Dakika Biyar Hausa Novels Complete
[24/10, 9:33 am] +234 803 800 7509: 🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐
*DAƘIƘA BIYAR*
🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai*
_3_
*Garabasa , garabasa, 😁🥰, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰*
Farar fuskarta dake d’auke da kwontacen gashi a gaban goshinta, wanda lafcecen hijabinta bai hana su bayyana ba ne ke d’aukan jajaja, kumatunta na neman kumbura lokaci daya ta sake duban fuskarsa, a sanyaye ainun ta ce” Motar wa ka samu yau kuma?”
Goshinsa ya dafe da hannunsa yana furta” Oh shiiit, flowrs wai ba zaki shigo din bane sai na yi fushi na yi tafiyata? Why kike min irin haka ne, sai kace wani bakonki ko wanda zai maki lahani? Ke kin san ni ba mugunki bane, in kuma yanzu tsorona kike yi fine, bara na tafi kawai.”
Zuciyarta ce ta ji ta buga, zata iya irga mutanen da bata had’a b’acin ransu da kowa a duniya, idan har ta ga alamun b’acin rai a fuskarsu sai inda k’arfinta ya k’are, bale ace itace silar b’acin ran?, Ko kusa ba zata iya yarda da hakan ba.
A hankali ta daka hannunta mai d’auke da awarwaraye na roba irin masu kyalin nan kwaya biyu bak’ak’e sidik ta bud’e motar ta shiga ta zauna ta rufo ta juyo zata sake tambayarsa a inda ya samo mota, bayan ta san bashi da ita ta ganshi daf da ita, idan nace daf da ita ina nufin kusancin da take iya shakar numfashinsa ya kuma shaki nata.
Da sauri ta ja baya, tana doka bayanta da jikin madubin motar, hannunta daya kuwa tana kokarin ture shi ta hanyar dorawa a saman fuskarsa ta tura muryarta a dan dage ta ce” Subahanalah meye haka kuma?”
Fuskarsa dake dauke da walwala ce ta yi kici kicin , ya saka hannunsa ya rike nata yana kallonta ya ce” Me kike yi haka ne Flowers, ban gane menene haka ba, wani abu zan maku ne kamar kin ga dodo daga matsowa daf da ke dan na ji wannan turaran mai kanshi kuma yaya sunnansa shikenan sai ki wani zabura kammar kin ga dodo? Haba dan Allah, idan kina min irin haka sai na ji hankalina na tashi, sai na yi tunanin sam baki yarda da ni ba, sai na ringa hasaso kamar tsorona kike yi, ko kina min kallon dan iska, bayan kin san ni da zuciya daya nake sonki, a kan sonki ina iya rasa raina, burina aurenki, yau koda jikinki na taba nawa ne, kowa ya sani mutane ne kawai ba’a tara suka sheda ba, wanda nake tunanin soon zamu kai ga ci, da zarar na gama shafe bangarena na gidanmu, ke kin san a kanki na bar yan mata, bana kula kowace, kin san akoy yan matan dake kawo min kansu na so su, ama na ja na tirje ni sai ke, ama sai ki ringa wani abu baya baya kamar wani wanda zan maki Fyade?”
Cikin dabara ta janye hannunta, tana mayar da shi cikin hijabinta gaba daya, fuskarta a matukar raunane ta ce” Ba haka bane Khalb, kai ka san nima ina sonka, ka san ba zan taba duban waninka ba, ama kuma a kulun ina fada maka, ka daina nuna zalamarka a kan jikina, bana so, Abanmu na fadi cewa bai halata namijin da ba huruminki ba ya ringa taba kofa hannunki ne, haramun ne khalb, kuma fa ka san lamari na shedan.”
Nan da nan ya yi takwaf takwaf da fuskarsa, ya cire dubansa ya maida bakin layi, a kausashe ya ce” shikenan, tunda ba zaki taba yarda da ni ba shikenan, ama ki sani so fa ba kiyaya bane, ke kin san irin dogon wajen da na ratso na zo, kin kuma san in ba so ba, babu abinda zai kawo ni da wannan tsohon daren anguwar nan, na zo zaki saka min da haka dan kawai na ji kanshi mai dadi a jikinki na so matsowa dan na ji shi da kyau, ki yi hakuri, ki sauka ki koma gida, nina san ni kadai nake wahala a sonki, tunda na ganki ya wadatar, Allah ya bamu alkhairi.”
Gaba daya sai ta ji kamar yana neman dakatar da numfashinta ne, a hankali ta fitar da hannayenta tana murzasu hankalinta a tashe ta ce” Dan Allah, ka yi hakuri, ka yi hakuri, ni fa ba nufina kennan ba, haba wani maganar zaka cuceni kuma, da kana cutana ai da ka yi ba yau ba…”
“To me kike nufi dan kawai na nufo fuskarki zaki wani zabura kina ture ni? Ko sun maki wani abu a gidan cen naku da basa kaunarki?” Ya fada a wani zazafan shi a dole ga wanda ya isa da ita.
Da sauri ta girgiza kanta, tana auna maganarsa wai wani akai mata a gidansu da ba’a sonta, a saninta sandiyar haduwarta da shi ta fito daga gidansu wani lokaci da mahaifiyarta ta wulakantata, tana kuka suka hade, hi kuma zai je anguwa da yama, tana kuka ta rasa inda zata nufa ya ringa binta yana yi mata magana har sai da ta dakata daga saurin da take, tana kallonsa ta fashe da kuka, domin inda zata fadi damuwarta take nema a lokacin, a ranar ne ya ringa nuna damuwarsa har sai da ta sanar masa daga gidansu ne, irin rudanin zuciya ya sakata cewa ba’a sonta a gidansu, dan shine kadai amsar da ta zo bakinta, domin ba zata iya dubansa ta sanar masa mahaifiyarta ce bata sonta ba.
A hankali ta sake girgiza kai, muryarya na rawa ainun ta budi baki zata yi magana wayarsa ta dauki ringa.
Kamar yadfa ya saba sai ya kawar da screen din daga fuskarta ko zai dauki kira haka ne yauma, sai da ya kawar da wayar sosai ya duba mai kiran nasa sannan ya daga kiran, sai dai ya yi mantuwa da Bluetooth din ya yi connectng da motar yana shan kidan Davido , hakan na nufin abinda zai fito daga wayar zai shiga kunnen kowa ne ba iya shi ba
“Hello?, Hello abokina ina ji salama alaikum” ya fada yana kai wayar kunnensa.
“Wa’alaika salam, kai wai yayane tun dazu muke jiranka mu wuce ka wani shanya mu a nan, kar ka ce min ka je wajen wannan banzar yarinyar ne mana!” Abokin nasa ya fada hadi da dan jan tsaki, hakan ya saka shi dan zabura yana waigowa wajenta dan sai a lokacin ya shiga neman wajen da zai datse hakan, ama bai sani ba, hasalima hadawarma sai da aka hada masa, tukin motarma ya iya mota ne irin iyawar nan ta garari , domin a hannun abokansa ya’yan masu da shi yake warta yana dannawa har aka dace.
A dan hargitse ya bude motar ya fice, sai dai bai yi nisa da motar ba kasa kasa sosai ya ce” Kai me yasa baka da hankali ne, amsa amon motar fa a bayane yake kake magana tana jinka meye haka?”
Abokin nasa ya ja tsaki, wanda maganar tasa ne kawai take iya ji, bata iya jin me ma’awiyan yake fada, dan ya rufo motar ama yana daf da motar
Da yannayi na rashin kunya ya ce” Ka katse mana ai laifinka ne malan zaka wani shanya manyan babs ka je wajen da ko lebe ba za’a barka ka darza ba kamar wani an fika tsatson kirki bayan mun san……………….”
A lokacin ne kuma maganar ta dauke, dan ba shiri ya yi gaba da sauri yana amsa kiran.
A hankali Ta bude nanauyun idannuwanta da suka cenza launi suka yi wani irin ja ta sake zubawa a kan hanyar da ya mika yana amsa wayar
Wani irin nauyi jikinta ya dauka, nauyi mai zafin gaske, tamkar yau kunnayenta suka fara jiyo mata magana irin ta wulakanci da zagin nasabarta…..ko dan wannan ya fito daga bangaren wanda ta riga ta aminta cewa mutuwa ce kawai zata iya rabata da shi, sannan babu ɗa namijin da zai iya sonta ya kare hakinta irinsa?
Da kyar ta iya bude motar, bayan ta kasheta ta bar masa makulin a jiki, dan kar wani ya zo ya gane ba kowa ya yi gaba da ita, ta rufe ta shiga tafia jiki a sanyaye tamkar zata kifa kasa dan ciwon da zuciyarta ke yi
Tana karasowa kusa fa gidan abokin hadin bakin nata yana tsaye jikinsa sai bari yake, adu’arsa daya kar Oga ya fito a lokacin da zata dawo, fatansa daya ta dawo ta shige gidan nan tun kafin a san bata cikinsa,
Magana yake yi mata jikinsa na rawa yana nuna mata maza ta shige, Oga fa na nan, hakan ya sa gabanta sake yankewa ya fadi, duda bata gane wane a cikin ogannin nasu ba, abinda ta sani shine su dukka ogannin nasu babu daya da yake wasa da su, daga wansa zai iya saka bulala ya zane masu jiki tas, sai wanda kallonsa ke fasara idan ka yarda ya damkeka sai dai wani ba kai ba
Hakan ya sa ta dan daga kafa, sannan ta shanye abinda ke ranta ta shige gidan a darare ta bi ta cikin shukoki har ta samu ta isa wajen babar bishiyar da take zama lokuta da dama , a lokacin ta ja ta tsaya tana jin tamkar fitsari zai zubo mata sakamakon jin an ce WAYE?
Jikinta ne ya dauki rawa, zufa na neman karyo mata, lokaci daya kuma ta juyo wajen da aka daleta da hasken fitila dan koma waye ya gane wacece din da yake son sani.
A hankali ya sake zuba mata ido, tun daga yannayin tsayuwarta, gumin da take tsatsafawa, idannuwanta dake ta kasa sunna sama, fuskarta da ta d’auki ka, har zuwa hannayenta da ta damk’e hijabinta take wani abu kamar mai jin kashi.
Sake daleta ya yi da hasken nan yana kallonta , muryarsa a dake ya ce” Fitsari kike ji ne?”
Tambayar tasa ta yanzu ta sakata gane wanene a wajen
Shikenan, ashe ogan da ake nufi yana gidan kennan? Ai su sun zatama an tada shi daga garin an maida shi wani garin har sunna murna da samun yanci a cikin duniyarsu, sai gashi yai ta yi gamo da muryarsa a irin wannan lokacin da ta kwaso tarin tashin hankalinta.
Kai ta sada, hawaye ya shiga bin kumatunta, hawayen da ita kanta bata san tana iya zubat da su ba, batama san a kan me zata zubar da su a nan a gaban wannan mutumen da ta san yana cikin masu kyankyaminta…..to wannan tambaya tashi batama san ta mecece ba sam.
A hankali ta sake sada kanta sosai, ta kasa bashi amsa.
Baki ya tabe ya kashe fitilar ya mayar aljihunsa sannan ya yi gaba wajen motarsa ya shige ya tayar ya shiga juyar da ita dan barin gidan.
Da sauri ta dage hijabinta ta kalkala da gudu ta bi ta cen baya , hakan ya saka shi take birki ya zubawa hanyar ido, sannan ya sake dawo da yannayinta a cikin idannuwansa.
A hankali ya ji kansa ya sarra masa, sanadiyar wani tunani da ya shigo cikin kwakwaluwarsa.
Take motar ya yi ya fice a gidan da gudun gaske dan tuni aka bude masa get.
Cikin sand’a ta lek’a falo, gabanta ne ya sake kwonci kwonci ya fad’i sakamakon hangi Hajia na falo bata hau sama ba, duda baban fargabarta ace hajiar ta hau saman ta bi dakunnansu ita bata sameta a nata ba, gaskiya ba zata kuma yarda ta fita a irin wannan lokacin ba, haka kawai salon ya sakata a uku , bama zata kuma fita inda yake ba, domin ba zata zauna rayuwarta a gida a tsangwameta a tare da shi a tsangwameta ba.
Ta jima a tsaye a wajen nan tana addu’a tana zufa, har dai Hajia ta mike ta kakashe fitilu da sauransu sannan ta sahiga hawa sama da carbinta a hannunta da gilashinta na karrin karfin gani.
Da sanda take dan bin bayanta har ta shige dakin farko, ita kuma da sauri ta kama kofarta ta bude ta shige cikin hanzari ta rufo ta cire hijabinta ta yi wurgi da shi cen san bed, tana kiciniyar cire rigar dake jikinta ta ji an bud’e k’ofar an shigo lokaci daya ta idasa sakarwa ta nemi samin fitsarin mararta har abinda ke d’aure da gashin kanta wato Ribom ya fad’o k’as ya daki k’afafuwanta.
K’afafuwan nata Hajia ta bi da kallo, sannan ta sake d’auko kallon ta dawo da shi har zuwa wajen fuskarta.
Tsare fuskarta ta yi da kallo, hakan ya sa ta sake d’aukan yanayi irin na wanda ta d’auka a d’azu da take gaban wancen mutunen.
“Ke zo nan!” Hajia ta fad’a da d’an k’arfi tana nuna mata gabanta bayan ta nunata.
*Alhamdulillah.*
[24/10, 9:33 am] +234 803 800 7509: 🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐
*DAƘIƘA BIYAR*
🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai*
_4_
*Garabasa , garabasa, 😁🥰, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰*
“Ke! Zo nan.” Hajia ta fad’a a dake da d’an k’arfi, sannan tana nuna gabanta, zabure ta duka ta d’auko ribom d’inta da ya fadi ta shiga daura shi jikinta na bari tamkar zata kifa ta nufo wajen hajiar ta nemi dan dukawa dan ba zata tsaya mata k’erere ba, hajia bata d’aukan wannan rainin.
Damkar hannunta hajia ta yi ta janyota sosai ta shiga dube dube a jikinta har zuwa sket dinta da ya saketa sosai bai rike jikinta ba
Sake zuba mata ido ta yi sannan ta saki b’oyayyar yar ajiyar zuciya a hankali ta ce” Kuka kika yi ne? Me kike yi har karfe goma sha daya na dare ke neman yi baki kwonta kin yi barci ba?”
Bakinta dake bari kad’an ta bud’e a hankali ta ce” Mamah,dama, sallah zan yi ne.”
Fuskarta ta sake kurewa da ido, sai kuma ta ja numfashi ta shigo da kyau dakin ta zauna bakin gado ta ce” Je ki yi alwallar ki fito.”
Da sauri ta juya ta shige tana zarro ido had’i da dafe gaban kirjinta, da kyar ta iya dauro alwallar ta fito ta nufi salayar da Hajia ta nuna mata still tana binta da kallo.
Hijabinta ta saka ta haye salayar ta tayar da sallah , a hankali a hankali jikinta dake bari ya daina har ta zurfafa ta yi raka’a biyu kadai ta salame ta shiga danna yan yatsunta kanta a kasa.
Hajia ta bud’e baki a nutse bayan ta ga ta gama sallar ta ce” Shafa’i da wuturi ne kika yi, ko nafila ne tun yanzu?”
A hankali ta juyo tana kallonya, a sanyaye ta ce” Nafila ne Mamah ”
Hajia ta gyada kanta ta juya tana sake kallon kofarta ta ce” An fi son nafila idan dare ya tsala, a lokacin da babu hayaniya babu yawan kai kawo, a irin lokacin da wasu bayin ke barci kai ka kokarta ka mike ka gabatar, ka nemi lahira sannan ka nemi duniya, a irin wannan lokacin Allah ya fi amsar addu’ar bayinsa kin ji Zahra?”
Kai ta gyada tana sadda kanta
Hajia ta dan yi jimmmm ta ci gaba fa fadin” Ba zan taba gajiyawa da tunatar da ku baban abu mafi mahimmanci a rayuwar y’a mace ba, shine mutunci, Zahrah ki kasance cikin bayin da zasu rike mutuncinsu domin Allah, ko me kike ciki ki ringa fadawa Allah sannan kina kokarin kiyaye hakokin adinninki, ke mace ce, kina da daraja sosai, Allah ya yi ki mai rauni sai dai ya dora maki aiki mafi daraja a duniya, shine haihuwa da tarbiyantarda, idan ka tuna zaka haihu wata rana, zaka bada tarbiya sai ka sake kame kanka, ka ci gaba da kare mutuncin kanka, dukkan abinda sauran dunniya zata dubeka kuwa ko menene ka musu uzuri, mafi wawan cikinsu shine wanda ya shagala har ya manta cewa Allah baya kare halitar bawa da daina dora masa jarabawa har sai an saka shi a cikin kabarinsa, FATIMAH na san kina fuskantar abubuwa fiye da tunanin kwakwaluwarki, ki ci gaba fa addu’a ki daina kuka sannan ki rike amanarmu mu iyayenki, ki yi mana adalci, ki yi kokarin saka mana ta hanyar kare mutuncin kanki kin ji?”
Wani irin rauni ne ya daskare zuciyarta, da kyar ta iya amsawa Mamah har ta tashi ta fita ta rufo mata dakin tana sake kallon yannayin kofarta da tunanin lalle da wahala idan ba fita ta yi ba, sai dai tunanin ta ina ? Ya dakata kawar da wannan tunanin ta ci gaba da ziyartar sauran dakunan yan matanta, su uku ne dama sai ZAHRA ta hudu, a cikinsu babu wace ta yi barci, wayama suke yi sai Ummi auta dake karatu dan tana fa exam gobe, dukansu kuma da sun ji alamun motsin hajiar sukan boye abinda suke yi ne, sarai tana fahimta, itama cikin nata hikimar take ta yiwa tufkar hanci da kuma tsayuwar dare tana rokon Allah ya kare mata, dan abu ne ya riga ya zama gama duniya, ko baka ba yaron waya ba za’a bashi a waje, Docter dai ne baya son zance, ba’a yi masa zance, idan ka tsaya da saurayi an kusa aurenku ne kawai, shima ba wai da dare ba, no, zaka zo ne da yama ku gaisa ka tafi, sauran maganar kwa yi a waya, shima ba wai masifafiyar wayar nan ba
Fatima Zahra kuwa, Mamah na barin dakinta ta samu kanta da fashewa da kuka har ta kasa zama da kyau sai da ta kwonta tana nade jikinta a cikin hijabi
Innalilahi wa inna ilaihi raj’une, shin me yake damun kanta ne? Me yake faruwa da ita ne? Ko dai dan abin ya taba nasabarta ne ya sa yake bibiyarta? Yaya aka yi yai har Ma’awiyah ya ci galabar sakata fitowa a irin wannan lokacin daga gidan shehin malamin da ake koyo da tarbiyar gidansa ta tarda shi? Da ace ya daneta a cikin motar nan ya yi mata wata muguntar kuwa me zata dubi wannan matar mai daraja ta ce mata?, Yaya zata ce da matar da ta rungumeta bayan mahaifiyarta ta tsangwameta ne? Ita ta san idan ta dauko abin kunya Allahn da ya haliceta da kuma Hajia sai Abah sunne wa’inda zata ji tsoron haduwa da su, shin menene wannan masifar dake bibiyarta ne? Ita da kanta ta san tana yiwa Ma’awiyah son da ya dace ta daidaita ko dan rayuwa, shin idan har ya gujeta yaya zata yi kennan? Yanzu haka tana tsintar magangannun da basu yi mata ba sam, idan abu ya sake rikicewa yaya kennan??
Da kyar ta iya samun barci, shima mai wartar nan ne mai wahala bayan ta yiwa kanta alkawarin duk rintsi ba zata kuma fita da dare haka ba, gwarama su rinha haduwar yammarsu kamar yadda suka saba in har ta ci gaba da kulashin wai!
_________________________________
A gajiye ya karaso gidansa, hakan ya sa bai leka bangaren matarsa ba, duda ya san sunna da baki yan uwanta da suke nan yau kwana hudu kennan
Wanka ya yi, ya saka jalabiya a saman karamin wando sannan ya fito dan zuwa wajen diner, domin shi a rayuwa baya wasa da lamarin cikinsa, sai kuma ya yi Sa’a ya fado kan wace take iya yinta a harkar girki, gaskiya bata da laifi a lamarin sarafa hannu, wannan ya sa yake girmama girkinta sosai
Yana zama ya shiga bubudewa hadi da zubawa abincin ido yana nazarin yau kuma wani sabon salon aka girka masa ne?
“Barka da zuwa mijin Manal” ta fada a lokacin da ta shigo take karasowa a hankali sakamakon ciwon da mararta ke yi tamkar zata zage gida biyu, kai lalle ta sarawa maganin matan nan na wajen yar uwarta, lahauli da ta sani da bata sha shi da wuri ba walahi, gayanan yana neman fasa mata mararta
Dan murmushi ya yi yana zubawa , bai ce komai ba har ta ja kujera ta zauna tana sake kashe idannuwanta da salon kisa irin tamu ta mata ta ce” Yaya gajiya, yaya aiki da fama da mu?”
Dan tsai ya yi yana kallonta,….tana acting like mai rikaken wayon nan, ….. Lokuta da yawa takan kwatanta irin halayan nan idan tana cikin bukatar wani abu mai girma ko tana son tafia mai tsayi……., Abin ya kasun masa gida biyu, na farko ya yi tunanin kirsa ce irin ta mata…….sai daga baya ya fahimci idan ta yi haka tana tunanin cin galaba dan ta girme shi da shekara biyu……, Shi kuma yana matukar jin dadin zuba mata ido idan tana irin haka, dan yana son hakan……ba dan komai ba sai dan karra karantar *WOMEN* da yake yi rana zuwa rana daga wajenta
“Oga, wai dog din nan bayar da shi zaka yi da gaske? Bayan kana son sa sosai?” Ta sake fada cikin yannayi na tsantsar kisa, da layewa abu dan cinma wani abin irin namu na mata
“Yeah” ya bata amsa a takaice yana sake daukan abincin da ya masa dadin dandano a bakinsa ya sake kaiwa bakinsa ya ci…, Wato zai iya cewa zab’insa yana tafe daidai da tsamaninsa, ko yace baban kokarin zabinsa na kayatar da shi daidai misali…….., Ta kasance wace ta ci gasar iya sarafa abinci……., Tana daya daga cikin manyan masu yiwa yan mata nasiha………………, Ba laifi tana yin iya kokarinta dan tafiyarsu ta yi karko, kuma yana yaba hakan
Sake sauke dan ajiyar zuciya ta yi, ta ce” Gani na yi du cikin karnukan nan babu wanda yake da kishi da iya ba ababen kiwon nan tsaro irinsa, ba’a isa a tunkari wajen kajin cen manya ba fa, sosai yake bada tsaro a wajajen nan, sauran sunna bin bayansa ne……”
Ruwa, marrar sanyi ya sha, a hankali ya lumshe idannuwansa yana adu’ar godiya ga Allah, hannunsa daya kuwa a saman shafafen cikinsa , tamkar ba a ciki aka zuba abincin ba, asalima idan kana kallon cikin sai ka dauka baya wani ci, dan gida gidan nan na masu gymn ne da shi, dama su in dai zasu rike shi dole sai da abinci mai gina jiki sosai, in ba haka ba kuwa akoy matsala
Manyan idannuwansa ya dauka ya sake dorawa a kanta, yanna kula da ita tunda ta shigo tana yawan dan tsamure fuska, sai kuma ta yi gagawar saki in ta kula zai dubeta
A hankali ya ce” Kin sha maganinki kuwa?”
Yannayin da ta shigo da shi na tabaci da sannin abinda take yi ne ya so kubuce mata, sakamakon tuna mata da ya yi a yanzu haka a irin zaman da suke zama ne dan an yi da wajewa ya buga ya buga itama ta ja ta ja cewar ta yarda ba maganar haihuwar, ba dan komai ba dai dan a lokacin aurensu basu je suka yi gwaji ba, sai a bayan aurensu aka tabatar da jinninsu irin jinnin nan ne mai dauke da cutar da idan suka haihu tare yaron na iya rayuwa cikin wahala, eh lalle abu ne na gwaje gwajen zamani, sai dai gaskiyar itace hakane!, Yaron na iya zuwa duniya da cutar nan mai karfi watau cutar kashi, ita ke dauke da mai karfin watau SS, shi tasa sunnan yana da ita ne kawai , kasancewarsa mutun mai kokari da sport da komai, sai ya zo masa da sauki, inma ba ya yi niyar tunawa ba akan mance cewar yana dauke da ciwon, damuwar daya ce idan har suka hadu suka haihu zasu samu yaro mai ciwon mai karfi, yawanci za’a zo a yo ta wahalar rayuwa da yaron, astagfrulah lamari ne na ubangiji domin da yawa sun take, wasun kuwa haka za’a yi ta fama yau da gobe, yau da gobe sai hamdallah, wannan abu da aka gani ya saka shi shiga tashin hankali a lokacin da ta taɓa yin wani bari, saima suka tsaya a matsaya guda cewar zasu tafi a haka….watau babu haihuwar, domin ya yi ya yi ya sawake mata ta nuna yanzu ta ga wajen zama, tana daukan magani ne na hanna daukan ciki, wanda ba kulun ba dan wani sa’in saima ta manta da shi kwata kwata, bama irin yanzu da yayarta ke cewa a kan me zasu yi haka? Ta tabata Docter Ahmad bashi da labari, da ya sanar masu ai komai na Allah ne, itana ta san mijinta bashi da wajen gannin rauni irin yara, shi yasa ya zabi kar ya haihun a haka.
A sanyaye ta ce” Na sha”
Dan tsai ya yi, sai kuma ya kawar da maganar ta hanyar fadin” Auren su Aba karami ya tashi……”
Nan take yannayin fuskarta ya so cenzawa, da kyar ta iya kokarin kawar da maganar tana fadin” Oh wauh har auren ya tashi? Masha Allah kace bana akoy aurw aure, yan matan uku ne ko?”
Da idannuwansa kawai ya amsata,
Ita kuma ta ci gaba da magana ta ce” Masha Allah, bana muna da shagulgula, plz mijina kar ka saka rana daya da na gidan aunty, dan abin zai cakule min , yanzu haka kai kawai take jira da maganar kayan auren ƴaƴan nata ta koma a ci gaba da shirye shirye, ina gannin a cen garin su mahaifinta za’a yi daurin auren”
Dan tsai ya sake yi da abinda yake yi ya sake dubanta, …….ita fa haka take, da ake cewa mace na daidaita lokutan tambayar abu daga wajen mijinta, ko ta kasance mai ragewa mijinta wani kashe kashen….., Noh, banda tashi matar, hajiar gidansa bata da wannan tsarin a cikin tsarin rayuwarta, yana gannin irin wannan taruwa ta yan uwanta ya san da walaki, ama bai yi tunanin kayan dakin ƴaƴan yayarta ne zai yi ba, tunda a sanninsa ai da ubansu, ko dan bata gidansa ne za’a yi abu irin na gadarar nan,a nuna masa shine talaka ba’a son nasa?…….. Lalle da sun fado babu nauyi, domin ba zai yiwa ƴaƴan kadajen gidan aure ba, domin mahaifinsu da rai, yana da halin haka, ya kuma isa da gidansa, ba zai taba zamowa mai kama masu wajen yada wasu manufofinsu na jin dadi ba
“Ba zan yi gadaje ba, ba kuma zaki kayade min abinda ya dace na yi ba” daga wannan ya mike ya sake yin samansa dan hutawa
Cikinta sai da ya nemi hautsinewa, idan aka hada da ciwon da yake yi mata, ga kuma wannan magana mai son saka bawa hauka sai ta nemi zubewa a kasa daga saman kujerar bata shirye ba
A zabure ta mike tsaye hankalinta na neman dugunzuma ya tashi dan bata yi tunanin haka ba ko kadan
Da sasarfa take taka matatakalar, zufa na keto mata, cikinta na sake rikice mata har ta haye ta tura kofar dakinsa a sanyaye dan ba zata taba yarda ta shiga da girgirwar kai ko isa ba,
Yana sanye da kayan barci ne riga da dogon wando, yana shirin kwonciya ya juyo ya zuba mata idannuwansa a fuskarta
A dan birkice ta so fara magana tana dan dudukewa, sai kuma ta dafe cikinta a rikice ta ce”…
*Alhamdulillah.*
[24/10, 9:33 am] +234 803 800 7509: 🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐
*DAƘIƘA BIYAR*
🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai*
_1_
*Garabasa , garabasa, 😁🥰, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰*
Su biyar ne a zagaye da shi, ko na ce a zazzaune suna kallon in da yake zaune saman kujera mai zaman mutum d’aya irin ta manyan office, hannayansa a cikin juna yana kallon takardar dake gabansa mai son saka shi daria, da kuma son saka shi amai.
A nutse ya d’auke idanuwansa ya d’ora a kan manyan ma’aikatan dake k’asa da shi su biyar cif, a cikinsu d’aya tak ne ya girma, hud’un nan harda wanda ya kai haihuwarsa , sai dai lamari na aikin gwamnati ya saka dole zasu yi masa biyayya a matsayinsa na babbansu.
Takardar ya turo gaban mai bi masa a girman kujera , sai kuma ya kalli wanda ya girma a haife, wanda suke kamanni irin na k’arfin jini, kana ganinsa gan’nin farko zaka iya kiransa da Ɗan uwansa. Hannunsa mai d’auke da agogo, k’irar kampanin *CHOPARD CARATS* wacce a k’iyasin kud’inta million ashirin da biyar ce Euro, <<the watch is so majestic, so elegant, so classy, so luxurious>> balle da ta hau saman tsintsiyar hannunsa mai d’auke da gashi mai ruwan maroon haka kad’an irin gargasar nan dake zaunawa a jikin wasu yaren, bama irin larabawa, fulani, buzaye, dai da sauransu.
Kamar zai yi furuci ne da goggagan turanci irin wanda a k’asar turawa kawai zaka iya jinsa, sai ko a TV, sai gashi ya bud’e bakinsa, da muryarsa mai tafiyar da yannayin halitar jikinsa, watau ELEGANY Voice, ROCK voice ya ce” Abin mamaki, a wannan takardar harda saka hannunka?”
A hankali wanda ya yi nuni ya yiwa maganar ya sadda kansa cike da jin nauyi, baki ya tab’e ya kalli sauran ma’aikatan, da yannayi na Expression din fuskarsa ya ce” Sorry fa, ban fad’i haka dan na raina maku ba, na yi mamaki ne a matsayinsa na jinin AHMAD SULAIMANE yana saka hannu a tab’argazar tabbatar tallafi wajen sake rugujewar tarbiyar y’a’yanmu a garin da ya riga ya rasa banban gurno na tarbiyyar wasu yaren, ta hanyar yin riko da al’adun wasu masu jan kunnayen da Ba da dabi’a!…”
Ya ajiye maganarsa hankali kwance, sannan ya bud’e computer da ya rufe sakamakon shigowarsu cikin gaggawa , tsari irin na wanda ya lak’anci abin, ya dadannata sannan ya rufe ya mik’a hannu ya d’auki rigar suit d’insa ya ratayata a tsintsiyar hannunsa, da d’ayan hannun kuwa ya sake gyara zaman yar k’aramar bindigarsa mai ruwan zeba ya lab’eta da kyau ya zagayo hankali kwomance da niyyar fita ya bar masu office d’in, idan ya so in sun gama sa rufe, wanda haka d’in ma magana ce mai girma ya dank’ara masu.
Da girmamawa sosai, Général ya dube shi,muryarsa a tausashe ya ce” MARÉCHAL, ka yi hakuri idan mun b’ata maka, ka san daga ina wannan order d’in ya zo, yau kusan sati biyu kenan ana jiran saka hannunka, ka sani, muma abin ba dad’i zai yi mana ba, tab’arb’arewar y’a’yanmu a cikin gari yana damunmu, balle an yi masu dalilin maida hankali da yi hankali kwonce suna da masu basu tsaro sai ya ya kennan? Sai dai ka san shi umarni umarni ne, kamar yadda kana bamu umarni babu ja ba tsayawa muke aikatawa.”
Idasa fitowar ya yi ya k’araso inda yake tsaye, sai da ya tsaya a gabansa ta yadda ya sake gannin tsayinsa da nasa ba d’aya ba, duda shekarun da ya bashi na haihuwa bai hanna shi nuna masa idan shi shekaru ya bashi, shi a takardar nan ce ya riga ya sha gabansa,
A dake,muryarsa na amsa amo mai k’arfin mak’ogwaro ya ce”SO WHAT?”
Da sauri General ya d’an ja baya ya d’ora hannunsa gaban goshinsa yana sara masa, da yar gaggawar maganarsa irin yadda yake yi ya furta” I’m sorry Sir!”
Hak’orinsa ya d’an dantse yana yi masu kallon k’asa k’asa…Gaba d’aya yanzun kowa ya zama baya son rigima, sai a ringa baya baya da masifa, bayan du jaraba dai sai dai a kashe ka, mutuwa kuwa ai kowama yi zai yi, shi bai ga abin tsoro a mutuwa ba gaskiya!
A kausashe yana dubansu ya ce” Ban ce ba zan saka hannu ba, but ina buk’atar lokaci dan na sake bin lungu, lungu na sake karantar haukan yan matan garin nan da kuma k’arfin decision d’in nan, idan na ga ba zan iya saka hannu ba kawai kunna iya zartar da aiki da ita a haka, dan babu d’an Adam d’in da zai saka ni yiwa kaina k’ofa a gidan wuta!”
Yana idasawa ya fice d’in ya barsu a nan, sakatariyarsa na ganin fitowarsa ta mik’e tana sara masa had’i da yi masa fatan sauka lafiya, dan ba zata ce masa mu kwana lafiya ba, kowani lokaci ana iya ganin dawowarsa, ya ga damar dare ya tsala ya zo ya fita da patrouille, ko kuma sai an sakankance ya zo ya fita da kansa bakin babbar hanyar TILABERY hanyar da yan ta’ada ke d’an gabatar da d’an sakin jikinsu dan morewa.
K’arar rufo k’ofar , sai da ya saka S FULANI rintse ido, domin kamar a kansa aka buga K’ofar, Attahir ne ya dira hannayensa a saman table din dake ajiye yana kallonsu ya ce” Kuma kun sani, ba zai tab’ a saka hannu a wannan takardar ba, kuma idan muka kai cen wajen yallaɓai babu yadda ya iya da shi, wannan abu ne na ra’ayi,yace baya ra’ayin bada tallafi a haka, bai dace mu ce zamu had’u mu zo mu same shi ba, yana bamu girmanmu, mun sani sarai yana girmamam furfurarmu, ya kamata mu iya kanmu, mu kiyaye haye masa, mu da kanmu dan bamu da karfin kiyawa a zauna lafiyar ne irin nasa, da na rantse maku ba zan saka hannuna a cikin rakardar ba yan mata karfin idan sunna so su yi yawo da pant a cikin gari ba, wai du wanda ya zage su, ko ya nunasu, balle ace ya taba su muna nan zamu kama mutun, mu aikawa alkali shi, a yanke masa hukunci mai tsanani, me kennan muke son yi? Bayan rikicewar al’umarmu ta yanzu, basa gidan Tiktok, basa gidan Instagram, basa nan basa cen, sunna yadd’a kalar tasu bad’alar ta hanyar cutar kansu da kansu a matsayin wayewa sai mu k’ara rik’e masu mara taf dan su baje kolin rashin da’arsu hankali kwonce? Sunnan K’ASAR MU K’ASAR MUSULMAI!, zamu yi abinda a *DAKIKA BIYAR* zamu halaka kawunnanmu, MARCHAL yana da damar k’iyawa, ya k’iya mu kaita hakanan ina rok’on ku.”
Wanda yake christan cikinsu , wato JOEL ne ya d’auki magana yana fadin” Ko mu Christian, ba zamu so irin tab’arb’arewar y’ayanmu ta yanzu ta nin’ninku ba, but kowa yana da zabin yadda zai tafiyar da rayuwarsa ai, mu a adininmu ba takura shi yasa adininmu ya fi dad’i sosai.”
Su dukansu hud’un kallonsa suke har ya dire ayarsa, ajiyar zuciya COMMANDANT AMIR AHMAD SULAIMANE ya yi yana dubansa shima, murmushi ya yi kawai yana girgiza kansa ya k’araso inda yake tsaye, hannunsa ya d’ora ya daka a gefen kafad’arsa kad’an ya ce” Ba’a halice mu dan mu zo mu ji dadin rayuwarmu ba!, A sanina, an halicemu ne dan mu bautawa wanda ya halicemu,……mu kuma ka ga yadda muke kallon namu adinin, kuma mun yarda da haka……, Kun ga ni fa ko a haka na yi iya yina, kyalenin nan da ya yi na rantse bai kyale ni ba, ina nan ina jiran sakamakona dan kar ku manta bayan boss dina a nan, yayana ne a gida!, Komai zai iya faruwa, magariba na shigowa zan je na samu jam’i sannan na wuce gida.”
Daga karshe dai kowa haka ya kama gabansa, abinda suka zo da shi din basu samu ba suka koma da takardar da nufin zasu kaita haka idan aka kwana biyu ya masu shiru, suma sun san abu ne mai wahala, yawanci abinda ya sa ake kai ruwa rana da shi kennan, inda yake da k’arfi daya ne tak, gurbin da yake kai a yanzu ba siyasa ce ta d’orashi ba, a buga a buga a yi k’asa, a yi sama sai dai a dawo a sasanta yadda za’a fahimci juna, ama ba dai a yi masa barazanar za’a cire shi daga kujerarsa idan bai yi biyaya ba, powernsa tana sama da ta mai gidansa, wanda siyasa ta d’ora a kujerarsa, dole zasu je a sannu dan su ci gaba da gaisawa koda hali na kujera ya juye da d’aya.
Sakatariyarsa na tsaye ne a kofar office din sai da kowa ya fito ta shiga ta sake duba komai yadda yake sannan ta rufo kofar ta koma bakin aikinta, dan ita ba zata tashi da wuri ba yau, akoy aiyukan da zata yi masu yawan gaske, mijintama yau ba zai sauka da wuri ba dan sun fita dauko wani mai laifi idan sun tashi sai su yi tafiyarsu gida tare.
________________
A hankali yake tukinsa, har ya k’arasa anguwar mahaifansa, wa’inda ya kwana biyu cif bai lek’o su ba, bai k’arasa gidan direct ba sai da ya biya ta wata majalisar samarin anguwa ya ajiye motarsa daga nesa kadan dan baya so ya karaso daf da su wani ya nemi guduwa, harka ce ta samari idan wane yana jin magana wane baya ji, sai hakuri da addu’a kawai, shi kuma yana shiga cikinsu ne dan a nan yana k’ara samun ilimi na matasanmu.
Saukarsa kawai suka gani a gabansu, hakan ya sa Yusuf mik’ewa tsaye a ba zata yana kallonsa, sai kuma ya koma da sauri da idanuwansa yana yiwa Bashir ido kan maganar da suke yi, lokaci d’aya kuma suka ringa yi masa sannu da zuwa kusan du aka nemi tashi a bashi abin zama.
Murmushi ya yi ya zauna saman kujera yana gyara zamansa da kyau ya kalli Yusuf, wanda shine uban dabar ya ce” Baba zan samu shayin kuwa?”
Yusuf ya wani dan duk’ar da kai ya ce” Sai oga, shayi kai akoyshi oga, bari na ziga maka shi.”
Daga haka ya yi shiru, haka wajenma gaba daya tarin samarin ya d’auki shiru kamar ba kowa, har sai da aka zuba masa shayin nan ya amsa ya sha sannan ya mik’e yana murmushi ya d’aga masu hannu ya masu salama ya k’arasa cen wajen motarsa ya bud’e ya shige ya tafi.
Wata wawuyar ajiyar zuciya Abbas ya sauke yana d’aga yar yatsarsa da ya murje sigarin da yake busawa da ita ya talabe hab’arsa da hannayensa bibbiyu ya ce” Baba dama oga na kawo ziyara nan har na zo da wannan askin na kuma kunna sigari?”
Yusuf ya saki daria yana kallonsa ya ce” Kai baba yanzu fa ka gama cewa kai shege ne, ina cewa yanzu ka gama d’udd’urawa masu kaki ashariya kace kai ba dai mutun ba sai dai Allah?”
Abbas ya yi dariar shima yana mayar da kwalin sigarinsa cikin aljihun wandonsa ya mike yana gyara takalminsa k’ato mai nauyi ya ce” To kun ji, ni kam na k’ara gaba, kai in ba wulak’anci ba Baba ta yaya zaka had’a karnukan sojoji da ubansu? Mutumen nan fa baya duka kwata kwata, ni da idona na ga ya mari kannin matarsa ya summa, uban wa ya aikeni wasa da numfashi? Ce maka na yi ina fafatawa da k’annanun karnukan ba wai SULAIMANA ba , na fasa kawai sai kum faso.”
Kusan d’aid’aikun yan jagaliyar watsewa suka yi, dan sun gani sarai ciki ya shige, yana anguwar , ba zasu d’auki kasadar d’ora daba a wajen ba yau, dan komai na iya faruwa ciki harda ya tub’eka ya zaneka tasss yace baya son rashin kunya kuma babu abinda ubanka ko babarka zasu yi, hasalima ce masa suke Yah SAYYADI.
A nutse yake tafia cikin babban filin gidansu, jifa jifan yakan had’u da samarin gidan, su gaishe shi da girmamawa sannan su wuce bayan ya amsa masu ta hanyar basu hannu, sannan ya d’an ja ya tsaya yana k’are maka kallo, hakan ke saka su saurin sadda kai su ringa kame kame kamar sun aikata laifi, bayan shi ba Dukansu yake yi ba, babu wanda zai ce ga ranar da ya saka hannu ya dake shi a gidan nan, ama sun fi jin tsoronsa tamkar ransu fiye da wanda yake da masifar maganar da dukansu kamar zai kashe su da zarar sun yi laifi.
A kofar falon mahaifinsa ya ja ya tsaya yana dan sake gyara shigarsa, ya sani ne koda ABAH bai ce komai ba sai ya bishi da kallon an yi girman wofi saboda shigarsa
Da wannan ya yi dan murmushi ya kama abin bud’ewar ya shige yar k’ofar farko sannan ya dannan abin budewa ya ja ya tsaya, ya san za’a haska fuskarsa ta camera kafin ya samu shiga
Minti biyu tsakani jar wutar ta bada blue, hakan ya saka shi murdawa ya shiga , a nutse ya cire takalman kafafuwansa yana dan satar kallon Mahaifinsa dake zaune saman kujera zaman mutun biyu yana murmushi yana fad’in” Marhababika Abahna.”
Dan murmushi ya yi yana tsayen nan har amaryar Docter Ahmad SULAIMANE ta shinfid’a sabuwar darduma a saman lalausan cafet din dake malale mai kyan gaske da tsafta tana murmushi da zumbulelen hijabinta tana nuna masa tare da fadin” Babangida barka da zuwa, Bismillah Abah.”
Murmushi ya sake yi ya k’arasa a nutse ya hau saman dardumar dake daf da kaffafuwan mahaifinsa, ya sada kansa sosai a tausashe ya mika hannayensa biyu dan amsar na mahaifinsa dake miko masa ya ce” Barka da hutawa ABAH, yaya ibada?”
Musabaha suka yi mahaifinsa na kallon agogon hannunsa har suka gama ya zauna a nan kusa da kaffafuwan nasa ya dauki kaffafuwan ya dora saman wandonsa a hankali yana dan murzawa yana jin muryar mahaifinsa a tausashe ya ce” Yaya iyali?, Yaya fama da jama’a?”
Murmushi ya yi kasa kasa ya ce” Alhamdulilah…”
Sai kuma ya dago yana kallon fuskar mahaifinsa mai dauke da furfura fara kal a gemunsa baki daya, sai tsili tsilin bakin gashi ya ce ” Yaushe rabon Docter da zuwa gidan nan?”
Kin bashi amsa Docter Ahmad ya yi ta hanyar kamo wata maganar ya ce” Abahna, na tambayeka iyali baka ce komai ba?”
Aunty amarya ce ta yi murmushi bayan ta zuba masa ruwa a kofi mai kyau da tsafta ta ajiye ta ce” Babangida, ai ba zai baka amsa ba , Docter baya son ganin likita, sau biyu yana zuwa yana kin bashi dama, dama so nake ka zo na sanar maka.”
Baki Docter Ahmad ya kama yana kallonta, sai kuma ya yi murmushi ya ce” Gaba kad’an zan ringa lab’ewa ne tunda an fara saka min ido a gidan nan, in ba abin Umman *FATIMA ZAHRA* ba me ya yi saura da ya wuce shiga kabari? Wai ku Docter zai cewa na daina cin nama, sai dai Allah ya bashi hakuri domin babu abinda zan daina d’and’annawa a cikin launin dandanon dake dadad’a min zuciya dan gudun abinda yake rubutace ba kuma zai kauce ba.”
A hankali *SULAIMANE AHMAD SULAIMANE* ya d’an zubawa fuskar Aunty amarya ido dan gannin reaction d’inta, sanadiyar sunnan da ABAH ya ambata , sai ya ga kanta a kasa na yan dak’ik’u sannan ta mike ta nufi Kicin ba tare da ta kuma furta koda A ba.
Kansa ya maido wajen ABAH , a lokacin da ya girgiza kai bayan ta bar wajen ya ce”…
*Alhamdulillah.*
[24/10, 9:33 am] +234 803 800 7509: 🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐
*DAƘIƘA BIYAR*
🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai*
_2_
*Garabasa , garabasa, 😁🥰, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰*
Kansa ya maido wajen ABAH, a lokacin da ya girgiza kai bayan ta bar wajen ya ce” Ban san ranar da zata fuskanci rayuwa a kan y’ar da ta haifa da cikinta ba, Allah shi kyauta.”
Bai ce komai ba, sai ci gaba da ya yi da dan mamatsa ƙafafuwan Aban nasa, a haka Aban ke ta yi masa bayani a kan abubuwan da suke da buk’ata, ba wai kayan abinci, sutura ko harkar wutar lantarki ba, a’a, abubuwa na rayuwa dake iya b’illowa yau ko gobe, wasu taimako ne da sauransu, sannan ya kawo masa karar kanninsu mai sunna JAMILU cewar an kawo karar baya karatu a makaranta, ya yi abokan banza yana yawace yawace a makarantar, har ya yi sa’in’sa da malaminsu, a nan nema ya dan yi dan tsam ya ce” Shi JAMEEL din?”
Aba ya sheda masa kwarai kuwa,
Bai ce komai ba ya ci gaba da sauraron Aban har ya dawo kan maganar yan mata biyu da za’a aurar da kuma k’anninsa AMIR Ahmad SULAIMANE, shi ake jira ya saka rana da dai sauransu, watau bayanin kud’ad’en gadajensu da dukkan abinda ake yi.
Murmushi ya yi ya sake d’agowa ya dubi mahaifinsa ya ce” In sha Allah, za’a yi komai, Abah, sai kana hutawa fa, ka ringa rage magana sosai da yaren nan, idan sun yi ba daidai ba ka saka a kawo su cen in sha Allah zamu zauna mu tattauna.”
Baki da Hanci ABAH ya bud’e yana kallonsa, sai kuma ya yi daria ya ce” Kai Babangida, kai Babangida, so kake ka yiwa Y’a’yana mugunta ko? Gaka nan fuska fara, hannaye farare ama ban san me kake yi masu a cikin duhu ba da suke jin tsoronka, shikenan dan sun min laifi sai na tura maka su cen inda bana nan ba zan tare masu ba? Aa gwara ka daka a gabana ta yadda idan zaka karya zan tare. ”
Shima murmushi ya yi yana sake sada kansa tamkar wani wanda ke gaban sirikansa , yanzun ma bai ce komai ba.
Sosai ABAH ke hirantarsa, shima yana bashi amsa a matsayinsa na wanda ya fi sakewa a gabansa fiye da kowa, sai da ya d’auki lokaci a gabansa sannan ya mik’e yana yi masa sallama da niyyar bi d’aki d’aki ya gaisar da iyayensa har zuwa na mahaifiyarsa sannan ya wuce gida.
A hankali Abah dake kallonsa ya ce” Nace ba, wannan agogo kuwa tai min kyau, nawa ka siyeta ne?”
Ja ya yi ya tsaya, ya juyo yana kallon Mahaifinsa, dama tunda ya ga yana bin agogon nan da kallo ya san da wata a k’asa, watan kuwa ba komai bace face son sanin kud’inta, dan ya tabbata so yake yi ya san shin ya sayeta da mak’uddan kud’i ko da sauk’i? In da mugun tsada ne yanzu a bud’e babin wa’azi kala kala harda su maganar zakka, bayan Alhamdulilah yana kamanta abinda adini ya zo da shi.
Murmushi ya yi ya dawo ya duka yana balewa ya ajiye a daf da hannun Mahaifinsa a tausashe ya ce” Abah, bata da tsada kuwa, gatanan ina so ka saka , Allah ya karra maka lafiya…..Docter zai zo gobe da sasafe in sha Allah, ka taimaka ya dubaka, kafafuwanka sun tasa….bana so na ga sun tasa ka ji?”
Irin yadda ya tsatsareshi da ido sai da ya ji kwallah na taruwa a tasa,
Murmushi ya yi ya dauki agogon ya mayar masa a hannunsa ya ce” Kai kuwa, abinku na yara me ya hadani da shi, ina dai jin tausayinka ne, kuma ina dan son yin nasiha, lokaci zuwa lokaci a ringa rage siyan tsada sosia, dan nauyin kar ya yi yawa a zo a shiga hurumin gwamnati da kuma harkar talakawa…., Abahna ka san ko me bawa zai yi, idan bai rike bakinsa daa hannunsa da cin haram ba da sauki, ka kiyaye cin zali ko yayane, ka ji tsoron Allah shi shi kadai, bayan wannan ko waye ka barshi ya gwada ikonsa cikin damar da Allah ya bashi ka ji?”
Murmushi ya yi a hankali ya gyada kansa, ya dauki agogon ya mayar a hannunsa,, dan ba zai yi musu da mahaifinsa ba, ba kuma zai ja ya ja ba, haka kuma ba zai tsaya yace masa kar ya masa nasiha ba , dan nasiharsa shine kwarin gwuiwarsa, mahaifinsa shine na biyu a cikin layin abinda ke saka shi kiyaye dokokin Allah, daga Alkur’ani sai shi, ba zai iya duban idannuwan mahaifinsa yace da shi wannan agogo ya siyeta ne dan halin haka ya bashi dama, ba zai kwatanta masa a yanzu yana samun kudin da bai san yaya zai kamanta su ba, kamar wanda ake bashi rabonsa ,……bashi da abin fadi sai hamdallah, kuma in sha Allah zai rage siyan tsadar, dan a gaskiya yana siyan tsada, da wannan ya fice, Mahaifinsa ya bi shi da kallon tausayi da kuma addu’a, cikin ikon Allah sai da ya ringa haihuwar ya’ya har bakwai da matansa biyu sunna komawa ga ubangijinsa , shine na farko da ya zauna, daga shi kuma har yanzu babu wanda ya rasu, bai wani dauki shekaru ba, dan bai fi talatin da biyar ba, ama a haka Allah ya saka masa albarka, bayan dogon karatu ya fito ya damki aiki mai daraja har ya zamo kafada mahutar dangi da jama’ar gari
A muntuce ya ringa bi daki daki, tun daga kan aunty Amarya, har zuwa dakin mahaifiyarsa wato uwar gidan Docter Hajia ZUWAIRIYA ,
Kowance idan ya shiga bangarenta ya gaisheta, yakan saurara ya saurari bukatunta, da kawo kararta da sauransu dai, abinda ba za’a rasa ba , ba zai bar wajen ba har sai ya biya mata dukkaan bukatunta da yake iyawa, wa’inda baya iyawa kuwa yakan yi addu’a ne ya tashi
A dakin Aunty amarya kawai ya shiga ya fito bata ce tana bukatar kudi ba, ko ta kawo karar yar uwarta ba, har ya gama dan zama ya mike ya bar bangarenta ta bishi da addu’a kanta a sade dan fushin mijin bai saketa ba, watau da ya fadi sunnan da bata so, bata kauna ba kuma zata tana so ba!
Irin zaman da ya yi a saman kujera yana dan cakalar dankalin turawan da Hajia ta zuba masa da kanta irin zama ne da akan yi idan an zo gaban mahaifiya, wato ba d’ar ba dari d’ari.
Abincin yake ci, bata yi masa magana har sai da ya gama ta yi kiran daya daga cikin yarenta ta umarceta kan ta kwashe , ta kwashe ta mayar kicin ta kimtsa wajen sannan ta dawo sumui sumui ta haye sama numfashinta a makogwaro har ta shige sannan ta ja numfashi tana shigewa dakinta hadi da adu’ar Allah ya sa kar Hajia ta sanar masa cewar yau bata yi wanke wanke ba, wancen bara gurbin ta saka ta yi mata ya ci kakanin babaninta!
Hajia ta sake zubawa fuskarsa ido, sai kuma ta tabe baki tana cire kanta kasa kasa ta ce” wannan ja na lebenka kamar dai ba na lafiya ba……”
Kasancewar yana kallon fuskarta ne, kuma yana jin dukkan abunda take fada, sai ya yi murmushi bai ce komai ba, bai san me yasa kalar lebensa yake saka mahaifiyarsa koda yaushe mita a kai ba, shi dai ko goro baya taunawa bale a kai ga sigari ko giya, hasalima kamaninsa da na mahaifinsa tamkar kaki ya yi ya tofar, itace baka sannan a kaf ya’yan mahaifinsa su uku ne suka yi farinsa, ama Hajia sai tace shi nashi jan ya yi yawa anya na lafiya ne?
“Baban gida, na san abanka ya maka maganar kayan lefen yaren nan ko?” Hajia ta fada tana dubansa
A nutse ya amsata yana sake dubanta
Hajia ta hade fuska sosai ta ce” To bari ka ji abinda zan fada maka, ban lamunce maka kwasar kudi ka je ka kwashi kaya na makudan kudade ka zubawa ya’yan da kwanan duniya iyayensu ke koya masu tsanarka da kiyayarka ba, ka sani ni na haifeka babu wanda zai fi ni sonka ko sannin zafinka a duniya, ka kula Baban gida, idan nace bana so kar ka saki ka yi!”
A hankali ya dago kansa dake sade, shin yaya zai yi da iyayensa ne? Idan wannan ya ce ga abinda yake so a yi, sai wancen ya ce kar a saki a yi, ya kuma yi aiki da karfinsa da ikonsa a kansa
Bai san me yasa Hajia take yin wasu abubuwan ba wani lokacin, bayan shi ya sani mahaifiyarsa mutun ce mai matukar kyauta da son mutane
“Yaya zaka tsareni da ido kana min wani kallo kamsr sa’ arka Baban gida?, So nake ka fada min abinda abanka yace kaf ina saurare” ta sake fada harda harde ƙafafuwanta, irin jira take ta ji abinda bai yi mata ba a yi wada za’a yi
Ajiyar zuciya ya sauke a tausashe ya ce” ABAH bai ce min komai ba, nine nake so mu yi maganar da ke, sai na ga abinda ya dace a yi, MAMAH kar ki manta nine baba a gidan nan, ko me za’a yi ya zama wajibi na shanye na kuma nuna masu halin girma, da haka ne zasu yi koyi da ni idan kowa ya malaki hankalin kansa ya rike zumunci duk rintsi, Mamah, dukkan abinda suke yi ko giya suka sha babu wanda zai tunkarenk, tun daga kan AMIR har zuwa kan ummi Auta…, Ko a haka aka tsaya da sauki a irin tab’arb’arewar zamani da zumunci…”
Zama ta gyara da kyau tana kallonsa ta katse maganarsa a harzuke ta ce” Ba zai yiwu ba fa, ba zai yiwu ba, su rike zumunci ko kar su rike wannan damuwarsu ne, ba zai yiwu a taru a kashe min ɗa ba, na tabata abanku ba wani tausayinka yake ji ba, bari ka ji, idan ya ce sai ka yiwa ya’ya mata kayan daki da komai ba laifi ka yi, bayansu idan ka yarda ka yiwa matansa ko maza kayan aure ban yafe ba! Nace ban yafe ba baban gida, bama irin matar nan da yake sakawa a gaba tsofai tsofai da shi yana ikirarin soyaya, wace soyaya kuma Allah na tuba gayar yawun tsufa, na yanke magana Baban gida ba zai yiwu ba!”
Idannuwansa kawai ya mayar ya rintse, lokuta da dama yakan rasa ina mahaifiyarsa ta dosa,
A lokacin da Aba ya auri matar nan baki dayansu sun nuna mata kiyaya, uwa uba y’ar da Abah ya kawo matsayin tata ya kuma nuna ta zama tasa, yarinyar na fuskantar tsangwama da kyara a wajen dangi dan ta zamto wace aka haifa ba da aure ba, wulakanci kala kala na rayuwa tale gani, mahaifiyarta da ta haifeta da cikinta ta fi kowa tsanarta dan ko kofi ta taba ba zata taba ba, rana tsaka MAMAH ta ba kowa mamaki ta dauko yarinyar nan ta hada da ƴaƴanta ta kuma jajirce a kan yarinyar ta sakata makaranta take kuma tsaye a kan tarbiyarta, har yau an kasa gane me hakan yake nufi, domin a bangarenta yarinyar ke rayuwa, a wajen mama ba zata taba fuskantar kyara ko tsangwama ba, hasalima tana rike da ita da zuciya daya kamar yadda zata taro ƴaƴanta ko ta gyara haka zata yi mata, takan ce yarinya tata ce, ama bata son uwarta, hakan na ba kowa mamaki, sai dai a duniya ita Mama bata iya rayuwa ta munafurci ba, idan tana yinka tana yinka ne, idan bata yinka bata iya boye boye ko yi da gangan ba, FATIMA ZAHRAH tana samun hutu ne da kwonciyyar hankali idan tana gaban Mamah, du fada irin na Mamah tana jin du duniya bata da wajen mafaka sai a saman kafadunta, zaka ga Mamah ta wanke ƴaƴan kaf da fada kowa ya gudu ama ita sai ta karaso ta duka ta dora kanta a saman cinyiyinta ta yi ta sauke ajiyar zuciya……….wannan tsakani nasu na ba kowa mamaki ciki harda Docter Ahmad SULAIMANE
Wannan babin Mamah ta rufe ta sake dauko na iyalinsa,
Hirar da sam bata wani so, ba kuma ya farin cikin sauraro, sai dai wace ke yi din nan itace Allah ba zai saka shi aljannah ba idan har bata daga kafarta ba, du duniya itace take kallon idannuwansa tace zan fa ci ubanka babana, kuma a saurara a yi murmushi dan ta isa, bayanta ko mahaifinsa a yanzu sun zo bigiri din da yake lalaba shi, yake kuma yi masa komai a hankali du zafi irin na AHMAD SULAIMANE.
*A bayan Layi*
A tsaye take tana bin motar mai kirar Corolla da ido sannan tana jin muryarsa yana sake kiran sunnanta a karro na uku
A hankali ta dauko idannuwanta masu kama da na mashayiya, uwa uba tsarin halitarsu tanaa da girma daidai misali, sannan fattar saman mai bugun ido ce,, irin kana kallon su zaka so fara kawar da dubanka, dan ba irin idannuwan da ake tsatsarewa da kallo bane, ga wani ruwa ruwa mai nuni da daf ake da iya fara kuka, koma sama da haka, bayan babu maganar kuka a kusa kusa a cikin tsarinta, ba dan ta kasance mai tsaurin ido ko mai taurin kai bane, ko daya, hasalima ana iya kiranta da farar kura dan tsabar tsoronta, dan tana da saurin jin tsoro, ama kuma halitarta mai bayar da tsoro ce
Farar fuskarta dake dauke da kwontacen gashi a gaban goshinta, wanda lafcecen hijabinta bai hanna su bayana ba ne ke daukan jajaja, kumatunta na neman kumbura lokaci d’aya.
*Alhamdulillah.*
Leave a Comment