Dan Majalisa Hausa Novels Complete

Dan Majalisa Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

[18/10, 12:53 pm] +234 816 362 6370: 🌹 *ƊAN MAJALISA* 🌹

( Love story )

 

 

 

*Mallakar*

_AUTAR MANYA_🌹

 

 

~~~~~~~

📚 *HOME OF QUALITIES WRITTER’S ASS*

~~~~~~~

 

_Dasunan ALLAH Mai Rahama Mai Jin Ƙai_

 

 

🅿️ *1*

 

 

Daƙarfin gaske ya bugi ƙaton table ɗin dake gabansa wanda yake shaqe da tarin takardu, sannan ya ɗago rinannun idanunshi waɗanda suka cika da zallan ɓacin rai marar misaltuwa ya zubasu akan p.a wanda yake gurfane agabansa cike da ɓarin jiki dana zuci.

 

“Me kake son kacemin _P.A_ kana nufin aikin da mukai ya lalace”!! yafaɗi maganar fuskarsa cike da tarin bakin ciki marar misaltuwa.

 

Wanda aka kira da p.a ne ya qara rissinar da kansa a qasa tare da kallon uban gidan nasu cikin rawar jiki.

 

“Wallahi tallahi nima ɗazu habu wakili yake sanar dani cewar aikin da mukai a Ɗawisu l.g ya lalace sannan kuma ansamu wasu ɓata garin samari sun haura cikin makarantar ƴammatah ta ɗawisun har sunyiwa guda uku fyaɗe” yakai maganar yana sadda kansa a qasa batare daya kalli uban gidan nashiba.

 

Rintse idanunshi yay harna wajan mintuna biyar kafin ya warasu yana bin _p.a_ dasu cike da tarin ɓacin rai ya ɗaga masa hannun alamun yabar masa office.

 

Cike da sassarfa _p.a_ ya miqe ya nufi hanyar barin office ɗin.

 

Tare da qara rissinawa yace. ALLAH ya taimaki _Megirma *MAS*!_ yakuma huci zuciyar ka mutumin qwarai fari mai farar zuciya sukari bakai farin banza ba yaro mai jini ajika wanda duniya take yayi ALLAH yacigaba da dafa maka adukkan lamuranka yasa maqiyanka suzama fadawanka!!

 

Yana kaiwa nan yaja masa qofar office ɗin ya fita sanin halin _mai girma *MAS* mutum marar son yawan kirari ko fadanci.

 

 

Da sauri ya koma da baya ya faɗa saman kujerar office ɗin nasa ya ɗaga kansa sama yana kallon rufin p.o.p office ɗin cike da bakin ciki yana ayyana yadda zewa ma’aikatan daya baiwa wannan contract ɗin rashin mutunci danshi mutum ne tsayayye sam baya son, son zuciya shiyasa baya zama da duk wani mutum marar amana.

 

Cike da qwarin gwiwa ya ɗauki wayarsa wadda take yashe a saman table ɗin yafara neman layi…..

 

Ringing biyu aka ɗaga daga can ɓangaren tare da cewa.”ALLAH ya taimaki _Maigirma *MAS*……..”

 

Bai tsaya jiran cigaba da maganar na cikin wayan tashiba yafara magana cike da ɓacin rai “Haba sardauna yaya zakuyi mana haka mu baku aiki amman kuyi mana almun dahana kasan dai halina kuma kasan waye ni natsani rashin gaskiya arayuwata wannan dalilin yasa waccan tafiyar ban baku aiki ko ɗaya ba” yakai maganar yana komawa ya lafe a saman kujerar daya ke kai.

 

Cike da bakin ciki wanda aka kira da sardauna ya mayar da abinda ya taso masa zuciyarsa tare da qaqalo murmushin qarya sannan ya soma bawa _Maigirma MAS_ hakuri tare da cewa shima bai san haka yaransa sukai aikinba amman gobe monday zeje yagani,

 

 

Batare daya tanka masa ba ya katse kiran cikin rashin jin dadi.

 

Kiran sakataren sa yay a waya ya sanar masa. ya cewa _p.a_ ya kai masa jaka mota ya tashi. Cikin muntuna biyar ya haɗa tarkacan sa yabar office ɗin ransa duk ajagule.

 

Dagudu gourd’s ɗinshi suka rufa masa baya tare da saurin bude masa marufin wata shegiyar mota ya faɗa cikin gajiya yana gyara links ɗin hannun rigarsa.

 

Acikin mintunan da basu wuce goma ba motarsa tabi hanyar babban titin cikin garin ƊAWISU.

 

 

Gabaki ɗaya kowa yaga yadda manyan motocin bayan motar daya ke ciki, suke gudu yasan babu lafiya dan haka jama,a sukaita matsawa suna bawa motocin hanya waɗanda aqalla zasuyi guda goma.

 

 

Bai sanar da ƴan jarida ko wani cewar ze fita ba dagashi sesu habu p.a da sauran gourds ɗinshi haka suka nufi cikin garin ɗawisu.

 

Wanda zuwa lokaci kaɗan zancan zuwan bazatan da *ƊAN MAJALISA MAI GIRMA MUHAMMAD ANWARR SAMEER ( MAS )* yay cikin garin ɗawisu ya gama cika gari wanda yasa ma’aikatan sardauna constuructions suka shiga ɗimuwa

 

Abakin tafkeken qaton gate ɗin makarantar *ƊAWISU BORDING SCHOOL* ya dakatar da drivern sa da kansa ya buɗe marufin motar tare da ziro da santala santalan fararen qafafunshi waje.

See also  Download Gidan Uncle Complete Hausa Novel

 

Cikin azama duk wasu masu bashi tsaro sukayo caa! akansa tare da rufa masa baya wanda ya taka da qafafunshi har cikin makarantar.

 

Da gudu – gudu principal ɗin makarantar tayo wajansa wadda zancan zuwansa ya kaɗa mata ciki zubewa tai agabansa tana kwasar gaisuwa sannn ta miqe tai masa jagora har wajan aikin daya bayar na kwangilar sola.

 

Zagaye yay sosai acikin makarantar sannan ya koma can wajan office ɗin principal inda aka miko masa farar kujera ya zauna akanta.

 

Da rikitattun idanunsa waɗanda suke kama dana maijin bacci ya dubi. p.c yana jefa mata tambayoyinsa masu kama dana ɗan jarida akan yadda akai har garada suka hauro cikin makarantar batare da malamai ko ita sun luraba wanda alhakin kula da students ɗin akansu yake.

 

Gumine ya tsurgo mata sannan ta soma basa haquri akan wannan lamari tare da shaida masa qaddara ce babu yadda zasuyi.

 

Taune qasan laɓansa yay yana jin tsigar jikinsa tana miqewa babu abinda yafi tsana a duniya kamar zina babban abinda yake ɗaga masa hankali yaji anyiwa ƴammata ko yara fyaɗe wallahi jiyake inda zega waɗannan garadan da babu abinda ze hana ya kashe tsinannu.

 

Ɗago idonsa yay ya kalli p.c sannan ya nemi data turo masa dukkan wasu masu ɗankwali na cikin makarantar da kuma mamomin ɗakuna dan yana son sanin asalin yadda lamarin ya faru.

 

Cike da sauri p.c ta baxa sakonsa sannan ta koma ta tsugunna agabansa tana jimanta abun aranta.

 

 

Hostel!

 

Dagudu wata baqar budurwa mai ɗan tsaho ta, taho wajan wata farar yarinya mai ɗan tsaho kaɗan marar jiki wadda take ɗaure da ɗaurin kirji ajikinta tana wanke hause ware masu kalar blue.

 

Cikin haki ta karaso gabanta.

Ɗaka mata duka tai tare da cewa.

“F.K kizo kece shugabar makaranta wallahi *ƊAN MAJALISARMU* yazo akan zancan haurowar da yaya gardi yayi kuma ya nemi da akira duk wasu masu ɗan kwalin cikin makarantar nan yanxu haka p.c tana can tana nemanki ashe kekina nan kina wanki.

 

Wadda aka kira da f.k ita ta ɗago da sauri tana kallon wadda take mata maganar cike da sanyin hali “kai lebour ni wallahi harkin bani tsoro wallahi canake wani gardin ne ai wannan murya haka”

 

Dariya lebour tai sannan ta kalli F.K malama nasanki da sanyin jiki sefa kinyi da gaske sabida kiran gaggawane dan ALLAH kada ki tsaya wannan yangar taki.

 

Tsaki F.K tai sannan ta tsame hannunta ta wanke ta nufi hanyar ɗakinsu.

 

Kwanarsu taje ta dauki qaton hijabi har qasa sannan ta dubi walida wadda suke kwana ɗaya da ita cikin nutsuwa “walida zanje kiran p.c dan ALLAH ki tsaman idomie ta kada ta jiqe takai maganar a nutse” wadda ke zaune daga gefe tana karatu ta ɗago ido ta kalli f.k.

 

“Waidaman feenah baki ci abincin nan ba tun ɗazu nifa narasa kanki tunda muka dawo daga wannan hutun naga kin sauya sanyin jikinki ya qaru kodai su baffa ne suka kuma….” kallon walidan tai cikin basarwa “nidai idan naxo mayi magana dan ALLAH ki tsaman” takai maganar tana futa daga cikin kwanar tasu.

 

Hanyar area class tai cikin sanyin jiki wai ahakama tana sauri.

 

Adai dai bakin office ɗin p.c taji sautin bugun zuciyarta yana qaruwa fiye da nada wanda qaddara tasa ta gamu dashi batare data shirya ba.

 

Addu,a tacigaba dayi hartaja qafafunta zuwa bakin office ɗin.

 

Seda ta kutsa kanta sabida yawan jama,a ga security’s kota ina ga malamansu haka ta samu ta qarasa wajan da aka ce musu su taru ta tsugunna tana saukar da kanta a qasa.

 

Yawan bugun zuciyarta da rawar jikinta dasuka tsananta sune suka saka babu shiri ta haɗe jikinta waje ɗaya tana tsukewa kamar maijin shigar sanyi.

 

Kafin taji wani daddaɗan mayen kamshin turare ya cika mata hancinta wanda take tunanin ina ta sanshi?

 

Ɗago kanta sama tai wanda adai dai wannan lokacin shima yake neman waje akan kujerar da aka ware masa dan ya zauna.

 

Cike da tsoro ta ware idanunta duka waje meya kawosa nan?”…….*ƊAN MAJALISSA BA SABO BANE AKWAI COMPLT DOCUMENTS ƊINSA MAI SO NAIRA 500 NE SEYA TURA KUƊIN TA WANNAN BANKIN 0078174806 STERLING BANK SHEDAR BIYAN TA WANNAN NUMBER 08142105218*

See also  Hajiya Gwale Hausa Novel Complete

[18/10, 12:53 pm] +234 816 362 6370: 🌹 *ƊAN MAJALISA* 🌹

( Love story )

 

 

 

*Mallakar*

_AUTAR MANYA_🌹

 

 

~~~~~~~

📚 *HOME OF QUALITIES WRITTER’S ASS*

~~~~~~~

 

_Dasunan ALLAH Mai Rahama Mai Jin Ƙai_

 

 

🅿️ *2*

 

 

Lumshe manyan idanunta tayi tare da sake warasu akansa tana jin wata iriyar nutsuwa ta shigeta kafin taji sautin bugun zuciyarta yafi nada qaruwa sosai ta shagala da kallonsa wanda takejin kamar ta dawwama a haka tana kallonsa batare data gajiyaba.

Cikin zuciyarta kuma matsanancin mamakine fall tayaya yazo cikin makarantarsu? ita data gansa a ƊAWISU GENERAL HOSPITAL har takai masa files ɗin kaka, anya kuwa shine kodai aljanine tayaya yazo a ƊAN MAJALISAR SU? Kuma ta gansa a matsayin likita wannan lamari ya cuɗa mata kanta ya hanata sukuni tabbas tana da tarin tambayoyi aranta amman babu mai bata amsarsu dan haka ta kuma jan jikinta ta tsuke tana ayyana koma dai waye shi ita taji ta gani!!

Ta cikin wutsiyar idanunta take kallon yadda yake motsa ɗan madai daicin bakinsa yanawa ɗaya daga cikin masu tsaronsa magana wadda ba lallai na nesa dashi yaji miyake cewaba.

Mintuna kusan goma suna tsugunne kafin taga p.c ta miqe tsaye tanawa baba vise magana wanda kafin hankalinta ya dawo kanta taji yana kiran sunanta.

“Nafeesa Kabeer” taji baba vise ya kira sunanta yana kuma umartarta data matso gaba ana son ganinta.

Cikin rawar jiki f.k ta miqe daman can ita bamai yawan magana bace ba sannan kuma batada sakewa acikin mutane tun fill azal balle yanzu dataga taron maza damasu ɗammara wannan dalili yasa tafara karanto addu,oi cikin bakinta harta samu ta qarasa gaban p.c ta sake tsugunnawa.

 

P.c ce ta umarceta akan ta matsa gabansa wanda faɗin hakan da p.c tai yakusan sakata ta ɗimauce bada ban qarfin addu,aba da tabbas seta faɗi a wajan.

Cike da sanyin jiki dana zuciya ta qarasa gabansa wanda yake zaune akan kujera ya ɗora qafa ɗaya kan ɗaya gefensa masu tsaronsa ne duk sun riqe bindigogi se wasu mutane daban dake bayansa suma a tsaye.

 

Agabansa ta tsugunna tare da mayar da kanta a qasa tana zana qasar gabanta da yatsun hannunta tana jin wani sanyi yana ratsata ga wata iriyar faɗuwar gaba data qaru acikin kirjinta.

Wata qwalla ta matso mai zafi tare da saka gefen hijabinta ta share a fakaice tana kallonsa yadda yay kamar bai san da ɗan adam a wajanba seda taga wani mutum ya risina yay masa raɗa a kunnensa sannan ya ɗago ya jefeta da wani shu’umin kallo mai kama dana raini da qasqanci.

 

“Ke”! yafaɗa muryarsa a daqile kamar wani basarake cike da saurin jiki p.c ta daka mata tsawa “ke nafisa ba magana ake maki ba” cikin sanyinta ta ɗago idanunta waɗanda suka soma yin jaa! sabida damuwar data taso mata ta diresu akansa tana kallonsa batare data tanka masa ba kuma batare data ɗauke idanunta daga kan nasa ba.

 

Cike da mamaki _mai girma MAS_ Yake kallon yarinyar gaban nasa wanda take yaji wani ɓacin rai ya ziyarcesa jiyana mata magana ta mayar dashi kamar wani wawa tsaki yaja kaɗan tare da lumshe idanunsa waɗanda yake jifanta da kallonsa na rainin hankali dasu kafin ya furzar da iska mai zafin gaske ganin tana son ta ɓata masa lokaci.

“Ke wace irin wawiya ce ana maki magana kinyiwa mutane banza hala bebiyace”! ya faɗi maganar muryarsa adake!!

F.k wadda ta shagala a kallonsa lumshe idanunta tai cikin muryarta mai dadin sauraro mai kama data mai jin sanyi ta fara magana “ALLAH ya baka haquri banji kaba” tana faɗin maganar taja bakinta tai gum jikinta duk ya dauki rawa sakama kon wani wawan kallon wulaqanci daya mako mata.

 

Ɗan tsaki kaɗan yaja cike da halin ko in kula yafara yi mata bayani akan yadda zasuna kula da ɗakunansu suna tsare kansu batare da sun jira malamai sunzo ba a yayin da garada suka hauro masu.

Cikin tattausan lafazi yake mata bayanin wanda idan ka kallesu seka rantse wata magana suke ta soyayya.

Abinda yafi bata mamaki yadda taga duk magana ɗaya seya lumshe idanunsa sannan yake faɗinta dalla dalla kuma yake mata maganar yadda zata fahimta sedai kuma ta lura kamar yanada ɗan saurin magana kaɗan.

See also  Zabin Shi Ne Hausa Novel Download

Har yay yagama bayanin nasa bata fuskanci komaiba illa wata karin damuwar daya kuma jefata aciki tare da shiga ruɗun rashin makama akansa haka ta miqe jiki na rawa tai masa godiya tabar wajan.

Kafin ta qarasa wajan da aka tsaidasu taji maganganu sun karade wajan akan yay masu kyautar maqudan kuɗi.

Sallamarsu akai akan su tafi se an nemusu, inda shikuma ya miqe aka rufa masa baya ya nufi wajan ganin aikin daya zuba ai acikin makarantar.

 

HOSTEL

 

Tana tafe tana haɗe hanya kamar wata zararriya haka ta qarasa cikin ɗakinsu akwanar su ta yada zango tare da tube hijabin jikinta, da gudu walida tazo ta rungumeta “wayyo shugabar makaranta naji abin alkairi _mai girma MAS_ yabamu kyautar kuɗi masu yawa sannan yasa a dauke waɗanda akaiwa fyaɗe a fitar dasu waje aga lafiyansu mudai ALLAH yasa a rarrabamana kuɗinnan kinsan halin malaman nan kowa kansa yake gyarawa”

Ganin kamar f.k bata hayyacinta yasa walida taɓata “F.k lafiyanki kuwa?” ɗago kanta tai ta kalli walida da idanunta waɗanda sukai jawur! sannan ta mayar da kanta saman gado ta kifa tana kuka kamar babu gobe…

“Subuhanallahi Nafeesa kabeer lafiyanki?” walida ta kira complt sunanta, tare da kai hannunta ta ɗagota ta jawota jikinta tana rarrashinta “Dan ALLAH feena badan niba kigayamin abinda yake damunki bana son wannan zurfin cikin naki na fuskanci tunda muka dawo wannan hutun kin rage walwala ko muqamin da aka bakine bakyaso ko agidane su baffa sukai maki wani abun?” ko idanun kakane ciwonsu suka motsa?” walida ta jera mata wannan tambayoyin tana jiran amsarsu.

Seda tai kukanta mai isarta sannnn ta ɗago fuskarta tai jawur idanunta ya qara girma.

 

“Walida na shiga uku!! walida zuciyata batamin adalciba takaini inda zan wahala takaini inda za,a wulaqantani wallahi walida sonshi nake da gaske!!!

“Miyasa aduk sanda zan gansa seya gayamin baqar magana miyasa duk sanda zan gansa senaji kamar na mutu walida sonsa ze kasheni idan na rasu kicewa kaka akan sonshine” takai maganar cikin gushewar tunani tana kuka kamar zata shiɗe.

Cikin damuwa walida ta ɗagota “feena waye wannan ki gayamin a ina yake waye mai sa,a dayay nasarar samun kamilar mace kamarki?” takai maganar tana tallafo feena ajikinta.

Jada baya feeanah tayi tana jan numfashinta.

“Walida baya sona kuma nasan baze taɓa sona ba naganshi tun kafin nasan shiɗin ƊAN MAJALISSARMU ne naso shi tunkafin nasan shiɗinne walida na haɗu dashi ranar talata da safe acikin ƊAWISU HOSPITAL naje kai files ɗin idanun kaka sabida munji sanawar za,a tallafawa marasa lafiyar idanu mutum ɗari a wannan rana shine da mukaje muka samu shiga aka bani file ɗin kaka nakaiwa babban likitan wajan daxe ɗauki hoton idanun dasauransu naje office ɗin wanda naga anrubuta *DR. ANWARR S.* ajiki da manyan harufa da sauri na tura qofar office ɗin danna shigar da, qafafuna sedai kash nai rashin sa,a domin hango wani haɗaɗɗan kamilallan mutum danai zaune da glass a idanunsa yana rubutu da sauri da sauri da tulin takaddu a gabansa,ban tsaya kare masa kallo ba sedai gani guda nai masa yasami nasarar sace zuciyata, dirin tashin masifarsa acikin dodon kunnena shiya saka na yada file ɗin na gudu daga wajan .”shinke mahaukaciya ce daxaki shigomin office babu permision!! naji saukar amon daddaɗar muryarsa da sauri akaina yana surfan masifa wallahi walida tunda na baro asibitin haryau ban kuma ganinshiba se yau kuma kullum senayi mafarkinsa” takai maganar tana cigaba da kukanta.

 
Lindsey Hill, the San Diego woman who accuses Trevor Bauer of sexual assault
.
.
Littafan Hausa Guda 1000 Download

.
.
.
Gidan Uncle Hausa Novel Complete

.
.
.

Kalaman Soyayya Masu Dadi
.
.
.

Download Izzar So Complete Episode
.
.
.
tsofaffin hausa novels wattpad

Sannan ta cigaba…..

“Seyau kawai na gansa wai ashe shine ɗan majalissarmu mutumin danaji kowa yana yabonsa da fadar alkairinsa amman nikam senaga kamar ya tsaneni yauma seda ya kirani da wawiya, walida yaya zanyi nasanshi na shaqu dashi harma ya soni sannan ina son nasan tayaya ya zama ɗan majalisarmu bayan ni a likita na sanshi………!!

*ƊAN MAJALISSA BA SABO BANE AKWAI COMPLT DOCUMENT ƊINSA NAIRA 500 MAI SO SEYA TURA TANAN 0078174806 Sterling bank shedar biya tanan 08142105218*

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top