Littafan Hausa Novels

Captain Aminu Hausa Novel Page 61

Captain Aminu Hausa Novel Page 61

 

 

 

 

 

 

 

 

CAPTAIN AMINU

 

 

BY FIRDAUSI SALISU BALA

 

 

 

ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION*

{R.S.W.A}

Amanar So Hausa Novel Page 16

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

ALK’ALAMINMU Y’ANCINMU✍️✍️✍️

 

 

Page*****61 to 65

 

 

_________Yau ko dana tashi daga, bacci jikina duk yayi wani yaushi kona ce wani sanyi, wanka nayi tare da saka tsantsareriyar Atamfata Golding Wax, asharp mai aljihu kalar chocolate, tare da falat shoa na milk chocolate, ta buga d’aurina yayi d’as dashi.

 

 

Ah kitchen na samu su Mommy da Ammi suna famam girke-girke, Mommy na fara rungumewa tare da cewa “good morning my beautiful mommy”.

 

” Morning dear, how was your night”.

 

“Alhamdulillah” na fad’a tare da maida akalata ga Ammi nace “morning my one”.

 

“Morning d’iyar Mommy, an tashi lafiya?”

 

“k’alau Alhamdulillh Ammi”,

 

“to masha Allah” cewar Ammy.

 

Sallamar su Aunty Hidayatu na jiyo aiko da guduna naje na d’auki Ummul Nasri, tare da cillata sama ina mata watsa, inda Abul-nasri kecewa “Kai Umaimata, bikiyi missing d’inaba ko”,

“am sorry dear how can you say it, I really miss you dear baby Nasri”.

 

 

Jansu nayi zuwa wajen Mommy tare da cemata, “Mommyn ga takwararki fa”.

 

“kai wallahi Mommy dama dake take kama, inna tashi inta ce mata ko dawa take kama ashe da mai sunanta take kama”.

 

Haka muka cigaba da firarmu, don ance jirgin su Aysha sai biyu zai sauka, wucewata d’akina nayi tare da kwanciya ta.

 

cikin sleeping dress d’ina nake dogon Wandone tare da rigarsa mai hannu Vest, orange colour,kannan nawa da yasha kitso bako hula, cikin takuna nake tare da ‘yar shagwab’ata nake kwad’awa Abbina k’ira, tare da cewa “Abbi your dota is feeling hungry”.

 

Ban k’arasa fad’a ba kasancewar wanda na gani,d’an waskewa nayi tare da fad’in, “oyoyo- oyoyo my blood Sister tare da rungumar juna,Aysha ce tace “daman mu ‘yan uwan juna ne tabas wannan shak’uwar ta jini ce”.

 

Kallonsa nayi tare da cewa “barka da isowa Hamma Papi”

 

barka k’awai yace min tare da mika akalarsa gasu Bro Deeni, wanda Inka gansu sai kai zaton sun saba,tare da nunawa junansu so, d’auke kaina nayi tare da jin haushi abinda yayimin,to komaine na damuwa tunda bason sa kikeba oho.

 

“Kallon Meamea nayi tare da fad’in “iye ashe ina da K’anwar

mace a duniya”.

 

dariya tayi tare da rungumeni, haka muka cigaba da hirarmu.

 

 

A falo na iske shi kansa saman cinyar Ammina inda take tanbayar sa game da auransa, ganina ne yasa shi ce wa “Umaimata Yarinyar da nike so bata sona, kuma ko kin manta da alk’awarin ki na cewa ‘yarki ta cikin ki zaki auramin” cikin hanzari nabar wajen dan banada buk’atar jin amsar ta.

 

 

“Eh ban manta da alk’awarina ba, amma kace aikana da wadda kake so ko?”

 

“eh Umaima, bakowa bace illMabaruka,kuma ita bata sona”,

 

da sauri ta dago inda Idanunta suka nuna alamun jin dad’i tare da fad’in, “Papina da gaske kake?”,

 

“eh wallahi Umaimata sonta zai iya kasheni”,

 

“A’a Papi indai uwa ta isa ga ‘Ya’yanta to tabbas zan aura maku junanku”.

 

“Tab wannan son kan yayi yaw”,

 

“A’a Mommy kin mance da cewa duk su biyun na isa, dama kece saina ce , tabbas kin isa da mabaruka Amma Papi nawa ne hakama Mabaruka don hakan koyau na mutu duk wanda ya fara bijirewa maganar nan ban yafe masa ba”.

 

“Anya Amaryata bakiyi sauriba”

cewar daddy.

 

daman sunan da yake k’iran Ammi kenan, da yake shigowarsu kenan tare da Abbi, “A’a koni kam ina alfahari da cewa Papi zai aure ‘yata tilo a duniya, koba komai zai kula da ita da bata kyakykyawar rayuwa tare da rik’emin Mabaruka tsakaninsa da Allah” cewar Abbi.

 

 

Zaune nake kusa da Mommy inda take shafamin kai, kallona tayi tare da fad’in “Mabaruka nasan kinsan duk abun da ke faruwa a cikin gidannan, kuma na mai tabbatar maki da cewa inhar ba kya sonsa,to ni zansa a soke wanna had’in da suke sonyi”.

 

 

Kallon ta nayi harzan ce A’a ,wata zuciyar tace “haba dai Mabaruka, mommy cefa, duk da abun da suka maki ,amma da wanna zaki saka musu”.

 

“fad’i duk abinda ke cikin zuciyar ki ‘yata”.

 

harga Allah bansan sanda nace mata “ina son sa”.

 

” Allah maku albarka ”

“ameen” nace.

 

Kamar wasa magana ta zama gaskiya,batun kuma soyayyarmu da Yusuf tun randa ya zo guna Yaya Deeni ya basa hank’uri tare da ce masa anyi min miji, naci kuka har nayi zazzab’i,don bantab’a zaton ba zan auri Yusuf ba.

 

 

WANENE YUSUF

 

“Bazan taba mantawa da wata ranar da naje dinnar Labila K’awata , a canne wurin dinner d’in na had’u da shi, shak’uwa da soyayya mai k’arfi ta shiga tsakaninmu, kuma shi d’ane tal tilo na miji ga minister of fairness d’in Nigeria, cikakken sunansa kuwa Yusuf Abubakar Yusuf mai Naira,shi cikakken d’an kasuwa ne tare da Kamfanoni masu tarin yawa ga tarin dukiya.

 

 

Kasancewar sauk’in da na samu ne yasa ni fitowa daga d’akina, shika dai na gani a falo shiya sani komawa, zuciya tace tacemin hakkan zai nuna masa kina tsoron sa, jin hakan ne yasa ni nufar falon, tare da ce masa “good afternoon hamma Papi”

banza yayi dani, har naji haushin kaina dana gaishe shi.

 

 

Mik’ewa nake da niyyaryi kawai yace min “ke bakisan in kinzo wuri kiyi sallama ba?”

 

d’agowa nayi domin kallon sa gani nayi hankalinsa naga laptop d’in hannunsa ya sani murgud’a baki tare da cewa “Assalamu alaikum”.

“wa’alaiki salam” ya ce tare da kalloni.

 

 

ya ce “mai yasa kika mik’e ba tare da bani amsata ba?” “sa bo da bana sonka” da sauri yad’ago ya kalleni tare da fad’in,”to mai yasa kika cewa Mommy kina sona?”

 

” don bazan iya gaya mata bana son D’anta ba kuma D’an uwana”.

 

“Dalilin kifa?”, “to idan mutane suka ji nida nake ‘Yar uwarka na k’ira to wazaiba ka ‘Yarsa?”.

murmushi yayi najin wannan wautar tata tare da cewa,”tomai yasa biki gayawa Umaimata bakya sona ba?”,”don tun kafin tasan zata haifeni taimaka Al’kawarin zata aura makani, da ace tana da wata y’ar sai nak’i amincewa, amma bazan iya watsama mahaifiyar da ta nuna’min k’auna k’asa a ido ba”na fad’a tare da wucewata nabar masa fallon ma.

 

TAKU HAR KULLUN FEEDOR MANAGER OR FEDY

Add Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!