Hausa Novels

Dangan taka Hausa Novel Complete

Dangan taka Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Saukowanshi kenan daga stairs yana kiran ammi Wanda take kitchen tana hada breakfast.

karasawa yayi cikin kitchen ba tare da ya kula masu aiki su biyu da suke gaisheshi ba,a hankali yace ammi I’m running late pls a bani breakfast dina yunwa nakeji.

Murmushi ammin tayi tace “to sarkin ci saura kadan na karasa”.dan murmushi Yayi Wanda ya kara masa kyau, yace me’ake dafawane ammi? chips ne ameenu tafada tadan murmushi.

Sai ya dan bata fiska ya langwabar da kanshi.Alamun baison sunan kuma gashi a gaban masu aiki.murmushi tayi tana shafo kanshi sannan tace “sorry son”.

Ahankali yace its ok ammina,ina yaran nan ne ma.Najisu shiru.

ajiyar zuciya ta sauke tace fiddausi da sulaiman sun tafi gidan baffanku,nuruddeen kuma ya fita tun da dazu da asuba sabida yana da surgery dazaiyi da safe.da sauri yace omg ammi yakamata nima na tafi i’m running late.

Tace abincin fa?karka tafi pls baka sa komai a cikinka ba.sai ta debo fried chips a plate ta bawa asabe ta kaimasa dinning.

Duba agogon hannunshi yayi ganin da dan sauran time sannan ya sauke ajiyan zuciya ya wuce dinning din cikin falo.Already asabe ta ajiye masa tayi masa setting din komai,a hanzarce ya dan ci kadan ya kurbi tea ya ajiye kofin sannan ya dauki soft tissue ya goge bakinsa da hannunsa.

Mikewansa yayi daidai da fitowar ammi daga kitchen ta barsu asabe su karasa goge komai da akayi amfani dashi.ammi tace son ya akayi baka ci duka na.

Yamutsa fiska yayi yace ammi nayi latti wlhy i have to go.matsowa yayi ya dan sunkuya ya mata peck a kumatu yace bye sweet ammi saina dawo,.

cike da jin dadi ammin tace “Allah kiyaye hanya son.

Pls kayi addu’a and be careful,Bye take care.

Ficewa yayi ya isa wurin bakar “Mercedes benz c class” sabuwa dal kaman ba a hawanta.

Shiga yayi ya kunnata sannan ya saita hancin motar izuwa babban gate din gida wanda ya gama haduwa.Horn ya danna da sauri baba arii mai gadi ya fito bude masa gate ya fice. yana isowa ma’aikatanshi mai suna “Mai takobi business holdings”

Shahararren kamfanin da yayi suna a fadin duniya wanda ake ji dashi a kasar Nigeria dama kashashen ketare. da sauri PA’nshi ta iso wurinshi cikin karairaya tace welcome sir tare da karba masa jakarsa.

What are the schedules for today.Cikin iyayi da rausaya tace”sir you have meeting with flames enterprises today da misalin 9:30,sannan akwai baki daga china dasuke son su gana dakai bayan meeting din,akwai kuma investing rice bags da zasu shigo anjuma da misalin karfe biyu.

Duk suna tafiya take masa wannan bayanin batareda ya kalli gefenta ba, yana latsa wayanshi kirar iphone 13 pro max.sun iso wurin lifter din da zai kaisu saman bene na karshe inda office dinshi yake.

ya danna floor dinda zai kaisu sannan suka shige,haneefa kam ganin bai kulata ba yasa tai shiru bayan ta gama masa bayani.

Daman inda sabo yaci ace ta saba da wannan basarwan nashi.suna isa elevator din ya bude zuwa wani kata faren filin aiki inda kowa ke zirga2.

mustapah shigo kuwa? da azarbabi ta amsa eh tundazun yashigo, wuceta yayi yanufi office dinsa da ya gama tsaruwa sosai,komai neat ga daddadan room fresher na tashi hade da sanyin AC.

a gaban personal table da chair dinsa da kuma na attendant guda biyu Wanda suke gaban table suna fuskantan juna din akwai wasu sofas da dan karamin center table a tsakiya sai ya zama kaman mini palour a wurin.ga water dispenser a can gefe.sai cupboard din da kenan a rufe da alama office files ne a ciki.

ba wani tarkace a office din, komai yayi tsari kuma yayi kyau.cire suit dinshi yayi ya rataya a saman chair dinsa,ya bar red long sleeve din ciki da tie.ya zauna a saman chair yana jawo laptop dinshi gabanshi ya fara operating dinshi cike da kwarewa.Bai juma da farawaba aka bude kofar office din.dagoda sleepy eyes dinshi yayi domin ganin wayene.

 

 

 

Name: [DANGAN TAKA HAUSA NOVEL ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: November, 2021

 


Leave a Comment

error: Content is protected !!