Hausa Novels

Dan Ƙaramin Sauro Tada Uwar Giwa

Dan Ƙaramin Sauro Tada Uwar Giwa

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Dan Ƙaramin Sauro Tada Uwar Giwa

.*Zahra Surbajo*

 

 

*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai*

 

*wannan littafi me suna asama labarine da yake ƙirƙirarre,ban yi shi dan cin zarafin kowa ba,seda nishaɗantarwa da faɗakarwa gamida ilimantarwa,abinda zanyi daidai Allah yabani lada wanda nayi kuskure Allah ya yafemin*

 

*shine ze maye gurbin littafin gimbiya sabrina,maana na sauya masa suna,kuma ba free bane, meso seya biya kan ya karanta,dan gujewa ɗaukar hakkin da ba nasa ba*

 

*07044600044 domin biya afara tuntuɓar wannan number ta whatsapp ngd*

 

 

*1*

 

 

 

“Jalila you have to be very smart akan mijin nan naki,na gama lura dashi ɗan ɗaukar ƙafane,wanda kuma be dace musa ido muna kallonshi ba”cewar Aunty Sakeena dake cika tana batsewa.

 

Wacce aka kira da Jalila gyara zamanta tayi ta ƙyaɓe fuska irin ta ƴaƴan hutu tace a shagwaɓe”Aunty sakeena,nayi iya yina,amma wallahi bilal baya gani,kullum faɗa banyo kaza ba ban iya kaza ba, toni bansan ya yakeso in masa ba wallahi”

 

“mtsuuu rubish, why can’t you tell him that ke ba ƴar wahala bace?ko be san daga inda ya auroki bane, kinga nifa Bilal ɗin nan raga mishi nake dan kina sonshi amma har shi waye daze dinga sa miki dokoki na banza da wofi.”

Karanta Littafin Fitar Rabo Hausa Novel

“Nide aunty sakeena ki taimaka min wallahi gaba ɗaya banida kwanciyar hankali dan jiya yasha alwashin ƙaro aure matuƙar ban gyara ba kuma wlh aunty in ya faɗi magana baya sauyawa,”

 

A fusace sakeena ta miƙe tsaye tana gyara tsayuwar mayafinta tace da kakkausar murya”shekarun mahaifiyarmu talatin agidan babanmu,ko budurwa daddy be taɓa gigin yiba,dan haka muma ba namijin daya isa yay mana kishiya wallahi ko ɗan gidan uban waye,dan haka ki kwantar da hankalinki”tana kaiwa nan ta sury handbag ɗinta ta kwashi key ɗin motarta tace.

 

 

“Da zaran ya dawo daga tafiyar ki sanar dani zanzo na sameshi har gida inji uban daya ɗaure masa gindi yake miki abinda yaga dama”

 

Bata jira amsawar jalilar ba tasa kai tai ficewarta cikin takun isa da jinkai da izza da ƙasaita ta masu faɗa aji.

 

Motarta ta faɗa tai mata key,ta fice daga harabar gidan na ƙanwarta,zuwa nata wanda tsabar haɗuwar gidan nata bazaka ɗauka aduniyar mutane yake ba.

 

Tana parking ta fito masu aykin gidan tuni suka iso kwasar gaisuwa, bata kula ko ɗaya acikinsu ba,ta wuce cikin gidan,ranta a ɓace.

 

 

*******

 

 

Jalila da Sakeena ya da ƙanwa ne uwarsu ɗaya ubansu ɗaya,ƴaƴane ga attajirin ɗan kasuwar nan,Alhaji Habu Ɗan iya,me kamfanin Ɗan iya investiment limited dake afaɗin ƙasar nan baki ɗaya,

 

Akwai shaƙuwa me ƙarfi atsakaninsu,da soyayya me girma,sakeena nason jalila fiye da tunani,shiyasa duk abinda ze dameta take iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta kawar mata dashi, kome girma da tsananinsa.

 

 

Tun daga primary har jamia a ƙasar holland suka yi,kasancewar mahaifiyarsu can take zaune,dan kasuwancin mahaifinsu yafi ƙarfi aƙasar.

 

 

Jaleela sun haɗu da mijinta bilal a can ƙasar ta holland,suka fara soyayya wanda ƙarshe akai musu aure kasancewar shima ubansa ƙusane aƙasar tamu.

 

Bayan auransu da shekara guda suka yo ƙaura zuwa nigeria,dan ci gaba da faɗaɗa kasuwancinsu.wanda shima bilal dole tasa ya baro holland badan yaso ba sedan farincikin matarshi.

 

Sakeena,ko Shekararta biyar kenan da auranta inda take auran Ɗan Hamshaƙin ɗan kasuwar nan wanda duniya ma tasan da zamansa sabida shura da shaharar sa.wato,Alhaji Aliyu wanda aka fi sani da Abu turab me suna Amdaz Abu turab.

 

 

Tun Auransu da Amdaz take sha ƙwayoyin hanz haihuwa dan ɗawainiyar yara baya daga cikin burinta,bata son haihuwa ma ita kwatata.

 

Sakeena mace ce me tsananin kishi da ji da kanta,bata son ƙasƙanci koya yake,kuma bata ƙaunar ko ƙuda ne inde na mace ne ya gogi mijinta,tana masifar sonshi shima kuma haka yake tsananin ƙaunarta.

 

 

Suna zaune a garin Abuja su duka,harda jalila da nata mijin Bilal da iyayensu sede kowa unguwarsa da ban.

 

 

Muje zywa

 

Surbajo for life.

Leave a Comment

error: Content is protected !!