Kiyon Lafiya

Bayanai Akan Laulayin Ciki

 Bayanai A Kan Laulayin Ciki

Laulayin ciki abu ne wanda ke damun mata masu ciki.

Wata Laulayin ta ya na zuwa da sauki wata ko sai ya kai ga an kwantar da ita asibiti na tsawon lokaci.

Me Ke Kawo Laulayin Ciki

Laulayin ciki na kasance wa ne saboda sinadaran da ake kira hormones da ke bayyana a jinin mace a lokacin da ta ke dauke da ciki. Wadannan sinadaran su ke riƙe ciki domin kosawar jariri har a kai ga lokacin haihuwa. Haka Allah Ya tsara abin.

Me Ya sa Laulayin Ciki Ke Tsanani a Wasu Masu Ciki

Laulayin ciki na tsanani a wasu mata saboda haka Allah Ya halicce su. Kuma wani lokaci a na gadon sa. Misali idan uwar mace tana matsanancin laulayi to ita ma yar ta ta na iya yin haka a lokacin da take ɗauke da juna biyu.

Alamomin Laulayin Ciki Mai Tsanani 

– Amai: musamman idan amai ya wuce sau 3 ga yini. Wannan yana zuwa da alamomin olsa wani lokaci har da aman jini.

– Rashin cin abinci ko shan abin sha: Musamman idan mace ba ta iya cin abinci ko shan abubuwa masu ruwa

– Kasala da gajiya: musamman idan mace ba ta iya komai sai dai kwanciya

– Rama: Rama wanda ya wuce wuri har ya kai ga kashin fuska ko na wuya su bayyana

– Rashin isasshen jini: Wannan a na ganewa ne ta hanyar bincike a asibiti.

Matakan Da Ya kamata A Ɗauka Domin Hana Laulayin Ciki Ya Kawo Matsala Ga Mai Juna Biyu

1. A rinƙa lura da yanayin mai ciki musamman ciki na farko. Kuma ba laifi bane a fara awo daga ranar da mace ta ɗauki ciki domin kula da lafiyar ta.

2. A duk lokacin da aka kula da mai ciki na da alamomin da muka bayyana a sama to ya kamata a kai ta Asibiti domin a duba ta. Ka da a zauna gida ana kara mata ruwa. A kai ta wurin likitoci ko nurses ko ungozoma a asibiti.

3. akwai magunguna a asibiti wadanda ake baiwa mai tsananin Laulayin ciki domin ta samu sauƙin Laulayin. a wani lokaci za a kwantar da ita a Asibiti kuma a saka mata ruwa wanda ya dace da matsalolin ta a wannan lokacin

4. Kwantar da mace mai tsananin Laulayin ciki a Asibiti domin kula da ita abu ne mai kyau kuma so dayawa ya na hana salwantar rayuwa. Idan ta samu sauki za a sallame ta idan kuma an ga bayan sallama da satuttuka Laulayin ya kara tsanani ana iya mai da ita Asibiti. Duk wadannan matakai ne na kula da lafiyar ta da lafiyar jaririn ta.

5. A daina zuwa chemist haka kawai ba tare da shawarar masana kiwon lafiya ba domin sai wa mai tsananin Laulayin ciki magani. Duk maganin da mace mai ciki zata sha ya kamata ya kasance likita ko nurses ko masana kiwon lafiya ne suka rubuta.

Allah Ya sa mu dace.

Allah Ya sauke mana duk masu ciki lafiya Ya kuma bada yara maza ko mata rayayyu.

Ameen.

Dr Auwal Ahmed Musaa

Leave a Comment

error: Content is protected !!