Boss Bature Hausa Novel Part 1
_💋Boss Bature_
dawowa major yayi shida dr Emran,a cikin ɗakin da aka kwantar dasu hossana,fuskar major ɗauke da murmushi yace. “An yi discharge ɗinku,kwanan asibiti ya ƙare yanzu zamu wace gida,”
Murmushi suka saki gaba ɗayansu,jiki na rawa hossana ta sauko daga saman gadon,itama jahad lalla6awa tayi a hankali ta sauko saboda ƙafarta,
Kallonsu dr emran yayi tare da cewa”zamu yi missing ɗinku sosai gsky,amma tun da a wurin omar ku ke, zamu dinga zuwa muna ganinku,”
Murmushi suka saki gaba ɗayansu,gaisawa major ya ƙara yi da dr emran sannan yayi mashi sallama,
shiga gaba yayi su hossana suka bi bayanshi, daker jahad ke taka ƙafarta da taimakon hossana take tafiya saboda ta dafa kafaɗarta gudun karta fama ciwon ƙafarta,
A haka har suka ƙaraso harabar asibitin wurin ajiye motocinsu, hannu major yasa tare da buɗe masu ƙopar back seat don su shiga su zauna,har jahad tasa kai zata shigo suka jiyo muryar nurse camila tana cewa “wait !! Wait !!,
Dakatawa su kayi gaba dayansu suna kallonta dama kuma sun so su tambaye ta,ɗan zaman da su kayi da ita ba ƙaramin shiga ransu tayi ba, ƙarasowa tayi kusa dasu tana faman sauke ajiyar zuciya hannunta na ruƙe da jakar kaya, daga bisani ta ɗago fuskar nan ɗauke da murmushi tace”ba sallama twins?yanzu da banzo ba shikenan zaku tafi ko? Ku barni da kewarku,
murmushi sukayi gaba ɗayansu jahad tace “a’a bamu ganki bane shiyasa,”
kallon major tayi tare da cewa “tare dani zaku tafi, saboda already mun yi magana da marshal omar, ya dauke ni amatsayin wadda zata cigaba da kula da lafiyarsu,inaso naga gidan saboda in na tashi zuwa,
wani irin farin ciki ne ya rufe su hossana da jahad saboda sun lura da irin mutuncin dake gare ta, ba ƙaramin kula zasu samu a wurinta ba,
Murmushi major yayi tare da cewa “naji daɗin jin hakan sosai,saboda na lura da yadda kikeson yaran ina fata zaki kasance tare dasu,kuma zaki riƙe su amana,”.
Jinjina kai Camila tayi tare da cewa “NA RIƘE AMANA,”
daganan suka shiga cikin motar jahad da hossana suna a back seat,major na a mazaunin driver yayin da Camila ke Zaune a other seat ɗin,”
a hankali yake driving dinsu harya fuce daga asibitin,ya miƙi shantalelen titi dasu, ajiyar zuciya kawai suke sauke wa ga wani farin ciki daya baibayesu, ba don komai ba sai don sanin cewa Ƙarshen wahalarsu yazo, yanzu lokacine da zasu huta ma rayuwarsu,suyi rayuwa ta ƴanci kamar kowane ɗan adam, batare da an ƙuntata masu ba ko an cutar 😇
Lokacin da suka ƙaraso gidan Uncle Abusufyan nan fa hossana ta zaro ido tare da buɗe baki alamar mamaki yarda kasan ƴar babyn roba haka ta koma sam bakinta yaƙi rufuwa don murna, ita kanta jahad bakinta a buɗe don murna fararen hakoran nan nata kamar gonar auduga, adai dai bakin gate ɗin major ya tsayar da motar sannan ya danna horn da ƙarfin gaske,
sai gashi an buɗe masu gate ɗin ta ciki, ba kowa bane face abokin Major ɗan leƙen asirin shi, acikin gidan ya kwana saboda omar ya dauke shi aiki, bayan alherin da yayi masa na kyautar mota sabuwa mai kyau da tsadar gaske, ga kuma uban salary daya yanka masa,😇
A hankali major ya shigar da motar cikin gate ɗin ɗan dagatawa yayi da driving ya zuge glass ɗin motar ya kalli osman yace “Shege mutumina, ka ga yarda ka canza jiya izuwa yau har wani haske ka fara? Cike da zolaya yayi maganar,
Dariya Osman yayi tare da cewa “ba dole kaga canji ba,an gaya ma yin karin kumallo da farfesun kaza wasa ne? mutun ya kwana a ac,sannan yayi wanka acikin kwami haba ae dole ma ne in canza,”
gaba ɗaya suka fashe da dariya jin abunda yace,
Major yace “nifa wasa nake maka malam, taya zaka canza kawai daga jiya zuwa yau don ka kwana a ac, kayi breakfast da farfesun kaza? Nace sannu ko uban son banza ae sai nan da irin one month haka,nan zamu ga canji,
Murmushi osman yayi tare da cewa ” ka shiga ciki ka sauke su,in ka dawo zamuyi magana dakai, akwai labari mai daɗi,”
Major yace “okey bari nazo,” yayi maganar tare da sauke glass din motar ya wuce dasu ciki, adai adai stairs ɗin da zai sadaka da main palour ɗin gidan ya sauke su,
Buɗe motar Camila tayi ta fito, sannan suma su jahad suka fito daga ciki suna ƙarewa katafaren gidan kallo ya haɗu iya haɗuwa abun ba’a magana, Omar yasa an canza mashi komai nashi an ƙara ƙawata gidan sosai,
gaba dayansu sun ƙame suna kallon haɗuwar gidan, ganin basu da niyyar shiga daga ciki yasa major cewa “let’s go in pls,”
Cikin rashin sani jahad ta take ƙafarta ba don komai ba sai don hankalinta daya tafi wurin ƙarewa gidan kallo,ƙara tasaki tana yarfa hannu tana faɗin “wash Allah na,” jin haka yasa camila tayi saurin dawowa ta inda suke, ta taimaka mata wurin yin tafiya don su shiga ciki,
Major ne yayi masu jagora su kuma suna abayan shi, har suka shiga cikin haɗaɗɗen jigunannan falon,nan fa suka baza ido suna kallon haduwarshi, wasu irin matsiyatan royal sofa set ne acikin sa masu numfashi ɗunɗuma ɗunɗuma a jere launin su brown colour,ga wasu set na Cushions Jere asamansu difference colour,duk gasu nan ba ƙaramin ƙawata kujerun su kayi ba, daga tsakiya wani ƙayataccen table ne legs dinshi brown ne, while daga saman glass ne, an ajiye flower asaman shi, ga fruits basket mai dauke da kayan mar mari, ba komai yafi tafiya da hankalin hossana ba face tanƙameman kwan filitar dake bama ɗakin haske tamkar zai faɗo ma mutun akai haka yake, sai kuma tv stand din dakin faskekiyar plasma ma ce mai dauke da speakers na jin sauti, ga wani telephone table dage a gefe, bari dae in taƙaice maku zance komai wannan da kuka sani a palour an zuba masu shi,
Sai faman yarfa hannu hossana take yi, yarinya fa takusa zauce wa ganin irin gidan da yaya Omar dinsu ya gwangwaje su dashi, wani abun ma sai mun shiga bedroom,
Jahad kuwa murmushi kawai take saki tana bin ko’ina da kallo,ita kanta Camila gidan ba ƙaramin burgeta yayi ba komai tsaf a natse ba tarkacen hauka,
Can dae hossana tace “Allah yasa ba mafarki nake yi ba,dan Allah koma mafarki nake yi jahad kada ku tashe ni,” ta fadi tana faman hadiyar yawu,
Dariya su kayi gaba ɗayansu, Major yace “wannan zahiran ne ba mafarki ba ne, kaɗan daga cikin irin son da ya’ya omar dinku yake yi maku kenan,zai iya yin komai akanku more than u think, ni dae fatana agare ku shine ku kasance masu yi mashi biyayya, ku bishi sau da ƙafa kada kuyi amfani da son da yake yi maku wurin karya mashi zuciya,ko ku ce zaku canza halayyarku saboda wata dama da kuka samu, yanzu lokaci ne da zaku more rayuwarku bayan duk wahalar da kuka sha,”
Sosai major yashiga yi masu nasiha, duk sun kasa kunne suna sauraronshi,sannan kuma suna amsa mashi da insha Allah,
Bayan ya kammala daga ƙarshe yace “ku samu wuri ku zauna mana,nasan kuna jin yunwa yanzu zan sa ayi maku oder na abincin da zaku ci, sannan ga bedroom nan zaku iya shiga ciki ku huta,”
A natse suka ƙarasa tare da samun wuri suka zauna fuskar nan fa awashe,
Mayar da idonshi yayi kan Camila yace “zamu tafi tare ne? Na sauke ki a asibitin ko kuwa,”
cikin sauri tace “no i will stay here wit them,cos i ave done my work bani da sauran duty till tomorrow,”
Murmushi kawai major yayi sannan yace “okey,” sannan yasa kai ya fuce,
A jiyar zuciya ta sauke tare da samun wuri itama ta zauna, bayan ta ajiye jakan kayan data zo da ita,
kallon juna suka shiga yi suna murmushi,yanayin iskar falon badae daɗi ba yadda sanyin ac ke ratsa sassan jikin mutun,
Ganin sun zauna shiru yasa Camila cewa “ba ku buƙatar shiga daga ciki ne? ta tambaya tana kallonsu
Jahad ce tafara cewa “inason nayi wanka, hossana ma tace “nima,”
tashi camila tayi tare da cewa “mu shiga daga cikin ɗakin to, nima inason nayi wankan,” tayi maganar tare da ɗaukar jakar kayanta,
gaba tayi suka bi bayanta ɗaya daga cikin bedrooms ɗin suka tunkara, ƙoparsa a rufe take amma bada key aka datse ta ba, hannu tasa ta tura nan take ƙopar ta buɗe, shiga ciki su kayi atare,
haɗaɗden bedroom mai ɗauke da tafkeken gado fankacece, yaji lumbutsetsiyar katifa lallausar gaske ga wasu matassan kai masu laushi asama an jera su, irin gadon da kana hawa saman shi ko bakayi niyyar yin bacci ba nan take zai ɗauke ke saboda daɗinsa 🥱 an gyare komai an shimfiɗe shi da bedsheet,side by side na gadon akwai side drawers, masu ɗauke da lamps,
daga can ɗayan bangaren ɗakin kuwa wurin Closet dinsu ne, ga wani haɗaɗɗen Dressing mirror an cika masu front dinshi da kayan make up da tsadaddun mayuka na jiki, komai an sanya masu, jerin wurin takalmansu,hand bags da sauran abubuwa da dama ba abun da omar yabari komai ansa masu,
jahad ce tafara shiga toilet ɗin don a ƙagare take da tayi wanka,lokacin da ta shiga cikin toilet nan fa taga zallar haɗuwa ta jima tana bin ko’ina da kallo kafin daga bisa ni tayi wankar daker tare da yin alwala saboda in an kira sallah tayi, fitowa tayi a hankali waist dinta daure da towel mai ɗan tsayi wanda ta samu acikin toilet ɗin, hannunta na ruƙe da doguwar rigarta da ta cire, samun su tayi zazzaune daga gefen gadon suna fira da hossana da Camila,
Ganin ta fito yasa camila tashi ta shiga toilet ɗin,
a cikin laundry basket ta turo rigar, sannan ta ɗan juya ta kalli hossana dake ta faman lumshe ido alamar bacci tace “karfa kiyi bacci don na son halinki, ki bari kiyi wanka ke ma,”
Murmushi tayi kafin tace”ae bazan iya bacci ba jahad, saboda gani nake kamar in na kwanta zan farka na ganni a gidan wannan matar da ta azabtar damu,nakasa yarda cewa wai mune acikin wannan katafaren gidan nan mu kaɗai abun mu,gsky yaya omar ba ƙaramin ƙaunarmu yake yi ba,”
Jahad tace”nikaina ina mamakin hakan hossana,ashe akwai wata rana da zato mana irin wannan,mun samu yaya mai son mu tamkar ƙannensa duk don saboda mu ya Omar yabar komai nasa don ya ceci rayuwarmu,har yanzu ina mamamkin hakan hossana, yaya omar ya sanar dani cewa ɗan uwanshi yana kwance rai hannun Allah babu tabbacin cewa zai rayu,amma a hakan ya tsallake shi yazo wurin mu wannan wane irin mutun ne?samun mai iri Kyakkyawar zuciyarshi zaiyi wuya a faɗin duniya,
(shiyasa Hafsat bature take kamu) 🙄
ta yi maganar ne a lokacin datakai wurin closet tana neman ta inda zata buɗe shi,tana aza hannunta a jikin closet din nan take doors din dake jiki suka zuge da kansu, har sai da jahad ta ɗan tsorata tayi baya,
tasowa hossana tayi itama tana kallon wurin kayan nasu, yadda suke tagwaye haka omar yasa aka jera masu komai kala biyu, jerin wurin pyjamas ɗinsu daban, jerin wurin dogayen riguna daban,jerin wurin jeans da t shirt daban, ga jerin under wears shima daban, komai nasawa ajiki an zuba masu shi,har sun wuce iyaka,
“jahad har naji inason nayi wanka wlh,saboda in canza kayan jikina,” acewar hossana dake ta faman yarfa hannu tana kallon kayan,
Hannu jahad tasa tare da curo wasu pakistan masu kyan gaske,tana shafa jikinsu tunkan tasa har ta gano kyan da zasu mata,
a gefen gado ta ajiye su, sannan ta koma gaban mirror tana shafe jikinta da ɗaya daga cikin mayukan da tagani ajare, bayan ta kammala ta kuma feshe jikinta da turare mai ƙamshin gaske,
Sannan ta dawo ta tsaya a gefen gadon tana zura kayan ajikinta, duk hossana na can tsaye wurin closet ɗin tana ƴan ta6e ta6e,ji take tamkar tabi kowannansu ta gwada ajikinta,
Bayan jahad ta gama kimtsawa cikin pakistan din komawa tayi gaban mirror tana kallon jikinta,riga ce mai dogon hannu har guiwar ƙafarta sai wandon burgujeje irin nasu,ta yafa mayafin asaman kafaɗarta, sumar kanta kuma ta zubo a bayanta, murmushi kawai takeyi tana kallon kanta a cikin mirrow,
Muryar hossana ce ta katse ta da cewa”kinyi kyau sosai jahad saina ga kin koma mun tamkar ketrina kef,”
Jahad tace”sannu shugaban makaryata ni bada ketrina nake kama ba sai dae helen,oumma tace kamannin mu sak irin nata,’ tayi maganar tana gyara gefen gashinta da hannunta,
Hossana tace”wacece helen kuma”?
“Ƴar film ce mana ta ƙasar ethiopia,” Jahad ta bata amsa atakaice, kafin hossana ta ƙara cewa wani abu, sai ga Camila tafi to daga toilet din daga ita sai ɗan pant da bra, cikin sauri suka sanya tafukan hannayensu tare da rufe fuskokinsu cikin jin kunya,
tsayawa tayi tana kallonsu cikin mamaki take cewa”why are u hidding ur face pls? Can i know
Jahad tace”mun ji kunya ne,”
Murmushi camilla tayi tare da girgiza kai tace”kuna da kunya sosai,in dae haka ne kam ba zaku iya rayuwa a ƙasar mu ba,”
“Wata ƙasa ce”? Hossana ta tambaya,
Camila tace “Mexico,”
Jinjina kai tayi tare da cewa”ni ko sunan ƙasar ma ban ta6a ji ba gsky….”jahad ce ta katse ta da cewa “hossana zoki wuce kije kiyi wankan kema,”
Amsa mata tayi da toh sannan ta wuce cikin toilet ɗin,
Ita kuma jahad ta kama hanyar fita daga ɗakin har lokacin fuskarta na rufe da tafin hannayenta, abun sai ya ba camilla dariya sosai,
Sai da ta fita daga bedroom ɗin sannan ta soma sauke ajiyar zuciya, shiga cikin falon tayi, tana ƙare masa kallo, zagaye shi ta shiga yi tana tatta6a dogayen curtains ɗin dake kewaye dashi,
Sallamar Osman ce ta dakatar da ita, cikin sauri ta amsa mashi da wa’alaikum salam,sai da ya fara tambayar iznin shiga daga ciki, ta amsa mashi sannan yasa kai cikin falon,
Hannun shi na ruƙe da manya ledoji na abincin da yayi masu oder a restaurant,yarda yaga jahad ta kimtsa tamkar ba ita bace ya gani acikin daji ba sume cikin ciyayi,ba don akwai dressing na ciwo a forhead dinta ba, da bazai iya shaida taba,
.murmushi kawai yayi tare da miƙa mata ledojin hannun shi, cikin sauri tasa hannu ta kar6a tana yi masa godiya,
Har ya juya zai fita sai kuma ya juyo ya kalle ta yace”pls game da abunda ya faru da ku a gidan yayan Omar,wurin matar yayan shi kada ku sanar dashi komai don nasan zai tambaye ku ne,
Murmushi jahad tayi tace”insha Allah ba zamu sanar mashi ba,”
“Yawwa” ya faɗi tare da juyawa yasa kai ya fuce,
Ajiyar zuciya ta sauke tare da ajiye ledojin a saman table,tana jiran su kammala kimtsa wa su fito suci atare,
Goya hannayenta tayi a ƙirjinta tana faman sakin murmushi,bakowa ne ke faɗo mata aranta ba face yaya Omar dinsu,ta ƙosa ta sashi a idonta saboda tayi mashi godiya sosai,kuma tayi missing din wannan kyakkyawar fuskar tashi,
tana cikin wannan tsayuwar sai ga Camila ta fito fes abunta har ta canza kayan jikinta,v neck shirt ce ajikinta fara sai wando jeans, ta ɗaure sumar kanta da ribbom,fuskarta asake ta ƙaraso tare da samun wuri saman 3 seater ta zauna tana kallon jahad tace”kina so ciwon naki ya dawo sabo mu koma asibiti gobe ko?
Girgiza kai jahad tayi tare da cewa”a’a bansan na take ta bane,ciwon bai mun zafi yanzu ina ji kamar naji sauƙi ma,”
Tace “duk da haka yakama ki kula just in case,”
Amsa mata tayi da toh sannan tace “ga abinci nan,an aiko mana shi,” ta fadi tare da ƙarasawa wurin table ɗin ta matsar mata dashi kusa da kujerar da take zaune,
Sannan itama ta samu wuri ta zauna a kusa da ita,hannu camila tasa ta buɗe ledar ta farkon,kayan ciye ciye ne gasu nan chips, bugger, shawarma da sauran wasu tarkacen, ɗayar ledar kuma da ta bude masu fried meat ne (tsiren nama) mai yawan gaske yaji kayan haɗi sai ƙamshi yake yi,
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza 3
-
Zuciya ta
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi
-
Aure da haihuwa
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya
-
Gangar Shedan
-
Angon mata biyu
-
A gidan mu take
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
Powered by: www.mynovels.com.ng
Dole ne su buƙaci plate don haka jahad ta tashi tare da cewa “bari na ɗauko mana plate,” camila tace “plate yayi kaɗan tray zaki samo mana,”
Amsa mata tayi sannan ta tunkari doors din dake a cikin falon tana neman kitchen babu alamar kitchen na a wurin,
“Ki duba down stairs baza arasa acan ba,” acewar camila,
Cikin sauri jahad ta hau benen da zai sauke ta a dowm stairs tana sauka cikin sittingroom din ta hango kitchen ɗin, tasha mamakin ganin yarda aka ƙawata ɗakin,
Cikin hanzari ta wuce kitchen ɗin an tsara shi sosai,ƙarasawa tayi jikin kitchen shelves anan ta samu trays a jere ta ɗauki ɗaya,komai na cikinsa sabone wasu acikin kwalinsu wasu kuma a buɗe suke, tare da cokali ta haɗo masu da knife saboda taga tsiren naman basu zuge shi ba acikin tsinken shi yake,zasu buƙaci su yayyanka shi in zasu ci,
Fitowa tayi daga kitchen ɗin sannan ta koma upstairs ɗin, tunkan ta ƙarasawa ta samu hossana zaune agefen camila hannunta ɗauke da tsiren naman nan ta tura abaki sai ci take kamar kura,hankalinta kwance, bakomai bane ya burge jahad ba face ganin yarda hossana tayi wani irin kyau cikin gajeran skirt mini tare da riga ƴar t shirt tabi shape din jikinta, hada ƴar hoda ta shafa ma fuskarta da jan baki,
Ganin jahad ta soma washe mata baki, girgiza kai jahad tayi tare da cewa “dama nasan dole kiyi ƙara’e hossana irin wannan ɗaukar wanka haka,”
“Kaɗan kika fara gani ma,aunty camila ma tace in ta samu hutun aiki zata kaimu saloon a gyara mana gashi tare da ƙunshi ma duka za’a yi mana,”
murmushi jahad tayi a lokacin taƙarasa wurin table ɗin, aza tray ɗin tayi asaman shi sannan ta samu wuri ta zauna itama suka saka Camilla a tsakiyarsu,
ita ta baje masu tsiren acikin tray ɗin ta jera masu shi,sannan ta zuba masu chips ɗin daga gefe,
Nan fa suka gyara zama duka ukun suka tasar ma kayan lashe lashen, ba baka sai kunne, ba kaji komai sai sautin taunar shi da suke abakinsu,
**********************SEHRISH
tun da english teacher ɗinsu ta fita daga class ɗin, sehrish ta kifa kanta asaman desk din gabanta tana ta sharar bacci, har amrish ta gane mata daga jiya izuwa yau sam bata gajiya da yin bacci,alamu ma sun nuna cewa bata fahimtar komai kanta dashi da kwankwon ashana duk ɗaya suke,tashi amrish tayi tare da fitowa daga seat ɗinta ta ɗan sa hannunta tare da bubbuga bayan sehrish tace”ki tashi mu tafi time ɗin break yayi,” kusan sau uku tana tashinta daƙer ta buɗe idonta da suka canza launi saboda bacci, miƙa tayi tare da yin hamma alamar yunwa take ji ga baccin ma bai isheta ba, fitowa tayi daga seat ɗin nata tana cewa”ashe har lokacin break yayi ”
Amrish tace”taya za’ae ki sani, bayan baccinki kawai kike tasha, anya kuwa ma kina yin bacci a gida ne? Ta tambaya tana kallonta a yayin da suke fita daga class ɗin,
“Ina yin bacci mana sosai,”_
“To meyasa kike yin bacci a class?ko karatu ma bakya saurara salon azo yin test ko exam kiyi ta baza idanu kina kallon question paper kina cizon biro ko? Ta fadi fuskarta ɗauke da dariya, itama sehrish din dariya tayi tana cewa “insha Allah hakan ma bazata faru ba,kafin lokacin zanyi karatu sosai,”
Suna tafiya suna fira har suka isa Lunch room ɗin nasu atare suka shiga ciki, students duk sun hallara suna ta having lunch dinsu,
ruƙo hannun sehrish tayi tare da kaita gaban table ɗin da zasu zauna,sai da rishi ta zauna saman table chairs din sannan amrish ta wuce ciki don ta amso masu abunda zasu ci,
Ajiyar zuciya sehrish ta saki tana kallon students din dake zaune a wurin suna cin abincinsu suna shan fira abunsu,zahiri su take kallo amma abaɗi ba komai take tunawa ba face fuskar SGR ɗinta,murmushi ta saki aranta tana cewa “koyana ina yanzu?me yake yi?ko yaci abincinsa?Allah yasa dae baibar cikin shi da yunwa ba,
babu mai bata amsar tambayarta, cigaba da cewa tayi”bani da wani burin daya wuce naganshi cikin nishaɗi batare da wata damuwa ba,amma narasa dalilin dayasa kullum fuskarshi aɗaure baison yin fara’a,inaso na kawo sauyi a cikin zuciyar shi ya Allah ka bani wannan damar da zan zama ɗaya daga cikin farin cikin ran shi,”
Gaba ɗaya tayi nisa acikin tunaninta, batasan meke wakana ba kwatsam taji hannun mutun a ƙirjinta an shafa mata, a wani irin firgice ta buɗe idanunta gabanta na faɗuwa,
Bin su da kallo tayi atsananin tsorace, kai kana ganinsu kasan tantiran ƴan iska ne,su biyu ne mata jikinsu na sanye da uniform riga da wannan mini skirt ɗin,kai kace ba musulmai ba saboda ko head babu akansu, iya gashi ne kawai suka ɗaure abayansu shima ɗin na ƙari ne, ga uban bleaching sun sha abun dae kawai ba’a magana,.
Kallon juna su kayi suna dariya kafin ɗayar tace “wow gaskiya an mana nisa, Sofia tun yaushe aka kawo wannan zazzafar a school ɗinmu batare da sanin mu ba”? ta tambaya tana faman sakin murmushi gefen fuska, tuni jikin sehrish yayi mugun sanyi bakomai ta tuna ba face nasihar da kanal yusuf yayi mata kafin tafara zuwa school,
wadda ta kira da sofia tace”ni kaina bansani ba, amma yanzu tunda Allah ya haɗamu da ita, zatayi mana bayani ne, ta faɗi tana kallon sehrish tare da kashe mata ido ɗaya tace”ƴan mata,naga kin ɗaure fuska may be don na shafa chest ɗinki ne batare da izninki ba,ae mun afwa irin salon tamu gaisuwar kenan,ya sunanki ne”?
ƙara tamke fuska sehrish tayi jikinta na rawa Allah Allah take yi Amrish tadawo don tasan ita zata iya dasu,
ɗan ta6e baki zeenat tayi tare da cewa”Can’t u talk to us? May be don baki son ko mu su wanene ba a school ɗin nan ba,zamu yi maki uziri ne,” ta faɗi tana yarfa hannunta, yatsun nan zira zira tayi fixing nails dogaye a hannunta,
shiru sehrish tayi burinta amrish ta ƙaraso in ba haka ba tashi zatayi tabar musu table din gaba ɗaya ta koma Class, duk da yunwar da take ji acikinta,
Suna cikin zaman ne sai ga Amrish ta ƙaraso fuskar nan ɗauke da murmushi ta ruƙo tray a hannunta mai ɗauke da plate biyu na abincinsu tare da coke,
Sehrish na ganinta ta shiga sauke ajiyar zuciya,amma abunda ya daure mata kai time ɗin da amrish ta ƙaraso kai tsaye bayan ta ajiye masu tray ɗin asaman table din, sai ta miƙa ma Zeenat hannu suka gaisa tare da cewa”Am really glad to see u guys, nayi missing ɗinki sosai my zeenat,” murmushi zeenat tayi tare da cewa”nayi missing ɗinki nima,bcox of u na matsa wa mommy sai mun dawo nigeria sbd a ƙagare nake da na haɗu dake ko fa isasshen bacci bana samu saboda rashinki,”
bin su da kallo kawai sehrish takeyi baki asake, yarda suke magana tamkar irin mace da namijin nan,
Muryar sofia ce ta katse su da cewa “oh ni ba’a ma ta tawa ko Amrish? Zeenat kaɗai kika gani shikenan bari na tafi,” ta faɗi tana ƙoƙarin tashi cikin sauri Amrish tayi holding hands dinta tana cewa”am sorry kada ki tashi pls, in naga zeenat ina mantawa da komai ne,”
ɗaure fuska sofia tayi tace”i can’t stay here,cos am getting jealous bazan iya jure yarda kike son Zeenat ba,
Dariya zeenat tayi tana cewa”in dai akan Soyayyata da amrish ne ke 6ata maki rai sai dae ki mutu,”
ta faɗi tana mayar da idonta akan sehrish da tayi zugudun tana kallon ikon Allah,
wuri Amrish tasamu ta zauna, kusa da sehrish suna facing ɗin su Sofia da zeenat,
ɗan kallonta amrish tayi tare da cewa”am sorry my friend nabarki da yunwa ko”? ta faɗi tana kallon Sehrish wadda jikinta ya gama mutuwa,
“A’a” ta bata amsa a takaice,
Mayar da idonta tayi kansu zeenat tace”bansan zaku zo ba ae dana haɗo mana abincin tare,amma bari na tashi yanzu naje na ƙaro mana yadda zai ishe mu,”
cikin sauri zeenat tace”no ba sai kinje ba its ok ba mu jin yunwa a ƙoshe muke,”
murmushi amrish ta saki tare da kallon sehrish tace”bismillah mufara ci time ɗin komawa class ya kusa,”
Gaba daya hannunta kerma yakeyi a haka ta ɗauki spoon ɗin zata fara cin fried rice din da takawo masu shaqe da plate,tana ɗebowa shinkafar na zube wa saboda rashin natsuwar da take ciki ba don komai ba sai don zeenat data tsare ta da waɗannan manyan idanun nata zubin na karuwai a tsaitsaye suke ga eye lashes da tayi fixing sinsu kamar ɗiyar roba,
Ganin yarda hannun sehrish ke kerma ta kasa kai koda one spoon ne yasa Amrish ɗagowa ta kalli zeenat wadda ta zuba mata ido ko kyafta su bata yi,
ɗan gyaran murya Amrish tayi tare da cewa”Zeeta pls kidaina kallonta hakan na hana ta samun natsuwa,class mate ɗina ce jiya tafara zuwa school bata saba da kowa ba,”
ƙayataccen murmushi zeenat ta saki tare da cewa”its okey,ashe new comer ce, tayi mun kyau ne shiyasa nagaza janye idona akanta,ina fata kin sanar da ita komai game da zama cikin team ɗin mu?
Cikin sauri amrish tace”a’a pls mubar maganar nan,ita ba’a team ɗinmu take ba kawai class muka haɗa da ita,”
zeenat tace”that’s impossible amrish tun da har kina yawo da ita a school dole ta zama ɗaya daga cikin mu,not only that yarinyar ta burgeni sosai……..’kasa ƙarasa maganar tayi saboda ƙarar cokalin amrish data bugi gefen plate dinta dashi tace”Zeeenat! Nace kidaina wannan maganar agabanta bana so,” rai a6ace tayi maganar sannan ta mayar da idonta kan sehrish tace”pls ki ci abincin ki,”
gyaɗa kai sehrish tayi tare da mayar da hankalinta akan abincin dake gabanta,ci take amma batasan inda abincin ke zuwa ba,saboda tsoro da ruɗin da ta shiga,
yunƙurawa su kayi su biyun atare suka miƙe, cikin sanyin murya amrish tace”Am sorry zeenat i don’t mean to hurts u,just bana son muna wannan maganar agabanta ne,saboda batasan komai ba ko mutane batason shiga cikinsu,” hankali atashe take maganar tana kallon su,
atare suka yatsina fuska sannan zeenat tace,kinsan bana fushi dake amrish shiyasa kike mun duk abunda kika ga dama,amma ina so ki sani 6ata mun rai tamkar 6atawa mommynki raine, kuma kinsan mai zo biyu baya ya zama dole kibi umarnin duk abunda nace, don haka wannan yarinyar dole tashiga team ɗin mu !!!
tana gama faɗin hakan taja hannun sofiya suka fuce daga lunch room din
ita dae sehrish zuru tayi tana kallon ikon Allah bayan sun fuce ta mayar da idonta kan amrish wadda jikinta yayi mugun sanyi tuni kuma idonta sun cicciko da kwalla, amma bata bari sun zubo mata ba, sai ma kallon sehrish da tayi tare da ƙaƙaro murmushi tace”ki ci gaba da cin abincin ki mana,naga kin tsaya,”
jiki asanyaye sehrish ta mayar da hankalinta kan abincin tana ci amma zuciyarta ajagule saboda halin da taga Amrish ta shiga akan waɗannan ƴan matan da suka zo,ko su wanene oho,
Ta tambayi kanta,
***************************Twins
Fitowarsu kenan daga wanka atare kamar yarda suka saba kwatsam sai ga haroon ya turo ƙopar ɗakin nasu fuskarshi ɗauke da wannan shu’umin murmushin nashi, tsayawa yayi yana binsu da wani irin kallo jikinshi na sanye da Crazy jeans tare da wata figaggar riga daya sanya, ya tada kwalar rigar tsaye,sam haroon baya kama da musulmai ko a fuska, balle ma daya kasance yana sanya chain a wuyan shi da kuma earrings irin yarda jigunannun ƴan iska ke sakawa,
Kallon juna su kayi atare kafin suka mayar da idanunsu akanshi,tuni ran Jahan ya 6aci ganin yarda yake bin jikinsu da kallo kamar wani tsohon maye, dama daga su sai short towels ajikinsu, farar surar ne mai jan hankali ta bayyana muraran,
ɗaure fuska jahan yayi tare da cewa “me ya kawo ka ɗakin mu? me kuma kake buƙata,indai kuɗi ne suna nan zamu baka,”
ta6e baki haroon yayi tare da yatsina fuska yace “yakamata kasan yarda zakayi magana dani with respect,ko don darajar wannan videon dake ajiye acikin wayata,’
tsuke fuska su kayi atare zuciyarsu na tafarfasa tamkar su rufe shi da bugu haka suke ji,
Cigaba da magana yayi “zuwa nayi don na ƙara tunasar daku, don na lura kamar kun manta da maganar dukiyata dake a wurinku, saboda waccan farin balbelen ɗan uwan naku da bai lfy na lura duk kun wani tashi hankali akanshi,’
Buga tsoki ayaan yayi yace “kada ka sake kiran shi da sunan balbela kadaina haɗa sunayen mu dana dabbobi domin kuwa mu bamuyin munayen ɗabi’un da za a haɗa sunan mu dana dabba, domin kuwa dabba yasan inda yake”
waro ido waje haroon yayi jin abunda ayaan yace a tsananin mamaki yace “Ayaan ni kake kira da sunan dabba”?! Ya tambaya a dan fusace
Cikin sauri jahan yace”kayi shiru ayaan kada kaja mana wani bala’en don na lura bai da Imani ko misƙala zarratin, tunda har bai damu da halin da ɗan uwansa ke ciki ba, burinsa kawai ya ƙuntata ma rayuwarmu,” yayi maganar yana jefar haroon din da mugun kallo,
fashewa da dariya haroon yayi hada dafe cikinsa kafin yace “Waye kuma ɗan uwana? ae ni bana ɗaukarku jini na,ko ajinsi ku farare ne ni kuma baƙar fata ne, in fact ni bani da wata alaƙa daku, Uba fa kowa muka haɗa uwa kuma kowa da tashi, bayan shi kuma sai me?
shiru su kayi suna sauraron shi gaba ɗaya tsanarshi ƙara ninkuwa take yi acikin zuciyarsu,
juyawa yayi tare da cewa “Zan wuce ni ku huta lpy ƴan samari,” yana faɗin hakan ya fuce yana sakin dariya kamar zautacce,
Mayar da ido ayaan yayi kan jahan yace “bro i ave an advise abt that bastard, why not mu kashe shi kawai kowa ya huta, cos i don’t think ko mun bashi kuɗin zai goge videon,”
aɗan razane jahan ya kalle shi yace “ashe baka da hankali ayaan, kisa fa kace? Mu zamu kashe shi? In muka jefa kanmu cikin matsala fa? ya fadi yana kallon sa,
Ayaan yace “ba wata matsala jahan, just lettus kill him kowa ya huta !!!!!!!!!
“Mu bashi time in har muka bashi kuɗin bai goge videon ba, sai mu kashe shi kawai,don da abunda zai ta6a mutuncin family dinmu gwara abunda zai tada masu hankali na ɗan wani lokaci ya wuce” Acewar jahan,
Gaba daya sun amince da shawarar kashe haroon 😳
Duk mutanen da suka zo duba fawan duk sun ragu, har sun mai dashi daki sun kwantar dashi tun ɗazu,
Junaid kuwa lokacin da Abban su yashigo dashi ɗakin shi ya wuce dashi tare da kwantar dashi ya farfaɗo daga suman da yayi amma ya dasa da bacci,
Yanzu wanda suka rage a cikin gidan daga su matasan gidan sai abokin su sgr Shattima sun hallara a garden din gidan suna tattaunawa tare da marshal Omar dashi babban yayan,
Cg Abbas ya jima da tafiya amma yabar Amani a gidan saboda yace zai dawo da daddare ya ɗauke ta, duk ita ta taya azmee rarraba ma masu zuwa dubiya lemun a cups har suka lafa,
shigowa ɗakin Abbansu yayi yana kallon junaid dake baje asaman bed dinsa yana ta sharar bacci, ƙarasawa yayi wurin shi tare da zama daga gefen gadon nashi, sannan yaɗan sa hannun shi tare da bubbuga ƙafar junaid kamar mai jira aikuwa a firgice ya tashi zaune yana faman zazzare kyawawan idanun shi da suka canza launi saboda bacci, yana jin muryar abbansu ya kira sunan shi nan take ya fashe da wani sabon kukan yana cewa “Abba yaya fawan ! Yana ina ! meya faru dashi…..’
Murmushi abbansu yayi yana kallon shi yarda yake kuka yana magana red lips din nan nashi na shagwa6a66u sun tatta6e,
Cikin natsuwa abban nasu ya soma cewa “Calm down ur mind junaid,ɗan uwanka yana cikin ƙoshin lpy yanzu haka yana can medical room dinmu mun kwantar dashi, shima sai kiran sunanka yake yi yana cewa Abba ina junaid akawo mun shi in ganshi, inaso in ganshi,”
jin wannan maganar ta abban nasu yasa junaid dakatawa da yin kukan nashi ya zuro da ƙafarsa zai sauko daga saman gadon, abbansu ya ruko hannun shi tare da cewa “pls junaid kada kaje mashi kana wannan kukan saika tayar mashi da hankali yaga kamar mutuwa zaiyi,
Cikin sauri junaid yasanya tafin hannayenshi tare da share hawayen dake zubo masa sannan abban nasu ya saki hannun shi, jikin shi har rawa yake yi wurin saukowa daga gadon, bin shi da kallo abban yayi har cikin ranshi yana mamakin yarda junaid ke tsananin son ƴan uwanshi don ji yake yi da wani abu ya same su kwara shi ya same shi koda mutuwa ce,akwai wani lokaci da abbansu bazai ta6a mantawa ba in ya tuna abunda ya faru har dariya yake yi wani sa’in kuma yaji saukar hawaye, wannan ba kowane lokaci bane face lokacin da junaid yana da kananun shekaru, idan suka je masallaci tare dashi suke zuwa saiya bari an kammala salla an natsu liman na kora addu’a, sai shi kuma ya ɗaga hannayen shi sama ya ɗaga murya yana cewa “Ya Allah ya Allah kasa na riga Abbana mutuwa da ƴan uwana,ya Allah kafara ɗaukar raina kafin nasu,” a lokacin kowa mamaki ya kama shi jin abunda ƙaramin yaron kecewa, har wasu ke tambayarshi dalilin dayasa yake son ya riga abban nasu mutuwa da yan uwan shi sai cewa yayi “Saboda idan na riga su mutuwa bazan ga tasu mutuwar ba in tazo,zuciyata zata samu salama akan na rasa su da raina,” gaba daya mutanen dake a masallacin abun ya basu mamaki sosai, kuma ka’ida ne duk in suka je masallaci tare dashi dole liman ya jira shi ya kammala addu’o’in shi mutane na amsa mashi da ameen, kafin shi liman yayi tashi addu’ar saboda rigimarshi,
Murmushi abbansu ya saki lokacin daya kammala tunanin nashi aranshi yace “Allah yabar mana kai junaid,ni kuma banaso naga mutuwarka nafiso nariga kowannan ku mutuwa don bazan juri ganin gawar ɗaya daga cikinku ba a kan idona,” jikin shi a kasalance yake wannan zancen zucin,
Wayarsa ce ta soma ringing daga cikin aljihun rigarsa ta yadi, cikin sauri ya zura hannu ya ɗauko ta tare da duba sunan mai kiran nasa sunan AMMI ne ya bayyana akan screen din wayar hakan na nufin mahaifiyarshi ce Ammi ke kiransa
Nan da nan ya shiga natsuwarshi tare da ɗaga kiran ya kara a kunnan shi ya zabga sallama,
daga can bangaren Ammi ta amsa mashi sallamar sannan tace”yaro na ya kake ya kuma jikokin nawa? Naji abunda ya faru da fawan shiyasa ma na kira don na tambayi ya jikin nashi,
Tamkar yana agabanta cikin biyayya ya soma magana “lpy lou ammi suna cikin ƙoshin lpy,amma ba zaki zo gida ki duba jikin nashi ba?
“Hmmmm ni me zanzo inyi agidanka? Ae yafi ƙarfi na, daga nan ma zan iya yi masa ya jiki ba sai na kwaso jiki nazo ba balle inga abun tashin hankali abun kunya,’
nan da nan fuskar Abban nasu ta canza jin abunda tace,
“Ammi dan Allah kidaina faɗin hakan bana jin daɗi saboda me zaki ce gidana yafi ƙarfinki bayan nikaina a ƙarƙashin ikonki nake ke fa kika haife ni, kuma wane irin abun tashin hankali da abun kunya kike magana akai”? yayi maganar fuskarshi a yamutse,
tsoki taja tamkar zata fasa screen din wayar sannan tace “babu wani iko da nake dashi akanka hussein! Tunda har ban isa nasaka abuba kayi, wato son ƴa’ƴa ya rufe maka ido ko? ka daina ganin kowa da gashi? ba yarda banyi dakai ba akan ka tattara ƴa’ƴan nan duka ka haɗasu ka aurar kaƙi jin maganata, ka tara ƙattan maza,garada acikin gida sai sinturi suke yi acikin gidan ka,kaine jagoransu kai Gwauro su kuma tazurai gasu nan jibga jigba dasu kaƙi aurar dasu, daga anyi magana sai kace baka son ka takura masu ko kace ba su isa suyi aure ba don ka rainawa mutane hankali, dukansu kaf babu wanda in aka aura masa mace bazai iya yi mata ciki ba hatta wancan shagwa6a66en daka sangarta…….’
runtse ido abbansu yayi tare da saurin cewa “Ammi dan Allah kidaina fadin hakan, aure fa lokaci ne kuma in yayi duk zan aurar dasu ne…..’
wani tsokin ta sake buga mashi kafin ta kuma cewa “haka kullum kake faɗamin, narasa meyasa ƴa’ƴana duk basu jin maganata,daga kai har azeeman da wancan fitsararren da yayi hijra yabar ƙasar batare da sani na ba, ban ta6a tunain hussein zaka yi mun haka ba saboda duk kafi yi mun biyayya acikinsu amma yanxunn. …..’ kukan da ta fashe dashi ne ya yasa ta kasa ƙarasa maganar nan take hankalin abbansu ya tashi, muryarsa har rawa take yi wurin cewa”Ammi dan Allah kidainamun kuka, ke fa mahaifiyata ce saboda me zakiyi mun kuka, hakan zai iya jefa rayuwata cikin matsala,dan Allah kidaina na roƙe ki mommyna indai akan wannan maganar ne yasa kike mun kuka wlh ashirye nake da nayi maki biyayya koba da son ransu ba, zan aurar dasu ne kawai saboda farin cikin ki !!!!!
jin abunda yace ne yasa ta sassauta kukan nata tace “yaushe kenan zaka aiwatar da hakan? kasan natsufa sosai kada na mutu ba’ayi auran nan ba, dan Allah hussein ka tattarasu duka ka aurar a lokaci ɗaya in har kayi mun hakan zan shaida cewa kai hussein ɗinane dana haifa,’
Ajiyar zuciya abban nasu ya sauke yana kara gyara wayar a kunnan shi yace “Insha Allah ammi nan bada jimawa ba,amma ki ban time saboda yanzu muna cikin fargaba game da waɗanda suka kaima su fawan hari,kin san sunce fansa suke ɗauka,kuma babban tashin hankalin ma maca ce AVENGER ɗin,’
shiru ammi ta ɗanyi kafin tace “Shikenan hussein,nima na shiga damuwa dana ji hakan,dama nasan dole hakan ya faru saboda mahaifinku kafin yabar duniya ya tara maƙiya sosai kasancewarshi kwararren jami’en Soja sun halaka dubban masu tada ƙayar baya a ƙasar nan, shiyasa nake tunanin ko daga 6angarensa ne maƙiyan suke son ɗaukar fansa,duk da nasan cewa wannan mai shuɗin idon baya rasa maƙiya don mutun ne mai haɗarin gaske shima baya gajiya da kame ƴa’ƴan mutane yana kaisu lahira, kaga kuwa dole su ɗauki fansa suma,yakamata kasanya tsaro sosai agidanka, kuma akwai shawarwarin da nakeso na baka,”
Abba yace “Ammi dan Allah kixo gida mana,ina ga zaifi in kika zo sai mu zauna mu tattauna akan matsalar tunda wannan abun ya shafi zuri’armu, kuma nama fi jin cewa akaina abin zai ƙare tunda ni ne na tara ƴa’ƴa,”
Ammi tace “shikenan zan fidda lokaci nazo insha Allah, amma inaso ka sani in zanzo saina tattara ƴan matan family ɗinmu gaba ɗaya na kwaso su don suzo ayiwa ƴa’ƴanka baiko dasu,”
dariya kawai abba yayi yana sauraronta sun jima suna fira kafin daga bisani su kayi Sallama 😊
ya ajiye wayar gefen shi yana ɗan murmushi,
A can kuwa junaid na isa ɗakin da fawan yake kwance yana bacci, cike da tausayi yake kallon shi yadda yake jan numfashi da ƙarfi da ƙarfi,
ƙarasawa yayi tare da hayewa saman gadon yayi zaman cin tuwo tare da zabga uban tagumi yana kallon shi hawaye na zuba a fuskarshi,
Jin shessheƙar kukan junaid a kunnan shi yasa shi farkawa daga baccin da yake yi, ya buɗe idon shi a hankali yana kallon shi, yarda ya tallabe fuskarshi hannu bibbiyu ya tasa shi gaba yana sharar kwalla,a hankali fawan ya furta “junaid ”
Kallon shi kawai junaid yake yana cigaba da matsar kwallo,hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yarda jikin fawan yayi ruɗu ruɗu da bulali wurin yayi jawur ya faffashe duk da anyi masa dressing na wurin an shafa masa magunguna,ga kuma ɗinkin da akayi masa a chest ɗinshi,
dakyar ya daddage ya tashi daga zaune yana fuskantar junaid ɗin daya tasa shi gaba,
“Junaid,” fawan ya sake ambaton sunan shi a karo na biyu ganin yarda ya zabga tagumi yana kallon shi hawaye na zubowa gefe da gefen fuskarshi, zama su kayi suna fuskantar juna, kallon shi kawai junaid keyi batare da yace uffan ba,
daƙyar fawan ya ƙaƙaro murmushi yana kallon shi, hannun shi yakai tare da shafa gefen fuskar junaid yace “bari nabaka wani labari ƙanina,”
junaid ya zuba mashi ido yana sauraron shi,
fawan yace “lokacin da waɗannan miyagun suka ɗauke ni ko, suka shiga dani wani ƙogon dutse mai rikitarwa, suka ban za6i biyu, su kashe ni ko su azabtar dani wanne nakeso, kasan me nace masu? ya fadi yana kallon shi, girgiza kai junaid yayi alamar a’a,
Fawan yaci gaba da cewa “a lokacin kai kawai ka faɗo mun araina, aranar da zamu tafi kai ta zabga kuka kana cewa babu inda zamuje ƙafarka ƙafarmu dakyar abba ya shawo kanka, ka tuna abunda ka faɗamun lokacin?
shiru junaid yayi yana tuna lokacin daya cakumi rigar fawan yana ce “ya fawan kayimun alƙawarin cewa zaka dawo araye inaso na sake ganin ka,’ a lokacin fawan yace mashi “junaid ae tafiya ba mutuwa bace, insha Allah zan dawo araye in Allah ya yarda,” murmushi junaid yayi tuna wannan
shima fawan murmushin yayi sannan yaci gaba da cewa “saina ce masu ni bana tsoran mutuwa, ban isa na hana kaina mutuwa ba in lokacina yayi, kamar yarda kuma baku isa ku hana kan ku mutuwa ba idan tazo maku, sai ɗaya daga cikin su yace mun “Ka za6i ka mutu kenan? mu kashe ka kawai? Saina girgiza kai nace “a’a ku azabtar dani kuyi mun duk irin hukuncin da zakuyi mun amma kubar ni da raina saboda akwai ƙaramin ƙanina da nayi ma alƙawarin cewa zandawo da raina, inaso na cika mashi wannan alƙawarin nasa na gani na araye, bana so na karya mashi zuciya nafiso ko mutuwarce ma to na mutu agabanshi yadai ganni da raina……………’ dakatawa fawan yayi da maganar saboda hawayen da suka zuzzubo mashi, junaid kuwa tuni ya fashe da wani irin matsanancin kuka mai cin rai,
haɗe kansu su kayi wuri ɗaya suna faman shessheƙar kuka atare,
dakyar fawan yaci gaba da cewa “Shine suka bankamun kayan maye sannan suka ɗaure ni tamkar dabba, su ka dunga zuba mun bulali da kaca a jikina har saida suka ga jini na zuzzuba ajikina amma hakan bai ishe su ba, ba don su babban yayan mu sun zo ba to da tabbas kashe ni sukayi niyyar yi a lokacin, Amma alhamdlh naji daɗi sosai da Allah yacika mun burina na ganin na rayu don na cika maka alƙawarinka……
.. murmushi junaid ya saki tuni ya ji sanyi ya ratsa mashi zuciyarsa,
janye kansa yayi daga na fawan sannan yace “kana jin yunwa in kawo maka abinci”?
girgiza kai fawan yayi tare da cewa “junaid a ƙoshe nake,ɗazu azmee ta haɗamun kakkauran tea tare da fruits na sha,naji daɗin su sosai,”
“Bari nabarka ka huta sosai, na katse maka baccinka, amma ka sani zan dawo don atare zamu kwana,” yayi maganar yana ƙara jaddada masa ayayin da yake sauka daga saman gadon,
Murmushi kawai fawan ke bin shi dashi harya fice daga ɗakin,komawa yayi a hankali ya kwantar da bayansa saman filonsa tare da lumshe idon shi,
Cikin sauri junaid ya fito tare da tunkarar hanyar fita saboda tunawa da sehrish wadda ke a school, lokacin tashin su yayi gashi time na salla na kokarin wuce shi, yana dab da fita daga ƙopar Amani ta kwada masa kira, dakatawa yayi tare da juyawa yana kallon ta da murmushi a fuskarsa, cikin sauri ta ƙaraso gab dashi tana cewa “ina zaka je ne? Junaid yace “inaso zance masallaci ne nayi sallah, daganan zan wuce na dauko sehrish daga school,”
ɗan jinjina kai tayi kafin tace “wannan yarinyar da muka gani ɗazu itace sehrish”? Ta tambaya tana kallon shi duk da tasan akanta yake magana
“Yeah itace,” ya bata amsa atakaice tare da fucewa yana cewa “Sauri nake aunty amani time ɗin sallah zai wuce ni,”
Juyawa amani tayi tana jinjina kai, a ƙagare take da junaid ya dauko yarinyar daga school saboda tana son ta sake ganinta har ma ta yi magana da ita,
*wannan kenan*😍👍
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Leave a Comment