Hausa Novels

Boyayyar Kauna Hausa Novel Complete

Boyayyar Kauna Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: BOYAYYAR ƘAUNA

{  _Eternity Love_  }

 

NA

*AUTAR MANYA*

 

HOME OF QUALITIES WRT ASS….

 

_Bisimillahir Rahmanir Rahim_

 

001

 

Idanunshi yayi jajir gaba ɗaya jijiyoyin dake kansa sun tashi farar fatar fuskarshi tai jajir abinka da farin mutum,Miskilin murmushi ya saki wanda iyakacinsa saman leɓɓansa kana ya kuma tsiramata Manyan dara daran idanunshi waɗanda sukai jajir yana kallonta dasu.

Ita ko bata ma kula da yanayin dayake ciki ba face ƙara tsuke fuskarta datai haɗi da kuma kiran sunansa a karo na farko acikin rayuwarta.

“AHMAD”

Da sauri ya kuma ɗagowa yana kallonta domin yayi mamakin yadda yaji sunanshi raɗau abakinta abinda bata taɓa faɗiba kenan kasancewar tana karanta mai suna a matsayinsa na takwaran mahaifinta.

Seda ya aro jarumta sannan yace.

“Na’am hajiyata”

Murya can ƙasa yayi maganar.

“Ina gargaɗina gareka shin bance kada ka kuma taimakwon kowa acikin gidan nan ba, wai tukunna ma nifa sam ban gane maka ba anya matan gidannan ba asiri sukai maka ba ace komai kai komai kai su basu da ƴaƴane?”

Tafaɗi maganar da tsananin kishin abokan zaman nata tare da baƙin cikin abinda ɗan nata ke masu acikin gidan.

Ta inda ta shiga bata nan take fita ba bakinta har kumfa yake sabida jarabar faɗa, hartai ta ƙare bai iya ce mata komi ba koda yake daman can magana ba sana’arshi bace ba.

Daga ƙarshe tashi tai daga wajan tai cikin ɗakinta tana faman sababi daman kowa yasan hajiya badai faɗan tsiya ba abu kaɗan ne ze tunzura zuciyarta tahau bala’i.

Ya jima yana saƙawa da kwancewa acikin zuciyarshi kafin yaja ajiyar zuciya mai ƙarfi kana ya tashi yabar falon.

Koda ya fito sashen mazan gidan ya nufa makulli yasa ya buɗe ɗakinsa tare da shiga ciki ya zauna a gefen gadonshi hannu ya saka ya tallafi kansa yana kuma jin zuciyarshi babu daɗi sam.

A tarin lokuta yana mamakin halin mahaifiyarshi wani bin intai abu yakan yi tunanin anya ma kuwa ita ta haifeshi, Abinda yasa yake tunanin hakan sabida shi sam bai gado halinta ba.

Lumshe idanunshi yayi tare da mayar da kansa saman pillow yana mayar da ajiyar zuciya mai ƙarfi.

Wayarshi dake gefenshi ya kallah ƙarfe huɗun yamma harda rabi,Yasan bacci baze yuwu mai cikin wannan yammaci ba sabida haka seya ware tare da nufar bathroom yaɗanyi uzirin dazeyi aciki sannan ya fita daga ɗakin,Kai tsaye gate ya nufa ya buɗe ƙaramar ƙofa ya fita bakin titi yaje can wajan wani gaban shagon provision wanda yawanci matasan anguwar ke zama a wajen, Samun saman banci yayi ya zauna nan da nan abokansa dake zaune a wajan suka hau miƙo mai hannu suna gaisawa cikin raha.

Hirace ta ɓarke atsakanin su amman shiko Ahmad ba um bare um’um illah tsirama hanyar titi idanu dayay bako ƙiftawa, Har wajan biyar da rabi yana wajan, Ganin yamma tai sosai yasa ya miƙe ya ƙarasa cikin ƴar tiredar dake kusa da shagon provision ɗin, Taba ya amso kara ɗaya ya amshi lighter ya kunna yana busawa tamkar bashi ba.

Wani irin murmushin mugunta ya saki lokacin dayaga ƙarasowarta, Hannunta ɗauke da jakar datake fita aiki da ita saukarta kenan a napep idanunta yay ja alamun yunwa ce ta kamata ba kaɗanba.

Da tsageranci ya cigaba da zuƙar sigarin tasa harya ƙaraso wajan abokansa ya zauna tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana cigaba da shan tabar tasa.

Cikin haka tazo zata gifta ta wajan sosai ya ɗaga murya yadda zataji yacewa mujaheed abokinsa.

“Mj yaya farashin daushen goro ya koma ne hala har yanzu akwai tsada koya karye?”

Dariya Mj yayi tare da cewa.

“Ai goro daushe yay kwantai kasan duk abinda yayi kwantai ba kasafai ya fiye daraja ba,Koda kuwa ga riƙaƙƙun ƴammata ne waɗanda suka jima a ƙasa……

Dariya mai sauti sauran ƴan wajan suka saki banda Ahmad daya cigaba da shan tabarsa yana jin ransa wasai batare dayaji tashin zugin maganar hajiya ta ɗazu ba.

 

 

Ƙafafuna ne suka soma rawa bayan nayi namijin ƙoƙarin Saurin wucewa daga dandazon majalissar tsagerun anguwarmu, Hawayene mai zafi ya soma sintiri akan kumatuna Mai naiwa Ahmad! yaro ƙanin bayana ya sakoni agaba.

Mai naiwa kowa ne nazama tamkar mujiya acikin alummah, nikenan bani da majinginar dazan sha iska wannan shi ake kira da rana zafi inuwa ƙuna,Duk uban yunwar dana kwaso tare da gajiya jinai sun zube sakamakon ɓacin ran dana riska a yanzu.

Shikenan ƙaddarar jinkirin aure tazama abar gorantawa? nice nai kaina shin ba Allah ne yayini ba,Kullum cikin gida gori awaje matasan layi basu barni ba.

Littafan Hausa Novels

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan
Harna iso gaban gate ɗin gidan ban dawo dai dai ba, Haka na tura ƙaramar ƙofar na shiga jikina sanyi ƙalau tamkar wadda akama dukan tsiya, Gaisawa nai damai gadin dake zaune a saman banci yana jin rediyo sannan naja ƙafafuna nai cikin gidan a barandar data raba kowani sashe muka haɗu da,Hajiya da sauri na raɓe nai baya sabida gudun mugun furucinta agareni wanda nai imanin kaf gidan nafi kowa fuskantar matsalar hajiya tare da ɗanta.

 

Seda tai nisa sannan na fito daga maɓoyata kama hanyar sashen mu nai da sauri har Na karasa bakin ƙofarmu banga kowa nadaga cikin mutan gidan namu ba, Hamdala nai ga sarki Allah sannan na gyara nutsuwa kana na tura ƙofar na shiga bakina ɗauke da sallama.

 

Cikin falonmu na nufa bayan na tube takalmana a bakin ƙofa jin muryata yasa Umma dake zaune a saman kujera saurin tashi tana laluban sandarta.

Da sauri naje gareta inajin ƙaruwar soyayyarta acikin zuciyata, Duk da tarin halin damuwar data jefamu aciki amman hakan bazesa na juya mata baya ba domin uwa! uwace bakuma a taɓa sauya mata suna.

 

Riƙo hannayenta nai ina mata magana cikin nutsuwata wadda wasu ke tunanin izzace da girman kai wanda ko kusa ba hakan bane ba.

“Ummata karki damu gani gareki mai kike buƙata na taimaka maki dashi?”

Murmushine a saman kyakykyawar fuskarta cikinsa kuma tace.

“Sannu ƴar albarka wallahi duk hankalina ba a kwance yake ba inata zuba idanun ganin ɓullowarki dafatan dai lafiya duk da banda idanu amman dai nasan yau lokacinki ya ƙure na dawowa”

Zaunar da ita nai a gefen kujera sannan na saka hannu na tube hijabin jikina ina yamutsa fuskata sabida gajiyar dake cina.

“Ummah yau Mun karɓi mai haihuwa ne shiyasa Naɗan jima kinsan muke taimakon dr da ɗan kawo wancan haɗo wancan”

Nafaɗa cikin gajiyawa sabida yadda dukkan gaɓɓaina ke faman ciwon gajiya.

“Alhamdulillahi Allah ya taimaka maza tashi kije kici abinci ki wuce cikin gida domin bana son matan gidan su soma ƙorafin baki fita aikin abincin dare ba”

Batare dana nuna ɓacin raina ba, Na ɗauki jakata tare da hijabin dana cire na nufi ɗakin gadonmu.

 

Aje jakar nai sannan na soma tube kayana wani irin mugun zafi nakeji don haka zani kaɗai na ɗaura a kirjina tare da shigewa cikin bayin dake cikin ɗakin babu ruwa ko ɗaya aciki hakan yasa naja ɗan ƙaramin tsuka tare da ɗaukar boket na fito falo mayafin umma na ɗauka na yafa a kaina na fita can Fanfunan bakin farfajiyar gidan domin na ɗibo ruwan.

Kaina sun kuye a ina wasa da ruwan dake zuba cikin bokitin naji shewa akaina.

Kafin na ɗago naga masu maganar seji nai ance.

“Kinganta nan se girman kan tsiya da baƙin hali tai kwantai taƙi auruwa duk ƴaƴanmu sunata ɗagawa itako babu ko kare wai ita nursing……………

 

 

*Ayi haƙuri abi labarin a yadda yazo wannan karon salon na musamman ne*

Leave a Comment

error: Content is protected !!