Hausa Novels

BINTU DIYAR BAYI CE HAUSA NOVEL COMPLETE

BINTU DIYAR BAYI CE HAUSA NOVEL COMPLETE

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

KADAN DAGA CIKIN LITTAFIN…

[DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI✍🏼

SHIMFID’A

NIAMEY

Niamey shi ne babban birnin Jamhuriyar Nijar, wanda shi ne birni mafi girma a kasar, dake da girman murabba’in kilo mita (239.30) Tun a karni na 18 ne aka kirkiro Niamey, sai dai a wancan lokacin ba’a dauke shi da wani muhimmanci ba har sai bayan da Faransa ta kafa cibiyarta a wajen a shekarun (1890). A shekarar (1926) ya zamo babbar birnin kasar ta Nijar. Sannu a hankali yawan jama’ar yankin ya yi ta karuwa daga (3,000) a shekarar (1930) zuwa kimanin (30,000) a shekarar (1960). Yawan jama’ar Niamey ya kai (250,000) a (1980), a shekara ta (2000) kuma (800,000). Babban musabbabin karuwar jama’a a Niamey shi ne na yawan kaurar jama’a a lokutan fari.

A matsayinsa na babban birnin Jamhuriyar Nijar, akwai wuraren tarihi da suka hada da gidan tarihi na kasa da gidan zoo, akwai kuma cibiyoyin nuna al’adun gargajiya na Amurka da Faransa da Nijar. Hakanan kuma akwai manyan kasuwanni bakwai a birnin. Kashi (90)cikin dari na jama’ar Niamey Musulmai ne, anan ne kuma ake da hedkwatar mabiya darikar kirista ta Roman Katolika.

SA’AYRASA

MASARAUTAR SA’AYRASA yana bangaren kudu maso gabashin Nijar, kuma yana da girman murabba’in kilo mita (156,906). Masarautar Sa’ayrasa na iyaka da Masarautar Fabarusa, ta Arewaci da Zindar ta Yammaci da Najeriya ta kudanci sai kuma Chadi ta Gabashi. Masarautar Sa’ayrasa ta kasance d’aya daga cikin masarautar da ba su da yawan jama’a, wanda kidayar shekara ta (2001), ta nuna yawan mutanen masarautar ya kusa dubu dari hudu. Jama’ar Masarautar Sa’ayrasa sun hada da Kanuri da Tubawa Hausawa da Fulani da Larabawa. Tattalin arzikin masarautar ya ta’allaka ne kan kiwo da noman rani da kuma na damina. Abubuwan da aka fi nomawa a yankin sun hada da gero da masara da shinkafa da kayan lambu irin timatir da barkono. Sai dai kuma duk da noman da ake yi a masarautar, masarautar ta kasance mafi koma baya ta fuskar noma a Nijar saboda fari.

FABARUSA

MASARAUTAR FABARUSA shi ne ya fi kowanne yanki girma a masarautar Nijar, wanda girmansa ya kai murabba’in kilo mita (634,209), watau kwatankwacin kashi hamsin da biyu cikin dari na girman Nijar baki daya. Masarautar Fabarusa ta had’a da Hamadar Tenere da Bilma da kuma yankin Air mai cike da tsaunuka. Mafi yawancin jama’ar Masarautar buzaye ne; akwai kuma Tubawa da Fulani da kuma Hausawa. Babbar sana’ar jamaar masarautar ta asali itace cinikin gishiri da dabino, sai dai a shekarun (1990), harkar bude ido ta zama wata babbar sana’ar yankin, hakanan karfen Uranium da ake samu a garin Arlit na samawa Nijar kashi (20)cikin dari na kudin shigar da take samu.

NIAMEY 1/01/2000

Tafe su ke cikin mota,tin da suka baro masarautar su wato Sa’ayara ta tsunduma cikin kogin tunani, ba ta gushe ba har su ka shigo Niamey, in da makarantar su wato SOVEREING GIRLS SECONDRY SCHOOL ta ke. Wato ‘ya’yan manya da sarakuna na sassa,masarauta da yankunan jamhuriyyar Nijar waannan makarantar su ke. Ajiyar zuci ta saki ganin sun doshi kofar makarantar, yayin da motoci biyu da ke gaban ta su su faka, ta su wacce ta ke ta uku ita ma ta faka. Waigawa ta yi dan ganin ko d’ayar da ke tafe bayan ta su ta sami isowa,ile kuwa sai gasu sun karaso a hankali su ka faka bayan ta su. Hankalin ta ta mayar kan kofar makarantar ta su. Motoci huɗu ne jere reres su ka taho kawo Gimbya Binta yar sarkin Sa’ayrasa makaranta. Ta fari ɗauke da dogarawa guda biyu da direba, ta biyu bayi ne mata su huɗu, sai kuma wacce Gimbiyar ‘yar sarki mai dole ke zaune gidan baya, ta yi ɗai-ɗai ta na shan kamshi, tare da ita baiwar ta ce Bintu zaune gaban mota da kuma direba,sai cikon na hud’un dogarawa ne su huɗu zaune, biyu gaba biyu baya.

Tsawar da ta ji an daka mata ya sa ta yi firgit ta dawo cikin hayyacin ta, jin an furta,
‘’idan kin gama rubuta wasikar jakin da ki ka saba sai ki fita’’.
Faɗin _(driver)_ matu’kin mota ya na mai muzurai. Hakan ya sa ta saurin fitowa daga motar dan kuwa har sun shigo farfajiyar makarantar ba ta sani ba. Tini sauran bayi yan uwanta sun yi sahu suna jiran fitowar Gimbiya Binta. Cikin su Bintu ta shige ta tsaya kan na ta sahun, yayin da dogarai su ka karaso cikin azama, su ka yi na su sahun ta ɗayan ɓangaran. Daga bayin har dogarawa kalar yadin da ke sanye jikin su ɗaya, ruwan toka ne da shuɗi. Rigar ruwan toka sai zanin shuɗi.

Kan su sunkuye babu mai motsi kai kace gumaka aka aje, matu’kin ya buɗewa Gimbiya Binta kofa. K’afafun ta fara fiddowa waje, sanye cikin takalmi fata mai dankaran tsada, sai bayan wasu yan dik’ik’a sannan ta k’arasa fitowa. Tuni suka fara ma ta kirari da faɗin,
‘’taka a hankali Gimbiya yar sarki mai dole, takawan ki lafiya sarauniyar mata’’.

Sanye ta ke cikin kayan makaranta, riga da _skert_ buje sai kuma hijabi wanda ke tsayawa iyaka kafaɗa. Alkyabba ce ta alfarma ɗaure bisa kayan makarantar. Cikin sarauta da tak’ama ta ke takawa ɗaya bayan ɗaya ta wuce, su ka rufa mata baya. Haka su ka wuce ciki zuciyar Bintu cike da tunanin halin da akwatin karfen ta zai shiga matukar ba ta dawo da wuri ba dan Ado matu’ki ba mutunci gare shi ba, dan ya koma da kayan Kuka Sheka ba k’aramin aikin sa ba ne. Hantar cikin ta tuni ta kaɗa

Motoci sai shiga da fice su ke kasancewar yau rana ce ta dawowar ɗalibai daga hutun zango na uku. Kai tsaye sashen ɗakin kwanan ɗalibai su ka nufa, wanda a k’a’ida kowanne ɗaki dan d’alibai biyu aka yi. A dai-dai katangar da ta raba harabar makaranta da sashen ɗakin kwanan ɗalibai su ka tsaya, dan kuwa babu damar dogarai su shiga ɗakin kwanan kasacencewar dokar makaranta ta hana maza shiga. Nan su ke jiran dogarawa masu ɗauke da akwatina su k’araso su karb’i akwatunan dan karasawa da su ciki. Ita kuwa Gimbiya Binta kai tsaye ta shige,biyu daga cikin bayim biye da ita, ya rage daga Bintu sai bayi guda biyu. Dan sauri jikin ta har ɓari yake, Allah-Allah ta ke su samu su shigar da kayan Gimbiya Binta dan ta samu damar kwaso na ta. Sai da su ka ɗauki kusan minti goma kafin su k’araso ɗauke da kaya niki-niki, wanda kuwa faɗar adadadin su aiki ne ja, wai kuma a hakan ma akwai saura cikin mota. Haka suka shiga jidar kayan su na hawa da su sama,bhar bene na uku tukanna ka isa ɗakin Gimbiya. Ta nan kishingiɗe kan gado, ɗakin yayi fes-fes dama tin ana sauran kwana uku a dawo makaranta a ke gyarawa.

]

KU SAUKE CIKAKKEN LITTAFIN ANAN KASA👇👇👇

 

 

Preview: [DOWNLOAD COMPLETE BOOK 👇👇👇]
 

Name: Bintu diyar Complete
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: MYNOVELS.COM.NG
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books
Groups/Writers: Billyn Abdul, Benaxir Oumar, Eyshat, Nadia Buhari, My Novels, Zamani Writers Association, Exclusive Writers,Alheri writers,Best Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: July, 2021

 

3 Comments

Leave a Comment