Wasu dalilai da ke sa a kasa tashi sallar subaahi

 DALILIN DA YASA KAKE KASA TASHI SALLAR ASUBAHI

GABATARWA:

Muhammad Umar Baballe.

Akwai dalilai da yawa da suke janyo wa ɗan adam musulmi rashin tashi yayi sallar asubahi acikin jam’i tareda mutane”

“Babban dalili na farko shi ne shaiɗan, wanda tun farkon lamari yayi alƙawari a gaban Allah maɗaukakin sarki cewa sai ya ɓatar da bayinsa daga kan hanyarsa madaidaiciya, to wannan itace nasara ta farko da yake samu daga gurin gajiyayyun bayi musulmai waɗanda suka yi sakaci acikin lamarin ubangijinsu

“Dalili na biyu kuwa shine sakacin bawa da rashin maida hankalinsa ga lamarin Allah, wanda shima hakan yana da matuƙar tasiri wajen hana bawa bautar ubangijinsa yadda aka buƙata, wanda hakan baya rasa alaƙa da tasirin shaiɗan shima akansa”

To amma kunsan ta yaya shaiɗan ɗin yake yin nasara akan bawa kuwa harma ya hanashi tashi yayi sallar?, tasirin hakan yana da alaƙa daku ne, ko dalili kuke buƙata akan wannan batun ne?, to bari na faɗa muku kaɗan daga cikinsu:

Akwai rashin addu’a yayin kwanciya bacci.

Akwai rashin ƙudurin zuci na yin sallar.

Akwai rashin kwanciya bacci da wuri.

Akwai rashin kwanciya cikin tsarki.

“Yau inda ace bawa zai riƙi waɗannan abubuwan acikin zuciyarsa, ya dinga yin aiki dasu ya kiyaye su ya kaucewa rashinsu, to lallai in Allah yaso zaiyi nasara akan shaiɗan ya kuma yaƙeshi a lokacin tashin sa domin yin sallar asubahi”

“Amma yau Allah ya ara mana lokacin kasantuwa acikin wani irin zamani, wanda wayar hanunka sai ta rinjaye ka, ta hana ka kwanciya da wuri, ta hanaka tashi yin sallar cikin dare, sannan kuma ta hanaka yin sallar farillah akan lokaci, domin duk ta cinye maka lokacin ta hanyar chatting, kallon fina-finai, karance-karance marasa amfani ga addinin ka”

See also  Ina zinar yaya mata ta samo asali

“Wannan wata musiba ce wacce take cinmu da yaƙi ga rayuwar mu da kuma rayuwar addinin mu, wacce kaɗan daga cikin bayi suke lura da hakan”

“Sallar asubahi ɗaya ce daga cikin manya manyan wajiban salloli guda biyar da muke dasu a cikin yini, rashin yinta akan lokaci yana daga cikin alamu na munafunci, domin tana da nauyi akan munafukai, ba koda yaushe bane Allah yake basu ikon yinta akan lokacinta, kuma inda ace sun san abinda yake acikinta na babban rabo, to lallai da kuwa sun zo gareta koda kuwa da rarrafe ne”

Allah ya bamu ikon cin galaba akan shaiɗan cikin dukkanin lamuran mu, Ameen.

Muhammad Umar Baballe

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top