Sirrin Rike Miji

Cikakken Namiji Acikin Maza

Cikakken Namiji Acikin Maza

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

“Maza kala kala ne, akwai waɗanda suke amsa sunan su na mazaje akwai kuma waɗanda suke basa amsa wannan sunan a gurin matayensu”

🍁”Cikakken namiji wanda yasan ƙiyamah da darajar matarsa, shine wanda yake damuwa da damuwar ta, yake kwantar mata da hankali a lokacin da take tsaka da damuwa, wanda yake faranta mata rai a lokacin da ranta ya ɓaci”

🍁”Shine wanda yake nuna tsantsar soyayya da kulawarsa ga matarsa, wanda baya taɓa hantara ko zagi da cin mutuncin ta ko zagin danginta, shine wanda yasan dukkanin ilahirin haƙƙin ta wanda yake akansa kuma yake ƙoƙarin sauke shi domin ya faranta mata rai kuma ya yiwa ubangijinsa biyayya acikin sauke haƙƙin da ya rataya a wuyansa na aure”

🍁”Cikakken namiji kuma gwarzo acikin mazaje, shine wanda yake ɗaukar matarsa a matsayin abokiyar rayuwarsa, wacce suke mutunta juna a tsakãninsu, shaiɗan baya nasara acikin zamantakewar rayuwar aurensu, zargi baya shiga tsakaninsu, kullum saidai batun girmama juna da kuma ganin mutuncin juna”

🍁”Cikakken namiji bashi bane mai yawan dukan matarsa, kuma bashi bane mai yawan zagin ta, cikakken namji shine mai yawan furta albarka akan matarsa, mai yawan ambaton ta da alkhairi, baya taɓa yarda ya furta mummunar magana game da ita, yana kare mata ƙima da darajarta a duk inda ya tsinci kansa, baya tozarta ta a gaban abokansa ko sauran mutane”

🍁”Dukkanin namijin da bai iya biyan buƙatun iyalansa na yau da kullum ba, to lallai wannan ba cikakken namiji bane, kasancewar ka cikakken namiji, yana farawa ne daga lokacin da ka iya ɗaukewa iyalanka dukkanin nauyinsu wanda ya rataya a wuyanka, kullum burinka ya zamto cewa ka kyautata musu ne, ka yalwata musu, ka kangesu daga haram”

🍁”Yana daga cikin siffar cikakken namiji, shine: wanda ya iya kare mutuncin gidansa, wanda yake kare tarbiyyar iyalansa, tun daga kan matayensa na aure har izuwa kan ƴaƴansa, matuƙar namji bai basu kyakkyawar tarbiyya ba, to lallai haƙiƙa wannan ba cikakken namji bane, domin lallai ya bari gidansa yafi ƙarfinsa, sabida ita tarbiyya daga gida take farawa, to shi kuma yayi sake da ta iyalansa”

“Ka kasance mai yawan tarairayar matarka bawai mai yawan hantararta ba, itama tanada haƙƙi akanka, sannan ko babu komai ai ita matattarar sirrikan ka ce, sabida haka kada ka sake ka tozarta ta a rayuwar aurenku”

 

Leave a Comment

error: Content is protected !!