Budurcina Yancina Hausa Novel Complete
Tag: Budurcina Yancina Hausa Novel Complete
Sunana Ambar,Rayuwata tana cike da
darasi,tausayi,alajabi, haushi dakuma dana
sani, bana kaunar kowacce ya mace ta
kasance acikin halin dana shiga koda kuwa
makiyata ne, zanbaku labarina nasan bani
kadai bace nake abunda na aikata, tabbas
akwai wasu mata, donhaka inafatan duk
wacce taji labarina inta kasance tanayi
tadaina!, duniya makarantace! Inhar baki
daina lokacin da idonki da kafafunki ke
taimakonki ba, zakiyi danasani wanda nima
nayi!
Sunana Ambar sadiq, mu biyune agun
iyayena, dani da kanwata amina,tsakanina
da amina shekara bakwai ne, kasancewata
yar fari na kasance tauraruwa a idon
iyayena, duk abinda nakeso anamin, ko baa
minba ni saina nema hanyan dana samu ta
dadi ko ta tsiya, tun ina shekara shida
mahaifina suke tafiya dani umra, har aka
haifi amina, muka fara zuwa da ita,
mahaifina banzan wani irin mutum bane a
addinin ma, izala ne? Shia ne? Dariqa ne?
Oho nidai nasan muna ibada, duk hakkin
musulunci yana karewa , dad dina dan siyasa
ne gaba da baya kuma mai sarauta ,jin
hakan basai na kara bayani ba mai karatu
kunsan irin dadin danake ciki, inada fannina
wanda da akace muzauna da ameena,anma
tsabar jinin mu bai haduba yasa dole daddy
yasa aka gyra mata wani fanni, fannina ciki
da falo da toilet saikuma library na, duk
abinda yakamata ace na mallakeshi a gydan
mijina toh na mallaka agydan ubana, daddy
yasha: gayamun duk abinda yakeyi yanayi
ne don insamu na huta, sannan kar zamani
ta rudeni, kar samari su huremin kunne
donshi bayason samarinnan, inbari nagama
makaranta nafara aiki tukun, nace tohm,
dama waya kam na malleketa don ina
primary 6 dady yasiyamin waya yacemun na
rike, bazan manta ba kaf age mates dina
nikadai keda waya, kowa na amfani dana
gydansu, haka daddy yasiyamin samsung s1
nafara amfani da ita, a lokacin facebook
kawai akeyi donhaka tuni nima nafarayi,
daddy na duk wannan kayan duniyan da
yakemin, hakan baisa ya takuraniba, komi
nakeso zaasiya akawo, bazai bari ko kofar
gyda najeba kullum ina gyda, inbanda
makaranta saikuma gyda, sai islamiya, kuma
shima kaimu akeyi nida amina direba yajira
mugama mudawo, rayuwata tana tafiya cikin
kwanciyan hankali babu takuri babu
damuwa, dama daddy yasiyamin laptop, nida
amina, muyi game, muyi kallo, inyi chatn a
facebook, ko nayi karatu, ko na taya mama
aiki, duk da gatan danake ciki hakan baisa
nazama doluwa ba, ni nake daukan nadaya a
ajinmu rayuwata cikin walwala, anma
saime???????
Nice