Dan Ba Kara Hausa Novel Complete

Dan Ba Kara Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Dan Ba Kara Hausa Novel Complete

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

ƊAN BA ƘARA

 

 

© AMEERA ADAM

_AmeeraAdam60_

*@Wattpad*

 

*FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION*

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*

 

 

*1st/Nov/2020*

 

1&2

 

” Mejidda mejidda wai kina Ina sai kwala Miki Kira nake kin shanyani daga d’aukan kallabi tuni kin shafe lokaci har na Fara gajiya, ko so kike mu rasa motar kina sane dai yau juma’a ga Rana da d’aga ” goggo larai ce ke tsaye da shirinta da alama fita zasuyi, mejidda ce ta karaso mayafinta ahannu tana kokarin d’aura D’an kwali, cikin mita da tsiwa take yiwa goggo larai magana, ” haba goggo ke kincika raki duk kibi ki tayiwa mutane sanabe muje ni ko a soro na sa hijabin ” rike haba goggo larai tayi cikin takaicin abinda mejidda tayi Mata tayi kwafa tace, ” Allah ya shiryaki Y’ar Nan kinji Allah ya nunamun ranar da zanga auranki, mejidda kinsan dai banasan laifinki Amma ni meyasa bakya shayin fad’a mun magana ne? ” Mejidda ko ta Kan goggo batabi ba ta cigaba da sabgar gabanta.

 

Har sunje kofa suka ji me kifi na talla da sauri goggo ta tsaidashi, har ya kusa Shan kwana ya dawo guda uku aka zubawa goggo suka Fara ciniki da ita, sunyita ciniki ita da me kifi har suka karkare a dari hudu da hamsin, goggo har ta zuge kajarta ( _D’an aljihun da akewa tsofaffi ajikin sket dinsu na ciki_ ) ta ciro kud’i tuni me kifi ya yanka kifi Yana Shirin zubawa acikin leda aykuwa mejidda tai karaf tace, ” goggo wannan mitsi-mitsin kifin Zaki siya dari hudu da hamsin wallahi ya daki hancinki wannan kifin da Bai wuce d’ari da hamsin ba, chabdi lallai ma kudin ne sukayi Miki yawa”

 

Aykuwa da sauri me kifi ya kulleta Yana watsa Mata harara, goggo jin kalaman mejidda tuni ta hau ta zauna ya mutsa fuska gogg tayi sannan tace, ” Kai yaro jeka da kifinka wallahi na fasa siya tunda mejidda tace yayi tsada idan munje rumfar D’an Tani ma saya inajin nashi sunfi wannan arha dama ajiyeshi zanyi sai yamma idan mun dawo, kila ma ragowar na jiya ne Kar naje ya buga kafin mu dawo, Dan yanda naga wannan jagulallen kifin Nan da alama kwantai ne” me kifi sakin Baki yayi Yana kallan goggo larai, tuni me jidda ta karb’e zancen, ” kema goggo da wayace ki tsaidashi sai wani zubawa mutane ido yake kamar mujiya, ni irin dama masu tallan kifin Nan ban yarda da kifinsu ba, gaskiya mu wuce Kar muje arufe hanyar masallaci kinsan dai basa d’aga k’afa ” goggo najin Haka ta yi gaba me jidda da mukulli ahannunta tasa Masa key ta rufe sukabar me kifi atsaye da yankakken kifi a hannu mejidda harda bangazar robar kifinsa da gefen hannunsa bisa tsautsayi kifin hannunsa rabi ya zube tayi gaba abinta ko ajikinta.

 

Karin wasu littafai da zaku so

Su Inna na zuwa titi suka tari bus din da zata kaisu Rimi asibiti, me jidda akan maleji ta zauna goggo na kujera sannan suka tafi, bayan wani lokaci motar dasu goggo suka hau ta cika makil har maleji, fad’a ne ya tirke tsakanin me jidda da wata Yarinya ba kunya goggo ta shigar Mata, saboda ko kadan goggo batasan laifin ta Dan mahaifi da mahaifiyar me jidda sun rasu shiyasa ta taso a hannun goggo asangarce ba kwab’a sai abinda tayi niyya shi take yi, kuma komai tayi goggo bazata Mata fad’a ko tsawatarwa ba, har suka K’arasa goggo nata masifa gidan babban D’an goggo sukaje, shi ma Kuma dama me jidda ce ta damu sai sunje saboda shima kawu haruna mutum ne bame fad’a ba akwai shi da sanyin hali shiyasa tasu tazo d’aya da me jidda.

 

Su goggo basu suka dawo ba Sai yamma likis, goggo na bud’e kofa wasu y’an Mata suka k’araso da sauri gurinta kowa da karar Daya kawo Mata ta mejidda, tsuke fuska tayi ta zage su tass sannan ta koresu, haushin goggo ne ya kamasu suka tafi suna gunguni suna watsawa mejidda mugun kallo, sanin halin mejidda ba kanwar lasa bace shiyasa yasuyi gigin tab’a ta ba, Amma yanda suke Jin haushin mejidda yaci su nad’a mata dukan tsiya.

 

Bayan sun shiga cikin gidan goggo tabarma ta shinfid’a tana maida numfashin gajiya, mejidda ma gefen Goggo ta kwanta ta d’ora kanta akan cinyar Goggo.

Karni-karnin kifi Goggo ke ji Dan waige takeyi tana neman inda zataji yake karnin, bayan sun huta goggo tashi tayi zata d’ora Musu girki tana d’auko tukunya ta bud’e sai ganin yankakken kifi tayi aciki tana kallan kwayar idan d’aya ya kirfta Mata ido.

 

 

_Ummou Aslam Bint Adam_

 

*DUBU JIKAR MAI CARBI*

 

 

©AMEERA ADAM

 

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

 

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

 

 

FREE PAGE 1

 

Babban gida ne mai É—auke da É“angare daban-daban har kusan sashen mutum goma sha biyu. A taÆ™aice za mu iya cewa gidan gandu ne da ya haÉ—a Kakanni, ‘ya’yaye da jikoki. Garin ÆŠangwauro yana É—aya daga cikin Æ™anana Æ™auyukan da ke cikin Æ™waryar Kano, Allah ya azurta su da noma, kiwo da kasuwansu. Gidan Malam Muhammadu mai dogon Carbi sanannan gida ne a kaf cikin garin ÆŠangwauro. Tun daga titi idan ka tambaya za a kai ka har cikin gidan, sakamakon gida ne gidan yawa don wani lokaci mutane na yi masa laÆ™abi da gidan ‘Ya’ya da yawa.

 

Gidan Mai dogon Carbi cike yake da mutane sakamakom wayar gari da suka yi da rasuwar rashin wannan Dattijo mai yawan shekaru, ba iya gidan ba hatta garin Ɗangwauro ya girgiza da rashin wannan Dattijon mai dogon zamani. Yaya Babba da Inna Furai sune matan wannan Dattijo da ya rasu mutuwar ba ƙarmin taɓa su ta yi ba.

See also  Kwarton Manya Hausa Novel

 

Bisa ga al’adar Malam bahaushe a ranar da aka yi mutuwa mutane sun fi nuna damuwarsu ta hanyar koke-koke, kukan ma yana taÆ™aita yawancin bayan ankai mammaci. Hakan ce ta faru a gidan Mai dogon carbi domin an fita da gawarsa a yi mata sallah yara da Manya sai kuka suke yi.

 

A gefe ɗaya Hali dubu na hango rakuɓe sai muzurai take lokaci-lokaci tana share hawaye, sai dai cikin zuciyarta haushin mutanen gidan take ji saboda ta lura babu wanda yake bi ta kanta don ya rarrasheta, duk kuwa da irin gursheƙen kukan da take yi. Kallonsu ta fara yi tana ayyana irin abin da za ta yi domin ta janyo hankulansu kanta. Tun da ai ita gani take kamar ta fi su jin mutuwar koda suna yawan faɗa da Mai dogon carbi amma kafin ya rasu, ai ita ma Kakanta ne.

 

Sumi sumi sumi ta tashi da yaÆ™unannan hijabinta ta bi hanyar soron gidan tana waiwaye, sai da ta je soron Æ™arshe daga shi sai fita Hali dubu ta É—ora hannuwa biyu akanta ta dawo cikin gidan da gudu tana cewa, “Wayyo Allah! Wayyo ni na shiga uku na lalace.” Lokaci É—aya hankulan mutanen gidan ya dawo kanta, da sauri aka yi carko-carko a kanta masu jero tambaya na yi. Zuciyarta Æ™al don ko ba komai ita ma za a rarrasheta kamar yanda aka saka su Yaya Babba ana basu haÆ™uri. A fakaice take satar kallonsu tana sake sharce hawaye amma ta yi biris babu wanda ta tankawa duk irin tambayoyin da mutane suke yi mata. Baba Munkaila ne ya shigo ya hango cincirindon mutane a tsaitsaye da sauri ya Æ™arasa wurin, ganin Hali dubu a zaune ya sa ya ja guntun tsaki sannan ya buga mata tsawa, “Ke lafiya kike yi wa mutane ihu?” Kamar sabuwar Marainiya haka ta É—ago shanyayyin idanuwanta ta kalle shi sai kuma ta waiga ta saci kallon Æ™ofa ta kuma duÆ™unÆ™une kanta cikin alamun tsoro da firgici. Kamar haÉ—in baki dukansu suka kalli bakin Æ™ofar suna neman Æ™arin bayani, babu abin da ta furta musu sai ma kuka da take yi tana nuna musu Æ™ofar da É—an yatsanta. Baba Munkaila tsawa ya sake buga mata ya ce, “Me ye a cen É—in?” Hali dubu ta kuma kallon Æ™ofar ta rushe da kuka tana cewa, “Baffa ne!” Cikin haÉ—in baki duka suka ce, “Baffa kuma? Wane Baffan?”

 

Bata bi ta kansu ba sai kawai ta baje a wurin ta fara wata irin birgima tana cewa, “Wayyo Baffa ne ya tafi ya barni!” Takaici ne ya rufe Baba Munkaila domin ya san za a rina don ya tabbata ganin Dubulliya tana wannan kukan ba banza ba. Cikin faÉ—a-faÉ—a ya fara yi mata magana amma ko gezau ba ta motsa ba. Can gefe ya hango wata igiyar dabbobi ai kuwa bai yi wata-wata ba ya fara tafka mata, tana jin shigar bulala ta tashi ta yi cikin gida ta gudu.

 

Can É—akin Yaya Babba ta shiga ta haye Æ™arshen gado tana kuka, ga haushin Baba Munkaila ya tsinkata a cikin mutane. Tambayar duniya Yaya Babba ta yi amma Dubuliyya kanzil! Bata ce da ita ba. Sai ma ta yi zamanta a nan domin duk duniya babu abin da tafi tsana kamar taron jama’a a gidansu. Domin ba Æ™aramin takura take yi ba, dalilinta na haka kuwa ta yanda za ta ji mutane na bata ji ko kuma ta cika rashin ji kamar Æ´ar aljanu. Tana daga kwance dabara ta faÉ—o mata ta yanda za ta kore jama’ar gidan ta ruwan sanyi domin ta san yanda danginsu suke sai a kusa arba’in da mutuwar da sauran baÆ™i tsiraru. Saboda haka Baffa mai dogon Carbi ya saba musu tun yana raye, idan suka zo taro baya barin Æ´an uwansa su koma a kwana kusa. Wannan dabara tata ba Æ™aramin daÉ—inta ta ji ba don har sai da ta murmusa saboda farin ciki. Kamar wacce aka tsirawa allura haka ta zabura da sauri ta fice daga É—akin Yaya Babba, ita kanta Yaya Babba ba Æ™aramin daÉ—i ta ji ba kasancewar duk duniya babu Jikarta da take so kamar ita sakamakon Marainiya ce gaba da baya.

 

Dubu tana fita ta yi garau da ita kamar ba ita ta sharɓi kuka ba, nan fa mutane suka fara yi mata tsiya, har da masu cewa dama ita zuma ce sai da wuta. Wasu kuma su ce gara da ya yi mata haka ga shi ta ware ta fara harkokinta. Shiru ta yi babu wacce ta tankawa sai dai duk wacce ta yi magana tana auna maganar tata a mizani domin ta san irin hukuncin da za ta yi mata.

 

Tun da Magriba ta doso Dubulliya ta fara haÉ—a kayan aikinta a fakaice cikin hikima da basira, ba tare da wani ya fahimci halin da take ciki ba. Sakamakon babban gida ne kowa da wurin da yake nema ya kwanta saboda ko ina a wadace yake hakan ne ya sa Yaya Babba bata damu ba da Hali dubu ta ce za ta sashen Baba Munkaila ta kwana a cen.

 

DA DADDARE

 

Da daddare gidan ya yi tsit ban da kukan tsintsaye da Æ™ananan dabbobi babu abin da yake tashi, sai munsharin bacci da yake tashi daga É—akunan daban-daban. Dubuliyya tana daga sashen Baba Rufa’i cikin É—aya daga cikin É—akunan Æ´aÆ´an gidan. Sai da ta ci baccinta ta more sannan ta farka cikin talatainin dare ta ji gidan tsit kowa ya yi bacci sannan ta saci jiki ta zaro kayan marigayi Baffa ta saka rigarsa da babbar riga har da hula ta naÉ—a rawaninsa ta É—auki zabgegen carbinsa ta maÆ™ala ta fito, hasken farin wata ne ya haska mata hanyar da za ta rinÆ™a bi har fice daga sashen gabaÉ—aya. Can wurin da ya zamewa Marigayi Baffa mai carbi wurin alwala can ta je ta tsugunna, daga nesa idan ka hango Dubu a tsugunne sai ka rantse da Allah Baffa ne, sai da ta waiga hagu da dama sannan ta taÆ™arÆ™are ta fara zabgo kaki irin yanda Baffa yake yi, Baba Sule da ke kwance cikin baccinsa ya fara jin alamar kaki tamkar yanda mahaifinsu yake yi duk asuba. Fakare ya yi yana zare idanu, yana cikin wannan yanayin ya sake jin an yi kaki har da irin tarin tsofaffin nan da Baffa yake yi. Janyo wayarsa ya yi yana dubawa ya ga Æ™arfe biyun dare, nan take ya hau murza idanu yana sake kasa kunne. Dubu kamar ta san ana sauraronta ta kausashe murya sai ka rantse da Allah Baffa ne yake magana ta fara cewa, “Tabbas rayuwar barzahu daÉ—i gare ta.” Baba Sule ya waro idanu wace cikinsa na karta masa, don ya tabbata hatta dabbobin gidan da suna magana za su ce sun shaida maganar Baffa ce cikin daren nan.

See also  Hakki Ne Hausa Novel Zahra Surbajo

 

Dubu na tsugunne ta ji alamun tahowa wata zuciyar ta ce mata ta tashi ta É“uya, wata kuma ta ce ta zauna ta ci gaba da abin da take yi. Tarin Inna Furai ta ji ta saci kallonta ta hangota da Æ´ar buta a riÆ™e za ta je banÉ—aki. Dubu wani kakin ta sake yi tana daga tsugunne, hasken farin wata ne ya hasko mata mutum durÆ™ushe da fararen kaya da rawani tamkar marigayin mijinsu. Gabanta ne ya yi mummunan faÉ—uwa ta fara motsa baki cikin addu’a don a zatonta mugun gamo ta yi.

 

ÆŠauke kai ta yi don ma kar ta ci gaba da kallon wurin da Dubu take ta ci gaba da tsoratata, sai da ta kusa da wurin da Dubu take ta ji muryar marigayin mijinsu raÉ—au a kunnenta yana cewa, “Wato ita dai rayuwar barzahu daÉ—i gare ta. Babban daÉ—in idan ka kawo ziyara tsohuwar rayuwarka sai kuma ka tafi da matarka.” Inna Furai na jin haka ta dafe Æ™irji tana ja da baya jikinta har tsuma yake ta ce, “Yau na haÉ—u da zazzagar rayuwa ni Furaira. Allah na roÆ™eka karka jarrabe ni ta wannan fannin.” Dubu na jin haka ta miÆ™e tsaye tana gyara zaman babbar rigar jikinta ta sake kausashe murya ta ce, “Wuni É—aya har na yi abokai miliyan É—aya da É—ari biyar a cikin Fatalen har da masu tashi sama. Ƴan sama jannati ku zo ga wani naman mun samu, kuma daga yau mun fara É—auka kenan a gidan nan. Duk wanda ya wayi gari ya ga likkafani a jikin kayansa shi za mu yi wa É—aukan amarya.” Inna Furai tuni fitsarin da take riÆ™ewa ya samu sukunin tsiyayowa, sakin butar hannunta ta yi jikinta na tsuma donma bongon da ke bayanta ya tokareta.

 

Dariya ce ta so Æ™wacewa Dubu amma ta maze ta ce, “Ƴan uwana Æ´an sama Jannati! Ku zo na fara samo muku Æ´ar uwa.” Inna Furai ta saki salati tana cewa, “Yau na haÉ—u da zazzagar rayuwa shi kenan tawa ta zo Æ™arshe.” Dubu sunkuyar da kai Æ™asa ta yi ta fara takowa gaban Inna Fuarai ta ce, “Idan kina son fansar kanki sai kin sake shayar da Æ´aÆ´anki tamkar yanda kika shayar da su suna jarirai, tun daga kan Larai (Ita ce babbar Ƴar Inna Furai) har zuwa kan Sabi’u (Shi ne autanta) idan kika kuskurewa haka tabbaci haÆ™iÆ™a sai mun zo ido biyu mun tafi da ke babu wanda ya isa ya hana.”

 

Baba Sule tuni cikinsa ya É—uri ruwa yana son fita domin ceton Matar Mahaifinsa tsoro ya cika masa ciki, bai gama tsinkewa da lamarin ba da ya ji an fara kiran yan sama jannati. Dubu don ta Æ™ara razana Inna Furai ta sake dakushe murya ta ce, “Ki isarwa da mutanen gidan nan saÆ™ona muddin suka ci gaba da kwanaki sai na yi musu É—auki É—aiÉ—ai. Shi kuma na É—aki da yake laÉ“e yana sauraronmu, shi kuma É—auke shi za mu yi gabaÉ—aya.” Dubu na cikin magana sai gani ta yi Inna Furai ta zube Æ™asa. Gabanta ne ya faÉ—i ta ji fargabar kar tsohuwar mutane ta mutu a hannunta. Da sauri dubu ta waiga sai kuma ta kurma ihu tana maÆ™e murya ta zunduma ihu, sannan ta zuba a guje ta yi cikin gida. Ta nufi ma’ajiyar kayan Baffa ta lallaÉ“a ta shige ta kwanta.

 

Ihun da Dubu ta yi ba Æ™aramin razana Baba Sule ya yi ba da jim kalaman da da aka ce za a É—auke shi matuÆ™ar ya saki hannun matarsa. Yana daga gefen gado da sauri ya matsa ya kama hannuwan matarsa ya riÆ™e Æ™am, don kar a neme shi a rasa. Cikin bacci Sahura ta fara masifa da yake Allah ya yi ta masifaffiyar macece. Tana jin ya riÆ™o mata hannu ta ce, “Don Allah sakarni Uban Æ´an naniÆ™a.” Da yake bacci ya hau kanta bata kuma tanka masa komai ba.

 

Daga É—aki mai kallon gabas Baba Auwalu ne ya É—aga labule yana haskowa da fitila zaraf matarsa Yahanasu ta miÆ™e tana tambayarsa da yake su sabbabun amare ne. Daga can nesa suka hango Inna a yashe tana ko numfashi bata yi. Gabansa ne ya faÉ—i yace, “Wa nake gani kamar Inna a Æ™asa.” Sahura ta dafa kafaÉ—arsa ta ce, “Auwaluna ni ban yarda ita bace kawai magauta ne suka yi maka ture.”

 

Duk duniya babu abin da Auwalu ya tsana sama da a É“ata ran Yahanasu amma tabbas wannan karon ba zai iya haÆ™ura ya bar Mahaifiyarsa a wannan yanayin ba. Kasancewar dare ne amma bai hana sakar mata murmushi ba ya ce, “Allah shi zai kare ni amma bana tunanin wani zai yi mini ture cikin dare.” Kafin ta yi magana tuni Auwalu ya yi gaba, ganin haka ya sa ta ja tinga ta tsaya don har ga Allah a tsorace take musamman da ya kasance ranar ne aka yi rasuwa.

 

Hankali a tashe ya fara yayyafawa Inna ruwa ganin ta fara motsi ya sa ya kamata yana bubbuga Æ™ofar Baba Sule, Baba Sule na ji ya yi fakare kamar mai bacci don gabaÉ—aya ya gama rikicewa. Sama-sama Sahura ta fara jin bugun Æ™ofa firgigit ta miÆ™e sai ji ta yi Sule ya riÆ™e hannunta gam, tana shirin yin magana Baba Sule ya janyota cikin raÉ—a ya fara cewa, “Kada ki yi magana za su yi sama da ke” Waigawa Sahura ta yi tana kallon Æ™ofa don ita a tunaninta masu buga Æ™ofar ne za su yi sama da ita. Suka Æ™arajin bugun Æ™ofa Auwalu yana cewa, “Yaya Sule fito ka taimaka mini jikin Inna ya yi tsanani ina jin makewayi za ta ta faÉ—i.” Sahura ta ja guntun tsaki ta ce,

 

“To! Sai ka tashi tun da ta ka ji muryar Auwalu.” Baba sule ya sake Æ™asa da murya yanda daga shi sai Sahura ne za su ji abin da yake faÉ—a ya ce, “Ki koma ki kwanta kawai ina ji a jikina waÉ—annan Æ´an sama jannati ne suka rikiÉ—a. Takaici ya kama Sahura yanda ta ga Maigidanta yana rawar É—ari ga shi ba lokacin zafi ba, ta miÆ™e tana fusgar hannu ta ce, “Sakarni ko Æ´an Æ™asa jannati ne babu abin da zai hanani fita.”Tana jan hannu Baba sule yana ja don a tunaninsa muddin ta saki hannunsa shi kenan za su yi sama da shi.

See also  Doctor Eshaat Hausa Novel Complete

 

Sororo Sahura ta yi tana kallon ikon Allah, don ita a iya saninta da Sule ba su taÉ“a irin wannan wasan da shi, don haka ta sake É“ata fusaka ta ce, “Sule wai wani abu ne yake damunka ko gamo ka yi cikin dare n sani ba?” Baba Sule ya yi wura-wura yana kallon hagu da dama ya sake Æ™anÆ™ance murya ya ce, “Sahura a kowanne lokaci za a iya yin sama da ni.” Wani takaicin ne ya sake rufe ta, ta miÆ™e tana Æ™oÆ™arin fisge hanunta amma abin ya ci tura don Æ™arfin mace dana namiji ba É—aya.

 

Auwalu da ke jin Æ™usur-Æ™usur a É—aki sai ya sungumi Inna don a ganinsa bai kamata ya sake buga Æ™ofar É—akin ma’aurata cikin dare ba. Can sashen su Inna Furai ya nufa Yahanasu ta Æ™walla masa kira tana cewa, “Auwaluna ina za ka ni dai tsoro nake ji.” Auwalu ya waigo ya ce, “Shiga É—aki Inna zan kai na dawo.”

 

Dubu na daga É—aki tana jin duk abin da yake faruwa, tana jin Baba Auwalu ya tafi ta yi zaraf ta fito cikin sanÉ—a sai da ta zo daga bakin Æ™ofar Yahanasu ta yi gyaran murya ta sake kausashe murya irin ta Marigayi mai carbi ta ce, “Wato ita rayuwar barzahu daÉ—i gare ta ni Mamman. Yanzu tun da na zagayo rayuwata ta baya dole na É—auki mai É—akin nan.” Cikin Yahanasu ne ya kaÉ—a nan take jikinta ya hau karkarawa kamar mazari. Dubu ta yi irin tarin tsofaffin ta sake cewa, “Amma ita Yahanasu za mu É—aga mata Æ™afa sai dole ta bi sharaÉ—inmu ko ba haka ba Æ´an sama jannati?” Dubu ta sake sauya murya ta ce, “Ai dole ma ta bi umarninmu ko yanzu mu faÉ—a É—akin.” Yahanasu bata san lokacin da ta yi farat ta ce, “Wallahi ku faÉ—a ko meye zan bi.”

 

Dubu ta maÆ™ale murya ta ce, “Dole ki zama makauniyar Æ™arfi da ya ji muddin kika buÉ—e idonki sai dai ki wayi gari a Æ™iyama.” Tun Dubu bata rufe baki ba Yahanasu ta runtse ido biyu ta ce, “Wallahi na rufe har abada ba zan sake buÉ—e su ba amma don Allah karku cutar da ni.”

 

Dubu har da Æ´ar tsawarta ta ce, “Kin tabbata kin rufe ko na aiko da Ƴan sama jannati su shigo?” Yahanasu ta sake runtse idonta tana cewa, “Na rufe wallahi na rufe.” Dubu ta saki murmushin mugunta a Æ™asan zuciyarta tana cewa, “Yau zan ga Æ™aryar soyayya kullin a ishe mu da Auwaluna.” A fili Dubu ta ce mata, “Maza tashi tsaye ki rungume bango.” Da sauri Yahanasu ta fara lalaube-lalube har ta taÉ“o bango.

 

A hankali Dubu ta zura kai ta leÆ™a ta hango Yahanasu na rungumar bango, zuruf ta faÉ—a É—akin cikin sanÉ—a. Sai da ta je daidai wurin Yahanasu sannan ta É—aga zabgegen Carbin Marigayi ta zabgawa Yahanasu a Æ™eya, sai ta fara wani gunji tana cewa, “GargaÉ—in yan sama jannati kenan.” Tana faÉ—ar haka har ta fice daga cikin É—akin.

 

Yahanasu tun da ta gantsare take hawaye a tsaye sai dai ta kasa buÉ—e idonta saboda tsoron abin da kaje ya zo.

 

Duk abin da yake faruwa a kunnen Sahura da Baba Sule, cikin Baba sule ne ya sake É—urar ruwa. Sahura ita kanta jikinta ya fara sanyi musamman da ta jiyo Ihun Yahanasu, shiru ta yi kamar ruwa ya cinye ta duk masifar da take yi ta daina. Domin da alama zancen Sule ya tabbata.

 

Lokacin da Auwalu ya Æ™arasa É—akin Inna Furai, har lokacin bata dawo hayyacinta ba. Yana shiga ya kwantar da ita akan Æ™aramin gado, sannan ya fara tashin Æ™anwar Mahaifinsu Lantan da ta zo daga garin Zariya. Ganin halin da Inna Furai take ciki ba Æ™aramin É—aga hankulan mutanen É—akin ya yi ba. Auwalu ya juya zai fita Inna Furai ta riÆ™o hannunsa ta ce, “Auwalu! Yau na haÉ—u da zazzagar rayuwa. Don haka ka haÉ—o mini kawunan Æ´an uwanka mazan su da matan su a yanzun nan. Idan ba haka ba wallahi sai na zazzagar da albarkasu kowa ya lalace.”

 

Auwalu da sauran mutanen É—akin sun yi tsammanin zafin ciwo ne ya sa Inna Furai take sumbatu. Lantan ta Æ™ara matsawa kusa da Inna Furai ta ce, “Furaira sanu kin ji Allah sa dai ba akan makarai kika faÉ—i ba.” Wannan magana ba Æ™aramin fusata Inna Furai ta yi ba, a zafafe ta É—ago ta ce, “A kan bulikiya na faÉ—i! Lantan bana son zazzagar wulaÆ™anci. Kai Auwalu ka tara mini Æ´an uwanka a daren wallahi tun ban zazzage albarkar da ke kanka ba.” Kamar sabon munafiki haka Auwalu ya fice sum sum sum daga É—akin. Haka ya rinÆ™a bi É—aya bayan É—aya yana taso su. Wannan tashin da Auwalu yake yi wa Æ´an uwansa ne ya sa kusan rabin mutanen gidan suka tashi daÉ—in daÉ—awa idan kowa ya ji ance Inna Furai ta faÉ—i a hanyar banÉ—aki sai ya wartsake masu tafiya É—akinta na yi masu jaje suma suna yi.

 

Kafin wani lokaci tuni É—akin Inna Furai ya cika da Æ´aÆ´anta su rai takwas maza biyar mata uku. Sai da ta kalle su É—aya bayan É—aya sai kawai suka ga ta É—aga riga ta ce, “Larai bisimillah” Larai zuciyar ta É—aya ta É—auka Inna Furai so take a Æ™arasa cire mata riga, nan take ta fara cikiniyar tuÉ“e mata riga. Cikin Æ™araji Inna Furai ta fisge tana cewa, “Larai yanzu bijirewa umarnina za ki yi? Ni za ki zazzagewa albarka a ka” Sai ji suka yi Inna Furai ta fashe da matsanancin kuka. Lokaci É—aya suka kalli juna domin ba su ga abin da zai sa Inna Furai kuka ba. Auwalu ya sunkuyo ya ce, “Inna ki yi hakuri me kike so?”

 

Inna Furai ta É—ago mamanta É—aya ta ce, “Mahaifinku ya zazzage mini albarka É—azu nan domin daga zuwansa lahira har ya haÉ—a kai da Æ´an sama jannati. Ba zan zazzage maka bayani gabaÉ—aya ba amma Auwalu ungo sha ka ji.”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top