Dare da duhu Hausa Novel

Dare da duhu Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

DARE DA DUHU

 

_Bright pens of✍🏾_

Nimcyluv

Ayushercool

Zee kumurya

 

1……

 

 

 

 

 

Saukar ruwan saman, bai hanashi tafiya da sauri a filin Headquarter, dake nan Abuja ba. Cikin izza, taƙama, da taurin zuciya irinta sojoji, yake taka ƙafafuwan nasa, ruwan na sauka da ƙarfi a jikinsa, da ka ganshi kaga ingarman namiji.

 

Gaba ɗaya sansanin sojojin cike yake, da manya da ƙana nan sojoji. (Part of Nigerian Armed forces headquarters Abuja, Motto (s) victory is from God Alone!”.

 

Gaba ɗaya sojojin dake cikin Headquarter ɗin, basu damu da ruwan dake sauka kamar da bakin ƙwarya ba, wasu na tsaye, wasu na zaune wasu kuma suna abinda ya shafe su, wasu kuma suna in da babu ruwan suna shan Cigarettes (sigari).

 

Tun yana tafiya da sauri har ya fara daidaita tafiyarsa ,wanda daman hakan al’adar sa ce, duk inda ya gilma cikin Headquarter ɗin hannu ake sara masa zuwa sama, alama dai shi ɗin Babban mutum ne, matsayi mai girma gareshi a cikin sojojin.

 

Wani office ya nufa cike da nutsuwa, yana zuwa aka bashi hanya ya shige, yana shiga office ɗin ya ƙame!.. tare da ɗaga hannunsa sama alamar girmamawa da masu ɗamara kewa junansu.  Sojan da yake zaune sanye da kaaki, yayi Murmushi cikin sakin fuska yace

 

“Have a seat..” yai Maganar yana nuna masa kujera.

Kamar ba zai zauna ba, se kuma ya zauna saman Kujera. General Ibrahim A.M ya kalli matashin saurayin dake gabansa kafin yace “Munyi magana da Chief of Army staff, akan Operation da za’a fita, aiki ne mai wahala kuma bama son, Kidnappers ɗin su samu information na aikin nan, dan opretion ne me hatsarin gaske, yana da kyau ku kula, bamu da tabbaci kowa zai dawo da rai acikin ku, dan kun san komai dai”

 

Matashin dai kansa yake a ƙasa, yana sauraren General babu alamar zai magana, ya tattara dukkan nutsuwarsa yana sauraren shugaban nasa.

General Ibrahim ya buɗe wani file yana dubawa kafin ya kalli saurayin yace

 

“Hope you are ready for it, and  kayi sallama da iyalanka?” .

 

Sai a lokacin Matashin saurayin ya ɗaga idanunsa wanda sukai ja sosai ya kalli General Ibrahim, kallon da yake masa yasa General Ibrahim faɗin “Oh, I forgot  you just came back from Zamfara yesterday”

Matashin dai bai ce komai ba, da Idanu kawai yake bin General.

 

General Ibrahim yace “Zaka iya tafiya, jirgi na jiranku a airport, and airforce zasu rigaku zuwa ku kula da kyau akan dukkanin bayanan da zasu baku, da kuma umarnin da zaku samu daga garemu”

 

Matashin saurayin ya miƙe tsaye yace “ok sir” tare da sake sara masa, sannan ya juya, yana tafiya a hankali har ya fice daga cikin office ɗin General Ibrahim.

 

Cikin nutsuwa General Ibrahim ya ɗauki Wayarsa tare da danna wasu lambobi, babu jimawa aka ɗauki wayar daya kira, ƙasa ya yi da Murya yace

 

“Akwai kyakykyawan labari” daga cikin wayar wata shaƙaƙƙiyar murya ta bayyana akace “Mene labarin?”

 

General Ibrahim ya ce “Chief of Army staff, ya bada umarni ga Sojojin da suke Headquarter na nan Abuja zuwa Naija state, kai tsaye kuma cikin Dajin Zugurma in da kuke tsare da yaran nan, kuma a wannan karon sun samu cikakken ikon yin harbi,  umarni ne daga NAC. _Nigerian Army council_”

 

Mutumin da General Ibrahim ya kira ya yi dariya kafin ya ce. “Ganganci haihuwa da damuna, a tunaninsu zasu Iya ƙwace ƴan matan da mukai  kidnapping ne? Bayan gwamnati ta hanamu abinda muka buƙata?”

 

General Ibrahim yace “Na kira dai dan in sanar maka da zuwan su, a Kowane lokaci sojojin sama zasu tsinkayi dajin, nine zan tsara komai na Operation ɗin tare da jami’anmu na nan Naija state,  zan sanar maka da duk wani arrangement na yaƙin, kaga kuna da damar da zaku samu galaba a kansu, dan haka se ku shirya zuwansu”

 

Mutumin ya yi dariya yace “Daman ance da ɗan gari akanci gari, mune mutanan banza, kai kuma maci amanar ƙasa”

General Ibrahim ya yi Murmushi yace “To Rayuwar sai da haka, in ba haka ba a banza za ka gama aiki Kai retire amma na abinci ya gagareka, ko a kashe ka a banza gurin kare ƙasar da ta gaza biyawa masu bata tsaro buƙatunsu, dan haka zan tura maka account number, ka bani share ɗina saboda na samu labarin wasu daga iyayen yaran sun baku kuɗi akan ku sakar musu yaransu”

 

Mutumin  yace “Zanci kaza kazanka, a gidan uwar wa zanga pos ko Networkina cikin tsakiyar jeji?”

 

Ibrahim yace “Haka ne, ka shirya min kuɗina  zan san yadda zan in karɓa, dan Ina da buƙatarsu” yana faɗin hakan ya kashe Wayarsa, yana jin akan kuɗi babu abinda ba zai ba.

 

 

Tabbas da ɗan gari ake cin gari.

 

 

Matashin na fitowa daga cikin office ɗin General ya nufi wani waje domin ɗakko jakarsa, tsaye ya yi ganin wata budurwa sanye da kayan sojoji ta nufu inda yake, hakan yasa ya ƙara haɗe ransa sosai. Budurwar mai suna Salima tace

 

“Haba Captain at least yau kayi min Murmushi, saboda kai nabar Maiduguri nazo Abuja” Wanda aka kira da Captain ɗin, ya kalli Salima se kuma ya ɗauke kansa, Salima ta haɗe rai tace

 

“Ban san me nayi maka ba, sama da shekaru biyar nake bibiyar ka, tun kafin kayi Aure” Captain ya gyara tsaiwa cikin tsare gira, murya a kaushashe yace “Bana harka da mutunan banza, ba zan mu’amala da karuwa kazar kowa ba” Yawo mai ɗaci Salima ta haɗiye tace “Yanzu har akwai mutumin kirki a cikin sojoji? Gashi nan kullum tara mata kuke, kuma mu matan dan mun nemi maza sai ya zama iftila’i, nifa a yau kace kana so na, zan zama iya taka kai ɗaya ban damu da matan da zakai harka dasu ba, indai zaka biya min tawa buƙatar”

 

tsaki Captain yaja tare da ratsa wa ta gefenta ya shige.. duk inda ya gilma sai yaga mace da namiji manne da juna tare da sheƙe a yarsu, ko kunya babu..

 

Sanarwa aka fara yi, wanda ya Sanya Captain ɗaukan jakarsa, ya nufi filin wajan, Salima taso hadda ita za’ai posting zuwa Naija state.

 

 

Farar safiya ce, A ranar  Asabar wanda yayi daidai ga 25 ga watan Mayu, shekara ta dubu biyu da goma sha ɗaya. Jirgin Sojoji ne (Helicopter). Yake shawagi a saman dajin Zugurma na jihar Naija state. Sosai jirgin yake zaga dajin ta sama, sautinsa ya cika ko ina a dajin, ya dinga bada wata irin amsa kuwwa.

 

Ƙarfe 12 daidai, jirgin su Captain na sojoji ya sauka a filin tashi da saukar jirage na Niger state, cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala duk wani shiri da za suyi, suka nufi cikin dajin.

 

 

Tafe suke a cikin manyan motocin yaƙi, ciki har da egwa yayin da wasu suke tafe a ƙasa, suna tafe suna ‘yan iface ifacensu na sojoji, kafin samu umarnin cewar su tsaya su yada zango a wani guri, kasancewar sunyi tafiya me nisa, ba tare da jin wani ƙwaƙwaran motsi a dajin ba.

Daga cikin ɗaya daga cikin motocin, Wani matashi ne zaune, a kujerar mazaunin direba, Zame abin kansa yayi a hankali,  yana fitowa daga cikin motar, Idanunsa akan wani matashi wanda yake gyara zaman bindigar sa, cikin rashin ko in kula na sojoji ya nemi waje ya zauna. Musulman cikin su na ƙoƙarin yin alwala suyi salla, wasu suna cin Abinci yayin da wasu suka keɓe suna shan sigari.

 

Captain Denial ya buɗe jajayen idanunsa akan wani soja yace “Ka gama naka aikin, tun da ka kawo mu cikin wannan jejin” ya faɗa cikin harshen turanci.  ya shafa kansa yace

“War is not mine”

 

Captain Denial ya yi Murmushi yace “You go see” ma’ana zaka gani!.

 

Duk sun sauka daga motar, se wani soja wanda tun da aka sauka cikin dajin bai ɗago kansa ba, balle yayi magana. Daniel ya kalleshi kafin yace

 

“Captain Khamal” wanda aka kira da Captain Khamal ɗin, ya ɗago kansa a hankali, Baƙi ne shi sosai, irin baƙin nan mai kyau da kuma ɗaukan Idanu, ( _He’s dark-skinned yet handsome_ ).

Kana ganinsa kasan bashi da son wasa, zuciyarsa a tsaye take! Tsayyen mutum akan ra’ayinsa, fuskarsa nan tasa a ɗaure take koda yaushe. (But Friendly to his family).

 

“Akwai matsala ne?” Captain ya Girgiza kansa, yana ƙoƙarin sanya rigarsa ta uniform ɗin soja.

 

Ɗaya sojan ya nisa yace  “Wannan  yaƙi ne mai hatsari sosai, idan a kai nasara  zaka iya samun matsayi mai girma, saboda kana ƙoƙari sosai akan harkar tsaro ka san aiki sosai, akwai yiwuwar ka samu ƙarin matsayi me girma, amma naga kamar baka farin ciki?”

 

 

Captain Khamal ya ware manyan idanunsa akan Jamil, cikin rashin damuwa yace

 

“Ihu zan tayi ke nan? Saboda na fito

yaƙi, za’a ƙaran girma? Ko mene?”

Jamil ya ɗaga kafaɗa tare da watsa hannunsa yace “Kada ka gayan ba daɗi Malam, ƙilan masifa ka haɗawa kanka, rabonka da Matarka watanni wajan biyar kenan, dole ka rasa walwala ga matan nan birjik kawai ka rage zafi, gaba ɗaya duniyar nawa take daga kano sai Abuja fa, amma ka takure kanka kamar wani gunki” Taɓe baki Captain Khamal ya yi yana gyara zaman bindigar sa, ganin yayi masa banza yasa Jamil faɗin “I advise you, as you best friend, not as coulliqe”.

 

Captain yaja tsaki yace

“Ko kaɗan, mahaukacin banza ba abunda kake tunani bane”

 

Jamil ya ware idanunsa yana ƙoƙarin hana kansa dariya, ganin yadda Khamal ya hayyayaƙo masa, amma ya san tastuniyar gizo ba ta wuce ƙoƙi yace “Nine mahaukacin? Wallahi akwai wata yarinya tana zuwa gidana kullum, kawai zan bar baka ita, in mun koma Abuja” tsaki Khamal yaja yana yin waje yana faɗin “Dana aikata zina, gwara na mutu” yana faɗin hakan ya fita daga cikin motar. Jamil yabi bayansa da kallo yana Mamakin ƙarfin imani da haƙuri irin na Khamal, da yawan sojoji suna da hanyar ragewa kansu damuwa, amma banda Khamal da ya kasance me tsantseni.

 

Captain babban matsayi ne a cikin sojoji. A rank in the military and maritime service, and the highest-ranking company officer. A Captain gets three vertically aligned silver stars on the shoulders. This is the highest rank among the tactical troop organization. Idan ka shige matakin Captain ka fara hawa babban matsayi  a Nigerian Army council (NAC).

 

Captain Khamal yabi cikin dajin da kallo yana mamakin girman da yake dashi, ta ina zasu fara lalubar waɗan nan ƴan matan? Zasu koma gida duka da ransu ko yaya ne? Yana tsaye hannunsa zube cikin Aljihu gaba ɗaya jikinsa kayan yaƙi ne, Daga baya yaji an dafa shi da sauri ya juya yana zare Bindiga, Captain Denial yayi Murmushi yana busa hayaƙin sigari yace

 

“Kai da kake a daji ai ba kai babu tsoro” Khamal dai ya taɓe baki yana jin warin Tabar na juya masa ciki, Denial ya ɗauki photo daga cikin aljihun Wandonsa ya miƙewa Captain Khamal photon yace “Ka ajjiye a wajanka” A hankali Captain yake bin photon da kallo ganin photon mace da kuma ƙaramar yarinya ɗauke a hannunta, cikin rashin fahimta yace. “me zan dashi?” Denial yace “Koda zan mutu a nan, ka bawa matata domin jikina yana bani ba kowa zai bar dajin nan da ransa ba a cikin mu, za’ai artabu duba da information ɗin da muka samu akan ‘yan bindigar”

 

Khamal kallon Denial kawai yake, ba tare da yace komai ba ya saka photon cikin aljihun Wandonsa.

 

Tunda suka sauka cikin jejin basa jin motsin komai sai na kukan mugwayen dabbobi, A hankali Khamal ke tafiya yana zuwa wajan wata Bishiya ya yi saurin ɗauke kansa, saboda ganin Denial da yayi tsaye da wata Sojan mace suna murje jikin juna, ko tsoran a kawo musu hari basa yi.

 

Ya bar gurin yana jin ɓacin rai akan abunda ya gani, ya koma in da sauran sojojin suke,  Jamil ne yace “Captain yanzu idan ka samu nasara shi kenan ka daina fita yaƙi?”

Captain ya ɗaga kafaɗa alamar bai sani ba, waje suka nema suka zauna, suna kallon yadda ake ta haɗa kayan yaƙi da alama abokan harin nasu basu farga dasu a dajin ba, ko kuma suma duk cikin irin na su shirin ne ba wanda ya sani sai Allah.

 

Jamil ya ɗauki Wayarsa zai vedio call da watsastsiyyar budurwarsa amma babu network gaba ɗaya cikin dajin, sai kawai ya ɗauki pen da paper ya fara Rubutu, yana tsaka da Rubutun suka fara jiyo ƙarar  bindigogi ta ko’ina.

 

Garin sauri Jamil ya danƙawa Captain paper hannunsa. Kafin kace wani abu dajin ya ƙaraɗe da ƙarar Bindigu.

 

Cikin azama suma zaratan sojojin suka fara maida martani, tare da fara sakin harsashi cikin ƙwarewa da dakiya irin ta aiki, kan kace kwabo amsa kuwwar sautin bindigogin ya karaɗe dajin gaba ɗaya.

 

Sun kwashi dogon lokaci suna bata kashi, babu Sallah ga Musulmin cikin su babu abinci, hankalin duka sojojin a tashe ganin an fara kashe su ana neman aci galaba a kansu, ba tare sun kai ga in da ‘yan mata suke ba.

An raunata da dama daga cikin sojojin, bayan komai ya lafa nan likitocin cikinsu suka fara aikin ba su taimakon gaggawa.

 

 

Cikin dare kowa ya ɓoye a inda yake, wayar Khamal ya fara haske da mamaki yake kallon wayar ganin screen ɗin wayar ya nuna sunan _My wife_ har zai katse sai ya tuna rabon da yayi waya da matarsa wata biyu kenan ciff. Bashi da tabbacin zai bar nan a raye, a nutse ya ɗaga kiran yana faɗin “Hey Beb…” Daga can Garin Kano matar Khamal mai suna Na’ima tace

“Hankali na, yaƙi kwanciya Dear” shiru yayi mata saboda motsin da yaji a daf da in da yake, A hankali Na’ima tace “Nayi kewarka tare da Babynka dake cikina, gaba ɗaya hankalina a tashe yake, ga bana samunka a waya, bana son wani abu ya sameka” idanunsa ya lumshe cikin ƙasa da murya yace “I miss you, ki kula, ina aiki ne yanzu” yana faɗin haka ya kashe wayar baki ɗaya.

A hankali ya fara tafiya a ƙasa, yana jan cikinsa a ƙasa zuwa inda yake hango mutum a kwance, mamaki ya kama shi ganin wata matashiyar yarinya kwance cikin jini se numfarfashi take, duk an yage suturar jikimta, da alamar fyaɗe akai mata, ba mutum ɗaya bama, saboda yanayin da take yafi ƙarfin ace mutum ɗaya ne yai mata.

 

Yarinyar ta kama hannun Khamal ta riƙe sosai muryarta na rawa, ganin ta kasa magana gashi se rirriƙeshi take yasa Khamal ya ɗora kunnansa a bakinta, A hankali yarinyar tace

 

“Ya…Ya… Yaaya” sai kuma tai shiru numfashinta na fisga da ƙarfi, tana ƙanƙame hannun Khamal tace “Basu da imani, basu da tausayi, kada ka barsu Yaya, kada ka barsu Yayaaa in ba kuyi sauri ba sauran ma haka za suyi musu, fyaɗe suke mana” ta ƙarasa maganar tana shaƙuwa.

A kiɗime Khamal ya shiga girgiza yarinyar amma ina tuni rai yayi halinsa, wani irin numfashi ya fara fitarwa jikinsa ya ɗauki rawa, yana da tabbaci tana ɗaya daga cikin ƴan matan da aka sace, runste idanunsa yayi a hankali ya rufe mata Idanunta tare da jan zanin jikinta ya rufeta, har yanzu tana riƙe da hannunsa, wani irin baƙin ciki yana ratsa zuciyarsa, ace a ƙasarka amma ranka da mutuncinka ba a bakin komai yake ba, kai mutuwar wulaƙanci irin wannan saboda son zuciyar wasu tsirarun mutane.

 

Cikin dare Khamal ya dinga bincikar dajin, yana zagawa da map ɗin da ke hannunsa, da yake akwai hasken farin wata.

A haka Khamal ya gano suna daf da in da yaran suke, saboda hayaniyar da ya dinga jin tana tasowa nesa kaɗan da in da yake, dan haka cikin ƙwarewa irin ta aiki Khamal da jama’arsa suka ƙarasa in da suke, Nan da nan suma suka farga, suka fara musayar wuta, wasu daga ciki ga yara a hannunsa,wasu kuma jikinsu duk jini alamar ba’a jima dayi musu fyaɗe ba. Yaran suna a matuƙar galabaice.

 

A daren su Captain basu iya bacci ba, duk yawan bataliyar nan ta sojojin, an kashe da dama daga cikinsu, an illata wasu, a daren suka kama wasu daga cikin ‘yan ta’addan yayin da wasu daga cikin su suka samu nasarar tserewa zuwa cikin dajin.

 

Sanyin safiyar yasa Captain Miƙewa yana tafiya a hankali, suka tattare ‘yan matan guri guda, duk sun galabaita saboda wahala, wasunsu ba su da lafiya wasu babu suturar kirki a jikinsu, nan sojojin suka fara yiwa ‘yan matan jagora dan fitar da su daga cikin sarƙaƙiyar dajin, yayin da wasu sojojin ke ta kwaso gawarwakin’yan uwansu da aka kashe.

 

“Khamal” aka kira sunansa, da sauri ya juya ganin Jamil kwance cikin jini, anyi masa harbi kusan guda uku, jikinsa na rawa yace “Jamil” Jamil ya girgiza kai yace “Khamal ina maka fatan tsira da ranka, kaje wajan matata kace ta yafe min, wlh ban san adadin ƴan matan da nayi mu’amala dasu ba, yanzu haka ina ɗauke da Hiv, ina da tabbacin matata ma tana dashi, bata san hawa ba bata san sauka ba, na ɗora mata mugun ciwo” Khamal ya Girgiza kansa yace

“Kayi salati” Khamal ya fara salati Jamil yana maimaita wa, a nan jikin Khamal Ubangiji ya ɗauki ran Jamil….

 

Kwanan su wajan uku, cikin dajin gaba ɗaya kuma sun kwashe ƴan matan an fita da su, a kwanaki ukun nan, kullum se sunyi musayar wuta da ‘yan bindiga.

sojojin duk sun ƙare, se wanda ba’a rasa ba, da gudu Major yake tafiya ganin wata budurwa yashe a ƙasa, kafin ya Ƙarasa wajanta yaji ance

 

“Kaiiii” Aka daka masa tsawa da karfi, Juyawa yayi ya ware idanunsa ganin wani riƙe da bindiga zai harbeshi, Denial ya tare harbin hakan yasa aka harbi Denial a ƙirji…

 

Captain ya zaro bindiga ya fara Harbin ɗan ta’addan , sai daya kashe shi sannan ya nufi wajan Denial yace “Mene yasa haka Denial?” Denial ya girgiza kai yace “Kai na musamman ne, gwara na mutu kai ka rayu, bana faɗa maka ba? Daman nasan mutuwa zan, kada ka manta da abinda na baka, a cikin mu akwai maciya amanar ƙasa, amma kai da gaske kake naka aikin, Khamal na baka amanar iyali na.. zaka iya, nasan zaka iya ka kula dasu”

 

Yana faɗin hakan rai yayi halinsa, wani irin ihu Khamal ya saki mene yasa haka ke faruwa? Su sojoji a haka rayuwarsu zata ƙare ne? Sunyi shiri na gaske akan faɗan nan, amma kamar ‘yan ta’addan sun san da zuwansuz duk sun samu nasarar kashe zaratan sojoji masu ƙoƙari, ciki har da makusantan abokansa, Miƙewa ya yi, gaba ɗaya jikinsa jini ne kayansa duk sun yage, ga yunwa, ƙishirwa.

 

Yana zaune a ƙasa yaji shawagen Helicopter, da alamar General ne ya ƙaraso,yasan ɗauki gaggawa aka kawo musu, kasa Miƙewa yayi har sai da wani soja yazo wajansa ya ɗaga sa, yana faɗin “Komai yazo ƙarshe Captain”

 

Sauran gawarwakin aka kwashe zuwa cikin wata babbar motar sojoji, raguwar ‘yan ta’addan da sojojin suka kama suka ɗaure, suma aka zuba su cikin mota, suma sauran mutanen da suka tsitstsinto anyi garkuwa da su, a wata mota aka zuba su, Khamal ya miƙe ya na tafiya a hankali, kamar daga sama kunnansa ya fara jiyo masa kukan ƙaramin yaro,  tsaye yayi, yai shiruu, jin kamar ba kuka bane yasa ya cigaba da tafiya.  yana ƙoƙarin sanya ƙafarsa cikin mota, ya ƙara jiyo sautin kuka, a wannan karon kuma ya tabbatar gaskiya kunnansa ya jiyo masa, kuka ne da gaske, fasa hawa motar yai, sauran sojojin na kiransa amma be kula ba, a hankali yake tafiya jiki a sanyaye da ƙyar yake ɗaga ƙafarsa saboda wahala, ganin baiga kowa ba sai ya fara tunanin ko aljanu ne? Ko kuma kukan wata dabbar ce, wani kukan ya sake jiyowa da sauri ya juya zuwa inda yake jin kukan, ya ƙara nausawa cikin dajin, ware idanunsa yayi kan ƙaramar yarinyar dake zaune a ƙasa ta ƙanƙame jikinta waje guda, Idanunta rufe da alama gaba ɗaya a firgice take, Khamal ya ware idanunsa akan yarinyar gaba ɗaya ba zata shige shekara uku ba (3Years) fara ce sosai kamar buzuwa kamar kuma Balarabiya, tafi kama da ruwa biyu (Half-caste) domin gashinta wanda yafi ƙarfin kanta ya sauka har ƙasa kasancewar a zaune take, farar fatar jikinta tayi baƙi sosai, ga raunuka a jikinta..

 

Sosai Khamal ya girgiza da ganin ƙaramar yarinya a cikin jejin nan, sai ya fara tunanin ko dai Aljana ce?ko a cikin matan da akai kidnapping take, Samun kansa ya yi da cewa

 

“Ke” shiru tayi masa sai kukanta take tana ƙanƙame jikinta, cikin rashin sanin cewa yarinyar nada ƙarancin ji a kunnanta yasa Khamal ƙara cewa “Kee” nan ma tayi masa shiru.

 

“kada ka kuskura ka ɗauki yarinyar nan, ita ba kidnapping ɗinta mukai ba, ita tamu ce, rainonta za muyi, ‘yar mu ce” Cewar wani mutum da ke tsaye, hannunsa riƙe da bindiga.

 

Captain Khamal ya kalli mutumin sai kuma ya kalli Yarinyar, kana yaja baya kaɗan yace “To me zan da ita tun da taku ce?” Ya faɗa yana Juyawa, mutumin ya sunkuya zai ɗauki yarinyar kenan yaji saukar bullet a bayansa, ihu ya saki yana faɗuwa ƙasa, cikin zafin zuciya Khamal ya fisgo Yarinyar yace “Keeee….” Sai a lokacin taji saukar muryarsa a kunnanta, fararen idanunta ta ɗaga, wanda yasa zuciyar Khamal bugawa, Yarinyar ta washe bakinta ta nufi wajan Captain Khamal tace

 

“Abbi…” Ta faɗi hakan tana ƙanƙame ƙafafuwan Khamal, “Abbi?” Khamal ya maimaita a zuciyarsa a fili kuma sunkuyawa yayi ya ɗauki yarinyar a kafaɗarsa, kai tsaye ya nufi in da motocin su suke da ita yana ƙoƙarin shiga cikin mota yaji saukar wani abu mai kama da kibiya ko mashi a gefen cikinsa, a hankali kuma yaji zafin  saukar abu a jikinsa tsananin azaba yasa sam bai kawo cewa harbinsa akai ba, ƙafarsa ya ɗaga da ƙyar yana sauke Yarinyar muryarsa na rawa yace

 

“Shiga ciki” watsa hannunta tayi tace “Abbi” alamar bata gane zan can nasa ba, da hannunsa yayi mata alamar ta shiga cikin motar, sauran sojojin na ciki basu san meke faruwa ba, bayan ta shiga cikin motar Khamal ya ɗaga ƙafarsa da ƙyar zai shiga cikin Motar ya ƙara jin saukar wani harbin a gefen cikinsa…

 

😂😁 Ya kuka ji salon Bright pens?….. Daban ne… Share share share as so much as you can!.

#Nimcyluv

#Zee kumurya

#Ayushercool

[21/09, 10:34 am] +234 803 192 1625: *✷ DARE DA HUDU ✷*

 

_Bright pens of✍🏾_

Nimcyluv

Ayushercool

Zee kumurya

 

 

 

 

Ƙirƙirarren labari me, ba mu yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba, idan yai kamanceceniya da rayuwar wani ko wata Arashi ne.

 

 

Littafin DARE DA DUHU haƙƙin mallakar mu ne, bamu yar da a juya shi ta kowace siga ba, ko a sashi a wata kafa ba ba tare da izinin mu ba.

 

 

BISMILLAHIRAHMANIRAHIM

 

 

ELEGANT ONLINE WRITER’S

 

 

P2…..

 

 

 

Jin sautin harbin da ya sake tashi ne, ya sa yarinyar fitowa daga cikin Motar da sauri ta tsaya tana kallon Captain.

 

Jini ne ya shiga zuba a gadon bayansa, ga na cikinsa da yake zuba shi ma, cike da jarumta irin ta soja yake ƙoƙarin tsayuwa kan ƙafafunsa, ya kuma ƙoƙarin ya yunƙura ya ɗaga ƙafarsa, sai dai yaji jikinsa yai masa nauyi, ga wani danshi da yake ji ya jiƙa masa kaya, sai a lokacin ya fuskanci harbi ne, a nan take duhu ya maye gurbin hasken ranar da ya haska dajin a idon Captain, a hankali yai baya ji kake timm ya faɗi ƙasa.

 

Sam ba ta san me ya faru da mutumin ba, wanda ya karɓo ta a hannun waɗan nan mutanen, sai dai ta zuba masa manya manyan idanunta, sai jujjuya ƙwayar idanunta take a kansa.

Sautin Wani harbin ne ya kuma tashi, cikin azama wani soja ya fito daga cikin Motar, ya danƙi yarinyar ya kwantar da ita flat a ƙasa, ya shiga danna nakiyar ta sa bindigar shima a saitin in da ƙarar harbin ke tasowa.

Sautin Command ɗin Commander Land army ya jiyo nesa kaɗan da in da suke, yana bawa tawagar sojojin umarni, cikin dakakkiyar muryarsa dake amsa kuwwa a dajin, tare da ƙarar motocin sojojin na yaƙi, hakan ya tabbatar masa, da an turo wasu sojojin domin kawo musu ɗauki.

See also  Yadda Ake Korar Shaidanun Aljanu Daga Gida Ko Gona Ko Fili

 

Nan da nan ƙarar harbi ya sake cika dajin, tamkar za’a tsaga dajin.

 

Tai lamoo a ƙasa, duk wannan ba ta kashin, da ƙarar bindigogin da ke tashi, can ƙasa ƙasa take jiyo sautin kaɗan kaɗan a cikin kunnenta.

 

Gaba ɗaya hankalinta yana kan mutumin nan da ya ɗakko ta, da yake kwance a ƙasa, ba ya ko motsi.

 

Ba tare da tunanin komai ba, ta miƙe zata nufi in da yake ƙasa a kwance, sojan nan da ya kwantar da ita flat a ƙasa, ya fizgota cikin tsawa yace “Lay down before they shoot you” shiru tai tana son gane me yake cewa.

 

Ya sake kwantar da ita a ƙasa, hellcopter nan kuwa tuni ya tashi ya fara shawagi a sama, suna communicating da sojojin dake ƙasa.

 

An kwashi kusan awanni biyu ana wannan musayar wuta a tsakanin ‘yan ta’addan da kuma sojojin, wanda a ƙarshe Allah ya bawa sojojin nasarar fatattakar maharan, suka kashe na kashewa.

 

Sai bayan da ƙura ta lafa, sannan Lieutenant Faruk ya migirna a hankali, saboda harbin shima da akayi masa a dantsensa.

 

 

Cikin jarumta ya miƙe tsaye, sai dai jiri ne ke ɗibar sa, saboda jini da yake zubarwa a dantsen nasa, yana tashi ita ma yarinyar ta tashi tsaye, sannu a hankali ya ƙarasa in da Captain yake kwance a sume cikin jini, ya durƙusa ya ɗago shi, tare da kara kunnensa a saitin zuciyarsa, can ƙasa ƙasa yaji bugun zuciyarsa alamar yana da rai.

Bin su kawai take da ido, tana sake zura kai tana kallon Captain da idanunsa ke rufe.

 

Tawagar sojojin da suka shigo dajin kawo musu ɗauki ne suka fara ɓullowa, suna ta tattara gawarwakin ‘yan uwansu, da wanda a kaiwa rauni.

 

Cikin hanzari suka ƙaraso in da su Captain suke. Lieutenant Faruk na zaune rungume da Captain a jikinsa, Chief Commander yace “Are you ok?”

 

Faruk yace “Yes sir, but Captain K Buba needs first aid, he is seriously bleeding”

 

“Is he alive?” Ya sake tambayarsa.

 

“Yes, but am not sure”

 

Nan da nan aka ɗauki Captain zuwa inda aka kwantar da wanda suke buƙatar taimakon gaggawa, wanɗanda akaiwa rauni.

 

Nan Army doctors, likitocin sojoji suka rufu akan Captain dan ceto rayuwarsa, aka fara ƙoƙarin cire bullet ɗin dake cikinsa.

 

Sun yi nasarar cire na bayansa, amma na cikinsa ba su samu cire shi ba, sukace sai an koma can Barack za’a iya cire shi a Asibiti. Nan su kai ƙoƙarin tsaida jinin da ke zuba a jikinsa.

 

Lieutenant Faruk ma an cire masa bullet ɗin da ke damtsensa, an saka bandage an nannaɗe masa hannun.

 

“Hey, what this little baby is doing here?” Chief Commander ya faɗa yana nuna yarinyar da Captain ya tsinta.

 

Faruk yace “Captain ne ya tsinto ta”.

 

“Is she among the victims?”

 

Faruk yace “No, I don’t think so, maybe she was kidnapped too, I don’t actually knows where she belongs to”

 

Ita dai bakunan su kawai take bi da kallo, Tare da son fuskantar me suke faɗa.

 

Mota daban aka ware, aka tara gawarwakin sojojin da suka rasa rayukansu akan ceto wannan ɗalibai da akai garkuwa da su (may the gentle soul of the fallen heroes, rest in perfect peace).

 

Aka samu wata motar aka saka wanɗanda suka ji rauni, tana ganin an ɗauki Captain ita ma ta miƙe ta bisu, dan kar su ɓace mata, aka saka shi a mota ita ma ta fara ƙoƙarin shiga Motar.

 

“Hey, Carry this girl with you” Commander yai maganar yana nuna wani soja.

 

Ganin ya danƙi hannunta zai shiga da ita wata motar ya sa ta fashewa da kuka.

 

“Shut up!” Yai mata tsawa, duk da ba ta iya jin sautin abunda ya faɗa sosai amma ba ƙaramin razana ta yai ba, gaba ɗaya tsoron su ya shige ta, har ta fara tunanin ko irin mutanen da suka sato ta ne.

 

Lieutenant Faruk ne ya ƙaraso, ya kamo hannunta suka shiga wata Motar, sai leƙa window take, tana nunawa Faruk motar da aka saka Captain a ciki, bai kula ta ba ya jingina da jikin kujera tare da lumshe ido.

 

 

 

 

 

A daidaita sahu ce ta tsaya a ƙofar wani Babban Asibiti, mutane sai shiga suke suna fita, tare da salallami, fuskokinsu duk babu daɗi.

A gigice wata mata ta sakko daga cikin adaidaita sahun, hannunta ɗauke da wani yaro da bai fi shekaru huɗu ba, jikinsa sai rawar sanyi yake, haƙoransa na datsewa.

Bayan ta sallami mai a daidaita sahun, cikin gudu_gudu sauri_sauri ta shiga cikin Asibitin, ta nufi ɓangaren Accident and emmrgency, wato sashen bada taimakon gaggawa.

Teburin Nurses ta nufa hannunta riƙe da yaron tace “Bayin Allah dan Allah ku taimaka min, yaro na kawo”.

 

Ɗaya ta ɗago ta kalleta tace “Ba mu da gado”

 

Cikin tashin hankali tace “Dan girman Allah ku duba min yaron nan, kar shima in rasa shi, duk ‘yan uwansa babu sai shi kaɗai ku temaka dan Allah”

 

A fusace wata Nurse tace “kinji mace, muka ce miki ba mu da gado, ko ransa a hannunmu yake? In Allah ya ga dama karɓar shi zai yi, ko kina so ko ba kya so, waɗanda kike gani a kwance ma sallamar su za muyi, likitoci yajin aiki zasu tafi, in kina da kuɗi kuma zaki iya kai shi Asibitin kuɗi a duba shi”

 

Cikin kuka tace “Wanne zan kai shi wanda zan samu likita a dubamin shi”

 

Nurse ɗin tai murmushi ta ce “yanzun nan aka kira likitan da yake duba marasa lafiya a nan, duk ranar Talata yske zuwa, kuma awa uku kawai yake ya tafi, doctor G.Y ya tafi Asibitinsa, ki je ki same shi a can sai ya fi duba miki yaron yadda yakamata, a bashi duk abunda yake buƙata”.

 

“Au dama ba’a shiga yajin aikin ba?” Ta tambaya tana rarraba ido.

 

Nurse ɗin ta ce “eh ba’a shiga ba tukuna, amma ai na gaya miki bamu da gado ko? Kuma ana shirye-shiryen tsunduma yajin aikin likitoci”

 

“To shikenan, ina ne Asibitin nasa?”

 

Suka kwatanta mata Asibitin, haka ta kuma fitowa da yaron, cikin tashin hankali ta tafi in da aka kwatanta mata.

 

 

 

 

 

G.Y BULAMA HOSPITAL AND MERTERNITY, shine a rubuce a katafaren ginin, Manyan motoci na ta shiga suna fita a cikin harabar Asibitin.

 

Tana rungume da yaron ta shiga cikin Asibitin, kai tsaye ta nufi in da wasu Nurses ke zaune tace “Sannunku, dan Allah mara lafiya muka kawo” tai maganar tana nuna musu yaron da ke hannunta.

 

“Kuna da file a nan ne?” Wata Nurse ta tambaya.

 

“A’a, Wallahi mun je Asibiti uku duk sai ace mana ba gado, a na ƙarshen ne aka ce mana wai yajin aiki likitoci za suyi, shine aka kwatanta mana nan”

 

“To ai Hajiya sai kun buɗe file sannan likita zai ganku”

 

Ta ce “To nawa ne buɗe file ɗin?”

 

“Naira dubu biyar ne, single file”

Turus tai, dan kuɗin hannunta dama dubu bakwai ne, sun ƙarar da biyu a yawon Asibitoci.

 

Dubu biyar ɗin kenan ta rage a hannunta, a sanyaye ta ce “To a buɗe mana”

 

Haka ta biya kuɗin nan, aka buɗe musu file, bayan an buɗe aka ce su biya dubu uku kuɗin ganin likita.

 

Ta kalli Nurse ɗin ta ce “Wallahi suke nan a jikina, ki taimaka min baiwar Allah, kar in rasa ɗana, dan Allah ku duba shi”

 

“Baiwar Allah, ba fa Asibiti na bane, kuma ba Asibitin gwamnati bane, haka ƙa’idar Asibitin take.

 

Ta koma gefe kawai ta fashe da kuka.

 

Wani dogon mutum ne fari sol, ya fito daga wani ɗaki jikinsa sanye da farar rigar likitoci, Nurses na biye da shi sun riƙo masa files, ganin mace ta saka ɗa a gaba tana kuka ya sa ya tsaya ya kalleta ya kalli yaron ya ce “Lafiya baiwar Allah, baki san akwai marasa lafiya a kwance ba kika ware murya kina wannan kukan?”

 

Cikin kukan ta ce “dan Allah likita kai min rai, ka dubamin yaron nan, dubu biyar ɗin kenan na biya kuɗin buɗe file, kuma yanzu ance sai na biya na ganinka dan Allah ka dubamin shi”.

 

Ɗan shiru yai yana kallon ta, daga bisani ya durƙusa ya tattaɓa yaron, ya buɗe idon yaron, sannan ya miƙe tsaye yace “ku biya naira dubu hamsin, kwantar da yaron za’ai ya galabaita sosai”

 

Daga haka bai kuma cewa komai ba, ya fara tafiya.

 

Take hawayen idonta suka bushe jin an ambato dubu hamsin, dan basu da ita ba su da dalilinta, dan Mai_ gidanta ɗan acaɓa ne.

 

Jiki na rawa ta ɗakko ‘yar ƙaramar wayar ta mai madannai, ta nemi lambar mijin nata, cikin kuka tai masa bayanin halin da ake ciki.

 

Yace “ki kwantar da hankalinki, kice su yi masa duk abun da ya dace, zan bada jinginar babur ɗina, in kawo kuɗin.

 

Allah sarki uwa, kamar zata zare haka ta kuma tashi, ta nufi ofishin likitan nan, ta tarar yana duba wani mara lafiya, a hanzarce ta ce “likita dan Allah ka zo a fara bashi magani, babansa yace gashi nan zuwa zai zo ya biya kuɗin”

 

 

Cike da ƙosawa da ƙufula ya ce “hajiya baki ga mara lafiya nake dubawa bane? Mu nan Asibitin bama haka, ki je idan kun kawo kuɗin a bashi maganin, kar ki sake shigo min office haka ba izini”

 

Da ƙyar ta iya jan ƙafafuwanta da su kai mata nauyi, ta bar office ɗin, ta koma in da ta kwantar da yaron, sai jijjiga yake, jikinsa rauu da zazzaɓi, bakinsa se zubar da dafara yake, ta samu guri ta zauna ta ɗora yaron a kan ƙirjinta tana jin yadda zuciyar sa ke bugawa, kamar zata fasa ƙirjinsa ta fito. Ta lumshe ido tana zubar da hawaye tana kallon yadda kumfa ke fite a bakin yaron, amma cikin ma’aikatan ba wanda ya kalle su da idon tausayawa.

 

Tana nan a zaune sai ga mijin nata kamar korarrare ya shigo hankali a tashe, ya ƙarasa in da take zaune da yaron yana faɗin “Zainabu, an duba shi kuwa?”

 

Kasa Magana tai sai sake rushewa da kuka, yace “ki kwantar da hankalinki, na bada jinginar babur ɗina, na karɓo kuɗin a gurin maƙocinmu, a ina za’a biya kuɗin?”

 

Ta nuna masa reception, in da zai je ya biya, ya je ya biya ya zo ya ɗauki yaron, ya rungume shi a jikinsa, da receipt ɗin biyan kuɗin a hannunsa.

 

Aka nuna musu ofishin likitan, Ya shiga da yaron a jikinsa, likitan ya kalle shi ya nuna masa gadon da ke cikin Office ɗin yace ya kwantar da yaron ya je waje.

 

Haka ya kwantar da shi ya fice, ya koma in da ya bar matarsa ya dinga rarashinta yana bata baki.

 

Nurses ɗin jira suke suga doctor ya taso ya duba yaron, amma yace “This boy will not survive, da tun zuwansu sun ba da kuɗi ne, da maybe mu iya ceto shi, but for now, ba zai surving ba”

 

“But doctor, da an jarraba dai ko Allah zai sa a ceto shi” wata Nurse tai Maganar cike da tausayawa.

 

“Will you shut up, zaki koyamin aiki ne?” Yai maganar yana zazzare ido.

 

Ta ce “No am sorry Sir”

 

Wata matashiyar budurwa ce, sanye da uniform ta shigo hannunta da file ta kalli likitan ta ce “Doctor, ‘yan uwan matar nan da za’aiwa CS a cikinsu duk babu me irin blood group ɗinta, Amma an samu mai O negative a cikinsu, wanda zeyi daidai da jinin Alhajin nan da aka rasa samun jinin da za’a saka masa”

 

Ya ce “ok, yanzu abunda za’ai shine, ku ɗebi 2 pints of blood, a jikin shi mai O negative ɗin, sai kun ɗiba zuwa anjima sai ku ce musu kun sake gwadawa  jinin bai yi ba, su sake samo wasu mutanen, idan ya so a siyarawa da Alhajin jinin, 20thousands each pints, leda biyu 40 thousands kenan”

 

Tace “ok Sir”

 

Ya cigaba da sabgar gabansa, yayin da wannan yaro na kan gado ya cigaba da convulsing, ya kai mintuna talatin a haka, daga bisani rai yai halinsa.

 

Sai da yaron ya rasu, Sannan Ya miƙe ya saka safar hannu, yai parking ɗin gawar, sannan ya fita daga office ɗin, cikin rige rige iyayen yaron suka ƙaraso suna tambayar ya jikinsa, cikin ko in kula doctor GY yace “He’s gone, Allah yai masa rasuwa”

 

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” shi suka dinga maimaitawa, yayin da mahaifiyar yaron ta koma gefe tana zub da hawaye, shikenan guda ɗaya yaron, shima gashi ta rasa shi.

Shi kuwa doctor G.Y yai gaba abunsa.

 

Wasu daga cikin patient suka dinga bata baki, akan tayi tawakalli Allah ya bata wani.

 

Cikin kuka ta kalli Nurses ɗin tace “Wataƙila da kun taimaka mana, ko da magani ne lokacin da muka zo yana suma, da wata ƙila bai rasu ba”

 

 

Wata Nurse tace “ki ji min mata kamar jahila, maza kiyi saɓo kinji, mutane kamar ba musulmai ba ba tawakalli”

 

Duk dauriya da jarumta irin ta namiji, sai da mahaifin yaron yai kuka, yace “ki dena faɗar haka Zainab, kinga hankalin mutane ya fara dawowa kan ki, ana gaya miki magana, Khalifa lokacinsa ne ya riga ya yi, Allah ya karɓe shi, Allah ya jiƙansa bari in je in samo adaidaita sahu, mu ɗau gawar”.

 

Haka ya fita dan neman adaidaita sahun da zata kai su gida.

 

Bayan ya samu adaidaita sahun ya shigo Asibitin, ya koma reception ya tarar da wanda ya biya kuɗin Asibitin a gurinta ya ce “To, baiwar Allah tunda ba’a kwantar da yaron nan ba, Allah ya karɓi abunsa, ko ba duka ba dan Allah ku rago min kuɗin da na biya”

 

Jinjina kai tayi tace “Ga doctor Bulama can, shine mai Asibitin wanda ya duba ɗanka, kaje ka same shi kai masa bayani”.

 

Bai yi ƙasa a gwiwa ba, yabi bayan doctor Bulama, tare da maimaita masa abunda ya gayawa receptionist.

 

A wulaƙance ya dube shi sannan yace “Ka taɓa ganin wanda ya je ƙiyama ya dawo?”

 

Ya girgiza Kai yace “A’a”

 

“To nan Asibitin, no refundable after payment, kuɗi sun riga sun shiga asusun Asibiti, dan haka sai dai ka haƙura”.

 

Kamar zai shige cikin doctor Garba, haka ya duƙa yana cewa “Dan Allah ka taimaka min, Wallahi babur ɗina da nake neman Abinci na bada jingina, na karɓo kuɗin”

 

A fusace doctor yace “kaga i have something to attend to, ka san ba ka da ƙarfi meyasa ka taho nan?”

 

“Wallahi an rasa gado ne, kuma akace ma yajin aiki likitoci za su tafi shiyasa, dan Allah ka temaka mana…”

 

Ai bai tsaya saurar sauran zancen ba, ya wuce a bar shi a gurin, ɗauke da baƙi ciki goma da Ashirin!.

 

 

 

 

 

 

 

 

Kantagora Army barrack Naija state, nan ne in da aka kai gawarwakin sojojin da suka rasa ransu, da wanda a kaiwa rauni, kai tsaye aka wuce da su babban Asibitin da ke cikin barikin sojojin.

Duk in da Faruk ya saka ƙafarsa, a nan yarinyar nan take mayar da tata ƙafar, ita kaɗai a cikin zaratan sojojin nan sai binsu take.

 

Wani Babban soja yai umarni da a kaita cikin yaran da aka kuɓutar, ko itama a samu nata iyayen.

 

Wani soja ya ce “To ai wannan yarinyar ba tai kama da ‘yan Nigeria ba ma, ko ma dai daga maƙotan ƙasashen nan akai kidnapping ɗin ta?”

 

Faruk ya ce “i have no idea about it, abunda na sani shine ba ta cikin wancan yaran da aka kuɓutar, dan haka ba cikin su Yakamata a haɗata ba, daban za’ai cigiyar iyayenta, abunyi Yanzu shine ko Madam Halima ce a bata ita ta zauna da ita, kan a san abunyi akanta”.

 

Su kai na’am da shawarar da Faruk ya bayar, akan ta zauna a gurin Madam Halima, itama soja ce a cikin tawagar, mijinta ma soja ne suna zaune a nan cikin barrack ɗin tare.

 

Madam Halima ta kalli kyakkyawar fuskar yarinyar, wadda tai duƙun duƙun, ‘yar rigar jikinta tai futu futu da datti, ga gashin kanta a hargitse duk datti da ƙasa.

 

Cike da tausaywa yadda ‘yar ƙanƙanuwar yarinyar tai rayuwa a hannun ‘yan ta’adda babu kulawa ta ce “ya sunan ki?”

 

Maimakon ta amsa sai tai ƙuri da ido tana kallon Madam Halima.

 

“Ya sunan ki na ce?” Madam ta kuma maimaitawa, amma shiru ba tai responding ba.

 

Faruk ya ce “ina ga fa ba ta Magana, da tunda aka tsinto ta banji tayi Magana ba”.

 

Madam ta ce “Allah sarki, Allah kaɗai ya san halin da iyayenta ke ciki, ai ita ma a Asibitin zamu bar ta a duba lafiyar ta tukunna”

 

Faruk ya ce. “ok hakan ya yi”.

 

‘Yan matan nan ma da aka kuɓutar, duk nan Asibitin cikin barrack aka kawo su, dan binciken lafiyar su, kafin a miƙa su ga iyayensu.

 

Gaba ɗaya ganinta take kamar a wata duniyar ta daban, Madam Halima taiwa yarinyar nan wanka tsaf, aka samo wata rigar aka saka mata, aka kwantar da ita akan gadon marasa lafiya, ba ta umm ba ta um’um, sai aukin rarraba idanu, babban burinta bai wuce ta ga wannan mutumin da ya ɗakkota daga hannun wannan mutanen ba.

Sai dai ba ta san in da aka kai shi ba, wasu mutanen ne daban suke zuwa suna duba ta, suka dinga soka mata allura suna ɗibar mata jini, sai da suka saka ta kuka, dan haka gaba ɗaya tsoron gurin take ji.

 

“Ashhadu alla ila ha illallah, Rabbana alaika tawakalna wa ilaika anabna wa ilaikal masir” shine abunda ya ke ta maimaitawa, tare da ƙoƙarin buɗe idanunsa a hankali.

 

Dumm yake ji a kansa, ga shi dishi dishi yake gani, a hankali ya cigaba da lumshe idonsa yana buɗewa har Allah ya sa ya buɗe su yana ganin komai clearly.

 

“Congratulations Captain, you survive” wani matashin likita ya faɗa yana murmushi.

 

A hankali ya yunƙura zai tashi zaune, amma Likitan yai saurin cewa “No relax, ba’a daɗe da fitowa da kai daga tiyata ba, mun cire maka bullet a cikinka ne.

 

Ajiyar zuciya yai yace “Alhamdilillah, yaran fa suna ina?”

 

“Suna nan tare da mu a cikin Asibitin nan, ana musu gwaje gwaje kan a sada su da ‘yan uwansu”

 

Kamar dirar mikiya, haka yarinyar da ya tsinta ta faɗo masa, da sauri ya ce “There was one little baby, da na samo a cikin dajin, tana ina?”

 

Likitan ya ɗan yi shiru sannan yace “kai gaskiya ni banga yarinya ƙarama a cikin yaran nan ba, duk ‘yan makaranta ne”

 

Da sauri ya ce “No, their is one little girl, ba tafi 3 years ba, wata fara haka”

 

Doctor ya ce “Please calm down, kaga yanzu muka fito da kai, ka kwantar da hankalinka kar jininka ya hau”.

 

Captain ya girgiza kai yace “dole a nemo ta, she’s not among the students, ba a cikin su take ba”.

 

“Shikenan is ok, za’a nemo ta insha Allah, bari inje in duba amma for now, dan Allah ka kwanta ka samu nustuwa”

 

“Nutsuwata ɗaya, shine a ga yarinyar nan”

 

“Ok, bari inje a duba”.

 

Captain ya koma ya gyara kwanciyar sa yana lumshe ido.

 

Doctor da yaiwa Captain aiki ya cire masa bullet ya fita, dan neman yarinyar da Captain ya saka shi.

 

Sai dai duk iya binciken da yai, babu wanda ya ga yarinyar, kowa ya tanbaya sai ya ce bai ganta ba, iya ɗaliban nan suke nan babu wata yarinya ‘yar shekaru uku a cikin su.

 

Har mutuary ya je, ya duba cikin gawarwakin yaran, amma babu wata yarinya ƙarama a cikin su.

 

Komawa ɗakin da Captain yake yai, ya tarar an zaunar da shi, wani likitan ya kammala yi masa dressing ɗin in da ya samu rauni a bayansa.

 

Ɗagowa Captain yai ya ɗan tsura masa idanu, yana jiran jin amsar da zai ba shi, duk da kasancewar likitan soja ne, amma sai da gabansa ya faɗi da irin kallon da Captain ke masa, saboda kasancewar sa mutum me matuƙar kwarjini.

 

“Am.. duk cikin yaran nan an duba ba ta ciki, kuma har gawarwaki na duba amma babu ita a ciki, kowa na tambaya sai ya ce babu wata yarinya ƙarama a cikin yaran da aka kuɓutar duk matasa ne ‘yan makaranta.

 

“Impossible” Captain ya faɗa yana ƙoƙarin tashi.

 

Saurin riƙe shi su kai suna cewa yayi haƙuri.

 

“Ya za’ai yarinyar da na saka a Mota, ace ba’a ganta ba, a gabana fa ta shiga Motar?”

 

“Ka yi haƙuri a sake dubawa za’a ganta”.

 

“No, zan duba da kaina” yai maganar yana ƙoƙarin miƙewa, sai dai jiri ya kwashe shi, da tsananin azaba da cikinsa ke yi, hakan ya tilasta masa komawa ya zauna.

 

 

 

 

 

Comment and Share please

Nimcyluv

Ayshercool

Zee kumurya.

[21/09, 10:35 am] +234 803 192 1625: *✷DARE DA DUHU✷*

 

_Bright pens of✍🏾_

Nimcyluv

Ayushercool

Zee kumurya

 

*3……*

Elegant Online writers

 

_Ƙirƙirarren labari ne, ba mu yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba, idan yai kamanceceniya da rayuwar wani ko wata Arashi ne🫣_

 

_Littafin DARE DA DUHU haƙƙin mallakar mu ne, bamu yar da a juya shi ta kowace siga ba, ko a sashi a wata kafa ba ba tare da izinin mu ba_

 

 

 

 

 

Dafe kansa dake barazanar tarwatse masa ya yi, tare da taune lips ɗinsa na ƙasa cikin taurin zuciya.

 

Likitan da ya je nemo yarinyar bai ganta ba ya dube shi, cikin girmamawa da son kwantar masa da hankali ya ce. “Ka kwantar da hankalinka Sir, Insha Allah, za’a ganta”

 

Runtse idonsa ya yi, gently ya ƙara buɗe su yana kallon su ya ce. “Where is my phone?”

 

Likitan ya ce. “Tana nan tare da uniform ɗinka, da za’a yi maka surgery ne aka cire su.” Bai ce komai ba sai alama da ya yi masa da hannu akan ya kawo masa wayar. Likitan ya sara masa sannan ya fice. Gyara masa kwanciya ɗayan Likitan ya yi, shi ma ya fice.

 

Lumshe idonsa ya yi yana tuna Jamil da Danniel cikin jini a kallon ƙarshe da ya yi musu, sosai mutuwar su take dukan zuciyarsa. Numfashi ya fesar mai zafi lokacin da ya tuno fuskar ƙaramar yarinyar da ya gani, bai san me yasa ya ji ya damu da ita ba a cikin zuciyarsa, ji yake yi kamar ya fizge drip ɗin hannunsa ya fita ya nemo ta da kansa. A fili ya furta

 

“Where is She?What kind of situation is she in? who will take care of her?” Ya yi maganar cikin damuwa. he just felt worried about the little girl.

 

General Ibrahim A.M ne yake ta kaiwa da komowa a cikin office ɗinsa, shi kaɗai cikin tsananin ɓacin rai. Lokaci ɗaya ya koma mazauninsa ya zauna yana fesar da wani numfashi mai zafi, duk da kasancewar office ɗin da A.c amma gumi ne kawai yake tsatstsafo masa ta ko’ina a jikinsa. Hannunsa dafe da kansa sai karkaɗa ƙafafuwansa yake yi.

Da ƙarfi ya buga table ɗin gabansa tare da faɗin. “Damn it!”

 

Wayarsa ce ta fara ruri tana neman agaji, tsaki ya ja har kiran ya katse bai bi ta kan sa ba, dan ba ta shi yake ba. Sai da aka yi masa 4 missed call sannan ya janyo wayar cikin ɗacin rai a fusace ya ɗaga ba tare da ya duba mai kiran ba.

 

Daga cikin wayar wata shaƙaƙƙiyar murya ya ce. “An samu bacin rana!”

 

Ajiyar zuciya General Ibrahim ya sauke yace

“Har da na Inuwa ma duk an samu Gwaska.”

 

Gwaska ya ce “Ba a taɓa mun

Ɓarna irin wannan ba tunda na fara harkan nan, ya akai haka ta faru?.” Cikin ɓacin rai General ya ce. “Ba za ka gane baƙin cikin da nake ci da wannan Nasara da yaran nan suka samu ba, ban taɓa tunanin hakan za ta faru ba, a yanda na san ka na san taƙadirancinka ko rundunar sojoji million aka turo za ka iya gamawa da su, na baka komai a tsare, umarnin harbin da aka basu ne ya ɓata komai, kuma aka shirya wata rundunar aka tura ba tare da sanina ba,  shiyasa su suka yi galaba a kanku. Babban baƙin cikina da wancan yaron Khamal ya dawo a raye ba, kuma na san duk nasarar da aka samu sanadiyyar sa ne, dan ba ƙaramin jajircewa ce da shi akan aikinsa ba, yana aiki ne da jikinsa gami da zuciyarsa, He knows the value of his work, especially if he wears military uniforms on his body, he feels like he is carrying the whole country in his shoulder, gaba ɗaya yanzu idan manyanmu a kansa yake”.

See also  Zauren Fiqhu Tambayoyi da Amsa Whatsapp Number

 

Gwaska ya yi wata shegiyar dariya ya ce. “Indai kere na yawo, zabo na yawo wata rana za’a haɗu, Wallahi sai na ɗauki fansar kisan yarana da akai mun da kuma harsashin da ya huda jikina, zan yi ɓarnar da sena girgiza ƙasar nan girgiza ta gaske makuwa, kuma dole a sakarmin yarana da aka kama ko kuma aga abunda ba’a so” Cikin mamaki General ya ce. “What? You mean kai ma sun yi nasarar harbin k……,”

 

kiran da ya shigo cikin wayarsa ne ya katse masa abun da yake cewa. Janye wayar ya yi daga kunnensa ya duba, ganin Chief of Army staff ne yasa cikin sauri ya cewa Gwaska “Ina zuwa, I will call you later.” Bai jira amsarsa ba ya ɗaga kiran Chief ɗin.

 

Ƙamewa ya yi kamar yana gabansa with so much respect ya ce. “Morning Sir.” Daga ɗaya ɓangaren Chief ya ce. “Morning General, ka shirya kai da sojoji kamar 20 anjima za mu zo mu je mu dubo yaranmu na Naija state, sanann mu jagoranci miƙa yaran nan ga iyayensu ”

 

“Done Sir.” General ya faɗa tare da sara masa.

 

Dungurar da wayar ya yi bayan ya katse kiran cikin tsananin takaici. Abun da yake ƙara baƙanta ran General idan ya tuna yanda Nigeria da duniya gaba-ɗaya ta ɗauka da zancen nasarar da su Captain Khamal suka samu akan ƴan ta’addan, duk inda mutum ya duba a social media zancen ake yi ana yaba musu da jinjina musu akan bajintar da suka yi. Kuma daga faruwar abun jiya har Chief zai je ya dubo su da kansa da sauran manyan muƙarabban gwamnati, duk kuwa da tarin sabgogin dake kansu. Tsaki ya ja a fili ya ce

 

“Sai ka ce akansu aka fara fita operation, mu da duk da muke zuwa uban wa ya yi mana haka?” Sumar kansa ya yamutsa cikin rashin sanin abun yi, duk wannan abubuwan ba su wani dame shi ba kamar irin ace za’a ƙarawa Captain matsayi, domin ya san tabbas idan hakan ta faru gaba_gaba Captain zai kamo matsayinsa ko ma ya wuce shi tunda mutum ne shi jajirtacce akan aikinsa, kuma ze iya bankaɗo muguwar harƙallar da yake aikatawa.

 

Table ɗin gabansa ya ƙara bugawa da dukkan ƙarfinsa idanunsa duka a waje ya ce “Impossible! Wallahi ko zan rasa aikina ba zan taɓa bari a ƙarawa yaron nan girma ba.” Kamar mahaukaci ya ɗauki wayarsa ya fice fuuuu!! daga office ɗin tamkar zai tashi sama.

 

 

A hankali ta buɗe idonta tana bin inda take kallo, kunnuwanta na jiyo mata sauti mai kama da maganganun mutane ƙasa_ƙasa. Hannun hagunta ta ji ya ɗaure mata, ga wani abu da take ji daga hannun yana shiga cikin jikinta a hankali. Yunƙurin tashi zaune ta yi, Madam Halima dake zaune a kujerar gaban gadon da take, ta yi saurin tashi tsaye tana faɗin. “Kin farka, sannu Dear.”

 

Da ido kawai take bin ta dan ba ta jin abun da take cewa sosai, kamar mai yin magana cikin raɗa haka take ji. Madam Halima ta mayar da ita ta kwanta, cikin kulawa ta ce.

 

“Let me call the doctor”

 

ta juya ta fara tafiya, Yarinyar dake kwance saman gado, ta bi ta ido har ta ɓacewa ganin ta, kalle-kalle ta shiga yi a ward ɗin da suke mai ɗauke da gadajen marasa lafiya guda huɗu, duk yara ne ƙanana kamarta sai masu jinyar su. Tare Madam Halima suka dawo da Doctor Zainab, dudduba jikinta ta yi bayan ta yi mata sannu, d Doctor ta dubi Madam Halima  ta ce “Madam a ba ta ko ruwan tea ne ta sha dan tana tattare da yunwa, anjima idan ruwan nan ya ƙare za’a iya discharging ɗinku, because gaba-ɗaya results ɗin gwaje-gwajen da aka yi mata ya nuna ba ta da wani ciwo mai illa a jikinta.”

 

Madam ta ce. “Masha Allah, Mun gode sosai fa Doctor.”

 

Doctor ta yi murmurshi ta ce. “Don’t mind.” Sannan ta shafa cukurkuɗaɗɗan gashin Yarinyar ta ce. “Cute Baby Allah ya ƙara lafiya.” Da ido kawai yarinyar ta bita.

 

Bayan fitar Doctor, Madam Halima ta bar ta a hannun wata Nurse ta tafi haɗo mata kayan tea ta dawo.

 

Har lokacin idanunta biyu ba ta koma barcin ba. Bayan ta haɗa mata tea ɗin ta tashe ta zaune ta jingina bayanta a jikin pillow sannan ta ɗauko cup ɗin da spoon ta deɓo tea ɗin ta kai bakinta. Kawar da kai ta yi dan ba ta taɓa ganin irin wannan abun ba.

 

Madam Halima ta kamo hannunta ta ce “What happen?” Duk da ba ta ji abun da ta ce sosai ba amma sai ta girgiza mata kai. Tsayawa Madam Halima ta yi tana kallon ta, har yanzu yanayinta ya nuna tana cikin tsoro, ba tare da ta yi zato ba ta ji cikin muryar yara  da ƙarfin sauti ta ce. “Zan yi fitsari.”

Madam Halima da ta yi tunanin duk  yanayin tsoron da yarinyar take ciki ne yasa ta yin maganar da ƙarfi, cikin farinciki ta ce. “Alhamdulillah, baki ya buɗe kenan?”

 

Yana nan kwance Likitan da ya je ɗauko masa wayarsa ya dawo ya kawo masa.

 

More than 50 missed call ya tarar, fiye da rabi duk na Family ɗinsa ne.

 

Numbern Mahaifiyarsa da ya yi saving da First  love ya fara bin bayan kiran, amma har ya kira sau biyu not

respond, numfashi ya sauke ya kira numbern My wife, still ita ma no respond.

 

Tsaki ya ja ya ajiye wayar  a gefensa tare da lumshe idonsa yana sauraren bugun zuciyarsa, gefe guda kuma raɗaɗi da ciwon harbin jikinsa na ɗan damunsa, musamman da ya kasance sai dai ya kwanta ta ɓari ɗaya. Gently ya ji an turo ƙofar ɗakin an shigo tare da yin sallama, buɗe idonsa ya yi ya sauke akan wanda ya shigo.

 

Lieutenant Faruk ne, da mamaki Khamal yake duban shi ganin hannunsa nannaɗe da bandage, alamar shima an harbeshi.

 

Murmurshi Lieutenant Faruk ya sakar masa tare da sake yin sallama. Amsa masa ya yi a can ƙasan maƙoshi. Faruk ya ƙaraso tare da janyo kujera da hannunsa mai lafiya ya zauna a gabansa.

 

“Good Morning Captain” Ya faɗa cikin respect.

 

Ɗaga masa kai kawai Captain ya yi.

 

Cikin kulawa Faruƙ ya ce “Ya jikin naka?”

 

Cikin dakakkiyar muryarsa ya ce. “Alhamdulillah, and you?” Faruk ya ce. “Da sauƙi Alhamdulillah.” Jinjina kai Captain ya yi tare da runtse idanunsa, lokaci ɗaya kuma ya buɗe idon kamar an tsikare shi ya ce.

 

“Faruk I want to ask you something?” Faruk ya ce. “Okay Sir.”

 

Captain yana kallon cikin idonsa ya ce. “Akwai wata little Baby da na ɗauko jiya tana ina, ance ba’a ganta ba?”

 

Faruk ya ce. “Tana cikin asibitin nan, ana bincikar lafiyar jikinta, Madam Halima ce tare da ita.”

 

Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi ya ce. “Ina fatan dai babu wani abu da ya same ta ko?”

 

Lieutenant Faruk ya ce. “Babu Sir.”

 

Ajiyar zuciya ya ƙara saukewa, yana jin yanda nutsuwa ta fara mamaye zuciyarsa.

 

Faruk ya cigaba da magana.

 

“Muna jiran a tabbatar tana cikin ƙoshin lafiya ne kafin mu fara cigiyar iyayenta, su sauran yaran ɗazu aka kaisu gidan gwamnati, za’a miƙa su ga iyayensu, ita kuma ba wanda ya san daga ina take, za’ai cigiyar iyayenta”

 

Da sauri Captain Khamal ya ce. ”

 

No, not now.”

 

Da mamaki Faruk yake kallon shi, da son jin dalilin da ya sa yace ba yanzu ba.

 

gyaɗa masa kai Khamal ya yi ya ce.

 

“A bar ta a hannun Madam Halima har zuwa lokacin da zan samu lafiya, da kaina nake son yin bincike a kanta.”

 

“But Sir….”

 

Ɗaga masa hannu ya yi fuskarsa a haɗe, alamar ya ƙosa da maganganun Faruk, hakan yasa Faruk ya haɗiye maganarsa, amma cikin ransa fal mamaki ne akan abun da Captain ya faɗa.

 

A sanin da ya yi masa mutum ne wanda babu ruwansa da shiga shirgin da ba nasa ba, komai zaka yi sai dai ya bika da ido amma ba zai tanka ba. But bai san dalilinsa na yin hakan akan yarinyar ba. Ɗan taɓe baki ya yi ya miƙe ya yi masa sallama ya fita.

 

Ƙarfe ɗaya saura na rana tawagar su Chief of Army staff ta sauka a Kantagora Army barrack Naija state, direct inda Captain Khamal yake ya ce a fara kai su.

 

Su uku suka fara shiga ɗakin da yake,  Chief da General Ibrahim sai wani Colonel, daga baya kuma Ministan tsaro da na sufuri da wasu jami’an tsaron suma suka shiga.

 

Yana kwance idanunsa a lumshe kamar mai bacci, amma ba baccin yake ba, wani likita na tsaye a kansa yana dudduba shi. Ƙamewa Likitan ya yi ya sarawa su Chief of Army staff tare da welcoming ɗinsu. Hakan ya saka ya buɗe idanunsa ya waiwaya ya kalle su.

 

Da sauri ya ɗago kansa tare da ƙoƙarin yin salute daga kwancen da yake. Chief ya ƙarasa kusa da shi ya kama hannunsa yana murmurshi ya ce. “No need, our Lion the king of the jungle, I salute you Captain Khamal Khamis”

 

Ƙasa ya yi da kansa cikin respect ya ce. “Welcome Sir.”

 

Chief ya ce. “Thank you, How are you feeling now?”

 

Ya ce. “Better Alhamdulillah.” Chief ya ce.

 

“Masha Allah, Allah ya ƙara lafiya, rundunar soja tana matuƙar Alfahari da samun jajirtacce kamar ka, shugaban ƙasa ma ya yabawa ƙoƙarin da ku kai, duk da baya gari amma ya turo wakilansa, muna tare da ministan tsaro da na sufuri, duk muka zo duba ku.”

 

Captain Khamal ya jinjina kai tare da faɗin “Thank you sir”

 

General Ibrahim ya ƙaraso cikin ƙoƙarin ɓoye halin da yake ciki ya yi masa sannu ba yabo ba fallasa, shi ma ya amsa masa a haka.

 

Minista kuwa cikin fara’a ya yi masa sannu tare da yi masa jinjina akan aikin da suka yi.

 

Ta gefen ido General ya dinga hararar Khamal cikin tsananin baƙin ciki. Chief ya zauna a kujerar da Likitan ya kawo masa, yana duban Captain Khamal cikin jinjina ya ce.

 

“Sannu da ƙoƙari Captain, tabbas kai ɗin na daban ne kuma mai sa’a ne ko a cikin sojoji. Irinku Jajirtattu masu aiki domin Allah ƙasar mu take buƙata, da ace ƙasar mu za ta samu kamar ka su fi rinjaye a cikin jami’an tsaro da ma mutane da  an samu sauƙin ta’addanci da duk wani criminals acts a cikin ƙasar nan. An daɗe ba’a samu Nasara a fita operation kamar wannan da kuka fita ba, hakan ya ƙara nuna mana jajircewarka Hukumar sojojin ƙasa ta yaba muku kuma ta jinjina muku.”

 

Captain ya ce. “Thank you Sir.” Chief ya ce. “Allah ya ƙara lafiya, bari mu zagaya mu duba sauran soldiers ɗin daga nan zamu wuce government House na nan garin, dan miƙa yaran nan ga iyayensu.

 

” Captain ya ce. “Okay Sir, a fito lafiya.”

 

Cikin yaƙe General Ibrahim ya ce masa. “Allah ya ƙara lafiya Captain” A ransa kuwa cewa ya yi. ‘By the grace of God ba zaka tashi daga wannan ciwon ba sai dai a ɗauki gawarka daga gurin nan, ba dai ka taka da ƙafafuwanka ka bar shi ba.’

 

Da ƙyar Madam Halima ta saka yarinyar, ta sha tea ɗin kaɗan bayan ta saka mata Fo ta yi fitsarin a ciki.

 

Abun mamaki kuma mijin Madam Halima yana kawo  Banana ta karɓa ta fara ci cikin sauri-sauri, hakan ya ƙara nuna tana jin yunwa sosai.

 

Cikin mamaki Madam Halima ta dubi Mijinta Captain Abdussamad ta ce. “Captain ka ga abun mamaki, yarinyar nan ɗazu daƙyar ta sha tea kamar zata yi kuka, amma ka ga yanzu yanda take cin Bananan.”

 

Captain dake kallon Yarinyar ya ce. “May be tana son ta ne that is why.” Madam Halima ta jinjina kai ta ce. “She is so cute, amma har yanzu a cikin firgici take, ta ƙi sakin ranta ta nutsu, kamar ma a firgice take da environment ɗin”

 

Captain ya ce. “Dole ai, tunda babu wanda ya san tsawon lokacin da ta ɗauka a hannun azzaluman mutanen can, kuma a cikin dokar daji”

 

Numfashi Madam Halima ta sauke ta ce. “Allah Sarki, yanzu haka maybe iyayenta sun yi cigiyar ta har sun gaji.”

 

Captain ya ce. “Wa ya faɗa miki iyaye suna gajiya da neman ɗansu? Ai sai dai masu bincika musun su gaji.”

 

Madam Halima ta ce. “Haka ne, amma yarinyar nan ba ta mun kala da ‘ƴan Africa ba, ko shi yasa idan muka yi mata magana ba ta ganewa, ko ba bahushiya bace? amma kuma ɗazu ta yi mun Hausa.”

 

Captain ya ce “Komai ma zai iya kasancewa, may be ba ta jin hausan ne sosai.”

 

Jinjina kai kawai Madam Halima ta yi Idanunta akan yarinyar, ita kam har cikin ranta take jin tausayi da k’aunar Yarinyar, ko dan ba ta Ƴaƴa ne ya saka?

 

Gaba ɗaya ransa a dagule yake, yana cigaba da lissafin ta ina ze sake ɓullowa lamarin, dan wannan galabar da aka samu akan ‘yan ta’adda kamar koma baya ne a gare shi, da samun raunin yadda a tsakanin sa da su Gwaska.

 

Wayarsa ce ta fara ringing, kamar ba ze ɗauka ba, se kuma ya miƙa hannu ya ɗauka, cikin hamzari ya miƙe tsaye yana sarawa wanda yake Maganar da shi a waya, kamar yana gabansa.

 

 

Daga cikin wayar aka ce “Mr. President ya dawo gari, ze yi zaman gaggawa da mu yau da daddare, akan harkar tsaro”

 

General Ibrahim yace “ok Sir” ya sake ƙamewa, sannan ya ajiye wayar.

 

Yana ajiyewa ya wani sake haɗe rai, tare da yin ƙwafa, ya daki tebur yai waje cikin sauri.

 

Manya manyan masu ruwa da tsaki a harkar al’amuran tsaro duk sun hallara, kama daga Chief of Army staff, AVM General General na sojoji, babba da ƙaramin ministan tsaro, masu bawa shugaban ƙasa shawara akan harkar tsaro, da sauran manya masu bada shawara akan harkar tsaro, da shi kansa shugaban ƙasan, sun hallara a cikin katafaren ofishin da shugaban ƙasa ke ganawar sirri, babu ɗan Jarida babu masu saka ido, babu duk wata Camera ta ɗauka, saboda ganawa ce ta sirri.

 

Shugaban ƙasa yai gyaran murya cikin harshen turanci yace “To nayi farin ciki matuƙa da irin nasarar da jami’an tsaron mu suka samu, akan ceto yaran nan da aka sace, dama gaba ɗaya idon duniya a kanmu yake, dan ganin ƙoƙarin da za muyi, to Alhamdilillah yaran sun kuɓuta kamar yadda na samu labari, duk da wasu sun rasa rayukansu, mun bada sanarwar jaje ga ahalin wannan yara.

Yanzu abu na gaba shine, wane mataki zamu ɗauka akan kawo ƙarshen sace mana ɗalibai da ake a makarantun kwana da ma na jeka ka dawo?

 

Ƙaramin ministan tsaro yace “Ai your Excellency, a nawa ganin a rufe Dukkanin makarantun sakandare da na primary na yankin gabashin ƙasar nan, tun da a nan rashin tsaron yake, zuwa a ga yadda hali ze yi”

 

Baban ministan tsaro yace “A’ wannan ba shawara bace ai, shikenan se mu ajiye yaranmu a gida ba makaranta? Wanan ai kawo koma baya ne da naƙasu ga ilimin al’ummar yankin”

 

Ƙaramin ministan tsaro a ransa yace “wannan shine baban burinmu, al’ummar yankin suyi ta saun koma baya”

 

 

Haka akai ta tattaunawa, har aka samu matsaya akan cewar, dole a rufe makarantun a dakatar da ilimin wannan yankin, har se zuwa lokacin da za’a samar da tsaro.

 

Magana ta gaba kuma, shugaban ƙasa yai bayanin cewa, akwai ƙasashen da sukai alƙawarin tallafawa ƙasa da maƙudan kuɗaɗe dan siyo makamai da za’a bawa Sojoji dan cigaba da yaƙi.

 

Nan suma sojojin suka faɗi ƙorafe ƙorafensu, abubuwan da suke buƙata, da yadda kuɗaɗen da ake warewa harkar tsaro ba sa isa yadda Yakamata.

 

Shugaban ƙasa yai alƙawarin kafa kwamitin bibiya, akan yadda ake amfani da kuɗaɗen da ake warewa harkar tsaron.

 

Aka tattauna batutuwa masu mahimmanci, da shawarwari akan yadda za’a shawo kan matsalolin tsaro.

 

General Ibrahim yana komawa gida, ya samu wani keɓaɓɓen guri, ya fara kiran waya.

Dashshiyar muryar Gwaska ta bayyana a cikin wayar “ya, dama kai muke dako, kunyi zama da shugaban ƙasa, me ake ciki?”

 

“Dama kiran da nai maka kenan, yau me magana da yawun shugaban ƙasa ze sanar da rufe makarantun firamare da na sakandare na yankin gabashin ƙasar nan, har zuwa lokacin da za’a samu tsaro, Sannan akwai maƙudan kuɗaɗe da za’a bawa ƙasar nan tallafi dan siyo makamai da cigaba da yaƙar ku” gaba ɗaya ya kwashe Abinda aka tattauna ya gayawa Gwaska.

 

Wata irin mahaukaciya dariya Gwaska ya saki, kai da jin wannan dariya ka san me ita ya samu rauni a imaninsa ya tsagaita da dariyar yace

“Yankin mu na ta samun koma baya ta kowace siga, yayin da ta wani fannin hakan ya zama hanyar samawa ƙasa hanyoyin samun kuɗaɗen da manyan ƙasar suke kashe mu raba. Hakan yayi kya a satin nan zamu ƙaddamar da babban harin da yafi wanda mu kai a baya.

Muna nan muna cigaba da saurarenka, duk yadda ake ciki game da shirin rundunar ku, muna sauraren ka, abunda ya shafi shirin gwamnati shima muna da masu kawo mana rahoto, ka huta..” daga haka Gwaska ya kashe wayarsa.

 

Bayan Sallar la’asar Captain yana zaune yana shan coffee ɗin da ya saka aka kawo masa a hankali aka turo ƙofar ɗakin da yake da ƙarfi.

 

Ɗaga kansa ya yi cikin sauri saboda ƙamshin da yaji ya ziyarci hancinsa, da mamaki yake kallon matashiyar kyakkyawar matar dake tsaye tana kallon sa hawaye na shatata daga cikin idanunta.

 

Ajiye cup ɗin hannunsa ya yi cikin tsananin mamaki, duk da tsohon cikin da matar ke ɗauke da shi haka ta tako cikin gudu ta zo ta rungume shi tana sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da fashewa da kuka. Ɗan ture ta ya yi daga jikinsa a hankali saboda yanda take ƙoƙarin fama masa ciwukan jikinsa. Cikin dauriya ya kwantar da kanta akan kafaɗarsa, Gently ya shiga bubbuga bayanta alamar rarrashi cikin sauke ajiyar zuciya ba tare da ya ce komai ba.

 

Lumshe idanunsa ya yi yana shaƙar ƙamshinta da ya yi bala’in missing ɗinsa. Tsahon 5 minutes suna haka sannan ya ɗago ta ya shiga share mata hawaye tare da girgiza mata kai. Ta gane me yake nufi, hakan yasa ta haɗiye kukanta. Cikin muryar da ta ci kuka ta ƙoshi ta ce. “My Man, sun kusa kashe mun kai ko?” Hannunta ya kamo ya shiga murzawa slowly cikin tsananin ƙaunarta ya ce. “Ba su kusa ba, tunda Allah bai yi ba gani a raye.”

 

Ta ɓata fuska ta ce. “Wannan manyan raunikan dake jikinka fa My Man? Na san ba dan Allah ya yi da nisan kwananka a gaba ba da tuni na rasa ka.” Ta ƙarashe maganar tana sakin kuka. Cikin sanyin murya ya ce. “Aikin sojan kenan My Wife, kar ki manta sai da muka rantse za mu kare rayukan al’umma kafin mu fara aikin. Ki bar kukan nan haka, just pray for me.” Ta ja hanci ta ce. “Allah ya baka lafiya My Man.” Karan hancinta ya ja tare da ɗan yin murmurshi ya ce. “Ameen My wife, ya aka yi kika san ina nan har kika zo?” Ta zauna a gefensa tana kallon cikin idonsa ta ce. “Ta yanda labarin irin bajintar da kuka yi ya zagaye duniya, kafafen yaɗa labarai ko ina ana ta sanarwa, kuma an kira Baffa an sanar masa.

 

 

Yana shafa cikinta a hankali ya ce. “How was My unborn Baby? I missed both of you so much.”

 

Kwantar da kanta ta yi akan kafad’arsa ta ce. “We missed you too, Baby yana lafiya, sai dai jiya na san yanda ban yi bacci ba shima bai yi ba, saboda yanda ya dinga wutsil-wutsil kamar zai fito duniya ya tarewa Dad ɗinsa harbin da aka yi masa.”

 

Murmurshi ya yi irin wanda shi kansa ya manta rabon da ya yi kamar sa ya ce. “Zai iya ai, tunda shi ma Jarumi ne kamar Babansa.” Dai-dai nan aka turo ƙofar ɗakin aka shigo.

 

 

 

 

Share, share share Please

Nimcyluv

Zee kumurya

Ayshercool.

 

 

‘m selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!

BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I’m

selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Whatsapp OR

Call *08066268951*

[21/09, 10:35 am] +234 803 192 1625: *✷ DARE DA DUHU ✷*

 

_Bright pens✍🏾_

Nimcyluv

Ayushercool

Zee kumurya

 

*4…..*

Elegant Online writer’s

 

_Kuyi following wannan acct ɗin a Arewabooks_

https://arewabooks.com/u/nimcyluv

 

Captain Khamal ya yi saurin zame kan matarsa dake kafaɗarsa, idanunsa ya ware tare da sakin kwantaccen Murmushi, saboda ganin waɗanda suka shigo Room ɗin. Babbar mace ce, fara tas da ita zata iya yin shekaru hamsin a duniya.

 

“Finally, my son survived Alhamdilillah” Hajiya A’isha ta ce, tana ƙarasawa bakin gadon da Major Khamal yake kwance.

 

Lumshe idanunsa ya yi, He breathed slowly kafin ya ware idanunsa akan matar cikin ƙasa da murya yace.

“First love” Ya Faɗi maganar yana ƙara sakar mata Murmushi. hannunsa ta kama tare dayi masa ƙuri da Idanunta, she tries to understand, if there is something wrong with him.

 

A Hankali tace “Hankali na, ya tashi sosai Babana, na kasa samun nutsuwa bana son aikin nan naka, kullum cikin zullumi nake da tashin hankali” Captain Khamal ya kama hannun Hajiya A’isha wacce ta kasance Uwa a gare shi, ya ɗan yi murmushi yace

 

“First love, ba gashi kinga lafiya nake ba? Zan warke insha Allah”

 

“Tsoro take kada a kashe mata Jaruminta” Da sauri Captain Khamal ya ɗaga kansa, with so much surprise yake kallon mai maganar, Sai a lokacin ya kula dashi.

 

“Baffa” Captain ya ce, yana ware idanunsa akan mahaifinsa dake tsaye cikin shigar manyan kaya, kamarsa da Major Khamal ta bayyana sosai, hatta baƙar fatar Captain irinta Baffa ce.

 

Baffa ya harari Khamal, cikin wasa ya ce “An manta da Baffa saboda anga first love? Shine ni aka ƙi kulani”

 

“It’s not like that, Baffa” waje Baffa ya nema tare da zama cikin tausayin ɗan nasa ya ce “Ya jikin naka?” .

 

“Jiki Alhamdilillah Baffa”

Jinjina kai Baffa ya yi yana kallon wajan da aka harbi Khamal, cikin sanyin murya Baffa yace

 

“I received a call on phone, from the military command in Abuja, sun gaya min Wanda suka rasa rayukansu a dajin, hankali na ya tashi sosai, mun ɗauka ko har da kai, Sai daga baya muka samu full information akan cewar kai raunuka ka samu”

Captain dai murmushi yake, yana son iyayensa bashi da kamar su.

“Yaya K, ya jiki?” Cewar wani matashin saurayi. Khamal ya kalli ƙaninsa Shureim yace “You?” Shureim ya kwaɓe fuska tare da faɗin “Duk na damu zan rasa Big bro, shine ya kula kowa banda ni”

 

“Sorry Shureim”

Shureim ya ce “Ya jikin Yaya K?” Captain ya rufe idanunsa A hankali ya ce “I’m good” surutun da yake yi, gaba ɗaya ya fama masa ciwon, yana jin yadda gurin yake masa zafi sosai.

 

Na’ima dake gefensa, ji take kamar ta ɗauke mijinta su tafi gida haka take ji. Tayi kewarsa sosai, har tsanar aikin take saboda tsayin lokacin da suke ɗauka basa tare.

 

Army Doctor ɗin daya shigo ne, ya kalli su Baffa cikin sakin fuska ya ce “Ana buƙatar ya samu nutsuwa, wajan harsashin bai warke ba haryanzu”

See also  The sexy boss Hausa Novel

Baffa ya miƙe tsaye, Yana faɗin “Daman da yaya aka barmu muka shigo ganinsa, tafiya za mu yi tunda kun mana fin ƙarfi” Dr ɗin dai murmushi ya yi, Baffa ya yi waje. Hajiya A’isha ta kalli Captain ta ce “Allah ya ƙara sauƙi Babana, Zuwa yaushe zaka dawo gida ka huta?”.

 

“First love ban sani ba, but Soon in sha Allah”

ta ce “To, Allah ya tsare min kai”

 

yunƙurawa ya yi zai tashi da sauri Na’ima ta kamashi tana faɗin “Be careful”

Duk yadda yaso miƙewa kasawa ya yi, Dole ya koma tare da zama ya ce “Allah ya kiyaye hanya first love” fita duk sukai hadda Shureim.

 

Na’ima ta kalleshi tace “My man, ni ina nan tare da kai ko?”

 

Ya ware Idanu ya ce “Are You sure?” Kai ta ɗaga masa tana kama hannunsa tace “I really really miss you Man, Over eight months banji ɗumin ka ba”

 

hancinta ya ja “I miss you both, i mean you and my unborn child” Lamo tai a kafaɗar sa, kewarsa na fisgarta, She misses every single thing about him, she wants to be with her husband.

 

Madam Halima kuwa ta rasa ya ya zatai da Yarinyar kuka kawai take tana kiran “Abbi” cikin damuwa da kuma son rarrashin Yarinyar Madam Halima tace

 

“Me kike so?” Yarinyar

Taƙi cewa komai, domin bama ta gane me Madam Halima ta ce ba.

 

Madam Halima tace “Jama’a na shiga Uku, wacce irin yarinya ce wannan?”

 

Miƙewa ta yi tare da zama kusa da yarinyar cikin rarrashi tace.

“Kin ga stop crying, A good child never cry.”

 

Ƙanƙame jikinta tayi, bata so ko taɓa ta ayi, She’s afraid of everything. Babu wanda take son gani sai Mutumin daya ɗakko ta, Idanunta na hango mata shi cikin jini.

 

Da hannu Madam Halima tai mata nuni irin Sign language ɗin nan tace.

“Ke, kuka ki daina babu kyau”.

 

“Abbi…”

Yarinyar Ta faɗa da ɗan ƙarfi, shiru Madam Halima tai, ko mahaifinta ne Abbi?.

 

Kallon yarinyar tayi, fara ce sosai, irin farin nan ƙal, But she looks very similar to Arabs, her eyes, hair, almost everything.

 

“ماذا تريد اين والدك”

Ma’ana “me kike so, ina mahaifin ki yake?” Madam Halima ta tambayeta da larabci, a tunaninta tunda tayi mata kala da Larabawa, may be tana jin larabci, bata san cewa gaba ɗaya maganar ce ba sosai take jinta ba.

 

Cikin rarrashi ta ce

“Kee, yanzu zan kira Abbinki.. kina so?” Da sauri ta ɗaga mata kai tana mata ƙuri da Idanunta, ta fuskanci hakan ne saboda bakin Madam da ta kalla, Madam Halima tai Murmushi tana bata Teddy tace “sai Kinyi bacci Abbi zai zo, kwanta” tai mata alama da data kwanta, ganin ta sake ambatar Abbi yasa Yarinyar kwanciya ta sakin ajjiyar zuciya, kana ganinta kasan akwai ɓoyayyan abu a tattare da ita.

 

Sai da Madam Halima taga tayi bacci, ta zare mata yatsarta dake baki, a firgice ta farka tana shirin sakin kuka Madam Halima ta mayar mata da yatsar bakinta.

 

Duk a wahale take, ta jima Idanunta bai ga bacci ba, ihun dabbobin jeji, da kuma tsoro yasa bata wani baccin kirki. Girgiza kai Madam Halima tayi Ubangiji kaɗai yasan halin da Yarinyar ta shiga, ko ƴar ina ce? Su waye iyayenta, they are alive or dead, Ohho!?. Wayarta ta ɗauka tare da kiran Lieutanant Faruk, ta faɗa masa She wants to see him immediately.

 

Faruk daya shigo yanzu, shima ya kalli yarinyar kafin ya juya ya kalli Madam Halima yace “what happened now?”

 

Madam Halima ta ce “Honestly, Her memory may be impaired idan taci gaba da kasancewa haka, a Yanzu ma kamar tana da wata ɓoyayyiyar larura” Faruk kasa cewa komai ya yi, yana mamakin yadda ƙaramar yarinya ta kasance a cikin wannan jejin, ko me ya kaita oho? Ko iyayenta akai kidnapping tai escaping ko wani abun ne, Allah ne ya barwa kansa sani.

 

Faruk yai ajiyar zuciya yace “I will speak to Captain Khamal, Whatever he said, I will get back to you, Amma Banga kyautatuwar zamanta a nan ba”

 

Madam Halima taja numfashi kafin ta nemi waje ta zauna tace “you said she was not among the school children kidnapped?”

 

“Haka yace” Faruk ya faɗa yana taɓe fuska.

Madam Halima tace “Waye yace?”

yace “Captain Khamal, kin san taurin kansa ai, bakomai ze tsaya yai maka bayani ba”

Tace “To, Allah ya kyauta”

Daga nan Faruk juyawa ya yi, tare da yin waje, yabar Madam da baki a buɗe.

 

Wata matashiyar budurwa ce tsaye, da gajeren wanddo da farar shirt irin na sojoji, kanta ya sha a wigs, tai parking ɗin sa a bayanta, ta sarawa Lieutanant Faruk daya fito ta ce “Sir, Abu babu daɗi Allah ya tsare gaba. Amma nayi farin ciki sosai da nasarar da kuka samu”

 

Faruk yace “Thank you,Salima yaushe kika shigo Naija state?”

 

Tace “Not too long, Ina Captain ne?”

 

Murmushi kawai Faruk ya yi mata, dan yasan tatsuniyar gizo baya shige koƙi Yace “Shi kika biyo ke nan?.

 

Tace “A’a, za’ai posting ɗin mu zuwa wani waje ne, shine muka biyo ta nan zamu shige da sauran”

 

Faruk yace “I see, yanzu Captain ba lallai ki ganshi ba, lokacin treatment ɗin sa ya yi”

 

Salima tace “My be zuwa Dare” Faruk ya kalli Salima in a serious tone yace “Zan iya cewa wani abu, Salima?”.

 

“All ears. Sir Faruk”

 

Salima ta faɗi hakan tana kallon Faruk sosai. “Meyasa ba zaki iya haƙuri da soyayyar Captain Khamal ba?”

 

Salima was speechless. Bata san cewa Abinda Faruk zai faɗa mata ke nan ba. Cikin sanyin Murya ta ce “I can’t stop thinking about him, I always want to be with him, Wallah Sir Faruk ban san me zan ba, nace masa koda bai auren ba, kawai mu kasance tare, duk abinda yake so zan masa, like how every woman takes care of her husband”

 

Shiru Faruk ya yi ta kallon Salima, If he is not mistaken, bata da burin daya shige Captain ya kwanta da ita, ta ɓullo masa ta barikanci ya ƙi yarda, tace ya aureta nan ma yaƙi.

 

Faruk yace “Captain daban yake a cikin mu, rashin matarsa kusa dashi bai sa yabi matan banza ba, Ni shaida ne, You are wasting your time Salima, ko Captain zai kula wata ai banda irinki,ke fa duk kusan mazan Barrack ɗin Abuja ba wanda bai san yaya kike ba, Among the men, including me”

 

“Alright, kace kishi ka ke dani? Ya ware hannunsa tare da yin gaba yana faɗin ” ko ɗan, it’s just a suggestion”…

 

 

The next day at night.

Captain na zaune Sanye da vest fara ƙal, sai gajeren wando, ƙafarsa sanye cikin wani baƙin takalmi, Leutanant Faruk ne ya buɗe ƙofar ya shigo, cikin girmamawa ya gaida Captain.

 

Sipping coffee Captain Khamal yake a nutse, a hankali ta dinga leƙo da kanta daga bayan Faruk tana leƙen Captain

 

Sam Captain bai lura da ita ba, yaji a jikinsa akwai wanda ke kallonsa dai.

 

“Abbi ɗin, kike leƙa kuma?” Faruk ya faɗa da ɗan ƙarfi yadda za taji abinda yake cewa. Captain ya ɗago kansa da sauri, farin hannunta mai ɗauke da Teddy ya hango. Gaba ɗaya ta ɓoye jikinta da fuskarta a bayan Faruk.

 

Da sauri Faruk yaja baya yana murmushi ya ce “Ai baki isa ba, yadda kika ɗaga hankalin kowa shine yanzu zaki ɓoye a bayana?” Yarinyar ta rufe Idanunta tana ƙanƙame Teddyn da Madam Halima ta bata, riga da wando ne jikinta masu kyau, peach colour. An raba mata gashin kanta gida biyu ya kwanta har baya.

 

A nutse Captain yake ƙare mata kallo, ko wanne kalar sauyin ta samu, ba zai mance kamanninta ba, duk yanzu tsaf take, saɓanin lokacin da ya tsinceta cikin datti. Zame Teddyn tayi daga kan fuskarta, tare da buɗe Idanunta.

 

Idanu suka haɗa da Captain Khamal, ya ware mata manyan idanunsa, ƙara ta saki tana ƙanƙame Teddy. Sosai ya bata tsoro, bayan kuma shi take ta kuka za tazo wajensa.

 

Murmushi Captain ya saki, yana ɗan rufe idanunsa, seeing how she was scared by what he did to her.

 

“Come here”.

Captain ya ce mata, yana miƙa mata hannunsa, ƙuri tayi masa da Manyan idanunta, da suke farare ta tass, Ganin yadda ta kafeshi da Idanu, kamar bata taɓa ganinsa ba, yasa Captain ya ƙara ware mata manyan idanunsa yana sane.

 

Maimakon yaga tayi ƙara, sai kawai yaga ta saki Teddyn tare da ta zuwa wajansa da gudu. Zamewa ya yi kaɗan yana gyara zamansa, saboda ciwon jikinsa.

 

“Abbi”

Yarinyar ta ce, tana tsayawa gaban Captain tare da leƙa fuskarsa, Murmushi ya sakar mata, itama ta washe white teeths ɗin ta, tana ƙara zura kanta tare da leƙa fuskarsa sosai. Faruk dai ikon Allah yake kallo, tunda aka kawo yarinyar take kuka, amma yanzu gata harda dariya.

 

“Abbi”

Ta kuma cewa tana nuna masa ciwon jikinsa sai kuma tace “Shhhhhh” tana kwaɓe fuska tare da Girgiza kanta, alamar bata son ganin ciwon gaba ɗaya. Musamman daya kasance a jikin Abbi ɗinta.

Fuskarta ya tallafo, a zuciyarsa yana jinjina kyan da Ubangiji ya yi mata, mai fisgar Hankalin jama’a. Caraf yaji ta kama tafin hannunsa wanda yasa Captain saurin rufe ido, sai kuma ya buɗe lokaci guda!.

 

“How are you?”

Cewar Captain yana buɗe idanunsa akan innocent face ɗin ta, bata san mene yace ba, amma sosai taji sautin kamilalliyar muryarsa a kunnanta, ta samu kanta da ɗaga masa kai tana faɗin “Abbi”

Ya fahimci kalmar “Abbi”. Ita kawai ta riƙe cikin bakinta, idan ba Captain ba, kallon kowa take matsayin wani abu daban.

 

“Sir yanzu wanne suna za’a ce mata, tun da naga ko sunanta ba ta sani ba?”

Gently Captain ya kalli Faruk, sai kuma ya kalli fuskar yarinyar kafin ya rufe idanunsa yace.

 

“ABRA KHAMAL KHAMIS BUBA”

“Abra…?” Faruk ya ɗan zaro ido ya maimaita a zuciyarsa, kafin yace “Allah ya raya, Abra..” “Amin, thank you” cewar Captain

 

Faruk yace “Amma yallaɓai, naji ka haɗa sunan nata da naka, ba za’a nemo iyayenta ba kenan?”

 

Shiru Captain yai, bai bawa Faruk amsar tambayar da yai masa ba.

 

Abra kuwa ta ƙurawa tea ɗin dake gefen Captain Idanu, shima ya Kalli tea ɗin, da hannunsa ya yi mata alamar zata sha ne? Domin ba zai iya yin ihun magana ba. Ta ɗaga masa kai tare da faɗin “Abbi” hannunsa yasa tare da ɗaga ta Cak zuwa saman cinyarsa, a nutse yake bata tea ɗin tana sha, sai da tasha sosai ta janye bakinta, idanunsa akan Faruk yace.

 

“Wannan kan nata, abuɗe kamar ƴar arna, kai kuma kamar maye ka zuba mata ido Mtwss”

 

Murmushi Faruk ya yi, tare da ɗauke idanunsa daga kan Abra yace “Haka aka ban ita nima, idan maye ni me zan da Abra sai dai Abbin Abra”

 

Murmushi kawai Captain ya yi, a hankali kuma yaji numfashi Abra na sauka alamar tai bacci kwance a nan jikinsa. Yatsarsa data saka a baki tana tsotsa ta ɗauka nata ne, shi ya zame a hankali yace.

 

“She is sleeping, come and pick her up” ya faɗa yana hura iska sosai a kunnanta, Just to confirm abinda yake tunani, amma ko motsawa ba tayi ba, sai ma firgita da tayi tana riƙe hannunsa tace “Abbi”

Captain bai ce komai ba, amma har zuciyarsa yake tsananin so da tausayin Abra. Faruk ya ɗauke ta, yana yin waje

“Tell Madam Halima, that she should took a good care of her, ina tsoran Barrack.”. Faruk ya jinjina kai.

 

Babu jimawa da fitar Faruk, Na’ima ta shigo, hakan yasa ba taga Abra ba sam, tana zuba ƙamshi sosai ta Ƙarasa wajan Captain, tare da zama gefensa tace “Man”

Hannunta ya kama tare da murzawa “Wife” ya faɗa a taushashe, ƙamshinta na ɗaukan hankalinsa, shi kansa dauriya yake sosai a kanta.

“When will you be discharged?” Na’ima tayi magana tana bin Captain da wani irin kallo, mai kama da zallar buƙatar mata ga mijinta.

 

“to tomorrow or the day after” yace yana kissing lip’s ɗinta, ta rufe idanunta, ya yi mata side hug, tare da ƙurawa cikinta idanu, wanda ya girma sosai saura kaɗan EDD nata ya cika.

 

Wayar Na’ima ta ɗauki ringing, ta yi wani kalar zabura tana tura baki gaba, Captain ya yi Murmushi, a hankali ta ɗauki wayar daga cikin wayar akace “Waye ne?”

Na’ima tace “Nice Granny”

tace “Kewa?”

Ta ce “Na’ima” da sauri Granny dake cikin wayar tace

“Auzubillah, wata abace Na’ima kuma? Kinga ba ruwana dake, cewa zan daman ki kirani, irin kiran nan mai motsi” kashe wayar Na’ima tayi dake akwai Wi-Fi sai ta kira number Granny a V.c Fuskar wata tsohuwa ta bayyana a screen ɗin wayar Na’ima, tana hakimce akan kujera ta lafta wani glasses a Fuskarta, a cewarta kwana biyu baki ke son kamata. Ganin fuskar Na’ima, yasa Granny runtse idanunta tace “A’a me zan da naki fuskar kuma? Maza kamo min fuskar Kamalu” Captain Khamal ya ɗura kansa a kafaɗar Na’ima, a sanyaye ya ce.

 

“Granny” fashe masa tayi kuka sosai tace “Allah ya isa, Allah ya isa, Allah dai ya isa har sau uku” ya yi Murmushi ya ce “Ɗaya ta Isa” da sauri tace “Wlh bata isa ba, guda goma na su yi, amma na barta a guda uku, kuma gaba ɗaya da matarka Na’ima nake, ai ba uwata bace da zanji tsoranta”

 

Captain dai ya kasa cewa komai, Granny tana matse Idanunta tace “Abinda matarka tai min, Allah kaɗai na barwa, shi yasan yadda zai da ita, banda haka mace bata san darajar ɗan fari ba, tai ta gantali da narkeken ciki a gaba, duniya duk ta lalace da ɓata gari, haka kurum ta haɗu da wani mayen ya lashe ɗan Tun a ciki? To ya bazan mata Allah ya isa ba? Nifa shi yasa tun farko nace kawai kayi mata huɗu ko wacce tayi ta kanta, amma yanzu zanta shela wacce taga Allah taga Ma”aiki ta aureka”

Captain ya kalli Na’ima data haɗe fuska yace “Granny, Soon zan ƙara mata ai…” Granny ta waro Idanunta tace “kace Allah?” Ya ɗaga mata kai.

 

Tayi ƙasa da murya tace

“To ai kaga haka yafi? Nayi magana cikin azanci, kuma ka fahimcen, Amma wannan matar taka mai kama da sadaka yalla sam ba tai min ba, ƴar banza ce, tana kallon kuwa a wulaƙance”

Haka tai ta surutu daga ƙarshe ta kashe wayar. Na’ima ta cika tai fam, Captain ya jawota yana matseta yace “Sorry, Wife… Zo kiji”.

 

Kwanan Na’ima huɗu wajan Captain a gidan da aka ware masa, shi kuma yana Hospital, kullum sai Faruk ya kawo masa Abra, amma basu taɓa samun Na’ima a wajan ba, hakan ya yi wa Captain daɗi, dan yasan rikicin Na’ima, Abra kullum da kuka take barin Wajan Abbi ɗinta.

 

Yana zaune, cikin wasu ƙana nan kaya masu kyau, a hankali aka turo ƙofar tare da shigowa, tunda ta Shigo yake binta da kallo, idanunsa ya ɗauke cikin sanyin jiki Salima ta Ƙarasa tare da faɗin “Ya jiki dear?” Captain ya yi mata banza, wajansa ta Ƙarasa kafin ya tashi ta riƙe ƙafarsa tare da fashewa da kuka sosai tace.

“Dan girman Allah, kaji tausayi na Khamal, ka daina azabtar dani da soyayyarka”

Daka bakin ƙofa akace “Kutirin Ubanki zaici ba tausayi ba, Shegiya karuwa mai bin mazan mutane”

 

Da sauri Salima ta miƙe tsaye, shi kansa Captain a rikice yake kallon Na’ima, tana zuwa ta ɗauke Salima da maruka tace “Wlh wlh sai naga bayanki, akan mijina sai na kashe mutum, mijina nawa ne kawai, da ƴa ƴan da zan haifa masa, karuwa kawai” Salima ta haɗe fuska tace “I am not a prostitute” Na’ima ta cire mayafinta, ko cikin jikinta bata gani ta shaƙo wuyan Salima tace “Na faɗa karuwa, idan ba karuwa ba gantalalliya wace za tana bin mijin wata tana cewa ya so ta? Wlh sai na kashe ki na kashe Captain na kashe kaina, gaba ɗaya mu tafi lahira ai mana hisabi a can, babu wata banzar data isa ta shiga rayuwar mijina, ina son mijina fiye da komai” da ƙyar Captain ya ƙwace Salima da ga hannun Na’ima, tare da daka mata tsawa yace “Stop this nonsense, Na’ima.” With so much surprise Na’ima ke kallon Captain. Ya kalli Salima yace “Get out”

 

Salima ta kalli Na’ima ta ce “Zaki gane da karuwa kike magana, Wlh sai na shigo gidan ki, sai na auri Mijinki, sai na rabaki dashi”

Wani ihu Na’ima ta saki, ta shiga ƙundumawa Salima zagi, tana ƙoƙarin ɗaukan wata kwalba zata kwaɗa mata, Captain ya riƙe Na’ima yace “I Said Get out, Salima” fita Salima tayi. Na’ima ta fashe da kuka sosai, Captain ya kasa ce mata komai ya jata jikinsa sosai ya rungome ta yana faɗin “meyasa kike hakane? Matar nan soja ce ga ciki a jikinki ba kya tsoron tai miki illa?”.

 

“Wallahi in dai akan ka ne, bana tsoronta” ta ƙarasa Maganar tare da zame jikinta daga nasa tai waje.

 

 

G.Y Bulama hospital and Merternity.

Dr G.Y ya kalli mutumin dake gabansa kafin yace “ranka ya daɗe, zamu shiga tiyata da ita”

 

Mutumin yace “Dr Ka taimaki matata, I don’t want to lose her” yanayin yadda yai maganar zaka gane, tsohon ɗan boko ne.

 

G.Y yace “Tunda ka kawo kuɗin aikin da wuri, Don’t worry, she will be fine insha Allah”. Yana faɗin haka ya nufi theatre room inda aka kai matar mutumin.

 

Ƙyakƙyawan yaron dake kusa da Mutumin a ƙalla ze shekara goma sha ɗaya, kamarsa ɗaya sak da mutumin yace “Abu, Mami na”

 

Mutumin ya shafa kan yaron nasa yace “Mami zata samu lafiya, stop crying My son” yanayinsu ya nuna suna da cikakken ilimi sosai. Both arabi da boko.

 

Dr G.y ya kalli matar dake kwance akan gadon tiyata, cikin jikinta sai juyawa yake, duk abinda ke cikin nata shima wahala yake sha sosai, ya matso yazo duniya.

 

Cikin ko in kula ya kalli wata Nurse yace “Ina wannan yaron mai ciwon Sikila?”

Tace “Yana male Ward”

 

“Shine wanda za’a ƙarawa jini, Iyayensa sune masu kuɗin nan?” Ta ɗaga masa kai.

 

yyace “Ok a ɗauki 1 Pints of blood, da aka ajiye na wannan matar, naga irin jinin su ɗaya, sai a kaiwa iyayensa su bada 50k a sawa yaron”

 

Nurse ɗin tace “Dr ita kuma matar fa? C.s za’ai mata fa,kuma zata buƙaci jini immediately in an fito da ita, ai bai dace a ɗauki nata ba”

 

Dr G.y ya nemi waje ya gyara tsayuwarsa yana faɗin “Who is the boss between me and you?”.

 

Cikin girmamawa tace “kai ne Sir” yace

“So do as i said, is hardly for her to survive”

 

Kamar za tai kuka Nurse ɗin tace

“Amma aka amshi kuɗin aiki har 180k, Dr? But You can still try to help her.”

 

Dr ya haɗe rai sosai ya ce “Ke nan, zuwa asibitin duk a banza? Ra’ayi na ne haka, har a gado aka kwantar da ita, and bance ba za’ai mata komai ba, za’a cire abunda ke cikin nata, but she’s hypotensive and at the same time she has hyperglycemia, is hardly for her to survive”.

 

Nurse ɗin tai zuguum tana kallon cikin tiyatar in da matar ke kwance, take ta jujjuya kanta, alamar tana jin jiki.

 

Wani likitan ne ya shigo cikin tiyatar, yana faɗin “an haɗa komai?”

G.Y ysce “Eh an haɗa komai mu shiga”

 

Suka je suka kewaye matar, sukai mata allurai aka kashe daga cikin ta zuwa ƙafafuwan ta, sannan suka fara ƙoƙarin yankata, GY ya samata ruwa da allurai a ciki sannan suka fara aikin.

 

Suna tsaka da yi numfashinta ya fara sama yana ƙasa, SPO2 ɗinta was very low, ga PR ɗinta was very high.

 

Da sauri ɗaya likitan yace “what’s going wrong? GY wace allurar ka sa mata a ruwan nan ne?”

 

GY ya gaya masa, ya duba ruwan ya ɗakko kwalaban alluran ya duba, a take ya zare ido yace “GY ka manta she’s hypertensive ne? Kuma allurar ai ba ita bace”.

 

Da sauri GY ya duba tabbas yayi kuskure gurin saka allurar, na da nan suka tsaida ruwan, suka cigaba da ƙoƙarin ciro ɗan, amma yaron haka suka ciro shi babu rai.

 

Tuni ta galabaita matar, ta fita hayyacinta ba ta gane koma, ga jini da ya ɓalle kamar an kunna famfo, da ƙyar su ka ɗinke cikin nata, Amma ta ƙasanta jini sai ambaliya yake, ɗaya likitan yai mata duk alluran da suka kamata, amma jini be tsaya ba, ya kalli GY Yace “maza maza da an kaita ward, a saka mata jini, sannan ƴan uwanta su sake kawo wani jinin”.

 

Mutumin nan da ɗansa suna tsaye aka fito da matar, gaba ɗaya abunda aka rufeta da shi, jini ya ɓata har ɗiga yake, aikuwa yaron ya bi bayansu da sauri

 

GY ya kalli Nurse yace “maza aje lap, a ɗakko jinin nan a sakamata”.

 

Nurse tace “Doctor, har ka manta kace a siyarwa da iyayen yaran nan me sickler?”

Ɗaya likitan yace “GY harƙallarka tayi yawa Wallahi, yanzu ya za muyi da matar nan, she needs blood urgently, naga ance she has hyperglycemia, a bani glucometer in sake gwadawa”

 

Sai dai yana gwadawa ya ga sugan nata yai ƙasa sosai, ya duba file ɗinta, tun da tai awo a Asibitin, ba’a taɓa cewa tana da sugar ba sai yanzu.

 

“Waye ya duba sugarn nan kan a shiga tiyata”

 

Nurse ɗin dake biye da su tace “Nurse Bintu ce”

 

“Yaushe ta zama Nurse? Ba food hygiene tai ba? Dan me za ta dinga aikin Nurses, gaskiya GY Asibitinka da gyara”.

 

Duk wannan mujadalar, yaron na tsaye a bakin ƙofa, yaji duk abunda suke faɗa.

 

Ya ja da baya ya koma in da ya baro mahaifinsa, cikin damuwa yace “My son, kayi mana Maminka addu’a”

 

Shiru Yaron yai bai ce komai ba, Su GY suka fito a tare ya kalli mutumin yace “Sai dai kuyi haƙuri, mun rasa ɗan da ke cikin ta, ita ma kuyi ta Addu’a muna kan ƙoƙarin ceto ranta ne”

 

Ba su kuma yi musu wani bayani ba, suka wuce, yaron ya kama hannun mahaifinsa ya ja shi zuwa ɗakin da take ciki, tana kwance jini na ta ɗinga daga kan gadon da take!

 

 

 

For seven days now, Captain is being treating in the military hospital, in Naija State military base.

Chief of Army staff ne, da General Ibrahim, da Chief Commander tsaye a cikin Room ɗin, Chief ya kalli Captain yace “Congratulations Captain, we were confirmed that today you will be discharged ”

 

Captain yace “Thank you, sir”

Chief ya ce “akwai Good news, but it will be surprising..” Captain ya ware idanunsa sosai, Chief Commander ya yi Murmushi kafin ya kalli Captain ya ce.

“Jirgi na jiranka an gama komai, Allah ya ƙara sauƙi Captain, kai na musamman ne” General dai hararar Captain yake, yana tunanin yadda zai ga bayansa.

Gaba ɗaya fita sukai waje. A hankali Captain ya fito cikin wata farar singlet irinta sojoji yana ƙarewa harabar Barrack ɗin kallo. Tunanin yadda zai tafi da Abra yake ga Na’ima, gashi Chief ya tilasta sai an bincka iyayenta.

Yana tsaye yaga Faruk ya nufu wajansa, Captain ya ce “What happened?”

Faruk ya Girgiza kai yace “Abra” a hargitse Captain yace “Abra What? Don’t tell Anything mara kyau akan Yarinyata” Faruk yace “Abra was missing, tun safe babu Abra gaba ɗaya n duba cikin Barrack ɗin nan babu ita… Abra ta ɓata!.

 

Bright pens

Nimcyluv

Zee kumurya

Ayushercool✍🏾🤘🏼

 

‘m selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!

BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I’m

selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Whatsapp OR

Call *08066268951*

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top