Hausa Novels

Ciwo A Jikin Wani Hausa Novel

CIWO A JIKIN WANI Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
CIWO A JIKIN WANI

“`(Kᴡᴀʀɪ)“`

 

 

 

 

 

*HAWWA__B__KUMO.*

(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕

*WATTPAD:@REAL-SMASHER.*

*AREWABOOKS:@REALSMASHER.*

 

 

“`Iɴ ᴅᴇᴅɪᴄᴀᴛɪᴏɴ ᴛᴏ ᴍʏ ʟᴀᴛᴇ ᴅᴀᴅ Aʟʜ Mᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ Bᴀʙᴀ Usᴍᴀɴ (B–KUMO)“`

••••••••••••••

“`Masu buƙatar a tallata hajarsu u should contact me ta number na,kou kuyi magana kai tsaye ta “`

 

 

 

02

 

 

 

#Munafukin_zama

 

Bacci take amma sam babu nutsuwa ko sukuni tattare da ita,sosai gabanta ke sake yankewa yana faɗuwa a cikin bacci cike da wasu irin matarkai marasa kan gado,sanda ƴan rakiyar amarya suka shigo gidan wasu danginta suna ta shewa da waƙe irin na mutanen da,wasu kuma suna ɗaga murya suna cewa “tou gafararku dai masu gida.. Amarya Allah ya nufa,alƙawari tsakanin Zannah da Ruqayya,maƙi gani Allah ya kawar da shi kou da uwarsa ce” maganganu dai na rashin mutunci da ɗiban albarka haka sukaita fama,har suka shigo cikin gidan inda su Yagana suke tsaitsaye suna masu barka da zuwa,few suka amsa suma tsofaffin da suka shigo da ita ne,sauran kam sai kallon banza da ganin basu isa ba har suka kai amarya ɗakinta babu maganar a kaita gurin uwar gida a gaisa duk da tana cikin gidan,Yagana ta riƙe baki tana kallon ikon Allah,wata matar Ƙanin Babansu Fandi irin bakatsinan nan ce ta taɓe baki tace “Yagana anya za’a yi zaman lafiya kuwa a gidan nan?” Yagana tace “muna fatan haka Mama Kubra” Mama Kubra tace “gaskiya banga alama ba,tabbas Zannah ya ɗebo ruwan dafa kansa,Allah dai ya tsare Fandi,ita da ba hayaniya ta iya ba ko a gida..” Yagana dai murmushi kawai tayi bata sake cewa komai ba suka koma ɗakin da kujerun Fandi suke suka zauna suna ɗan hirar abunda ya faru. Lokacin da ƴan kawo amarya suka kaita ɗakinta,tsofaffin da suka tarar masu jere suka ce ba haka ake ba,su suka sa akai Ruqayya gurin su Yagana,sukai sallama parlon da Yagana suke,sanda suka shiga wata ƙanwar Baban Ruqayya tace “kuyi haƙuri dan Allah ba’a fara kawota kun gaisa ba” Mama Kubra tace “a’a babu komai hakan ma” aka gaisa suke tambayar “ina uwar gidan Zannah?” Yagana da ta gama ɗaukar cikinsu tace “eyyahh! Bata jin daɗi ne yanzun nan ta samu bacci taita jiran isowarku,tou da baku zo ba ciwo yana neman kayar da ita nace ta samu ta kwanta ai muma idan aka ganmu kamar an ganta ne,kuma abu ma dai da zasu zauna gida ɗaya” tsohuwar tace “kayyade! Allah ya bata lafiya” Yagana ta nuna masu Sanda da Abbor da suke cikin ɗakin tace “ga ƴaƴanta nan dai” ta ƙasan mayafi Ruqayya ta kirasu,tace “wane ne Sanda a cikinku?” Abbor ya nuna ƙaninsa,ta kalleshi tace “kai ne Abbor kou?” Yace “Ehh nine” yanda ta ɗaura Sanda akan cinyarta sai duk wanda suke ɗakin jikinsu yayi sanyi,bayan su Yagana sun karɓi amanar Ruqayya da ƙanwar Babanta ta basu tare da cewa “dan Allah ku kula da ita idan kunga tayi wani abu ba dai² ba ku gyara mata,bata da kowa garin nan banda Zannah sai kou Fandi dake abokiyar zamanta” su Yagana suka ce “babu komai ai an zama ɗaya in sha Allah” daga nan suka mayar da Ruqayya ɗakinta bayan sun ƙara yi mata nasiha sannan sukai mata sallama dan a lokacin za su juya,duka basu wuce mintuna ba suka yi sallama da su Yagana suka tafi,gidan ya rage su Yagana kawai,suna ta ɗan ƙus² ɗin yanda wasu cikin ƴan uwan amaryar sukaita kallonsu ɗai² badan da tsofaffin bama da babu wanda za suyi gaisawar mutunci da shi,dangin Ruqayya suna tafiya kuwa suma suka fara shirin tafiya dan maghreeb ta kawo jiki,bayan sun gyara gidan sun sa turare irin nasu na mutanen Kanuri mai matuƙar kyau,Yagana ta shiga ta tashi Fandi dake bacci tace “tou mu za mu tafi kina ta bacci,har ƴan kawo amarya sun zo sun tafi” da sauri ta sauko saman sabon gadonta da Zannah ya sake mata duk cikin kyautatawar yanda ta sauko da wuri,ta biyo Yagana sukai sallama da ƴan uwanta tana tai masu godiyar yanda suka gyara gidan,kamar kada su tafi a haka dai suka wuce,gida ya rage daga ita sai ƴaƴanta da tasa a ɗaki sukai sallah tare,tana ta sauraren surutunsu da ba fahimtar me suke cewa take ba,kamar jira Zannah yake ana yin ishaa ya shigo gidan sanda ya fara shigowa ɗakinta ta ɗaga kai ta kalleshi ya shigo bakinsa ya ƙi rufuwa kana kallonsa ka ga ango,ya ajiye mata ledar kajin da ya shigo da shi,ko zama baiba yace “bari na leƙa gurin ƙanwarki na dawo” tace “a fito lafiya” tunda ya fita ɗakin Fandi bata ƙara ganinsa ba sai washe gari da safe kusan ƙarfe taran safe tana kitchen ta gama haɗa breakfast tana cikin adonta kamar kullum duk da dai ta rame amma sosai tai kyau,ƙananun 2 step kitson kanta sun sauka bayanta,da sallama ya shigo kitchen ɗin ta amsa ta daure ta saki fuskarta ta gaisheshi,ya amsa yana kallonta cike da ɗan jin nauyin yanda bai koma ba da dare yace “kiyi haƙuri jiya ban dawo ba kuma” tace “babu komai.. Ga breakfast ɗinku” yace “mun gode.. Amma da ruwan zafi kika bani nayi wanka,banyi sallar asuba ba har yanzu” kallonsa ta ɗaga kai ta dunga yi da mamaki,tsayin zamanta da Zannah bai taɓa barin sallah ta wuce shi akan lokaci ba sai yau,bata dai ce masa komai ba ta ɗora masa ruwan,ta ɗauki abincin yaranta ta fita,a gaba tasa su suka ci tare,bayan sun gama ta fita da komai,sanda tayi wanke² ta fara shirin ɗora lunch,lokacin sai ga Ruqayya ta fito da fara’a a fuskarta ta gaisheta,babu laifi itama fara ce sai dai bata kai Fandi kyau ba,bayan sun gaisa take tambayar su Sanda,Fandi tai murmushi tace “ga su can suna wasa a ɗaki” Ruqayya tayi murmushi tace “me zan tayaki?” Fandi ta girgiza kai tana murmusawa tace “a’a wallahi kije ki huta,ai amarya bata aiki” duk yanda taso hana Ruqayya tayata aikin nan bata fasa ba,sai da ta kama mata suna yi suna ɗan hira sama²,duka kuma kusan tambayarta Ruqayya keyi,bayan sun gama ma bin Fandi tayi parlonta tana ta hira da su Sanda tana masu tambaya akan makaranta,abu ɗaya data fahimta yaran dukansu akwai ƙwaƙwalwa dan duk tambayar da za tayi masu sai sun bata amsa, wannan dalilin yasa Zannah yake mugun son su musamman Sanda da komai Zannah zai magana akai indai ya shafi rayuwarsa da iyalinsa zai wahala bai maganar sa ba,a haka Zannah da ya fita gurin aiki ya dawo ya samesu kasancewarsa ma’aikacin gwamnati,shi kansa ya ji daɗin yanda ya tarar da su zaune though ba hira suke ba,amma yanda yaga Ruqayya tana jan ƴaƴansa a jiki abun yai masa daɗi,nan ya zauna shima suka ci gaba da hiran tare. Kullum tunda aka kawo Ruqayya Fandi ke yin girkin safe,rana da dare kuma tare suke yi da Ruqayya dake shige mata,dai² sau ɗaya Zannah baice mata komai game da matarsa ba har lokacin itama batai masa maganar ba,ko even ya haɗa su matsayin matansa yayi masu nasiha,kullum zai shigo ya gansu tare ya zauna suyi hira,ranan da Ruqayya ta cika kwana bakwai da tarewa daren na 8,wamda a ranan ne zai bar ɗakinta kamar yanda shari’a ta tsara,shiru² Fandi tana jiran shigowar Zannah dan duk sauran kwanakin tare take kwana da yaranta amma yau da yake ta san kwananta ne bisa shari’a sai ta kwantar da su ɗakinsu,har tai bacci baza tace ta ji motsinsa ba,da safe ma ko da ta tashi still taga wayam,abun ya taɓa mata zuciya,ta danne duk yanda take jin kuka ta shiga kitchen ta shirya abincin safe,bayan ta gama ta yiwa yaranta wanka ta shiryasu kamar kullum ta zaunar da su ta kawo masu abinci,suna cikin ci Zannah ya shigo parlon,Fandi bata ɗago ba ta gaisheshi yara ma haka ya amsa,sanda ya zauna yana kallon fuskarta yace “kiyi haƙuri jiya ban shigo ba har kikai bacci,ƙanwarki ce bata jin daɗi shi yasa na tsaya gurinta” ta gyaɗa kai tace “Allah ya bata lafiya” ya amsa,har ya tashi zai fita ko me ya tuna ya waigo yace “na sha’afa har yau bamu zauna da ku ba..” Ita dai bata ce komai ba tana bawa Sanda shayin da ta gama fifita masa,Zannah dake kallonta yace “idan kun gama ki shiga ki dubata,kuje tare da yara su gaisa da Aunty’nsu” idan Fandi tai magana tou kujeran da suke parlon sun motsa,ya gaji da maganarsa yai gaba,bayan sun gama suka shiga sukai wa Ruqayya sannu da jiki,the way take wani irin narkewa Fandi ta fahimci lafiyarta lau tsabar iya kisisina ne,suna gama abunda ya kawo su ta kaɗa yaranta suka fita,Zannah kuwa tunda ya fita bata kuma ganinsa ba sai da dare ya shigo,shima kuma tunda ya kwanta bai ƙara motsi ba sai da asubah da ta tasheshi yaje sallah,kafin ya shigo tana ji ya shiga ɗakin amaryarsa har bacci ya ɗauketa bata ji shigowarsa ɗakin ba. A hankali kwanaki suka fara turawa,a ɓangaren zamanta da shi kawai dai za tace gashi nan ne,haka kou yara ma tun zuwan Ruqayya gidan idan ya dawo za suje da gudu suyi masa oyoyo,wani lokacin har su bishi ɗakin amaryar tasa,sai dai Fandi ta jiyo ana cewa “kuje gurin Maamanku” ko “ku tafi kuyi wasa” tun al’amarinsa na damunta sama² har ya fara neman fin ƙarfinta,ranan da ta gaji da sauraren zai raba masu girki da ayyukan gida tai masa magana tunda kullum ita keyin komai shi ne fa ta samu dai ya zauna da su ranan ya raba masu kwana biyu-biyu har ya ɗan masu ƴar nasihar zaman lafiya da juna.. Alhamdulillah! Kuma suna zaman lafiyar,dan tunda aka kawo Ruqayya duk inda ya kamata Fandi ta kaita cikin dangin Zannah ta yi,wani lokaci kou gidansu za taje tare suke zuwa,yanda take nunawa ƴan uwan Fandi so tana masu hidima wani abun kou ita Fandin bata masu,cikin lokacin Ruqayya ta fara laulayi,duk da ba wani mai zafi bane,amma a hakan Fandi ke kula da komai da ita tunda suna zaman lafiya,har zuwa lokacin da cikinta ya tsufa,ranan da Allah ya sauketa ta haifi ɗa namiji,kada kuso ganin murna gurin Zannah,sai nan² yake duk da ba wannan ne karon farko da aka fara masa haihuwa ba,yanayin hidimar da yake yi zaisa mutum yaji wani iri,Fandi ta yi ƙoƙarin ɗauke kai saboda kada tunanin wani abu ya shiga ranta,tunda suna zaman lafiya da Ruqayya,ranan suna yaro yaci sunan baban Ruqayya Nuhu,faɗan irin kayan da Zannah yaiwa iyalinsa kusan ɓata baki ne,haka manyan ragunan da ya yanka,washe garin suna Ƙanwar Baban Ruqayya da take gidan tunda Ruqayya ta haihu da Ruqayya sukai sallama da Fandi saboda za taje wanka gida,dama an bari ne har ayi suna,kamar kada su rabu saboda sabo,yara kam har da kukansu sai sun bi Aunty,da ƙyar aka rarrashe su,Ruqayya suka tafi suna ɗaga masu hannu. Tunda Ruqayya ta tafi Sokoto kulawar Zannah ke kansu Fandi ita da yara,wani sabon shafin soyayya ya buɗe masu,a haka kwanaki sukai ta tafiya. Kamar yau Ruqayya ta tafi sanda ta share wata uku a Sokoto,kullum sai Fandi ta tambayeshi yaushe za ta dawo,zaice mata dai suna hanya,shiru² har sai da sukai wata biyar ciff,zuwa lokacin wasu kam ma har sun fara zargin ko sakinta Zannah yayi yake ɓoye masu,rana a tsaka Zannah yake sanar da Fandi dawowarta,Fandi tayi masu addu’ar sauka lafiya,washe garin ranar kuwa sai ga Ruqayya ta doka sallama,Fandi ta amsa ta fito ɗaki tana mata sannu da zuwa da kuma hanya,tunda Ruqayya ta kalleta sau ɗaya ta wani ɗauke kai,a can ƙarshen wuya ta amsa da “Yawwa! Ya kike?” Jikin Fandi a sanyaya ta amsa,ta tambayeta lafiyar Nuhu da suke kira da Khalifa,bata amsa ba ta wuce ta buɗe ɗakinta ta shige,tunda Ruqayya ta dawo al’amura suka sauya,gaba ɗaya ta daina shiga harkar Fandi,girki da komai Fandi keyi a gidan sarauniyar sai dai taci ta kwanta,and kou za su haɗu a tsakar gidan Fandi bata isheta kallo ba bare gaisuwa ko tambayarta yaranta,sanda take yiwa Zannah maganar raba girki,tunda Ruqayya ta dawo yace ta bari zai mata magana yana sane,daga nan sanda suka ɗauki hanyar wata guda a haka,har lokacin bai magana ba sai dai tashin zance,data sake masa a karo na biyu ya fara faɗa “ni bansan me yake damunki ba wallahi,kwanakin nan wani ganin ido kike ji da shi,mene ne dan kin yi girki da aikin gida? Tunda dai yaranki dake kuke ɓatawa” tunda yai wannan maganar Fandi bata kuma ce masa komai ba akan maganar ta ci gaba da kula da gidan da ƴaƴanta kamar yanda ta saba,girki ne dai tai alƙawarin baza ta kuma yi da shi kou matarsa ba indai ba wai yana ɗakinta ba,duk da har yanzu babu wani bambanci tsakanin ranar kwananta da na Ruqayya inda yaga dama nan zai kwana,duk abunda yaga dama shi yake yi a tsakaninsu,ita kuma tai alƙawarin baza ta sake masa magana akan komai da zai yi ba. A hankali yanayin zaman nasu gaba ɗaya ya canja,kulawar da yake masu a da da yanzu komai ya fara bambanta,ko ɗan wasan da yake yi da yara ma duk ya dena,za suyi masa sannu da zuwa duk sanda ya shigo gida zai amsa fuska babu wadataccen annuri da zaran ya shige ɗakin matarsa can za ta jiyo dariyarsu yana ɗaga ɗansa yana masa wasa,duk wanda zai shigo gidan zai yi tunanin suna zaman lafiya ne saboda duk wani hanyar da zaisa a fahimci wani abu tsakaninsu Ruqayya bata bada fuskar da za’a fahimci komai,haka kou ta ɓangaren Fandi duk wanda zai tambayeta kou akwai wani abu ta kan ce babu,a zahiri duk ƴan uwanta suna ganin yanda tayi rama me munin gaske,duk mai hankali ya kalleta kuma zai fahimci tana cikin damuwa,amma ko an tambaya ba ta cewa komai,hatta Baba idan taje gida yana yawan tambayarta idan da wani abu ta sanar masa,sai dai ta girgiza kai tayi masa murmushi,tace “babu komai Baba” zai tambayeta yara tace “suna nan lafiya” haka kou yanayin zamansu da kishiyarta ma za tace masa lafiya lau. Haka rayuwa taita tafiya,a kwana a tashi babu wuya gurin Allah,yara suna girma suna fuskantar yanda rayuwa take sauyawa,duk lokacin da Ruqayya za taje ganin gida kuwa dama ba ta dawowa da wuri,sannan duk dawowar da za tayi sai an samu wani sabon abu ya sake ɓullowa,da daɗi da rashinsa haka nan Fandi ke rayuwa cikin gidan,tunda Zannah bai ce ya sawwaƙe mata ba bare ta tattara ta tafi gidansu,cikin lokacin yaranta duk sun fara zama samari dan Abbor har ya shiga matakin jami’a,while Sanda ya kammala secondary School,a ɓangaren zamansu a gidan da rayuwarsu kusan za su iya cewa mahaifiyarsu ce komai nasu,baza su ma iya tuna wani abu da mahaifinsu yayi masu ba ko ya yiwa mahaifiyarsu,sai dai yanzu da suka fara mallakar hankulansu su suke taimaka mata,tun daga aikin gida har zuwa abunda za su ci,kou da Abbor ya samu gurbin karatu a Jami’ar Maiduguri boarding ya tafi sai idan ya samu hutun ƙarshen semester kou weekends,sai gidan ya rage Sanda da mahaifiyarsu sai kuma kishiyarta da ƴaƴanta da ta kafa sabon mulki,komai ita ke cewa ayi a gidan yanzu,da zaran ta furta kuma babu musu ne Zannah zai yi,Sanda duk yana ganin abubuwan da ake na rashin adalci,sau da yawa yakan yiwa Mahaifiyarsu magana yace “Maama wai me yasa Baaba yake yiwa Aunty kaza ke baya maki?” Sai tace “nima yana min mana,kai ne dai baka sanin lokacin da yake yi ɗin” to daga haka zai bar maganar,dan idan ya takura lallai sai ya san abunda yayi mata rufeshi take da faɗa,ya kan bata haƙuri daga nan bazai kuma magana ba,dan Allah ya yi shi mutum mai sauƙin kai sai dai idan ka taɓo shi akwai faɗa sannan idan gaskiya tazo ko da iyayensa ne ya kan faɗa masu,kou da al’amura suka ci gaba da tafiya a haka ya samu Baaban yai masa maganar yanda yake yiwa mahaifiyarsu abubuwan da basa kamata,uban ya shigo gida ya rufe Maama Fandi da faɗa har yana kiranta da munafuka,ai ya san duk ita ke zaunar da yaran tana kitsa masu ƙarairayi,yanzu in banda lalacewa har nawa Sanda yake da zai sameshi yana faɗa masa magana,abun yaiwa Fandi ciwon da tai kuka har ta godewa Allah,da dare Sanda ya shigo gidan tai masa faɗa sosai tace idan bazai iya cire idonsa akan abubuwan da suke faruwa a gidan ba tou ita dai za ta daina kula shi,haƙuri ya bata sosai yai mata alƙawarin bazai sake magana ba tunda ba ta so,ya tashi ya tafi ya kwanta yana ta tunanin wa zai samu ya sanarwa ya yiwa Baaba faɗan abunda yake bai kamata ba,a lokacin kakansu mahaifin Fandi ya jima da rasuwa,sai Ƙannensa da kuma ƴan uwan Baabansu Zannah,tunda shi dama maraya ya taso babu uwa bare uba,kou da ya kai ƙarar baban ma dai abunda ya faru ne ya sake maimaita kansa,haushin yanda Sanda ke zuwa yana haɗa shi da ƴan uwa yasa shi sakin Fandi,lokacin tai kukan rashin iyayenta a raye dan ko zaman gidansu ma yanzu wani irin zama ake tunda Baba ya rasu kowa ya kama kan iyalinsa ya ware gidan duk an kacalcalasa wasu sun fitar da kansu daga gidan gandun sun kange iya sashen su,abinci da ƙyar ake sammata,har ta gwammace zaman gidan mijinta da nan,dole tasa ta yiwa Abbor aike makaranta dan lokacin bai jima da komawa ba hutun 1st semester level 3,cikin weekend yazo ya tarar da ita da halin da take ciki,dole ya kira Sanda suka je suka bawa Baabansu haƙuri,shi ne fa suka samu ya mayar da ita da yake saki 1 yayi mata bayan mugayen sharuɗan da ya gindaya,suka ce sun ji sun amince,a ranan Maama Fandi ta dawo gidan,tun daga ranan Sanda yake iya ƙoƙarin ganin ya ɗauke idanunsa akan al’amuran gidan sai dai tsakaninsa da matar Babansu harara dan kou gaisheta ma ya daina yi,ita kuma wannan abun ya fi komai ɓata mata rai,haka kou tsakaninsa da Ƴaƴanta duk wanda yai masa abu duk ƙanƙantarsa yanzu zai kama yaro ya make,sai dai suje mata suna kuka,idan ta tambayi mene ne suce Yaya Sanda ne ya dake su,abun yana bata haushi ta rasa yanda za tayi da Sanda,duk ta inda ta ɓullo shi kuma sai ya san yanda yayi ya cusguna mata taji baƙin ciki,Sanda ya zame mata ciwon ido a gidan. Ana cikin haka ne ya samu Baaba yace yana son ya nemar masa admission ya gaji da zama gara kou makarantar da Yaa Abbor yake ne shima a nemar masa,Baaba yace ya bari yayi shawara,ƙarshe dai sai tashin zance,abun ya bawa Sanda haushi dan ya san duk lokacin da Baaba yace zai shawara ba shawarar kowa zai nema ba sai na Aunty,a lokacin Aunty’n nasu kuma bata jima ba tayi tafiya garinsu,amma wannan lokacin bata yi irin jimawar da take ba ta dawo,bai haƙura ba ya sake samun Baaba da maganar makaranta,Baaba yace bai da halin saka su duka a makaranta yanzu,sai dai ya bari idan Abbor ya gama,yace tou ya nemar masa aiki da Secondary certificate ɗinsa,idan yaso daga baya sai ya nemi tafiya ƙarin karatu,shima again yace ya jira sai ya yi shawara…

 

 

 

This book isn’t for free,normal ₦300 posting 5 days excluding weekend,VIP ₦500 posting daily,SP 1K all via 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank. Then u show ur evidence of payment via https://wa.me/+2348165726609. If u are willing to pay,my sister pay it now before the price will go up,after it is completed the price is ₦500.

 

 

 

#Follow

#Vote

#Comment

#Share fisabilillah!

#Asli Smasher.

[29/09, 11:45 pm] +234 803 192 1625: 💠💠💠💠💠

©®AS-2022.

 

 

 

 

 

 

 

*♡CIWO A JIKIN WANI¸.•💥*

“`(Kᴡᴀʀɪ)“`

 

 

 

 

 

*HAWWA__B__KUMO.*

(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕

*WATTPAD:@REAL-SMASHER.*

*AREWABOOKS:@REALSMASHER.*

 

“`Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ.“`

 

“`D̶I̶S̶C̶L̶A̶I̶M̶E̶R̶:Tʜɪs ʙᴏᴏᴋ ɪs ᴀ ᴍɪx ᴏғ ғɪᴄᴛɪᴏɴ ᴀɴᴅ ʜᴇᴛᴇʀᴏʙɪᴏɢʀᴀᴘʜʏ. ɪᴛ ʀᴇғʟᴇᴄᴛs ᴛʜᴇ ᴀᴜᴛʜᴏʀ’s ᴘʀᴇsᴇɴᴛ ʀᴇᴄᴏʟʟᴇᴄᴛɪᴏɴs ᴏғ ᴇxᴘᴇʀɪᴇɴᴄᴇs ᴏᴠᴇʀ ᴛɪᴍᴇ. sᴏᴍᴇ ɴᴀᴍᴇs ᴀɴᴅ ᴄʜᴀʀᴀᴄᴛᴇʀɪsᴛɪᴄs ʜᴀᴠᴇ ʙᴇᴇɴ ᴄʜᴀɴɢᴇᴅ,sᴏᴍᴇ ᴇᴠᴇɴᴛs ʜᴀᴠᴇ ʙᴇᴇɴ ᴄᴏᴍᴘʀᴇssᴇᴅ,ᴀɴᴅ sᴏᴍᴇ ᴅɪᴀʟᴏɢᴜᴇ ʜᴀs ʙᴇᴇɴ ʀᴇᴄʀᴇᴀᴛᴇᴅ. I ʜᴏᴘᴇ ᴜ ᴡɪʟʟ ʟɪᴋᴇ ᴛʜᴇ sᴛᴏʀʏ ᴛʜᴇ ᴡᴀʏ ɪᴛ ᴄᴏᴍᴇs ᴛᴏ ᴜ.“`

 

“`W̶A̶R̶N̶I̶N̶G̶⚠: Tʜɪs ʙᴏᴏᴋ ᴡɪʟʟ ʜᴀᴠᴇ ᴍᴀᴛᴜʀᴇ ᴄᴏɴᴛᴇɴᴛ ᴀɴᴅ sᴛʀᴏɴɢ ʟᴀɴɢᴜᴀɢᴇ,ɪ’ʟʟ ᴡᴀʀɴ ᴜ ɪғ ᴜ’ʀᴇ ᴀᴛ ᴀ ʏᴏᴜɴɢ ᴀɢᴇ,ɪ ᴡᴏɴ’ᴛ ʙᴇ ʀᴇsᴘᴏɴsɪʙʟᴇ..“`

 

“`Iɴ ᴅᴇᴅɪᴄᴀᴛɪᴏɴ ᴛᴏ ᴍʏ ʟᴀᴛᴇ ғᴀᴛʜᴇʀ Aʟʜ Mᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ Bᴀʙᴀ Usᴍᴀɴ (B–KUMO). Yᴀ ᴀʟʟᴀʜ ғᴏʀɢɪᴠᴇ ᴍʏ ғᴀᴛʜᴇʀ ᴀɴᴅ ᴇʟᴇᴠᴀᴛᴇ ʜɪs sᴛᴀᴛɪᴏɴ ᴀᴍᴏɴɢ ᴛʜᴏsᴇ ᴡʜᴏ ᴀʀᴇ ɢᴜɪᴅᴇᴅ,sᴇɴᴅ ʜɪᴍ ᴀʟᴏɴɢ ᴛʜᴇ ᴘᴀᴛʜ ᴏғ ᴛʜᴏsᴇ ᴡʜᴏ ᴄᴀᴍᴇ ʙᴇғᴏʀᴇ,ᴀɴᴅ ғᴏʀɢɪᴠᴇ ᴜs ᴀɴᴅ ʜɪᴍ,ᴏ ʟᴏʀᴅ ᴏғ ᴛʜᴇ ᴡᴏʀʟᴅs! Eɴʟᴀʀɢᴇ ғᴏʀ ʜɪᴍ ʜɪs ɢʀᴀᴠᴇ ᴀɴᴅ sʜᴇᴅ ʟɪɢʜᴛ ᴜᴘᴏɴ ʜɪᴍ ɪɴ ɪᴛ.. Aɴᴅ ᴍᴀʏ ʜɪᴍ ʙᴇ ᴀᴍᴏɴɢ ᴛʜᴇ ᴍᴇɴs ᴏғ ᴊᴀɴɴᴀᴛᴜʟ-ғɪʀᴅᴀᴜs,ᴛʜᴇ ᴍᴏsᴛ ʙᴇᴀᴜᴛɪғᴜʟ ᴘᴀʀᴀᴅɪsᴇ.. ᴀᴍᴇᴇɴ.🤲“`

••••••••••••••

 

 

01

 

 

 

#Tushe

 

“`YERWA,DANBOA LGA..“`

*BORNO STATE*

 

•••Gida ne babba,traditional building mai ɗauke da babban zaure sai filin tsakar gida dake baibaye da ɗakuna birjik kamar gidan haya,shigowar kyakkyawan farin dattijon mai cikar kamala da ba zai wuce 84yrs ba yasa tarin ƴan mata da samarin da suke zazzaune tsakar gidan ana cacar baki da hayaniya bazama kowa ya fara ƙoƙarin yin ta kansa,a tsakar gidan ya tsaya daga inda yake bayan ya ƙarewa ko ina kallo ya girgiza kai sannan ya fara ƙwala kiran *”FANDI!”* Kwance take bacci har ya fara ɗaukarta,duk da ba da niyyar jimawa suka zo ba ta jiyo kiran da mahaifinta yake mata,a ɗan razane gabanta na faɗuwa ta buɗe ido ta waigo tana kallon ƙofa,da sanyayyar muryarta mara hayaniya sanda yake sake danno mata kira tace “na’am Baba ina fitowa ne ɗankwali nake nema” juyo da kansa yayi ya zubowa ƙofar ɗakin kallo,a hankali ta ɗaga yalolon labulen ɗakin mara nauyi ta sako kyakykyawar farar ƙafarta waje,tunda ta shigo gidan bayan sun gaisa da mahaifin nata a ƙofar gida tabi ɗaki² ta gaisa da matan gidan,kasancewar Allah ya yiwa mahaifiyarta rasuwa shekaru da dama ta wuce can ta shiga ɗakinsu tun zamanin tana ƴan mata,da sauri ta zuro sauran jikita ta fito,kyakkyawar mace ce fara ta gaban kwatance,kallo ɗaya za kai mata kayi zaton ta haɗa jini da larabawa hancinta da huji,ko da yake asalinta ta fito ne daga ƙabilar Kanuri gaba da baya,wanda suke zaune Maiduguri a wani gari da ake kira Yerwa dake cikin Damboa local government. Kanuri suna ne na wata ƙabila daga cikin manyan ƙabilun Arewacin Najeriya,waɗanda suka taɓa kafa ɗaya daga cikin dauloli guda biyu mafiya girma a duk faɗin Afirka ta yau. Mutane ne da suka samo asali daga Yemen suna da matuƙar riƙo da al’adunsu na gargajiya,addini,karɓar baƙi da kuma uwa-uba hidimtawa Alƙur’ani da masu hulɗa da shi da suka shafi koyo,koyarwa,hadda,rubutawa da kuma masu karanta shi. Babban garinsu wato Maiduguri,ana yi masa kallon matsugunni ko kuma masaukin mahaddata da kuma makaranta Alƙur’ani,akwai wata kalma ko kuma lambar girmamawa da suke baiwa duk mutumin da ya ƙware matuƙa gaya wajen karanta Alƙur’ani (Goni) wanda da Hausa ake cewa Gwani. Daga cikin kyawawan al’adun Kanurai ababen ambato akwai girmama na gaba,zaman lafiya da kuma haƙuri da juna wanda ya janyo ake yiwa garin lakabi da Cibiyar Zaman Lafiya (wato Home of Peace) a Turance,wadda take ita ce babbar Jahar Kanurai. Manufar wannan rubutu da ka ke karantawa itace yin bayani bakin gwargwado game da suna,asali,da kuma wasu daga cikin kyawawan halayen mutanen da suke kiran kansu da suna Kanuri,bahaushe kuma yake kiransu da sunan Barebari. “Sunan Kanuri haɗaɗɗe ne daga wasu kalmomin Kanuri guda biyu KA wadda ke da ma’ana ta sanda,da kuma NURI ma’anar haske,wadda ita kuma tushenta shi ne Larabci Nur” waɗannan kalmomi KA da NURI su aka haɗa suka zama Kanuri. Dalilin samuwar wannan suna Kanuri,kamar yadda ya bayyana a tarihi shi ne cewa a farkon lamari su Kanurai sun kasance mutane ne makiyaya masu riƙe da sanda,sannan kuma fuskarsu tana haske. Saboda haka a ƙoƙarinsu na bambance su daga cikin sauran ƙabilun gurin da suke suma makiyayan ne,sai wata ƙabila mai suna Sau suka riƙa kiransu da wannan suna Kanuri. Wato kenan idan abun mu kwatanta ne sai mu iya cewa,mutane masu kama da haske waɗanda suke riƙe da sanda. Amma a wani faɗin kuma asalin sunan Kanuri gauraye ne na kalmomin Larabci guda biyu KAL da kuma NUR waɗanda idan aka haɗesu suke zama KAN-NURI a bisa ƙa’idar Larabci,waɗanda kuma za a iya fassarasu da kamar haske,kamar yadda muka ji daga kakaninmu,daga baya kuma aka jirkita su suka koma Kanuri. Kenan idan muka yiwa wannan suna fassara ta kwatance sai mu ce,mutane masu kama da haske,hakan ya nuna cewa akwai kusanci a tsakanin waɗannan maganganu guda biyu,sai dai Hausawa da kuma Yarabawa amma na iIlori kawai,suna kiransu da sunaye Barebari da kuma Baruba. Abunda za’a iya danganta shi da sunan da Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo (1974) ya kira su da shi:”Waɗannan Barbar ɗin,ragowar Barbar ɗin da suka rayu ne a tsakankanin ƙasashen Arewacin Afirka da kuma Habasha..” Wannan shi ne sunan da Bahaushe ya jirkita shi zuwa Barebari,shi kuma Bayaraben iIlori yace Baruba. Wannan kuma saboda kusancinsu duka biyun ne da Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo,albarkacin Jahadin Shehu Ɗanfodiyo wanda Hausawa da Yarabawan duk abu ya shafesu. Wannan suna na Kanuri shi ne sunan da ƙabilu da yawa suke kiran su da shi,musamman ma Sau,Larabawa,Kotoko,Sudaniyawa,Turawa,Itofiyawa,Turkawa,Mandarawa,Marghi,Babur,Karekare,Ngizem da sauransu,haka nan kuma ana kiran su da wasu sunayen mabambanta,yayin da wasu Ƙabilun Chadi da Sudan da suka haɗa da Najdi,Baggara da kuma Hejazi suke kiransu da suna Barnowaji,Fulani kuma suna kiran su da Kolejo. Asali Magana mafi shahara itace cewa,Kanurai mutanen Yemen ne,sun zo ne daga Zirin Yankin Larabawa (Arabian Peninsula) sannan suka zauna a wani guri mai tazarar kusan kilomita 640 daga arewacin Tafkin Chadi wanda daga baya ya zama ƙasaitacciyar daular Kanem-Bornu. Sannan kuma Sarkin Musulmi Muhammad Ballo (1974) ya ce:”Waɗannan Barebarin,ragowar Barebarin da suka rayu ne a tsakankanin ƙasashen Arewacin Afirka da kuma Habasha,su ne waɗanda Humayyar (Sunan ƙabila ne) suka kora daga Yemen..” Wanda kuma a ƙarshen bayanin nasa ya ƙare da cewa:”Sannan suka gangaro Kanem,suka zaune ta.. Asalinsu daga Yemen ne,sun taho tare da ƴan’uwansu Kanurai suka rabu da su a Ngazargamau” Yaren Kanuri kala ɗaya ne tal! Amma sannu a hankali sakamakon yanayin siyasar rayuwa da ta haddasa gaurayuwar Kanurai da wasu baƙin yarurrukan kodai ta hanyar zuwansu garuruwan Kanurai ko kuma zuwan Kanurai wasu garuruwan ya haifar da hayayyafar wannan yare inda har takai ga an samu bambamce-bambamcen wasu kalmomi ko kuma ma canjin yaren kaco-kam,daga cikin rabe-raben Kanuri akwai:Wuje,Gumati,Manga,Bodoi,Kanembu,Morr,Kwayam,Suwurti,Buduma da sauransu. 100% ɗin Kanurai Musulmi ne waɗanda suka riƙi addinin Musulunci a matsayin tafarkin rayuwarsu sannan kuma Annabi Muhammadu samfurinsu..” Gudunmawar Kanurai wajen yaɗa addinin Musulunci Gazali (2014) ya bayyana Kanurai a matsayin mutanen da suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci da harkar malunta a Afirka ta Yamma a matakin farko da kuma dukkan faɗin Afirka baki ɗaya. Sarkin Musulmi Muhammad Ballo (1974) ya siffanta su a matsayin mutanen da Musulunci ya yi matuƙar yaɗuwa a duk faɗin daularsu a tsakankani sarakunansu da waziransu da sauran jama’arsu,har ta kai ga yana faɗin cewa:”Kai! Ba za ka taɓa samun jama’a a cikin waɗannan garuruwan ba face sun himmatu da karatun Alƙur’ani da tajawidinsa (Hukunce-hukuncen karatun Alƙur’ani),haddace shi da kuma rubuta shi. Kanurai suna da tsagar gado a fuskarsu,wannan tsaga ta su kuwa guda tara ce da suke yin ɗaya a tsakiyar goshi wadda take farawa daga farkon goshi ta sama har zuwa ƙarshen ƙasan doron hanci,sai guda biyu-biyu a kan kumatu,da kuma ƙarin wasu guda biyu-biyu a ɓarin dama da hagu na fuska,sannan kuma dukkan tsagogin nasu dogaye ne (kalli fuskar marigayi Janar Abacha a matsayin misali..) Turus ta tsaya ganin yayyunta maza da ƙanne da suke ƴan maza zar dukansu kowanne ya watse a gurin,kamar ba yanzun nan ta shiga ta barsu ba,gidan da ke cike da hayaniya kamar suna rigima,shi ne cikin ɗan lokaci har kowa ya kama gabansa daga shigowar Baba,a hankali ta ƙarasa gaban mahaifin nata,durƙusawa tayi kanta ƙasa tace “ga ni Baba” ɗan girgiza kai Baba yayi yace “kiyi haƙuri Fandi.. Duk da na san ke me haƙuri ce,amma a wannan karon ina maki nasiha da ki ƙara akan wanda kike da shi,zama ku biyu a gurin miji sai kin koyi yanda za ki kai zuciyarki nesa..” Daga nan ƴar nasiha yayi mata mai shiga jiki sannan yace “tashi kije *ZANNAH* na jiranki za ku tafi.. Allah ya saɓa hali,ya baku zaman lafiya” gyaɗa kai tayi jikinta a sanyaye tana share hawaye tace “ameen Baba,na gode Allah ya saka da alkhairi” fuskarta sam bai nuna fara’a ba sai dai zallar biyayya,ta shiga ɗaki ta ɗauko hijabinta,dama ya faɗa mata baza su jima ba ko sunje gidan,sai dai batai zaton ƙararta zai kawo gurin mahaifin nata ba,sanda ta fito sai da tabi ɗakunan matan ƙannen mahaifinta tayi masu sallama sannan ta kama hanyar fita gidan,a ƙatuwar rumfar dake ƙofar gidan wanda Baba suke zaman hira ta tarar da maihaifin nata zaune yana sake yiwa Zannah da kansa ke ƙasa nasihar ya kasance mai adalci tsakanin matansa,shi kuma yana gyaɗa masa kai yace “in sha Allah.. Na gode Baba” yara biyu maza kyawawa zaune kusa da shi,kana kallonsu ka san duk inda suka fito jini ɗaya suke,suna ta wasansu bakinsu da alawa mai tsinke da Baba ya basu,babban duka bazai wuce shekaru 7 ba,sai ƙaramin mai 4 yrs,ganin fitowarta yasa yaran tashi,ƙaramin ciki ya rugo da gudu yana cewa “Maama yau ban yi wasan ƙasa ba,Yaa Abbor ne yake yi” wansa da ya kira da Abbor yace “Maama banyi ba,ƙarya Sanda yake yi” da kallo tabi yaranta da suke tsananin kama da juna wasu irin hawaye suna kawowa idonta,tai saurin wucewa bata kulasu ba tana share fuskarta kada yaran su gani,ta buɗe motar dake ƙofar gidan ƙirar Peugeot ash colour,sallama da Baba Zannah yayi ya taso ya kama hannun yaransa yace “baku yiwa Kaka sallama ba” suka juya sukace “sai anjima Baba” while shi kuma yana cewa “mun barku lafiya Baba” dattijon kakan nasu ya ɗaga masu hannu yace “tou Allah ya kaimu,Allah ya tsare,ayi ta haƙuri da juna..” Zannah yace “in sha Allah,mun gode sosai Baba..” Tunda ya shiga mota bayan ya buɗewa yaran back seat yake kallon yanda ta rufe fuska da hijab tana kuka,kasa ce mata komai yayi har suka bar ƙofar gidan nasu,sanda suka iso line gidansu duk a cikin Yerwa yayi parking ƙofar wani ɗan madaidaicin gida mai kyau ya kashe motar sannan ya sauka,yaran ya buɗewa duka suka sauka,ya rufe motar lokacin da Fandi ta buɗe itama ta sauka,kana kallon fuskarta za ka san ta ci kuka,abunka da farar mace fuskarta har tai jaa,shi ya buɗe masu gidan suna gaba tare da yaran tana bayansu,tsakar gida ne wadatacce dake malale da siminti sai ƙatuwar bishiyar Umbrella a tsakiya da ya bawa gidan inuwa,kana kallon gidan da iyalin gidan za ka san mai gidan Allah ya yi masa rufin asiri dai² nasa,ɗaki Fandi ta wuce ta bar yaran tare da Babansu suna ta masa hira yana biye masu,da ya gaji da saurarensu yace “maza kuje kuyi wasanku banda faɗa bari naje gurin Maama” suka ce “tou Baaba” ya tashi ya barsu a tsakar gidan,ɗakin da ta shiga ya ɗaga labule da sallama a bakinsa ya shigo,wani mad ƙamshi ya daki hancinsa ya lumshe idanunsa,tana jinsa amma bata iya ɗagowa ta kalleshi ba,ya ƙarasa bakin gadon da take kwance ya zauna,gaba ɗaya ya rasa me zaice dan har yanzu kuka take,cikin wani irin sanyin da jikinsa yayi yace “Fandi! Tashi ki saurareni magana nake so muyi” bata ɗago ba tana share hawayenta tace “ka faɗi duk abunda ya kawoka ina saurarenka” yace “kukan nan fa da kike ba zai mana maganin komai ba,sannan ba shi zaisa na fasa auren nan ba” tashi tayi ta zauna tana kallonsa hawaye suna ci gaba da sauka fuskarta tace “ƙwarai na san kukana bazai hanaka ƙara aure ba,dan Allah tunda kaima ka faɗa da bakinka ka rabu dani naji da abu ɗaya” kallonta yake babu ko ƙiftawa yace “yanzu kin fi so muyi ta zama cikin wannan yanayin? Na kula tunda na sanar maki maganar ƙarin aurena kika daina walwala.. Wanda a da ba haka muke zaune ba,ko so kike sai yaranmu sun fahimci halin da muke ciki? Dan Allah ki kwantar da hankalinki Fandi,idan baki kwantar da hankali ba ni ya kike so nayi? Sannan ita da za ta shigo duk fa da yanda kika karɓeta da haka za ku zauna,ni kuma abunda ba na so kenan,ina so ku zauna lafiya da juna,ta yanda kan ƴaƴanmu zai zama a haɗe..” Gyaɗa kai tayi tana share wasu hawaye masu zafi da suka zubo idonta tace “shi kenan.. Allah ya baku zaman lafiya” yace “ke banda ke?” Ta masa wani kallo bata ce komai ba,ya kwantar da kai yace “dan Allah ki kwantar da hankali ta haka kawai zan samu damar sauke nauyinku duka” ita dai bata ce komai ba kallonsa kawai tace,yace “ki ce wai abu uwar gidana,kuma uwar ƴaƴana” tace “babu abunda zance ka sani,aurene ka ce sai ka yi,shi kenan Allah ya baku zaman lafiya” ganin duk ta inda ya biyo ta ƙi sauka dole ya haƙura,kiran sallar asr yasa shi tashi yace “bari naje masallaci na ji ana kiran sallah” bata kalleshi ba tace “a dawo lafiya” har zai fita yace “kiyi haƙuri Fandi..” Ta ɗago a wani irin fusace dan haushi tace “wai idan ban yi haƙuri ba ya zanyi tou? Ka ce baza ka fasa aure ba,shi kenan ta shigo mana ba dai kai bane ai baza’a rabaka biyu ba dai kou?” Yanda take magana cike da kishi yasa shi girgiza kai ya fita,yaran yasa sukai alwala sannan suka fita masallaci,kafin su dawo ta tashi tayi alwala tai sallah,after tayi addu’o’inta sannan ta fita ta share tsakar gidan ta sake gyarawa ta turare gidan ko ina ya ɗauki ƙamshi,ganin har about 5pm basu shigo ba,ta shiga kitchen ɗaura masu abincin dare. Kou da suka shigo gidan wajen ƙarfe 6 ne saura na yamma,a lokacin ta kusa gama girki,Zannah ya sha mamakin yanda yaga ta kula da gidan har ta shiga kitchen,kou da yake Fandi ba daga nan ba indai wajen kula da gida ne,akwai ta da tsafta sosai ko ina yai fess sai ƙamshi yake mai kwantar da rai,fuskarta ce kawai da take babu fara’a ya dakushe shi daga yawan magana,tai masa sannu da zuwa ganin da ledoji a hannunsa ta ƙaraso inda yake ta durƙusa ta karɓa ta wuce kitchen,sanda ta ajiye ta fito ta ɗauko masu babban tabarma ta shimfiɗa,ta kawo masa ruwa,lokacin yake sanar mata “kin duba kin cire naman dake ciki?” Ta girgiza kai tana miƙewa tace “a’a” daga haka ta tafi kitchen ya bita da kallo cike da so da kulawa,sannan ya taso ya biyo bayanta,tana ta aikinta bata ɗaga kai ta kalleshi ba tace “akwai abunda kake so ne?” Yace “a’a zuwa nayi dai na rage maki wani abun” ta girgiza kai wasu hawaye suna kawowa idonta tace “a’a na kusa gamawa,kaje yanzu zan fito” kallonta ya dunga yi yanda ta juya masa baya,daga muryarta ya fahimci kuka take da shirin yi,bayanta ya ƙaraso ya rungumeta cike da rarrashi yace “me yasa kike son hana ni kusantar inda kike,bayan mun saba aiki tare?” Iya yinta tayi wajen danne kukanta,a hankali yace “dan Allah ba don ni ba kiyi haƙuri Fandi,duk abunda kika ga ya samu bawa akwai manufar faruwarsa” juyowa tayi ta shige jikinsa tana fashewa da kuka,gaba ɗaya hankalinsa ya tashi,duk yanda zai ya rarrasheta sai da yayi,kafin ya samu tai shiru,suka ƙarasa aikin tare kamar yanda suka saba tun aurensu kafin su haifi yaransu,sanda suka fito yana ta janta da hira,tun bata tankasa har ta fara,after sunje sallar maghreeb suna dawowa ta kawo masu abinci,tare suka ci da yaran,bayan sun gama sukai ta hira har aka kira ishaa. Da dare sanda suke kwance bayan sun kwantar da yaran ɗakinsu yaga ta koma can edge of the bed,haƙuri ya fara bata tai murmushi kawai underneath kishi ke cinta tana jin wani irin yanayi yana saukar mata,tunda ya fara maganar auren nan ta daina cikakken bacci,nutsuwa kuwa idan tace tana da ita tou ta yi ƙarya,sam hankalinta yaƙi kwanciya da maganar aurensa,kawai dai tana ƙoƙarin dannewa ne kamar yanda Baba yayi mata nasiha,amma ta wani ɓangaren tana mamakin dalili da abunda ta ragesa da shi,wai daga zuwa bikin aboki shi kenan mutum ya dawo mata a firgice shi aure yake so,ta kasa gane me yake faruwa da shi,lumshe idanunta tayi jinsa a kusa da ita a hankali har bacci ya fara ɗaukanta. A haka kwanaki suka ci gaba da tafiya ta ɓangaren zamansu da Zannah tana ta ƙoƙarin ɓoye damuwarta ganin yanda duk ya damu,while a gefensa shi kuma ganin yanda ta kwantar da hankalinta hakan yai masa daɗi sosai,sanda ya kawo mata kayan faɗan kishiya tai murmushi tana ta danne kukan dake son ƙwace mata tai masa godiya,ya yiwa yaransu ma ɗinkuna sosai kamar lokacin sallah,sosai cikin lokacin yai masu hidima,ya canza mata kayan ɗaki,aka sake gyara gidan,kana gani kasan amarya tana hanyar shigowa ne,sati biyu tsakani aka ɗaura auren Zannah da amaryarsa Ruqayya da ya auro daga garin Sokoto,tunda aka fara bikin kullum ne sai Fandi tai kuka saboda damuwa,ga wani irin fargaba dake damunta,wanda yasa tai rama fiye da zato,ranan da amarya za ta tare few daga cikin ƴan Sokoto manyan mata suka zo jere kafin a taho da amarya,tunda Zannah ya shigo lokacin Fandi tana tsakiyar ƴan uwanta ya sanar mata amarya da danginta suna hanya,yanda yake rawar jiki ranan tun bayan da aka ɗaura auren gaba ɗaya taji ta sare,shiga ɗaya fita ɗaya zaiwa ƴan uwan amaryarsa sannu ga shi sai hidima yake masu kamar dai zai goyasu dan so,haka kawai gaban Fandi ke ta faɗuwa,sanda ta samu wata babbar yayarsu Yagana ta faɗa mata ƴan kawo amarya suna hanya,dama kuma sune suke ta hidimarsu da sauran ƴan gidansu,yaranta kuwa suna can suna ta wasansu ba hankali ne da su ba bare su gane me ake ciki,nan tai shigewarta ɗaki ta kwanta saboda wani irin ciwon da kanta ke yi,bayan sallar asr motoci daga garin Sokoto suka fara parking ƙofar gidan,guɗa da shewar mata ya tabbatarwa ƴan uwan Fandi amarya da danginta sun iso…

 

 

 

This book isn’t for free,normal ₦300 posting 5 days excluding weekend,VIP ₦500 posting daily,SP 1K all via 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank. Then u show ur evidence of payment via https://wa.me/+2348165726609. If u are willing to pay,my sister pay it now before the price will go up,after it is completed the price is ₦500.

 

 

 

 

#Follow

#Vote

#Comment

#Share fisabilillah!

#Asli Smasher.[29/09, 11:45 pm] +234 803 192 1625: 💠💠💠💠💠

©®AS-2022.

 

 

 

 

 

 

 

 

*♡CIWO A JIKIN WANI¸.•💥*

“`(Kᴡᴀʀɪ)“`

 

 

 

 

 

*HAWWA__B__KUMO.*

(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕

*WATTPAD:@REAL-SMASHER.*

*AREWABOOKS:@REALSMASHER.*

 

 

“`Iɴ ᴅᴇᴅɪᴄᴀᴛɪᴏɴ ᴛᴏ ᴍʏ ʟᴀᴛᴇ ᴅᴀᴅ Aʟʜ Mᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ Bᴀʙᴀ Usᴍᴀɴ (B–KUMO).“`

••••••••••••••

“`Masu buƙatar a tallata hajarsu u should contact me directly via “`

 

 

03

 

#Wace ce ita?

 

 

 

Da dare Sanda ya shigo gidan da sallama,hannunsa riƙe da ƴar baƙin leda,kasancewar yana sana’arsa na gyaran babura da motoci a wani garage,shima kuma Yaa Abbor ne ya neman masa maganin zaman banza,a lokacin idan ka ganshi ƙwandala akace ka siye shi baza ka siya ba,duk rana idan suka tashi aiki aka biyashi ba ya shigowa gida sai ya siyo wani abu ya kawowa mahaifiyarsu,ƙofar ɗakin Maama yayi sallama,ta amsa tana ɗan murmusawa tace “shigo mana ka tsaya waje” ya ɗaga labulen ya shiga da wani sallamar a bakinsa,Maama ta amsa tana masa sannu,yayi murmushi ya ajiye mata ledar naman da ya shigo da shi,ta bishi da kallo cike da so tana ta sawa rayuwarsa albarka,yayi murmushi yace “Maama bari nayi wanka muyi fira” tace “tou Sanda,ga ruwan zafi nan a flask na ajiye maka” yace “na gode Maama” ya fita ɗakin ya ɗebi ruwa a famfo yazo ya karɓi ruwan zafin da Maama take cewa ta ajiye masa,ya sirka ruwan ya ɗauka ya tafi banɗaki yayi wanka,da ya fito ɗakinsu ya shiga ya shirya cikin gajeren wando da riga armless,yana gamawa ya fito yayi sallama ɗakin Maama,ta amsa masa tace “shigo ni kaɗai ce a ɗakin” ya shiga sai kuma ya ɗanyi tsaye yace “Maama abinci fa?” Tace “yana dai inda ka saba ɗauka” yace “okay!” Ya fita ya shiga kitchen ya ɗauko flask ɗinsa na abinci,zai fito suka kusan karo da Aunty dake shigowa,da sauri ya koma baya ya bata hanya da faɗin “sorry” wani kallo tai masa cikin ɗaga murya tace “kaifa Sanda baka da mutunci,yanzu idan uwarka ce za ka bangajeta ne?” Ya ɗaga kai ya kalleta jin yanda ta ambaci mahaifiyarsa,ya gyaɗa kai ya wuce zai fita without saying anything,a fusace ta biyoshi tana zaginsa kamar wanda ya rungumeta,sanin da yayi idan yayi magana sai Maama tai masa faɗa,kawai ya ɗaga labule zai shiga ɗakin,Aunty dake biye da shi ta wani kamo bayan rigarsa ta fizgosa,sosai ransa ya kuma ɓaci,ya juyo da niyyar yai mata rashin kunya,tunda abunda take so kenan,ta ɗaukesa da lafiyayyen mari,tsaiwa yayi yana kallonta speechless,Maama dake jin zage²n Aunty ta fito da hanzari tana tambayar “lafiya?” Cikin fushi Sanda yace “Maama kawai zan fito kitchen na kusa bigeta,na bata haƙuri shi ne ta biyo ni tana zagina” haƙuri Maama ta bawa Aunty ta kama hannun Sanda da zuciyarsa ke tafasa suka shige ɗaki,duk da haka Aunty bata tafi ba,sai da tayi haukarta mai isarta ta tafi,sun yi zaton maganar ya wuce daga nan,kou da Baaba ya dawo gidan Aunty ta haɗa ƙarya da gaskiya ta sanar masa har da yanda Sanda ya fita harkarta ya daina gaisheta,Baaba ya kira Sanda bai tsaya tambayar ba’asi ba ya rufesa da faɗa,abun ya ɓatawa Sanda rai yai zuciya ya tashi yai wucewarsa tunda Baaba ya ƙi sauraransa,kuma shi ne har da sawa ya bawa Aunty haƙuri a gabansa wai yai masu sulhu daga yau kar ya sake ji ko ganin bai gaisheta ba,munafukar har da wani kisisina tana murmushi tace “ya wuce ai Sanda ɗa ne a gurina..” Tun daga wannan faɗan da Baaba yayi masa,Sanda ya dena sakin fuska idan ba a gaban Maama yake ba,sai ko idan Yaa Abbor yana nan,tsakaninsa da Aunty kuwa wani irin sabon tsanarta ya dunga gwadawa a cikin gidan,duk abunda zai yi da zaran ta sa baki akai ko ta taɓa,gaba ɗaya ma ya daina amfani da shi kenan,dan wani shishige masan da ta fara tunda Baaba yayi masu sulhu,shi kuma iya yinsa yake yi na ganin basu haɗa hanya kou magana ta shiga tsakaninsu ba,a haka har Abbor ya shiga final year ɗinsa a jami’a,tun daga nan sai ba’a sake samun wani matsalar da za takaici ƙararsa ba. Cikin daren wata ranar Alhamis,Sanda ya fito ya shiga banɗaki fitsari,sai ya bar ƙofar ɗakinsu a buɗe,so ya saba dama ya kan fito da dare irin haka ya shiga banɗaki ko shan ruwa,har ya gama abunda zai da yake ranan Baaba yana ɗakin Maama ne,kansa tsaye kasancewar Abbor yana school ya rufe ɗakin ya koma ya kwanta,can bacci ya fara ɗaukansa yaji an fasa ihu,a firgice ya tashi ya zauna yana kalle²n ɗakin dake da duhu,fitowar Baaba da Maama suna tambayar ihun me suka ji yasa shima ya tashi ya buɗe ƙofar ya fita,Baaba ya kalleshi yace “baka ji wani ƙara ba?” Sanda yace “na ji yanzu shi ne ma yasa ni fitowa,dan ban jima da fitowa naje banɗaki ba” duk sukai Allah ya kiyaye,Baaba yace “amma lafiya Aunty’nku bata fito ba?” Sanda ya wani haɗe rai ya juya zai koma ɗaki,Baaba ya ƙarasa ƙofar ɗakin Aunty yayi knocking,shiru yaji batai magana ba,ya fara kiranta sai yaji ta amsa cikin shesheƙar kuka,sannan ta taso ta buɗe ƙofar,kallonta ya dunga yi cikin hasken farin wata yace “lafiya?” Cikin kuka tace “idan da lafiya me zai sa ni kuka a irin wannan lokacin?” Hankalin Maama duk yana kanta tana sauraranta,Baaba yace “ki sanar da ni kukan me kike da daren nan” Aunty tace “mu bari dai da safe kada ace na cika fitina” Baaba yace “wane irin safe kuma,ki sanar min yanzun nan” cikin kuka tace “gaskiya abunda ɗanka yake yi a cikin gidan nan bai kamata ba,da ina gani ina yin shiru amma yau sai naga abun yana neman wuce gona da iri” Baaba ya gaji da dogon zancen da ta ɗauka yace “wai mene ne yake yi ne? Ki sanar da ni Kai tsaye” tana goge hawaye tace “ai shi ne zan sanar maka” yace “ke nake sauraro” tace “yanzu saboda Allah duk duniyar nan,idan zai tsallake²nsa ai bai kamata ace yayi a cikin gida ba kou?” Kansu duk ya ɗaure sun kasa fahimtar me take son cewa,tace “duk ranar da ba ka ɗakina ya kan fito yazo yana ƙwanƙwasa min ƙafa,ban taɓa sanar maka bane dai,amma ace ya rasa wanda zai nemi ya keɓe da ita sai ni kuma da ranka,naga kou mutuwa kayi ai matsayin uwa nake a gurinsa tunda nake matar ubansa,idan har zai kwanta da ni me zai hana yayi da uwarsa” jikin Baaba ne ya fara tsuma banda kallonta babu abunda yake yace “wane ɗan nawa?” Tace “wane ɗa kuwa banda Sanda” salati Maama ta ɗauka saboda maganar sam hankali bazai ɗauka ba,Sanda kam da yaji maganar sosai ya shiga shock ya ma kasa ko wane irin motsi dan bai kai ga komawa ɗakin ba Maana ta riƙosa ta tsayar da shi,Baaba yace “a cikin gidana za’a yi wannan ƙazantar? Kuma ɗan cikina?” Maama tai saurin tarar numfarfashin Baaba tace “a’a Babansu kada kayi saurin yarda,ni dai ina da tabbacin Sanda bazai taɓa aikata haka ba,haba yama za’ayi ko tunanin haka yayi? Ai idan mafaɗin magana wawa ne majiyinta baya zama ba” cikin kuka da ihu Aunty tace “kenan dai kina nufin ƙarya nai masa?” Maama za ta sake magana Baaba yayi mata tsawa,cikin ɓacin rai ya fara faɗa ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba,Sanda har lokacin yana tsaye ne a gurin amma kwata² ya dena fuskantar abunda suke faɗa,har sai da Baaba ya kama wuyan rigarsa ya fara jansa ya nufi ƙofar fita daga gidan,Maama ta fashe da kuka tana kallon yanda Baaba ke jan Sanda tace “dan Allah Baaba kayi haƙuri,ni na haifi Sanda halayensa babu wanda ban sani ba,na san abunda zai iya aikatawa da wanda bazai ba,dan Allah kabi komai a sannu kayi bincike,kada ka yanke hukuncin da za kazo daga baya kana nadama..” Baaba bai saurareta ba sanda ya buɗe ƙofar duk gari yai shiru baka jin motsin kowa,waje ya cilla Sanda cikin tarin ɓacin rai yana ɗaga murya yace “kaje na yafe ka wa duniya tunda har rashin tarbiyyarka ya kai ka iya neman matar ubanka,tsinanne la’ananne,Allah ya wadaranka ya wadaran uwar data haifeka,in sha Allahu yanda ka nemi tozarta ni sai ƴaƴan cikinka sun maka fiye da haka,kaje na yafe ka daga yau,babu ni babu kai ko a hanya ka ganni ka nuna ka sanni Allah ya isa,ɗan iskan yaro watsatstse,kusa da ni inda hali ba na fatan ka sake zuwa,kaje Allah ya isa tsakanina da kai.. Idan na mutu ko kan gawata ban yarda ka zo ba,idan kazo kuma ban yafe ba..” Maama tana kuka cikin soron gida ganin Baaba zai rufe ƙofa ta ɗaga murya tace “Sanda kana ji na? Maza kaje gidanmu zanzo in sha Allah gobe” bata ƙarasa ba Baaba ya buɗe ƙofar daya rufe ya watso masa kaf kayansa masu kyau da marasa shi,duk wani abu da ya san mallakinsa ne bai barshi ba sai da ya tattaro shi,ya kalli Sanda dake durƙushe ƙofar gidan bisa guiwowinsa yace “idan kaje gurin wasu cikin dangina ko na mahaifiyarku ban yafe ba.. Ga tsiyarka nan daga yau ka ɗauka ba nine mahaifinka ba,nima zan ɗauka cewa ka mutu” Maama dake soron tana kuka tace “Sanda kada abunda mahaifinku yayi maka a yau yasa ka yi zuciya ka aikata wani abu ba dai² ba,ka ɗauka cewa iya abunda yake rubuce cikin ƙaddarar rayuwarka shi ne iya abunda zai same ka.. Masoyi ko maƙiyi babu wanda zai iya sauya komai,ka riƙe wannan kada manta..” Gaba ɗaya duniyar yaji tai masa zafi ya rasa me zai yi,har Baaba ya rufe gidansa bai iya motsawa daga gurin ba,bacci da komai ya ƙaurace masa,tunanin mafita kawai yake amma ya rasa,Maama da ta kirashi² taji shiru,batai zaton yana nan har lokacin ba,jikinta a sanyaye tana sharar ƙwalla masu zafi taja ƙafafunta ta koma cikin ɗakinta,har kusan asuba Sanda yana durƙushe gurin ya kasa tuna komai,kiran farko ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya shiga,jikinsa a mugun sanyaye ya tashi saboda yanda ƙafafuwansa suka riƙe ya tattara kayansa da Baaba ya watso masa ya bar ƙofar gidan,can masallaci ya wuce ya shiga bayan ya adana kayansa a waje ya canja na jikinsa zuwa manyan kaya ya zauna ya jinginar da kansa da bango,sai lokacin wasu irin hawaye suka zubo daga ƙeƙasassun idanunsa daga nan kuma suka sake ɗaukewa,ya ɗauke shi lokaci yana tunani kafin ya fita daga masallacin yayi alwala,yana zaune wajen yana tunanin maganar Baaba tsuntsuwa ta sauka kan wani bishiyar da aka sare,da kallo ya bita jin wani irin sautin kuka da take mara daɗi,ko da ya ɗaga kai ya kalleta mujiya ce tsaye kan iccen tana kallonsa kamar yanda yake,sai da aka kira sallah a karo na biyu sannan ya tashi ya koma cikin masallaci yana waiwayenta,a hankali mutane suka fara fitowa gidaje suna shigowa masallacin,bayan an idar da sallah ya miƙe yabi ayarin masu fita daga masallaci ya fita sanda ya ɗauki kayansa sannan ya ɗauki hanyar barin garin,tafiya kawai yake bai san ina yake nufa ba,bakinsa ya bushe saboda tsananin tashin hankali. Har gari ya waye rana ta fito bai daina tafiya ba,sai da ƙishirwa ta fara damunsa sannan ya tsaya yana kallon inda zai samu ruwa ya sha,hankalinsa sam bai jikinsa shi yasa kou a hanya mutane suke masa magana bai tanka su har ya fita daga Yerwa. A can gidansu ma dai yanda Sanda bai iya samun bacci ba haka Maama ta kwana tana kuka,ga wani irin tausayin Sanda da halin da zai shiga,ta san shi da zuciya akan abu,bare wannan da a gabanta ta ji furucin Baaba akansa,ta tabbatar tunda ya nemi ko haɗa hanya kada ya sake yi da shi,zuciyarsa baza ta bari ya sake haɗuwa da shi ba,ita duk ba ma wannan ne damuwarta ba fatanta Allah yasa kada yace zai bar garin,bata san ina zaice zai nufa ba,har tayi sallah hankalinta bai kwanta ba,da safe kuwa da yake Baaba yace in ta fita kou baya nan a bakin aurenta hankalinta duk ya tashi nan ta aika maƙota aka kira mata wani abokin Sandan tace yaje gida ya tambaya kou Sanda ya zo? Bai jima ba ya dawo da saƙon bai jeba,a taƙaice duk inda take zaton zai iya zuwa ta aika amma kou ganinsa babu wanda yace ya yi,tai kuka kamar ranta zai fita,taiwa Abbor aike makaranta da duk abunda ya faru,hankalin yayan nasa idan ya kai dubu duk sai da ya tashi,gashi lokacin babu waya sai hannun wane da wane,ga jarabawar data sakoshi a gaba babu halin yaje gida,dole haka yake danne damuwarsa yana addu’ar Allah yasa ba barin gari Sanda yayi ba. A ɓangaren Sanda kuwa kamar yanda zuciyarsa ta saƙa masa daga Damboa bai zame ko ina ba sai Biu LGA gidansu wani abokinsa,ya samu masauki wajen Bashir da yake tare sukai makaranta,da suna zaune can Yerwa sai suka tashi suka dawo nan cikin Biu,ranan da ya fara sauka gurinsa bai yarda ya sanar da shi abunda ya rabosa da gıda ba,kawai yace masa yazo ne cike takardan ɗaukan Soja da yaji ana sanarwa a radio,Bashir ya saukeshi a ɗakinsa yana tai masa addu’ar Allah yasa ya samu,ya amsa da ɗan murmushin yaƙe da ya aro ya lanƙaya a fuskarsa,ranan Litinin Bashir ya raka Sanda har barrack na Biu ya cike komai da takardunsa na secondary da sukai kyau,ya gwammace ya nemansa kansa madafa da yaita gararamba a gari bai san ina ya nufa ba,satinsa ɗaya da cikewa da yake kullum yana kan bibiyar yanda lamarin yake ya samu sun amshe shii,ranar da za’ayi secreaning ya shirya yaje,duk abunda ake buƙata tsayi da komai hatta lafiyarsa duk babu matsala,nan aka sanar masu ranan da zasu fara training,tunda ya sanar da Bashir ya fara tattara nasa ya nasa,ranan da za su shiga camp yayi sallama da Bashir da iyayen Bashir ɗin da yake sun san har Baaba,tunda Sanda ya shiga gidan horo na soja zuciyarsa a bushe yake komai,duk training ɗin da za ayi masu komai wahalar da zai sha baza ka ganta a fuskarsa ba,haka nan kwanaki sukai ta zuwa suna wucewa. Idan ya tuna yanda mahaifinsa yayi expelling ɗinsa daga gida abun yana taɓa masa rai,yayin da tsanar Aunty kullum yake ƙaruwa a ransa,duk dare da mafarkin abun yake farkawa,hoping that al’amarin zai ƙare iya nan,but da ya farka zai tarar da saɓanin haka,while soyayyar Maama da Yaa Abbor ke maƙale ransa,duk sanda zai tuna Maama da halin da take ciki yanzu nan zai rasa nutsuwarsa,soyayyarta mai girma tare da tausayinta suna cin zuciyarsa,a haka ya kwashe watanni shida yana karɓar horo,zuwa lokacin kam shi dai bazai ce ga abunda ya faru ba,kawai ya tsinci kansa cikin mugun yanayin ta’amalli da giya,yawan ganinsa da abokai keyi shiru cikin damuwa suka jashi ya fara ɗaga kwalba,cikin lokaci kaɗan ya manta da kowa da komai kansa kawai ya sani,ada ya kan fita cikin gari amma yanzu gaba ɗaya bai son fita idan ba da dare ba,ya koma killace kansa tamkar sabuwar amarya. A can gidansu kuwa damuwar inda ya shiga ya fi komai tayarwa da Maama da Abbor hankali,tunda ya gama karatunsa ya dawo gida suke ta neman inda yake amma basu samu wanda yace masu ya sani ba,a haka aka ɗauki tsayin lokaci,wata rana Bashir suka haɗu da Abbor yake tambayarsa ko ya ga Sanda cikin lokacin nan? Bashir da mamaki lokacin da Abbor ya bashi labarin Sanda ba ya gida basu ma san inda yake ba a halin yanzu,Bashir yace “ai yana Biu” Abbor yace “me yake a Biu?” Bashir yace “ya nemi aikin soja kuma alhamdulillah ya samu,yanzu haka ya fara aiki ma,muna yawan haɗuwa da shi yana zuwa gurina sosai” jikin Abbor har tsuma yake jin an samu labarin inda ɗan uwansa yake yace “ai kuwa zanje na sanar ma Maama inda yake,a yau zan bika muje gurinsa” nan ya bawa Bashir labarin abunda ya faru daya raba Sanda da gida,Bashir yai mamaki yace “amma ni Sanda bai taɓa faɗa min matsala ya samu da gida ba,ko da yaje Biu gidanmu ya sauka gurina,har sai da ya nemi aikin nan,sai da za su fara training sannan ya bar gurina” Abbor yace “ka san mutuminka da fushi,sannan zurfin cikinsa ma bazai bari yayi maganar da kowa ba,kuma tun daga lokacin bai ƙara waiwayo gida ba,hankalin Maama duk yana kansa,kullum sai tai kukan rashin sanin inda ya tafi” Bashir yace “aikuwa ka bata haƙuri sannan kayi mata albishir ɗanta yana nan lafiya ya zama soja” Abbor yace “in sha Allah zan sanar mata kuma yau ba gobe ba zan bika mu tafi Biu na ganshi.. Ya kamata ya dawo gida,kou bazai koma gidan ba dai aƙalla musan yana kusa damu hankalinmu zai fi kwanciya” Bashir yace “gaskiya kam” bayan Abbor ya shiga gida da murnansa ya samu Maama a ɗaki ya sanar mata inda Sanda yake,Maama tana kuka tace “Abbor kai gaggawa kaje ka nemo min shi,bana jin daɗin rashin ganinsa a kusa da ni,ko gidan wani ɗan uwan nawa ne gara na nemi alfarma ya zauna can da dai ace ina zaune nan ban san halin da yake ciki ba” Abbor yace “in sha Allah Maama a yau na yi alƙawarin bin Bashir tunda ya san inda yake zanje na dawo maki da Sanda” Maama dake kuka tace “Allah yasa ya yarda ya biyoka” Abbor yace “ameen..” After asr Abbor yayi sallama da Maama suka tafi Biu tare da Bashir,lokacin da suka sauka yamma yayi,Bashir yace suje gidansu ya kwana zuwa gobe sai suje Barrack,Abbor yace a’a gara yaje yau,baya son saɓa alƙawarin da ya ɗaukarwa Maama,dole bayan sun yi sallar maghreeb suka ɗauki hanya cikin taxi,fatan Abbor bai wuce yaga Sanda ba su koma gida tare,a Barrack lokacin da suka zo suka faɗi gurin wanda suka zo wani Soja yace “taɓɓɓ ɗin ai kuwa Sanda ya bar garin nan” Abbor ya kalli sojan yace “wane gari ya tafi dan Allah?” Yace “an tura shi Anambra state yau da safe” jikin Abbor yai sanyi yace “dan Allah ko zan iya samun address ɗin inda aka tura shi?” Sojan yace “babu matsala” da yake yaga kamar Abbor da Sanda sosai,shi yasa ya gane ƴan uwane su,Abbor da yai shiru cikin wani yanayi bayan sojan ya rubuta masa ya bashi,haka kawai ya ƙurawa takardar ido hawaye suna zuba idonsa yace “me yasa za ka tafi ba tare da kaje ka yi sallama da Maama ba?” Sosai yake kuka yana surutu kamar wanda Sanda yake gabansa,da ƙyar Bashir ya rarrashi Abbor sukaiwa sojan sallama,duk jikinsu yai sanyi da al’amarin haka suka koma gidansu Bashir babu mai yiwa ɗan uwansa magana,washe garin ranar da safe Abbor ya koma Yerwa,tunda Maama ta ganshi shi kaɗai take tambaya “ina Sandan yake?” Abbor da yayi shiru ya girgiza mata kai hawaye suna sauka fuskarsa yace “ban same shi ba,ance sun tafi Anambra jiya da safe” Maama tai shiru tana tunani can tace “yanzu ya za muyi?” Abbor yace “zan siyar da machine ɗina sai nayi kuɗin mota na bishi can” Maama ta girgiza masa kai tace “a’a baza ayi haka ba,akwai ɗankunne na tun wanda Baba ya bani na Mama zan baka ka siyar da shi sai kayi kuɗin motar ka tafi.. Yanzu yaushe za ka fara shirin tafiyar?” Yace “cikin satin nan in Allah ya yarda” Maama tace “Allah ya yarda” ya amsa,cikin kwanakin duk abunda ya kamata sun yi,lokacin da Abbor zai tafiyar bayan sun yi sallama da Maama ya kama hanya,tsaf yabi kwatancen da Sojan nan ya basu,sai dai abun mamakin ko da yaje an sanar masa Sanda bai zo ba,hasalima babu sunansa a cikin jerin sojojin da aka turo Anambra,kwanan Abbor biyu a garin ya koma Maiduguri,sanda ya sanar da Maama nan ma dai kuka kam ta yi shi har ta bawa uku lada,tun daga ranan duk inda za suji labarin anga Sanda basa gajiya da wuri suke yin shawara Abbor zai tafi nemansa,sai dai idan sunje baza su sameshi ba,kamar mai cin layar ɓata,sam sun rasa shi,a garuruwan Nigeria 36 ɗai² ne basu je ba kan neman Sanda a cikin shekara guda,kou da suka fuskanci neman nasa ma kamar ya zama wani jaraba,tunda ko sun je ma basa samunsa duka suka miƙa lamarin gurin Allah,a hankali lokaci ya dunga tafiya shekaru suka fara nisa,lokaci ɗaya Sanda ya ɓace aka neme shi aka rasa,har dai lokacin da labarinsa ya shuɗe ya zama tahiri a gurin mutane,wasu kam ko tunawa da shi ma suka daina,yayin da a gefen Maama da Abbor suka cire rai da tunanin wai yana raye cikin duniyar da suke…

 

*Many years later…*

 

“`ZANGO,KMC (Kano State)“`

 

Wani irin unguwa ce da kana kallo za ka san cewa talakawa sun fi yawa cikinta fiye da masu hannu da shuni,musamman idan kai la’akari da tsarin yanda gine²n unguwar suka kasance a wani irin cunkushe asalin Ghetto area wanda ke ɗauke da mutane iri daban²,Zango unguwa ce dake kusa da kasuwannin Rimi market,Ƙofar Wambai,Kwari da kuma Marina (Kano dye fit) al’ummar cikin unguwar zango sam basu damu da karatun boko sosai ba,sai dai sana’a ko wane iri ne na hannu za ka samesu suna yinsa,matansu da mazansu gwanaye ne wajen neman na kai,sai dai duk da hakan bai hana samun gurɓatattu ba,kamar ƴan shaye² da sauransu.. Fitowar ƴar matashiyar yarinyar daga ɗan madaidaicin gidan around 9:30pm bai sa masu wucewa ta layin da wanda suke zaune cikin majalisu sun kula da ita ba,yarinya ce da baza ta wuce 16yrs ba,duk da kasancewar dare amma hakan bai hana a gane kyaunta,doguwa ce fara idanunta dake manya masu cike da wani irin sirri suna lumshewa da buɗewa kamar wanda ke shirin yin bacci,a hankali ta miƙi hanya tana tafiya ita kaɗanta babu tsoro ko fargar komai da zai iya faruwa duk da yanayin dabanci,ƙwace da satar mutane da ake fama sanadiyyar rashin kyakkyawan tsaro a ƙasa,tunda ta fito bata tsaya ko ina ba sai bakin titi,motoci da sauran vehicles suna ta wucewa ita dai tana tsaye ba tare da ta tsayar da abun hawa ba,can daga tsallake cikin wani majalisa irin na masu zaman banza gaban wani Plaza wani mutum da tun tsaiwarta gurin ya kula da ita yake kallonta,sanda ta shafe a ƙalla 30 minutes a gurin,ganin ba ta da niyyar tafiya ne,kamar bazai taso ba can bayan lokaci yayi tsam ya miƙe daga cikin abokan kartarsa ya nufi inda take,ya tsallako titi a hankali ya tsaya kusa da ita yai sallama,waigowa tayi ta kalleshi da manyan idanunta,yayi mata murmushi yana kallonta,underneath yake yabon kyaunta yana hasaso lokacin da za ta zama cikakkiyar budurwa,yana sauke wani numfashi yace “ƴan mata ina zaki da daren nan? Ba kya jin tsoron tafiya ke kaɗai?” Shiru tayi bata amsa ba ta juya ta ci gaba da kallon ababen hawan da suke ta wucewa,ya sake cewa “kou ba kya magana ne? Nace ina za kije da daren nan kusan ƙarfe 10? Ba kya tsoron dare?” Yanda yaga ta kalleshi idanunta suna lullumshewa yasa shi tsayawa yana kallonta,lokaci ɗaya ya riƙe hannunta yana sake ƙureta da wani kallo,yanda manyan lamppost ɗin titin suka haska ko ina,haka shima ya kureta da mayen kallo a hankali ya furta “ke yarinya ina za kije? Ina ne gidanku? Ina iyayenki suke?” Buɗe lumsassun manyan fararen idanuwanta tayi tana kallonsa,a hankali ta sake mayar da su ta lumshe tana layi kamar za ta faɗi saboda azababben baccin dake cin idanunta,ya kai hannu shoulders ɗinta ya girgiza ta yana sake tambayarta “yarinya daga ina kika fito? Ina ne gidanku?” Sake buɗe ido tayi tana yin baya kamar za ta faɗi,sai dai ta ƙi yin magana,ganin haka mutumin ya fara tunanin abun yi,dan ya gama fahimtar tsabar magagin bacci gareta,can daga cikin majalisar da ya taso,wani ya ƙwalo masa kira da faɗin “Alh Sardauna lafiya? Meke faruwa a nan gurin?”

 

 

 

 

 

This book isn’t for free,normal ₦300 posting 5 days excluding weekend,VIP ₦500 posting daily,SP VIP 1K all via 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank. Then u show ur evidence of payment via https://wa.me/+2348165726609. If u are willing to pay,my sister pay it now before the price will go up,after it is completed the price is ₦500.

 

 

 

 

 

#Follow

#Vote

#Comment

#Share fisabilillah!

#Asli Smasher.

[29/09, 11:45 pm] +234 803 192 1625: 💠💠💠💠💠

©®AS-2022.

 

 

 

 

 

 

 

 

*♡CIWO A JIKIN WANI¸.•💥*

“`(Kᴡᴀʀɪ)“`

 

 

 

 

 

*HAWWA__B__KUMO.*

(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕

*WATTPAD:@REAL-SMASHER.*

*AREWABOOKS:@REALSMASHER.*

 

 

“`Iɴ ᴅᴇᴅɪᴄᴀᴛɪᴏɴ ᴛᴏ ᴍʏ ʟᴀᴛᴇ ᴅᴀᴅ Aʟʜ Mᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ Bᴀʙᴀ Usᴍᴀɴ (B–KUMO).“`

••••••••••••••

“`Masu buƙatar a tallata hajarsu u should contact me ta number na,kou kuyi magana da ni kai tsaye ta “`

 

 

04

 

 

#Fannah

 

Mutumin da aka kira da Alh Sardauna yace “Falaki taso dan Allah kai ne ɗan unguwa” saurin tashi Falaki yayi yasa takalminsa ya tsallako titin while yana cewa “ina za taje ne?” Alh Sardauna yace “kai dai duk ba wannan ba,zo ka duba yarinyar nan kaga kou ka santa?” Falaki da ya ƙaraso ya kalleta da kyau lokaci ɗaya yace “a’ah! wannan ai ƙawar ƴata ce Nana Hafsah.. Na santa wallahi babanta maƙocina ne,mutumin ma ka sanshi wani Alh Umar,yana yawan zuwa majalisar mu sosai ayi hira” Alh Adamu yace “ba dai Harkas ba?” Falaki yace “shi kuwa” Alh Adamu yace “Alhamdulillah ta kwana gidan sauƙi” yana riƙe da hannunta yace “muje dan Allah ka rakani mu mayar masa da ita,ina ga ba’a san ta fito daga gida ba” Falaki yace “tou bismillah muje,dama ina son keƙawa gida..” Tunda ya fara janta take binsa kamar raƙumi da akala har suka iso ƙofar gidansu,Alh Sardauna yai sallama soron gidan da yake bai da zurfi,Falaki da suke tare yace “bari na shiga na fito” Alh Sardauna yace “alright! Hope ba zaka daɗe ba?” Yace “ehhh yanzu zan fito” Alh Sardauna yace “a fito lafiya” bayan ƴan mintuna wata ƴar budurwa da baza ta wuce 19yrs ba ta fito gidan,itama fara ce kamar yarinyar da suka rako sai dai bata kaita kyau ba,ganin babban mutum ta gaishesa,ta kalli yarinyar da yake riƙe da hannunta lokaci ɗaya ta wani zaro ido tace *”FANNAH!* Ina kika tafi? Daga tashinki kiyi fitsari shi ne kika fita?” Alh Sardauna yayi murmushi yana kallon mai maganar yace “ƴan mata babanku yana nan?” Ta girgiza masa kai tace “bai dawo ba” yace “okay! Idan ya dawo kice masa Alh Adam Sardauna yana gaisheshi” ta gyaɗa kai tana kama hannun Fannah tace “zo muje ki kwanta,banza me magagin bacci kawai” ɗan dariya Alh Adam Sardauna yayi yace “ke ya sunanki?” Tace “Aalima..” Yace “maa sha Allah.. Aalima ku dunga kula da ita a dena bari tana fita da dare,tunda kun san tana da nauyin bacci a samu wani ya dunga rakata,saboda duniya babu gaskiya,kada wani abu ya sameta,though ba fata muke ba” Aalima ta gyaɗa kai tace “tou! In sha Allah” 5k ya ciro aljihunsa ya bata yace “ga wannan babu yawa ku sai sweet” Aalima ta girgiza kai tace “a’a ka barshi mun gode” yace “karɓa ai ku ƴaƴana ne,kou dan ban taɓa zuwa gidanku ba?” Ta girgiza kai tana sakin murmushi,yace “karɓi tou idan babanku ya dawo ki tambayeshi shi ya sanni ai” hannu biyu tasa ta karɓa tace “angode Allah ya saka da alkhairi” yace “babu komai ku shiga gida” tace “tou” tana juyawa ya bisu da kallo,a zahiri Aalima ba daga nan ba itama mai kyau ce,sai dai idan Fannah tana kusa an gama magana,yarinya ce amma Allah yai mata kyau sosai²,duk inda mace take ta kai har tana neman fi ma a kyaun fuska da surar jiki,Falaki da tun zuwansu ya shiga gidansa ya fito yaga sai murmushi Alh Adam Sardauna yake,ya kalleshi yace “tou ya akayi ne? Akwai latest?” Alh Adam Sardauna yace “kai haka mutumin nan yake da kyawawan yara ban sani ba?” Falaki yayi wani dariya yace “wallahi banda dai kajin maƙota ne nima da tuni na jima da dafa su a tukunyata,tou wai ina fita hakkin maƙotaka ne” Alh Adamu yace “ehhh! Dama ku idan kun ɗaga ƙafa babu laifi,mu dai mu ɗaga ɗin ne yake da matsala.. Yanzu duk bama wannan ba shi Harkas ya san akwai irin ɗanyen jinin nan a gidansa yake haɗa mu da tsofaffin guzumaye?” Falaki ya fashe da wata dariyar mugunta yace “a’a tou wannan kuma sai kayi magana da shi” Alh Adamu ya wani haƙiƙance yace “wallahi zan yi masa,kou ɗaya cikin na gidansa ne ya bamu mu taɓa,wancan duk tsofin hannu yake nemowa,ka san shi kuma inji yana son service,amma idan da hali ni sai na aure ɗaya ciki kawai na samu ta fita zagayen duniya..” Suna ta hira da dariya har suka koma majalisa. Suna shiga gida sai da Aalima ta kai Fannah tai fitsari sannan ta kama hannunta suka shiga ɗakinsu,wasu ƴan mata ne guda biyu kwance kan ƙatuwar katifa,kowa da inda take sai dai duka karatun novels suke a waya,a hankali suka juyo suka kallesu lokaci ɗaya suka kalli juna,ɗaya tana dariya ta nuna Fannah da idonta ke cike da bacci tace “a ina kika samota? Yau kuma wace hanyar tabi?” Aalima tace “kema Yaa Adija kin san halinta kika ce taje tayi fitsari,Allah ne fa ya kiyaye wani abokin Baffa ya ganta ya dawo da ita gida,kinga ma har ya bamu 5k musai sweet” wani saurin ƙwace kuɗin Adija tayi tace “dallah can kiyi ƙasa² sai kin janyo Baffa ya shigo yana tambayar ina kuɗin suke,kin san dai karɓewa zai babu abunda ya damesa,kuma da safe ya tambayi abun kari” Aalima ta turo baki tace “tou ai baya nan fa bai dawo ba” Adija tace “dallah ki rufawa mutane baki,kin san shi dai ana maganar nan yanzu ya shigo wallahi ƙwacewa zai babu ruwansa,da safe idan yaga babu labari yai ficewarsa mu ta shafa muci ko mu mutu bai damu da cikinmu ba” ɗayan budurwar ta taɓe baki tace “ai ni na rasa wane irin sabo Baffa yayi da kuɗi da ko a zuci ka ambacesu sai yace “na ji ana maganar kuɗi a fito da su ko nayi caje” Adija da Aalima suka fashe da dariya,Adija tace “gaskiya Ashey baki da dama” Aalima tace “yanzu Baffan kike kwaikwayon yanda yake yi?” Ashey ta juya ido cike da tsoro tace “Aalima stop mentioning his name,idan ya shigo Allah zance bansan da wa kike ba” Adija da Aalima suka fashe da dariya har da ƙyaƙyatawa,Fannah kam tunda ta samu guri ta kwanta bata sake sanin me suke ba,sosai suka raba dare suna ta hira,yayin da fiye da rabin maganar tasu ya ta’allaƙa kan maganar Baffa da kuɗi har dai suka gaji suka kwanta bacci.

 

 

*LAKE VIEW,JABI* “`(FCT ABUJA)“`

“`@09:25pm“`

 

Wani irin kantame²n 7 bedroom DTD (detached terraced duplex) ne dake zaune cikin estate ɗin da yai shiru baka jin motsin komai sai kukan ƙwari da tsuntsaye,kwance take cikim ɗaya daga ɗakunan barci tana wani irin kuka mai cin rai tana sake duƙun²ewa saman makeken lafiyayyan bed dake ɗakin da bai da wadataccen haske sai na lampshades,tun yana cikin bathroom yake sauri² ya fito yaji mene ne matsalarta da dare ma bata ɗaga masa ƙafa ba sai ta tada masa hankali,sanda ta gama fusata da shirun da yayi yaƙi kulata ta tashi ta fara watsar da tarin pillows da suke kan gadon,a haukace ta kai hannu ta ture haɗaɗɗen lampshade dake zaune saman bedside drawer tana gunjin kuka tamkar mahaukaciyar da ta ƙwace daga turu,da wani irin zafin nama ta ɗauki glass cup dake aje saman side drawer ɗin ta jefi ƙaton mirror dake can gefe guda na cikin ɗakin,wani irin tsawa glass ɗin yayi kafin ya fara zubewa ƙasa,ƙarar fashewar glasses yasa shi ɗaukan robe da sauri yasa sannan ya buɗe ƙofar ya fito kamar an cillosa ya kai hannu ya kunna fitilu ɗakin nan da nan haske ya mamaye ko ina,matashi ne kyakkyawan gaske da ba zai wuce 38yrs ba,dogo ne fari sai dai ba irin farin turawa ba,irin namu na Africans dake da sirkin baƙi,asalin tsadadden fari garesa da idan yana tare da turawa za ka iya kiransa black Americans,while idan yana cikin ƴan uwanmu Hausawa sai ka ganshi ya koma fari,muscles ɗinsa dake murɗe irin na mazan da suka amsa sunansu mazaje,ba iya jinsin mata kawai ba,hatta ƴan uwansa maza duk wanda ya kalleshi sau ɗaya za kaso ace ka sake,saboda wani irin sirrintaccen kyau da yake da shi,idanuwansa da suke madaidaita masu ɗauke da light brown ƙwayoyi wanda ake kira (gaze) suna wani irin tsukewa kamar yanda fuskarsa ke rikiɗewa lokaci ɗaya zuwa yanayin ɓacin rai,bakinsa masu ɗauke da wasu irin lips masu taushi da suka kasance masu ɗan duhu suka tafi brown yake buɗewa alamun yana daf da zuba tijara,sai dai abunda ya gani yasa shi tsaiwa turus yana kallonta,he looked really handsome a irin yanayin,cikin tarin ɓacin rai da gajiya da kula haukanta,yana mata wani irin kallo da wani murya mai amo ya furta *”HAMDIYYA!* What’s wrong with u? Me yasa ba kya son zaman lafiya please,da daren ma baza ki bari muyi bacci cikin nutsuwa ba,kullum sai kin kawo abunda zai ja rayuka su ɓaci.. What’s ur problem wai?” Ɗago rinannun idanunta wanda ya kira Hamdiyya tayi da kamar suke a juye,asalin ƙwayoyin idonta dai² suke kamar na kowa sai dai idan ta kafe abu da kallo za kaga kamar ba abun take kalla ba,fara ce tas kyaunta dai² nata,kana ganinta ka ga ƴar masu shi dan yanda fatarta yake a goge da hutu,wasu irin hawaye suna tsiyaya daga idanunta,tana ta ƙoƙarin ganin ta danne kukanta tace “haba *MUTALLAB!* Ya kake so nayi wai,danginka duk sunbi sun ɗoran karan tsana kamar nice na hana kaina haihuwa,kana dai kallon yanda dai kullum sai sun goranta min suna cewa na kasa baka kids,sannan kace bazan damu ba..” Sororo ya tsaya kallonta ya ma kasa cewa komai,dan bai yi zaton abunda zai fito daga bakinta ba kenan,hakan yasa Hamdiyya sake kecewa da kuka,tace “ai dama na san dole wata rana kaima ka gaji,ai ka yi ƙoƙari ma a haka da har muka shekara 8 ba tare da ka nunan komai ba.. Amma kada ku manta cewa Allah ne yake bada haihuwa ba mutum ba,kuma idan son raina ne,nima ai bazan kawo yanzu ace ban haihu ba..” Yanda take magana duk zafin da kansa ya ɗauka da lamarinta sai yaji kuma ta bashi tausayi,a hankali ya girgiza kansa ya taho inda take yana faɗin “c’mon DIYA,wai sau nawa kike so naita maimaita maki maganar nan,ni ban damu da rashin haihuwar ki ba,because i knew har da lokaci da bai ba,idan Allah yaso ko a yau sai ya azurta mu da haihuwa,me yasa za ki ɗauki maganar nan kisa a ranki? Kinga na damu ko Mimi ta maki maganar rashin haihuwa?” Girgiza masa kai tayi tana share hawaye da bayan hannu,ya zauna kusa da ita ya kai hannayensa ya janyota ya sata cikin jikinsa yana kallon fuskarta yace “ok then?” Ta turo masa baki tana kallonsa da idanunta da zaka iya rantsewa ba shi take kallo ba,kissing lips ɗinta yayi yace “I love u the way u are” da sauri tace “i love u too,but..” Sai tayi shiru,yace “whaattt?” Yana kallonta,ta wani irin shagwaɓe tace “hope u didn’t forget my promise” yace “wane alƙawari kenan?” Tace “wanda kaimin tun aurenmu,baza kai min kishiya ba no matter what” taɓe baki yayi cikin gajiya da magana yace “let’s forget the matter please” yana lumshe idanunsa ya kalli ɗakin data hargitsa ta wutsiyar ido,ya wani ɗaure fuska yace “yanzu haka za mu kwanta kin ɓata ɗakin?” A shagwaɓe tace “ehh ai ba ƙasa za mu kwana ba naga” bai mamakin abunda tace ba dan ya san dama za’a rina,ya girgiza kansa yace “no muje wani room ɗin dai” tana kallonsa kamar za tayi magana sai kuma ta fasa tace “okay” yaja hancinta yace “shall we?” Ta gyaɗa masa kai kamar bata so,tashi yayi da sauri ya ɗauketa sukai waje tana masa raɗa a kunne yayi murmushi yace “okay! Bazan yi ba,but ya kamata gobe muje hospital” da sauri tace “waye bai da lafiya?” Yace “babu kowa mu za muje ganin doctor akan matsalar mu” tsuke fuska tayi tace “ban gane ba?” Yace “mene ne abunda baki gane ba?” Tace “kaima baka yarda da rashin haihuwar mu daga Allah bane?” Yace “nah! Kawai dai za muje ne saboda musan matsayin da muke,if baza mu taɓa haihuwa ba kinga gara mu sanar da masu maganar muna planning ne,am i right?” Kallonsa ta dunga yi sai kuma tayi wani murmushi mai ciwo tace “a’a kawai dai kace min kana zaton matsalar rashin haihuwar daga gurina ne,ka gaji kana son ganin ƙwanka a duniya yana yawo,ka fito kanka tsaye ka bar min ɓoye² please” tana faɗan haka ta fashe da wani sabon kukan,ɗan numfashi ya fesar yana kallonta yace “okay! Yanzu ya kike so muyi Diya,ni ina neman mana mafita,ke kuma kina kuka,please ya kamata ki tsayar da kukan nan naki saboda musan abun yi,ni ba na son rikici wallahi,ke kuma kina son tada min hankali” Hamdiyya data sassauta kukan da take tace “tou a bari next 2 days” yace “saboda me yasa za’a bari har 2 days?” Tace “ni ina da abun yi ne gobe” yace “a’a ki bari muje dai goben” ta girgiza masa kai,zai magana tace “ni wallahi ka dena min maganar zuwa hospital ɗin nan gobe nace sai next 2 days,ni gobe ina da abun yi” ya gyaɗa kai bayan ya sauketa bakin gadon ɗakin da suka shiga yayi folding hannuwansa a ƙirji yace “saboda abun yin naki is more important than lafiyarki da matsalar da muke tunanin yanda za’ai solving this problem da muka samu kanmu ciki ba tare da wani ya sani ba,right?” Tsuke fuska tayi tace “haba Mutallab ya kake so nayi da raina wai akan matsalar nan,na ce maka ka bari in the next 2 days,why don’t u just understand me? I said a bari kwana biyu,ba na jin daɗin yanda kake treating ɗina kwanakin nan kai da danginka,idan kuma za ka zaɓi family’nka ne akaina fine,ai na san dama alƙawarin da kayi ba lallai ka iya cikamin ba..” Kallonta ya tsaya yi ko ƙiftawa babu,lokaci ɗaya ya tsuke fuska yace “Diya! Stop mentioning my family,na faɗa maki idan muna magana ba na son kina sa min kowa,yanda bazan sa ƴan uwanki ba,stop mentioning mine..” Sororo ta tsaya kallonsa da mamaki tace “ohh! Really? Ai fitowa za kayi kace min sun fini muhimmanci a gurinka da rayuwarka” cikin ɗaga murya yace “i said ki dena mentioning ɗin family na cikin maganar nan.. Mene ne matsalarki da su? Dan sun yi maganar haihuwa sai ki ɗora masu karan tsana,komai sukai basu iya ba a gurinki,idan kinga suna magana kice dake suke,me yasa wai? Baki da matsala da kowa sai family na?” Yanda ya buɗe mata wuta kamar zai haɗiyeta yasa ta miƙewa tsaye akan gadon tana watsa hannuwanta cikin takaici tace “yess! Kamar yanda basu da magana sai ta naƙi haihuwa haka nima bani da magana sai ta sa min idon da suka yi.. Akan me? Ko cikinsu akwai wanda za ta iya maka abunda nake maka ne?” Yace “wace tsiyar kike min? Auren da ba sanin mutuncinsa kikai ba bare ki iya ɗauke nauyina? Gaya min me kike min?” Tace “ai dama ku maza halinku ɗaya ne,komai ƙoƙarin da mace take ta faranta maku idan baku ƙuntata mata ba baku bane” wani disgust kallo ya mata,yayi tsaki sannan ya juya ya fice ya bar mata ɗakin ransa a ɓace,tsakin itama tayi ta harari ƙofa tana ƙananan mita cikin ɓacin rai tace “yanda ka tafi ma haka za ka dawo,tunda babu wacce kake aure cikinsu bare ta iya ɗaukar matsalolinka” daga nan tayi kwanciyarta ta kashe hasken ɗakin,babu jimawa bacci yayi gaba da ita. Tunda ya fito ya canja ɗaki takaicinta ke damunsa,bai san wace irin mace ce ba Hamdiyya,kullum dare sai ta nemo abunda zai ɓata masa rai,ita bata da lokacin faɗa masa matsalolinta sai lokacin bacci ko lokacin cin abinci,ƙarshe kuma shi zai ɓige da bata haƙuri duk inda suka kai da rashin jituwarsu,ya kasa fahimtar a wane aji zai ajiyeta a sahun mata,matsalarsa sam bai gabanta,abunda tafi ganewa kullum tayi wanka ta saka suite ta tafi office tana entertaining client amma mijinta bata san yaya za ta kula da shi ba,yana cikin farin ciki ko akasin haka ita ba damuwarta bane,saɓani kuwa idan ya gindaya tsakaninsu shima babu abunda ya dameta,bata san bawa miji haƙuri ba idan tai masa laifi,sai dai shi ya bata a matsayinsa na namiji,wata irin bauɗaɗɗiyar mace ce da za’a iya kiranta mata ta rako,amma sam bata cikin jerin matan,ta duk ɓangaren da za’a biyo idan maki ake rabawa ya tabbatar ma kansa baza ta wuce 20 ba,sai iyayi da feleƙen mijinta wani ne,juyi yayi a karo na babu adadi yana tuna Mimi,he’s really missing his Mom,yau kawai da baije ya ganta ba ji yake kamar yai shekara,lokaci ɗaya ya tashi ya buɗe ƙofar ya fita,asalin master bedroom ɗinsa da Hamdiyya ta hargitsa ya shiga ya kunna haske,lokaci ɗaya yabi ɗakin da kallon takaici kafin ya ƙarasa ɗayan bedside drawer ya ɗauki tsadadden wayarsa Samsung Galaxy A series,duk ransa a wani irin cunkushe ya zauna bakin gadon yana kiran number da yayi saving da “My world” then yasa a speaker,ring biyu aka ɗauka cikin muryarsa da yai sanyi saboda damuwa yace “good evening Mimi” cikin murya mai sanyi da kamala mahaifiyar tasa da taji yanayinsa tace “are u okay?” Ya lumshe idanunsa a hankali yana shafa sumar kansa da ba mai yawa ba yace “Mmmm” cikin wani yanayi tace “yauma kun yi faɗan ne?” Ya gyaɗa kai kamar yana gabanta yace “yess!” Tace “me yasa kake biye mata ne? Kaifa namiji ne shi kenan sai ka dunga biye mace kuna sa’insa,baka san shi yasa ta rainaka ba?” Yace “Mimi ban san ya take so nai ba,kullum ba ta da lokacin nemana da faɗa sai lokacin bacci.. I’m so tired,na gaji da halinta” Mimi tace “a’a baka gaji ba Mutallab..” Ya wani shagwaɓe yace “wallahi na gaji Mimi” tace “idan ka gaji why baza ka ƙara aure ba? Tunda matarka ba hankali ne da ita ba i think kishiyar dai itace best solution da zai kawo zaman lafiya a gidanka” zaro duk girman idanunsa yayi yace “Mimi taya zan iya da mata biyu ina ɗan yaro da ni? Ɗaya ma take bani headache ina kuma ace na haɗa su biyu” tace “okay! Tunda haka ka zaɓa shi kenan zan tai maka addu’ah,yanzu sai kaje ka bata haƙuri tunda haka ka saba mata” a shagwaɓe yace “Mimi!” tace “uhmn! Mu kwana lafiya” yace “okay! Bye” tace “bye” ita ta katse kiran saboda takaici,yabi wayar da kallo ya san ta ji haushinsa ne,yayi ɗan murmushi yana shafa kansa,gaskiyar Mimi ne haƙurin dai zai je ya bata,dan bai jin zai iya wani yin aure,mace ɗaya ya tsara rayuwarsa da ita,sai dai duk da yana jin bai sa’a ba ba ya ma lissafin sake yin wani aure gaba ɗaya a rayuwarsa. Tashi yayi ya kashe wutar ɗakin ya fita,kamar bai son zuwa inda take ya daure ya buɗe bedroom ɗinta ya shiga,bai yi mamaki ba da ya sameta tana bacci,ya haura gadon bayan ya yi addu’o’in kwanciya ya lumshe idanunsa yana nazarin wasu abubuwa game da Hamdiyya da ta rasa,a haka har bacci ya ɗaukesa. Da safe kasancewar weekends ko da ta tashi ta fito tsakar gida tana miƙa,kallonta Adija suka tsaya yi,lokaci ɗaya Aalima dake chopping onion tana dariyar tsokana tace “Allah ya taimaki gimbiya sai yanzu aka fito?” Ashey tana cikin kitchen tana kwaɓin fulawa tace “gimbiya mai magagin bacci?” Suka kwashe da wata dariyar tsokana,ware manyan idanunta tayi ta turo baki idanunta cike da wani irin yanayin shagwaɓa ta kalli yayyun nata uku da duk ita suke kallo,sai kuma ta kalli babbar cikinsu da Baby voice ɗinta tace “Yaa Adija kinga ki masu magana su daina tsokanata” taɓe baki Adija tayi tace “dallah wuce ki wanke baki ni kizo in aikeki,tun ɗazu ke nake jira” hawaye ne suka zubo idonta tace “tou kuma baza kice su daina tsokanata ba?” A masife Adija tace “bazance ba,wallahi idan baki wuce ba na tashi sai na maki shegen duka” kuka sosai tasa tana buga ƙafa tana mita,Adija ta fusata ta tashi tai kanta,kafin ta ƙaraso da gudu Fannah ta suri buta ta shige banɗaki tana kuka,Adija taja tsaki tace “da kin tsaya ai” kusan minti goma sannan Fannah ta fito jikinta da alamun ruwa,duk suka bita da kallo,fuskarta ɗaure ta wuce ɗakinsu,sanda ta canja kayan jikinta tasa doguwar riga ta ɗaura hijab a sama sannan ta fito,a hankali ta ƙarasa gurin da Adija ke zaune bakin ƙaramin kitchen ɗinsu tace “na gama” wani shegen kallo Adija ta mata tace “dan ubanki saura na aikeki ki yar min da canjin yauma,wallahi zaneki zan dan ban gaji asara ba.. Sannan idan Baffa ya ganki dama kika ce ni na aikeki ko kika bari yaga kuɗin nan wallahi yau sai dai ki san yanda za kiyi da cikinki amma baki da rabo cikin abunda duk za ki gani” turo baki tayi idanunta sun yi rau²,Aalima dake dariya tace “wallahi yarinyar nan muguwar sakarai ce,ji daga magana za taiwa mutane kuka” Adija ta bata 2k a ɓoye tace “kije kiosk ɗin Labaran ki auno min shinkafa kwano ɗaya,sai ki siyo maggi da sauran canjin” gyaɗa kai tayi tana goge idonta sannan ta fita gidan,a hanya tana tafiya fuskar nan a ɗaure saboda an ɓata mata rai,tunda ta wucesa ya tsaya ya bita da kallo yana jin kamar zuciyarsa zai narke,kyakykyawan matashin saurayi ne black beauty da bazai wuce 32yrs ba,ganin tana neman yi masa nisa wata zuciyar ta bashi shawara,da sauri ya biyota a baya,alamu taji kamar ana binta,lokaci ɗaya ta juya a tsorace,suna haɗa ido yayi mata sallama,tsuke ɗan bakinta tayi tana masa wani kallo gabanta yana faɗuwa kamar za tayi kuka,Baby voice ɗinta na rawa tace “malam lafiya kake bina,ka san yanda kasa naji tsoro?” Yayi mata murmushinsa mai kyau yace “sorry! Amma ban yi niyyar tsorata ki ba” ta kalleshi kawai bata saurareshi ba tai wucewarta tana murguɗa baki,har kiosk ɗin Labaran ya bita ta dunga kallonsa ta wutsiyar ido tana juya kuɗin hannunta ta kasa cewa ga abunda za’a bata,shi kuma yana gefe yana ta kallon fararen ƙafafuwanta da suke ɗauke da ragowar jan lalle da zanensa yai kyau yana jiranta,Labaran ya gaji da jiran tai magana yace “me za’a baki Fannah?” Ta harari guy ɗin tana tsuke ɗan bakinta still ta ƙi magana,tana jin sanda ya maimaita sunanta da Labaran me kanti ya ambata,kusan minti goma ta gaji da jiran ya tafi tayi shahada ta miƙawa Labaran kuɗin tace “Mmmm! A ban.. Mmm” sai kuma tayi shiru,Labaran dai dariya kawai yayi yace “me za’a baki?” Tana runtse idanuwa can ƙarshen throat tace masa “shinkafa kwano 1,sai maggi star na sauran canjin” Allah ya so ita Labaran ɗin yake kallo sanda tai magana,sai yasa ya fahimci me tace,ya auna mata komai ya miƙo mata,ta karɓa tasa cikin hijab fuskarta ɗaure ta wuce da sauri kamar za ta faɗi,guy ɗin ya kuma binta suna ta tafiya,har ƙofar gidansu bai sake mata magana ba,sanda ta ɗan juya ta saci kallonsa kafin ta shige ciki da gudu,Aalima suna ta hira suka ga ta faɗo gidan kamar an cillota tana haki,Ashey tace “ke lafiya?” Kuka ta fashe da shi tace “ba wani ne yake ta bina ba har kiosk ɗin Labaran,kuma shi ne yanzu ma ya sake biyo ni” baki sake suka dunga kallonta da mamaki,Adija taja tsaki tace “ina aiken da nai maki?” Tana share hawaye tace “ga shi” ta miƙa mata,Aalima dai kallon Fannah take ta kasa magana,lokaci ɗaya tace “ina yake wanda yake bin naki?” Tace “yana waje” Aalima ta ɗauki hijab ɗinta kan igiyar da suke shanya da ba’a jima ba ta shigo daga aike itama,ta nufi ƙofar gida tana saka hijab ɗin,a tsaye taga mutum daga ɗan nesa yana kallon ƙofar gidan,lokaci ɗaya yayi murmushi ya taho he thought Fannah ce,sai da yazo kusa yaga basa kama sam sai dai na jini,calmly yayi mata sallama,Aalima dake kallonsa tace “kaine ka biyo Fannah?” Ya gyaɗa mata kai lokaci ɗaya yayi murmushi da ya tuna yanda ta shige gida da gudu dimples ɗinsa suka bayyana,yace “Fannah’s Sis?” Ta gyaɗa masa kai tace “kayi haƙuri dan Allah karatu take yanzu ba’a bata damar tsaiwa da saurayi ba” yayi murmushi yace “u don’t worry about it,nima na shigo unguwar ne gaisuwa sai na ganta,unfortunately sai naji bazan iya tafiya,ba tare da nai magana da ita ba,but kou zan iya zuwa muna gaisawa?” Aalima ta ɗan zaro idonta sai kuma tayi dariya tace “sai dai ka nemi izini gurin Baffanmu” ya gyaɗa kai yace “in sha Allah.. Kamar wane lokaci ake samunsa gida,na san yanzu dai maybe baya nan,right?” Tace “Ehh! In the evening yake dawowa” ya lumshe idanunsa yace “thanks for ur time and help.. But ur name please?” Tace “Aalima!” Yayi mata murmushi yace “na gode Sis Aalima.. Ni suna na Yusuf Khaleel Yusuf..” Ta mayar masa da murmushin da yayi mata tace “babu komai” yace “in sha Allah idan na dawo zan nemeki” tace “okay! Allah ya kawo ka lafiya” yace “ameen..” Then yayi sallama da ita ya tafi,tana tsaye har sanda taga ya buɗe wani irin Honda Accord na zamani,ta juya cikin gida da gudu tana ihun murna,Ashey da Adija suka kalleta,tace “kunga guy ɗin da Auta ta fallo mana kuwa? Sunansa Yusuf yace min,ya shigo gaisuwar mutuwa ya ganta shi ne banzar ta birkice taƙi tsaiwa ta shigo da gudu” Adija tayi murmushi tana kallon Fannah data ɗaure fuska tana cin wainar fulawan da Ashey ke soyawa tace “oohh! Su Auta tou kunya kike ji ne aga kin tsaya da saurayi?” Fannah bata kalleta ba kuma taƙi cewa komai,fuskarta kaɗai za ka kalla kasan a wuya take,Ashey tace “ke yarinya kada ki tsaya kanki yayi murfi,mu da muke neman samarin bamu samu ba,shi ne ke kin samu saboda rashin hankali za ki nemi butulcewa Allah? Kullum addu’ar da nake mana yanda muke zaune gida daga mu sai Baffa,muna fita ana zunɗenmu da zaginmu munƙi aure mun tsaya zaɓe dan munga Allah ya mana kyau,dole mu roƙi Allah ya yanke mana ya kawo mana mazaje muyi aure,kou za mu samu sauƙin rayuwar da muka tsinci kanmu a ciki.. Kina dai kallon yanda kullum muke fafutukar neman abincin da za mu ci,babu wanda ya san a yanda muke rayuwa,amma kullum mune a bakin mutane,basu da magana sai ta mu,babu abunda ba’a kiranmu da shi,ance mana yan iska,babu ma irin sunan da ba’a kiranmu da shi,tou me yasa ke za ki ƙi amfani da damarki?” Jikin Fannah a sanyaye ta ɗago kanta tana kallon Adija idanunta cike da hawaye,tunani take duka fa shekarun Adija 23 ne,sannan a cikinsu duka babu mai girman jikin da za’a ce shekarun sun bayyana a jikinsu,idan ba faɗa maka aka yi ba dukansu aka zube maka su,za ka iya cewa bai fi shekara 1-1 ne tsakaninsu ba,Ashey yanzu tana da 20,sai Aalima mai 19 sai ita da ke da 16yrs going to 17 dan akwai sauran months kafin ta cika 17,tashi tayi ta wuce ɗaki cikin sanyin jiki tana share ƙwalla,suka bita da kallo cike da tausayi,kwanciya tayi saman ƙatuwar katifarsu tana kuka,tabbas rayuwarsu cike yake da ƙalubale,a zahiri idan ka kallesu duka babu mummuna saboda kou Baffansu ka kalla ka san lokacin ƙuruciyarsa anyi kyakkyawan matashi,wanda ƴan mata suka sha dambatuwa da juna a kansa,haka kou hotunan Mamansu ka kalleta za ka san cewa Allah ya yi halitta a gurin,kyakkyawar bafulatana ce ta gaske,duk a yanzu ba tunanin komai ne ya tsaya mata a rai ba,irin yanda ƴan uwanta ke zaune babu samari,ta ya ma za’ayi ita tana ƙarama za ta so ace ta yi aure ta tafi ta barsu cikin wahala da rashi? Kullum fafutuka suke su nema su ciyar da su har da mahaifinsu da ta kasa gane amfaninsa a tare da su,tabbas dole tace haka dan kuwa kou yana da shi bazai basu ba,ya gwammace yaje ya zuba su a caca a cinye ya tashi babu ko kobo,ƙarshe idan yaji azabar talauci ya fara binsu yana su bashi na hannunsu,idan basu bayar ba ya shiga ɗakin ya bincike,babu ruwansa kuma haka zai dawo da yunwa su ɗauki abunda suka sarrafa su kai masa yasa hannu ya cinye ko sannu bare tambayarsu inda suka samo,samari kuwa dama na zamanin nan ɓata gari sun fi yawa,mafi yawancin wanda za su biyosu Adija ƴan shan minti ne,da zarar sunga wankakkiya burinsu su hure mata kunne su canja mata ra’ayi,da sun yi nasarar ɓata mata tarbiyya shi kenan burinsu ya cika sai kuma a fara yawo da ita hotel²,idan tafiya tai nisa su mayar dake kamar matarsu,wannan duk tunanin da take maganganun su Adija ne idan suna hira kowa tana faɗan matsalar da take fuskanta game da samarin da suke biyota da yanayin yanda tsarin zamansu yake kasancewa,idan kuma suka fuskanci ba irin hannunsu bace,tuni za su cika wandonsu da iska,ajiyar zuciya ta dunga saukewa kafin wani irin bacci ya sake yin gaba da ita…

 

 

 

 

This book isn’t for free,normal ₦300 posting 5 days excluding weekend,VIP ₦500 posting daily,SP VIP 1K all via 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank. Then u show ur evidence of payment via https://wa.me/+2348165726609. If u are willing to pay,my sister pay it now before the price will go up,after it is completed the price is ₦500.

 

 

 

#Follow

#Vote

#Comment

#Share fisabilillah!

#Asli Smasher.

Leave a Comment

error: Content is protected !!