Bello Turji Hotunan Shi Tare Yaran Sa
Bello Turji ko yana raye?
SHUGABAN ‘YAN BINDIGA BELLO TURJI YANA RAYE
Ku Kalli Hotunan Yadda Yake Duniyanci Da Jama’arsa A Sansaninsa
Daga Datti Assalafiy
Kamar yadda zaku gani a hoto, Béllo Turji yana zaune a kan kujera cikin kakin ‘yan sanda, ga bindigar RPG jingine jikin bishiya ta bayansa, sannan ga sauran mayakansa wasu a cikin kakin sojoji tare da sauran jama’arsu da matansu suna zaune cikin izza.
Kuma dai har yanzu Béllo Turji yana rike da wasu kauyuka suna karkashin ikonsa a jihar Zamfara da Sokoto, musamman kauyukan Gusami da Gora wanda suke karamar hukumar Birnin Magaji jihar Zamfara.
Bello Yabo: Labarin Wata Matar Aure Da Aka Yiwa Fyade
Duk wanda yayi nazarin wadannan hotuna ya kalle su da kyau ya ga irin makamai da abin hawa da suke gurin barayin zai fahimci cewa mutanen nan suna samun taimako da daurin gindi daga gurin manyan maciya amanar tsaron Nigeria da miyagun ‘yan siyasa.
Muna rokon Allah Ya kawo mana karshen ‘yan ta’adda da maciya amanar tsaron Nijeriya.
Béllo Turji Hotunan sa
Leave a Comment