Addini Nasiha

Bello Yabo: Labarin Wata Matar Aure Da Aka Yiwa Fyade

Bello Yabo: Labarin Wata Matar Aure Da Aka Yiwa Fyade

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Bello yabo

Wata matar aure a jihar Sokoto, masu garkuwa da mutane sunje gidan wani Alhaji a Sokoto suka kama matarsa da ‘ya’yansa budurwai guda biyu suka yiwa uwar fyade suka yiwa ‘ya’yan fyade.

 

Addu’o’i guda 27 da ya kamata mu rika yiwa yayan mu

Da suka tafi da matar sai suka kira mijin a waya akan ya kawo kudin fansa, sai matar ta karbi waya a gaban kidnappers din tace wa mijin kar ya biya ko kisin kobo, don ko ta dawo gida ba zata rayuwa ba saboda bakin ciki kidnappers sun kwanta da ita sun kwanta da ‘ya’yanta.

 

Akwai bidiyon wata mata da na gani, ita ma kidnappers sun tare ta a mota a hanyar Kaduna ita da mijinta suka tafi dasu jeji, sun yi mata fyade a gaban mijinta, sannan sun yi Luwadi da mijinta a gabanta, bayan sun biya kudin fansa sun fito, shine suka sayar da kadarorinsu suka bar Nigeria zuwa wata kasa.

 

Bello Yabo

Wannan labarin mai taba zuciyar imani ne, Sheikh Bello yace shugaba Muhammadu Buhari sai Allah Ya tuhumeshi akan wadannan abubuwa da suke faruwa.

 

Muna rokon Allah Ya amintar damu daga dukkan sharri.

 

Bello yabo

Leave a Comment

error: Content is protected !!