Bororoji Hausa Novels Complete
Tag: Bororoji Hausa Novels Complete
BABI NA ƊAYA
Niger Republic.
Tayi makotaka da wasu ƙasashen har guda bakwai.
Chad
Burkina faso
Benin republic
Libya
Algeria
Mali
Nigeria.
Kuma dukkan su ƙasashen a zagaye suke da kabilar Wodaadabe Bororo da wasu dangin Fulanin…
2000/ May/08
Nishi take a hankali, tare da cizon bakinta. Iska ta kuma ja alamar tana cikin tsananin zafin nakuda, juya kai tayi cikin tsannanin takaici da bakin ciki, ga wani abu da ya tsaya mata a makogaronta. Yau kimanin wata goma sha biyar kenan da take jin abin a ranta, har yanzun bata ji saukar shi ba.
“Sannun Abuh ga ruwan addu’o’in sha Insha Allah zaki sauka akan gwiwar lafiya.” D’ago kai tayi ta kalle shi cikin tsannanin k’iyayya da bakin ciki, sannan ta sunkuyar da kanta, tare da had’a kai da jikin itaccen da akayi gadon kara dashi. Ta kuma sauke wata ƙatuwar nishi a hankali jariri ya fado daga kasanta, cikin wani irin kakkarin kuka bayan ya zabga atishawa, Allah da idon shi ya diro da uwa baki daya.
Murmushi tayi lokacin da ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, tare da wuccewar abinda ya tokare mata kirjinta. A hankali ta mike tare da ɗaukar wani mayafi da zani ta daura sannan ta dauki babban zanin da yake sayo mata, tayi kunzugu dashi. Kafin ta isa gaban shi tace mishi.
“Kowacce rayuwa akwai samu akwai rashi, akwai nasara akwai faduwa. Kamar yadda ka zalince ni Ya Allah Ya ninka maka abinda kayi min. Kamar yadda ka saka ni kuka Ya Allah Ya sakaka kuka. Bororoji
Kamar yadda ka hanani farin ciki Ya Allah Ya hanaka, zan so Ubangiji ya jefa ka, kasar jahannama. Ya turaka ƙarƙashin fir’anuna da hamana, Ubangiji ya haɗaka da masifa da bala’i, Ya Allah Ya sanyaka bakin ciki sama da yadda ka saka ni.”
Takowa tayi gaban Jaririn ta juyar da shi, tana me kallon Mutumin da yake tsaye, ta sake murmushi me had’e da kuka, tace mishi.
“Ba zan yi fatan kayi irin na wancan mujirimin ba, zan so kayi rayuwa cikin salama, wannan mutumin da ya samar da kai mugu ne, mugu mara alkibla, fasiki mara imani, kazami me dauke da datti da kazamta na bala’i da masifa da jahilci ya goga maka bakin fanti na har karshen rayuwar ka.
Iya haka ma ya ishe ka, ka tsani wanda ya bada gudummawar jazaman ƙaddararka”
Sannan ta tako gaban shi cikin bakin ciki mara iyaka, tace mishi. “Sama’ila kenan, gamu ga ka ga duniya ga Allah ya tsayawa me gaskiya.” Ta juya ta nufi kofar dakin zata fita.
Riko hannunta yayi tare da zuba gwiwar shi a kasa, cikin tashin hankali yace mata.
“Don Allah ki rufa min asiri, ki dauki Yaronki, bai da gatar da yafi naki, Zainabu zan gyara kuskuren da nayi a shirye nake na isa gaban danginki don Allah ki rufa min asiri karki juya mana baya a daidai lokacin da muke bukatar ki”
Cak ta tsaya tare da sake wata irin kuka da sai yanzun ta samu damar yi, tare da shasheka.
“Aminci Allah Rahaman Allah, jin kan Allah Ubangiji ya hanaka su tun daga duniya har lahira” sannan ta saka ta bar dakin da rugar baki daya, tana tafiya tana kuka dukda sulisin dare ne, bai hanata tafiya ba, sai da tayi dogon tafiya kafin ta isa wata iyar karamar gari, tun daga nesa take hango kamar fili ne sahara babu kome sai rairayi. Kurawa gurin ido tayi alamar kamar ba nan take nima ba, dan haka ta cigaba da tafiya har alfijir ya keto sanyin Asuba ya kuma gabatowa zama tayi a kasar wata bishiya tare da kusa hannunta kasar cikin ta da yake murɗa mata jini na zuba a hankali. Barcin gajiya ce ya dauke ta.
Kamar yadda Zainabu ta fita daga dakin da rugar baki daya, zama yayi yana kallon jaririn da yake ta kyankyara kuka kamar zai shiɗe, a hankali yake jin muryan jaririn zaaa a kunnen shi.
Har ya kasa jure kukan jaririn, ya dauki wata zani ya lullube shi, tare da kallon fuskar shi, kamar ya shake shi. Amma ya fasa, can wata zuciya ta kuma bashi shawaran ta kashe shi ya huta da godon abin kunyan da ya aikata. Bororoji.
Zama yayi tare da kurawa jaririn ido, babu abinda ya bar mishi. Domin kwayar idanun shi tarr akan na Ubanshi, kwallar da yake cikin idanun shi ce ta sauka akan na jaririn, ya kuma ware idanun shi tare lumshe nashi. Kwayar idanun yaron kamar an ja shi da kwali, cikin idanun zaiba ce kamar wanda aka zana da ruwan zinari. Sai dan digon bakin tsakiyar ya Kawata kwayar idanun Yaron goshinsa kuwa cike yake da gashi me shegen laushi da tsantsi.
Gashin giran shi a haɗe yake da juna, karan hancin shi har bakin shi, bakin shi karami me kyau dai-dai ta jarirai, wanda Uban yake hangowa sakamakon hasken fitilar kwai da take ci.
Hannun shi ya saka a bakin shi yana tsotsa cikin hakuri da juriya, wani irin kukan danasani ne ya shiga saukarwa Uban.
Me yasa ya aikata abinda yake ganin dai-dai ne, me yasa bai hakura da Zainabu a ranar ba, me yasa ya rushe mata na ta farin ciki.
Yana sane da iyayen ta, sun bar gurin su, ina zasu kuma haduwarl bayan yasan suma Bororoji ne, ba ma zauna bane kuma ba zasu tsaya ba.
Zai yi wuya su tsaya tunda su din Fulanin tashi ne. Bai ga amfanin fitowar shi a cikin kabilar Wodaadabe Bororo ba, bai ga amfanin amsa sunan Bororo ba. Ya zai yi da rayuwar jaririn nan?
Ya rabata da kowa nata, ya raba ta da farin cikin ta, ya kawo ta inda yayi ta gasata da bakin ciki da tashin hankalin, me yasa bayiwa rayuwar shi adalci ba? Me yasa bai tuna da wannan lokacin ba? Ya lalata rayuwar jinjirin shi, ya lalata kome nashi, me zai cewa duniya me zai gayawa mutanen da suka bugi kirji suka amsa karyar shi a a madadin gaskiyar shi? Wacce irin son zuciya ce ta kai shi da aikata wannan kuskuren! Lallai tafiyar shi rugar Alu yaja mishi bakin cikin da zai mutu yana danasanin kuntatta mata da yayi. Kukan jaririn da kiran sallar farko ya sa shi, fahimtar asuba yayi. A hankali ya mai da jinjinrin kamar ya kashe shi amma yana jin kamar haka ba zai yiwu ba.
Tunda yasan makotan bukkar su. Wani irin tausayin jaririn ne ya kuma kama shi. Dan haka ya mike tare da d’aga labulen ya fita a hankali lokacin har anyi Sallah asuba.
—
Bayan yayi alola ne ya dawo D’akin ya rasa yadda zai yi da jaririn, domin ya cikawa mishi kunne da ihu, har ta kai makotar shi sun fara zargin ko uwar yaron ta gudu ne yaki gaya musu, kuma har zuwa lokacin bai raba yaron da cibiyar shi ba, dan haka yayi ta zaman dakin yana kallon jinjirin.
“Gafara dai Sama’ila, me nake ji a gari ana ta fadar cewa Abuh ta gudu ta bar maka jariri ba dai abinda su.?” Yadda ta kalle shi cikin tashin hankali, shima kuma ya sunkuyar da kai tare da mika mata jinjinrin yasata fashewa da kuka. Tare da cewa. Bororoji.
“Kaico wannan wacce irin ƙaddara ce? Me yasa kayi haka? Gashi nan abinda kayi ya lalace ya Barka da kunya me yasa ka aikata haka? Me yasa ka rushe yarda da ke tsakanin mu? Meye muka gaza maka? Ni mijina Hamma Sama’ila ka cuci wanna abin ka zalince me zaka ce mishi idan ma abinda ake zargin ka dashi haka ne me yasa?
Me yasa ka tozarta baiwar Allah, innalillahi wa’inna ilaihi rajioun.” Ta kuma fashe da mugun kuka tana kara rike dan jinjirin. Tana kuka kallon shi, sannan ta fita da jaririn tana wani irin kuka me ban tausayi, duk bukkar da ta shige sai taji sun ce mata “tir” har ta isa bukkar ta, mijinta me suna Sanda ya fito tare da kallonta da dan luɗi, yace mata.
“Kabo lafiya?”
“Sanda me zanyiwa Hamma Sama’ila ya fahimci abinda ya aikata? Me yasa yake da mugun son kanshi? Meye ya saka shi aikata abinda zai saka mu kuka har karshen rayuwar mu.”. Shiru yayi sannan yayi kwafa. Kafin yace mata.
“Shiga da jaririn ciki an fara cika mana” juyawa tayi ga wasu daga cikin mutanen da suke kewaye dasu har sun fara fito mishi, dan haka ya shiga cikin dakin, tare da sake labulen. Ta saka jaririn a gaba tana kuka..
Shi kuma ya nufi bukkar Sama’ila.
Yana shiga ya same shi zaune ya cusa hannu a cikin gashin kanshi, yana nazarin makomar rayuwarsa da na abinda aka haifa.
“Sama’ila meye ya faru? Ina Abuh?”
“Ta tafi, kome ya lalace kuma nayi farin cikin faruwar haka. Domin ta haka ne zai saka na girbi abinda na aikata, kuskuren ne babba ka kalubalanci kaddarar wani, amma babban tashin hankalin yadda rayuwa zata juya maka idan har duniya ta san waye kai? Meye matsiyin shi a cikin al’umma? Meye zance mishi a cikin al’umma,? Me zan mishi idan ya min tambaya daya tak? Sai yaushe zamu daina aikata laifukan ci da karfi? Yaushe kuka zata daina wanzuwa a zukatar mutanen da suka fada irin abinda na aikata?
Yan mata nawa ne zasu daina kuka? Yan mata nawa ne zasu daina gudun kabilar Wodaadabe? Me yasa muka yi kaurin suna ta hanyar lalata farin cikin wasu? Me yasa na san wani sirri har na saka Iyaye da yawa kuka? Sanda nayi tir da Allah wadaran halin irin nawa, a wancan ranar abinda take so ta zab’a amma na kasa Fahimtar haka,.
Iyayen ta sun gudu sabida abin kunya, mijin da zata aura ya tare ni naashi dukar da sai dai wani ba shi ba. Tir tir tir da halina.” Ya fada yana me fashewa da kuka. Can kuma ya shanye kukan yana kallon Sanda wanda yake kallon shi cikin tausayi.
“Babu kome ya yaron yake ka duba min shi”
Ta faɗa tare da juya mishi baya, yana kuka sosai, haka sanda ya fita daga dakin, shima idanun shi yana cika da kwalla, sau daya ake aikata kuskure amma sai ka kai sau dubu kana danasani mara amfani.Yau ga abinda ya nusar dashi ya faru karka zama mara adalci a rayuwarka domin goben ka zata maka rashin adalci.
Koda ya koma gida ya samu tayiwa jinjirin wanka tass, sannan ta kuma yanke cibiyar da ba a yanke ba. Ta binne shi sannan ta nad’e shi cikin farin mayafi, kallon jinjirin take tana mamakin yadda bakin jinjirin ya bayyana tun bai sha iskar duniya ba, dan haka ta dauko kasko ta fara gasa mishi cibi yana ihu da kuka. Kafin ta gama ta kuma kwantar dashi dan ya sha ruwa ainun.
—
Bude ido tayi tare da kallon dakin da take, kokarin tashi take taji alamar an saka mata abu a hannunta, kallon gurin tayi taga ƙarin ruwa ne. Da sauri ta bude bakinta zata yi magana.
Wani farin dogon mutum ne ya shigo, cikin farin labcoat. Ya kalle ta yana murmushi.
“Sannun ya jikinki?”
“Da sauki” ta faɗa tare da juyar da kanta gefe
Safar hannun ya saka tare da nufar kanta, zai duba ta tace mishi.
“Karka tab’a” jan kujeran yayi yana kallonta, kafin ya nutsu ta fara kokarin dubata.
“Kin haihu baki tsaya duba matsalarki ba, kika baro can din jini na zuba miki, me yasa kike haka?”
“Me yasa ba zan yi haka ba? Me yasa kowa ya guje ni? Kai ma ai sabida ina kawo tallar nono nan yasa”
“Zainab!” D’ago kai tayi tare da kallon shi.
“Har yanzun babu abinda ya sauya! Kuma ban ga laifin su dan sun gudu ba, sai dai akwai matukar ciwo abinda ya faru dake, kuma ba dukkan iyaye bane zasu fahimci girman kaddarar da ta.”
“Me yasa ita ƙaddarar bata biyo ta kan kowa ba sai ni? Me yasa babu wanda ya gane akwai ƙaddara sai da ya faɗa min, idan har da gaske batu ne na kaddara jeka dawo da da ahalina da suka tserewa ƙaddara ta, idan kayi haka zan Fahimci girman abinda kake nufi da ƙaddara.”
“Kin jahilci ƙaddara amma zan barki nan da kwana uku idan kin ji sauki muje a dauko abinda kika haifa, ko ya mutu ne?”
Cikin wani irin bakin cikin tace mishi.
“Bai mutu ba,amma kuma ba zan dauke shi ba, ya zauna ya girbi kuskuren da uban shi yayi.”
“Me yasa baki da tausayi? Me yasa baki da hankali? Me yasa baki da imani, toh zamu je mu dauko shi.”
Cikin fushi ya fice daga dakin , ta fashe da kuka wanda take tun daga kasar zucuyarta. Tasan tunda ta ganta a cikin asibitin tabbas ta shigo garin Maradi ne, tunda dama a wani kauyen Maradi suke….
**
Yau kwana biyar da haihuwar Yaron, amma baki daya kauyen an tsangwame su, musamman Sama’ila wanda shi ya fi kowa fuskarta matsa kai ko masalaci, ya je ba a sallah dashi, wannan dalilin yasa aka daina ganin shi a masallacin baki ɗaya.
Shiru da ta daina ganin dan uwanta shine tazo duba shi, dake ko aika ne an hana yara mata, tana tafe tana jijjiga yaron, wanda nonon akuya ake bashi yake sha. Abin tausayi, yana ta kyankyara kuka, tana isa bukkar ta d’aga labulen wayam ta gani, cikin tsoro ta kuma shiga dakin Babu Sama’ila babu dalilin shi, sai wata yar tsohuwar fatar rago da yayi rubutu da harshen ajami da shi ya rubuta mata.
كي حقر مثني مك لف بذ أي ذم ا غرنني يثن بر غرا اني إكا قام الحر
Kuka ne ya kuma kwace mata, tana gani da sauri ta fitar dashi wa mijinta domin bata san me ya rubuta ba, kuma duk abinda ya rubuta ba zai wuce bankwana ba. Dan haka ta fita tana gudu ana kauce mata a hanya, koda ta isa gidan tana shiga ta mika mishi. Yana dubawa yaga sakon.
“Kash! Sama’ila me yasa baka da kirki? Me yasa baka da hankali kana tir” ya faɗa da karfi dan ya gama jin haushi kamar zai yi wani abu.
“Ina fama da matsalar Ardo ya sallame mu a garin. Kuma haka shine mafi alkhairi domin idan muka cigaba da kallon wannan yanayin zamu iya shiga tashin hankalin da yafi wannan abin kunyar, kuma wannan abin zai fi mu shiga tashin hankalin da yafi ba mu. Dan haka zamu wuce Maradi kawai.”
“Wannan shine adalcin da zamu yi mishi.”
Name: | [Bororoji HAUSA NOVEL ] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | November, 2021 |
Yayi sosai
allah yasa mudace