Hausa Novels

Budaddiyar Soyayya Hausa Novels Complete

Budaddiyar Soyayya Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah._

 

 

 

 

 

 

_Shimfiɗar labarin_

 

_Labarin Jameel da Bintul Hudah da kuma Anisha masoyane wanda suke tare da junansu koda kuwa ɗaya a cikinsu yayi nisa da juna ma’ana baya garin baki ɗaya idan yana cikin masifa dan uwashi zaiji saboda zuciyoyinsu a haɗe suke….hmmmm *THE NAKED LOVE* kenan_

 

 

_Bai yarda da so ba kuma masu yin soyayya ma haushi suke bashi,dan gani yake rashin aikin yi ne yajasu har suka tsunduma a cikin soyayya ,yana masu ganin mararsa wayau infact bai cika magana da maiyin soyayya ba saboda haushinsu da yake ji. Maigirma Jameel kenan_

 

 

_Gata fara gata kyawkyawa gata da komae Allah ya bata,kowa ya ganta sai yazo yace yana sonta ,amman ta rufe ido tace bata son kowa, duk da kyaun da take dashi da kudin da gidansu suke dashi da class dinta ,amman duk ta ajiyesu gefe tace bata son kowa sai Jameel, ita yar’asalin kasar London ce amman saboda soyayya ta taitaro kayanta ta dawo nigeria da zama dan kawae ta samu soyayyar Jameel Hajia Anisha kenan maiji da ajinta_

 

 

_Ga natsuwa ga hankali ga kuma hakuri ba ruwanta da kowa neman na abinci kawae take ,duk da tana black amman kyaunta bai boye ba ,dan kyawunta har ya wuce yanda za’a faɗashi ,duk da kasancewarta yar’aikin gida amman bata yarda aka keta mata mutuncinta tana fama da ƙera da tsungama a gidan da take aikin nata,amman hakuri tasa tana mai cigaba da rayuwarta a haka ,saboda tasan bata da inda zataje inda tace zata bar masu gidan nan dai ne rufen asirinta ,rayuwa dai ba dadi Bintul Hudah kenan wanda suke kira da Hudah_

 

 

 

_wowoho garin dadi na nesa inji angulu da ta faɗa masai,*BUƊARDIYAR SOYAYYA* dai ne keda wannan gwaramar na mutane guda ukku da suke shiga hali da rayuwa mai ban tausayi duk akan soyayya_

 

 

_Shin wannan wata irin soyayya ce_

_wata irin wahalar rayuwa suke fuskanta kudai biyoni tsundun a cikin labarin dan jin ya zata kaya_

 

 

 

 

 

 

*

*Ba sai ma tsaya yi maku bayani ba, banyishi domin wata ko wani ba, sannan ban yarda a satarman fasaha ba*

 

 

 

بسم الله الرحمن الر حيم

 

Page 1-2

“Hudah wai ubamai kikeyi a cikin kitchen din nan, da har yanzun baki fito ba kika fara shirya dining table din nan ba? Ko sai Jamel ya shigo ya tadda ba’a gama shirya tarbar shi ba.”

 

 

Ƙarma wanda aka kira da Hudah ta farayi, dan ita batasan ya zatayi ba, tun asuba bata samu ta rintsa ba cikin gidan nan,duk abincin da aka dafama Jamel itace ta girka su, yanzun ma shirya abincin bisa dining ita zatayi shi dan kawai ta fito a yar’aikin gida yar’wahala, kuma kitchen din take gyarawa, hawaye ta share sannan tace. “Yi hakuri Hajiya ina gyara kitchen ne, amman yanzun zan fito.”

 

 

Cikin fushi da kulewa Hajiya Jalila ta fara magana. “dan ubanki har yanzun baki gama gyara kitchen din ba? Wai ke wata iri malalaciyar yarinya ce? Amman wallahi mudun na shigo kitchen din nan, kasheki ne kawai ba zanyi ba, yar’iskar yarinya, zaki fito ko sai zo na takaki.”

 

 

Allah sarki rayuwa, haka Hudah, ta fito ta jera abincin bisa dining, sannan ta kara gyara makeken parlon ta kunna bona, haka kuma taji ana kara kwala mata Kira ana cewa. “Maza kizo ki gogeman wannan takalmin, shin zaki taho ko sai na kwalkwale maki wannan tsananun idanun naki da kika tsareni dasu sai kace idon maiya.”?

 

 

 

Batayi mamakin zagin da Anisah tayi mata ba, dan tasan zatayi mata fiye da haka ma, saboda ta tsaneta sosai tunda aka kawo ta aiki gidan , bata taba jindadin zama da kowa ba sai Amal, itace kadai takejin dama dama a wajenta itama ba sosai ba, dan ko ita tunda take bata taɓa ganin Jameel ba, sai dai tanajin maganarshi a bakinsu lokacin da tazo ya tafi Paris karatu, ji tayi an wanketa da marika, dafe kuncinta tayi tana kallon Anisah, wurga mata harara Anisah tayi sannan tace. “Matsiyaciya, wato Ina maki magana kinyi banza kin kyaleni kin tsaye kina kallona kamar tsohuwar maiya, to wallahi kurwata kur, sai dai kici kanki dangin mayu dangin tsiya kawae.”

 

 

Itadai Hudah kasa tayi da kanta, tana matse kwalla, Amal ce ta fito cikin wata dakakiyar shadda wanda tasha aikin stone work, da yake anko sukayi da Anisah, kallon Hudah tayi ta kauda kai, sannan tace. “Anisah kizo muje ki ida shiryawa kafin a daukoshi, karda ki biyema Hudah wannan fadan naku bamai ƙarewa bane, kuma kinsan yau dai masoyinki yake dawowa yau ranar farinciki ce a gareki,karki tsaya ki biyema wannan yarinyar.”

 

 

Harara Anisah ta warga ma Hudah, dan ta tsaneta sosai, tsaki tayi sannan ta kalli Amal tana murmushi tace. “Hakane fa kanwar mijin babu kamarki, oya mu wuce.”

 

 

Haka suka fita abun gwanin ban shi’awa, itama Hudah wucewa tayi room dinta ta shiga wanka tana mamakin tsanar da Anisah tayi mata ita da Hajiya Jalila.

 

Sosai Amal ta zauna ta tsarama Anisah kwaliya ta gani ta fade, kallonta tayi tana murmushi sannan tace.

 

 

“Kin san Allah duk izzar Yaya Jamel da jiji da kanshi yau dole ya bude baki yace maki kinyi kyau, ke bama cewa kiyin kyau ba wallahi sai yace Anisah ina sonki.”

 

 

Rumgume Amal Anisah tayi, dan ji take kamar taba Amal kyautar Mota, kallon Amal tayi sannan tace. “Inason Yaya Jamel, kodan halayenshi bai damu da mace ba, sannan bai damu da yace yana son mace ba, shi mata basu gabanshi nima kaina taya ya yarda zai aureni? Dan kawai Mom tace dole, kinga kenan Amal ba Anisah ba kishiya, zan zauna dagani sai mijina.”

 

 

Ita dai Amal murmushi kawai tayi ta cigaba da gyara ƙawar tata, kuma budurwar Yayanta wanda suke shirin yi masu baiko.

 

 

★★★ ★★★

 

 

Wadansu mercedes S classes sukaxo filin jirgi na Nnamdi Azikiwe international na Abuja,suna jiran jirgi kafin mutin talatin ya sauka, wa’annan mutanan suna tsayuwar jiran ogan su, lokacin jirgin ya sauka bayan Awa daya kowane passenger suka sauka daga jirgin, sannan passenger suka fara fitowa a jirgin, Bodyguard din nan, har yanzu suna jiran Ogan su, da zasu dauka.

 

 

Kowa da kowa a airpot din suna jiran suga wanene wa’annan Bodyguard din suke jira, wajen minti Goma da fara fitowar pessenger’s , sai ga wannan Ogan nasu ya fito daga cikin jirgi, tafiya yake kamar baya son taka step din jirgin,kallo ɗaya zakayi mai kaga zallar kasaita da izza da take dawainiya dashi,handsome guy na hango dogone amman ba sosai ba, gashi yana da faɗaɗan kirji infact komai nashi yayi.

 

 

Yana tafiya cikin takama,class kam akwashi a wajen yanda kasan shugaban kasa, suna ganinshi da sauri bodyguard din suka nufo shi, suka Ruga cikin tsoro da suka ƙame suna cemashi.” Boss you are highly welcome Sir.” Wani kallo ya tsaya yi masu, sai da yayi second talatin, kana yace.” thank uh let’s go.”

 

 

Wadanan Mercedes S classes dama tuni anyi park dinsu, Bodyguard din suka Ruga d gudu suka bude mashi kofa ya shiga don sukai shi gida, suka kama hanyarsu daga Nnamdi Azikiwe international airport, zuwa Maitama Sule Estate central area Abuja.

 

 

motocin guda Goma ne Mercedes S classes suka daukoshi, daga filin jirgi zuwa gida, lokacin da suka kusa Isa gida Bodyguard guda Hudu sukayi sauri suka biyo motar boss dinsu kamar yarda akeyima shugaban kasa guda yana Kofar Drive kana guda ukku suna sauran kofufin, suna gudugudu, harzuwa gida kana mai Gadi ya bude masu kofa.

 

 

Shiga sukayi ciki, wata yar’sabuwar tafiya suka ƙara yi sannan aka wangwale masu wani makeken gate, nan suka ƙara danna hancin motocinsu wani irin katafaran parking space ne sukayi parking din mota’s dinsu, sai da sukayi kusan 20 minute sanann suka bude mashi kofar motar, sai da akayi 8 minute da bude mashi kofar sannna ya ziro kafarshi daya kasa, sannan ya sake fiddo gudar, fitowa yayi sannan ya fara tafiya cikin izzar da gadara, da gudu Amal ta fito ta rungumeshi tana cewa.” oyoyo ga Yaya J.” murmushi kawai yayi mata sannan ya shafa gefe fuskarta, bataji komai ba dan tasan halin yayan nata, ba komai yake magana akan shi ba, sai abu mai mahimmanci, a tare suka jero shi da Amal har suka shigo cikin gida, Hajiya Jalila ce ta rungume ɗan nata, shima rungume ta yayi yana jin wani irin farinciki ganin Momyn tashi, kissing dinshi tayi a goshi sannan tace.” Son you highly welcome, nayi kewarka sosai.” Rungumeta shima yayi yana jin Kamar anyi mashi bushara da gidan aljana yace.” Nima nayi missing dinki sosai Mom.”

 

 

Tunda ya shigo Anisah take kallonshi tana jin wani irin sonshi yana fisgarta tanajin kaunarshi tana ratsa ko wane lungu da sako na jikinta, ida isa tayi wajenshi tana wani rangwaɗa da kisisina, cikin salo mai daukar hankali tace tana juya ido.” welcme back Yaya J.”

 

 

Kallo ɗaya yayi mata ya kauda kai, dan shi ya manta da rayuwar Anisah sai da ya dawo gida sannan, yasan yanzun zata cigaba da adabar rayuwarshi tana matsa mashi da shirmanta na banza wai so, dan shi bai yarda da soyayya ba, dan duk maiyin soyayya haushi yake bashi, kallon da yayi mata yasa Jikinta yayi sanyi, tana mamakin yanda Yaya J bai damu da ita ba, baya sonta bayan duk tarin masoyan ta amman taki kowa tace shi take so, saboda da son da take mashi ta baro london gidansu ta dawo nigeria da zama amman duk a banza komai tayi bata burgeshi.

 

 

Haɗa ido yayi da Hajiya Jalila ta wurga mashi harara, kauda kai yayi sanann yace. “Thank you Anisah.” murmushi tayi mashi dan taji dadin yanda yau ya kula har ya bata ansa kama hannunshi Amal tayi sannan tace. ” Yaya J kaje kayi wanka ka huta sai kazo kaci abinci nasan ka kwaso gajiya gashi mu kuma muna son muyi disturbing dinka.”

 

 

Kallonta yayi yana jin son ƙanwar tashi a zuciyarshi, dan ita ɗaya kadan tasan halinshi, kallo ɗaya zatayi mashi ta gane abunda yake nufi koda bai yi magana ba, duk sun cikashi da noise sun samai ciwon kai, kamashi Amal tayi hanyar part dinshi da shi, wani Kallo Mom tayi ma Anisah itama ta bi bayanshi da sauri dan su kaishi apartment dinshi.

2 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!