Hausa Novels

Budurwar Mijina Hausa Novel

Budurwar Mijina Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: BUDURWAR MIJINA

 

*NA SADNAF*

 

*E.W.F*

 

*Bismillahi Rahamanir Raheem*

 

*Page 1*

 

Wai saurin me kake yi ne haka”?

 

Wayar sa ya Kara duba wa tare da Kara sauri Yana “Jirana ake fa karki damu yanzu zan dawo bazan dade ba yace tare da yin waje da sauri.

 

Da ido na bishi har ya fice daga gidan naji karar tashin lifan dinsa.

 

Tagumi nayi tare da bin kulolin da na ajiye a tsakiyar kafet din palon da ido,abincin daren dana dau tsawon lokaci ina yinsa duk sabida na faranta Masa duk da cikin dake jikina ina jin yunwa haka na hakura da cin abincin sabida idan ya dawo muci tare kamar yanda Muka Saba sai gashi daga dawowar sa ya sake wanka ya fice daga gidan da Sunan kawunsa na neman sa.

 

Kwana biyu kenan Yana min haka.

 

Haka na zauna raina a b’ace Ina tsaki kasa kasa ganin idan na cigaba da zama a haka batare da naci abincin ba zan cutar da kaina da abinda ke cikina yasa na zuba abincin na fara ci.

 

Ban wani ci da yawa ba na rufe sauran na jawo wayata na fara chatting abinda kawai zai rage min kadaici da takaicin fitar da mahfuz yayi ya barni ni kadai a gida kamar Mayya.

 

Mahfuz bai dawo ba sai wajen goma na dare zuwa wanan lokacin Raina ya Kai kololuwa wajen b’aci kafa kawai nake girgiza wa Koda ya shigo da sallama ciki ciki na amsa mishi,ya saki murmushi Yana “Afuwan tawan wlh wani waje na raka kawu bansan zamu dade haka ba kiyi hakuri kinji matata”

 

Bansan Mai yasa bana iya dogon fushi da mahfuz ba Yana min murmushi da yar murya zanji na sauko.

 

Ledar daya shigo da ita ya bud’e Yana “Kinga kayan kwadayin dana taho Miki dashi

 

A binka da mai ciki da sauri na wafci ledar ganin alewar Madara da gulisuwa yasa na washe baki dan duk wani Abu Mai Madara da siga Ina so.

 

Sai da na fara Shan alewar Madarar na kalli mahfuz da ya zauna a kasan kafet Yana Danna wayarsa

 

“Baza ka ci abincin bane?”

 

“Wlh kawu ya tilasta min cin abinci a gidansa sai dai gobe ki dumama min kafin na fita”

 

“Yanzu ko cokali daya bazaka yi ba sabida Kai na girka fa”

 

“Ai nace Miki gobe sai kimin dumame wlh yanzu a koshe nake”

 

Badan raina naso ba na cigaba da Shan alewar Madarata shi kuma ya mike kafarsa da hannu bibiyu Yana latsa wayarsa har da dan murmushinsa.

Budurwar Mijina

Ido na zuba Masa Ina tunanin canjawar da yayi a kwanakin nan,Mahfuz mutum ne da bai wani damu da chatting ba dan sau tari ni nake tilasta Masa yin chatting sabida Ina tura Masa sakwanin ta watsapp,ada idan ya dawo gida ko waiwayar wayarsa baya Kara yi sai dai yayi ta jana da hira Yana bani labarai idan yaga na dauko wayata sai ya kwace yace a hakura da danna wayar nan azo a ji da ni amma a kwanakin nan har da asuba Zan ga Yana latsa wayarsa ban taba zarginsa ba bana Jin Zan Kuma zarge idan na tuna San da muke yiwa juna,ba Kuma mu dade da yin auren ba tunda yanzu shekara biyu da auren mu a yanzu Allah ya azurtani da samun ciki

 

“Wai Mai kake yi a wayar kake ta murmushi haka”?

 

Dagowa yayi da sauri Yana “Da Abdul muke hira fa sai dariya yake bani kinsan halinsa da barkwanci”

 

Murmushi nayi nima Ina “Gwauro ba har yanzu sai ruwan ido yake ya kasa tsayar da budurwar balle mu sha biki”

 

Yana chatting muna hira har zuwa sha daya da rabi na dare kafin mu tafi daki mu kwanta.

 

Fitsarin da nake ji ne ya farkar dani sai da na wartsake na mike zaune ga mamakina mahfuz baya d’akin har Kara shafawa nayi Naga ko dai lumewa yayi a bargon da muka lulluba sai dai bargone kawai baya d’akin.

 

Kasa kunnena nayi naji ko dai Yana bandakin a daidai lokacin da na daga kaina Ina kallon agogo d’akin karfe biyu da minti goma Sha biyar na dare.

 

Mik’ewa nayi a hankali Ina mamakin Inda Mahmud yayi dan nasan baya bandaki tunda banji motsi ba.

 

Sai dana kunna fitilar d’akin na nufi wajen k’ofar dakin da aka dan bud’e idan har zan tab’a k’ofar ba abinda zai hana yayi Kara daga d’akin Ina Jin maganarsa hakane yasa nake so naji mai yake cewa zuciyata fal da mamaki da wa Mahfuz yake magana a tsakar daren nan ya baroni a daki ni kadai.

 

A hankali na samu na fito daga d’akin batare da na bari kofar tayi Kara ba, cikin sand’a na fito na nufi palon da yake akwai siririn corridor kafin a iso palon.

 

Hasken wayarsa kawai nake hango wa yayi rub da ciki fitilar palon a kashe.

Budurwar Mijina

“Nifa bana ganinki sosai wai me hakane”?

 

Abinda ya sauka a kunnena kenan daya bala’in fadar min da gaba har sai dana dafe cikin jikina sabida motsawar da yayi.

 

Ban motsa ba na tsaya Ina cigaba da Jin hirarsa da macen da nake Jin saukar muryarta a kunnena.

 

“Bana so na kunna haske na tashi Ameera fa Wai yanzu baka ganina”

 

“Rowa kawai zaki min Kisani mafarki a banza”

 

Dariya macen ta kyalkyale dashi Yana shirin magana bansan rike numfashina nayi ba Ina sakin numfashin yayi jifa da wayar da sauri Yana “Lubna”

Budurwar Mijina

Duk da jikina balain rawa yake Ina hada gumi bansan ya akayi nayi jarumtaka wajen daidaita kaina Ina “Farkawa nayi zanyi fitsari da ban ganka a d’aki ba shine na fito”

 

“Ooo e’e’e motsi naji a waje shine na fito naga waye har waje na fita ma”

 

Yace Yana in’ina ya sunkuya dan ya dauki wayarsa na juya jikina na cigaba da rawa nabi bango na koma d’akin Yana daga bayana Yana fadin Yana tunanin barayi sun adabi unguwar bance Masa komai ba na kwanta tare da Jan bargo dan har wani zazzabi naji Yana neman rufeni.

 

Yana kwanciya a gefena ya fara k’ok’arin jawoni idan har na hana shi rungumeni zai zargi naji maganar da yake yi da mace.

 

Halin da nake ciki yasa ban iya jure rungumar da yamin ba dan gani nake kamar ya manna min garwashin wuta na janye jikina banaso nayi magana sabida Zan iya fallasa halin da nake ciki bana so nayi abinda zanzo Ina nadama inaso na samu nutsuwa nayi tunani Mai kyau.

 

Koda na janye jikina bai Kara jawo ni ba yace tom yau bbyn bayaso a tabaki kenan ya juyamin baya tare da Jan bargo saman kansa.

 

Ido na zubawa bayansa Ina Jin tashin maganarsa a kunnena nifa bana ganinki sosai wai me hakane

Rowa kawai zakimin kisani mafarki a banza.

 

Da wa Mahfuz ke video call da tsakar daren nan har ya barni a daki ya tafi palo wacce ce ita,har yaushe Muka yi Aure da mahfuz zai fara kula Yan Mata,Anya ma mahfuz dina ne wanan ko dai mafarki nake yi na mitsini kaina wai dan na tabbatar da ba mafarki nake ba.

 

Zuciyata wani irin zafi yake min na tsananin kishi mahfuz dama Yana da budurwa duk soyayyar Nan da yake min dama zai iya kula wata, mahfuz makota ma sun shaida irin kaunar da yake min.

 

Soyayya mai tsafta muka yi a shekara uku da muka hadu dashi,naje banki zan bude acct shi kuma anan yake aiki,tun ban dauki soyayyarsa da wani mahimmanci ba har sai da ya samu matsuguni a zuciyata,ba Wanda baisani dashi ba a cikin dangina haka ma danginsa,kawayena Kan roki Allah ya basu irin Mahfuz sabida yanda baya iya b’oye san da yake min a gaban kowa, nida kawayena mun Sha hada Kai mu siyi layi dan mu gwada shi,Yana Jin muryar mace zai kashe dan kafin muyi aure Ina balain saka kaina a matan da suka yi sa’a da dace samun nagartace kamar mahfuz ban fuskanci wani matsala ba har mukayi aure zan Kuma iya shaidarsa dan ba abinda yake boye min,a gurin mahaifiyarsa Hajiya Ammi kawai nake ganin ban wani samu karbuwa ba duk da da yawa ance haka take bata fiye sakarwa sirikanta fuska ba,da na auri Mahfuz sai na fuskanci idan kina so ta sakar Miki fuska ki bata abin duniya a ranar zata sakar Miki fuska na Kuma ji halayenta a wajen matar yayyen mahfuz Inda Suka ce Kar na sake duk wani abu da zai hadani da Mahfuz nace Zan Kai kararsa wajen mahaifiyarsa tsana zan janyowa kaina dan bata san laifin yayanta ko kad’an.

 

Daga aurena da mahfuz zuwa yanzu ban wani fuskanci matsala ba duk da kyautata min da yake Yi a waje da bambanci a yanzu da muka yi aure, dama can ba soyayar kudi muka yi ba shiyasa Koda muka yi aure ba wani kudi yake bani ba nima ban damu ba bansani ba ko dan ban Dade bane Zan bukaci kudi a gaba kayan abinci dan abinda bazaa rasa ba ban Kuma damu ba.

 

Zuciyata suya kawai take bacci ya kauracewa idona zuciyata nata sak’a min na tashe shi na tambaye shi da wa yake waya,wata zuciya.kuma na hanani akan nabi komai a hankali.

 

Kiran sallah asuba a kunnena dama Ina rigashi tashi sallah ni nake tashinsa.

 

Haushinsa da nakeji yasa ban tashe shi ba naje.na daura alwala inaga motsin rufe k’ofar bandakin ne ya tashe shi.

 

Koda ya mike Yana Hamma yace “Da ban tashi ba,bazaki tasheni ba kenan”?

 

Ban ma iya bashi amsa ba bama naso nayi magana dan wani abu ne ya tokareni a mak’oshi.

 

Banida burin daya wuce ya tafi massallaci na dan bincike wayarsa dan na tabbatar da zargina.

Budurwar Mijina

Sai dai yana fitowa daga bandaki ya zura wayarsa a jallabiyarsa yayi ficewarsa.

 

Zuwa yanzu zargin mahfuz nada budurwa ya tabbata dan a kwanakin nan yafara haka,amma baya fita da wayarsa har password dinsa nasani dan sunana ne.

 

Ina zaune ne kawai akan sallaya zuciyata fal da tunanin da mamakin mahfuz dana d’auko so da yarda na dora masa.

 

Mahfuz ba mutum bane da idan yaje massallaci Yake dadewa sai gashi har gari ya fara haske bai dawo gidan ba.

 

Tuni wani irin kishi ya turnike ni jikina har rawa Yake.

 

Har zan fita waje na koma dakina na dauki wayata tare da bin umarnin zuciya ta akan na gwada Kiran wayarsa naji ko dai wayar yake.

 

Ina kuwa kira ya nuna call waiting Wanda hakan ya kara saka kirjina nauyi sabida kishi ban hakura ba na cigaba da kira dan idan har ya daukeni da mahimmaci ya Kamata ace ya dauki wayata tunda nasan dole zai ga kirana sai dai bai dauka ba nima ban fasa Kira ba nasan bazai wuce layin unguwar ba dan gida uku ne tsakanin mu da massallaci da hijabin jikina na fita waje wayata Kare a kunne na a dakalin gidan makociyata na hangoshi a zaune.

 

Yana ganina ya katse wayar tare da mik’ewa tsananin bacin rai yasa tun kafin ya iso nace “Mahfuz da wa kake waya”?

 

Murmushi ya sakar min Yana da Abdul nake waya Mana

 

Katse shi nayi a dan tsawace Ina “Wlh karyane Mahfuz da mace kake waya bada Abdul kake waya ba”

 

“Ni nake miki karyar”?

 

Yace Yana nuna kirjinsa fuskarsa ta sauya daga murmushi zuwa bacin rai

 

“Ai nasan karyar ne mahfuz dan idan da Abdul zaka yi waya bazaka fito waje kayi wayar ba, jiya ai naji duk hirar da kake yi da budurwar ko zaka rantse ba da budurwa kake wayar ba,Mahfuz wacece ita?dudu yaushe muka yi aure da har wata zata fara d’auke maka hankali jiya har ka barni a daki ka fito Palo Kuna video call har kana ce wa zata saka kayi mafarki a banza”?

 

Dogon tsaki yaja ya ratsa ta gefena ya Shige ciki na juya da sauri raina na balain suya daki ya nufa nabi bayansa Ina cigaba da tambayar sa da wa yake waya amma ko kallona baiyi.

 

Takaici yasa na fashe da kuka Ina “Mahfuz wacece ita mai na maka da zaka sakamin da cin Amana”?

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

Banza ya bawa ajiya ta abinda bai tab’a min ba ya d’auko wayarsa ya fara lalatsawa kamar ba dashi nake magana ba,tun auren mu bamu taba hayaniya dashi ba,bamu taba dogon fada dashi ba,Mahfuz da nasani Ina d’an b’ata rai zai hau rarrashina Yana bani hakuri sai gashi yanzu kuka nake a gabansa amma ko kulani baiyi ba

 

Yanda ya watsar dani ya bawa banza ajiyata yasa na fusge wayar daga hannunsa a zuciye ya dago da idonsa da suka dan rine sabida b’acin rai ya mik’omin hannu Yana “Bani wayata Lubna kafin na sassab’a miki”

 

“Bazan bayar ba Mahfuz har sai ka Gaya min da wacce Yar iskar kake waya”

 

Mik’ewa yayi Yana k’ok’arin Magana naji wayar sa na vibrating a hannuna da alama ya cire ringing tone din a vibrating yasa.

 

Da sauri na juyo da wayar naga SR ke kira a waya a cikin Sakani na dauki wayar na Kara a kunnena yayo kaina da balain sauri a daidai lokacin dana ji muryar budurwar da bazan tab’a mantawa ba a rayuwata wacce ta watsa min farincikina ta kusa zautar dani.

 

“Sugar lafiya kuwa naji ka katse wayar”

 

Maganar daya fito a bakinta kenan

 

“Allah ya tsine Miki shegiya kwartuwa”

 

 

Ihu na saka sakamakon murd’emin hannu da yayi ya fusge wayar a hannuna Yana “Ke wacce irin wawiya ce mara hankali kinsan wacce kike zaginta”?

 

“Nice wawiya mara hankali sabida na zagi budurwar ka mahfuz”?

 

Nace Ina nuna kaina hawaye mai zafi ya hau zubomin yaja dogon tsaki ya nufi wajen wadrobe din kayansa ya fito da kanan kaya hawaye kawai nake Ina kallonsa har ya gama canza kayan jikinsa ko kallona baiyi ba ya fice daga d’akin.

 

Rawar da jikina keyi yasa na zube akan gwiwa ta na cigaba da kuka Ina tunanin ko dai mahfuz ba’a hayyacinsa yake ba har wani dumm na ringa ji a kunnena dana tuna sunan da Yar iskar ta Kira mahfuz dashi Sugar….

 

6 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!