Hausa Novels

Dace Da Juna hausa novel

 Part 1 to 5


Gidan Alhaji Bature gida me dauke da mata biyu, kuma babban gida ne wanda ya ginashi domin iyali biyu, kowacce da nata bangaren, nashi kuma yana tsakiya, haka akowane bangare akwai kofar dazata sadaka da falonshi, kuma kowace mata da kuna biyu ne a bangarenta.

matarshi ta farko sunanta Hauwa’u, tana da yara 3,  biyu maza daya mace, kuma yaran gidan suna kiranta da mama. Matarshi ta 2 sunanta Jamila, tana da yara 2, daya namiji daya mace, yaran gidan suna kiranta da Inne, shikuma megidan suna kiranshi da Malan.

Alhaji Bature principal ne a makarantar maza datake garin Mani jihar Katsina. Allah yayi shi da son ilimin boko shiyasa sam baya wasa da duk yaron da yakasance baya maida hankali a karatunshi.

Daya daga cikin matarshi ‘yar garin Mani ce wato uwar gidanshi mama, ta biyun kuma ‘Yar Mashi ce. Malan  yana matukar son yaranshi masu kokari, kuma akayi sa’a yaran Uwar gidanshi suna gane karatu sosai.

mama mace ce meson aso nata, kuma tana da nuna banbanci atsakanin yaranta, kasancewar Malan yana matukar son yaranta yasa takara jin ita din wata ce. Danta na farko shine Farouk, na biyu kuma Fahad, se macen kuma Farida.

Yaran Inne kuma na farkon sunanshi Faisal, se macen Fatima. Ra’ayin Malan ne san yama yaranshi suna me farin harafin (F), kuma ya hana a boyema kowa sunanshi, shiyasa ma besa sunan iyayenshi kona matanshi ba, kawai yazabi sunayen ne bisa ra’ayinshi.

Farouk yana Primary 6 a wata Private School dake Mani, shi kuma Fahad yana a primary 4, se Farida tana Primary 2. Kasancewar yaran Inne basu da kokari sosai, hakan yasa Malan ya ciresu daga makarantar kudi ya maidasu ta gwamnati, domin Faisal tsaran Fahad ne amma so biyu ana mashi repeating, hakan yasa haryanzu yake primary 3. Itama Fatima sa’ar Farida ce, amma yanzu a primary 1 take, saboda itama so biyu ana mata repeating, ko nursery da kyar ta wuce.

Haka ma a islamiya sam basa maida hankali, shiyasa sauran suka wuce su. Wannan rashin kokari nasu bakaramin batama Malan rai yake ba, domin shide yana da kokari sosai, shiyasa yake ganin laifin Inne ne da yaranta suka kasance marasa kokari.

Domin yana ganin ita Mama da suka dade tare da ita tasan yanda yake tafiyar da al’amuranshi, wannan dalilin ne yasa yake fifita yaran Mama kan na Inne. Kuma ganin yana asarar kudinshi yasa ya ciresu daga makarantar kudi yasasu ta gwamnati.

Duk da mutanan gari suna yawan yin tsegumi akan abinda yayi, sede sanin halinshi yasa babu wanda yataba tun kararshi da maganar. Malan da iyalanshi suna zaune a Quarters ta garin Mani, Mahaifinshi yarasu, se Mamarshi wadda yara suke kira da Kakaji ita kuma tana zaune a unguwar Kangiwa.

Itama tana matukar son yaran Mama, kuma haka take nuna banbanci atsakanin yaran Inne. Sede duk wannan abun da sukeyi Inne bata taba magana ba, kasancewarta mata me matukar hakuri, inda sabo tasaba, tun kafin ta haihu take ganin banbanci atsakaninta da Mama.

Domin Mama tafi Inne kyau sosai, kuma ta iya kwalliya da kissa, ta iya jan hankalin mijinta, wannan shine yakara mata kima da daraja awajen Malan, kuma haka ta koyama yaranta duk wani salo na kissa, yanda zasu saka soyayyarsu awajen mahaifinsu.

WANNAN SHINE TAKAI TACCEN TARIHIN MALAN BATURE DA IYALANSHI.


Zaune Mama take tana yima Farida kitso domin gobe monday akwai makaranta, Farouk kuma yana wanke ma kannanshi safar na makaranta domin tun ranar juma’a da yamma Mama take sasu su wanke kayansu su goge.

 yayin da Fahad yake share masu bangaren su. Bayan yagama Mama ta duba agogo ganin Malan yakusa shigowa tace ma Fahad yi sauri yaje ya share kofar falon Malan.

Daukar tsintsiyar yayi ya nufi kofar falon Malan yafara sharewa, duk da Faisal ya share tun dazu da yayi sharar kofarsu, amma saboda kissa ta Mama tasa Fahad yatafi ya share saboda taga lokacin dawowar Malan yayi.

Da sallama Malan yashigo,da sauri Farouk ya ajiye abinda yake yanufi awajenshi, shima Fahad aje tsintsiyar yayi ya nufi wajenshi, suna zuwa kowa ya karbi kayan daya shigo dasu suna fadin Malan sannu da zuwa ya aiki? Murmushi yayi tare da dafa kansu yana fadin yauwa yarana, aiki Alhamdulillah, Allah de yayi maku albarka.

Sakin kan Farida Mama tayi suka tashi tare suna fadin Malan sannu da zuwa ya aikin? Yace lafiya lau Mamar yara, kema sannu da kula da gida, tace yauwa Malan ai kaine da sannu kaida kafita tun safe domin kanemo mana abinda zamuci.

Murmushi yayi tare da zama, mazan suka fara matsa mashi kafarshi, wannan al’adar da Mama ta koyamasu ne. Ruwa ta miko mashi duk da ba ita bace da girki, domin shi atsarinshi idan yadawo duk wadda yafara haduwa da ita yakan zauna sudan gaisa kafin ya nufi dakin me girki. Shiyasa Mama ta maida harabar gate din wajen zamansu inde akace maka yamma tayi, kuma alokacin ne kawai take zama.

Kuma yana karbar ruwa daga wajen duk wadda yasamu a aharabar gidan. Kallon Fahad yayi yace sarkin shara, kaide baka gajiya, Allah yabaka kaima wadan da zasuyi maka fiye da abinda kamun, Fahad yace amin Malan, muma Allah yakara mana karfin da zamu temakeka.

Sosai yake jin dadi aduk lokacin da yaran sukayi mashi irin wannan addu’ar, sabanin yaran Inne, ita bayan sannu da zuwa bata koyama yaranta yanda zasu shiga jikin mahaifinsu ba, asalima basu saba zama dashi ba, kowani abu suke bukata cikin dari dari suke tambaya.

Shikuma aganinshi itace takeson koya masu tsanarshi, kuma take janyesu daga jikin ‘Yan uwansu. Ita ko Mama a duk lokacin da Malan yake tare da yaranta tana kokarin sasu su kira su Faisal amma se Malan yahana, yakance ta kyalesu tunda haka Uwarsu ta koya masu.

Bayan sun gama gaisawa yatashi yanufi bangaren Inne, zuciyarshi tana me cike dajin haushi. Yana shiga ya sameta zaune daga ita se daurin gaba tana tsefe ma Fatima kai. Kallonshi tayi tana murmushi tace sannu da zuwa Malan.

Kallonta yayi cike da haushi yace duk yinin yau wai mutum yazauna dagashi se daurin gaba, kuma gobe monday amma se yanzu kike ma diyarki tsifa gashi yamma tayi. Ya tsina fuska yayi yace yauwa sannunki da zama ba kaya.

Faisal ne yafito daga falo, kusa dashi yaje yace sannu da zuwa Malan, murmushi yayi yace yauwa sannu sarkin yawo, ai nadauka yau ma baka gida? Tashi Faisal yayi yashige daki.

Fatima tace sannu dazuwa Malan, yace yauwa sarkin kazanta, yanzu ke se yanzu ake tsefe maki kanki saboda shiriritarki, ga Farida can ita kitso ma ake mata amma ke seyanzu ake tsefewa. Wai summa wanke kayansu? Inne tace yanzu nakeso idan nayi sallar magriba in wanke masu.

Tsaki yaja yana fadin yanzu duk kwana biyun nan be isa ace kin wanke masu kayansu kin goge ba se yau ne zakice wai zaki wanke? Idan kuma basu kawo wuta ba fa dame zaki goge masu? Ko dayake kinsaba samasu haka sutafi makaranta Kamar wadan da zasu tafi ALMAJIRANCI.

Dayake Farouk me tsafta ne, tuni ya wanke masu ya goge masu, yanzu haka wankin safuna yake masu, shi kuma Fahad yana share mani kofar falo na, amma ke kin hana Faisal yaje yasamu lada. Inne tace wallahi tun dazu nasashi yashare.

Malan yace kika sashi yatafi yawo de, ai kullum haka kike fada, kuma idan nadawo se in samu wani yana sharewa, wallahi Inne kinji tsoron Allah, duk abinda kika koyama yaranki dashi zasu tashi, kuma wata rana ke abun ze dama bani ba, domin ni Allah yabani wasu.

Da’ace su kadai gareni shine zanshiga damuwa. Mutum yadawo daga aiki amma bakisan ki kawo mashi ruwan sha ba, kima iya tashi kimatso kusa dani ya gagara, ko dayake ba laifinki bane, kema kinajin kunyar daurin gaban da kikayi.

Haba Inne, sekace ba mace ba, kullum se nayi maki korafi akan wannan daurin gaban, to bari kiji, wallahi daga yau idan nakara shigowa na sameki a haka wallahi ranki seya baci. Bantaba nuna maki fushina akan wannan daurin gaban ba shiyasa kika kasa denawa.

To kowane lokaci idan naga dama zandawo, kuma idan na sameki ahaka nida kene. Shigewa falonshi yayi ta kofar da take bangarenta domin yayi alwala yatafi masallaci.

Yana fitowa yasamu su Farouk suna jiranshi abakin kofa, murmushi yayi yakama hannunsu suka nufi masallaci, sam be kula da Faisal da yake cikin masallacin ba, domin shi ya saba yana ganin lokacin sallah yayi yake tafiya masallaci, kuma ana sallamewa yake dawowarshi gida.

Amma kullum Malan cikin fada yake mashi wai bayason zuwa masallaci, kasancewar Faisal bame son magana bane yasa baya iya musama Malan duk abinda yace sede yabashi hakuri ya wuce. Su Fahad kuwa basa taba tafiya masallaci se idan Malan yana gida, kuma kullum se sun jirashi koda antada sallah, kuma betaba cewa surika tafiya ba idan sunga an tada, saboda yanajin dadi yaga yajero da yaranshi sun nufi masallaci.

Tagumi Inne tayi hawaye suna fita daga idonta, tabbas tana cikin tsaka me wuya, taya zata gyara wannan matsalar da take fuskanta? Tasan sarai batason saka kaya, amma meyasa yake ganin laifinta? Yanzu ba lokacin soyayya bane ita da ta aje yara har 2.

Lokacin kula da yaranta ne, meyasa Malan baze gane hakan ba? Shiyafiso kullum seyaga yaranta sunyi abu agabanshi sannan zeyarda sunayi? Ita kuma bataso tayi gasa da Mama, domin yaranta ne sukeyin haka. Goge idonta tayi tace inde nice daga yau nadena zama da daurin gaba, amma yarana bazasu rika aikin ganin ido ba.

Leave a Comment

error: Content is protected !!