Kannywood

Darasi Ga ‘yan Tiktok: Ga abinda yan uwan marigayiya Daso Suke Bukata

Darasi Ga ‘yan Tiktok: Ga abinda yan uwan marigayiya Daso Suke Bukata

Darasi Ga ‘yan Tiktok

An tabbatar da sauke shafin Instagram da Tiktok na marigayiya Saratu Gidado (DASO)

Sannan ‘yan uwanta suna rokon al’ummah duk wanda yake da wani bidiyo nata wanda bai dace ba da tayi a Tiktok ayi deleting 

Wannan darasi ne mai girma ga ‘yan Tiktok wanda suke yada abinda bai dace ba, ba shakka mutuwa sai ta bi ta kan kowa, muyi kokarin barin abin alheri a kafofin sada zumunta ba wanda za’a zo ana rokon a goge ba bayan mun mutu

Hakika Marigayiya Daso tayi wasu abubuwan da basu dace ba a Tiktok lura da shekarunta, yanzu gashi ‘yan uwanta na neman alfarma ga duk wanda ya mallaki bidiyonta ya goge

Muna fatan Allah Ya yafe mata kura-kuranta, Ya   sa tana cikin Rahamar Allah

Leave a Comment