Bazawara ce Hausa Novels Doc Download

Bazawara ce Hausa Novels Doc Download

 

 

 

 

KADAN DAGA CIKIN LITTAFIN…

[*🔥BAZAWARA CE🔥*

BY

*SUMMY M NA’IGE*
(Ummu Ja’afar)

*SADAUKARWA*
*LEEMAT PINKY💞*

🆓 *Page 1*

Da gudu na shigo gidan mu, tun a soron gida na ke ƙwalawa Amma kira amma bata ƙarɓa ba, ɗakin mu na shiga ko sallama babu na faɗa jikin Amma, ajiyar zuciya na sauke kana na dube Amma da kyau nace,

” Amma! Amma! Amma!”.

Sai da ta girgiza kai kana tace,

” Sajida lifiya? waya taɓamin ke haka?”.

” Ni ba wanda ya taɓani kawai na zo ne na shaida miki kije kiyiwa Baba magana wallahi aure nake so, yau watana biyar da ciki idda fa, amma ko an zo neman aure na sai Baba yace ba yanzu ba, to ba yanzu ba sai yaushe? ni fa bazawara nike ba budurwa ba, dan haka bari kiji Amma, tabbas bazan iya zama yadda su aunty suka zauna gida shakara da shekaru har tsofa ya fara taso musu babu miji kuma babu ɗa , amma in har Baba ya ce bazan yi aure ba Amma, to kisa ni! wallahi zan koma bazawara ta ai nahi kuma zanyi zawarci mai lasi-si!”.

Ta na gama faɗar haka ta tashi daga jikin Amma da take kwance.

Hannu Amma tasa ta na lalubar Sajida amma bata jita kusa da ita ba, a hankali Amma ta buɗa baki tace,

” Sajida ki ƙara haƙuri da halin mahaifinku…..tun ba rufe baki ba taji kamar ana ihu tsakar gida, da sauri Amma tace,

“Sajida wa Baban ki ke duka tsakar gida? dubamin kiyi sauri ki fitar dani tun bai zo ya dake ni ba, wallahi yau ban da lafiya bazan iya ɗaukar dukan shi ba”.
Ta faɗi haka jikinta na karkarwa.

” Kai tsaye Sajida tace,
” Mama Amarya ce ya ke duka, kuma wallahi bazam fitar da ke ba sai dai yazo ya da ke ki, amma ki sani! yana dukan ki sai nasa zawarawa na sun ci ubansa”.

Amma bata tsaya jin ƙarshin abinda Sajida ke faɗa ba ta laluba sandar ta tariƙa takawa a hankali har ta fita waje.

Tsaki Sajida tayi itama tamarawa Amma baya.

Koda na fita ƴan wahala duk sun fito waje sunyi layi ƙofar ɗakinsa, jikinsu sai karkarwa yake.

Dukan ta yake yana faɗar,
” Ni zan faɗa kina faɗa, wallahi ba’ayi wata ƴa mace ba wadda zan faɗa ta faɗa ba, kafin na sanki har na aureki nasan irinki dubu, dan haka wannan ya zama shine na farko kuma shine ƙarshe”.

Haƙuri ta riƙa bashi ta na kuka , sai da ya yi mata jagaf sannan ya kyleta .

Ko kallonsu Amma bai yi ba ya shega ɗakin sa kamar ɗan ƙaramin tawol ɗin da yake ɗaure dashi ya faɗi.

Yana shiga ɗakinsa na matso kusa da Amma nace,.
Amma Baba ya shiga ɗaki kije ki sanar dashi aure nake so wallahi, idan bakuyi min aure ba wallahi wallahi duk abin da naga dama shi zanyi”.

Amma bata ce da ita komai ba ta ɗau sandar ta ta koma ɗakin ta.

Shigarta ke da wuya ya fito riƙi da kwarya wadda ke ɗauke da shinkafar towu.

” Kubura! Kubura! Kubura!.

Haka yariƙa faɗa da karfi, Kubura ita ce amarya a halin yanzu kuma itace wadda ya gama duka yanzu.

Jikinta na rawa ta isa gareshi ta durƙusa ciki da ladabi tace,

” Gani Malam”.

Ƙwaryar da ke hannunsa ya bata yace,

” Kiyi sauri ki kammala girki dan yau kinsan kece da baraya!”.

Batare datayi masa musu ba tace,

” Tau Malam yanzu zan fara”.

Jiki na rawa ta shiga kicing dan ta ɗaura sanwa, tukunya ta ɗauko zata ɗaura kan wuta a dai-dai lokacin na shigo, tukunyar na bi da kallo, saboda iya gani na ban taɓa ganin irin wannan tukunyar ta gidanmu ba, ita kanta wadda zata ɗaura tukunyar na bi da kallo, dan tas za’a saka irinta biyu a cikin tukunyar a dafe.

Kubura yarinya ce wadda bazata wuce shekara ashirin ba, yarinya ce kyakyawa son kowa ƙin wanda ya rasa.

Dubanta na sakiyi naga wace kaddarace ta kawo ta wannan gidan? oho, hawayen da ke zuba a idonta ta goge kana taci gaba da ɗaura sanwar.

Tsaki nayi kana nabar wajan, kai tsaye ɗakin zawarawa part 2 na nufa, da yake gidan da muke haya gida ne mai ɗaki takwas, huɗu na matan gida, uku kuwa namu ne zawarawa, ɗaya tsofafin zawarawa, ɗaya ko shine na tsaka, ɗaya kuwa shine namu sababin zawarawa, ɗaya ko na Babamu ne, sai tsoron gida inda ƙanninmu maza ke bacci…..

Taku har kullum

*SUMMY M NA’IGE✍️*

*UMMU JA’AFAR✍️*

*SADAUKARWA:*
*💞LEEMAT PINKY💞*

_Wannan labarin na kuɗi ne, ga mai ɓuƙatar karatun wannan labari zai iya tura katin waya na 200 ta wannan Number, 07062118047. Sumayya Almustapha.Accont:5154576019.Bank:FCMB.nigar 250F_

*SAFI NA 2*

Da sallama na shiga ɗakin, ƙarɓawa suka yi suna zaune kan gunton keso wanda zance shine makwanci kowace bazawara a gidanmu.

Fira suke hankali kwance, amma kallo ɗaya zakayi ma ko wace ka gane yunwar cikinta ta isheta, bare a zo ga zanci gyaran jiki, kuma wallahi duk ƴan gidamu kyawawa ne na ƙarshe.

Kallonsu nayi da kyau kana na ƙaraso kusa da su na samu waje na zauna haɗi da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan nace,

” Ƴan uwana, ko nace Yayu na zawarawa”.
Nayi maganar tare da fitar da ido.

Basu karɓa ba sai dai ko wace ta ɗa go ido ta kalle ni ɗauke da mamaki a fuskarsu.

Murmishi nayi irin na zawarawa maso lasi-si kana tace,

” Dama zuwa nayi wajanku damon muyi wata ƴar magana wadda nake ganin zata anfane mu gaba ɗaya, kuma dan Allah kuyi duba mai kyau akan maganata dan Allah!”.

” Ajiyar zuciya suka sauke kana suka ce muna jinki ƴar ƙanwarmu” .

Zama na gyara kana na dubesu nace,

” Mi zai hana ku zo mu fara sana’a, dan gaskiya na ga duk muna cikin neman taimako, ga zaman zawarci, kuma ga yunwa, uwa uba kuma gashi ko kafin ka riƙa nira biyar sai anfi wata biyu, kuma ba fita ku ke ba bare ku samu zawarawa da samari su baku, to shine nace ku futo mu fara sana’a muma mu nemi na kan mu har lokacin da Baba ya yarda kuyi aure”.

” Atare suka ce kefa baza kijirashi ba?”.

Murmushi nayi na gyafin baki kana tace,

” Kafin ya bani damar haka na mutu ko na tsofa na koma irin su Auntys zawarawa, shine nake so na fara sana’a mai haɗi da zawarci, wallah-wallahi na riga da na fito duk Baba yace ba zai min aure ba sai na sashi ya yi kukan safi da dare, ni ba dole sai na haɗa da sana’a zanyi zawarci ba, a’a kune nake jiyema, gwara ku haɗa da sana’a idan kina so kiyi zawarcinki kiyi abinki hankali kwance batare da wani ko Baba sun samu ku ido ba, amma gaskiya zama haka babu daɗi, musamman in dare ya yi na rega naga yadda Baba ke holewa da matanshi”.

A jiyar zuciya suka sauke a tare saboda an tuno musu abinda ke ci ci musu towo a ƙwarya.

” To ke Sajida muda ba muda ko biyar ta ya ya zamu fara sana’a batare da mun samu kuɗin ba?”.

Hafsat ta faɗi haka wadda ita da Sajida basu da wata tazara tsakanin su.

” Inda akan ƙuɗi ne babu damuwa, saboda yanzu haka akwai wani bazawari na da mukayi zai zo ya bani kuɗin bikin ƙawata to shine idan an kawo zan rarraba muku kowace ta yi jari koda kowa na sayar da sabolo ne, saboda a wannan tafiya ba’a sun bazawara mai aji ta kasance babu sana’a saboda kariya ce ga duk wata bazawara ba mu kaɗai ba!”.

Godiya sukayi min saboda zaman gida ya zo ƙarshe, gashi ba wani jin daɗi bare so da ko wace ta san daɗin aure, kowa dai na faɗar albarkar bakinta ta gaji da zama gidannan gida kamar gidan yari, gani suke ko ƴan gidan yari sun fiso ƴanci saboda so za su ci su ƙoshi, amma su fa? kuma wani lokaci ƴan gidan yari za’a fitar da su su ga gari amma sufa, da ga shekara sai shekara ko idan an yi mutuwa.

Kuma babban abin da ke ɗaure musu kai ace duk wadda tayi aure cikin su ba wadda ke da ɗa ko ciki, tabbas ko ka fito da ciki mutum baya sati da fitowa cikin zai zube.
*******
Kubura na kammala aiki ta zubawa kowa nashi abinda ya samu sannan ta gyara gida kana tashiga ɗakin ta, da yake lokacin an fara kiran sallah magarb.

Wanka tayi kana tasa kananun kaya wanɗan da tasan ya na so, kana ta feshi jiki da turare sannan ta fito ta nufi ɗakin Babamu.
Har ta kusa ƙarasawo cikin ɗakin sai gashi ya fito riƙi da tabarma a hannunsa.

Cikin da ladabi ta zo ta karɓa tabarmar da ke hannunsa.

Tsoron gida ta kai ta shimfiɗa masa, bayan ta gama ta kai masa ruwa ban ɗaki ya yi wanka yana fitowa bai tsaya ko ina ba sai tsoron gida inda ta shimfiɗa masa tabarma, zama ya yi bai jima da zama ba sai gata ta zo riƙi da man shafawa a hannunta, zama tayi kusa da shi ta fara shafa masa mai sai lumsar ido ya ke.

Bayan ta kammala ta dawo kusa dashi ta zauna ta ɗauko abinci ta fara bashi har sai da ya ƙoshi, bayan ya yi gyatsa ne ya kwanta tare da janye ƙaramin tawol ɗin da ke jikinshi ya rage daga shi sai gajerin wando, tana gani haka a hankali ta ƙaraso gareshi ta ɗauko hannayenta ta ɗaura saman jikin shi, a hankali ta fara yi masa tausa, sosai ya ke jin daɗin abinda take masa har bai san lokacin da ya kai hannunshi ya fara zare mata kayan da ke jikinta ba, har sai da ya kai ba abinda ya rage na jikinta sai pant da bireziya.

Haka halin Babamu yake shiyasa da an idar da sallar isha’i ba mai sake fita gidan kuma ba mai saki shigowa saboda kada kayi mugun gani saboda haka ke kasancewa a girkin kowa ce daga cikinsu.. ……

*Dan Allah kutayani posting🙏*

*SUMMY M NA’IGE✍️*
🔥🔥BAZAWARA CE🔥🔥

By

*UMMU JA’AFAR✍️*

*SADAUKARWA*
*LEEMAT PINKY💞*

*SHAFI NA UKU*

Suna cikin haka sai na leƙo kai na na ga shin ko sunyi bacci kasancewar na daina jin mutsin su, abinda na gani ne nayi sauri na rufe idona ban shirya ba.

Ƙwafa nayi kana na ce,

” Shege Baba yanzu gashi sai jin daɗin aure yake amma mu gashi ya barmu zaune a gidan shi , in ya so mu mutu ! wallahi baza mu yarda ba!”.
Tsaki nayi kana na ɗauko ƙafa a hankali dan wallahi ko zai dawo hayacin shi bai isa ya hana min fita ba, haka na fara tafiya irin ta ɓarayi batare da nayi wani dogon mutsi ba bare yasa ɗayan su ya san an fita.

Ko da na fita ba kowa a ƙofar gida, da hanzari na kama hanyar da zata kai ni gidan ƙawata itama bazawara ce, amma ita gidan kanta gareta dan ita zawarce ta ke mai tsaf ta, ba irin namu na wahala ba, da ya ke shi bazawarin nawa a can mukayi da shi zamu hadu.

Tun ban ƙarasa gidan ba na hango motarshi ƙofar gidan, gyara tafiya ta nayi da ga ta sauri zuwa ta zawarawa waɗan da suka san kan su, a ta ki na gyara ɗaurin kallabi na, ban duba madubi ba amma tabbas na san nayi kyau. a hankali na ɗau hannuna na fara ƙwanƙwasa glass ɗin motar.

Zaune ya ke yana dubin ta inda zan fito sai ya ji ana buga glass ɗin motar, a hankali ya mai da dubanshi zuwa ga inda ake buga ƙofar, ido huɗu mukayi dashi , lokaci ɗaya nayi masa wani kallo wanda shi kanshi ya kasa gane ma’anarsa, cikin a zama ya washe haƙuran shi tare da sauri ya buɗe min ƙofar motar haɗi da faɗin,

” Bismillah hasken idaniya ta”.

Murmushi nayi masa wanda sanadin haka yasa kumatu na suka lotsa.

A hankali na buɗa baki nace,

” Kallon fa?”.

Murmushi ya yi min kana yace,

” Wallah Baby sai ƙara kyau ki ke, wai miye sirrin?”.

Ya faɗi haka shima a ɗan shagwaɓe.

Murmushi tayi saboda irin yadda ya yi maganar ta sani dariya kana nace,

” Ban da sharri, kai dai ka faɗi gaskiya, ko dai ka ga na ƙara muni ne?”.
Na faɗi haka tare da tauna cingum ɗin da ke cikin baki na.

Mun jima muna fira daga bisani nayi masa salma saboda na ga lokaci ya tafi ban kula ba saboda ni kai na na shiga shauƙin soyayya, saboda a rayuwata ina girmama soyayya, wallah shiyasa wani lokaci nake mamakin yadda mijina ya sake ni.

Ƙuɗin da zan saye kayan bikin ƙawata wanɗa da na ce masa su ya ɗauko ya bani, ban wani tsaya ƙirgawa ba nayi gaba cikin sauri haɗi da ɗaga masa hannu, alamar bye.

Sai da ya daina ganina sannan ya ta da motarshi ya bar wajan.

Yadda na barsu haka na dawo na same su, sai dai yanzu bacci suke rungumi da juna, kai tsaye na shige cikin gida haɗi da antayawa Babanmu harara.
Sai da na shiga cikin gida nayi tsaki nace ƙaton banza ko kunya baya ji, warin jikarka a ce ita ce matarka.

Salon So Hausa Novels
Kai tsaye ɗakin Ammata na shiga, zaune na sameta kan sallaya da alamu yanzu ta gama wuturi, saboda ita Amma sai idan zata kwanciya take yin wuturi saboda ita haka ne tsarin ta, ko ba komai ta na son ta kwanta tana da alwala.
Ba sallama haka na shiga ɗakin, wajan da kaya na suke na nufa, aikuwa Amma na jin mutsin mutum ya shigo ɗakin ta lalabu sandarta haɗi da faɗar,
” Waye ya shigo! waye ya shigo! waye ya shigo min ɗaki?”.
Ganin tana son ta tara min mutanin gida ne yasa na ja tsaki kana nace,

” Amma nice fa”.

” Sajida lafiya mike damunki wanda ya hanaki bacci har yanzu?”.

Ta faɗi haka ahankalin ta a tashe.

Baki na turu gaba nace,

” Amma kwantar da hankalinki ba abinda ke damu na, dama bazawari na ne ya kawo min ziyara yau”.

Haka na faɗa babu wata kunya ko tsoro a tare dani, dan wallahi yanzu yadda na ke ji ko gaban sarki ne zan iya faɗar haka bare wani Babanmu.

A jiyar zuciya Amma ta sauke mai nauyi kana ta ce,

” Sajida mi ke ke son ki zama dan Allah? dan Allah ki rufamin asiri wallahi ban iyawa da halin mahaifinki, dan na san idan ya tashi hukunci ba ke kaɗai ba har ni sai ya shafa, kinga yanzu ba isassar lafiya da ni ba , dan Allah ki rufamin asiri Sajida wallahi ke ɗai ce zan ji naji daɗi a raina, ban san kowa ba sai Mahaifinki kuma sai ke, kuma sai Allah ya kawo min jarabawa ta rasa ido, dan Allah ki taimaki rayuwata karki jamin abin magana!”.

Yanayin da tayi magana ne yasa taban tausayi sosai, ajiyar zuciya na sauke, sai da na kalleta tsaf kana na ce,

” Amma kin san shawar da zan baki gobe ki je ki sanar da Babanmu ki ce na ce aure na ke so, idan ya ban dama sai na turu mishi wanda ke so na, idan ki ka yi min haka kin gama min komai wallahi!.

Ina kai ƙarshin zancin na fice da ga ɗakin batare da na tsaya jin mi zata ce ba.
Ina ji ta na kirana na shareta, kai tsaye ɗakin zawara part 2 na nufa saboda ina so na gama da su tun a daren yau kafin na nufi ɗakin zawara part 1 saboda na san su part 3 basu da wuyar nuna musu hanya, saboda duk mune yara.

Koda na shiga wasu daga cikin su sunyi bacci, zama nayi haɗi da ƙwanƙwasa musu ƙofa na ce su tashi ina son nayi komai cikin sirri, bayan sun tashi ne na ɗauko kuɗin na rabawa ko wacin su dubu biyar-biyar na ce ko wace ta fara da ko da sayar da ƴan kunne ne, saboda na san tabbas nan gaba ko wacin ku zata samu jari mai yawan gaske, zama haka babu daɗi babu miji kuma ba bu cin mai kyau, dan haka mu tashi mu nemi na kan mu.

Sosai sukayi mata godiya akan wannan namijin ƙoƙari da tayi ace ita ce ƙaramarsu amma ita ke nuna musu hanyar neman kari mutuncin su.

Bayan sun gama shirya duk yadda abu zai kasance ta sa ƙafa ta koma ɗakin su.

Ko da tashiga ɗakin su, wato ɗakin zawarawa part 3 duk sunyi bacci, tsayuwa tayi ta bi su da kallo wai duk zawarawa ne su, ita abin ya ɗaure mata kai, miyasa duk suka zama zawara?.

Tsaki tayi saboda bata da amsar wannan tambaya dan haka ta je wajan da ƴar ƙaramar katifarta take ta kwanta idonta sai hango mata Babansu yake shida amarya sa.

Kiran sallah asuba ne ya tashi duk wanda ke cikin gidan namu wanda ke ko mawa kamar ana cin kasuwa saboda duk sun tashi sai layi ake na shiga ban haya.

Tsaki nayi haɗi da ƙara gara kwanciya ta saboda na san ko na tashi sai na bi layin shiga ban hanya gwara nayi kwanciya ta.

*Kutayani posting dan Allah🙏* ]

KU SAUKE CIKAKKEN LITTAFIN ANAN KASA👇👇👇

 

Preview: [DOWNLOAD COMPLETE BOOK 👇]
 

Name: Bazawara Ce
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: MYNOVELS.COM.NG
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books
Groups/Writers: Billyn Abdul, Benaxir Oumar, Eyshat, Nadia Buhari, My Novels, Zamani Writers Association, Exclusive Writers,Alheri writers,Best Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: July, 2021

 

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.