin ta, hankalinta a tashe zuciyarta a jagule kuma cike da fargaba, lallai idan abinda take tunani ya kasance ba itaba hatta masarautar Yamlash tana cikin tsaka me wuya.
Wani ɗaki ta shiga ta kulle kanta ta isa jikin wani madubin tsafi dake girke jikin bango ta dauki wata saƙalalliyar butar ƙarfe ta watsa jikin madubin tana me karanta wasu surkulle take wata guguwa ta taso daga cikin wannan madubi tayi tsiri sama tayi hanƙam tana wani irin gunji can bayan shuɗewar mintina guguwar ta fara yin ƙasa hardai ta ɓace gurin ya bada wani siririn rami take wani maciji ya sulalo ta ciki ya fasa kai kawai saiya rikiɗa ya zama wani gabjejen aljani ya rusuna gaban Nuwaira cikin muryarsa mara daɗin ji yace “Haƙiƙa duk sanda kira ya riskeni daga wannan masarauta nasan akwai wani abu rikitacce kuma cukurkuɗaɗɗe da yake shirin faruwa yake wannan Gimbiya kuma sarauniya meye ya tunkaroki ko kuma kike tsoron tunkarowarsa da yasa kika buƙaci taimakona?”
Numfashi ta sauke tace “Yakai aljani Hijaz kayi sani Kafin mutuwar mijina sarki Nu’uman ya sanar dani akwai wani lokaci da zamu riska nida ɗiyata Samha da zamu zama abokan gabar juna ta dalilin namiji ya sanar dani ba ƙasƙantacce bane saidai zai bayyana da siffa mafi ƙasƙanci ta bawa kuma zai ɓace cikin bayin wannan masarauta harsai yayi illa garemu sannan zai bayyana kansa, zuciyata tayi rauni hankalina ya tashi daga sanda naji Samha tana bincike akan bataccen bawan da yake bayyana mako biyu kenan duk ranar fitowar makonta”
Shiru ta gifta na lokaci me tsayi kafin aljani Hijaz ya ɗago idanunsa cike da ƙwalla yace “A lokacin ne ajalina zai riskeni bazan iya gujewa afkuwar hakan ba tabbas wannan lokaci ya ƙarato yake wannan Gimbiya kuma sarauniya amma bazan iya baki tabbaci akan kasantuwar wannan bawa ya kusa bayyana ko shine ya bayyana ba domin komansa a lulluɓe yake babu abinda yake bayyana daga gareshi”
Dukan kanta tayi tace “Ina bazan taɓa amincewa wannan abu da kuke hasashe ya faru ba saidai ko meye zai faru ya faru ina amfanin tsaron dana sanyawa abar ƙaunata kenan ina amfanin kangetan da nakeyi domin tsareta daga harin ƴaƴan manyan sarakan duniya domin naci alwashin Gimbiya bazatayi aure ba bare tayi nesa dani bazatayi aure ba bare ta kwankwaɗi ɗacin dana kwankwaɗa bazatayi aure ba bare darajarta ta fadi wani ƙasƙantacce wulaƙantacce yake jin shi a samanta yake inko har ya zama dole to saidai ya amince itace a samansa dole kamar yanda na rayu da ubanta nice matsayin miji shine matsayin mata to shima wanda ƙawarsa tasa ya nace sai Gimbiya to Saidai ya amince su rayu a haka in ko ba haka ba saidai ya haƙura…….