Hausa Novels

Daga Suna Hausa Novel

Daga Suna Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

_*DAGA SUNA*_

 

 

_Alƙalamin_

 

*Fateema Muhammad*

 

 

*SADAUKARWA*

 

_Na sadaukar da wannan littafi dukan sa ga Anty na Zainab Muhammad (Indian Girl) Allah ya tsare min ke sharrin maƙiya macen kwarai mai halin girma ga girmama mutane_

 

 

 

*GARGAƊI*

 

_Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ta kowace siga ba tare da izinina ba duk wanda yai min haka na barshi da Allah_

 

 

*NOTE*

 

_Wannan labari ƙirƙirarran labari ne wanda zai zo muku a duk yadda aka tsara dan haka dan Allah wanda ya san zai zage ni karya karanta min littafi dan Allah_

 

 

 

*Page 1&2*

 

__________________Cikin bacci taji wani irin ciwon mara da baya mai tsanani wanda yasa tai saurin farkawa daga baccin tana dafe marar.

 

“Inna lillahi wa inna ilaihirraju’un! wayyo Allah marata baya na zan mutu”

 

Shine abinda ta faɗa hawaye na zubowa daga idanunta.

 

A hankali ta samu ta sakko daga kan gadon tana runtse idanu.

 

“Yaya Isma’il dan Allah ka tashi zan mutu!”

 

Ta faɗa tana tashin mijinta dake kwance a kan gadon.

 

 

A hankali Isma’il ya buɗe idanunsa kafin yai saurin miƙewa ya sakko daga kan gadon.

 

“Zainab lafiya? Me yake damunki? Ko haihuwar ce?”

 

Duk ya jero mata waɗannan tambayoyin.

 

Zainab ta runtse ido wasu zafafan hawaye na zubo mata.

 

Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta

 

Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta

Ta ce”Nima ban sani ba Yaya amma ji nake kamar zan mutu”

 

Cikin ruɗewa Ya ce”Ok, sorry bari na fito da mota muje asibiti”

 

Bata iya magana ba sakamakon wani irin hautsinawa da cikinta yai.

 

Isma’il shima bai jira amsawar tata ba ganin halin da take ciki da sauri ya fice bayan ya ɗauki key ɗin mota.

 

Bayan fitarsa ciwo ya turnuƴe Zainab ta rasa yadda za tai aza ta isheta.

 

Ji tai wani irin kashi ya danno mata gashi ba zata iya zuwa toilet ba dan haka kawai ta daddage ta saki nishi, take yaro ya faɗo kafin ta gama jin wahalar wani ya biyo baya.

 

Wata wahalalliyar ajiyar zuciya ta sauke tana runtse ido.

 

Isma’il ne ya danno ƙofa tare da nufo inda take yana.

 

Ce wa”Bari muje asibi…”

 

Bai ƴarasa maganar ba yaga yaran kwance a ƙasa cikin jini ga mahaifar su a kusa da su.

 

Da sauri ya durƙusa ya ɗauki yara ba tare da ya dubi suna cikin ƙazanta ba ya rungume su yana hawaye wata irin ƙaunarsu na narkar da zuciyarsa.

 

“Sannu Zee kinji Allah ya baki lafiya nagode sosai da wannan kyauta da ubangiji yai mana sannan nagode miki”

 

Ɗan murmushi kawai Zainab tai tana kallonsa shi da yaran.

 

Bayan ta ɗan samu ta dawo hayyacinta nan suka gyara yaran itama ta gyara kanta sannan ta koma kan gado ta kwanta domin bacci take ji.

 

Isma’il da yaran ke hannunsa ya ƴaraso inda take yana, Ce wa”Zee sorry tashi ki ba su nono su sha saboda kin san ance ana so da an haifi yara a ba su nono saboda yana da amfani”

 

 

Ɗan ya tsina fuska Zainab tayi, Ta ce”Nifa gaskiya Yaya Isma’il bacci naks ji”

 

“Haƙuri zaki ki ɗan basu kin san an ce sinadari ne”

 

Isma’il ya faɗa yana ajiye yaran a gabanta.

 

Tashi zaune tai tana zumɓuro baki, Ta ce”Nifa Yaya Isma’il babu ruwa a nonon nan ka san wasu ba daga haihuwa suke samun ruwan nono ba”

 

Isma’il ya zauna bakin gadon kusa da ita yana, Ce wa”Eh na san da haka amma ki ba su haka su tsotsa”

 

“Ni gaskiya ba zan sa musu nono na su jamin ba tunda nace maka babu ruwa a ciki””

 

 

Zainab ta faɗa tana ƙoƴarin kwanciya.

 

Da sauri Isma’il ya riƙe hannunta yana, Ce wa”Ok bari bari na duba na gani”

 

Hannu yasa a cikin rigar tata ya fito da nono guda ɗaya ya kama kan ya matsa ɗan ƙara ta saki take ruwan nonon yai tsartuwa.

 

 

“Yawwa kinga da ruwa a ciki tai maka musu”

 

Ya faɗa yana ɗaukan jaririn ɗaya yana zaunar da shi a kan cinyarta yana sa masa nonon a baki.

 

Ai kuwa yaron ya cabka dake dama da yunwarsu suka zo duniyar…

 

 

 

*Comments da Sharhi*

 

 

*Shares saboda Allah*



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Daga Suna Hausa Novel]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!