Hausa Novels

Burina Hausa Novel Free Pages

Burina Hausa Novel Free Pages

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*BURINA*

 

 

_Na_

 

*Oum Fatima*

 

_{Sahibar Hausa}_

 

*_HAUSA WRITERS ASSOCIATION_*

 

_(Take:- Don cigaban Adabin Hausa da al’ummar Hausa)_

 

*Da yaren Hausa ka ɗai muke rubutun mu, ba ma sirkawa da kowanne yare, kishin yarenmu ka ɗai muke yi, ba ma aron yaren wasu, kowanne yare kishin yarensa yake yi, Hausa/Fulani tushen mu.* “`Hausa writers association ta Hausawa ce“`

 

 

*GODIYA.*

 

_Yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai kowa mai komai wanda ya bani ikon rubuta littafin BURINA, tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad S A W da iyalan gidansa da sahabbansa da wad’anda suka yi imani da gaskiya._

 

_Bisimillahir raha’manin Rahim._

 

 

*Page 1*

 

Katsina State, Dutsimma Local Government. Y’an daka Primary School.

 

K’arfe 12:30am ya yi dai dai da kaɗa k’ararrawar tashin daliban da aka yi a makarantar, ko ina ka hanga daliban ne ke tururuwar fitowa daga ajujuwansu don tafiya gida. Ahankali take saukowa daga saman matattakalar ajinsu tana waige – waige da alama da abin da take nema, ahankali ta sauke ajiyar zuciyar jindaɗin ganin ta ba tare da ta sha wahalar nemanta ba kallonta ta yi tare da cewa “Yauwa Azima mu yi sauri mu tafi gida na baro Ummana bata jin daɗi yau sai na koma zan d’aura abinci.”

Yayana Zain Hausa Novel Free Pages

“Subbahanallah mene ya sami Umman?”

 

Mubina taja ajiyar zuciya tare da bayyanar damuwa a kan fuskarta alamun ciwon mahaifiyar nata na damunta, cike da rauni ta amsa “Jikinnata ne ya motsa.

 

“Ya salam, Allah ya bata lafiya.”

 

“Ameen.”

 

Ta amsa tana shafa idanunta da hawaye ya kusa zubowa. Suka ci gaba da tafiya jikinsu a sanyaye, har suka k’araso in da zasu rabu, k’awarta Azima ta fara shigewa da yake unguwarsu ɗaya kuma a layi d’aya suke gida hudu ne a tsakanin su.

 

A natse ta shiga zauren gidansu d’auke da sallama kafin ta karasa shigewa cikin madai-daicin tsakar gidan da yake a tsaftace an ajiye komai a muhallinsa babu alamar datti, daga cikin baranda ta hango mahaifiyarta kwance akan shimfiɗa ta yi matashin kai da filo tana barci sallamar da ta kara yi a karo na biyu ita ta farkar da mahaifiyarta ta ta amsa mata a hankali tare da cewa “Mubeena har kin dawo?”

“Eh na dawo Ummana.”

 

Ta amsa a hankali tare da cewa “Ya jikin naki, kinji sauki?”

 

“Alhamdulillah, naji sauki Mubeena.”

 

” Allah ya karamaki lafiya da nisan kwana.”

 

” Ameen .”

 

“Yawwa Umma ina Abdulhalim.”

 

“Kinga tun d’azu na aikeshi bakin kasuwa yayo cefane inkin dawo ki daura abinci ban samu na yi ba, amma tamkar an aiki bawa garinsu.”

 

“Ok Umma bari in cire uniform sai in bishi na am…

 

Sallamar da aka yi ita ta hanata ƙarasa faɗar abin da ta yi niyya Abdulhalim ne ya shigo hannun sa d’auke da leda, karasowa ya yi ya aje ledar yana fadin “Wash Allah na.”

 

Mubeena ta kalleshi tana cewa “To uban shiririta aina katsaya tun ɗazun umma ta ce ta aikeka amma sai yanzu kake dawowa?.”

 

” Kai Ya Mubeena nifa ba in da na tsaya kawai masu wasan biri na gani shi ne fa na tsaya na kalli kaɗan.”

 

“Uhm Allah ya shiryeka.”

 

Ta furta cikin doka masa harara sannan ta shige d’akin da yake mallakinta. d’akin madai – daici ne mai d’auke da karamin gado da sip mai biyu na ajiyar kayan sawarta sai mirror mai d’auke da kayan kwalliyar yar matashiyar budurwar , k’asan d’akin cafet ne malale, komai dai tsaf tsaf masha Allah.

 

Ta ajiye jakar makarantarta a saman table din da take home work ta karasa wurin sip d’in ta ta bude ta d’auko kayan da zata sauya doguwar rigar atamfa ce dinkin A shape, ta saka ta d’auko hula ta saka a kanta dan bata damu da daura kallabi ba, ta fito ta nufi madai – daicin kitchen ta duba gas taga ya kare ta dauko murhun gawayi ta zuba gawayi ta kunna wuta ta d’aura ruwa yana tafasa ta wanke shinkafa ta zuba sannan ta nufi gyaran kayan miya acikin abin da bai fi awa biyu ba ta kammala dafa shinkafa da miyarta ta yanka salad ta haɗa komai tsaf kamar ba karamar yarinya yar shekara sha biyu zuwa sha ukku ba dan yanzu ne take ajin karshe a makarantar primary school su ne zasu fita zuwa makarantar secondary wato J S S.

 

Ba yi ta shiga ta d’aura arwalla ta shige d’akinta dan yin sallar azahar domin tuni Umman ta shige dakinta dan yin nata, Abdul kuma ya tafi masallaci, bayan sun idar suka yi zaman cin abinci gaba ɗayansu a kwano d’aya suke cin abincin, wannan itace aladarsu basa raba kwanon abinci sai dai in wani ne baya nan acikin su, bayan sun kammala sun sha ruwa Umma ta umarcesu su tashi su yi shirin tafiya islamiya har Abdul tunda ya ji sauki dayake shima ya tashi da dan zazzabi, shi ya hanashi zuwa makarantar Boko amma da yasha magani akamasa allura yanzu shi ke nan ya ware shi nefa har aka aikeshi yo cefane.

 

“To Umma .”

 

Suka amsa a ladafce, daga nan kowa ya shige d’akinsa itama Umman d’akinta ta shige a madai – daicin falonta ta dan kishingid’a a saman doguwar kujera wato 3 sitter dan ta huta domin har yanzu jikin nata ba kwari kawai tana daurewa ne sabo da damuwar da yaranta ke shiga da zarar sun ganta a kwance sannan da tasha magani taji sauki ba laifi amma har yanzu tana jin kirjinta na mata zafi da yake tana fama da (chronic ulcer) da hawan jini amma ulcer tafi matsa mata dan in ta tashi sai ta yi kamar ba zata rayu ba shi ya sa yaranta suke shiga matsananciyar damuwa saboda ita kaɗai garesu mahaifinsu Allah ya masa rasuwa da jimawa.

 

Mubeena ce ta fito daga d’akinta shirye cikin uniform arsh color, Riga da wando da kuma Hijab.

D’akin umma ta lek’a dan yi mata

Sallama tarussuna ta ce “Mun tafi Umma.”

 

“Adawo lafiya, Allah ya bada sa a.”

 

“Ameen Ummanmu.”

 

Jerawa suka yi ita da Abdul suka wuce a hanya suka had’u da Azima da k’annen ta Umar da Maryam. Tafiya suke yi cikin natsuwa suna hira har suka k’arasa Makarantar DARUL QUR’AN da ke a bayan layin su. Suna isa kowa ya nufi ajinsa. Mubeena da Azima ajinsu d’aya . Abdul da Umar ajinsu d’aya sai Maryam ita ce ajinta daban.

 

Kowa na shiga malamin su ya shigo suka fara karatu cikin maida hankali.

 

 

*Oum Fatima ce.*

_(Sahibar Hausa)_

Leave a Comment

error: Content is protected !!