Gyaran Jiki

Ingantattun Magunnan Gyaran Nono da yanda ake amfani da su

GYARAN NONO BREAST ENLARGEMENT

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag:  Gyaran Nono

Idan muka ce gyaran nono akasari ba kowace mace zata gane me muke nufi ba saboda basu dama da gyarawaba, alhali kuma rashin gyaran ba karamar illa yake yi masuba amma su basu sanhakanba, to gaskiya yana da matukar muhimmanci da tasiri ga mace AMARYA ko UWARGIDA, BUDURWA KO ZAWARA, da ku gyara nononku.

 

 

 

 

 

karki bar nononki hakanan sharaf ba kyan gani, sai kaga mace ta bar nono a zube, in tana shara mai gida yaga sona ta reto kamar anratayo agwagi a bayan keke, idan kuka lura sai kuga matan wadansu yarurrukan wadanda ba hausawa ba (kamar LARABAWA KO TURAWA) matansu sun tsufa ko sun manyanta amma martabar nonuwansu nanan daram ta yadda ko nonuwan wata budurwar a nan baza ka samesu a hakaba.

 

 

 

 

to hakan zai iya rage maki tasiri wajen maigida, hanyoyin da zaki bi don kada nononki ya fadi ko kuma idan ya fadi kuma

kina son ya tashi sune zaki samu:

alkama ki rinka yin kunu da ita kina sha safe da rana.

  • ko kisamu garin hulba
  • da garin tsamiya
  • da zuma farar saka
  • da lemun tsami

sai ki hadasu guri 1 ki rinka shafawa a nonon, bayan awa
daya ko ( 30 minutes) sai ki wanke ki shafa man zaitun,
malama zaki sha mamaki.

 

 

 

 

 

 

 

GYARAN NONO GA BUDURWA

wannan wani hadi ne da akeyi don gyaran nono musamman ga budurwa, shi wannan hadi kuma kowace macema intana bukata zata iya amfani dashi saboda tasirinshi, yanda akeyi shine za a samu.

  • garin waken soya
  • garin alkama
  • garin zogale
  • garin bawon lemun zaki
  • kunfan maliya
  • da zuma

sai kica kudasu guri daya sai ki rinka shafawa a nonon bayan 30mtn ko sama da haka sai ki wanke,sannan kuma ki rinka shan kunun alkama zaki sha mamaki.

 

DON DAWO DA MARTABAR NONO DA GIRMANSA 

 

ga matar da take son ta dawo da martabar nononta ko girmansa yanda zatayi shine zata samuganyen sabara mai kyauda ‘ya’yan alkama suma masu kyausai ki rinka kunu dasu, ko kunun gyada, ko kunun alkama, ko kunun shinkafa, ko kunun gero, ko ko ko duk dai wanda yasamu sai ki dafashi da wannan hadin mai albarka.

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

 

 

 

DON MAGANCE MATSALOLIN MA’AURATA AMARYA KO UWAR GIDA GA TSARABA

 

shi wannan hadin yana da banmamaki musamman wajen karin soyayya tsakaninki da mai gida, da martaba da farin cikin mai gida da nishadin amarya kuma yanasa maigida yaji dadin da bai misaltuwa zaki zama gagara gasar masu gasa, saboda shi wannan hadin manya mata ne.

 

 

 

  • ya’yan kankana
  • danyar gyada mai kyau
  • dabino
  • alkama
  • garin kumasoriyya
  • ya’yan zogale

sai ki dakesu suyi laushi sai ki rinka shan karamin cokali da madara ta ruwa safe da yamma kuma shima mijin zai iya sha

GYARAN NONO

kankana,gwanda,abarba,ayanka kanana a zuba aruwan zafi idan yayi laushi sai a shanye.

idan shayarwa akeyi man hulba cokali2 abi da zuma cokali1.

Idan ya zube ne a dafa hulba da yansun idan ya dafu atace,asha,sannan a kwaba hulbar da kwan salwa arika.Kafin shafawa.

GAYARAN NONO 2

IDAN nononki kanana ne kina so suyi man ya kamar yadda kikeso dai-dai kina iya yin wannan hadi domin samun lafiya nononki

  1. cukwul
  2. garin alkama
  3. aya
  4. nonon saniya
  5. madara
  6. garin hulba.

 

 

Cukwul wanda yawansa zai Kai guda uku sai ki samu garin alkama gwangwanin daya sai aya itama gwangwanin daya sai ki daka su zasu zama gari ki tankade ki samu nonon saniya idan kuma bakyashan nonon saniya ki samu madara ki zuba wannan garin kamar cokali 3 ki dama kina shan kullum Sau 1 sannan ki Lura lokacin da zakiyi wanka ki tafasa ruwa da garin hulba a ciki ki Bari yayi sanyi sai ki wanke nonon da shi sannan Kiyi wankan.

GYARAN NONO KAFIN AYI YAYE 3

garin habba,hulba,danyen shinkafa,garin alkama,gyada,plaintain,ayanka a busar da plaintain din,sai ahada acikin su hulba din da garin shinkafa dana alkama,sannan ajika ahada ga gyada akai nika atace ruwan shi za’a dafa kuma dashi za’a dama garin sai ayi salala,sanna arika sanya kindirmo mara tsami da zuma ana sha(idan ya rage saura kawana7 ayi yayen,yana gyara mace sosai)yana hana ciwon breast da yamushewa.

KWANCIYAR NONO 4

Idan kuma kwanciya sukayi kinaso su tsaya sai ki nemo wadannan kayan zasu tashi_

  1. hulba
  2.  ruwan dumi

ki kwaba hulba da ruwan dumi, wato garin hulba ya sanyi kauri kar yayi ruwa sosai, sai kin tabbatar kin gama abinda zakiyi, kin so kwanciya sai ki shafa, ki kawo ( breziya ) damammiya ki saka, da safe sai ki wanke da ruwan dumi, shima wannan ( matar aure zatayi )

YANDA AKE GYARA NONO KOWANNE IRI

 

GYARAN NONO

mace tana fara fitar da nono daidai lokacin fara jinin al’ada yayinda allah ya banbanta halittar sa jinsi daban daban ta yanda jinsin al’ummar africa bakaken fata ya banbanta dana wasu kasashen don haka abu na farko daya kamata jama’a su fara sani akwai banbanci tsakanin nonon baturiya dana bakar fata dan haka maganin gyaransu da namu ya banbanta

dan haka idan gyara nono kikeso girmansu ko tsayuwarsu tareda kyawunsu ba tareda yayi miki illah ba dole saidai kiyi amfanida na gargajiya.

akwai banbanci tsakanin tsayar da nono da girmansa to amma saidai abu daya baya samuwa dole sai an hada da wani ma’ana bazaiyu nono ya tsaya kadai ba har sai girmansa ya karu haka zalika bazaiyu ace nono ya girma ace bai tsayaba kuma wadanda sukafi matsala a gyara nono sune wadanda ya kwanta shiyasa duk maganinda zai kara girman nono kuma ya tsayar dashi zai zama na musamman sannan za’a dauki lokaci ana shansa sabanin wanda kawai cikowa take bukata.

 

nonon mace yanada suffa kala kala nayi kokarin binciko bayanai akayi dareda bin diddigin magunguna daya dace masu suffar nonon suyi kai harma wanda zaiyi da kowanne

 

1 na farko AKwai nono mai (mango Shape) wato Shine wanda bakinsa (nipples) yaKe Kallon sama irin wannan nonon baya zubewa da wuri irn wannan batashan wahalar gyara dan haka
zaki iya wannan yanda zakiyi ki samu ayaba (plantain) ki yanyankata ta bushe sannan ki daka garin to saiki samu aya ki wanketa kisaka gyada kisaka amarkada miki
saiki tace ruwan kina diban wannan garin plantain din kina zuba madara peak kinasha kamar sau biyu arana kafin sati daya zakiga canji sosai nononki zasu tashi su ciko.

 

? sai kuma me bi masa wato (Pointed breast) shine zakuga yana kallon gaba (straight) gasKiya irin wannan nonon yana saurin faduwa domin riga kafin faduwarsa arinka kunun alkama wato idan aka nika alkamar sai ayi kununta asaka nono da zuma anasha, idan kuma zubewa yayi zaki hada farar shinkafa da alkama da garin habatussauda da aya da gyada ki nikasu suyi laushi ki tankade sai ki ajiye wannan garin kina hadashi da nono kinasha kullum wannan shine hadinda zaisa nono ya ciko ya kara girma kuma ko budurwa zata iyayi.

 

 

 

Gyara Nonon ki don daukar hankalin maza

 

?Akwai nono mai Kallon gefe (left and right) zakuga aKwai nisa sosai a tsaKanin nonuwa biyun zai iya kallon hagu ko dama wadannan sune sukafi matsala domin sa’ar mace wannan nono su zama kanana amma da zaran sun dan fara tashi to tabbas ta rasa nono domin gyaransu su dawo dole sai kinyi amfanida maganin nonon na musamman wato gari da akesha na kwana 30 ko 25 wannan kowanne irin nono mace take dashi zai temaka mata.

 

Domin anyi amfanida ingantattun magunguna kuma na gargajiya, gadalin nono da nonon kurciya da ‘ya’yan baure kumbura fage zakiyi garinsu
idan suka bushe a inuwa saiki samu hulba me kyau ki hada sai kuma kisamu aya da alkama da ridi da gyada da fafar shinkafa da waken suya

 

dukkansu ki gyarasu kamar gyada da ridi da waken suya saiki soya su sai kiyi garinsu adakasu ko nikawa saiki samu ruwan zafi kamar rabin kofi ki zuba garin cokali daya ki gauraya ki zuba zuma ko zugar da nono ko madara ta ruwa peak kinasha kullum kafin wani lokaci zasu tashi koda kanana ne.

16 Comments

Leave a Comment