Hausa Novels

Daren Amarcin Nabila Hausa Novel

Daren Amarcin Nabila Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

 

 

 

 

Yabo da godiya na musamman sun tabbata ga ALLAH makagi zamani, wanda keda ikon tasarrufi da bayinsa yadda yaso. Wanda ya halicci ko wanne dangi na abubuwa da jinsi kala biyu, ya kuma saka alaka tsakanin wadannan jinsi ta fuskokin da suka bambanta gwargwadon kalar jinsin ko halittar, ba shakka Allah mabuwayi ne a duk lamurransa.

 

 

ALLAH ya dada tsira ga annabi manzon karshe, wanda a nagarta ba tamkarsa. Wanda ko da wasa mutum ya kaucewa tafarkinsa ba shakka ya bata.

 

 

 

 

Ina mika godiyata ga mahaifiyata da tasha dawainiya da ni har na kai wannan mataki. Ba shakka kowa yanada mahiafiya, amma ni tawu ita ce sanyin idanuna, wacce nake rokon ubangiji da ya sadamu da ita a aljanna mafi daukaka.

 

 

 

Masoyana da bazarku ce nake taka rawa, ba yadda zan buda shafi ba tareda na jinjina maku ba. Inama ace inada dama, da na bude maku farfajiyar zuciyata domin kuga yadda na shimfida maku shimfidar alfarma domin ku sami nutsuwa a yayin zamanku a zuciyata, ku nawu ne, ni kuma naku.

 

 

 

Wannan labarin gajere ne, kuma na rubutashi ne domin nishadantarwa, labari ne mai dauke da ban dariya duk da cewa akwai ilmantarwa a ciki, na fi karkata kan nishadantarwa, labarin NABILA ne, wacce ta tafka katobara a daren amarcinta, dramar da suka sha ita da angonta sai kun shigo cikin labarin, amma ku tabbatar kun tanadi maganin ciwon ciki.

 

 

Sunan da nayi amfani da shi a littafin na wata kanwata ce kuma abokiyata, na nemi izininta kafin na aikata.

 

 

Sauran sunayen da zasu shigo a littafin na rubuta ne kai tsaye idan suka yi daidai da na wani ko wata ba da gangan ba ne.

 

 

 

Nayi wa littafin suna da KURUCI DANGIN HAUKA (daren amarcin nabila).

 

 

Ina rokon ALLAH da yayimin jagora.

 

 

 

 

 

ZAINUDDEEN ZAIN

*KURUCI DANGIN HAUKA* ( _daren amarcin Nabila_)

 

💗 6⃣-1⃣0⃣ 💗

 

 

 

 

 

 

© *ZAINUDDEEN ZAIN*

 

 

 

 

® _PEN WRITERS ASSOCIATION_

 

 

✍🏾

 

 

 

 

_dedicated to Maman Ahmad_

 

 

 

08034840276

 

 

 

 

 

 

Da misalin karfe shida ne na yamma, a unguwar Baiti da ke cikin garin Birnin Kebbi, unguwa ce da ko ba komai da maraice sosai akwai cinkoson jama’ah, kama daga masu dawowa daga wuraren kasuwanci daga ‘yar karamar kasuwar ‘yaryara, da masu dawowa daga filin kwallo, da musamman masu dawowa daga fadama, kasancewar mazauna unguwar suna bayar da lokutansu sasai a noman rani.

 

 

 

Daga wani gida a nan lokon Ango Sukola, hannun riga da gidan malam Shehu, ba abinda ke tashi face sauti da kida, wanda ya ja hankalina na karasa kusa domin na ga me ke faruwa, kunsan mutumin naku da gulma, ai ko nan na hango mata sun sha kwalliya kala-kala, a cen tsakiyar fili na hango amarya ta sha kwalliya kama tun daga takalminta har ya zuwa dankwalinta gwanin sha’awa, ba domin amarya ce ba da na tura tawu application lol. A gefe masu ba da kida ne, sai dai abin mamaki maza ne, tare da su akwai emcee da DJ sai mawakin da ya doka wakokin amarya, sai programmes ake ana kiran kawayen amarya da iyayen amarya, babban abin mamaki har da ango a filin wankin amarya, nan na dafe baki nace, “ashe wankin amarya ya canja fasali? Me kuma ya kawo ango a tsakiyar mata har da taka rawa? Sai ka ce al’adun yahudu da aljifan baya?” nan dai sai zuba kudi ake yi da sunan kari, ana kwasar rawa. Har isha, in da kusan duk wanda ke wurin ko sallar l’asar basuyi ba, daga nan camera man, ya yi wa abokani da kannen amarya interview kan auren da shagulgula, aka watse sai matan amarya suka fara jiran lokacin daukan amarya.

 

 

Da misalin sha daya saura motocin daukan amarya suka yada zango a kofar gidansu amarya da ke a unguwar Badariya da ke cikin Birnin Kebbi, haka aka fito da amarya cikin lullubi, duk gulamata na kasa gano fukarta, amarya ce a kujerar gaba inda wasu tsofaffi su uku suke zaune a kujerar baya, kusan motoci bakwai aka cika a ‘yan rakayar amarya, in da suka nufi unguwar masussuka da ke hannun riga da headqurter ta ‘yan sanda a nan garin Birnin Kebbi, a hankali ake tafiya, inda wakoki kala-kala ke tashi daga kowacce motar, wakoki ne da mata suka iya abinsu ban hardace ko daya ba da na rero maku, haka dai ake ta tafiya har aka karaso a wani gida wanda fentin jikinsa ya yi dai dai da kalar katon gate da aka yi kyaure da shi, sai guda ke tashi daga ta ko’ina kai ka ma rasa daga ina ne, in da aka saka amarya tsakiya kamar wata sarauniya ZABZABATU (Artabon sarakai), aka shiga da amarya wannan katafareren gida, wanda idan na tsaya misalta kyawunsa, kai tsaye nasan karyata ni za’ayi, nan tsofaffi da sauran jama’a suka watse, aka bar amarya tareda kawayenta su biyu Aisha da Amatullah.

 

Karin wasu littafai da zaku so

 

 

Sai surutu suke mata na aminai makusanta, amma ita zuciyarta cike take da tsoro da zullumin me zai faru a wannan daren nata da duk da ta sha nasihohi kala-kala wurin iyaye da gwagwanni har yanzu ta rasa makama, a ranta sai cewa take yi, “amma wallahi Usman ya raina ni, wato duk ajinnnan nawu na sabuwar amarya, fal a leda zai shanya ni haka, duk wannan kwalliyar da na rangwadamasa yana nufin a banza za ta tashi, ga shi har ta fara gogewa?” duk surutu da firar shagulgulan biki da su Amatu ke yi sam ba wanda ya shiga kunnenta domin ita ta dade da harzuka kan rashin shigowar angonnanta da wuri. Cen ta fara jiyo muryar abokinsa Shamsu yana tafe yana dariya, alamun zolayarsa ne yake yi, a daf da kyauren dakin Shamsu ya yi gyaran murya in da dayan abokinsu Yusuf ya yi sallama, kamar Aisha za ta amsa, sai Nabila ta daga mata hannu, alamun tayi shu, ganin sun yi sallama kusan sau biyar ba tareda an amsa ba, sai Shamsu ya ce, “yau kam ga ango da ya riga matarsa isowa,dakin angwanci, sarkin zumudi, tau mu shiga sai ka jira amaryar” Yusuf ne ya doke shi ta keyarsa ya ce “kai wane irin mahaukaci ne, inaga wallahi ka fara shaye-shaye, duba fa ka ga, ga takalmansu nan a bakin kofa” ya kasa furta komai, sai suka runtuma cikin dakin, nan wani kamshi har ba yadda zaka yi ka tantance daga ina ne ya ke fitowa ya kauri hancinsu, in da kamshin nasu jikin ya hadu da wanda suka tarar a dakin, sai ka ji wani kamshi mai dadi gaba daya ya kaure wurin, Yusuf ne ya soma, “wai ashe dama kuna jinmu kuka kyale, kuyi abinku iya yau ne jan ajin kuma dole ya kare a saukar da kai kasa” Amatu ta karbe “ko kusa ai mu namu ajin auto renewal yake da duk bayan second daya” ta kalli Aisha suka tafa. Nan Usman ya basu hakuri ya kuma sanar da su dalilin dadewarsu, bayan takaddama nan aka yi sayen baki da kyar kawayen amarya suka aminta suka wuce zuwa gidajensu, in da shi ma na shi abokanin suka bi ta bayansu domin su ajiye su gida. ya rage daga ango sai amaryarsa.

*KURUCI DANGIN HAUKA* ( _daren amarcin Nabila_)

 

💗 1⃣1⃣-1⃣5⃣ 💗

 

 

 

 

 

 

© *ZAINUDDEEN ZAIN*

 

 

 

 

® _PEN WRITERS ASSOCIATION_

 

 

✍🏾

 

 

 

 

_dedicated to Maman Ahmad_

 

 

 

08034840276

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Nan ya fita ya rufe kofofin shigowa gidan, sai ya dawo a dakin amaryarsa, cikin zumudi da shauki, ya fado dakin ba ko sallama, kai tsaye ya nufi kan gado, inda ya bar ta anan ya tara da ita, zaune a gefen gado lullube cikin jan mayafi inda ko fuskarta baka iya gani, kwalliyar hannunta ya fara kallo wacce ta yi kyawu sosai, ya matsa kusa da ita sai shakan kamshin turare yake yi wanda ya garwaye da kamshin nata jikin, sai ya ce da ita, “gimbiya sarautar mata, hasken ruhina rabin jikina, ai sai ki bude fuskarki ko na ji sanyi” kamar ba za ta motsa ba, kusan minti biyu, shi kuwa sai lallasarta yake yi, da kyar ta aminta ta bude fuskar, kanta a sunkuye, sai dakan uku uku gabanta ke yi, duk da da AC a dakin gumi ke kokarin karyomata a goshi da hamatanta, sai ya ce “yawwa! Ko ke fa, yanzu sai ki tashi mu je muyi alwala muyi sallah muyi addu’ah” ta tashi ba tareda ta ce da shi komai ba, shi kuwa sai kallonta yake yi, kallo kala biyu, na farko yana kallonta ne ta yadda ta sha kyau, duk da yasan kyakkyawa ce, yau dinnan kyawun ya kirashi na daban, domin har wani sabon sonta ya gayamin cewa sai ratsa shi yake yi. Na biyu yana kallonta ne na ta tashi zuwa alwala ba tareda tasan ina ne wurin alwalar ba, sai da ta isa bakin kofa sai ta ci birki, ta juyo taga idanuwansa kyam a kanta, idanuwansa ciki da shauki da kwadayi, ta sunkuyar da kanta da sauri tana so ta tambaye shi ina za su yti alwalar nauyi ya hana, da ya fahimci haka, sai sai ya fashe da dariya, ya ce da ita “ke da gidanki amma ba in da kika sani? Zo muje, ya shiga gaba, tana biyarsa, ya nunamata wuraren da suka fi muhimmanci, sai suka dawo dakin ya shiga da ita toilet, sukayi alwala suka fito, ya shige ta gaba ya ja su sallah, daga kammala sallar ya waigo ya kalleta cikin murmuhi, kallon da gaba daya sai da taji kamar ta fadi duk da a zaune take, ya ce “Nabila, inaso kisan cewa wannan sabuwar rayuwa ce muka shigo ba irin ta soyayya da muka fara ba, wannan rayuwa ce ta din-din-din rayuwar da za ta kai mu aljanna da yaradar Allah, amma hakan ba za ta yiwu ba dole sai mun baiwa juna hadin kai wurin kula dahakkokin da suka ratayu a kawunanmu, ina so mu gina rayuwar arenmu ta yadda zata amfanemu da ‘ya’yanmu har makota, saboda haka duk inda kika ga na yi ba daidai ba, sai ki kasance kamar uwa a gareni kimin fada har da jan kunne, abinda nake bukata a wurinki shi ne biyayya da tsare hakki, ni kuma insha Allah za ki sameni mai kokarin yi maki adalci. Nasan ki da rikon addini, ina so ki fi yadda na san ki, zan daukeki matsayin abokiya, ke kuwa inaso ki dinga kallona a matsayin shugaba gareki, insha Allah da haka zamanmu zai dore har karsshen rayuwarmu, inaso ki guje kawayen banza, haka duk abinda kike da rashin fahimta a kaina, ki tuntube ni, da ikon Allah ba zan maki karya ba zanmaki bayani…….”haka ya dinga yi mata nasiha har na wani lokaci, sai ya umaceta da su zauna kan gadon, zamansu ke da wuya, sai ya dora hannunsa a kanta da niyyar yayi addu’ar da manzon Allah ya karantar da mu duk lokacin da mukayi sabuwar amarya, ganin zai tabata ta buge hannunsa cikin zabura a lokaci daya kuma ta ja baya, cike da tsoro sai haki take kamar wacce ta share kilometer biyar tana rafkar gudun kwatar rai, cike da mamaki ya kalleta, kafin ya yi magana, ta ce “me ye wannan iskancin, dama ustazancin da kake nunawa lokacin da kake tahowa fira gidanmu na karya ne? da wanne dalili za ka tabani?” tana fada tana ja daga baya har ta kai karshen gadon, ganin haka sai yayi murmushi ya ce, “ni mijinki ne inada damar na taba ki, nayi duk yadda nakeso da kuma sarrafa duk inda nakeso na jikinki” “nikam a’a wallah”(sakkwatanci) “ba haka a ka koyar da ni ba, ka duba girman Allah ka mayar da ni gidanmu, wallahi zan yi maka kuwwa” “ban hanaki kiyi kuwwar ba duk wanda zai shigo, a gidana zai shigo kuma inada shaidar mallakarki a matsayin mata saboda haka banida haufi, bismillah Nabila, yiwa mijinki kuwwa” ya fada a fusace, ta mike tsaye ta nufi kofa cikin sauri, ganin za ta fita sai ya yai sauri ya riketa, nan ta fashe da kuka “wayyo Allah na na shiga uku, zai lalatamin rayuwa, haba Usman ashe dama da lalata ka auroni, ba zaman aure kake so muyi ba, so kake ka lalatamani rayuwa, wallahi sai Allah ya sakamani” “haba Nabila sai ka ce wata daga shekaru dubu da suka wuce? Zatona a wannan zamani ba za a taba samun mace mai irin wannan tunanin naki ba, mijnki fa ne ni, kina so ki gayamin cewa bakisan hakkokina da suke rataye a kanki ba” “sosai nasani mana, ance inmaka biyayya, inkula da kai sosai, amma ni ba wanda ya gayamin wannan da kake so kayi” “zo zauna ki ji” ya jawota ita kuwa taki, “wannan ma yana daga cikin hakkokina da suka rataya a kanki, kila a dunkule sukamaki bayani ko kuma ke ce baki fahimta ba, ki tuna fa ni masoyiki ne, ba yadda zan cutar da ke, ke da kanki kika ce ni ustazu ne lokacin da nake zowa fira gidanku, shi zai nunamaki tunda na nuna haka yanzu, kin halarta a gareni” “ni wallahi banyarda ba, kawai ka maidani gidanmu” “ai gidanku idan kika ga kin tafi sai dai ziyara ko idan wani abu ya taso, munanan tare” ta fashe da wani sabon kuka, a lokacin da ta ga ya cire babbar rigar da ke jikinsa ya kuma cire ‘yar ciki, daga shi sai singlet, da yake mutum ne mai fadadden kirji ga kuma kwarjini, nan hankalinta ya kara tashi, ta ji ina ma ita tsuntsuwa ce ta fira ta fice daga dakin, ya nufu inda ta ke a tsaye a bakin kofa, ganin haka ta sheka da gudu ya bi ta bayanta sai zagayar daki suke yi, idan ta gudu nan ya bita idan ta gudu cen ya bita, har daga karshe ya kamata, yace “wai wace irin wasa ce wannan? Ta isa mana” cikin kuka ta ce “wasa fa Usman wallahi da ka lalatani gara in rasa raina” zancen da ya bashi tsoro tareda tunzurar da shi kenan, cikin rufewar idanu ya fara cire kayan jikinta, kasancewar ya dorata ne kan gado ya hau ta kanta, ta yi amfani da damar hankalinsa na kan cire mata kayan jiki, ta cije masa hannu har sai da ta hadiye jinin kasancewar ya fito da yawa, ya rafka kuwwa ya saketa, ta dauko plate na glass da ya dora naman kazar da ya siyo musu ta maka masa a kai, jini ya fito, ya fadi sumamme, ta yi yunkurin ta fita a dakin, amma sai ta ji kofar a rufe, ta bincika a aljifansa ba makulli, ganin ya fara motsin farfadowa ta yi sauri ta shige a toilet ta rufe kanta. A gigice ya farka, gaba daya jini yayi masa kwalliya da ‘yar farar kykkyawar fuskarsa da kasumba ya cika ga wani dan buzu-buzun gemen da shima tuni jini ya jika shi, ya yi yunkurin ya mike tsaye, kasancewar jini ya fita da yawa a jikinsa sai ya kasa, nan ya samu ya ja jiki ya zauna ya jingina kansa da gado, sai haki yake. Nabila kuwa cike da tsoro ga ta cikin toilet ta rasa ya za ta yi, ita a cewarta tana kokarin kare mutuncinta ne kar mijinta ya ketamata budurci.

 

 

 

Name: [KYAWUNA JARABTA TA]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Leave a Comment

error: Content is protected !!